Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani ɗan Adam a rayuwarta ba, kamar yadda take tausayin Yazid. Ita kawai kyawawan halayensa take kallo, sai taga kamar idan aka cutar da shi ba a yi masa adalci ba, yana da halaye masu kyau, ba ya cutar da kowa to shi mai zai saka a dinga cutar da shi.
Ta tuna irin kasadarsa mussaman a ɗakin jarrabawa, dan kar wani ya faɗi, da tsananin biyyarsa ga malamai, amma hakan bai hana a dinga dizga shi a gaban aji, ba tare da duba halayensa masu kyau ba.
Dafe goshinta tayi, ji tayi kamar kanta ya fashe Saboda rasa mafita.

Ɓangaren Khalil ma yana cikin ɗumbin damuwa, Hafsa ta buɗe what's app a wayar da ya bata, har tayi masa magana ta what's ɗin, sai wani ƙara lallaɓa shi take, tana bashi kulawa ta mussaman, da Adduoi, nasiha gami da kalaman soyayya, wanda hakan ke ƙara masa sonta a ransa. Gaba ɗaya Mummy ta ɗauke masa wuta, ta daina shiga harkarsa, duk dan saboda yana son Hafsa.

Gaba ɗaya fushin da Mummy take yi da shi, bai yi masa daɗi ba, hakan ya sanya, ya kuma ƙoƙarin zuwa ya rarrasheta, sannan yayi mata bayanin halin da su Hafsa ke ciki, ko Allah ya sa ta fahimce shi.
Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mummyn, ya tarar da ita a kan gadonta, tana danna Computer, gefenta kuma ga calculator, da alama kuɗi take ƙirgawa.

Tun da ta ɗaga kai ta kalleshi sau ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da abin da take yi.

"Mummy sannu da aiki"

"Yauwa" ta amsa a daƙile ba tare da ta kalleshi ba.

"Mummy wurinki na zo"

"Ai na ganka, ina kuma jinka"

Khalil ya ɗan gyara zama tare da sosa kai ya ce "Mummy, dama game da Hafsa ne, yarinyar nan da aka ce miki an ganni a wurinta, Mummy yarinyar marainiya ce ne, Da mahaifinta mai abin hannunsa ne, kan ya rasu ya saya mata kadarori, sai dai bayan rasuwarsa dangin mahaifin suka ƙwace komai, shiyasa kika gansu a haka, amma tana da kirki da kuma hali mai kyau, ba ta da wata matsala yarinyar"

Ai tamkar dutse yayi wa wannan dogon jawabin, dan danna calculator kawai take tana shigarwa cikin Computer.

"Mummy ba ki ce komai ba"

"Me kake so in ce maka, ai kai an shanyeka, ni kuwa ba a shanye ni ba a hayyacina nake, nayi mamakin wurin wani malami suka je haka, da har ka iya zuwa ka tunkare ni ni Hajiya Zainab, kake mini wannan maganar banzan, ban sani ba ko orphanage Home ka buɗe, zaka fara rainon marayu da marasa galihu, da har zaka yayi mo min wannan shirgin tsiyar, Khalil banda rashin hankali irin naka, ina kai ina mai suyar Awara a titi, ba bu ilimi mai zurfi, ta gama zaman titi maza sun gama kalleta, in anjima ta ci kwalar namiji, kuma ka ce mini ita ce sirikata,ai kai ma ka san kayi ƙarya"

"Mummy wallahi ba haka Hafsa take ba, tana....

"Dalla rufe mini baki, ina magana kana wani kwantar da murya ce, cece, ni zaka lallaɓa in anince da auren 'yar matsiyata, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, daga yau babu kai babu yarinyar nan, na yanke duk wata alaƙa da take tsakaninka da ita, wallahi na bibiya na tarar ba ka rabu da ita ba, hukuncin da zan yanke maka ba zai maka daɗi ba"

"Mummy dan Allah, ki duba lamarin nan"

"Ni kake cewa in duba lamarin nan, wato sihirin har ya kai ka fifita ta a kaina"

Cikin rauni ya ce "Ba haka bane Mummy, wallahi ba suyi mini asiri ba, suna buƙatar tainako ne Mummy, kuma muna son juna sosai"

Mummy ta jinjina kai ta ce "Da kyau Khalil, suna buƙatar taimako ko, sannu gwamnati kowa naka, tashi ka fita ka bar mini ɗaki" ta nuna masa hanyar fita.

Zai kuma magana, ta sake haɗe rai ta nuna masa hanyar ficewa, haka ya haƙura ya bar mata ɗakin zuciyarsa babu daɗi.

Amina kuwa ba ƙaramin haushin abinda Daddy yayi mata taji ba, haka ta shiga ɗakinta, tayi alwala tayi sallar magariba, ta shiga kitchen ta hau aikin Abincin dare, kasancewar Hajara ce tayi na rana tunda ita tana makaranta.
Gaba ɗaya Amina a gajiye take, tunda kusan wuni tayi aikin da Daddy ya sakata, aikin da a ƙarshe ya sakamata da direta a titi yayi tafiyarsa saboda tayi maganar matarsa.
Ta gama girkin, ta kai dining, ta ɗau na Baba ta tafi ta kai masa, ta tarar da Baban a cikin ɗakinsa na gadi, yana jin radiyo.

Har zata fita, Baba ya kirawota, ta dawo ta zauna tana kallonsa.
Ya ɗauko wata 'yar jaka ya miƙa mata, ta sa hannu ta karɓa, ta buɗe jakar wani babban kwalin waya ta gani a ciki, ta saka hannu ta ciro wayar tana kallon Baba.
"Baba wannan wayar fa?"

Baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Alhaji Ahmad ne ya bani, ya ce in baki, wai saboda ki samu sauƙin karatu, sai dai har ga Allah ni bana son ki mallaki wayar hannu yanzu, amma bana son yi masa jayayya kuma naji ya ce saboda karatunki, ina fatan dai ba roƙonsa ki ka yi ba?"

"Haba Baba, ka san bana roƙo, wallahi ni ban roƙe shi ba"

"To sai kiyi masa godiya, duk da nima nayi masa"

"To, insha Allah zan masa"

Ta tashi tana jujjuya wayar ta bar ɗakin Baba.

Har ga Allah tana matuƙar son waya, mussaman duba da yadda ƙawayenta ke da wayar, amma ita ba ta da ita, sai dai da ta tuna da abin da Daddyn ya yi mata, sai haushi ya kamata har ta ce "Mayar masa zan yi, ban so" ta jiye wayar a gefen katifarta tana harar wayar tamkar Alhaji Ahmad ɗin ne a gabanta.

Washegari da Safe Amina bata da niyyar zuwa lesson, ta tashi ta hau aikace-aikacenta, ta shiga kitchen ta ɗora sanwa, ta yi girkin safe ta kammala, ta zo ta shiryawa masu gidan nasu Abincin, sannan ta kaiwa Baba nasa ta dawo, ta fara mopping ɗin falo.
Hajiya Zainab ce ta fara fitowa, Amina ta gaisheta ta amsa mata da ƙyar kamar an yi mata dole, sai kuma Fadila ta fito, Alhaji Ahmad ne ƙarshen fitowa, ba tare da Amina ta kalli in da yake ba, ta gaishe shi, yana jinta ya shareta, kamar ba da shi take ba.
"Good morning Daddy" Fadila ta faɗa tana ƙoƙarin haɗa tea.

"Morning sweetheart, how are you"

"Am fine Daddy"

Ya ɗan ƙara kallon Fadila ya ce "Meke damunki ne, you look dull today"

Fadila ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Nothing much, stress ne na school kawai"

"To Allah ya bada sa'a, yau weekends ki samu ki huta sosai"

"Ok Dad"

Ya mayar da hankalina kan Mummy ya ce "My Z ina Khalil ne?"

Mummy da ta kai loma bakinta, ta ƙarasa taunawa sannan ta ce "ƙyale shi kawai"

'in ƙyaleshi kamar yaya, ban gan shi a wurin cin Abinci ba"

"Ka san halinsa wasu lokutan, maybe bacci yake yi"

"Is ok" Daddy ya faɗa yana cigaba da cin Abincinsa. Yana yi yana satar kallon in da Amina ke mopping, tayi kicin kicin da rai, ko kallon in da suke bata yi, aikinta kawai take.
Ɗan guntun murmushi yayi, ya cigaba da cin Abincinsa.

Bayan sun kammala ci, Mummy ta miƙe tsaye, ta kalli Fadila ta ce "Fadila je ki shirya muje ki rakani gidan Hajiya Turai"

Fadila ta ɗan tsuke fuska ta ce "Mummy ki je ki kaɗai, ni bana son fita"

"Aikuwa sai kin je, tashi maza muje"

Fadila tana tura baki, haka ta tashi, ya wuce ɗaki, dan ta fara shirin yiwa Mummy rakiya, idan ba haka ba ta san halin Mummy, idan ta dinga mata mita sai taji babu daɗi.

Suka wate suka bar Daddy a falo, Amina kuma na zaune na goge TV.

"Ke da waye jiya na gani a tsaye a gidan nan?" Amina ta ɗaga kai ta duba falon, amma bata ga kowa ba, dan haka ta san da ita yake, maida kai tayi ta cigaba da aikinta.

"Ko in zo in maimaita miki ne?"

Ta ce "Ba kowa"

"Kina nufin ƙarya nake kenan?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ke da waye?"

"Bilal ne, a nan layin yake, bayan ka ajiye ni a hanya, ya ɗauko ni"

Alhaji Ahmad ya ce "Ban tambayeki wannan ba, abu ɗaya nake son gaya miki, kar ki sake kawo mini wani gida, kin zo gidan nan ne dan kin yi aiki da karatu, idan saɓanin haka ne a ranki, to zan sanar da Malam Hassan tun wuri ya san matakin da zai ɗauka,  karki ƙara kawo mini wani gida kinji na gaya miki, idan kuma aure kike so sai kiyi bayani, amma gidana ba wurin tara maza bane" kamar kibbau haka ta dinga jin maganganun Alhaji Ahmad, ba ƙaramin ƙona mata rai suka yi ba, ba tace masa uffan ba, sai wasu hawayen ɓacin rai da suka cika mata ido, bata son ya ga lagonta, dan haka ta tashi ta kwashe kayan aikin nata, ta bar masa falon.

Alhaji Ahmad ya shirya ya fita, sai dai ya ci karo da Wayar da ya sayawa Amina a cikin motarsa, ya ɗau wayar ya jujjuyata, ya ɗan yi shiru sannan ya jinjina kai tare da faɗin lallai ma yarinyar nan. Ya ajiye wayar ya cigaba da tuƙinsa.

Hajiya Zainab ce tare da Hajiya Turai a falonta suna hira, yayin da Fadila ke gefe a zaune tana latsa wayarta.

Hajiya Turai ta ce "Wallahi kar ki saurarawa yaron nan, kiyi dagaske ki miƙe a kan abinki, idan ba haka ba wallahi kina kallo za a shanye miki shi, sai yadda aka yi da shi"

Mummy ta ce "Wallahi Turai Khalil ya bani mamaki, ban taɓa zaton yaron nan zai kai kansa wurin maƙasƙanciya kamar mak awara ba, me aka yi a kai mai awara? Banda kalen tsiya da rashin sanin darajar kai, ya janyo mini abin faɗa a cikin ƙawaye"

"Bari Hajiya Zainab, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, banda abin Kalil waye yake janyo talaka jikinsa, ai kowa arziƙi yake nemawa kansa, ai baki ga abin haushi ba yadda yarinyar ke washe baki, kamar gonar gyaɗa, Allah ya kashe ya bata"

Mummy ta ce "To wallahi yayi kaɗan, muddin bai rabu da yarinyar ba, zaiga abin da zan masa daga shi har ita"

Turai ta ce "Ai zuwa zaki har gida, mu kasawa yarinya warning ita da uwarta"

Fadila dai ba ta tofa ba, dan a ganinta Khalil shi ne ya janyowa kansa, ga Yusra nan, ba abin da Allah ya rageta da shi, amma ya watsar da ita ya ce baya so.

Turai ta kalli Fadila ta ce "Daughter, ke kuma wa zaki kawo mana, ina fatan dai ba wahalalle kema zaki kwaso mana ba"

Fadila ta ɗan kwaɓe fuska da murmushin gefen baki.

Turai ta ce "Ai ba murmushin ba, ni dai ɗana ya gani ya ce yana so, insha Allah da ya dawo zan haɗaku, dan har Babanaa ya zan zancen"

Mummy ta ce "Ai na fara mata zancen kwanaki, kin san yaran naki ne, miskilaine kamar ubansu, na fara mata maganar ba ta ce mini komai ba dai tukuna, amma dai na san zasu daidaita"

Fadila ta sake gyara kwanciyarta a kan kujera, dan wannan hirarrakin nasu ya isheta, so take su tafi gida kawai.

Sai da Khalil ya tabattar da Mummy ta fita, sannan ya shiga falon, ya saka Hajara ta kawo masa kayan breakfast ya karya, ya ci ne dan kawai yana jin yunwa, ba dan yana son cin Abincin ba.
Bayan ya gama ya fito daga ɗakin, ya haɗu da Amina a kan baranda, ya kalleta fuskarsa ba walwala ya ce "Daga yanzu idan kun gama girki a dinga zuba nawa ana kai mini ɗakina"

Amina ta ce "To insha Allah"

Fadila har suka taho gida, Mummy tana yi mata bayanin yadda ɗan Hajiya Turai yake, ita dai Fadila lissafin, yadda zata yi da Kankiya da kuma batun Yazid ne ya dame ta.

Khalil kuwa gidansu Abdul ya wuce, dan ba shi da aminin da yake gayawa damuwarsa wanda ya wuce Abdul ɗin.
Tun a kallon fako, da Abdul ɗin ya yiwa Abokin nasa, ya san tabbas akwai damuwa, dan a yadda Khalil ya saba, da yazo yake fara zolayarsa, amma yau yana shigowa, ya wuce kan gadon Abdul ya kwanta, yayi shiru ba tare da ya ce musu komai ba.
Abdul bai kula shi ba, sai da ya kammala abin da yake yi, sannan ya dawo ya zauna a kusa da Khalil, ya kalli Khalil ya ce "Kalil, meke faruwa ne, tashi kayi mini bayani"

Kamar Khalil na jiran ƙiris, ya tashi zaune, yana share gumin da ya tsatsafo masa, ya kalli Abdul ya ce "Abdul, na ga samu, ina shirin ganin rashi"

"Kamar yaya kenan?"

"Abdul, Mummy, Mummy"

Abdul ya sake gyara zamansa ya ce "Me ya faru? Me Mummyn tayi"

Kamar Khalil zai yi kuka ya ce "Bayan wahalar da na sha wurin farautar soyayyar Hafsa, na yi nasara na samu, tana sona mun shaƙu, sai dai ina shirin zuwar wa da Mummy maganar Hafsa, ƙawaywen Mummy sun gano ni a wurin Hafsat, sun sanarwa da Mummy, baka ga cin mutuncin da ta mini ba, yanzu haka ma ta ce lallai in rabu da Hafsa, dan Allah Abdul yanzu ta yaya zan koma in janye maganata da Hafsa, bayan ta gama bank dukkanin yarda, da saka ran samun salama a wurina tayaya Abdul"

Abdul ya jinjina kai ya ce "Akwai damuwa, ka san iyaye gaba suke da dukkanin wani abu na san rai da son zuciyarmu, amma kuma yakamata ita ma Hafsa a duba a yi mata adalci, kaima kana da ƙanwa mace, alhakin Hafsa zai iya kama Fadila da bata ji ba bata gani ba"

"Kai Abdul, ba zan iya haƙura da Hafsa ba, duk da ban san wane irin mataki Mummy zata iya ɗauka a kaina ba, bana jun zan iya rayuwa babu ita!!!

DOMIN SHIGA VIP GROUP, POSTING KULLUM KU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR
08081012143
GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM
(AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)

P34


Abdul ya gyara zamansa ya sake fuskantar Khalil ya ce "Ibrahim, kai ka wuce aboki a wurina yanzu, kai ɗan uwana ne, ba zan so ka aikata abin da zaka zo kana dana sani ba, kar ka biyewa soyayya ka zo ka rasa yarda da soyayyar mahaifiyarka, Ka bi komai a hankali, har Allah yasa Mummy ta fahimta, shawara ta farko mai zai hana kaje ka samu Daddy, shi ka yi masa bayanin, na san zai fuskance ka kuma zai yiwa Mummyn bayani"

Khalil yayi wani guntun murmushi sannan ya ce "Abdul ya kake abu kamar ba ka san wacece Mummy ba ne? Kai ka san babu yadda za a yi na samu goyon bayan Daddy, muddin Mummy ba ta son abu, ba zata taɓa yarda ba, kuma wallahi ina matuƙar jin tausayin Hafsa, idan na rabu da ita ban san wane hali zata shiga ba, bari ayi sallar magariba, muje tare ka shaida yadda yarinyar nan ta shaƙu da ni, ta yarda dani ta saki jiki zan Aureta, amma Mummy tana barazanar rabani da ita, dan Allah Abdul ko Hafsa na da wani aibu da so ya rufe mini ido ban gani bane?"

Abdul a ransa ya ce 'Talauci, shine aibun da mahaifiyarka bata so' amma a fili ya ce "Ai Hafsa yarinyar kirki ce, ba ta da wani aibu, ba wanda ba zai so haɗa zuriya da ita ba, kuma tana cikin yanayin da take buƙatar taimako, zaman soya awarar nan bai dace da ita ba sam"

"Yauwa Abdul, ashe ka gane, wallahi yana daga cikin dalilan da ya sanya nake son taimakonta, Hafsa da gidan Aure ko makaranta ta dace, ba da zaman titi ba, Abdul na tsara irin rayuwar da zan yi da ita, yadda ta sha wahala a baya duk da farkon rayuwarta 'yar gata ce, amma ina son in ɗauke mata komai, yadda ba zata taɓa kukan wani abu ta rasa ba, sai abin da bani da damar sama mata, Abdul ba zaka gane ba, that girl deserve a shoulder to rest, akwai matsala idan Hafsa ta auri mutumin da bai San mecece ƙaddara ba, kuma bai san kimar mace ba, ya zan yi Mummy ta gane ne?"

Abdul ya jinjina kai, So kenan, mai sa mutum ya duƙa, ya susuce duk izzarsa da kuma taƙamarsa' A yadda Khalil yake ɗan gayu matashi mai ji da kuɗi, idan aka ce maka zai ɗauko mace kamar Hafsa ya ce yana so zaka ƙaryata, amma ya zauna sai sambatu yake yi.

Abdul ya ce "Khalil, naji duk bayananka, kuma na fuskance ka, zan tayaka da Addua, sannan zan cigaba da tunanin menene mafita ga al'amarin nan" da ƙyar Abdul ya ɗan rarrashi Khalil, ya rage damuwar da yake ciki.


Amina bayan barinta falo, da ta koma kitchen kuwa saida tayi kuka sosai, ita gaba ɗaya gorin nan da ake yi mata da kuma takura ya isheta, shikenan dan  tana karatu wani ba zai kulata ba, kuma ita Bilal ba cewa yayi yana sonta ba, 'yan ajinsu suyi ta bada labarin samarinsu, amma ita sai samarinta na ƙauye, gashi Alhaji Ahmad yayi mata gori kuma ya hanata tsayawa da saurayi, ta zauna a kitchen tana ta kukanta.
Hajara ta shiga kitchen ɗin ta tarar da ita, a zaune tana share hawaye.

"Amina kukan me kike kuma?"

"Ba komai" Amina ta faɗa a daƙile.

"Kawai jin daɗi ne ya sanya kika zauna kina kuka?"

"Nace miki bakomai, ki ƙyaleni" Amina ta faɗa a ƙufule, dan sa idon Hajara yayi yawa, komai ta gani so take sai taji ƙwaƙwaf, yadda aka fara da yadda za a ƙare.

Ta miƙe ta cigaba da aikin tana yi tana kuka, kamar ƙaramar yarinya.

Tun daga wannan ranar, Amina ba ta yadda ko hanya ta haɗata da Alhaji Ahmad, ganin idan ta gaishe shi ya daina amsawa, sai dai ya tsaya ta ƙureta da ido, dan haka gaisuwarma ta daina gaisheshi. Idan suka haɗu sai ta basar ta wuce abinta.

Da magariba Khalil ya takurawa Abdul, ya shirya suka tafi gidansu Hafsa, kasancewar ta san da zuwansu, ya kirata ya sanar mata, ya sanya ta shirya har da yi musu girki, ta saka ɗaya daga cikin kayan da ya kawo mata, a ɗinke, wani less mai matuƙar kyau da ya kawo mata shi a ɗinke.
Tun da ta fito hannunta riƙe da babbar darduma, Khalil yake kallonta,  tayi masa kyau fiye da kullum, ga wani irin tausayinta da ya ƙara mamaye masa zuciya.
Tana Zuwa tayi murmushi ta ce "Yaya Abdul, kwana biyu ka ɓuya da yawa"

Abdul yayi murmushi ya ce "Ai tunda Allah yasa ku ka daidaita, bai kuma nemana in masa rakiya ba, shiyasa ba kya gani na"

"Yaushe zan nemeka, ka zo ka samana ido" Khalil ya faɗa yana sake mayar da hankalinsa a kan Hafsa.

Ta shimfiɗa musu sallaya, suka zauna ita kuma ta zauna daga gefe.

"Babyna kina lafiya, ya kasuwa?"

"Alhamdilillah, ya gida ya su Mummy?"

"Suna lafiya ƙalau, kin yi mini kyau fiye da kullum, kamar in sace ki in gudu, Abdul ko zagawa zamuyi mu tataro mutane a ɗaura mana auren nan ne kawai mu huta?"

Abdul a ransa ya ce "Da ka ci ubanka la'ada waje a wurin babarku'

Amma a zahiri ya ce "Eh to idan ƙanwar tawa ta yadda, sai muje neman mutane a haɗu a ɗaura ai"

Hafsa sai sunkuyar da kai take tana jin kunya, Khalil ya leƙa fuskarta ya ce "Babyna, ki gaya masa kin amince, mun Matsu mu mallaki junanmu, ko yanzu a shirye muke a ɗaura"

Ƙunshe fuska Hafsa tayi, tana jin wata irin kunya tana ratsata, gaba ɗaya shi Khalil baya jin kunya.

"Ya kika yi shiru, in dai Abdul ne ki daina jin kunyarsa, a ɗaura mana aure next year by now insha Allah idan baki haihu ba to muna nan muna rainon Babynmu a cikinki"

Miƙewa Abdul yayi ya ce "Khalil wannan fitsarar ta ka, ba ita ba ni kaina kunyar kake bani, bari in koma mota In jiraka" Dariya Khalil yayi, Abdul ya nufi ƙarshen layi in da suka bar motarsu.

Khalil ya matsa ya sake mayar da hankalinsa kan Hafsa ya ce "Amaryata, ɗago mana in ƙare miki kallo, baki ga yadda kika mini kyau ba"

A ɗan shagwaɓe ta ce "Wai sai ka ta bani kunya a gaban mutane"

"Suwaye mutanen, Abdul ɗin? Ni banga wani abin Kunya ba"

"Ni na gani ai, amma kayi mini kyau sosai"

"Da gaske?"

Ta jinjina masa kai, yayi murmushi ya ce "Kyau sai ma ranar bikinmu yarinya"

Tayi shiru ba tace komai ba. "Babyna" ya faɗa murya ƙasa-ƙasa.

Ta ɗan ɗago ta kalleshi.

"Kiyi magana mana"

"Yau ba 'yan maganar, na rasa me zance"

"You must say something, bari muyi Auren zobe, wata azurfa na saya mana tun last month, sai wannan watan Allah ya sa suka iso"

Ya ciro wata 'yar ƙaramar box blue black, ya buɗe sai ga wasu zobuna masu matuƙar kyau a ciki.

Ya ɗauko na matan, ya kamo hannun Hafsa, ya kama yatsanta ya saka mata zoben. Da ɗan sauri ta janye hannun nata, tana jujjuya zoben tana murmushi.
Ya miƙa mata masa hannun, ya ce "Nima sa mini"

Ya miƙo mata yatsansa, cikin rashin sabo, ta zira masa zoben. Hannunta ya kamo cikin nasa, ya ciro wayarsa, ya ɗauki hoton hannunsa da nata sanye da zobunan.
Daga nan ya zarce yana ɗaukarta hoto, hannunta da ke cikin nasa ba ƙaramin takurata, yayi ba amma ta kasa cire hannunta daga nasa, yayi ta musu hoto. Ba tare da ya cire hannunsa a nata ba ya ce "Hafsa zaki aureni?"

"Meyasa kake yawan maimaita tambayar nan? I will marry you in sha Allah My" tayi maganar tana masa murmushi.

"Murmushin nan naki yana killing ɗina, ki ce kina sona?"

"Ina sonka sosai, duk ka koya mini rashin kunya"

"Kina da kunya sosai, amma naji daɗi da kika rageta sosai a kaina, ina son matata ta zama mai kula dani sosai, ina sonki Babyna, ki cigaba da yi mana addua, Allah ya tabattar da Aurenmu, ya bamu ikon cin duk wata jarrabwa da ka iya taso mana"

"Ina yi mana"

"Yauwa Habibty, zuba mini Abincin in ci, kuma a bakina zaki bani"

Ta noƙe kafaɗarta ta ce "A'a zan dai zuba maka, sai bayan nikah zan dinga baka a baki"

Haka ta zuba masa Abincin nan, yana ci yana zuba santi yana koɗata.

Ya kammala ci, ya ce "dama wancan ba ci zai yi ba, ya ce lemo kawai zai sha, na gode sosai matata in sha Allah, bari in tafi"

Hafsa ta marairaice ta ce. "Ni kar ka tafi yanzu, ban gaji da ganinka ba"

"Allah sarki sweetheart, ni kai na bana son tafiya, ban gaji da ganinki ba"

"Shikenan ma yi video call, kar kayi dare muje in raka ka mota"

Khalil ya ce "A'a, bana son ki wahala, ki ce ina gaida Mamana"

"Ni baka taɓa haɗani da Mummy na gaisheta ba"

Ɗan dam yayi, sai kuma ya ce "Karki damu zan haɗaku"

Yana nan tsaye, sai da ta shiga gida, sannan ya nufi in da motarsu take. Jiki a sanyaye ya shiga motar ya zauna.

Abdul ya kalleshi ya ce "Baban soyayya, ka shanyani kana can kana soyewa, Allah yasa baka ƙone ba"

Khalil ya Shafi gemunsa ya ce "Kamar kar in taho, ina son yarinyar nan"

"Nima na ga alama, zan taya ku da Addua in sha Allah".

Da haka Khalil ya ja motar, ya tafi kai Abdul gida.

Washegari Monday, su Amina zasu koma makaranta, ta yi gugar uniform ɗinta, ta wanke jaka da takalminta, ta shirya litattafanta, tana ta kallon jakarta tana jin shauƙi da farincikin komawa makaranta, ta dinga tuna rayuwar da tayi a ƙauye, yadda ta dinga makaranta a wahale, wataran sai dai ta saci hanya ta je makaranta, idan ta dawo ta ci duka, amma nan duk da tarin ƙalubalen da take fuskanta, akwai Abinci, akwai wurin kwana mai kyau, gashi duk wani aiki da ake sakata, ba a sakata lokacin makarantarta.
"Kai Allah ya saka maka da alkhairi" ta faɗa a fili, sai kuma ta tuna da abin da Alhaji Ahmad yayi mata, sai ta tura baki tana ƙunƙuni kamar tana gabansa, ta tashi ta tafi wurin Baba.

Ganin fara'a a fuskar Amina ya sanya Baba yin murmushi ya ce "Uwata, murmushin me kike haka ne?"

"Baba ka san gobe in Allah ya kaimu zamu koma makaranta, shine nake ta jin daɗi, na wanke uniform ɗina na goge, shi ne nake jin daɗi"

Baba ya ɗan yi ajiyar zuciya, ya ce ina zuwa.
Ya tashi ya shiga ɗakinsa ya fito da ƙatuwar leda, ya miƙawa Amina ya ce "Gashi in ji Alhaji Ahmad, jaka ce da takalmi ya ce a baki, kuma wai idan kinje makaranta ki je ki karɓa sabon kayan makaranta, Uwata ban taɓa zaton Alhaji Ahmad zai kyautata miki haka ba, bani da bakin yi masa godiya, sai fatan ya

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment