Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

man shanu fal da fura ta bawa Alhaji Ahmad, ya karɓa tare da yi mata godiya.

Amina ta kai Akwatinta mota, Inno ta rakota har ƙofar gida, a nan suka iske su Bala.

Amina ta ce "Daddy, ga 'yan uwan mahaifina nan, ga Baffa Lawan da Baffa Bala" Ta kalli su Bala ta ce "Baffa, ga Alhaji Ahmad, wanda muke zaune a gidansa ni da Baba.
Saboda tsananin kwarjini Alhaji Ahmad, haka suka zube jiki na rasa suka gaishe shi, ya amsa musu yayi musu alheri, sai dai sai da Amina tayi kuka da taga zata tafi ta bar Inno.

A motar da Alhaji Ahmad ya ke Amina ta shiga, yara suka taru suna ɗaga musu hannu suka bar ƙauyen.

"Daddy, wai yana ganka da 'yan sanda kamar zaka kama mai laifi?"

"Saboda tsaro, ai a ƙa'ida ina yawo da su saboda tsaron lafiyata, yanzunma dan doguwar tafiya zan yi ne, amma Allah ne ke karewa ai"

Ta ɗan kalli Daddy ta ce "Mmn kayan nan sun maka kyau, kamar wani ango sai ƙamshin turare kake"

Daddy ya gyara hular kansa ya kalleta ya ce "Kamar wani ango ko? Zaki maimaita a gabanta"

Amina ta tsuke fuska ta ce "Ita wa?"

"Lovely Zeena"

Ta ɗan taɓe baki ta ce "Lovely manya"

"Ke, kin fiye tsaurin ido fa, wai me matata tayi miki ne kike kishi da ita?, gaya mini gaskiya what is in your mind about her husband?" Yayi maganar muryarsa can ƙasa.

Amina ta kalleshi ta ce "Like?"

"Nothing" daga nan yaja bakinsa yayi shiru.

Ko da suka isa cikin garin Kano, maimakon su wuce gida, guest house ɗinsa suka wuce.

Amina ta kasa yin shiru ta ce "Daddy ya na ganmu a nan kuma, ba gida zamu wuce ba?"

"Eh ba gida zamu wuce ba" yayi maganar ransa a haɗe dan kar ta sake yi masa wata tambayar.
Gaba ɗaya ba haka ta so ba, da aka yi parking ma bai ce ta sauko ba, dan kanta ta sauko tabi bayansa.

Sai da suka je tsakiyar falon gidan, sannan ya kalleta ya ce "Ki shiga wancan ɗakin, kiyi sallolinki, za a kawo miki Abinci ki huta da la'asar Zakiru zai zo ya kai ki gida"

Jiki a sanyaye ta ce to, dan ita duk ba haka ta so ba.

Ta ware mayafinta ta yafa sosai, tayi sallar azahar, tayi adduointa, ta kira Inno ta sanar mata sun sauka, yanzu zasu ƙarasa gida, sun ɗan jima suna waya sannan Amina ta kashe wayar.

Ajiye mayafinta tayi a kan gadon dake ɗakin, ta tafi gaban mudubi tana duba fuskarta, ta kwance ɗan kwalin kanta tana sake gyara shi, kawai aka turo ƙofa, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya sai ta ɗan rikice, gashi tayi nesa da mayafinta da ke kan gado.
Lumshe idanunsa yayi ya buɗe, kamar wanda aka yiwa dole ya ce "Zo ki karɓa" yayi maganar yana miƙo mata leda.
Kasa motsi tayi daga in da take tsaye, saboda kunya da ta gama mamayeta.

"Meenal, am talking fa"

Sunkuyar da kanta tayi ƙasa, ta fara tafiya a hankali, tana jin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, ta ƙarasa in da yake tsaye ba tare da kalleshi ba.

"Menene? Ya naga kina sunkuyar da kai meyafaru" Yayi maganar tamkar bai san meya sanyata cikin ɗari-ɗari ba.

"Babu komai" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.

"Ga Abinci nan, da kin yi sallar la'asar kije haraba Zakiru na jiranki, ni zan tafi yanzu, zanje wani wuri"

Ta karɓi ledar hannunsa ta ce "Na gode"

Kamar yadda ya gaya mata, bayan sallar la'asar ta tarar da Zakiru a harabar gidan yazo ɗaukarta, ita har mamaki ma take yi, Daddy baya tsoron ko Zakirun ya gayawa Hajiya Zainab cewar suna yawo tare, har gidansa ya kai ta.

Zakiru bai nuna mata komai ba, sai tambayarta ya ta baro mutan gida, a haka har suka isa gida.

Baba na ganinsu ya taso da murnarsa zuwa wurin motar, Amina ta fito tana masa murmushi tare da gaishe shi.

Ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Ya hanya, ya babar taki?"

Amina ta ce "Lafiya lau Baba, kamar kar in dawo gida da daɗi"

Baba yayi murmushi ya ce "To ko zaki koma ne?"

"Ai Baba ba dan wannan tafiyar ta makarantar mu ba, da ba zan dawo yanzu ba"

"To shikenan, maza shiga ciki ki samu ki huta"

Amina ta juya ta ɗau Akwatinta da Zakiru ya fito mata da ita, Baba sai sannu yake masa, Amina ta ja Akwatinta zuwa cikin gidan.

A falo ta tarar da Hajiya Zainab da ƙawayenta su Turai, sun ci Abinci duk sun bar kwanukan.

Amina ta ce "Ina wuninku?"

A yamutse suka amsa mata, dan Hajiya Zainab bata amsa ba, sai ma kallonta da tayi ta ce "Zo ki kwashe kwanukan nan"

Mamakine ya kama Amina, Hajiya Zainab dai ba makauniya ba ce ba, taga Akwati a hannunta yanzu ta dawo, amma saboda tsabar son ta wulaƙantata wai ta zo ta kwashe kwanuka.

"Ko ba zaki zo bane, kika cake a wurin kina kallona?" Amina ta jingine Akwatin, ta zo tsakiyar falon, ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen, ta zo kuma kwashe sauran, Mummy ta kuma kallonta ta ce "Idan kin gama, na fito da labulaye na barsu a kan gado, zaca cire na part ɗina gaba ɗaya a sanya wannan, Carfet ɗin bedroom ɗina ma, zaa a canza wani, wannan fita da shi za ai, Zakiru ya kai shi Car wash.
Amina kawai ta jinjina kai ta tashi, ta kai kwanukan ta dawo ta ja Akwatinta.
Hajara ce ta fito daga ɗakinta, sanye da hijjabi alama salla tayi, ta washe baki tana faɗin "Amina ashe kin dawo ya hanya?"

"Lafiya lau Hajara, ya aikin?"

Hajara ta kwaɓe fuska ta ce "Aiki gashi nan, kin tafi kin barni, matar gidan nan da alama akwai abin da yake damunta, kullum cikin sauke mini kwandon bala'i take, da na motsa sai hantara, haka ita ma 'yar ta ta, kai wanan masifa ni Hajara wanan mutane kamar gadonta suka yi"

Amina ta ɗan taɓa baki ta ce "To Allah ya kyauta".


Hajiya Turai ce ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Ita kuma wannan 'yar aikin taki daga ina na ganta da uwar akwati?"

"Wai nan ƙauye ta je"

Turai ta ce "Ni fa gani nayi tana wani ƙara kyau"

"Ke ni bar ni da zancen banza, Hajiya Salma, ya batun yarinyar nan da kika ce in haɗata da Khalil, da wuri zan duk abin da ya dace, kan ya lallaɓa ya koma wurin waccan shahshashar ban sani ba"

Hajiya Salma ta ce "Karki damu duk ranar da kika shirya, ki zo muje kiga yarinyar"

"Allah ya kaimu jibi, zan zo muje"


Amina ta shiga aikin canza labulaye, kamar yadda Hajiya Zainab ta umarce ta, Amina ba ta gama aikin nan ba sai bayan sallar isha'i, gaba ɗaya ta gaji.

Kasancewar tafiyarsu ta ƙarato, ya sanya Amina ta duƙufa cigaba da bitar karatun da tayi, ana sallar isha'i, ta shige ɗakinta, hatta Abinci a ɗakinta ta ci.

Wajen sha ɗayan dare ta ga kiran Daddy, ta ɗaga ta saka wayar a handsfree taƙi magana.

A hankali ya ce "Meenalin Daddy"

"Na'am"

"Au na zaki kulani ba, ki ka ɗaga wayata ki ka yi shiru?"

"Ai kaima watarn haka kake mini"

"To naji, zan samu tea?"

Amina ta ɗan tura baki ta ce "Ni gaskiya a gajiye nake, daga dawowata aka sani canza labulaye da Carfet, da nayi niyyar ko girki na yi maka, amma ko akwatina ban ajiye ba aka sani aiki"

"Waye ya saki aikin?"

"Ai kai ma ka sani"

"To shikenan naji, da safe idan Allah ya kaimu, ki mini girki kin ji Meenalina, am missing your delicious food, kuma kinga kin fi kowa sanin Abincin da ya dace da ni"

Ta yi wani murmushi kamar tana gabansa ta ce "I Will in sha Allah"

"Ranar Wednesday zaku tafi, so ki cigaba da shiri, idan da wani abu da kike buƙata ki sanar da ni"

"Eh, abu ɗaya nake so"

Cikin zaƙuwa ya ce "What it is?"

"Your presence their" tayi maganar a shagwaɓe.

"Rigimar ce ko, sai da safe" ya kashe wayar. Ajiye wayar tayi tana cigaba da mita, ta mayar da hankali ga karatunta.



Cikin rashin samun mafita, da rashin karsashi Khalil ya kira Mummy a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ya samu ga ɗaga.

"Yau ka ga dama ka neme ni kenan?" Yaji muryarta maimakon ko gaisawa ta bari suyi.

A saɓule ya ce "A'a ba haka bane, bani da lafiya ne"

"Eh, ko ba baka da lafiya ba? Kana fama da ciwon so ko, gubar Asirin da suka zuba suka baka a Abinci bata sake ka ba, to ka sani in kai sun shanye ka ni basu shanye ni ba".

"Mummy dan Allah duk a bar wannan maganar, ni kiranki nayi na gaisheki"

"Ka riƙe gaisuwarka bana so, jibi in Allah ya kaimu zanje naga iyayen yarinyar da na zaɓa maka, next za a kai kuɗin Aurenka da ita"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah Mummy kar ki mini haka"

"Ai tuni ma an riga an yi, idan ka ga dama kayi mini biyayya, idan ba ka ga dama ba kabi 'yar matsiyata mai awara a hanya!!


AYSHERCOOL
08081012143

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment