Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan gadonta tayi tsuruu, gaba ɗaya mood ɗin da taga Yazid bai yi mata daɗi ba, haka nan ta ji ta damu, cikin ƙoƙarin kauda tunanin Yazid daga ranta, ya sanya ta ɗau wayarta ta fara game, ita a dole bata damu da Yazid ba.

Alhamdilillah, Hafsa ta ɗan farfaɗo ba kamar lokacin da aka kaita Asibiti ba, an samu jinin ya ɗan sauka.
Likita yayi ta mata nasiha, da rarrashinta a kan ata kwantar da hankalinta, ta miƙa lamuranta ga Allah, sannan ya sallamesu.
Kusan duk kuɗin hannunsu ya ƙare, saboda zaman Asibiti, ga babu kayan Abinci. Hafsa ta ɗan ji daɗin jikinta, sai dai ta kasa mantawa da batun Khalil, babu abin da ya canza daga soyayyar da take yiwa Khalil ɗin.
Kayan da Khalil ya bata ta tattara ta bashi bai karɓa ba,  a soron gidansu ya bar mata, dama tunu ta cire layin wayarta daga wayar da ya bata zuwa tsohuwar tata.
Da suka dawo gida ta duba wayar, sai ta ga missed calls ɗin Khalil rututu a ciki, da tarin messages, ba dan ta so ba haka ta saka lambar Khalil a blacklist, tana jin kamar da zuciyarta ta haɗa ta saka a black list ɗin.

Bayan Amina ta gama koke kokenta, kuma sai ta fara tunanin akan abin da ta yiwa Daddy, sai taga kamar bata kyauta ba, saboda ya kyautata mata har ƙarawa Baba albashi yayi ba tare da ko matar gidan ta sani ba, ita ma Baba da ya gaya mata ya gargaɗeta a kan kar wanda ta gayawa, dan Alhaji Ahmad ya ce masa ko Aminan kar ya gayawa, banda kyautatawa da yake mata a kai a kai da ƙoƙarin bata kariya a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin cin mutuncinta, gaba ɗaya kuma sai jikinta yayi sanyi.

Da magariba Hafsa na zaune, ta saka tuwon da Mama ta zuba mata, amma ta kasa ci, Mama sai hira take yi mata dan ta ɗebe mata kewa.
Wayar Hafsa ce ta kawo haske alamar kira ya shigo, kasancewar wayar a silent take, Mama ta ɗauko wayar ta miƙawa Hafsa.
Hafsa ta girgiza kai ta ce "Mama ƙyale wayar nan kawai"

"A'a ai ba a yi haka ba" Mama ta ɗaga wayar tare da yin sallama.

"Wa'alaikum salam, Mama ina wuni?"
Mama ta kalli Hafsa jin muryar Khalil.

"Lafiya lau Khalil, ya aiki?" Waro ido Hafsa ta yi jin Mama ta ambaci Khalil.

"Aiki lafiya lau Mama, ina ta kiran Hafsa a waya bata ɗagawa, daga baya ma wayar bata shiga"

Mama ta ce "Ai da yake ta ɗan yi rashin lafiya ne, ɗazu muka dawo daga Asibiti"

Cikin damuwa Khalil ya ce "Subhanallah, ya jikin nata?"

"Taji sauƙi Alhamdilillah, bari in bata wayar" Mama ta miƙawa Hafsa wayar, ta tashi ta bar ɗakin.

Hafsa ta kalli sabuwar lambar, sannan ta saka wayar a kunnenta.

"Assalamu alaikum, Hafsat"

"Na'am" ta amsa a sanyaye.

"Hafsa why? Meyasa laifin Mummy zai shafeni, ko mun rabu ai bai kamata ki yanke duk wata alaƙa da ni ba" Hafsa tayi shiri ba ta ce masa komai ba, sai ma jin kewarsa na damunta.

"Hafsa kiyi magana mana"

"To me zance?"

"Shikenan, Yanzu ya jikin naki?"

"Naji sauƙi"

"Allah ya baki lafiya, gaba ɗaya ina cikin damuwa ko aiki na kasa yi, na kira ba kya ɗagawa daga baya ta daina shiga, sai sabon layi na saya na saka na kira sannan kika ɗaga, dan Allah Hafsa kiyi haƙuri abin da Mummy ta yi miki ya wuce, ina ta ƙoƙarin saita komai, in Allah ya yarda za mu yi Aure"

Hafsa ta lumshe idanunta sannan ta buɗesu ta ce "Khalil"

"Na'am Hafsa"

"Duk abin da iyaye ba sa so aka aikata shi baya albarka, baya zuwa ko ina, dan Allah Khalil kayi haƙuri ka ƙyaleni, dole mu haƙura da juna"

Khalil ya maraice ya ce "Dan Allah Hafsa...

"Shhhhhh" ta katse shi.

"Ko Mama ce ta ce na rabu da kai, idan har bata son alƙarmu zan rabu da kai har abada, Yakamata mu yiwa Mummy biyayya, dan Allah Khalil kar ka sake kirana, kayi haƙuri"

"To ki tsaya kiji" ba ta jira mai zaice ba, ta kashea wayar, ta cire layin gaba ɗaya daga kan wayar.

Ta haɗe kai da gwiwa tana ta ƙoƙarin mayar da hawaywnta amma ta kasa.

Mama tayi sallama ta shigo ɗakin, ta zauna ta ce "Yaya kiran me yake miki?"

"Haƙuri yake bani, wai mu koma kamar da"

Mama ta girgiza kai ta ce "Ai hakan ba zai yiwu ba, tun da mahaifiyarsa bata so, Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi"

"Ameen" Hafsa ta amsa jiki a sanyaye.

Khalil kuwa sakin wayar yayi a ƙasa, sai a Yanzu yaji wasu irin lafiyayyun hawaye suna zubo masa, bai taɓa zaton zai iya kuka a kan mace ba, babban abin da yasa yake jin zai iya taking kowane risk saboda Hafsa shi ne ya sani ba kowane namiji ne zai iya karɓar Hafsa da ƙaddararta ba, gashi so yake mata na fisabilillahi, ji yake a duniya banda uwar da ta haifeta babu wanda ya kai shi ya sonta da ƙaunarta.

Daddare Amina zata kwanta bacci, ta dinga kallon wayarta, da sukan yi chatting da Daddy da daddare kafin tayi bacci, tayi ta masa shirme da shirirta yana biyeta. Sai dai yau ko saƙo ɗaya bai turo mata ba, ta duba what's app taga yana online.
Sallama tayi masa, sai dai ya buɗe ya gani amma ya share, ga zauna shiru shiru amma bai mata reply ba.
Ajiye wayar tayi cike da damuwa, tana sake ganin rashin kyautuwar abin da ta aikata wa Daddyn.

Kwanaki biyu kenan, babu wanda ya nemi wani tsakanin Fadila da Yazid, a kwana na uku kuwa bai zo makarantar ba gaba ɗaya, gashi ana ta shirye shirye na fara exams, ana fa teses baya nan, abu kamar wasa har aka tafi kwana na uku baya zuwa makaranta, gashi shi ba wani aboki ne da shi ba, balle ta tambaya.

"To ma ina ruwana da rashin zuwansa' ta tambayi kanta, ta cigaba da ƙoƙarin mantar da kanta batun Yazid.

Amina kuwa nadamar abinda ta aikata ya addabeta ya hanata sukuni, ta kai ta kawo, idan taga Daddy ta gaishe shi, sai dai ya amsa sama-sama, alamar fushi yake da ita.
Gashi ta rasa hanyar da zata bi wurin bashi haƙuri. Ranar asabar da safe, tana gyarawa Hajiya Zainab falo, ya shigo falon, Amina ta risuna ta gaishe shi.
"Lafiya lau" ya amsa. Ya wuceta ya nufi bedroom ɗin Hajiya Zainab.

A tsaye ya tarar da Hajiya Zainab, ta sanya skirt ɗin lace, tana kwalliya a gaban mudubi, ba ta saka rigar ba tukuna.
Ya ɗan ƙare mata kallo sannan ya nufi in da take yana faɗin "Bainu ba kya tsufa"

Ta ce "Hmm, ka fito kenan, ya ka kwana da jikin?"

"Ba zan amsa ba, tun da baki kwana da ni ba, duk da kin san jikina babu daɗi".

Hajiya Zainab ta waiwayo ta kalleshi ta ce "Sai kace wani ƙaramin yaro, da ban kwana da kai ɗinba, ba ga ka nan ras da kai ba, jikin yayi sauƙi".

Ya ƙarasa bayanta ya tsaya, ya rungumeta ta baya, ya zagaya hannayensa a cikinta, tare da kwantar da kansa a kan kafaɗarta ya ce "Ko ba komai kasancewarki a kusa dani, zai sa naji daɗi"

Ɗan ƙoƙarin ture hannunsa take ta ce "Kaima dai, ba magungunaka suna nan ba, ka sha ka kwanta kayi bacci, ko kaje Asibiti mana"

"Duk ba wannan nake buƙata ba, ke ɗin dai, attention ɗinki, kulawarki da hirarki domin ɗebe mini kewa, musamman na ɗauki hutun shekara saboda in kasance da ku, duba da yanayin aikin ina daɗewa bama tare amma duk kinfi mayar da hankali a kan 'ya'yanki, business ɗinki da sauransu, ni ba kya kulawa da ni sosai, ina buƙatar kulawa nima" yayi maganar yana cigaba da ƙanƙameta yana shaƙar ƙamshin man da ta shafa.

Ɗan tsuke fuska ta yi ta ce "Ahmad meye haka ne? Dan Allah Yakamata ka san yanzu ba da bace bafa, mun girma fa yanzu,da auren wuri muke yiwa yaranmu da yanzu muna da jikoki, yanzu jikinmu hutu yake buƙata ba wannan abin ba,  abin da aka yi a baya Allah ya amfana".

Alhaji Ahmad ya sake ƙasa da muryarsa ya ce "Am not old for that, ban san me kike nufi da ni ba, ban yi girman da na wuce samun kulawa da tatali daga iyalina ba, Please kar muyi haka da ke"

"Kaga dan Allah ka rabu da ni, unguwa zan fita ni"

"Unguwa ƙarfe goma na safe, ke kenan kullum cikin fita da wadda na amince, da wadda ban amince ba? Dan Allah ki zauna a gida mu wuni tare yau"

"A'a wallahi, fita ta tana da muhimmanci sosai, zan zaga shaguna na, daga nan zanje biki, classmate ɗinmu na auran 'ya" ta zame daga jikinsa tana ƙoƙarin ɗaukar rigar kayanta ta saka.

"Haba Zee, shikenan let's have some fun before you go" yayi maganar yana kuma ƙoƙarin rungumota.

Cikin tsawa ta ce "Wai meye haka ne, na ce maka bana so, dan Allah wai sai yaushe zaka girma, you don pass this level, haba dan Allah"

Lumshe idanunsa yayi, ransa a ɓace, ya kalleta da idanunsa suka fara sauya launi, "Zainab, ki bini a hankali tura ta kai bango"

"Da tura ta kai bango, saika rushe bangon ai, shikenan shekara da shekaru ana abu ɗaya, shekaru sun ja ma amma mutum bai san ya girma ba"
Daddy bai kuma ce mata uffan ba, ya juya ya fice.

Amina tana mopping a babban falo ya fito, kallo ɗaya tayi masa ta fuskanci akwai damuwa, amma bata da ikon magana, haka ya koma nasa sashin.

Babu daɗewa Hajiya Zainab ma ta fito, ta sha uban ado sai ƙamshi take, hannunta riƙe da mukullin mota, sai yatsuna fuska take ta dubi Amina da take ƙarasa mopping ta ce "Idan an tashi girkin rana, ba sai an yi da ni ba,  dinner ayi abinci mara nauyi"

Amina ta ɗan basar ta ce "Shikenan" dan a duniya idan da mutumin da ta tsana bai wuce Hajiya Zainab ba, saboda rashin mutunci da wulaƙancinta.

Fadila ta zuba wa wayarta ido, tun da garin Allah ya wayez tayi salla tayi wanka a ɗakinta ta karya, ta koma kan gadonta ta naɗe take chatting tana game, gaba ɗaya ba ta jin daɗin komai, ta rasa meye yake mata daɗi, Khalil baya nan, ta saba ko baya nan sukan yi chatting amma yanzu taga last seen ɗinsa ya kai 3days,taga alamar kamar ita ma haushinta yake ji.
Ta gaji da latsa wayar, ta ɗauko litattafanta ta fara karantawa, ta tsinci kanta da duba ire iren rubutun da Yazid kan yi mata a cikin littafi. Tayi ajiyar zuciya ta cigaba da karatun ta.

Hajara yau naɗewa tayi taƙi yin aikin komai, wai mura ce take nuƙurƙusarta, dan haka ba zata iya aikin komai ba, ta barwa Amina aikin gida gaba ɗaya, sam hakan bai dami Amina ba, yadda zata ga Daddy ta bashi haƙuri ne ya dameta.

Bayan girkin rana da tayi na duka gidan, ta koma ta ɗora faten wake da dankalin turawa saboda Alhaji Ahmad.

Ta tsara masa abinci, sai dai ta shiga zullumin karta kai masa ya yi mata wulaƙanci, tun da fushi yake da ita.

Ta fara zuba na Baba ta kai masa, sanan ta kaiwa Fadila nata ɗakinta, ta  tarar da Fadilan na toilet tana alwala, ta kalli yadda ta baza liatattafai a kan gado, kamar wata 'yar Nursery.
Ta kalli wani rubutun larabci, da ke rubuce a wani littafi da yake a buɗe.
Amina ta karanta larabcin, kasancewar Amina tana jin larabci kaɗan-kaɗan ya sanya ta fahimci rubutun na soyayya ne, daga ƙarshe ya rubuta sunansa Yazid.
Ɗan shiru Amina tayi tana tunanin a ina ta san wannan sunan na Yazid, jin alamun buɗe ƙofar banɗakin ya sanya Amina saurin ficewa daga ɗakin.

Amina, Tana fitowa taga fitar Alhaji Ahmad, ɗan dafe kanta tayi tana tunanin ina za shi haka bai ci Abinci ba, amma jin ana sallar azahar, ya sanya ta ce ko masallaci za shi.

Ta koma ɗakinta tayi wanka, tayi sallar azahar ita ma, ta canza kaya ta gyara jikinta.

Cikin sa'a da ta kuma fitowa, taga ya dawo, sai dai fuskar nan tasa babu annuri sam, ya wuce sashinsa.

Da sauri ta koma Kitchen, ta haɗo kayan Abinci a tray, har da favorite fruits ɗin sa, ta nufi falonsa tana Addu'a.

Sallama ta yi, amma ta ji shiru ba a amsa ba, tayi addu'a ta shiga, tana fatan Allah ya sa yana falon.
Aikuwa ta hangoshi kwance a kan 3seater, idanunsa a rufe. Ta ƙarasa gabansa ta ajiye trayn a ƙasa.

Ta miƙe ta kalli in da yake kwamce ta ce "Daddy"  ya buɗe idonsa ya kalleta.

"Ga Abincin rana na kawo maka" ya jinjina mata kai ya mayar da idonsa ya rufe.

Amina ta zauna a kan gwiwowinta a hankali ta fara magana "Daddy ka tashi ka ci Abincin"

Ba tare da ya buɗe idonsa ba ya ce "Ki bar shi a wurin zan ci"

A ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ka tashi zaune" sake buɗe idomsa yayi, ya tsareta da ido wanda sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa.

A hankali ya tashi zaune, ya kalli agogon hannunsa, ya fara shirin tashi tsaye, da sauri Amina ta ce "Daddy Abincin fa?"

"Ki bar shi a nan, ranar Alhamis in Allah ya kaimu, ki shirya da wuri, Zakiru zai kai ki ƙauye"

Kan ya tashi tsaye, Amina ta ƙarasa gabansa a kan gwiwowinta ta ce "Dan Allah Daddy, kayi haƙuri, na san ban kyauta ba kana fushi da ni, dan Allah kayi haƙuri"

Kallonta yayi ya ce "Laifin me ki ka yi mini kike bani haƙuri?"

"Daddy na maka laifi mana, baka cancanci in maka magana a yadda nayi maka ba, raina ne ya ɓaci sosai, amma ban kyauta ba, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba"

Ya ɗan girgiza kai ya ce "Hmmm"

"Dan Allah kayi magana, duk na damu da laifin da nayi maka, kayi haƙuri"

"Shikenan ya wuce"

"Ka haƙura?"

"Eh ya wuce"

Ta ɗan marairaice fuska ta ce "kamar ba ka haƙura ba fa"

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Meyasa kika ce haka?"

"Haryanzu ranka a haɗe yake fa"

"To ai bani da lafiya ne, amma nace miki ya wuce ai"

Cikin damuwa ta kalleshi ta ce "Jikin ne haryanzu? Sannu Allah ya baka lafiya"

Ya amsa da Amin.

"To in zuba maka Abincin?" Ya jinjina mata kai. Ta zuba masa Abincin a plate ta saka cokali ta miƙa masa.
Ya karɓa ya kalleta ya ce "Zauna a nan yayi maganar tare da nuna mata kusa da shi a kan kujera.
Ɗan turus tayi tana ganin rashin dacewar hakan. Amma kasancewar shiri take nema, haka ta tashi ta zauna a kusa da shi.

"Amina?".

"Na'am Daddy"

"Banji daɗin abin da ki ka yi mini ba, kema kina cikin masu mini kallon anfi ƙarfina a gidana ko? Duk abin da nake yi, ina da dalili ina ƙoƙarin baki kariya, bana son ki bar gidan nan karatunki ya samu matsala, amma saboda yadda nake da ke kika kalli tsabar idona ki gaya mini magana haka ko Amin? Da wani ne ya mini abin da kika mini saina hukunta shi, ko da kuwa matar gidan nan ce, amma shikenan. Idan kin dawo daga ƙauye upper week zaku tafi Abuja, before na so inje Abujan nima, in ga competitions ɗin naku, dan sun bani invitation as a special guest, amma I don't think zan samu zuwa"

Hawaye ne ya cika idon Amina ta ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri, gaba ɗaya na san ban kyauta ba, amma ba Baba ba, ko kai na gani wani ya maka haka sai inda ƙarfina ya ƙare, Matarka da 'yarka sun tsani Baba, ban san me yayi musu ba, wallahi ko dukana za suyi ba zan damu ba a kan su ci mutuncin Baba, ina jin zafi a raina, amma dan Allah Daddy kayi haƙuri, ba zan sake ba"

Ya kai lomar abinci bakinsa ya haɗiye, sannan ya ce "Ba komai ya wuce"

"To amma naga haryanzu ka haɗe rai"

"Abubuwa da yawa suna damuna, ga kuma yanayin jikina dan haka am not in mood, ai nace ya wuce"

Cikin damuwa ta ce "Sannu Allah ya baka lafiya, Daddy kaje Asibiti"

Ya ce "Zaki rakani?"

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya cigaba da cin abinci, can kuma ya ce "Yauwa, idan zaki tafi ƙauyen me kike ganin za a saya ki kai musu?"

"A'a ba sai an sai musu komai ba" Amina ta faɗa tana ƙoƙarin zuba wa Daddy ruwa.

"Idan zaki tafi ƙauye, me kike ganin ya dace a sai musu?" Ya kuma maimaitawa, hakan ya tabbatar mata he is serious.

Ta ce "Lemo da ayaba"

Ɗagowa yayi ya kalleta ya ce "Dubiya zaki je ko kai ziyara?"

"Ziyara"

"Kuma sai ki kai musu lemo da ayaba?"

Amina ta tura baki ta ce "To ni me zance?"

"Idan ina magana kina cewa ke me zaki ce, zamu ɓata"

"A'a na daina, bana son mu kuma ɓatawa, in muka ɓata ba na jin daɗi"

Murmushi ya yi ya ce "Are You serious?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"To shikenan, ki daina mini abin da zamu yi faɗa"

"In Allah ya yarda na daina Daddy, amma zaka zo wurin taron namu na Abujan?"

Daddy ya ce "Babu tabbas"

"Dan Allah Daddy ka zo, ko ba ka haƙura ba haryanzu?"

"Ai nace miki ya wuce"

"To shikenan, na gode sosai, Baba da kansa yayi mini maganar zuwa Abujan, Allah ya biyaka da Aljanna Daddy, in Allah ya yadda ba zan baku kunya ba, zan yi abin da ya dace"

Yayi murmushi ya ce "Allah ya sa, bayan sallar la'asar ki shirya, zaki rakani ganin likita"

Ta miƙe tsaye ta ce "To, amma me zance wa Baba?"

Ya miƙe ƙafafuwansa ya ce "Baba baya nan a lokacin"

"Ina za shi?"

Daddy ya yamutsa fuska ya ce "Tambayoyinki sun yi yawa"

"To yi haƙuri, na tafi".

Ya jinjina mata kai, tare da lumshe idanunsa"

Ta juya da tray ɗin Abincin ta fita.

A falo tayi kiciɓus da Hajara, Hajara ta dubeta ta ce "Amina daga ina haka?"

"Kaiwa maigidan nan Abinci"

Hajara ta waro ido waje ta ce "Ikon Allah, da kika kai masa kuma shi ne kika zauna kika jira ya gama kika fito da kwanukan, ni fa na zata ma ba kya nan, tun ɗazu nake falon nan ban ga gilmawarki ba"

"Hajara, na kai masa na rana, sai ki kai masa na dare kema" tayi tsaki ta wuce, dan ta fara ƙuluwa da shegen sa idon da Hajara take yi mata.

Amina na tsaye a gaban mudubi, ba wata kwalliya tayi ba, amma tayi kyau sosai, wata doguwar rigar abaya ta saka, wadda Babar Azima ta kuma aiko mata da ita, ta ɗan gyara fuskarta tayi tsaf da ita, ta riƙo wayarta a hannu ta fito falo.

Ko da ta fito ta tarar da Daddy a tsaye yana jiran fitowarta.
Kashe mata ido ɗaya yayi ya ce "You look beautiful in this outfit"

Murmushi Amina tayi ta ce "Thank you Daddy"

Hajara da ta daskare a wuri ɗaya, har ƙara leƙa fuskar Daddy take, dan ta sale tabattarwa kanta abin da take gani ba mafarki bane ba, babban abin da yake sake ɗaure mata kai, wanzuwarta a wurin ba ta sanyawa su bar abin da suke yi, bata ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da taga alamar fita zasu yi tare.

Corridor dake cikin sashin Hajiya Zainab Hajara tabi, ta leƙa dan akwai taga da take kallon wurin parking space, aikuwa idanunta suka dake gane mata Alhaji Ahmad ya buɗewa Amina gaban motarsa ta shige, shima ya zagaya ya shiga ya kunna motar.
Fita tayi da sauri ta nufi falo, taji tamkar taje ta kira Fadila ta ce ta zo taga cin amanar da akewa babarta, amma ta tuna Fadila ta tuna halinta na rashin mutunci, dan a 'yan kwanakin nan ta hanata zuwar mata ɗaki ma gaba ɗaya, Amina ce kawai ke kai mata Abinci idan na zata ci a dining ba, ko kuma gyara mata ɗaki.

Fadila na kwance a kan gadonta kamar mai ciwo, tana chatting a Instagram tana taya wata riga, notification na what's app ya shigo wayarta.
Komawa tayi what's app ɗin dan duba meke faruwa, saboda taga an yi maganganu da yawa a what's app group ɗin su na makaranta.

Da saƙon Captain ta fara cin karo "Yau na haɗu da wani abokina wanda ya san Yazid, ya ce Yazid na Asibiti babu lafiya sosai, ku sa shi a adduoinku Please"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un"




AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL

AREWABOOKS AYSHERCOOL7724
WATPAD AYSHERCOOL7724

43

Gaba ɗaya suka waiwaya dan ganin waye haka? Gaba ɗaya hankalin Amina ya riga ya gama tashi, Hajara ce a tsaye a wurin makunnin ƙwan, ganin duk suna zuba mata ido kuma sai ta hau kame-kame tana faɗin "Amm.... Ban san.."

Ɗauke kai Daddy yayi daga kallon in da Hajara take, ya mayar kan Amina ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Karki manta anjima zan aiko a kai ki banki, a buɗe miki account"

Noƙe faɗa tayi ta ɗan tura baki ta ce "Ni ba zani ba"

"Me kika ce?"

"Bakomai" ta faɗa taka sake tura baki.

Murmushi ya yi ya wuce sashinsa, Amina ta cigaba da mopping ɗin ta suka mayar da Hajar daidai da kujerun da suke falon.
Gaba ɗaya Hajara rasa abin yi tayi, a baya tunane tunanenta sun fi karkata ga zargi, amma a yau ta sake tabattar da abin da ke tsakanin Alhaji Ahmad da Amina wata alaƙa ce mai ƙarfi da girman gaske, wadda da alama alaƙar tayi ƙarfi sosai da sosai.

Kamar yadda Daddy ya ce, da kansa yaje makarantar su Amina, bayan an tashi sukaje banki, aka yi mata duk abinda yakamata, ya saka kuɗi a ciki naira dubu ɗari biyu.

Mamaki ne ya cika Amina ta ce "Daddy wannan maƙudan kuɗin me zan yi da su, idan Baba ya gane fa?"

Daddy ya ce "Ta yaya Baba zai gane, sai dai idan kece zaki gaya masa, kuma ai ba wasu kuɗi ne masu yawa ba, Zakiru zai kai ki ki sayi duk abin da kike so, ban fiye son shiga wurare bane saboda identity ɗina, ba dan ke ba wurare da yawa ba zan iya zuwansu ni kaɗai ba, kuma ni bana son a takura rayuta duk in da zaka sai da masu baka kariya"

"Amma meyasa baka so a ganka? Kar a ganmu tare aje a gayawa Maman su Khalil ko?"

Ya ce "Eh, kin san bana son ɓacin ranta da damuwarta"

"Eh amma ni kana son ganin nawa" tayi maganar da iya gaskiyarta.

"Mhmm, me yasa kike haɗa kanki da ita? Ita matata ce ke kuma"
Sai yayi shiru.

A ƙule Amina ta ce "Eh ita matarka ce, ni kuma 'yar aiki ba talaka mara galihu"

"Yauwa Ashe kin sani, amma ni bance miki talaka mara galihu ba" yayi maganar da salon ya sake kunna Amina.

Aikuwa ta kai ƙololuwa dan taji haushi ba kaɗan ba.

"Banda rigima irin taki, ina na taɓa ganin wannan ƙarfin hali in ba a wurinki ba, nace kina son mijinta kince me zaki da tsoho".

Cikin tsiwa ta ce "Allah ya kiyaye in yi kishi da wannan matar, ta kasheni da bala'i wadda ba ta san darajar ɗan Adam ba"

"Zaki fara ko? Ban gaya miki bana so ki dinga duk wata magana da zata shafi matata ba".

Amina ta ce "Amma ai kai ka fara bani ba, wallahi Daddy seriously yakamata ka kula sosai, Allah ya baka dukiyar da zaka amfanar da al'umma, amma an gindayeta wuri ɗaya daga ita sai iyalanta, duk wanda ya raɓoka zai mora an dinga yi masa gori kenan da kallon banza, wallahi idan baka gina lahirarka ba daga ranar da ka mutu, wanan dukiyar aka raba musu, su sadaka ma Allah ya kai ladan kabarinka sai wanda ya dubi Allah.
Na san naganganuna sun yi tsauri da yawa, amma dan Allah kayi haƙuri Daddy, wallahi gaskiya nake gaya maka. Dan Allah yanzu dan Allah ya baku arziki ya dace aje aci mutuncin 'yar mutane dan Khalil ya ce yana sonta, ba a gabana aka yi ba, amma yadda ya zo yana faɗar zancen naji zafi sosai saboda nima tsatson talaka ce, da na motsa a gidan nan sai kyara da gori, wallahi Daddy kaf mutanen da ke aiki a cikin gidanka suna yi ne dan basu da wata sana'ar da zasu samu su rufawa kansu asiri, ban da haka mai zai sa ka zauna a gabanka ana kiran mahaifinka nusari, soko da sauran miyagun maganganu?" Ta ƙarasa maganar hawaye mai ƙarfi suka ƙwace mata.
Ba ƙaramin tasiri maganganun Amina suka yi a zuciyarsa ba, duk da ba wata babba bace ba, amna wasu lokutan tana da matukar hangen nesa da son faɗar gaskiya. Yana jinta tana kukan Amma bai rarrasheta ba kuma bai ce mata komaia ba, har tayi ta gama tayi shiru.

Wasa² rashin sanin halin da Yazid yake ciki ya addabi Fadila, tun

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment