Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gurasarta ta ci, sai ga Hajara ta shigo da kwanuka, ta ajiye a gaban Amina, sannan ta zauna kusa da Amina ta ce "Ya sunan ki ne?".

"Sunana Amina".

"Masha Allah, ni kuma Hajara"

Nan Hajara ta dinga bawa Amina labarin yanayin mutan gidan, tare da sukar Hajiya Zainab da Fadila, ita kuwa Amina hankalinta sam baya kan Hajari, yana kan daddaɗar doya da miyar ƙwan da Hajara ta kawo mata, lokaci guda kuma tana tunanin Inno.

Daren ranar Amina kasa bacci ta yi, saboda tsoro da rashin sabo, haka ta kwana da fitila a kunne.

*************
Alhamdilillah kwanakin nan Hafsa tana yin ciniki sosai, dan har da dankali take haɗawa yanzu bayan awara. Dan har da miya take haɗawa idan mutum yana so ya siya da miya.
Wata mota ce tayi parking a ɗan gaban in da Hafsa take suyar awarar ta, mutumin ya sauke glass ya leƙo da kansa, ya kalli Hafsa yayi mata alama da taje.
Kallo ɗaya ta yi masa gabanta ya faɗi, ta ɗauke kanta ta cigaba da abin da take yi irin ba ta ganshi ɗin nan bama.
Wani almajiri ne yaje kanta ya tsaya ya ce "Wai ki zo inji mai motar can".

"Kace masa ba zan zo ba"

Almajiri ya koma ya sanarwa mutumin saƙon Hafsa.

Mutumin ya ce "Ka nuno mata ni kace ni nake kiranta".

Ko da yaron ya zo ya kuma sanar mata saƙon mutumin, ta kalli yaron a fusace ta ce "Zaka matsa daga kai na ko sai na kwaɗeka?"

Ba shiri yaron ya matasa ya bar wurin, da Hafsa ta iya tsare gida bata son wargi.

Mutumin ne ya fito daga motar ya ƙaraso kan Hafsa ya tsaya, ya dubeta a wulaƙance ya ce "Ke ni nake miki magana ki ka share ni?"

Ko nuna ta san ƙurar da ta kwaso shi ba ta yi ba, ta cigaba da fifita wutar gabanta.

"Aikin banza wulaƙatancciya, a haka zaki ƙare rayuwarki a wahala, daga ke har mahaifiyar ki haka zaku ƙare, kaɗan ma kuka gani, muddin ina raye sai kun fito titi kuna bara"

Wani murmushi ta yi mai ciwo, ta cigaba da sabgar gabanta.

Ya dinga jifanta da miyagun maganganu, a gaban mutane.

Mai shayin da ke gefen in da Hafsa ke sana'arta ne ya ce "Haba bawan Allah, ta yi shiru ba ta tanka maka ba, sai ci mata mutunci kake a gaban mutane ya haka ne?"

"Kaga saurara mini, ba da kai nake ba, ba ka san meye tsakanin mu ba"

"Koma meye tsakaninku wani abu ne da ya shafe ku, nan kuma titi ne bai kamata ba abin da kake yi".

Banza yayi masa ya cigaba da surfa rashin mutunci son ransa, amma duk yadda ya so Hafsa ta tanka masa taƙi, ya gama bala'in sa ya hau motarsa ya tafi.

Bayansa ta bi da kallo har ya ɓacewa ganinta, sai da ya bar wurin wasu hawaye masu zafi suka shiga zubowa daga idanunta 'Allah ka nuna mini ƙarshen mutumin nan da ire irensa kan ƙasa ta rufe idona'.

Ganin tana kuka, Mansur mai shayi ya ce "Kiyi haƙuri Hafsat, mutane irin wannan sai haƙuri ba su da mutunci ba su da kirki" Hafsa ba ta ce masa uffan ba ta cigaba da share hawaye, haka ta kammala cinikin nan babu daɗi ta haɗa kayanta ta koma gida.

Tun da Hafsa ta koma gida Mama ta fuskanci akwai damuwa a tattare da Hafsa, duk da Hafsa ba mai yawan magana ba ce, kuma ba Yarinya ce mai fara'a ba, amma shirunta da ƙaruwar haɗe fuskarta ya sanya Mama ta gane hakan.

"Hafsa lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a ciki.

"A'a ba lafiya ba, mai yake faruwa ne?"

"Mama bakomai fa".

"To koma meye Allah ya ye miki, Idan ba ki gaya mini damuwarki ba, ban sani ba ko akwai wani wanda ki ke da shi a waje da zaki gaya masa" Hafsa ba ta kuma cewa Mama komai ba, ta cigaba da abinda take yi. Wasu lokutan Mama tana jin haushin miskilancin Hafsa, amma kuma gado ta yi haka mahaifinta ma yake, amma har gara shi a kanta, babban abin da Mama take ji shi ne, ba kowane namiji ne zai iya jure halin Hafsa ba.

Mama ta zuba mata ido, saboda kar Mama ta cigaba da takura mata da tambaya, ya sanya ta dinga ƙaƙalo aiki tana yi, ta kwaso kayan wanki ta wanke a daren, ta tsiri wanke wanken  kayan kitchen gaba ɗaya, ta je ta sayo waken awarar gobe, duk wannan aikace-aikace da take yi, ba ta kula Mama ba, ta zauna zata fara gyaran wake, Mama ta yi gyaran murya ta ce "Ajiye waken nan, ki zo ki zauna ki huta, ba zan sake tambayar ki meke damunki ba, tunda dan gujewa tambayar tawa ya sa ki ke ta wannan aikace aikace". Aikuwa sum sum kamar munafuka Hafsa ta koma ɗaki, ta nemi wuri ta kwanta ba tare da ta ko ci Abincin dare ba, Mama kuma ba ta kulata ba ta ƙyaleta.

Amina ta wayi gari a birni, ta gabatar da sallar Asubahi, ta zauna ta na karanto azkar ɗin ta kamar yadda ta saba, tana nan zaune ta ji motsi dan haka ta tashi ta fita, aikuwa taga Hajara ce ke kaiwa tana komowa.

Amina ta gaida Hajara cikin girmamawa, dan dama Hajara ta girmeta, Hajara ta amsa tare da cewa "Har kin tashi?".

"Eh na tashi, nuna mini hanyar fita waje, in je in gaida Baba".

Hajara ta nuna mata, Amina ta fita ta tafi. A ƙofar ɗakin Baba ta tsaya ta ƙwanƙwasa, ya ce "Waye a nan?"

"Baba ni ce"

Baba Hassan ya buɗe ƙofar, ta durƙusa ƙasa ta gaishe shi, ya amsa sannan ya ce "Ya a kai kika fito da duku-duku haka?"

"Baba gaisheka na zo na yi, sannan in ganka"

Yayi murmushi ya ce "To bismillah" suka shiga ɗakin da Baba yake, abin ka da 'ya da uba, an daɗe ba a haɗu ba, suka dinga hira ta bashi labarin abubuwan da suka faru a ƙauye, har ƙazafin cikin da suka yi mata, da sayar da gonarsa da irin kayan da suka saya mata ta gaya masa.

Baba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Bakomai, watarana sai labari, ni dai fatana da burina ki mayar da hankali kiyi karatun nan kin ji uwata"

"To Baba zan yi insha Allah"

"Yawwa uwata, Allah yayi miki Albarka".

"Ameen Baba, amm ai zakaje ƙuye su biyaka gonarka ko?"

"A'a Amina, ai gona ta riga ta salwanta, zan dai je garin in musu bayanin kina wurina".

"Baba ba wani mataki da zaka ɗauka? Dubu ɗari uku fa suka sayar da gonar".

"Ba komai, Allah ya mayar mini da alkhairi".

"To Wallahi Baba ka yi musu Allah ya isa".

Baba Hassan ya buɗe baki ya ce "Uwaki nace, yayyen nawa zan yiwa Allah ya isa?"

Sai Amina ta fara hawaye "Haba Baba, tun da na buɗe ido suke cutarka, kai baka cewa komai, su yi ta zaluntar ka dan sun ga babu mai tare maka, Wallahi Allah zai saka maka"

Baba Hassan ya ƙurawa Amina ido, yana jin soyayyar 'yar ta sa a ransa, ita dai a duniya kar a taɓa mata shi, ko a cutar mata da shi.

Ya sa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce "Tashi maza ki koma ciki, kar su neme ki, zamu cigaba da hirar" da ƙyar Baba ya sa Amina ta tashi ta koma cikin gidan.

A falo ta tarar da Hajara, na ƙoƙarin fara moping, a nan ta tsaya Hajara ta dinga nuna mata yadda ake ayyukan gidan, da wuraren da suke ajiye kayan amfani.

Daga nan suka shiga kitchen, suka fara ƙoƙarin haɗa Abincin karin kumallo. Ƙarfe takwas da rabi suka kammala komai, Hajara ta lura Amina ba ta da ƙyuwa sam, ga kaifin basira.

Sun gama shirya Abincin a kan dining, Hajiya Zainab ta fito daga sashin Fadila, tana gaba Fadila na binta a baya.

Hajara ta risuna kamar baiwa tana gaida Mummy da Fadila, Amina kuwa da murmushi a fuskarta ta gaida su, sai dai yadda suka amsa gaisuwar a wulaƙance ne ya bawa Amina mamaki, dan ita Fadila ma ko amsa gaisuwar ba tayi ba.

Hajiya Zainab ta kalli Amina sannan ta mayar da kallonta ga Hajara ta ce "Ina fatan kin fara nuna mata yadda aikin gidan nan yake?".

"Eh Hajiya na fara nuna mata"

"Yawwa, ki buɗe kunnenki da kyau ki ji abin da zan gaya miki, da dokokina na gidan nan, idan kika karya mini doka korarki zan ki koma in da kika fito. Na farko bana son ƙazanta, bana son munafunci da sa ido, duk abin da zaki ga an yi a gidan ba ruwanki, tun da ba gidanku bane ba. Sannan bana son munafunci da gulma, sannan duk wanda ya saki a gidan nan kome kike dole ki ajiye kiyi abin da aka saki. Ina da yara biyu ɗayan namiji ne baya nan amma yana zuwa hutu gida, ba na son shishshigi a kan abinda ya shafi rayuwata da ta yarana. Abu na ƙarshe idan kin san ki na da wani mugun hali na sata ko makamancin haka ki tabattar kin baro su can a ƙauyenku, dan ba zan ɗauki duk wani rashin daraja da rashin ɗa'a ba" Amina ta ji haushin kalaman da Mummy ta yi amfani da su wurin yi mata bayanin aikin nata, amma ba ta nuna hakan ba sai ma cewa ta yi "Insha Allah zan kiyaye"

Mummy ta ce "Fadila do you have anything to say?"

"Nothing much, you have said it all. Kawai ni dai a bi abinda nake so a gidan nan a zauna lafiya, idan kuma akasin haka ya faru, za a ga abin da zai biyo baya"

Mummy ta ce "To, kar ki sa ran zuwan ki gidan nan, kamar buƙata ta biya ne, zan jarrabaki na 'yan kwanaki in ga kamun ludayin aikin naki, idan yayi mini shi kenan, idan bai mini ba kuma ki koma in da ki ka fito, idan yayi mini ɗin, sai in ga sashin da zaki din ga kula da shi a gidan nan".

Amina dai ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Hajara ta ce "Amina ta so muje mu cigaba da aikin"
Amina ta tashi ta bi Hajara, tana mamakin yadda Hajiya Zainab da 'yar ta ke gatsa magana ba girmama ɗan Adam sam.

Hajara ta ce "Amina sai fa kin yi haƙuri, idan har kina son zamanki a gidan nan dole ki ji ki ƙi ji, dan ba ki ga komai ba in dai wannan matar ce"
Amina tayi ajiyar zuciya tare da jinjinawa Hajara kai.

Ɗakin Fadila suka nufa, Suna shiga ɗakin Amina ta yi turus, ɗakin kaca kaca, har da kwanukan Abinci a ɗakin. Ga takardu da litattafai ko ina, har da kofi a kan gado, ta cire kaya duk ta watsar a ɗakin, banda takaddun biscuit da na chocolate duk a ɗakin a watse.
Ga ɗaki har ɗaki mai kyau, amma kamar makwancin mahaukaciya.

Amina ta ce "Wannan ɗakin waye?"

"Ɗakin 'yar masu gidan ce, kin ganshi nan dai kamar ɗakin jaka, gashi ba ta son ƙazanta, amma fa Komai sai dai a yi mata. Idan ta tashi daga kan gado, cire bedsheet ake a bayar a wanke, ana wanke mata banɗaki sau uku a rana. Haka ma gyaran ɗaki, kuma idan zaki gyara mata ɗaki sau goma idan ta shigo komai a in da ta ga dama zata watsar da shi. Idan ta dawo daga unguwa ko Makaranta, tun daga falo take fara zubar da kayanta, sai dai ki bi Falon ki kwaso mata kayan, tana da kyauta ba kamar uwatta ba, amma duk alkhairinki a gareta, rana ɗaya idan ki ka yi mata abin da bata so, sai ta ƙare miki cin mutuncin da sai kin rasa ina zaki saka kanki, idan ba ki sa'a ba kuwa har uwatta zasu haɗu su ci miki mutunci, dan haka sai ki shirya! Sai kin mayar da kan ki baiwa a wurinsu zaku zauna lafiya".

Nan take jikin Amina yayi sanyi, tana iya jure komai aiki wahala da makamantansu amma ba ta son wulaƙanci, ta fara wasi wasin anya zata iya kuwa? Zata iya jure a ci mata mutunci a kan abinda bai kai ya kawo ba?. Haka suka gyarawa Fadila ɗakinta, suka koma sashin Hajiya Zainab suka gyara ko ina, amma babban abin da ke sake bawa Amina mamaki bai wuce yadda Hajiya Zainab ke ta faman yi musu tsawa ba, ko Magana za a yi musu, sai cikin tsawa da harara.

Kwanaki biyu kenan ɓatan Amina ya karaɗe ƙauyen nan gaba ɗaya, ga Jarmai ya ɗagawa su Baffa Bala hankali, dan ya riga ya gama saka rai da samun Amina.

Inno kuwa tsawon kwanakin nan, ba ta iya cin Abinci, duk ta zube saboda kuka, da tashin hankali ko bacci bata iya yi, kullum tana kan sallaya tana riƙe da carbi.
Har malaman makaranta su Amina sai da suka zo, suka yiwa Inno jajen ɓatan Amina.

Kamar ko yaushe, Inno na zaune ta duƙufa tana jan carbi, ta jiyo muryar Saminu yana sallama.
Ta amsa masa tare da bashi damar shigowa, ya shiga ya zauna suka gaisa,  sannan ya ce "Baba Hassan ne ya aiko ni wurinki".

Inno ta ce "Ka sanar masa da batun ɓatan Amina ne?".

"Ai Amina ba ɓata tayi ba".

Inno ta kalleshi da mamaki, amma ta sunkuyar da kai ta ce "Na sani, Amina guduwa ta yi saboda wannan auren da za ayi mata, ba yadda ba ta yi dani ba a kan in sa baki, amma nasan ko na yi magana ba su ji ba, ni babbar damuwata babu wanda ya san in da take, ta ɓatawa kanta suna a garin nan" ta ƙarasa Maganar tana share hawaye.

"Maman Amina ki kwantar da hankalinki, Amina na tare da babanta a birni"

Dafe ƙirji Inno ta yi ta ce "Kamar yaya?".

Nan ya kwashe komai ya gaya mata, sannan ya ɗora da cewar "Baba Hassan ya ce, kar ki gayawa kowa, ya ce zai zo da kansa garin nan idan komai ya lafa, wayata ta ci speaker ne jiya, da na kira miki shi a waya".

Inno ta kuma ƙasa da muryarta ta ce "Dan Allah Saminu da gaske ka ke, tana lafiya ƙalau a wurin babanta?".

"Wallahi Babar Amina ba zan miki ƙarya ba, tana wurin Baba Hassan".

"To Alhamdilillah, Allah kai ne abin godiya, Allah na gode maka, Saminu Allah ya yi maka albarka, insha Allah zan shiru da bakina, babu wanda zan faɗawa sai ya zo da kansa"

Inno ji tayi tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan tsananin farin ciki.

Kwanakin Amina huɗu a gidan, Alhaji Ahmad ya shirya komawa wurin aikinsa, ya tabattar wa da Baba Hassan cewa, Khalil zai shigo gari, idan an koma Makaranta shi zai kai Amina Makaranta.

MEYE HASASHEN KU GAME DA LITTAFIN NAN? INA JIRAN RA'AYOYIN KU.
DAN ALLAH BANA SON THANKS ƊIN NAN, KO STICKER.


Domin samun update a kan lokaci Follow my Arewabooks Account
@ Ayshercool7724
My Watpad account@ Ayshercool 7724
Ayshercool
08081012143



GABA DA GABANTA

P8

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)



Amina ta yi murna sosai a kan batun kai ta makaranta, tsananin ɗoki da shauƙi ya sanya ta manta da duk wani batun rashin mutuncin da Hajiya Zainab da 'yar ta ke musu.
Kafin Alhaji Ahmad ya tafi, Baba ya tambaye shi yana son a bashi dama sati mai zuwa ya je ganin gida. Alhaji Ahmad ya amince masa da ya je.





Bayan an idar da sallar Asubahi, Rabi'u Jarmai ya ritsa kawu Bala yana masifa "Gaskiya Bala na gaji, yau kwanaki goma kenan ba yarinyar nan babu labarinta, dan haka na haƙura, kuje ku kwashe ruɓaɓun kayan da ku kai gidana, sannan ku dawo mini da kuɗaɗe na".

Kawu Bala ya ce "Haba Jarmai, ya zaka yi mana haka? Dan Allah ka yi haƙuri, na gaya maka ana ganin yarinyar nan, za a ɗaura muku aure a kai maka ita gidanka"

Jarmai ya ce "Allah ya sawwaƙe, yarinyar da ta iya guduwa daga gidan iyayenta tsawon kwanakin nan, ai kowa ya san bariki ta tafi, dama can waya sani ko a ɓoye yawon bokon nan abin da take yi kenan, kawai ku biyani kuɗina ko in kai ku wurin 'yan sanda a birni".

"A'a ba za ayi haka ba, insha Allah zamu dawo maka da kuɗaɗenka, ba zata kaimu ga haka ba"

"Ato a san abin yi tun da wuri, kan ta kacame mana".

Kawu Bala ya tafi gida yana jujjuya lamarin a zuciyarsa, ya san jarmai ba shi da mutunci a kan kuɗi ba abin da ba zai iya aikatawa ba.

Kawu Bala na zuwa gida, ya sa aka taso masa Lawan suka keɓe.

"Lawan, Jarmai fa na neman ya tona mana asiri a garin nan, yanzun nan ya tare ni a masallaci ya ce mu dawo masa da kuɗinsa ko ya kai mu wurin 'yan sandan birni"

"Kai Jarmai ba shi da mutunci Wallahi"

"Ai ba laifin Jarmai ba ne, duk laifin wannan shegiyar yarinyar ce, da ta na nan ai da duk haka ba ta faru ba, Allah wadaran yarinyar nan"

Kawu Lawan ya ce "matsiyaciya ba, na san tana can ta bazama bariki, dan da tana garin nan da tuni an ganota, ko ubanta ya san ta gudu oho"

"To waya san musu"

"Ni anya makuwa ba da haɗin bakin Hanne yarinyar nan ta gudu ba?"

"Nima na fara zargin haka, dan ban yadda da matar nan ba, amma yanzu yaya za muyi da Jarmai"

"To yanzu dai ya za ayi a mayarwa da wannan masifaffen kuɗinsa?"

Kawu Bala ya ce "Yanzu dai idan gari ya yi haske, aje gidansa a kwaso kayan nan, a mayarwa da Larai dillaliya, kai kuma ka lalubo abin da za a samu a wurinka".

"Me kuwa za a samu a kuɗin, kar ka manta a kuɗin aka saiwa Gali babur, ka cika kuɗi ka sai babbar gona, ai ni ban wani mori kuɗin nan ba".

Kawu Bala ya ce "Haka ne, amma duk da haka dole kayi wani abu, ko 'yar wurinka Abu zamu ba shi a madadin Amina?"

Kawu Lawan ya zaro idanu ya ce "Ni in ɗauki 'ya ta in bawa Jarmai, Allah ya kiyaye ya sutura, Wallahi gara ta mutu ba aure, sai ka ce baka san waye Jarmai ba? Ka aura masa Sa'a mana ai ita ma ta isa Aure".

"Kai baka Aura masa Abu ba, sai ni zan aura masa sa'a? Wannan mutumin banzan Allah ya kiyaye, dama dai Aminan ce. Yanzu dai idan gari ya yi haske, za a kwaso kayan a mayarwa dillaliya, mu san yadda za mu yi a haɗa masa kuɗinsa".

"To shikenan, Sai an jima, amma dai Wallahi ka je ka ritsa Hanne, dan wataƙila ta san komai, matar munafuka ce".

Bala ya ce "Bar ni da ita, zata gane kurenta"




Yauma wankan doguwar rigar da ta yi, ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba, sai da tun da ta shigo kallo ɗaya yayi mata suka haɗa ido, ya sauke idanunsa cike da fargabar kar ta yi masa wata tijarar a cikin mutane, dan ya fuskanci tamkar wani jin daɗi take yi idan ta ci mutuncin sa.
Kasancewar babu malami a ajin, ya sanya Captain ya ce wa Yazeed, ya fito ya ɗan yi musu tutorial, a kan wasu courses ɗin.
Yazeed bai musa ba, ya fito ya karɓi abin rubutu, sai da ya fara da addu'a, sannan ya kalli 'yan ajin ya fara yi musu bayani da yadda ya fahimci tambayar da malamin nan yayi a ranar da ya ce suyi amfani da waya, sannan ya shiga gaya musu dabarun da ya bi wurin gane amsar tambayar.

Fadila ji tayi ba zata iya zama jin shirmen da Yazeed yake yi ba, duk ajin a rasa wanda zai yi tutorial sai shi, ita gaba daya ta gama raina shi, ta ɗau jakarta tana mita, a fili take cewa "Instead of a nemo malamin da ze mana covering Wannan period ɗin, kawai an samu a gaba wani yana shirme, mutumin da ko turanci bai iya ba me zai koyawa wasu?".

"Babbar yarinya wai dan Allah mai yasa ki ke haka ne? Wannan fa ba girmanki ba ne, bawan Allah nan mutum ne, ba zai ji daɗi ba abin da ki ke yi masa".

"To kar Allah ya sa ji daɗin mana, ya daina shishshigi da son nuna ya fi kowa iyawa"

Babson ya ja wani uban tsaki ya ce "Dalla ku share wannan mahaukaciyar ku cigaba da yi mana abin da yakamata".

"Ba zan kula ka ba, barber ka ke ko me? Talauci ne yake ɗawainiya da kai ka ke wannan shirmen" ta yi tsaki ta fice.

Har ta yi ta gama Yazeed bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, ya karɓi wayar Captain, ya cigaba da yi musu bayani.

Captain ya ce "Yazeed, dan Allah ka yi haƙuri, na sani abin da yarinyar nan take yi maka babu daɗi, amma dan Allah ka yi haƙuri"

Cikin dakiya da basarwa Yazeed ya ce "Kar ka damu Captain, ni ban damu ba" ya cigaba da abin da yake yi.




"Kina Ina? Munafukar banza fito nan"

Sai da cikin Inno ya kaɗa, dan tun da taji muryar su Kawu Lawan, ta san ba alkhairi. Fitowa ta yi daga ɗaki tana faɗin "Lafiya kuwa?"

"Kya tambayi lafiya mana, munafuka ha'ina, ki zo ki fito mana da in da yarinyar nan Amina ta ke, dan babu yadda za a yi ta gudu ba tare da haɗin bakin ki ba".

"Haba Yaya Bala, ni meye nawa a ciki? Ya za ayi in goyi bayan Amina ta bijire muku, ko ta gudu? Nima fa Amina 'ya ce a wurina, ba zan goyi bayan ta aikata abin kunya ba, ni ban san in da take ba".

Bala ya ce "Ai kuwa ƙarya ki ke yi, kuma yadda ki ka haɗa baki da ita kika sa ta gudu, sai ki koma ki haɗo abin da ya samu a mayarwa da Jarmai kayan aurensa, tun da ta gudu".

"Meye haɗina da kayan auren Jarmai? Bayan kuɗinsa da komai ku ya dabƙawa kuma babu abin da kuka bamu a ciki?".

"Rufewa mutane baki, amma dai kin san abin da aka yi kuɗin ko? Kayan katako aka sayawa Amina da su"

"Amma yaya Bala, ina a kuɗin gonar mahaifinta aka saya mata kayan? Ni dan me za a ce in bada wani kuɗi"

"Au tuhumar mu zaki yi, to Wallahi sai kin kawo wani abu, dan sunan mu ba zai ɓaci a banza ba a dalilin ku ba, mutanen banza kawai"

Galala haka Inno ta bi su Lawan da kallon mamaki da kuma ƙarfin hali.




Amina aiki suke sha a gidan nan kamar ba gobe, kasancewar Amina nai kaifin ƙwaƙwalwa ya sanya nan da nan ta iya abubuwa, ita aikin fa suke ba ya damunta, dan in dai aiki ne ta riga ta saba da shi tun a ƙauye, dan sam ba ya mata wahala, ita wulaƙanci da kallon ƙasƙantattun da ake musu ne yake damunta, shima da tuna ga burinta da yake ranta wanda take sa ran cikawa sai ta yi ƙoƙari ta manta komai.
Dan kusan kullum idan ta je wurin Baba nasihar sa kenan a gareta, ta yi haƙuri.
Amina na ta saka ran ganin wanda zai kaita Makaranta ya dawo, amma shiru ba ta ga ya dawo ba, kuma ba ta ji ana batun dawowar ta sa ba, ta dai yi shiru ta danne abun a ranta, dan abin ya fara damunta, idan aka aiketa ita da Hajara, tana ganin 'yan Makaranta hakan ya tabattar mata da an koma Makaranta.

Yau sun gama aikin su kaf, sun gyara ko ina, wanda ƙarfin aikin ma Amina ce ta yi shi, ta zauna a falo tana kallon TV, sai ga Fadila ta dawo daga makaranta, ta shigo falon ba ko sallama, ta dire jakarta a falon, da mayafinta ta kalli Amina ta ce "Ki kawo mini su ɗaki".

Amina tabi bayan Fadila da kallo ta taɓe baki, a ranta ta ce "Kin shigo ba ki mini sallama ba balle sannu da gida, kuma kin yi dakon jaka da mayafi tun daga makarantar, ƙarasawa da su ɗakin ki shi ne aiki a wurinki, ai kuwa ba zan kai ba' daga haka ta tashi ta bar falon, tayi tafiyarta wurin Baba.

"Uwata, in ce ko dai kin gama duk ayyukan da aka saka ki kan zo nan?"

"Eh Baba, na gama komai".

"Yawwa Uwata ta kaina, banda ganda ko gardama dan Allah, yi nayi bari na bari".

"Insha Allahu Baba, nace yaushe zaka je ƙauye ne? Da na ji kace a wannan satin"

"Eh a wannan satin na so zuwa, amma nafi son in ga yaron nan da zai kai ki Makaranta ya dawo, an kai ki kin fara zuwa sai inje".

"Wallahi Baba kamar ka san abin da ke raina, na yi shiru ne kawai dan kar in takura maka, amma naga an koma Makaranta".

"Mu ƙara haƙuri

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment