Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kidnapping dinsa🥺 ita kuwa fadeelarh da zata nuna musu taurin Kai Amman da taga tana Shan wahala tafada musu komai da Kuma inda zasuje su Sami usman din............Yan sanda sunje har dajin gurin data kwatanta musu Amman Basu tarar da kowa bah dan haka suka kara xuwa gurinta lokacin su mommy duk sunxo harda samira da saudat dasu yaya daddy aka fito da fadeelarh wacce tayi wujiga wujiga saboda wahala.....da aka fada mata cewar anje Amman baa kowa bah ta fashe da kuka tare da cewa wlh nasan yaji labarin ankamani Kuma zan iya tona Masa asiri....wata iriyar tsawa d.p.o ya daka mata saudat tace masa Dana Allah yallabai kayi hakuri kadaina yi mata irin haka....ta zagayo ta zauna inda fadeelan take durkushe tace Yaya fadeelarh koh....kallonta fadilan tayi ta gyada mata Kai alamar eh.....saudat takama hannayenta tare da cigaba da magana ynx kinfi so a dinga yi miki ixaya ta yau daban ta gobe mah daban Mai yasa bazaki hutar dakanki bah ki taimakawa Yan sanda akama wannan azzalumin.......wlh Yar uwa inda na kwatanta musu anan yake bah karya nake bah...tohm na yarda ynx a Ina kike tunanin zaa iya samunsa.... fadeelarh tadan yi dan gajeran tunani kafin tace ywwah zaa iya samunsa a club din delsa dake anan Abuja indai ba'a samai sah bah tohm Yana guess house din Abbansa dake garin kanoo G.R.A gida mai number 100 guri biyun nan ina tunanin zaa sameshi dan baisan nasani bah......d.p.o yayi murmushi tare da cewa good Amaryarmu aikinki yayi kyau Faisal shima ya murmusa Yana fadar gsky mommyn baby kina da matukar basirar tambayar mutane cikin nutsuwa😊Anan take d.p.o yabaza Yan sanda masu fararan Kaya suje su nemo usman a delsa club yakira wani Amininsa a garin kano shima d.p.o neh da yake yasan case din shima yabaza Masa Yan sanda suka nufi G.R.A saudat ta tashi zata tafi fadeelarh ta tsugunna tare da rike mata hijabi tana fadar Dan Allah ki taimakeni ki fitar dani daga nan wlh nayi nadama Kuma bah laifinah bai neh KADDARATA tace Kuma mahaifina shine yaja min saboda san kudinsa Amman wlh bahaka nake bah idan banyi abinda usman yace min bah zai kasheni Kuma mahaifina zai tsine min bani da zabiii takarasa magana tana kuka mai tsima xuciya dukansu tabasu tausayi Yaya umar kuwa kuka yake yi sosai na tausayi er karamar yarinyar data sah kanta cikin wannan mummunar harka Amman tunda yaji tace mahaifinta shine silar shigarta cikin wannan mummunar harka sai ya shiga mamaki..........Zama saudat tayi tare da cewa Aunty fadila bah fahimta bah Kamar yah kina nufin mahaifinki shine sanadiyarki shiga wannan harkar taya mahaifi zaisa yarsa ta cikinsa yabata mata rayuwa........hmmmm Yar uwa ni kwata kwata baiyi sa'ar mahaifi bah....wlh wlh da ace zaa bani dama ni da kaina zan kashe babanah Amman duk da haka ban makara bah bazan kasheshi bah Amman insha Allah sai Allah ya wulakantashi anan duniya da Kuma ranar tashi Alkima........da ace Allah Yana bawa 'ya'ya damar su zabarwa mahaifinsu makomarsa wlh ni wuta zan zabarwa babah Kuma sai na tabbatar wutar da zan zabar masa tafi kowacce azaba dukkansu Suka zaro ido😳 Dan saudat har firgita tayi Samira kuwa kafafuwanta kasa daukarta sukayi duk zaka zagayo Suka zauna Dan sunga abin bana tsayuwa baneh😤😯


💔💧 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾💔
Page 160-161
Mommy ta dafa fadeelarh tare da cewa kai kuwa yarta mai yasa kike fadar irin wadannan maganganun akan mahaifinki........takalli mommy kawai tare da girgixa kai aunty shi yaja min duk irin halin dana tsinci kaina ynx saboda son xuciyarsa da kuma kudi bai damu da irin halin da zan tsinci kaina bah burinshi dai kawai kudi...kudi..kudi yafi yarsa kudi yafini mahaimanci a gurinsa takarasa maganar tana kuka😭😭😭
Yaya umar yace duk da haka fadeelarh bai kamata kifadi wannan mugayen kalaman bah ae hannunka baya taba rubewa kayanke kayar......ta dago dasauri tare da yin murmushi takaici hawaye shabeshabe a fuskanta tace Yaya waya gaya maka sai dai idan bai damaika bah Amman lokacin da zagaje asibiti ae yanke maka karabu da kaya bazaka sani bah....Kuma wlh wlh ni nayanke nayar Kuma har abada bazan kara kiranshi da mahaifina bah dan na tsaneshi duk duniya mutane biyun nan nayi matukar tsanarsu usman da kuma Ayuba😒kallonta yayi sosai sannan yace fadeelarh koh zan iya jin labarinki domin har nakagu inji mai mahaifinki yayi miki haka kikayi masa wannan tsanar..........hawaye na zuba daga idonta tace labarinah babu abinda zakaji a cikinsa sai bakin ciki da takaici game da son xuciya.....tafara da cewar da farko dai sunana fadeelarh Ayuba garba muna zaune da kishiyar mahaifiyata da Kuma mahaifina a garin sokoto mahaifiyata ta mutu ranar da tahaifeni a hannun Addah mariii na taso watau kishiyar mamah tunda na taso Addah Bata taba nuna min irin bakin hali bah koh ta nuna tafison yaranta akaina hasalima tafisona akan yaranta Dan komai tasamu ni take Fara bawa sannan tabawa yaranta ragowa....shi kuwa mahaifina yakasance mutum neh Mai tsananin son abin duniya bashi da wani buri irin yaga yayi kudi koh ta wacce hanyaceh.....ni kadai ceh yarsa mace Dan yaran adda duk maza neh sani,bukar da kuma auta khabir Dan haka ya dauki dogon buri ya daura akaina bama ni kadai bah harsu khabir mah a cewarsa ae mune kadararsa da mu zai nemi kudinsa a lokacin nazata kawai wasa neh irin nasa dan nasha jiii ana cewa duk mahaifi bazai so ace yasa yaransa cikin wani hali bah dan har nake bawa kawayena labari sai muyi ta dariya suce kawai fada yake taya zamu zama kadararsa sai kace wasu gidaje....haka dai zamuyi tayi hirar muna dariya dan har suke tsokanata suce kadarar babanta duk sanda suka fadi haka sai dai nayi dariya....... Ranar da bazan taba mantawa bah..ranar danaje na duba neco dinta Naga na ci 6 credit na shigo gida da gudu Ina murna na fada jikin adda nake fada mata na duba exam dina na cinye duka....itama taji matukar dadi burinki ya kusan cika kenan nazama cikakkiyar doctor sai samin aiki dariya nayi nace adda ae sai naje school of health sannan zan sami gurbin zama cikakkiyar doctor tace Awww ynx bayan wannan makarantar akwai wacce zaki kara yiii kenan nace mata ehmn ae dasaura.......shigowar babah neh yasa muka katse hirar nayi masa sannu da zuwa na tashi zan shiga daki yakira sunana fadeelarhtou dawo ki xauna ae yau dawowar taki ceh nayi mamaki sosai dajin abinda yace dan haka nadawo nazauna ina Jin naji Mai zai ceh.......
Anan zan dakata sai Kuma gobe idan Allah yakaimu👏🥰💔
Nice taku a kullum a koda yaushe Naanah Sha'aban💔✍🏾

💚💧 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾😁💔
Page 162-163
Baba ya kalleni sosai dan gaba daya na tattara nutsuwata da hankalina wajenshi domin jin mai yafaru dan nasan babah baya dawowa gida da ranar sai dai idan akwai abinda ya manta ko Kuma muhimmiyar maganar da zai fadawa Addah Amman yau da dawo Kuma yace saboda nii shiyasa na kagu inji mai zai fada.......
Gyaran murya yayi tare da cewa fadeelarhtou sai ki fara shirya kayanki da duk abinda zaki bukata domin anjima da daddare uban gidanki zaixo ku tafiyyy......dasauri na dago cike da rashin fahimtar mai baban yake nufiii......na bude Baki zanyi magana Addah ta rigani da cewar malam bangane uban gida bah dan Allah fahimtar damu Dan kasamu a duhu.... murmushi yayi😊 yace ae Daman nasha fada muku yarana gaba daya kadarata neh Dan haka na siyar da fadeelarhtou gurin wani yaron kirki Kuma wlh ya siyeta da daraja naira million 10 zabura nayi jin abinda baban yaceh Ina jaa da baya Ina maimaita innalillahi wainna ilaihi rajun....babah karka min haka wlh duk abinda kk so indai nayi karatu nasamu aiki zanyi maka wlh inmah dukka albashina kace nabaka zan baka......hmm fadeelarhtou kenan ae kawai ki rike wannan burinnaki lokacin idan na mutu pha ae gwanda ynx nasan inda na dosa so kike kiyi min bakin ciki tohm wlh Baki isa bah....gashi Dan albarkan yaronnan yace duk wata bayan wannan million 10 zan dinga bani million 1 mai na manta....ban iya cewa komai bah saboda wani irin kuka da nake Mai cike da bakin ciki na durkushe a kasa ina cigaba da yin kukana....tashi yayi zai fita Addah da bakin ciki yahanata magana kawai hawayene yake xuba daga idonta ta dakatar dashi da kiran sunansa....juyowa yayi tare da yi mata wani irin malalacin kallo Yana fadar Baki da hurumin da zakiyi magana domin idan kin manta bari in tuna Miki fadeelarh bake kika haifeta bah dan haka ki adana kalamanki Yana gama fadar haka ya juya yafita kamar kububuwa...,..rumgumeni Addah taxo tayi itama tana kuka tarasa mah ta inda zata fara rarrashina........wajen karfe 9pm sai ga babah sun shigo tare da wani muna zaune a gurin da yabarmu Ina cigaba da aikin kukana na kwantar da kaina akan cinyar Addah Dan har wani irin matsanancin ciwon Kai naji na rabin kai😣
Ywwah gata nan alhajii keh fadeelarh kin gama hada kayannaki...banza nayi dashi dan a lokacin nayi masa wata iriyar tsana dan koh ganinshi bana son yiiii......Jin mutumin da yakirawo Alhaji nayi Yana cewa ae babah bana bukar ta tafiyy da komai ita kadai kawai nake Soo......Ahh tohm ae shikenan faduwa taxo dai dai da Zama sai in siyar da kayannata ayi cefa nan gida.......ban ankara bah naji an rike min hannu dasauri na tashi Ina wani irin nishi Kamar wata zakanya na fisge hannunah cikin tsiwa nake ce masa karka Kara rike min hannu Dan wlh zan iya kasheka😡wani irin kallo yake min nakasan ido Yana sakin murmushi tohm shikenan fadeelarhtarh tashi mu tafiyy....bah inda zanje domin baka da hurumin da zaka daukeni Dan bah baiwarka baceh......wata iriyar dariya Suka saki shida babah Addah Kuma tashi tayi ta shige dakinta tana kuka.....hannunah yakama Yana jana Ina tirjewa har muka fita daga gidan ya turani cikin mota ya rufe sannan ya shiga yaja motar mun dade muna tafiyy sannan Naga ya tsaya a wani hotel🏨ya fita ya shiga cikin hotel din inda ni Dana ga yafita na shiga kokarin bude murfin motar domin in gudu Amman inaaa ya kulleni ta waje ya dade a cikin hotel din inda yafito ya shiga motar ya jaaa fedeelarh kenan da zakiyi hakuri kidena kukannan da yafiye miki dan kuwa na riga da na siyeki Kuma mahaifinki neh yaxo har inda nake yayi min tallarki.....Kuma ni nagani na yaba yafada Yana kallona ta mudubin motar dake rataye a jikin motar.......ban iya cewa komai bah sai shashshekar kukana da yake tashi a cikin motar a wani dagiii naga yayi parking yafita da tare da zagayowa nima ya bude min kofar......nayi Kamar mah bansan Yana yin bah dan nayi matukar tsanarsu☹️ ganin banda niyyar fitowa yace wai keh Baki da tarbiyyah neh Baki San girmama nagaba dake bah koh??? Dagowa nayi dasauri tare da jan tsaki yayi matukar kaiwa bango da abinda nayi masa Dan har a fuskarsa sai daya nunah ya fisgoni daga cikin motar har Ina bigewa wata bishiya aikuwa sai ga jini ya wanke min fuska kaina yayi wani irin sarawa na xuba a gurin ban Kara sani halin da nake ciki bah sai farkawa nayi naganni a wani daki duk jikina yayi min nauyi koh motsin kirki bana iyawa......

Ku dakaceni sai Kuma gobe nice dai taku a kullum akoda yaushe Naanah Sha'aban🥰✍🏾

💜💧 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾💜
Page 164-165
Abinda yafaru neh yashiga dawo min kuka nasaka Ina rokon Allah yasa dai babu abinda wannan Dan iskan yayi min motsin kofa naji alamar zaa budeta na kafe kofar da ido ina jiran Naga waye zai shigo......wannan dai mutumin neh na daxu kallonah yayi tare da shekewa da wata iriyar dariya har Yana tintsirawa🤣🤣
Hmmm fadeelarh koh...har kin gaji kin tashi kenan🙃kallonsa kawai nake daga kwance idanuwana na zubar da hawaye natashi dakyar duk jikina yana min wani irin xugi Mai kayi min.......wani irin kallo yayi min irin na cikakkun Yan bariki yace Awww tambayata kike ance miki ni irin mazannan neh marasa tunani in ajiye budurwa kamarki har tsawan kwana uku ace ban jiii dadinah bah........duk da irin kukan da nake sai da na firgita kenan shikenan yarabani da komai nawa.....cikin wani irin zafin rai na tashi a wahale na shiga buga Masa duk abinda na daukooo Ina fadar mugu azzalumin Allah ya isa tsakanina dakai fita yayi dagudu tare da rufe kofar....Amman duk da haka ban mah san yafita bah duk bayan kwalbah sai da na fasa na hargitsa dakiii nadawo Kamar wata mahaukaciii.....
A daidai anan fadeelarh ta tsaya tana cigaba da kukan idanuwanta nakan Yaya umar tace Yaayah kasan koh anan na tsaya wlh kasan mahaifina yayi min abinda bazan taba mantawa bah har nakoma ga Allah Dan Mai zan kii tsanarsa Dan Mai bazan yi Masa addu'ar Allah ya tozartashi bahh ya wulakanta.......mommy ceh ta toshe mata baki wacce ta girgiza da jin labrin fadeelarh Kuma tayi matukar tausaya mata sosai🥰🥀
Kiyi shuru kidaina fadar irin wadannan abun akan babanki ae komai yayi miki mahaifinki ae bazaki taba chanxashii bah Kuma insha Allah zamu fitar dake daga cikin halin da kike ciki Amman kemah sai kin taimaka mana ankama wannan azzalumin......insha Allah zan taimaka tayi maganar tana mai xubar da hawayeeee.....kiyi hkr kinji kanwata insha Allah indai ina raye bazan kara barinki kisha wahala bah karshen wahalarki taxo bijahi rasulullahi🙏💔Yaya umar yafada tare da Bata wani farin hankey takarba ta goge hawayenta tare da yi masa murmushi😊sun dade suna bata baki sannan suka tafiyy suka barta daga ita sai Yaya umar dan yace bazai tafiyy yanxu bah shi kuwa d.p.o tunda yaga yanda Umar Ibrahim yake ta lallaba fadeelan yasan da wata a kasa kuma ya shiga taitayinsa da irin abubuwan kyarar da yakewa fadeelarh....... fadeelarh kuwa taji matukar dadin yanda Yaya umar yake nuna mata kulawa Ashe daman akwai ranar da wani zai kula da ita zai bata lokacinsa akanta......kaiiii alhamdulilah😊🙏
Sai wajen karfe 8pm ya tafiyy bayan ya siyo mata abinci sai da yasata a gaba taciii ta koshi sannan yatafiyy ita kuma takoma cikin sell ta kwanta domin tayi bacci dan wani irin bacci take jii sosai🥱😴

BAYAN KWANA GOMA

Bangaren Fahid kuwa shida Samira yau watansu biyu da komawa gidansu wata iriyar soyayyah suke nunawa juna Kamar sa cinye juna😁 shurac da ifteesan yanxu watansu hudu Amman idan kagansu kai zagayi tunanin sunyi wata bakwai saboda irin girman da sukayi da wayoo ga Kuma gata da suke sha ta wajen iyayensu da kakanninsu🥰😘💔


Anan zan tsaya sai Allah yakaimu tomorrow✍🏾🥰

Nice taku a kullum akoda yaushe Naanah Sha'aban✍🏾💔

💔💜 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah Sha'aban✍🏾💜
Page 166-167
A yau akayi nasarar Kama usman bayan takaddamar da akayi kafin akashi d.p.o ya bukacii dasu mommy suxo domin akwai maganar da yakeso yayi dasu akan fadeelarh💔
Suna xuwa suka tarar dashiii a inda d.p.o din yake maganar da bakinsa dakuma masu laifii usman Yana durkushe ya sunkuyar da kansa bazaka iya ganeshi bah inbah dago kansa yayi bahh fadeelarh kuwa sunki barin tafito domin sunga zatayi musu hayaniya tana ganin Yaya umar ta shiga yin kuka tana fadin Yaya kace suu barnii wlh nii bani da laifii.......matsawa Umar yayi Yana murmushi yace haba kanwata meye abin kuka ynx zaa budeki kowa mah ae yasan Baki da laifii Amman dole sai kinje kotu domin kii bada shaida Dan alkalii zaiso jii daga gurinkiii.......
Tohm shikenan tafada tare da sauke ajiyar xuciya....... Mukullin sell din aka bashii ya budeta tana fitowa tayi gadan gadan gurin usman....lokacin shikuma ya dago da fuskarsa Yana Kara jaddawa d.p.o din cewar eh shi yace fadeelarh ta sace Samira.....wani irin azababban marii tayi Masa hagu da dama tana daukar duk abinda yaxo hannunta tana Dora Masa akaiiii ae kuwa kafiii kace Mai jini ya wanke Masa fuska saka makwan kwalbar da tarotsa Masa a goshiii mummy ceh ta riketa tana fadar haba fadeelarh menene kina so ki aekata laifiii.......mommy ku barni in kasheshi bashi da imanii...Kinga fadeelarh ki kwantar da hankalinki Mana abii komai a hankalii Yaya umar yafada Yana maii janta Suka koma gefe.... d.p.o Kuma ya Kira wani doctor domin axo a duba usman domin suu samu su cigaba da tambayarsa..........koda doctor yaxo yaga ae batayi Masa wani rauni sosai bahh....ya nade Masa Kai da bandage......aka mayar dashi sell d.p.o yace wah suu mommy da Abbah su shiga office dinsa Suka shiga Suka zauna akan kujerun office din d.p.o yafara magana Kamar haka Alhajii ynx dai komai insha Allah muna sa ran zai tayii Kamar yadda muke Soo Kuma zaku iya tafiii da fadeelarh Amman idan za'ayi zaman kotuu sai ta dinga xuwa Daman abinda yasan bamu bada bailing tah bah saboda baa kama shii aenahin Mai laifiii bahh.......... murmushi Abbah yayi tare da cewa Alhamdulilah Allah mun gode maka....mungode sosai sagir Abbah yafada Yana Mai fiddo da kudii ya ajiye masa a gabansa Yana fadar gashi wannan kasha ruwa😁😁shima godia yayi musu sosai sannan suka fita suna mah farin ciki...................
A motar Yaya umar fadeelarh ta shiga tana mai farin ciki da yiwa suu mommy godia da Suka tsaya tsayin daka har aka bada bailing tahh......shi kuwa Yaya umar sai satar kallonta yake Yana Kara jin wani irin abuuu a xuciyarsa game da yarinyar Dan yarasa maiyasa koh kallonta yayi sai yajii dadi a cikin xuciyarsa....idan Kuma bai ganta bah koda kuwa nah rana daya neh sai yajii duk babu dadii.......

Anan zan tsaya sai kuuu dakaceniii gobe kuji yadda zata kaya.....🔥🔥🔥
Nice taku akullum akoda yaushe Naanah Sha'aban💔🥀

💜💔 KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah Sha'aban✍🏾💜
Page 168-169
A yau aka yankewa usman hukuncin rataya bayan doguwar shari'ar da akayiii...... fadeelarh Suka dawo gida cike da farin ciki.....a faloo ta tarar da Yaya umar da yake shii bai samu damar xuwa bah saboda bashii da lafiya shine mommy tace ya zaunarh.......yaya....Yaya tafada tare da shigowa dakin da gudu koh sallama batayi bah....kana kallonta zaka San tana cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa.....kare mata kallo yayi shima Yana sakar mata wani irin sirritatcen murmushi.....Oyyah kafin kifada min lbr Mai dadi ki koma kiyi sallama😊💔Ohhh sorry Yaya tafada tare da dafe goshinta takoma......sannan ta dawoo dauke da sallama a bakinta duk suka amsa tare taxo ta xauna kusa dashii tana Masa ya jiki....dasauki sister anyi nasara kenan tunda Naga kin shigo kina tawani murmushi hakoranki Kamar gonar Audiga😁😁ehmn Yaya anyi nasara tambayi mommy kajii kaiii najii dadi sosai pha.......Ashe yayansuu bilkisu neh wacceh Yaya Ahmad zai aura....haba yafada tare da xaroo ido Yana kallonsu mommy.....mommy tace wlh yayansu neh usman Dan har kokarin Kama mahaifinsu yayi zai garkuwa dashiii......Allah bai basa sa'a bah shineh aka kamashii.....kaiii Amman tirr da wannan rayuwar daya daukarwa kansa......ifteehal ceh ta shigoo tare da Samira rike da ifteesan a hannunta shikuma shurac Yana bayanta dasauri fadeelarh ta tashi ta daukar mata ifteesan din ta dawo ta xauna a inda take tana mata sannu da zuwa......Samira taxo tare da amsawa da yawwah dafatan anyi nasara a kotun dai koh???? Fadeelarh ta gyada kaii tana murmushii tare da jijjiga ifteesan saboda kuka da tafara.....Masha Allah Alhamdulilah....Allah mungode maka...kawota nan uwar quya Yaya umar yafada tare da Mika hannu ya dauki iftee.....Samira ta gaishe dasu mommy Suka amsa mommy tace Ina toh shiii babban yayan koh kun barshi a gida....aa wlh tare muka tahoo ya ajiyemu a wajen aikinsa Muka karasoo sai xuwa anjima zaixo ya daukemuu da daddare...Allah yakaimu......
Yau yakama bikin suuu Yayah Ahmad saura satii daya anata shirye shiryen bikin......saudat kuwa cikinta ya tsufa sosai tare da Samira suke ta shirin bikin tare Dan har kayan da zasu sah iri daya neh wata iriyar shakuwa ceh a tsakaninsu Dan duk satii sai saudat taje gidan Samira Kuma itama samirar tana xuwa gidanta....... sun manta da abinda yafaruu a baya.....abbah yasa hada Auren fadila da yaya umar Tunda yaga alamar yaya umar din yana sonta Amman fadeelarh sam bata san da maganar bah shii yaya umar din Amman yasanii kuma yayi farin ciki da hakan sosai........... Ita da Asma'u mommy tabiya musu suka je gidan wata kawar fauxiyyah take musu gyaran jiki dubu 100........ Yau suna xaune da saudat da samira a babban falon mommy da yake biya sukaxo yau Zasu koma gidan mazajensu sai kuma biki... Mommy tana dakin abbah su biyu neh a falon suna hirarsu ta duniya....
Sukayi sallama yaya daddyne a gaba sai yaya umar suka Amsa fuskokinsu dauke da murmushiii... Saudat tana xolayar yana daddy ango sabon sarki a ganka Ana kare maka kallo kadai kusan tashiii daga gauroo... Harararta yayii sannan ya xaune shima yaya umar ya xauna yana dariya ae saudat bazai kulaki bah sabida baisamu yaga heartbeat dinsa bahhh sunje gyaran jiki.... Anyi masa dai kamar yadda akayi min dole Kayi hakuri dan uwa wlh kamar najawo satii dayan nan yafada yana yatsine fuska....... Dariya sukayi sosai samira tace kaiiiii kawu tohm ae kamar yau neh....... Dan haka kudai nah fushi haka saudat kuwa takasa daina dariya kaiiiii Chabbb ran maza yabaciii watau shine naga yauu kawani daure fuska Ahhhh Wallahi sun kyauta min😜😜😜😜dan Allah aunty saudat ki barni haka wlh bakiji xuciyata bah kamar zata fashe........ Ayyah sorry bro ka kwantar da hankalinka ae saboda kaiii zaayi mata gyaran Kaga kwata kwata sauran pha kwana biyar ahaka sukayi ta jansu da hira har suka waraiiiii suka dawo kamar daaa

Anan zan tsaya kuyi hkr kwana biyu bana yin typing wlh ina busy neh Amman Insha Allah ynx zan dinga yi muku akan kariii.....

Kuma sabon littafinmu da nace on 5 march ynx sai on 12 saboda bangama wannan littafin bahh

Nagode sosai🥰😘💙💞
Much love💕💕💕

❣️❣️KADDARATA😔✍🏾
Story and written by Naanah M Sha'aban✍🏾💖
Page 170-171
Yau Yakama za'a fara bikinsu Yaya Umar tun asuba gidan ya cika damkam da Yan uwansuu....
Amare sun cii kwalliya cikin wanii less kofi mai ratsin milk har su bilkisu mommy tasaka taka daukosu domin ayi bikin a gurin daya....Angoyen Kuma yau sun kaguu suje gurin partyn su hadu da babynsuu......fadeelarh ta kallii su bilkisu da Wanda suke ta waya da angwayen nasuu ita dai ta rasa maiyasa take jin gabanta Yana faduwa tun da suka dawo gida......kwantawa tayi akan kujerar da take zaune ringing din wayarta neh yasaka ta xura hannunta akan center table ta dauka sabuwar number tagani daaa kamar bazata daga bahhh Dan har ta mayar da wayar ta daukota ta daga tare da karawa a kunne Assalamu alaikum tajii wata murya Mai dadin sauraro tayi mata sallama Bata wani Sha wahalar gane Mai muryar bah Dan koh a mafarki tajii tah tasan waye mamallakinta wslm yayanah ina yinii ya taroo duk lokaci daya tayi maganar lpy alhamdulillah.....Masha Allah ina auntyna banganta a gurinsu aunty bilkisu bahhh murmushi yayi kamar tana ganinsa yace Awwww Ashe bakisanta bah koh....hmmm tohm Yaya taya zan santa bayan koh a picx baka taba nuna min ita bahh....Ohk karki damu so nake nayii miki surprised kyakkyawa ceh sosai muryarta abin son a saurara cehhh..... murmushi tayii tace tohm Yaya nasan daiii ae yauu zaayi walkiya inganta tunda yau zata fashe da yammah.....dariya yayi sosai Dan tunda take Bata Bata jin yayi dariya haka bahhh....uhmmm watauu abinda nafada neh ya baka dariya koh yaayah koh da yake ae yau ranarka ceh dole kayiiii....yesss my darling sis fadii kii Kara ae bani kadai bah harda kehh...Dan haka kiyi jam'i Kuma ae Baya zata fashe bah saii gibiiii Ido ta zaro tare da kashe wayar tana fadii baruwana wlh Yaya kafii karfinah😆😆
Fahid neh zaune rike da matarsa a dakinsuu nah gidan mommyy kallonsa take tana wani Dan murmushi Dear wlh kullum jin sonka nake Yana Kara shiga zuciyata bansan Mai yasa bahh jiii nake kamar idan Babu kaii bazan rayuu bah❣️Kara janta yayi kam jikinshiii Nima habibtee daga Ana suka shiga raya suna............
Wasu zafafan motoci neh suke ta fakin a babban gurin party dake garin abuja Wanda duk Wanda akace yakamashi bah karamin Mai kudi baneh......kusan motaci guda talatin neh sukayi parking......kowacceh daga cikin amaran mota guda ta shiga shine yazama nah motocin da amaren suke ciki neh a gaba...........duka suka fitoo suka shiga gurin partyn kamshii Yana tah tashiii......Angwayen duk suna zazzaune a katafaren xujerun alfarma gefen kowannansu akwai gurin da amaran zasu zauna...... fadeelarh ganin anxo gurin partyn sai taje ta nemi gurin mommy ta zauna kusa da ita Yaya Umar duk yaji Babu dadiii

Please Login or Register in order to submit comment