Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba daya fitowa samira tayi tana huci nufarsa tayi itama ta zabga masa mari tana fadar kunxo kunsaka mu acikin dakin kuna tunanin bamu d gata neh koh mudin bayinku neh kai harka isa ka mareni tohm nayi hakuri a wanchan lokacin har nabari wani da namiji yamareni Amman yanxu wallahi baku isa bah babu wani da daya isa ya mareni in kyalesa na fuskanci ku maza baku d imani baku ba tausayi Kuma d kake cewa Wai mutuwata tana kirana a yau din karkafasa koka kasheni duk maganganun d samira take sarki barkodi yana jinta Dan magana take dakarfi Kuma cikin fushi muryar yarinyar tana yimasa dadi duk dacewa ransa abace yake dan bacci yake kuma a kaidarsa ko da ace daya daga cikin mutanansa neh yake bacci yaxo Yana masa magana Yana tashi kasheshi yake tashi yayi ya fito waje inda yake jin sautin muryar yarinyar natashi Samira kuwa cigaba da magana tayi Kuma duk acikin mutanan sarki barkodi babu Wanda ya iya kokarin dakatar d ita ganin yadda tayiwa yankan baya wanda duk cikinsu shine ogansu daga shi sai Kuma sarkin muna bukatar zamu sha ruwa ina buga kofa kawai kabude kamareni watau Kai bakasan darajar mace bah koh toh wallahi idan ka kara marina sai na maka abinda bazaka taba mantawa bah Kuma bazaka taba tunkarar wata mace bah d niyyar cutar da ita kubani ruwa wata murya taji abayanta ita kanta muryar idan kajita sai kaji gabanka yafadi duk dacewa ta tsorata Amman sai tadake ta juya wani katon mutum tagani idanuwansa duk sun firfito xubinsa kamar wani aljanin Dan ita tayi tunanin mah aljani neh rike yake d zabgegiyar wukarsa ahannunsa
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m sha'aban✍🏼❤️
Page 38-39
Sarki barkodi yakarewa samira kallo kasancewar lokacin gari ya waye karfe 7:00 na safe kyakkyawace duk dacewar tana sanye d hijabi amman daga ganin yarinyar zakasan bayan kyan fuska da take dashi harda kyan diri niyyar dayake dashi nacewa yana xuwa zai datsewa yarinyar kai saboda ta tasheshi daga bacci lokacin tashinsa baiyi bah tuni ya ajiyesa gefe dan tunda ake kawo masa mata bai taba ganin wacce take d kyan wannan yarinyar bah ita kuwa samira taji tsoronsa matuka amman d ta tuna alkawarin d tayiwa kanta cewar bazata kara jin tsoron wani da namiji bah KO d ace tana jin tsoronsa zata barshi iya kacin zuciyarta bazata taba barin yagane tana jin tsoronsa bah dan a chan baya taji tsoron yaya fahid tamkar wani mala'ika amman yanxu babu wanda ya isa taji tsoronsa dan ta fuskanci maxa basu d tausayi basu san darajar mace bah ko kadan kallonsa take ido cikin ido abinda babu wata yarinya data taba tsayawa a gabansa mah bare tayi masa kallo ido cikin ido muna bukatar ruwa zamu sha tafada tana kara kare masa kallo su kuwa mutanansa yana fitowa duk suka yi masa sujjada da kuma wasu matan d suke aikin daukar buhunhuna Wanda bata san komai nene acikinsa bah sanye suke da wasu kaya wanda zata iya cewa dasu gwara babu yayi mamakin yadda yarinyar bataji tsoronsa bah kuma batayi sujjada kamar yadda bayinsa sukayi masa bah yankan baya sarki barkodi yayi kiransa d kakkausar murya zuwa yayi ya durkusa masa har kasa dan shi yankan baya a tunaninsa sarkin zai ce aje arataye yarinyar bama shi kadai bah har sauran bayin amman sai sukaji akasin haka kaje kadebo mata ruwa wanda zai isheta kabata cikin saurin yankan baya yatashi ya debowa samira ruwa awani dan karamin kofi dan dokar gidan ce ko su mutanan sarkin basa shan ruwan dayafi kofin bayi kuwa sai su wuni basu sha ruwa bah idan zaa basu rabin kofin zaa bazasu sai kuma gobe kamar lokacin zaa kara basu kallo daya tayiwa kofin tace baa wannan kofin bah dan bani kadai zan sha bah kuma koni zan sha wannan yayi min kadan tsawa yankan baya yadaka mata yana shirin yin magana sarki barkodi ya dakatar dashi da cewa yankan baya yakira sunansa cikin daka masa tsawa samira taji tsoro matuka amman sai ta dake shikuwa yankan baya mamaki ya shiga yau sarki barkodi ne yake daka masa tsawa sabida wata yarinya kodan yaganta kyakkyawace jiyayi yana cewa kaje kadebo mata ruwa iya yanda take so idan bai isheta bama ka karo mata yana gama fadar haka yayi hanyar dakinsa sama neh dakinsa kuma kusan matattakala guda ashirinne amman kamar aljani haka ya haura dakinsa xuciyarsa cike d farin cikin jibi kamar haka yana tare d wannan yarinyar bama ita kadai bah har d sauran wadanda aka kamosu tare d ita samira kuwa tsaki tayi sannan takalli yankan baya tace kadebo min ruwa koh bakaji abinda wanchan shashashan yace maka bah xuwa yayi ya debo mata ruwa cikin guga tashiga takai musu kowannansu sai d ya isheshi sannan tamayar da gugar fahid kuwa kusan kullum sai yaje gidan mommy idan ta tambayeshi ya babyna sai yace tana nan lpy yaya umar yadawo daga maiduguri wata rana yaya fahid din yaxo gidan duk suna tare abbane kadai bayanan yayi tafi kasar Uganda ana ta hira sai daddy yace kai gsky nadade rabon d naga babyn mommy Yadai zanje yaganta yaya umar mah yace wallahi nima zanje naganta kwana biyu idan nakirata baba samu mommy tace ay fahid yace wayarta ta lalace shiyasa amman nima ina kewar babynah fahid kuwa da gabansa sai faduwa yake yace eh wllh wayarta ta lalace kuma yau bata gida taje gidan hamxa gurin aisha ok gsky gwanda ta dinga xuwa tunda kuna kusa mommy tafada tadan jinjina kai yana dan murmushin yake amman yakamata yau kahadani d ita gsky idan tadawo tohm mommy sai kuma yamike yana fadar mommy bari intafi tohm shikenan yafita daga gidan watau yafitar d ita daga rayuwarsa bai huta bah tana kokarin kara jawo masa matsala duk da bata nan yanxu idan mommy tagano basa tare da samira yazanyi yasan iya fushi zatayi matukar fushi amman yasan daga karshe dole tahakura tunda shine danta shine dolenta ita kuma babu abinda yahadasu da ita ko iyayenta basu sani bah dan haka bai wani takurawa kansa akan tunanin bah yawatsar dashi ya shiga yin harkokinsa shi kuwa yaya umar bai san meyasa bah yaji xuciyarsa taki yarda da maganar da yayannasa yayi bah wai samira ce zaa ce wayarta ta lalace meyasa lokaci guda yatashi yatafi yasan lallai akwai abinda yaya fahid din yake boyewa kodai yakashe samira neh dasauri yadauki makullin motarsa sannan takalli daddy yace xo karaka ni mommy ta tambayeshi ina zai je yace mommy zanje gidan ahmad neh ok tohm sai kun dawo daddy yatashi yabi bayan yaya umar din har sunyi nisa daddy yaga umar yahuce hanyar da zata kaisu gidan ahmad abokin umar din yace yaya ay mun huce hanyar gidan yaya ahmad din eh ba chan zamuje bah gidan yaya hamxa xamuje daddy ina tunanin akwai abinda yaya fahid yake boye mana shuru yayi sannan kuma ya nisa yace kana tunanin babyn mommy bata gidan aunty aisha kawai yaya fahid yafada neh eh daddy haka nake tunani kuma akwai dalilin dayasa nake tunanin haka suna isa gidan sukayi packing din motar suka fito yaro suka aika sukace yaje yayi musu sallama d mai gidan yace su umar d daddyne kannan fahid koda yaron yaje aisha tace bayanan amman yace su shigo shiga sukayi ita kadai suka gani dukkansu sai d gabansu ya fadi daddy yayi saurin kallon aisha yace aunty aisha ina samira samira kuma tafada cike d mamaki ay samira tun ranar d muka kaita gidanta rabon d kaganta daddy ya zube kasa yana sakin kuka shikenan yanxu maganarka yaya umar ta tabbata inajin yaya fahid ya kashe samira shima umar xubewa yayi akan kujera yana kuka aisha duk tabi d daga hankalinta tana cewa ku fahimtar dani bangane abinda kuke cewa bah nan umar ha zaiyane mata duk abinda yaya fahid din yace yau dakuma abinda yake cewa idan an tambayeshi Ina samira yadaura da cewa kila aunty aisha yakashe mana samira idan shi ya tsaneta ay mu muna santa yakarashe. maganar cikin kuka itama din kuka take tadauko wayarta tashiga kiran mijinta dan tasanar dashi abinda kefaruwa
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️
Page 40-41
Aisha tana gama fadawa mijinnata abinda su umar suka fada mata baa fi mint 10 bah sai gashi ya shigo gidan dayake bah wani nisa yayi bah daman hakuri yabasu umar shima hankalinsa yatashi yanxu kiyayyar da fahid yake mata takai ga haka toh ina fahid yakai samira kodai kamar yadda suke fadar kasheta yayi innalillahi wainna ilaihi raju'un yashiga maimaitawa haka su umar suka tashi har bakin mota hamxa yaraka su yana rokarsu karsu gayawa kowa wannan maganar har sai sunyi magana da fahid din kawai jinsa suke amman daddy ya kuduri niyyar a yau dinnan sai yafadawa mommy tayama yaya hamxa zai ce wai kar a bari kowa yasani chabb ay wannan abune mara yiyuwa shima umar abinda ke xuciyarsa kenan motar suka shiga dukkansu suna isa gidan daddy ya bar umar acikin motar yanufi falo ya kiran mommy fuskarsa duk hawaye sharkaf mommy tafito daga dakinta a dai dai lokacin kuma umar yashigo falon shima anan take daddy yashiga zai yane mata komai yadora da cewa mommy yaya fahid ya rabamu d babynki shikenan yakasheta hankalinsa ya kwanta mommy kuwa yanke jiki tayi tafadi dasauri dukkansu suka nufota bata numfashi kuka suka saka dan sun san irin shakuwar dake tsakaninmu mommy da samirar abisitin cikin gidan suka nufa d ita zaune suke acikin dakin wata baiwar sarki barkodi ta kawo musu abinci har ta tashi samira tayi saurin kiranta baiwar Allah dan allah tsaya juyowa tayi batare da tace komai bah tashi samirar tayi takarasa har inda take tace tambayarki zanyi ina fatan zan samu dukkan amsoshin tambayata eh insha Allah duk dacewar nasan tambayar taki bazata huce akan gidannan bah tohm bari in baki dan takaitaccen labarin gidannan..... Gidannan dai duk wanda ya shigo shi karma yayi tunanin zai fita a raye dan sai sarki barkodi yagama amfanin dazaiyi dakai sannan zai saka ayi bikin mutuwarkun dan yasan baku wani mamora nayi mamaki kwarai dagaske danaga kin tashi kina ta ihu wanda naga koda sarki yaxo bai yimiki komai bah kinsan idan aka tashi sarki barkodi daga bacci koda kuwa daya daga cikin mutanansa neh kawai katabbata lokacin mutuwarka yayi yanxu ku babu abinda zakuyi masa nadaga aikin wahala dan kune amarensa na jibi wanda kuma a jibi zaayi bikin mutuwarsu lantana sai kuma tafara kuka duk da cewa samira ta kidima da jin labarin gidan amman dataga tana kuka sai zuciyarta takarye wacece lantanar daya daga cikin yammatan ta tambaya yar uwata ceh tare aka kawomu kenan yanxu kina nifin idan ya kusancemu yaga bamu d mamora sai yasaka aka kashemu kuma yasaka akawo masa wasu matan takara tambayarta samira tajuyo ta kallesu tana cewa yan uwana yakamata muhada karfi da karfe domin mukubar dakanmu da kuma su lantanar koh ta halin yaya dole Mubarak gidannan hakane mun goyi bayanki Dari bisa Dari dukkansu suka fada baiwar sarkin ta kallesu tace taya kuke ganin zaku iya fita daga cikin gidannan bayan irin hatsarin dayake dashi yar uwa zamu fita daga cikinsa koma tayayane ko so kike yabata mana rayuwa kuma daga karshe yamana mutuwar wulakanci Aa bana so nima na goyi bayanki amman yanxu menene mafita numfasawa samira tayi tare da cewa akwai mafita amman duk yadda zaa daga yau xuwa gobe zamu bar gidannan gingina kai sukayi gaba daya mommy ce kwance likitoci sunfi goma ne akanta suna takokarin cero rayuwarta umar d daddy sai kuka suke
❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️
Page 42-43
Umar yakira daddy yafada masa abinda kefaruwa da Kuma halin da Mommy take ciki a yanxu hankalinsa yatashi Dan haka a ranar ya shiga shirye shiryen tawowa abuja duk da bai gama abinda yakaishi bah abangaren fahid kuwa abokinsa yakirasa har gida Yana xuwa yaganshi da Aisha fuskokinsu duk a murtuke zama yayi Yana tunanin Mai yasamesu ko mutuwa akayi musu neh kallonsu sukayi gaba daya sannan daga bisani hamxa yatashi yakarasa har inda fahid din yake tambayar data girgizashi Kuma baiyi tsammanin tambayar daga gurinsa bah Ina Samira take abokina wannan wace iriyar tambayace Samira tana gida Mana ok tashi ka kaini gurinta akwai abinda nakeso na tambayeta shuru yayi sannan yace bata gida gaskiya toh tana Ina hamxa yakara gefo masa tambayar bansan inda take bah nima kamar yah zakace baka San inda take bah bayan kuna gida numfasawa yayi batare da ya damu da abinda zai fadawa abokinnasa bah yace nafitar da ita daga cikin rayuwarmu gaba daya nan yafada masa yadda yadauketa ya jefar da ita a wani daji dake cikin garin kano wani irin mari yaji hamxan yayi masa hagu da dama ita kuwa Aisha mutuwar zaune tayi fahid yadago Yana kallon abokinnasa yace yau ni hamxa ka mara akan waccen bakauyiyar yarinyar ba laifinka bane laifina neh danaxo gidanka Yana fadar haka yatashi yafita shikuwa hamxa ko a jikinsa Dan yau din haushi abokinsa yakeji matuka Samira ce zaune kusa da wannan matar Mai ciki da bata san ko wacece ita bah ko Kuma ya sunanta aunty gashi muna tare daku Amman babu Wanda nasan Koda sunansune barantana ya akayi aka kawoku nan numfasawa tayi dakyar tace dafarko dai ni sunana suraiya muna zaune a cikin garin kano unguwar tofa ni din marainiyace iyayena sun Dade da mutuwa mijina Yana shi yadauki dawainiyata Amman tunda ya auro wata matar nazama bora acikin gidan Banda wani yanci ana haka sai matarsa tanuna bazata iya zama Dani bah shine yayi min korar kare nafito daga gidansa babu inda zanje shine nahadu da wadannan mutanan Banda wasu yaran wannan cikin shi kadai neh daya daga cikin yammatan itama tafara gabatar dakanta sunana bilkisu mahaifina alhaji Usman lale Dan garin Paris neh akwai yayannina biyu Yaya fauzan sai Kuma Yaya usman sai ni sai autarmu nafisa ana ce mata feenart naxo hutu anan Wanda duk shekara idan an bada hutu mukan tahowa tare dasu mommyna Amman yanxu nikadai nataho su su mommynah sai karshen shekarar nan zasu xo a gidan kanwar daddyna nasauka aunty asabe Ashe aunty asabe sun hada Baki da wadannan mutanan akan zata badani zasu bata wasu kudadai masu tsoka wannan shine dalilin zuwana nan sauran yammatan suma suka gabatar dakansu itama Samira ta gabatar musu dakanta Amman kawai tace musu ita marainiyace itama kuma wani kanin babanta neh ya wurgar d ita a dajin Dan bata son kowa yasan irin rayuwar data Dan Dana tabakin ciki tana so ta fara sabuwar rayuwa ta manta da wadda tayi a baya bayan tagama Basu tace tohm yanxu dai dole mufara shirin guduwa daga gidannan tunda kunga gobe zaa kashe su lantana idan bamu gudu yau bah tohm shikenan rayuwarmu zata tagaiyara hakane bilkisu tafada chan Kuma Samira tahango wani window dake chan saman daki tayi murmushi tare dacewa nasamo mafita dasauri suraiya tace mecece mafitar ta window zamu fita tafada tare d nuna musu window dake saman dakin cikin saurin suraiya takara cewa Samira bayan takalli window tohm yanxu tafiya zakuyi kubarni tunda nasan ni bazan fita daga cikin window nan bah murmushi Samira tayi aa ay muma bazamu iya fita daga cikinsa bah tunda Dan karamine wani karfe takalla tare d nunasa tana cigaba dacewa Amman da wanchan karfen zamuyi amfani mubude window sosai tayadda zaki iya fita muma zamu iya murmushi suraiya tayi tana kara jin son Samira nakar shiga ranta haka suka bude window nan sosai sannan bayan baiwar sarki tashiga Samira tace Ina su lantana gasu nan sai da nabari duk nasa musu maganin bacci sun fara gyangyadi na fito dasu duk ta window suka fita ita kuwa suraiya da taimakon Samira tafita daga cikin window gudu suke daga ita sai suraiya Dan su bilkisu sun Kama gabansu durkushewa suraiya tayi Dan nakuda ce takamata Samira ta tsaya tana tambayarta meyafaru tace Samira inaji nakudace kawai ki tafi karsuxo su kasheki aa suraiya bazan taba barinki cikin wannan halin bah anan take Samira tafara taimakon suraiya Dan Daman wata kawarta zara tafada mata yadda ake karbar haihuwa suraiya tana haihuwa Samira takalli rezar dasu taho da ita sabuwa ce Dan haka ta yankewa jaririyar cibiya Samira ki kula min da yarinyata Dan nasan kekadai ce zaki iya kula da ita Kuma Ina rokonki Koda ce babanta yaxo ko danginsa karki Basu yarinyar nan ki dauketa tamkar yarki Danni nasan bazan rayu bah tana gama fadar haka tafara kalmar shada Samira sai kuka take tana fadar bazaki mutu bah suraiya Amman Ina suraiya tariga takoma ga mahaliccinta😢
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️
Page 44-45
Kuka sosai samira take rike d jaririyar a hannunta tana fadar suraiya karki tafi kibarnzi plx bansan inda zan saka raina bah jitayi an doso inda suke babu shakka tasan yaran sarki barkodi ne dan haka ta tashi rike da jaririyar a hannunta tafara tafi tana wai jen suraiya sai da tayi nisa sosai sannans u yankan baya suka iso inda suraiya ta don lokacin har maganin baccin yasakesu sarki barkodi yace suje su nemo duk inda suka shiga idan kuma basu dawo dasu bah suka sake suka dawo sai ya kashesu koda sukaga gawar suraiya haka suka kacaccalata yankan baya yakalli mikakkiyar hanya tare dacewa wannan matar sai da ta haihu sannan ta mutu kuma bamuga alamar jariri ina da tabbacin basuyi nisa bahh kuma dole murarrabu wasu subi wannan mikakkiyar hanya wasu bi hagu sai kuma wasu subi dama haka suka rabu yankan baya da wasu mutane hudu suka bi mikakkiyar hanya wadda itace samira tabi wani gida tagani dan akwai bukatar ace ta gyara yarinyar sai tacigaba d tafiya da sallama tashiga gidan wata matashiyar budurwa taga akan kujerar karfe tana tsifa ta amsa mata tare d binta ba kallo mahaifiyar yarinyar ceh tafito daga dakinta bayan samira tagaisheta tacewa matar Dan allah mamah taimako nake nema so nake nagyara yarinyata inna takalleta sosai sam yarinyar batayi kama da mara gaskiya bah kuma d alama yarinyarta ce tunda ga jini nan duk yabata mata kaya inna takarbi jaririyar tayi mata wanka kayan yarinyarta dabata huce shekara daya bah tasakawa jiririyar innah tace kema yakamata kiyi wanka ko kya samu karfin jikinki samira bata musa bah dan Daman taga duk kayanta yabaci kuma gashi zata dinga yin sallah bayan tafito daga wanka budurwar nan tabata kayanta d hijabinta ta goya jaririyar nan sannan tayi musu godia sannan tanufi hanyar waje su yankan baya tahango su tsaya a dai dai gidan sai da ta tabbatar sun bar gidan tafito batare d tasan ina zata bah abbane zaune akan gadon da aka kwantar d mommy yau kwanan mommy biyu bata farfado daga doguwar sumar d tayi bah a yau neh akesa ran zata farfado dakin yacika da mutane har saudat da aunty dakuma su ahmad suna cikin dakin duk da cewa saudat d mahaifiyarta murna sukayi jin baa san inda yarinyar nan take bah sadia tace ita kuma rahma da take wani suma tama tashi dan bikinku d fahid babu tashi dan dai kawai yar uwa tace da sai nace ay gwara tamutu mah gaskiya mom aykin bokannan yayi sosai a kwana uku pha duk abinda mukeso yafaru duk wannan hirar dasuke ahmad najinsu dan lokacin yana tukosu zai kawosu gidan mommyn a xuciyarsa yana jin bakin cikin cewar wai mahaifiyarsa dakuma yayarsa neh suke shirya wannan makircin kuma suke yiwa aunty rahma fatan mutuwa ina mah ace wannan bah mahaifiyarsa bace aunty binta ce tashigo dan xuwanta kenan kallo daya tayiwa hajiya sadia d saudat ta watsar tare d jan wani tsani dan kwata kwata basa jitu dasu ko kadan duk da cewar mommy taji haushin abinda aunty binta tayi musu amman babu yadda ta iya dole tabarta amman taci alwashin sai takoya mata hankali ita kuwa saudat harararta tayi amman lokacin aunty binta tajuya baya dan haka bata kula bahh da bazasu wanye ta dadi bahhhh
❤️❤️KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah m shaaban✍🏼❤️
Page 46-47
Fahid ne zaune akan daya daga cikin kujerun dake zagaye a tafkeken falon duk garin yayi masa zafi tun lokacin dayaji rashin lpyr mahaifiyarsa mommy yusuf neh yakirashi yake fada masa tun ranar da su yaya umar d yaya daddy suka fada mata wata magana tafadi a bangare guda kuma yana tuna maganar d abba yafada masa bayan yakirashi sun gaisa yace wallahi fahid kabani mamaki wannan ba irin tarbiyyar damuka baka bane bamu koya maka cutar da wani bah barantana samira d take tamkar yar uwarka abokinka hamxa yafada min cewar kaje kayarda ita a wani daji a garin kano toh hakan yayi maka kyau yanxu duk irin nasihar da nazaunar dakai nayi maka ashe bakaji bahh ace kaine babbah kuma kaine mai irin wannan dabi'ar tohm yanxu idan su umar sukayi bazan taba ganin laifinsu bahh numfasawa yayi yana fadar yanxu yarinyar nan nafitar d ita daga rayuwarmu ashe wata babbar matsalar na ballowa kaina Allah sarki momcy bazan iya xuwa gareki bah har sai kin wuce sannan abokinsa hamxa neh yafado masa a rai wanda tunda yaje gidansa sukayi baran baran bai kara bari sun hadu bah ko da kuwa a asibiti tsaki yaja daya tuna irin wulakancin da yayi masa akan wannan yarinyar bedroom dinsa yashiga ya kwanta mommy bata farka bah sai karfe 10pm nadare babu mutane da yawa a cikin dakin aunty sadia d saudat sun tafi dan daman ba xuwan allah d annabi baneh Ahmad ne sai umar da daddy da yusuf sai abbah dake kan gadon sai kuma aunty binta da taimakon abbah ta tashi zaune kuka ta fara sosai tana fadar yanxu Daddyn yara abinda wannan yaron yayi adalcine yarinyar nan fah marainiyace bata da kowa sai mu amman yayi mata wannan wulakanci kiyi hakuri rahma ki kwantar d hankalinki zamu shawo kan matsalar taya zan iya kwantar da hankalina bayan bamu san wane irin hali samira take bahh ya kasheta koh ina yakaita babu wanda yasani zamuyi magana idan muka koma gida yanxu fatanmu ki kwantar da hankalinki ki samu sauki dan komai yaxo mana dasauki shuru kawai tayi aunty binta tace sannu aunty rahma kai kawai ta gyada mata Ahmad kuwa a gidan ya kwana dan daman bayason zaman gidansu tafiya take duk tagama jigata rabon da ta saka abinci a cikinta harta manta ga jaririyar sai kuka take alamar tana son bukatar abinci tsayawa tayi kusa dawani babban shago hawaye zai gangarowa suke daga kan kuncinta mai shagone ya kula da ita yaga tana bukatar taimako dan haka yakirata tana xuwa yake tambayarta Meya faru nan take fada masa cewa dan allah ya taimaka mata d abinda koh jaririyar nan neh nabata toh babu damuwa zan taimaka miki kunce jaririyar tayi bayan yamiko mata wata fida da akasa madara d ruwan dumi aciki tasha sosai sannan bacci yakwasheta maida ita tayi tagoyata sannan takalli mai shagon tace ngde babu komai kawai ina son kiyi min addu'a neh dan a halin yanxu ita nake bukata sannan ya miko mata wani drink mai kauri yace kema gashi tohm ngde yadda kataimakeni allah ya taimakeka kaima amin daga haka tajuya ta cigaba d tafiya
❤️❤️ KADDARATA😔✍🏼
Story and written by Nanah M Sha'aban✍🏼❤️
Page 48-49
Mommy ceh zaune akan gado yau kwananta biyar da aka sallamota daga asibiti abbaneh akusa da ita ta kalleshi sannan tace daddyn yara dole muhada auren fahid d saudat tunda ya riga da ya jefar min da yarinyata bansan inda yakaita bah bansan a wane hali take ciki bah a dah naki aurensa da saudat saboda halayen saudat sam bata dace ace itace zata zama sirikarmu bahh Amman yanxu dole ya aureta ko Yana so ko baya so tunda Daman Ni nace ban yarda bah toh yanxu na yarda Abba baice komai bah Dan yasan duk cikin bacin rai take maganar Kuma yasan yadda take tsananin son samirar saboda bata da yarinya mace ita Kuma tana son yarinya mace tashi yayi yace toh ay duk abinda kika yanke banda tacewa Ni zan fita tayi masa adawo lpy sannan takira daddy a waya tace yakira fahid yace tana son ganinsa yace tohm baa fi mint

Please Login or Register in order to submit comment