Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hira kasancewar Inno ta san garinsu Zakiru yayarta tana aure a can.

Mutane sai shigowa suke suna sun zo yiwa Amina sannu da zuwa, nan kuwa gulma suke zuwa yi, suna ta maganganun Amina ta zama ƙatuwa, gashi ta yi fresh ta zama 'yar gayu, ga uwar waya a hannunta.

Zakiru ya kalli Amina ya ce "Amina ko zaki haɗani da wanda zasu tayani kwaso kayan da ke motar"

Amina ta miƙe tana faɗin "Ai ko nima sai in ɗauka"

Ya kalleta ya ce "Ki ɗauki me? Zo muje ki gani fa" Amina tabi bayan zakiru zuwa mota.

Ya saka hannu ya buɗe mata boot, waro ido tayi ta buɗe baki da tayi tozali da abin da ke cikin Boot ɗin.

Kayan Abinci ne kamar za a buɗe kanti, ta kalli Zakiru ta ce "Zakiru, wannan fa?"

"Aike Amina kin ciri tuta a gidan nan, shekaranjiya ya saka na ɗau motar nan muke je da shi muka sayo, jiya da daddare ya ce mini a wannan motar zamu tafi, kar in bari ki san da kayan"

"Na shigesu ni Amina, Zakiru kalli uban kayan fa"

"Ke ki gode Allah, Allah ne ya baki, da waccan matar ta sani ba zata bari a baki ba"

Amina ta ce "Zakiru kaima ka ɗiba"

"A'a nima ya sallameni, bari in kira wasu su tayani"

Haka aka dinga kwasar kaya ana shiga da su gidan su Amina, nan da nan sai ga matan su Baffa Lawan da yaransu sun cika gidan suma.

Sai da Zakiru ya tabattar da an gama kwashe kayan an shiga da su, yayi musu sallama ya ajiye musu bandir kuɗi ya ce in ji Alhaji Ahmad.

Gaba ɗaya Mamaki ya gama kashe Amina, amma ta basar kamar bata wani damu ba.

"Ohh Amina, kalli yadda kika koma, lallai yanzu kin wuce ajin Jarmai, birni ya karɓeki" Cewar Amaryar Kawu Bala.

Suka yi ta yaba Amina, suna son jin ƙwaƙwaf, ance musu gidan da Baba yake aiki a nan Amina ma take yi, amma shi tun da yake bai taɓa zuwa da wanan kayan ba, kuma ba a taɓa kawoshi a irin wannan mota ba sai Amina. Suna ta son su tanbaya suyi tsegumi, amma Amina ta haɗe rai ta haye Gadon Inno tana latsa wayarta, dan ba zata manta wulaƙanci da rashin mutuncin da suka dinga mata ba a baya.


Gaba ɗaya Fadila ji daɗin reaction ɗin da Yazid yayi ba, ji tayi gaba ɗaya bata son zaman makarantar, dan haka ta ɗauki motarta ta wuce gida.


Zuwa azahar sai ga su Baffa Lawan, an je har Gona an sanar da su, ga Amina can an kawota a wata ƙatuwar mota daga birni.
Basu ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka ɓangaren su Amina, suka tarar da uban kayan Abinci fal tsakar gida, cikin ɗaki kuma kayan sawa ne da kayan ciye-ciyen da Daddy ya saiwa Amina.

"Ke ina Aminar take, wanann kayan kuma na menene?" Cewar Baffa lawan yana shafa buhun shinkafa.

Inno ta ce "Bismillah Baffa ku shigo"

"Ba zamu shigo ɗin ba, ina Hassan ɗin ma tukuna?"
Inno ta fito tare da faɗin "Ai ita kaɗai ta dawo ban da shi, shi ya zazzo a 'yan kwanakin nan"

Bala ya ce "Ina Aminar ne?"

"Tana ɗaki"

"Eh lallai, rashin tarbiyyar ta ta har ta kai ta kasa fitowa ta gaishe mu?"

Inno ta ce "A'a ba haka bane ba, ke Amina fito mana" banda Inno ta saka baki babu abin da zai sanya Amina ta fito.

Gaba ɗaya suka bi ƙofar ɗakin Inno da kallo, Amina ta yi ƙiba, fatarta ta ƙara haske.

"Ina wuninku"

Kawu Bala ya riƙe baki ya ce "Ba shakka, yanzu dama irin wannan rayuwar Hassan ya zaɓi kiyi, shi ya sanya ya tattaraki ya kai ki birni? Ko in ce kuka haɗa baki kika gudu, yawon ta zubar ai shikenan gaki ga duniyar nan, kin ƙi sunnar ma'aiki kin shiga duniya bin yaran yahudawa"

"Kawu Bala, Tazubar kuma?"

"Eh yawon ta zubar mana, idan ba haka ba wani irin aiki ne kike yi haka da kika samo wannan kayan, tun da uban naki yake aikin a birni ya taɓa zuwa da makamancin haka ne?"

Ran Amina yayi bala'in ɓaci, kawai ta tashi ta bar musu tsakar gidan, dan idan ta cigaba da zama zata iya rama cin zarafin da suke mata.

"Ka gani ko Yaya Bala, wai mu muke mata magana ta tashi ta tafi, idan ba bariki ba mai zai kawo haka?" Ita dai Inno tayi mus shiru, suka gama cin mutuncinsu suka tafi.

Inno ta koma ta samu Amina a ɗaki ta ce "Amina kiyi haƙuri, wallahi tun da kika tafi suke surutai da ƙanann maganganu"

Amina ta ce "Aikuwa sai sai suyi, dan bani da lokacinsu, na gaba ya riga yayi gaba, kuma Inno a ɗibar musu wani daga kayan Abincin nan a basu, aniyarsu ta bisu"

Da yamma Amina ta shirya, ta tafi sada zumunci wurin sauran 'yan uwa, kowa sai son ya ganta yake yi, masu ƙananan maganganu kuma suka cigaba da yi.
Su Bala kuwa da aka ɗebi kayan Abinci aka basu, lumi suka karɓe duk da suna iƙrarin kayan haram ne.

Da daddare Amina da Inno suna tare, Amina tayi musu girkin dare, suna ta hira Inno na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, haka ita ma Amina ta dinga bawa Inno labarin birni makaranta da yanayin rayuwar mutanen birni.

"Gaskiya Inno an mana nisa, cigaba yana birni, in Allah ya yarda a dalilin karatun nan nawa sai garin nan ya samu cigaba na gaske"

"To Allah ya sa, amma da fari nima naso kiyi aurenki duk da ba Jarmai na ke so ki aura ba, amma yadda na ganki ɗin nan naji daɗi sosai, kin san bayan tafiyarki Jarmai mata biyu ya aura ya saka"

Amina ta ce "Allah ya rufa mini asiri, da tuni nima ina ciki"

Wayar Amina ce ta fara vibrating tana kawo haske, ganin sunan Daddy ya sanya ta kalli Inno ta ce "Ina zuwa"

Ta miƙe ta bar ɗakin ta koma wani, ta zauna sannan ta amsa wayar tare da yin sallama.

Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa ya ɗora da cewa "Da ba zaki ɗaga bane?"

"Wace ni in ƙi ɗaga wayarka, ina tare da Inno ne ina cin abinci"

"Ok, nayi zaton kin yi bacci ai"

"Ai dare bai yi ba sosai"

Daddy ya gyara kwanciyarsa Sannan ya ɗora da cewar "Ina fatan kin ci kin ƙoshi"

"Na ƙoshi sosai ma, gani ga Inno muka ci fa, nayi kewarta sosai"

Yayi murmushi ya ce "That's good, ni kuma na kasa cin Abincin"

Ɗan waro idonta tayi ta ce "Me yasa?"

"Ba a bani wanda nake so ba, fruit kawai naci na kwanta"

Cikin damuwa da tausayawa Amina ta ce "Meyasa baka sa an dafa maka wanda kake so ba? Kar ka kwana da yunwa fa"

Ya shafi cikinsa ya ce "Abincin ne bana jin daɗinsa idan bana ki ba, na san da kina nan zaki dafa mini abin da nake so"

"Kar ka kwana da yunwa kaji Daddy, dan Allah ka ci wani abu"

"To me zanci, kar ki damu zan kwana haka ba wata damuwa"

Noƙe kafaɗa tayi ta ce "Ni ban yarda ba"

Dariya yayi ya ce "Rigima ko?"

"Allah da ina gida da komai dare saina dafa maka Abinci, me zai sa a bar mai nemowa ya kwana da yunwa, rashin kyautawar yayi yawa"

Har cikin ransa yaji daɗin abin da ta faɗa, na nuna damuwa da shi sosai.

"Ai nace karki damu, na ƙoshi na sha fruit sosai da cock"

"Cock kuma?" Ta faɗa da ɗan ƙarfi.

"Eh Cock" ya bata amsa.

"Daddy ba a hanaka sha ba?"

"To ya zan yi idan ban sha ba?"

"Daddy baka kiyaye lafiyarka sai wani abu ya sameka, daga tafiyata ka cigaba da ciye-ciye ko"

Sosai ta bashi dariya ya ce "Da wasa nake yi, ban sha ba"

"Har naji daɗi na zata ka sha"

"Mhmm ban sha ba Meenali"

Amina ta ɗan numfasa ta ce "Daddy"

"Mmm"

Ta ɗan tura baki ta ce "Ka amsa mana"

"Na amsa ai" yayi maganar yana murmushi.

Ta ce "Kace Na'am Meenali"

Dariya yayi ya ce "Kina son sunan kenan?"

"Eh mana, idan ka faɗa sai in jini kamar wata irin babbar 'yar gayun nan, nan kuwa 'yar ƙauye ce"

Ba ƙaramin dariya ta bawa Daddyn ba, "Allah ya shirya mini ke"

Ta sake nutsuwa ta ce "Daddy, kayan daka saya muka taho da....."

"Shhhhhh" ya katseta.

"Daddy ka tsaya ka ji me zance"

"Keep quiet" yayi maganar cikin bada umarni.

"Daddy dan Allah ka bari nayi magana"

"I say keep quiet"

Ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah Daddy"

"Amina i said you should keep quiet, tun da ba kya ji saida safe"

Da sauri ta ce "Yi haƙuri dan Allah nayi shiru"

"Idan nace bana son abu just leave it immediately"

"To in sha Allah"

"Yauwa ko ke fa, i hope dai baki fita ko ina ba?"

Amina ta ɗan sosa kai ta ce "In gaya maka gaskiya?".

"Kin fita kenan?"

"A'a ai ban yi nisa ba, gidan 'yan uwanmu naje, kaga ba zan daɗe ba zan dawo"

"Meyasa baki gayamini ba"

"To kayi haƙuri"

Cikin kwaikwayonta ya ce "To kayi haƙuri, mara ji kawai, kije ki kwanta sai Allah ya kaimu da safe kuma"

"To Daddy, ko in hau Online"

"A'a hutawa zaki yi, kun sha tafiya, ki gaida Mutanen gidan"

Amina ji tayi bata son ta katse wayar, amma ta maze ta ce "To, Allah ya tashemu lafiya, don't forget to recite Suratul mulk before you sleep, zan kawo maka Abinci a mafarki" tayi maganar tana dariya.

"Meenalin Daddy, my joy giver zan karanta in sha Allah bye bye" ya kashe wayar, dan shima idan ya biye mata ba zai katse kiran ba.

Ya lumshe idanunsa tare da ɗora wayar a kan ƙirjinsa yana murmushi.

Ɗaki Amina ta koma, ta tarar Inno na shirin kwanciya.

"Inno har kin gama cin abincin?"

Inno ta ce "To yaya zan yi idan ban ci na tashi ba, kin je kin shantake kin shanyani, wai ma da wa kike wayar ne?"

Amina ta ɗan sosa kai ta ce "'yan ajinmu ne fa"

Inno ta gyaɗa kai ta ce lallai kam.

Fadila na zaune a babban falo, tana shan tea tana kallon wani Indiyan series, Mummy ta fito falon ita ma.

"Au baki bacci ba dama?"

Fadila ta ce "Eh Mummy, na kasa baccin ne"

Mummy ta zauna a kusa da Fadila ta ce "Ke, wata shwara Hajiya Salma ta bani a kan Khalil, kuma ina ga hakan zan yi, dan in nuna masa kuskurensa"

"Shawarar me kenan?"

"Ai da Abujan zanje in ga halin da yake ciki, ya ɗau gaba dani ko gaisheni baya yi sai ya ga dama, shi ne Salma ta ce in rabu da shi, kawai in nema masa aure sai dai in ce ya dawo ga mata"

Fadila ta kalli Mummy ta ce "Kuma kina ganin hakan mai yiwuwa ne?"

"Me zai hana shi yiwuwa? Hakan ne kawai zai sanya in yi maganinsa, kuma in raba shi da waccan yarinyar da ya ɗora ransa a kanta".

"Gaskiya bai kyauta ba sam, nima ko magana nayi masa sai ya ga dama yake kulawa, amma kar ki aura masa wadda baya so ya wahalar da 'yar mutane a banza, kin san halinsa".

"Shi ya isa, zan nemo masa yarinyar wadda ta dace da shi, ba wannan shiriritar gayyar tsiyar da ya kwaso ba"

Fadila ta ce "Shikenan, Allah ya sa a dace".

Hajiya Zainab ta amsa da "Ameen"


Ɓangaren Hafsa kuwa, sayar da ƙosai suka koma yi a cikin gida, da kayan su maggi da kayan kaɗin miya, Hafsa tayi iya ƙorainta ta cire Khalil daga ranta, amma abun ya gagara, a zahiri ta cigaba da sabgoginta, tare da nuna komai ya wuce, sai dai walwalarta ta ragu sosai tana ta dannewa dan kar Mama ta gane tana cikin damuwa, sai dai ita kanta Maman ta damu sosai da rabuwar ta su.
Har zuwa wannan lokacin, Hafsa ba ta daina ɓuya tayi kuka ba, saboda ba ƙaramin so take yiwa Khalil ba. Dan har a yanzu wasu lokutan ji take yi tamkar ta mayar da layinta ta kirashi, amma sai ta fasa ta cigaba da danne abin a zuciyarta, tare da miƙa lamuranta ga Allah.

Washegari jama'a basu fasa cigaba da zuwa ganin Amina ba tare da yi mata sannu da zuwa ba, wajen ƙarfe goma na safe tayi wanka ta kintsa, ta cewa Inno zata je makarantar bokonsu, ta gayar da malamanta na makaranta.
Inno ta amince, Amina ta shirya ta tafi makarantar.

Malamanta sun ji daɗin ganinta, Malam Sunusi ya ce "Amina, sai wayar gari muka yi muka samu labarin wai kin gudu, kwatsam na haɗu da mahaifinki a kasuwa ya ce ai kina can wurinsa a birni"

Amina ta ce "Wallahi Sir a lokacin nan bani da wani zaɓi da ya wuce in gudu wurin mahaifina, Auren dole 'yan uwan babana za suyi mini a lalata mini karatuna, ni kaina ba a son raina na tafi ba, amma ina can wurin Babana"

"To Masha Allah, ya karatun naki, yace mini kin cigaba da karatunki"

"Eh sir na cigaba, ni shekara mai kamawa in Allah ya yarda zan gama Sakandire"

Nan malaman suka yi ta saka mata albarka tare da yi mata fatan sa'a da nasara.

'yan ajinsu duk babu, wasu sun yi Aure wanda Allah ya taimake su kuma sun cigaba da karatun.

Sai wajen azahar Amina ta baro makarantar, ta nufi gida, sannu a hankali take tafiyarta sam bat jin zafin ranar nan, duk da akwai nisa a tsakaninsu da makarantar, amma bata damu ta hau abin hawa ba, a ƙafa ta tafi tana tafe tana tunanin abubuwan da suka faru a baya.

Sautin ƙarar wani akwalan babur ne ya cika mata kunne, tana ƙoƙarin kaucewa babur ɗin amma burki ya ƙwacewa mai baburin ji kake gauuuu!!

AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
             BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL


45

Gafe Amina tayi da sauri, shi kuma ya daki bishiya, ya kusa hantsilawa, Allah ya taimake shi bai faɗi ba, ya saki baki ya bi Amina galala da kallo "Amina" ya faɗa cikin mamaki.

Haɗe rai Amina tayi ta ce "Wannan wane irin abu ne, da ka bugeni fa shikenan ka cuce ni?"

"Haba Amina, ai kya bari mu gaisa, dama da gaske kin dawo garin nan, Allah mai iko"

"Kaga Jarmai, babu ruwanka dani dan Allah, ka fita daga harkata"

"Haba Amina, ki tsaya muyi magana mana"

Wata uwar harara Amina ta watsa masa ta ce "Muyi magana kace mini me? Da ka nemi jefa rayuwata cikin masifa"

"Amina ai shi masoyai ba zai taɓa zama maƙiyi ba"

"Can da yawarka, ai ni ban taɓa sonka ba, kuma ba zan ba ka fita daga harkata na gaya maka".

Ta juya ta cigaba da tafiya, hawa baburinsa yayi ya cigaba da binta, amma tayi masa banza kamar da dutse yake ba da ita ba, a haka har suka iso cikin gari, sai da ya bita har gida, amma ko ɗaga kai bata kuma yi ba, balle ya sanya ran zata saurareshi.

A tsakar gida ta tarar da Inno tayi alwalar sallar azahar.

"Amina ina kika tsaya haka kin daɗe?"

"Ina makaranta, na tsaya wurin su Malam Sunusi na taho hanya wannan Jarman ya kusa bugeni da babur har ƙofar gidan nan ya biyoni yana mini magana, wai in saurareshi"

Inno ta jinjina kai ta ce "Lallai Jarmai ba shi da kunya, kinga yadda ya dinga yiwa su Baffa Bala zarya, yana neman ya kai su ƙara, suka ce ya bari idan aka ganki zasu ba shi ke, ya ce ko kyauta suka bashi ke ba zai karɓa ba, wai kin tafi yawon duniya"

Amina t girgiza kai ta ce "Allah ya rabani yawon duniya, yaje aniyarsa ta  bishi"

"Kije kiyi salla, ki zo ki ɗibi Abinci, nayi waya da babanki a kan kayan nan da aka kawo, ya kira wayarki amma kin barta a gida, ya ce a ɗebarwa maƙota ma"

Amina ta ce "Na manta da wayar ne, a ɗebar musun, bari in yi salla"

"Aikuwa ana ta kiranki a wayar, ni dai ban iya ɗagawa ba haka na barta"

Amina ta ce "Idan nayi sallar na duba waɗanda suka kirani, na san ba zai wuce Daddy ba".



Tun ranar da Kankiya ya kori Yazid daga aji, bai kuma zuwa ba, Fadila dai ta gaji ta sake kiran wayarsa, cikin sa'a taji ta shiga, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga kiran.

"Assalamu alaikum"

Ta amsa da "Wa'alaikum salam warahmatullah, Yazid"

"Na'am" ya amsa yayi shiru.

"Kana jina?"

"Eh ina ji"

"Fadila ce"

"Na gane, ina jinki" taji haushin amsar da ya bata, amma ta basar ta ce "Ya jiki?"

Ya ce "Jiki Alhamdilillah, da sauƙi sosai"

"Naga baka kuma zuwa school ba tun ranar, shine na yi zaton ko jikin ne haryanzu".

"Hmm in zo saurayinki ya kuma korata, jikin ne ban gama warkewa ba, wurin da aka mini aikin yana ciwo, likita ya ce in zauna a gida, ina ga sai lokacin exams zan shigo"

"To Allah ya baka lafiya, tun lokacin da ka daina zuwa na sanarwa HOD in sha Allah duk zaka yi exams ɗinka ba wata matsala"

Yazid ya ce "Masha Allah, na gode sosai"

"Amma ka bani direction ɗin gidanku, ko Asibitin da kake, zan zo in dubaka"

"No, unguwarmu ta talakawa ce sosai, idan kika ce zaki zo, motarki zata iya ɓaci, kuma ba zan so in wahalar da ke ba, na gode sosai"

Jiki a sanyaye ta ce "Ba damuwa ka gaya mini in zo"

Ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, hakan ma na gode sosai, sai anjima" ya katse kiran. Ta sauke wayar daga hannunta tana bin wayar da kallo.

Haryanzu Khalil yana fama da ciwon kai mai zafi, duk da yana ta ƙoƙarin danne damuwar da yake ciki, amma kallon hotunan Hafsa da duba previous chats ɗinsu ya zame masa kamar ibada, idan bai yi ba baya jin daɗi, gaba ɗaya ya rame sosai.
Gidansa da yake ta ɗoki yana ginawa, yana ƙaƙale gaba ɗaya ya dakatar da ginin, dan ji yake idan ba Hafsa ba babua wadda zai iya sanyawa a cikin wannan gidan.
Bayan sallar la'asar yaga missed video call ɗin Fadila.
Kiranta yayi dan yaji dalilin kiran nasa da take yi. Ya ci sa'a tana Online, ta ɗaga wayar.

Ɗan zuba masa ido tayi, cikin damuwa ta ce "Yaya Khalil baka da lafiya ne?"

"Lafiyata ƙalau menene?"

Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Yaya Khalil me nayi maka ne?"

"Kamar yaya?"

"Naga idan nayi maka magana sai ka ga dama kake amsawa, ko a waya baka kirana"

Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ayyuka ne suka yi mini yawa sosai"

"Na sani, ba wani aiki da yayi maka yawa, ka rame fiye da yadda kake tunani, duk wanda ya ganka ya san kana cikin damuwa ne. Dama na kira in gaya maka ne, Mummy tana nan tana fushi da kai, wai kana gaba da ita, Hajiya Salma ta bata shawarar ta aura maka wata yarinyar, tun da haka ka zaɓa gara ka san abin yi"

Zaro ido yayi ya ce "Ban gane ba, kamar yaya a aura mini wata yarinyar, idan bana sonta fa?x"

"Nima ban sani ba, haka kawai Mummy ta gaya mini, gara ka dinga kiran Mummy kana gaisheta"

"Fadila ya ake so in yi da rayuwata? Yaya za ayi in gaba da Mummy, duk lokacin da na kirata sai ta mini faɗa ta ƙare mini zagi a kan Hafsa, ita kanta yarinyar mutuncina ya zube a idonta, ace uwata taje ta sameta ta ci mutuncinta wai ta rabu da ni, wanene ni ɗin? Kuma yanzu haka bama tare, yarinyar ce ta ƙarfafa mink gwiwa a kan mu rabu da juna, tun da Mummy bata so, amma gaskiya idan Mummy ta aura mini wata daban wadda bana so bata kyauta mini ba"

Fadila ta ce "To ni dai ban gaya maka dan ka tashi hankalinka ba, na gaya maka ne kawai dan ka san abin da kake ciki"

Ya jinjina kai tare da fesar iska daga bakinsa ya ce "Shikenan, na gode sosai" yayi disconnecting ɗin kiran, ya cillar da wayar gefe, ya dinga murza goshinsa, yana mamakin yadda Mummy ke biye shawarar ƙawayenta fiye da komai.

Sai da Amina ta idar da sallar azahar, sannan ta turawa Daddy saƙo "Can i call you?"

Kusan mintuna goma da tura masa saƙon, Daddy ya kirata.

Wani nishaɗi ne ya ratsa Amina, ganin kiran Daddy ta ɗaga wayar tare da faɗin "Ina wuni?"

"Kin dawo kenan?"

"Eh, amma makarantarmu naje na gaida malamaina, ba wani wurin naje ba"

"Kin dai fitan, baki gaya mini ba" ya faɗa yana kwance agogon hannunsa.

"Kayi haƙuri, zan dinga tambayarka"

"Well, ya gidan ya kowa da kowa?"

"Kowa lafiya lau, ka san wani abu?"

"A'a, sai kin faɗa"

"Jarmai fa na haɗu da shi a hanya ya biyoni" ɗan tsuke fuska Daddy yayi, amma ya ce "Wow, kin haɗu da tsohon zuma kenan?"

"Allah ya kiyaye, ka san yadda na tsani mutumin nan, Allah dai ya taimakeni, bayan tafiyata mata biyu ya aura ya saka"

Daddy ya girgiza kai ya ce "Kashh bai kyauta ba gaskiya, to ke yanzu idan ba kya son Jarmai wa zaki aura?"

"Kai fa kace ba zan yi soyayya Yanzu ba"

Kawai Daddy ya fara dariya, ita ma ta biye masa suna dariyar tare.

"Meenalin Daddy, am missing you gaskiya, da wurin zan tura a dawo mini da ke, ina son ganinki sosai"

"Wallahi Daddy nima ina son in ganka, kuma ka kusa komawa aiki ko?"

"Eh Meenal, hutuna ya kusa ƙarewa"

Ta ɗan langaɓar da kai ta ce "Shikenan idan ka tafi na daina ganinka sai a waya?"

"Will you miss me?" Yayi maganar yana ƙasa da muryarsa.

"Zan yi mana sosai"

"Ai zamu dinga waya, kin san kina dawowa zaku yi tafiyar nan, ki cigaba da karatunki kin ji"

"To Daddy amma daia zaka zo Abujan?".

"Babu tabbas, zan tura Khalil dai lokacin zai yi clashing da time ɗin aikina"

Ai sai Amina ta fara kuka tana diddira ƙafa "Daddy ba fa haka muka yi da kai ba, ni dai dan Allah ka zo, ko in fasa zuwan"

Daddy ya ɗan buɗe baki ya ce "Ki fasa zuwan, da kuwa munyi faɗa da ke"

"To dan Allah ka zo" shiru yayi yana sauraren yadda take masa shagwaɓa, ya lumshe idanunsa yana shafa ƙirjinsa, ya ɗan jaa numfashi ya ce "Meenal"

"Na'am"

"Bana son rigima, ki cigaba da karatunki, zan turo a ɗaukeki jibi in sha Allah"

"Daddy"

"Shhhhhh, maza kiyi abin da nace"

Ta rausayar da kai ta ce "To shikenan"

Ya ce "Yauwa Meenalina"

"To daddare zaka kirani?"

"Dare lokacin matata ne, sai da safe kuma in Allah ya kaimu" shiru tayi ba tayi magana ba.

"Hello, kina jina?"

"Eh, ina jinka" tayi maganar tana jin haushin amsar da ya bata ɗazu.

"Za muyi Video call da safe in sha Allah, ina son in ganki"

"Da safe aiki zan yiwa Inno"

Sai da dariya ta kusa ƙwacewa Daddy, ya ce "Idan kin gama aikin zan kiraki, ki ce ina gaisheta" daga haka ya katse kiran.

Ajiye wayar Amina tayi, tana hararar wayar.

Amina ta sada zumunci sosai a ƙauye, wasu ta burgesu matuƙa da suka ganta, wasu kuma ƙanan maganganu suka cigaba da yi a kanta.
Babu kunya babu tsoron Allah, Jarmai ya cigaba da sintiri a wurin Amina, bayan ba irin cin mutuncin da ƙagen da bai yiwa Aminan ba, bayan barinta ƙauyen.

Kwanan Amina huɗu ta fara haɗa kayanta, ji take kamar karta tafi, tun ana ya gobe zata tafi, Daddy yake kiranta a waya, yana jadadda mata ta shirya da wuri, zai aiko a tafi da ita.

Ƙarfe sha ɗaya na safe, Amina ta gama shirinta, yaran Baffa Lawan suka shigo gidan wai ga 'yan sanda nan, Amina ta zo.

Inno ta dafe ƙirji ta ce "'yan sanda kuma, meye haɗinmu da 'yan sanda?"

Amina ta ce "Bari in leƙa in gani"

Amina ta saka takalmanta, ta leƙa waje, motoci uku ta gani, da kuma 'yan sanda suna kaiwa suna komowa a ƙofar gidan, yara da matasa suka tsatstsaya suna kallo.

Baƙin glashin wata mota aka sauke, saiga Alhaji Ahmad a ciki a zaun, yana sanye da baƙin glass, da dark blue ɗin shadda ba ƙaramin kyau yayi ba.

Buɗe baki Amina tayi da mamaki ta ce "Daddy"

Alama yayi mata da hannu, tazo.

Ƙarasasa Amina tayi gaban motar tana masa murmushi.

"Daddy dama kai zaka zo ka ɗaukeni?"

"Eh mana ba gani ba, i hope kin gama shiryawa?"

"Na shirya, amma zaka zo ku gaisa da Inno ko?"

Daddy ya ce "Eh mana, je ki mini iso"

"Amma baka gaya mini zaka zo ba, da na maka girki"

"Kar ki damu, jeki mini iso mu gaisa"

Da sauri Amina ta nufi cikin gidan tana kiran Inno.

"Ke lafiya, meya kawo 'yan sanda?"

Cikin washe baki Amina ta ce "Inno Alhaji Ahmad ne fa, zai zo ku gaisa"

Amina bata tsaya ƙarasa yiwa Inno bayani ba, ta ɗauko uwar tabarma, ta shimfiɗa a tsakar gidan, ta ce "Inno ki sako mayafinki bari in ce ya shigo".

Tare da Amina suka jero suka shigo, ya samu wuri ya zauna a kan tabarma, Inno ta fito suka gaisa, ta shiga jero masa godiya, amma ya ce ba komai karta damu, ya zo tafiya da Amina ne, saboda makaranta.

Inno ta zubo

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment