Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinga yarda namayar da daddynki to kema haka zansa fahid ya dinga yimiki sai yanda kikayi dashi dariyar mugunta suka saka gaba daya.......... Kwance take idanuwanta a rufe kai zakayi tunanin bacci take Amman ko kadan ba bacci take bah yau kwannata goma bata yi yunkurin zuwa ko nan d bakin kofa bah tun ranar da ta fita tadauko jakarta kullum sai sunyi waya d mommy bata taba fada mata halin d take a cikin gidan bahh haka mah kawunta umar shima sai yakirata kullum yanxu mah sun gama waya dashi neh takwanta mommy kuwa da sassafe take kiranta kuma da daddare mag takira ta agogon dakinne ya buga karfe biyu dai dak tashi tayi ashiga toilet tayi alwala tadawo tayi sallah abangaren fahid yau bazai je office bahh dan baya jin dadin jikinsa zazzabi yake dan dashi yatashi sai rawar sanyi yake kiran sallah azahar dinne dayaji yasa yatashi dakyar yayi sallah bayan ya idar yajewo alqur'ani yafara karantawa dan fahid badaga baya bah wajen riko da addini ajiye alkur'anin yayi a inda yake ajiyewa ya mike zai koma kan gadon jiri yadebeshi yazuba akasa wani irin kara yasaki mai karfi achan bangaren samira tana idar da sallah taji irin karar da yaya fahid din yayi kamar tashare sai kuma tayi saurin nufar kofa tabude data tuna nasihar mommy samira bai kamata dan mutum yana maka mugunta bah ko ya tsaneka kaga wani abu zai faru dashi kana d halin taimaka masa ka ki idan kataimaka masa wallahi ko agurin Allah kinfishi dan baka zama irin shi bahh wannan nasihar ita mommy take mata akullum dakin fahid din tashiga aganinshi tayi akwan karasa tai gurinshi tana kokarin daga shi
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban ✍🏼❤️
Page 26-27
Duk da irin tsananin tsanar da yayi mata yasan a yau dai babu mai taimakonsa sai ita dan da data fara kokari daga shi tureta zaiyi amman sai yaji bama zai iya bah da taimakonsa tasamu tadaga shi tamayar dashi kan gadon agarin kwantowa tayi kamar zata fada jikinshi sabida ya damki hijabin dake jikinta dayake samira maabociyar sanya hijabi ceh wannan shine tarbiyyar da mommy tayi mata dan bata cireshi sai dai idan zata kwanta karki ga wai kinyi min alfarma kin taimakeni kizata hakan zai sa indai na tsanarki to kisani yanxu akafara kuma wallahi sai na fitar dake daga cikin rayuwarmu gaba daya banxa yar gidan talakawa duk da irin yadda taji zafin kalamansa amman kuma da tatuno maganar mummy ay babynah dayake wata rana mommy hk take cewa yayannan naki zuciyar karfe gareshi ji dakansa yake tamkar wani sarki koda kuwa yanxu kayi masa abun taimako sai ya nuna ay bakayi wani bajinta bah duk dacewa a cikin xuciyarsa yana jin dadin taimakon dakayi masa murmushi tayi tace mummy kinyi gaskiya a tunaninta acikin zuciyarta tafada haka sai ji tayi yajanyo ta tafado kan gadon duk da irin rashin karfin dayake ji amman haka bai sa yaki nunawa samira karfinshi akanta bah yaya fahid yana d jiki amman ba sosai bah amman zaa iya sakashi asahun masu kiba gaba daya yahau kanta gaba daya yamatseta dan karamin bakinta yakama yasaka hannunta guda daya ya matse yahada hannayenta guri daya yana fitar dawani irin numfashi watau dan kinga nataimaka na aureki kika samu damar fada min magana har inyi magana kice wai mummy tayi gsky koh kuka samira kawai take dan ko numfashi bata iya fitarwa sai dakyar yahaye kanta gashi yamata matsar da ko motsi batayi bakinta kuma sai fitar da jini yake hannayenta duk sunyi rudu rudu dan bakaramar matsa yayi musu bah sun dauki kusan minti 40 ahaka amman bashi da niyyar dagata gashi yamatse mata baki bazata iya magana bahh bare tabashi hakuri shi kuma ganin kukan datake yasa yayi murmushi yana fadar cigaba d magana mana mara kunya gurin daya ajiye wukar yakalla hannun daya matse bakinta yasaka yadauko wukar gaban samira ne yafadi anan tasake fashewa da sabon kuka tana fadar dan allah yaya karka kasheni allah bazan kara cemaka komai bah kuma ba rashin kunya namaka bah kallonta yayi yace au ba rashin kunya kika min bah koh yafada yana saka wukar ajikin wuyanta dan allah yaya can sai kuma tatuno da irin yanda idan saudat taxo gidansu d shigar banxa yake rutse ido duk da cewa tana matukar tsoran yaya fahid din amman dole yau tayi abinda zai ceci ranta wukar ta kalla sai kuma tayi murmushi tafara magana haba yaya fahid wai ko kaji dadin kwantawa akan jikina ne idan kaji dadi ni ba bakuwar zafi bace kawai kacire hijabin ay abin sai yafi koh bah haka bah tafada tana kokarin saka bakinta cikin nasa dasauri ya mike cikin fushi yace mara kunya fitsararriya kawai xo kifitar min daga daki hijabin ta tacire tana daga kwance Dan yau kam sai ta kunna yaya fahid din zata tafi daga ita sai rigar bacci ko gwiwa bata karasa bah kuma duk shara shara ce tace ayni yau kam adakin mijina zan kwana zance infita mah bai taso bah kawai kahawo kan gado dan kasan yar talakawa pha baa barta abaya bah wajen nunawa miji soyayyah tashi tayi taxauna idan naga duk rabin nononta duk awaje suke ya rintse ido ko d taga haka tayi murmushi tace haka akeyi nifa matarka ce amman kake wani rintse ido ko bakai bane kake son kasheni bah zo mana yaya amman plx ina son ka kasheni ina kan cinyarka abin sai yafi bada kala kuma barin mah ina tsotsar lips dinka Dan allah samira kixo kifitar min adaki yau pha nagaya maka a dakinnan zan kwanta jiyayi yana kokarin faduwa tayi saurin karasowa ta tareshi baby kana lpy wata uwar harara yayi mata ita kuwa dan takara kular dashi tafara kokarin kwantar dakanshi akan kirjinta dasaurin yaja da baya itama tamatso tacewa wai menene ajikina kai kanka yau kasan ay ko ina nawa acike yake kare mun kallo daga sama har kasa plx ka kasheni mana yayana tafada tana kwantawa akan kirjinsa dan yakai karshen bango takalli wukar dake hannunsa tadora akan wuyanta sannan tafara kokarin saka lips dinta cikin nasa dasauri yakana hannunta ya tura ta waje sannan yasaka key a dakin murmushi tayi tace muxuba mugani wallahi nima duk abinda kake min sai narama dakinta tashiga tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga pink nd black falo tafito tana cewa aranta daga yau bazaman daki kallo ta kunna tanayi tayi kyau sosai dan ko hijabi bata saka bahh
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️
Page 28-29
Shi kuwa fahid tunda yatura samira yazauna akan gado yana tunani wai daman haka samira take shi dai yasan achan gida ko kadan bata taba mayar masa da magana bah sai dai mah jikinta da zaiyi tabari idan ta ganshi kai ko muryarsa taji hankalinta yatashi kenan kodan yanxu taga shi din mijinta neh shine zata fara raina sah ay kuwa wallahi baki isa bah samira anan take kuma yaji tsanarta na ratsashi ita har ta isa tanuna masa fitsara ji yayi alamun an kunna kallo ya leka window a zaune ya hangota tana kallo gaba daya hankalinta nakan t.v wani film din Hausa akeyi atashar arewa 24 koba kallo bah wallahi zanyi maganinki haka ya lallaba ya shiga wanka shadda yasaka kalar sararin samani yayi kyau sosai makullin motarsa yadauka yafito falo inda samira take kallonsa tayi suka hada ido tayi murmushi dan ganin yadda yahade fuska samira har yanxu tana jin matukar tsoran yaya fahid din kawai dai yanxu tana boye tsoronne acikin zuciyarta yanxu mah data ganshi sai d taji gabanta yafadi har yahuceta yaji muryarta tana cewa honey adawo lpy wani irin bakin cikin ne yaturnuke acikin xuciyarsa ay dole mah yasan matakin da zai dauka akan yarinyar nan tafiyarsa yayi batare d yace mata komai bah hmm ta sauke ajiyar xuciya sannan tamayar d idonta kan kallon datake yi axuciyarta tana ta tunanin irin abinda zata dinga yiwa yaya fahid din sanye take cikin wasu matsastsun riga d wando dan tunda tadawo daga America tadene saka atamfa kwata kwata atsakiyar wasu classmate dinta dasukayi karatu tare take su biyune kuma dukkansu mazane kallonta dayan yayi cikin wata kasalalliyar muryarsa yace saudat yanxu duk irin son danake miki amman kice wai wani dan uwanki kike so ki aura yafada yana kamo hannunta tare da janta jikinsa murmushi tayi tace baby ay kaima kasan son danake maka daban yake karka manta pha saboda kai har Paris naje dan dai nafaranta maka ran baby ay koda na auri fahid bamu rabu bah zan dinga kawo maka ziyara har Paris murmushi shima yayi yace ok babyna nasanki da cika alkawari har naji dadi usman idris shine sunansa haifaffan garin Paris neh mahaifinsa yana da kudi sosai dan sanaarsa shine ya saro gwala gwale ya dinga siyarwa sun hadu da saudat a america dan shima yaje karatu achan yarinyar tana burgeshi dan kodayaje ya mika tayin soyayyarsa bataki bah dan tana so tanunawa kowa a makaranta ita ba matar kananan mutane bace harsai datake saudat kullum a dakin usman take kwana kuma koda yagama karatunsa dayake yarigata farawa har chan Paris din tabishi tayi sati biyu agidansu dayake shima iyayensa yan bokone ko kadan basu damu bah kuma shi kadaine dansu Ok baby kinsan kwana biyu nayi missing dinki pha nima haka baby abokinsa yayi murmushi yace lovers tohm Asha soyayyah lpy yana fadar haka yatashi yakoma mota yana jiran abokinnasa a xuciyarsa kuma yana ganin haukan yarinyar da har take cewa ko tayi aure basu rabu bah bata san yaudarar usman baneh sukuwa saudat dakinta suka shige ita d usman wa'iyaxubillah sai d suka gama abinda zasuyi suka fito tare da usman din hannunta a sakale danashi Ahmad suka gani yana kokarin shiga dakinsa ya kallesu ya Manda kansa ya shige daki har mota taraka shi sannan takoma cikin gidan tunda yafito daga gidan tuki yake xuciyarsa cike da bakin ciki dakuma tsanar samira wai adawo lpy honey maganar data fada masa takarshe kafin ya fito daga gidan watau harta samu fuskar tace masa honey lallai gidan abokinsa hamza yanufa hamza abokinsa neh iyayensa basu da wani karfi yana d mata daya sai yaransa biyu mace d namiji khaleesat d Mahmoud yana zuwa hamza a yayi masa iso har xuwa falonsu dan daman anan suke zama idan yaxo matar hamza Aisha tafito rike d tire a hannunta na abinci mijinnata yatareta yakarbi tire din mataka su hamza suna birge fahid sosai irin yadda sukeyin soyayyarsu dakuma rayuwarsu abun shaawa aisha ce tace ahh babban yaya ina Amarya tamu tsiki yaja inda hamza yace ay idan kina so kiga bacin ransa kitambayeshi ina samira take ya dorawa yarinya mai hankali kiyayyah kuma idan an tambayeshi meyasa yake mata haka wa ya tsaneta ne kawai
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️
Page 30-31
Fahid yakalli abokinnasa yace wai kai wannan mara kunyar yarinyar kake cewa mai hankali sai kuma yaja tsaki da yatuno irin abinda tayi masa yau aisha tace kaga wannan maganar abarta dayake tasan irin tsanar da yakeyiwa samira aisha tana zuwa har gidansu fahid tagaishe da mommy kuma iyayen hamza dasu abba suma sun san juna sanadiyar abotar hamxa da fahid din hamxa mutum neh meh hankali gashi da riko d addini a asibitin da fahid din yake aiki anan shima yake yi tohm yanxu yaushe zaa kawo min kanwar tawa tawuni musha hira hmmm abinda fahid din ya iya cewa kenan hamxa ya zauna tare d dire tire din abincin agaban fahid yana cewa matar tashi wallahi myy idan baso kike yadena xuwa gidannan bah tohm saiki cigaba tohm nayi wannan mah ni na isa nasa babban yaya yadena xuwa tafadi haka tana mai shigewa dakinta ya jikinnaka ko dayake naga alamar kaji sauki tunda har ka iya fitowa ay ko banyi niyyar fitowa bah dole nafito wannan fitsararriyar yarinyar bazata barni in huta bah dariya hamxa yayi yana cewa tohm ay dole kila itama tafara gajiya da irin abinda kake mata dasauri ya mike afusace zaiyi waje hamxa yasha gabansa tohm daga magana allah yabaka hakuri abokina ay indai zaka cigaba dayi min maganar wannan yarinyar ina mai tabbatar maka bazan kara xuwa gidanka bah tohm nadena yahakuri koma muje muci abinci koma wa sukayi bai wani ci abincin sosai bah yatashi yace zai tafi aisha tafito sukayi sallama hamxa yaraka shi har bakin mota sannan yakoma gida gidan mommy yanufa yana shiga yatarar da mommy d abba afalon sai kuma yusuf dake kan cinyar mommy suna hira yagaishe da mommy da abba cikin girmamawa suna suka amsa fuskokinsu dauke da murmushi mommy tace dafatan duk kuna lpy lpy klau mommy tohm ya babyna yadanyi murmushin yake yace hmm mommy itama tana lpy tohm Masha Allah yusuf neh yaxo yazauna akan ciyarsa yana fadar yaya fahid zaka kaini gurin aunty samira yadan ja dan karamin tsaki a xuciyarsa yana cewa kowa samira kowa samira wannan yarinyar kodai mayyah ceh kuka yusuf yasa dan shi atunaninsa yayannasa bazai kaishi bah dasauri yace Ehmn autar mommy mai zai hana dariya yaron yayi tare da yin tsalle ya nufi gurin mai aikinsu yana cewa bari inje gurin inna tahada min kayana mommy takalli fahid sosai tace kodai baka jin dadine eh wllh mommy ina dan zazzabine ina umar wallahi umar yau kwanansa uku an nemaisu agurin aikinsa yatafi kaduna zaro ido fahid yayi yace amman shine bai gaya min bah ay fushi yake dakai shiyasa saboda acewarsa kana takurawa samira kuma amana ceh a hannunsa mommy tafada abba yadanyi murmushi tohm kasha magani eh abbah nasha agidan hamxa nabiya tachan sannan nayo nan tohm kaga wanchan dan rigimar yatafi kayi sauri katafi dan magriba takawo kai kafin yafito dariya yayi sannan yace mommy tohm natafi yana tashi yusuf yafito rike da kaya niki niki dan har inna ta tayashi daukar wasu dasauri fahid yakarasa yakarbi na hannun innah yana mata sannu xuyawa inna tayi tashige bangarensu na masu aiki fahid yace tohm mommy zan tafi dashi kawai dan idan nabarshi zai dameki da rigima babu yanda mommy ta iya haka suka tafi da fahid da yusuf amota aka saka kayansawar yusuf a cikin boot dan akwatine babbah sai kuma yar karamar jaka suna isa gidan yusuf yafita daga motar dagudu yanufi hanyar falo bubbuga kofar yake achan cikin dakinta taji alamar ana buga kofar tasan dai bah fahid bane dan inda shine yana d makullin falon sai dai yabude ya shigo fitowa tayi sanye da hijabi har kasa tanufi kofar tana budewa taga yusuf cike da jindadin ganin yaron ta tsugunna tayi hugging din yaro tare d sumbatarsa akuncinsa duka biyu duk abinda takewa yaron fahid na kallonsu dan ita sam bama ta kula dashi bah sai d ta dago suka hada ido karasawa tayi kusa dashi rike da hannun yusuf takarbi akwatin hannunsa afalon tacewa yusuf yazauna inda tashiga masa da kayansa dakinta shikuwa fahid dakinsa ya shiga alwala yayi yafito tare d yusuf suka tafi masallacin koda samira tafito taga basanan tasan sun tafi masallaci dan haka itama takoma tayi alwala ta Tatar da sallah saudat ceh zaune cikin dakinta son fahid kullum kara shiga zuciyarta yake gashi mommynta tayi mata alkawarin zata saka fahid ya aureta koda kuwa baya so gashi yanxu kusan sati uku kenan babu alamar Auty rahma ko kuma abbansu fahid tashi tayi ta shirya cikin wata shara sharar doguwar rigar kanta ko dankwali bata daura bah ga uban kitson atac har gadon baya takalmi tasaka mai tsini makullin motarta tadauka ko mommyn bata yiwa sallama bah motarta tashiga sai gidan yaya fahid din shikuwa fahid dakyar ya iya dawowa gidan sabida zazzabi a falo yazauna inda Yusuf a rude ya shiga dakin samira yana fadin aunty samira yayi zai mutu sai wani irin Abu yake da Jikinsa tare suka fito da samira zaunawa tayi kusa dashi tana yimasa sannu irin damkar dayayi mata yana ta surutai yasa tadan Kalli yusuf tace dauko min bargo a dakin dasauri ya shiga dakin ko minti 2baiyi bah yafito dauke da bargo yaron yakoma dakin samira yana shan kuka bargon ta lulluba masa amman ina babu alamar raina rawar sanyi jawosa tayi sosai jikinta tare da kankameshi filo yayi da kirjinta hannayenta duka biyu yasaka ya zayeta bai ahaka saudat ta shigo falon ko sallama babu dasauri taja da baya tare da saka kuka
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m sha'aban✍🏼❤️
Page 32-33
Dasauri samira takalli gurin dan saudat take a tsaye tana kuka abinda tafada mata ranar daurin aurenta neh yafado mata da yammah Ana shiriye shiryen kai Amarya daga ita sai fauziyyah a dakin dashiga tana tawani yauki ko sallama babu takalli samira dake kuka takwashe da dariya tana fadar ay duk wanda yace zaiyi auren cushe karshensa kenan kuka mah yanxu kika fara saboda yaya fahid mijina neh ni kadai shishshigi cusa kai babu kwarjini nasan cewa kawai zaki auresa neh amman bazai taba hada jikinsa da kazamar yarinyah irinki bah banxa tsintacciyar mage a dai dai nan kuma tunanin samiran yakatse ayau dole tanunawa saudat cewa ruwa ba sa'ar kwando baneh duk da cewa ita ko kadan bata jin son yaya fahid a zuciyarta kawai tana taimaka masa neh dan allah dakuma irin halaccin da mommy tayi mata hannunta tasaka acikin sumarsa wacce takwanta tayi luf akansa sai sheki take tana kallon saudat tana yi mata murmushi saudat shigo mana kiga yadda yaya fahid yake kwance a jikin kazamar yarinyah kinsan idan yana tare dani baya ji kuma baya gani sai kuma takalli fahid din dabaima san meke faru bah sai sambatu yake saboda zazzabin har yanxu ko sauka bai yi bah ita kuma saudat sai tazata ay irin tsantsar bukatar samira ceh tasashi hk ga kuma hannayensa data gani zagaye a bayan samira maganar da samira take fadawa fahid dinne yasata kidi mah babyna kaji dadin kwanciyarne ko kuma muje daga ciki nabaka zumata kawai kai yadaga mata dan baima san me take fada bahh fita saudat tayi dagudu motarta tashiga taja dagudu har tana kokarin banke mai gadin gidan tsaki samira tayi tare dacewa ay idan kinsan wata baki san wata bah da kin tsaya wallahi dasai namiki abinda har ki mutu baxaki manta bah doctor din gidansu ta kira yaduba fahid yabasa magunguna mahaukacin tuki take wanda koh gabanta bata iya gani watau daman yaya fahid yaudarar kowa yake dacewa ya tsani wannan yarinyar ashe karya yake yana tsananin sonta allah neh kawai yasa zata kai gida lpy kai tsaye dakinta tashiga dayake mommy tana sama tana bacci kan gadon dakinta tafada tare da fashewa da kuka mommy kuwa kwanan yusuf biyar agidansu samira ta turo daddy wanda bai dade da dawowa daga maiduguri bah dayake shi soja neh yaxo yatafi da yusuf yana kuka yana rike samira ahaka ta lallabasa dacewa zataxo dakanta ta dawo dashi bazai kara komawa bah jin haka yasa ya yarda shikuwa fahid yasamu sauki sosai dan har yakoma aikinsa a yaune yaya fahid yaci kudurin wallahi sai yafitar da samira daga rayuwarsa bama shiba har su mommy mah bazasu kara ganinta bahh saudat kuwa tun daga ranar dataje gidansu fahid kullum cikin kuka take tafadawa mommynta ta duk abinda yafaru d kuma irin yanayin dataga fahid din lokacin dasuke tare da samirar itama hankalinta yatashi tashiga rarrashin yar tata dayi mata alkawarin sai tafitar d samira daga rayuwar fahid tadaura dacewa ke kadai kika dace da fahid kuma kedai zaki zauna dashi zakiga yadda zan rabasu bazasu kara kasancewa tare da juna bahhh
❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️
Page 34-35
Yana tashi daga asibitin kai tsaye gida ya nufa lokaci karfe biyar dai dai na yammah hannunsa rike d wata hodar gusar d hankali yana shigowa bai tarar da ita a falo bah dan daman ba sosai take zaman falon bah jakarsa ya ajiye akan kujera ya shiga dakin samira bai taba shiga dakin bah sai yau.....yau dinmah mugun kudunrinsa akan samirar neh yasa ya shigo sanye take da katon hijabi a zaune kan gado dan lokacin tagama waya d mommy kenan kallonsa tayi cike d mamakin mai yakawosa bata ankara bah sai ji tayi ya watsa mata wani abu bata kuma kara sanin inda kanta yake bah shikuwa fahid bayan ya watsa mata hodar gusar d hankali yadauketa cak dan bata d wani nauyi kuma ba kiba gareta bahhh a mota yasaka ta inda yafiji motar dagudu....gudu kawai yake akan titi dasauri yake ya isa inda yakeson yaje karfe 7 nadare takawoshi garin kanoo awani daji dake cikin garin inda babu alamar wani biladama guri yasamu yayi fakin ya fito tare d bude mazaunin baya yafito d samira ya shimfideta a gurin yaja motarsa yayi gaba sai hanyar garin abuja baya tunanin irin halin d zata kasance kawai burinsa yaga yadena ganinta kwata kwata acikin rayuwarsa ita kuwa samira ba tafarka a wannan dajin bah sai wajen karfe 8:40 tayi matukar tsorata ganin inda take a hankali kuma ta tuno d abinda Yaya fahid ya watsa mata a fuska kuka tasaka duk a tsorace take kuka tasaka tana fadar wayyo Allah ni samira ina Yaya fahid yakawoni jitayi andosota d fitila anacewa yawwah ku tsaya gawata chan mah kafin tasan abinyi taga wani kato ya sarka mata wata ijiya ahannu sannan ya daka mata tsawa yana fadar tashi muje kina bata mana lokaci sai sannan takula dawasu yammata da aka daure hannayesu da wani dogon ice kuma aka sakawa kowaccensu akafadarta dakyar suke tafiya daga ganinsu kasan sun galabaita mikewa tayi dan bata da wata mafita igiyar d aka daure mata hannu aka saka aka daure d icennan wani irin nauyi taji dayasa tayi taga taga zata fadi taji an zabga mata wata murtukekiyar bulala wata iriyar kara tasaka Ina Wanda ya zabga mata bulalar yace auu kina wani kokarin faduwa idan kika sake kika bata min lokaci zan miki a zabar d sai kin roki mutuwarki dakan ki tafiya suke inda dukkannin karfin samira yakare bama ita kadai bah harda sauran wani daki aka shigar dasu dan karamine duk kura d datti fitowa sukayi suka kullesu acikin dakin samira tabi yammata da kallo tunanin Mai wadannan mugaye zasuyi musu takeyi dukkannin yammatan kana kallonsu kasan a tsorace suke abangaren fahid kuwa Yana zuwa garin abuja dan lokacin karfe 10:00 dai dai wanka yayi sannan ya kwanta zuciyarsa cike d farin cikin yau burinsa ya cika yafitar d samira daga rayuwarsa dariya takeyi sosai tana cewa gsky mommy wlh kina burgeni kina sona sosai yanxu kina nufin na kusa nazama matar Yaya fahid indai mukayi abinda boka yace tohm mommy dan naje nakwana dashi ay bawata matsala bace Kuma indai Samira zata fita daga cikin rayuwar fahid ay nasan zaki iya shiyasa banji wata damuwa bah dan idan mah kikayi karuwarki ce zan mah yi momcyyy I love uh mommy tafita inda ita Kuma tashiga wanka tashirya makullin motarta tadauka bayan tashiya cikin shigarta wacce bata dace bahhh gidan bokan tanufa xuciyarta cike d farin ciki
❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️
Page 36-37
Kwana sukayi babu wanda ya rintsa atsakaninsu ga sauro duk sau kurukuruwa yake musu a kunne sai yanxu ta kula da wata mai ciki dake cikinsu cike d tausayawa takarasa gurinta wani irin nishi take inda numfashinta yake fita sama sama ga cikinnata yakai lokacin haihuwa ko yau ko gobe anan take takara tabbatarwa d cewa wadannan mutanan gaskiya basu d imani kwata kwata su goma ne duk yammatane sai ita d take d cikin sannu samira tace mata dakyar ta iya amsa mata d yawwah daya daga cikin yammatance Samira taji tana cewa ruwa ruwa dasauri tajuya takalleta ay bama ita kadai bah dukkansu suna bukatar ruwa yar karamar kofar tanufa tana bubbugawa ko kadai bata damu d mai zai biyo baya bah wani mara imani neh yabude idanuwansa jajawur fuskarsa baka kirin kallon Samira yayi lokaci guda Kuma ya dauketa d mari yana fadar Kai Baki d hankali koh sarki barkodi Yana bacci zakixo kina bubbuga mana kofa naga alama kina bukatar mutuwarki yau dinnan ya mayar d kofar zai kulle tasaka hannu tare d tura kofar d karfinta taga taga yiyi yana kokarin faduwa inda kofar tabude

Please Login or Register in order to submit comment