Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi salla, in ƙarasa ayyukan gidan".

Mama ta ce "Ai na gama komai ma, kiyi wanka ki ci Abincin".

Hafsa ta ce "Mama, ba ki da lafiya ki kayi aikin, da kin bari na dawo ai".

"A'a babu komai ai, na ji daɗin jikina Alhamdilillah".

"To Allah ya ƙara afuwa, bari in yi wankan".

"To shikenan" Mama ta amsa tana ƙoƙarin miƙewa daga kan sallayar.

****************
Kimanin kwanaki huɗu kenan da Amina ta yiwa Baba waya akan kuɗin jarrabawarta, amma shiru bai yi mata aike ba, hakan ya ƙara tabattar mata da ba shi da kuɗin ne, ga wannan 'yan uwan na sa, suna da shi ba basu da shi ba, amma ta san ko giya ta ke sha, ba ta isa ta tunkaresu da wani batu akan makarantar boko ba. Dan sun ɗau karatun bokon 'ya mace kamar wani karatun saɓon Allah, mussaman ita da suka sanyawa ido, suna ganin mahaifinta ya bata goyon baya ta cigaba da yawon boko, ya ƙi yi mata Aure, duk sa'aninta duk sun yi Aure, dan galibi tun a sha uku wasu ake aurar da su. Ita kuwa har yanzu babu ma batun Auren a gabanta, ta ƙi bawa kowa dama balle a nemi Aurenta.
  Misalin ƙarfe biyar na yammaci, Amina tana kan hanyarta ta dawowa gida da ga makarantar allo, ita kanta makarantar Allon duk babu sa'anninta, sai ƙannenta amma hakan bai dameta ba sam, haka ta ke shiryawa ta tafi makarantar allo idan ta dawo daga ta boko, ita ma a makarantar bokon ma ana yi musu ƙarin litattafan addini sosai, hakan ya sa a ilimin addini ma daidai gwargwado ta samu.
   "Kula mana karki faɗi". Da sauri ta dawo da ga duniyar tunanin da ta tafi, ta kalli mutumin da suka kusa yin karo da juna.
"Yi haƙuri"  shine abunda ta furta ta na ƙoƙarin wuce Mutumin.
Mutumin ya yi murmushi ya ce "Aminatu, ba gaisuwa ne?"
"Ina wuni" ta faɗa a daƙile, dan ba ta son doguwar magana, kowani abu da zai haɗata da shi sam.

"Lafiya ƙalau,ya Baban ki ko har yanzu bai shigo gari ba?".

"Eh bai shigo ba".

"Yawwa Amina, ni na gode Allah ma da yasa muka haɗu Yanzu, Amina ya Maganar mu ta kwanaki da na taɓa yi miki ne? Kinga yanzu lokacin kaka ne, da 'yan kuɗaɗena a hannuna, anyi mini girbi amfanin gona yayi kyau sosai, ki bani dama inje in ga babanki ayi Maganar Aurenmu".

Ta kalle shi, fuskarta babu walwala ta ce "Idan ka Aureni kakar kuma ta wuce fa? Da me zaka riƙeni?" Ta yi maganar tana watsa masa wani mugun kallo.

Mutumin ya gyara tsayuwarsa ya ce "Amina, kamar ba ki san waye ni a garin nan ba, ina da tarin gonaki da dabbobi, wanda ke kanki kin san ni ba talaka ba ne, yanzu haka wani daga cikin amfanin gona da na siyar, baki ga kuɗin da na sake tarawa ba, noman bana ba abin da zamu ce da Allah sai godiya".

Amina ta yamutse fuska ta ce. "To ina ruwana da kuɗinka? Kuɗin da ba cib
ake yi ba, kamar yadda na gaya maka a baya, yanzu ma zan maimaita maka ne, ni ba zan iya Auren ka ba, ka mini tsufa, duk garin nan ba wanda bai san ka akan auri saki ba, duk shekara lokacin kaka, sai ka yi Aure ka saki wasu, 'ya'ya a gidanka kamar babu me su dan yawa, sunata gararanba a gari, ba kulawa, nima haka ka ke so ka Aureni ka sakeni da 'ya'ya? Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga a cikin 'ya'yanka ma akawai ƙawata ai ana barin halak da kunya ma.
Ka dinga duba makomar wadda zaka aura, da tarin 'ya'yanka, sannan ni karatuna shine ya dameni ba aure ba a yanzu, dan haka dan Allah ka ƙyaleni".

Galala ya bi Amina da kallo, be taɓa zaton tana da baki haka ba, duba da ƙarancin shekarunta.

"Ke Yanzu kin gwammace ki tsufa a gari, ba kiyi aure ba? Kuma aike zan kashe miki kuɗi sosai, sai gidan da kike so zan sai miki, ba a cikin iyalina zan haɗaki ba".

"In dai Auren irin ka ne, da shi gara babu Wallahi, ni ka ga tafiyata ma" ba ta kuma saurarsa ba, ta tafi ta bar shi a gurin a tsaye cike da takaici.

**************
Mummy ce ta fito Falo, cikin wata dakakkiyar shadda ruwan toka, ta sha stone work, wuyanta zuwa hannunta duk gold ne, hannunta riƙe da mayafinta da jakarta.
A falo ta tarar da wata mata da yara guda biyu, kai da ganin matar ka san a wahala take, saboda yadda suke sanye da kaya tamkar tsumma, saboda koɗewa.
A wulaƙance Hajiya Zainab, wato Mummy ta bisu da kallo, ya yin da suka risina suna gaisheta.

Ba ta amsa ba, ta ce "Lafiya daga ina?"

Matar ta risuna ta ce "Hajiya baki gane ni ba? Azumi ce maƙociyarku ta nan bayan layi".

Mummy ta sake ɓata fuska ta ce "Ohhh, sai yanzu na gane ki, ke ɗin ce kullum ƙara lalacewa ki ke kina ƙara muni, lafiya kuwa?"

"Hajiya taimakon nan dai da ki ka saba, shine na sake zuwa yau ma a taimaka, Wallahi marayuna ne yau kwana uku ba abin da na iya ba su suka ci, su masu sickler ga ciwo ya tashi, ga babu Abinci, na buga na buga na rasa yadda zan yi, shine na ce bari in zo don Allah ko ƙanzo ne ki taimaka ki bani in ba su" ta ƙarasa maganar ta na fashewa da kuka.

"Ya isa ni dan Allah yi mini shiru, ku zo ku takurawa mutane, kuna wani kuka kamar ragon mayya ku a dole sai anji tausayinku, ku haifi yara kaɗan ba zaku iya ba, ku daɗi miji su yi ta kwanciya da ku kuna haihuwa, ƙarshe ko su gudu ko su mutu su barku da 'ya 'ya".

Fadila ce ta fito ita kuma cikin wani tsadadden material me kyau, tana faɗin "Mummy am ready" tana ganin su Azumi a falo, ta yi turus tare da toshe hanci ta ce "Mummy Warin meye haka?, su kuma wannan mai suke yi mana haka a falo?".

A wulaƙance Hajiya Zainab ta ce "Wai yau ma dawowa ta kuma yi, ta na neman taimako".

"Kuma shi ne za su shigo mana falo, sai warin datti suke yi, mai yasa ba su zauna a waje ba in kin fito kya same su?"

"To ya zan yi? Wannan sakaran mai gadin ya buɗe musu sun shigo".

Cike da ƙyama Fadila ta ce "dan Allah ku ɗan jirata a haraba mana, wannan gaba ɗaya kun canza tempreture ɗakin kamar zan yi amai. Ke wa kuke da suna Asabe ki ke kowa? Wata a cikin ku ta zo ta sake mopping ɗin ɗakin nan, a kunna turaren wuta".

Azumi ta ji haushin abun da Fadila ta yi mata, ita da babarta amma babu yadda ta iya, haka ta koma waje ta jira.

Duk wannan wulaƙanci da cin zarafin, dubu biyu kacal Hajiya Zainab ta iya bawa Azumi, wanda sai da Azumin ta durƙusa tana mata godiya.

Suna tafe a mota, Mummy na cigaba da mita, da nuna tsantsar ƙyamarta ga talaka, tare da nuna kamar iyawarta ce ta sa Allah yayi ta a cikin daula.

********
Abun duniya ya saka Amina a gaba, yau saura kwanaki uku ya rage, a rufe karɓar kuɗin jarrabawar su, gaba ɗaya ta sare, ta san Baba ba shi da kuɗin nan ne, dan da akwai su da tuni ya aiko mata da su.
Gefe guda baba Rabi'u ya uzzurawa rayuwarta da takura, akan Lallai sai ta amince da shi, ta yadda ya aureta.
   Fafur ita kuma ta ce ko maza sun ƙare, ba zata auri tsohon da bai san darajar mace ba, balle 'ya'yan da yake haifa.
Ga matsin lamba na gidansu, daga ɓangaren 'yan uwan mahaifinta, na takura da aike saka ta aiki kamar baiwarsu, ga gore-gore, har da sharrin yawon banza ta ke yi a gantalin makarantar bokon da ke yi.
Hakan ya haifarwa Amina shiga cikin matsananciyar damuwa, da tunani daban-daban a cikin ranta.
  

     Baba Hassan kuwa, ya yanke shawarar kiran maigidan a waya, wato baban Fadila kasancewar ba ya gari, ya roƙi Alfarmar ko a cikin albashinsa ne, a taimaka a bashi rancen kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin Makaranta.
Haka kuwa aka yi, ya kira maigidan ya sanar masa da halin da yake ciki, da buƙatar da yake da ita, ba tare da wani ɓata lokaci ba ya ce masa 'Zai kira Hajiya a waya ya sanar mata, ya je ya karɓa kawai a biya mata'.
Baba Hassan ya yi farinciki matuƙa, yayi ta godiya da karamcin Alhaji Ahmad, sai dai yadda zai tunkari Hajiya Zainab da maganar kuɗin kawai yake tunani, saboda rijiya ta sha bada ruwa guga ya hana a gidan nan.
Ƙiri-ƙiri mai gidan zai yi alheri ta hana, ko ya ce ayi taƙi yi, kusan duk me son wani abu agurinsa sai ya biyo ta hannun hajiya Zainab, idan kuwa ka na son abun a gurinta, sai ka ƙasƙantar da kanka tamkar bawa, ta gama wulaƙantaka kafin ka samu.

AMINU KANO, INTERNATIONAL AIRPORT.

Tafiya yake sannu a hankali, yana jan wata 'yar madaidaiciyar Akwati, hannusa ɗaya ɗauke da wayarsa ya kara ta a kunnensa yana tsumayin a ɗaga wayar da yake kira.

A ɗan hasale ya fara Magana "Wai dan Allah kana ina ne? Na sauka fa ina sauri inje gida, ni da nasan haka zaka yi mini, da babu abun da zai sa in ce kazo ka ɗaukeni" Yana gama maganar, ya sauke wayar zuwa cikin aljihunsa, yana jan guntun tsaki.

Sannu a hankali ya cigaba da tafiya, ba tsammani ya ji an ce "To shugaban masu haƙuri, ina daf da kai fa, amma ka kirani kana ta wannan masifar haka" Ya kalli Matashin da yake maganar ya ce "Dalla ware malam, kana sane ma ka shanyani kenan? Dana sani gida na yi waya azo a ɗaukeni".

Matashin yayi murmushi ya ce "Kai dai can da yawarka, masifaffe kawai, bani in tayaka ɗaukar jakar".

Ba tare da ya ce masa komai ba, ya sakar masa akwatin, yayi gaba abunsa.

Suna tafe a mota, ba wanda yake magana a cikinsu, can ɗayan ya kalli abokin tafiyar tasa ya ce "Haba Khalil, ka ɗan yi murmushi mana, ko har yanzu fushin ne?"

"Ban sani ba, ni dalla ka ƙara speed ɗin motar nan, mu yi muje gida".

"Ba zan ƙara ba, in ban sauke ka a titi ka hau Napep ba ba sunana Abdul ba"

Khalil ya ce "Saboda na hau motarka ka ke mini rashin mutunci?".

"Eh, uban waye ya sa ka kirani? na zo na taimaka maka amma kana mini wulaƙanci".

Jinjina kai Khalil Yayi ya ce "Good".

A bakin gate ɗin gidansu Khalil Abdul yayi parking, ya kalli Khalil Ya ce

"Mun zo sai ka sauka".

"Wai a nan zaka ajiyeni?".

Abdul Ya ce "Au ban maka ba? Wai kai mai yasa ba a iya maka ne? Ware Malam"

"Wallahi zaka gane ba ka da wayo, zan zo har gida in maka rashin mutunci"

Abdul ya ce "Rashin mutunci yau ka fara yi mini? dalla fita".

Ƙwafa kawai Khalil yayi, ya fice da ga motar.

Asabe ce ta shiga ɗakin Fadila, za ta gyara mata, tana gyaran tana mita ƙasa-ƙasa saboda yadda Fadila ta ke watsar da komai a ɗakin yadda ta ga dama. Hatta kwano sai ta ci Abinci ba zata ɗauke ba sai an ɗauke mata. "Dan Allah kalli ɗakin nan kamar sheƙar mahaukaciya, yarinya ta na mace amma ba ta san gyara ba, saboda tsabar sangarta da iskanci, ɗan kanfai ma, sai da ta saka ta tara sai mun wanke mata, Aikin banza kawai" haka Asabe ta cigaba da tattare shirgin da Fadila ta tara a ɗakin na ta, ta gyara ta wanke mata banɗaki, tare da wanke mata ƙananan kayanta da ta tara a cikin bokiti a banɗaki".

Asabe na kammalawa ta fito falo, ta tarar da Fadila ta na kallo, a wulaƙance Fadila ta kalli Asabe ta ce "ki cewa wannan wadda ku ke aikin tare, meye sunanta Hajara kowa? Za ta bar uwarta da yunwa ne, kamar yadda ta yi mini? Ta bar ni ina jiran ta kawo mini Abinci amma shiru".

Asabe ta risuna ta ce "zan gayamata insha Allah".

"Kar ki kuskura ki sake zuwa gabana da wannan ƙazamin hijjabin, ba kya jin yadda yake wari ne?"

Wani irin haushi ya kama Asabe, amma haka ta dake ta ce "To insha Allah"

Asabe na zuwa ɗakin girki, ta tarar da Hajara na ta ƙoƙarin haɗowa Fadila Abinci, ta kalli Hajara ta ce "Ance idan uwarki ce za ki bar ta da yunwa?"

Hajara ta kalli Asabe ta ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda aka ce in gaya miki"

Jiki a sanyaye Hajara ta ce "Allah ya bamu abun yi mu bar aiki a ƙarƙashin mutane marasa mutunci irin wannan, tun da na shigo gurin nan fa aikin Abincin nake"

"Hmm, ke dai bari, ni kaina na gaji, da ina da wata hanyar samun kuɗin, da tuni na bar gidan nan".

Haka suka cigaba da tattauna matsalolin gidan aikin nasu.

Bayan saukarsa daga motar Abdul, gate ɗin gidan ya nufa, ya na zuwa ya tura ƙofar gate ɗin ya ga ta buɗe.

Baba Hassan ya taso yana faɗin "Waye a nan?"

"Baba ni ne" Khalil ya furta a hankali.

Murmushin fuskar Baba Hassan ya faɗaɗa da yaga Khalil ya ce "Kai ne da zuwa haka ba sanarwa? Maimakon ka kira a zo a ɗauke ka".

"Bakomai Baba, Abdul ne ya ɗakko ni na same ku ƙalau?".

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya aikin?"

"Aiki Alhamdilillah".

Baba Hassan ya ce "bari in kai maka jakar"

Khalil ya ce "A'a ka bar shi Baba, na gode, kayi zamanka"

Khalil ya nufi cikin gidan.

"Oh my God Mummy brother" Fadila ta faɗa da ƙarfi, tana maƙalƙale Khalil.

Tureta Khalil yayi ya ce "Ni cikani kar ki kada ni".

Mummy ce ta fito tana faɗin "Au, ashe da gaske kike, wane irin zuwa ne wannan ba sanarwa a safiyar nan, kamar korarre?"

Khalil yayi murmushi ya ce "Mummy kullum idan zan shigo kuma sai na faɗa?".

"Ahh ai sanarwar yana da kyau, amma dai ba wannan babur ɗin ɗan sahun ka hawo ka dawo gida ba ko? Kar kasa maƙota su mana dariya"

"Mummy kenan, Abdul ne ya ɗakkoni daga filin jirgi".

Fadila ta tura baki ta ce "Sai murna na ke ka dawo, amma ko kallo ban isheka ba".

"To zan ɗauke ki ne ina ihu nima?"

Mummy ta ce "Amma yadda ta damu da kai ɗin nan, ai yakamata kaima ka nuna mata ka damu da ita".

Khalil ya ce "waye zai damu da wannan fitsararriyar? Bari in tafi ɗakina in ɗan watsa ruwa in huta".

Mummy ta ce "Bari a saka masu aikin nan su gyara maka, na san yayi ƙura, tun da saukar safe kayi, akwai sauran kayan karin kumallo, sai ka karya"

Ya ce "Ok shikenan".

Ya tashi ya tafi dining, ya zuba abinci yana ci, Fadila sai surutu ta ke masa".

Zuwa ƙarfe huɗu na yammaci, Khalil ya shirya cikin ƙananan kaya ya fice, da ƙudurin tafiya gidan su Abdul ya je ya ƙare masa rashin mutunci.

Yau kwana guda, da Baba ya roƙi Alhaji Ahamad kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin jarrabawa, kuma ya bashi damar ya karɓa a gurin matar gidan, amma sanin halinta ya sanya shi a fargabar yadda zai tunkare ta da wannan maganar.
Amma a rashin tayi akan bar arha, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya nemi Alfarmar, ko Allah yasa ya dace.

Jiki ba ƙwari, ƙasan zuciyarsa yana Addu'a, ya tunkari babban falon gidan.
Da sallama ya shiga falon, sai dai duk da girman nan nasa da shekarunsa, baya hana shi shiga fargaba, idan har yayi tozali da Fadila, saboda gudun tozarci da wulaƙanci, kamar yadda ta kasance yanzu, ya tarar da ita hakimce a falon tana aikin na ta, na danna waya wanda a shi tafi ƙwarewa, danna waya kallon talabijin kai lomar Abinci sai kuma bacci da tarin rashin mutunci.

"Barka da yamma ranki ya daɗe" Baba yayi Maganar yana risunawa.
Ba ta ɗago ta kalleshi ba ta amsa sa da 'Yawwa'.

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Dan Allah hajiya fa".

"Tana sashinta".

'Dama Alhaji ne ya aiko ni gurinta".

"Sai ka zauna ka jirata, sai ta fito".

Bai ce komai ba, ya rakuɓe a falon, yana rarraba ido.

Fadila ta kara waya a kunneta tare da faɗin "Uwar bacci, tun ɗazu na ke kiranki a waya, amma shiru ba kya ɗagawa, dama ce miki zan Brother ya shigo gari fa, gara ki shirya ki bayyana".

"Girl are you serious?".

"Amma kin san bana miki wasa a irin wannan lamarin ko".

"Wow, Alhamdilillah aikuwa zaki ganni yanzun nan" suka yi shewa a tare, sannan suka yi sallama.

Baba Hassan tun yana zaman da marmari, sai da ƙafafunsa suka yi sanyi, ya gaji sosai, dan a ƙalla ya kai awa guda a zaune.

Ba tsammani sai ga Hajiya Zainab ta fito, ita ma ɗauke da waya a kunnenta.

Ta zauna ta cigaba da wayarta, ba tare da ta saurari in da Baba Hassan yake zaune ba, hirar kasuwancinta kawai take yi, tare da ambaton Manyan kuɗaɗe a cikin wayar.

Sai da ta ƙare wayarta sannan ta kalleshi ta ce "Malam lafiya ka shigo mini falo ka ƙwafe haka kamar ana zaman fada?".

Baba Hassan ya gyara zamansa ya ce "Amm, dama gurinki na zo Hajiya, Alhaji ne ya aiko ni".

"Ya aiko ka, ya ce me?"

"Dama na kira shi a waya ne, yarinyata zata zana jarrabawa, bani da kuɗi, shine ya ce in zo in karɓa a gurinki".

"Kai kuwa malam Hassan, yakamata ka dinga jin tsoron Allah, yaushe aka baka albashi har da zaka dawo ka ce ga zance ga magana?"

Cikin rauni Baba Hassan ya ce "Dan Allah Hajiya ki taimaka, ni ko rance ne, bana son karatun 'ya ta ya samu naƙasu, idan ya so sai a cire a albashi na".

"Allah wadaran halin talaka, sam ba ku da godiyar Allah, mutum ko naman jikinsa ya ke yanka yana baku ba zaku gode ba. To ni bani da cash a hannuna, sai ka haƙura sai zuwa lokacin da aka ɗakko mini kuɗi a banki".

Ya sake duƙawa ya ce "Hajiya ki taimaka, za su rufe karɓar kuɗin ne".

Fadila a ƙufule ta ce "wai baka ganewa ne? Babu kuɗi a hannunta Yanzu, amma sai magiya ka ke".

Baba Hassan ya ce "to shikenan Hajiya, Na gode" ya tashi jiki a sanyaye ya bar Falon.

********

Zuwa yanzu Amina ta gama fidda rai da samun kuɗin da zata biya na jarrabawa, dan yanzu haka tana zuwa makaranta ne kawai, kafin wanɗanda suka biya kuɗin jarrabawar su fara.
Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, haka take tafiyar, tana ƙoƙarin shiga gida ta hangi Kawu Bala, a ƙofar gida yana alwala, kai da ganin alwalar ta sa kasan jahilci ya samu gindin zama a tare da shi, saboda yadda watsa ruwan alwalar nan ko ta ina.
Tana ƙoƙarin durƙusawa ta gaishe shi cikin masifa ya ce "Ke Amina zo nan".

Ba musu ta zo ta durƙusa ta ce "Gani kawu".

"Da ga gidan ubanwa ki ke?".

"Daga makaranta"

"Yawon barbaɗa da ta zubar ba?" Kallon Kawu Bala tayi, tare da jin haushin mummunar kalmar ta zubar da ya jinginata da ita.

Ya kalleta ya ce "Ina son sanin dalilin da yasa, Malam Rabi'u ya nuna yana sonki, amma dan iskanci ki ka yi masa rashin mutunci".

Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Kawu, ta yaya zan iya Aurensa, mata nawa ya aura ya saka a garin nan? Kalli yadda yaransa suke babu cikakkiyar kulawa, idan na Aureshi yayi yaya dani? Kuma ban fa gama Makaranta ba har yanzu".

"Kinga idan na kuma magana kika yi mini zancen bokon nan, saina karairaya ki, shashasha mara kan gado, na fuskanci akan bokon nan kike wannan iskancin, na fuskanci a can suke hure miki kunne, to ba zai yuwu ba, ubanki ya tsallake ya tafi nasa guri ya bar mu da ke, ke kuma ki ɗakko mana abun kunya ba, saboda wata boko ba, dan haka daga yau na kuma ganin kin je makarantar boko, Wallahi sai na saɓa miki kin ji na gaya miki.
Kuma kiji da kunnenki, zamu karɓi kuɗin Auren Malam Rabi'u, ba zaki cigaba da gandamewa a gida ba, sa'oinki na gidan Aure suna neman aljanna, ke kuma kina tamɓele a titi da uwar jaka da sunan boko, shegiyar bokon da ke ba kuɗi a ke baki ba sai wahala, da wannan wahalar banzar gara in ba zaki yi Auren ba, ki shiga cikin maza a dinga zuwa da ke gona kina noma".

Tuni hawaye ya wankewa Amina fuska ta ce "Dan Allah kawu kayi haƙuri, ku bari in ƙarasa makaranta, ko ina gamawa ne sai in yi Auren, in ya so ku aura mini wanda ku ke so, amma banda Malam Rabi'u dan Allah".

"Au ke zaki faɗi abunda ki ke so ayi?, ai kuwa ba ki isa ba, ko Hassan ubanki bai isa ya ja da maganata ba balle ke, tashi ki bani guri, Allah ya ƙara nuna mini kin fita daga cikin gidan nan da sunan wata makaranta, wuce ki bani guri, da ido kamar gujjiyar mayu".

Cikin kuka Amina ta shiga cikin gida, kai tsaye ɓangarensu ta wuce, ta tarar da Inno tana surfe.
Sakin taɓaryar Inno ta yi, ta nufo in da Amina ta shigo tana kuka, tare da faɗin "Ke Amina lafiya? Waye ya rasu kike wannan kukan?".

Cikin kuka Amina ta ce "Kawu Bala ne wai ya ce kar in sake zuwa makarantar boko, wai Aure za suyi mini".

Tsaki Inno tayi ta ce "Shine za ki shigo kina mini wannan uban ihun, bokon banza da na wofi, matsa daga kusa da ni kar in makeki".

"Haba Inno, kema haka zaki ce? Yanzu kin yarda su aura mini Malam Rabi'u baban su Furera?"

Zaro ido Inno tayi ta ce "Malam Rabi'u kuma? Wannan mara mutuncin?"

"Shi fa, kawu Bala ya ce wai za su karɓi kuɗinsa na Aurena".

Jiki a sanyaye Inno ta ce "To Amina kiyi haƙuri, kin san duk gidan nan babu wanda yake musu da Kawu Bala, ciki kuwa har da mahaifinki, shi yasa na so kafin su farga su yanke makamancin wannan hukuncin, ki fitar da mijin Aure, amma yanzu lokaci ya ƙure Amina, kin san tun da ya waiwaye ki ba wanda ya isa ya sanya shi canza Magana".

Amina ta ɗora hannu a ka, ta zunduma ihu ta durƙusa a gurin ta na faɗin "Wallahi idan aka aura mini mutumin nan an gama da rayuwata, sunana bazawara, dan Allah ku ƙyaleni in yi karatuna".

Inno ta ce ki rufa mana Asiri, kar ki sa su ɗauka wani abun ne, ki sa su shigo su yi mana tijara".

Miƙewa Amina tayi ta shige ɗakinsu, tana cigaba da kuka har cikin ranta.

********

Tamkar wasu taɓaɓɓu haka suke ta shewa a falon.
Wata siriyar yarinya ce Kamar Fadila, cikin skirt high west, da wata body hook, sai hula a kanta, ta yi simple make up.
Hatta yanayin rawar kanta da iyayinta irin na Fadila ne. Dama hausawa suka ce, sai hali yazo ɗaya ake abota.
Fadila ta kalli ƙawar tata ta ce "Yusra kin ga yadda ki kayi kyau kuwa? Ni kaina na yaba, ina ga shi wanda aka yiwa kwalliyar?".

Yusra ta ce "Girl brother nan naki sai a hankali, Allah ya sa in ishe shi kallo".

Fadila ta ce "dalla kar ki damu, zai yaba haba sai kace ba namiji ba, dole ya ƙyasa, yanzun nan zai shigo, muje ɗakina in ƙara gyara miki kwalliyar nan, a ƙara powder da turare".

Haka kuwa aka yi, suka shiga ɗakin Fadila, da yake Fadila gwanace gurin kwalliya da gyaran jikinta, tsaftar muhalli ce komai sai dai ayi mata.

Yusra ta kuma fitowa ta yi ras da Ita, suka dawo falo suka cigaba da hira.

Suna tsaka da hirar ne, suka ji shigowar mota gidan, Fadila ta leƙa ta window, da sauri ta dawo tana faɗin "Girl, gashi nan, shine ya dawo".

Cikin hanzari Yusra ta sake feffesa turare, da sake gyara zama.

Khalil ne ya shigo falon, hannunsa riƙe da wayarsa da makullin mota.

Yana shigowa gaba ɗaya Yusra ta rasa nutsuwarta, saboda tsananin kwarjinin da Khalil yake da shi.

"Ina wuni Brother" Yusra ta faɗa cikin fargaba.

"Yawwa sannunki" ya amsa yana ƙoƙarin shigewa.

Fadila ta ce "Brother, baka gane ta bane? Yusra ce fa".

Khalil yayi murmushi ya ce "Na ganeta mana, ai nace mata Hi ko?".

Yayi Maganar yana hararar Fadila.

Ba Yusra ba, Fadila kanta ta ji haushin yadda Khalil y nunawa ƙawarta halin ko in kula, duk da wannan tarin hoda da turare da ta saka saboda shi.

Gyara sharhi ko shawara
08081012143
Ayi following account ɗina a Arewabooks@ Ayshercool7724
Da kuma Watpad Ayshercool 7724

Share Please 🙏


GABA DA GABANTA

       Page3

             
By Aisha Adam (Ayshercool)

(Shin kin karanta littafin DARE DA DUHU?,

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment