Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama da duniya lafiya, Uwata ki same shi ki durƙusa har ƙasa ki yi masa godiya Amina"
Maimakon Amina tayi murna, sai ta ɗan tura baki, dan ji tayi ma kamar ta ce bata so.

"Uwata ya naga kin haɗe rai"

"Ba komai Baba murna nake yi, Allah ya saka masa da alkhairi, na gode sosai, amma ai ni takalmi na da jakata da Uniform ɗina suna da kyau"

"Ba sai ki adana abinki ba, kuma ya mini ƙorafin idan ya baki abu ba kya karɓa, wannan kuma kin yi daidai, ki cigaba da kula da mutuncinki"

"To, In sha Allah Baba Na gode sosai"

Ta miƙe da ledar a hannunta ta koma ciki, Hajara na ganin Amina da leda, ta fara washe baki, "Amina sayayya aka yo mana haka?" Ko kallonta Amina ba tayi ba, ta wuce ɗakinta.
Zuwa tayi ta zauna ta bubbuɗe ledar, jaka ce mai tsadar gaske, da takalmi da safa, kai da ganinka san kaya ne masu matuƙar tsada.

Fadila sai dubawa take taga Yazid a ajin, amma babu Yazid babu dalilinsa, har aka yi lectures ta farko aka gama, ba taga Yazid ya zo ba.
Suka yi ta 10_12 ma, still Yazid bai zo ba, gashi tana lectures ɗin 2-4 za suyi presentation ɗin nan, amma Yazid bai zo ba, gashi presentation ɗin nan shi ne zai ɗau maki mafi yawa.
Taje ta yo salla ta je Cafeteria ta ci Abinci, ta nufo aji.
  A wuri ɗaya ta hango shi a zaune, ya sunkuyar da kansa, da alama wani abu ne mai muhimmanci ya ɗauke masa hankali, ba ta san ya aka yi murmushi ya suɓuce mata ba, ta nufi in da yake zaune "Kai dama zaka zo school ɗin nan, amma kayi missing ɗin har lectures biyu?"
Tayi maganar ba tare da ta zauna ba, Yazid ya ɗago a hankali ya kalli Fadila, ya mayar da kansa ya cigaba da kallon wayarsa dake hannunsa.

"Am talking to you" tayi maganar tana kallonsa.

Ya ce "Ina jinki ai"

"Kana jina Kai mini banza?" Cigaba da kallon wayarsa ya yi.

Haushi ya kama Fadila, ta sa hannu ta zare wayar daga hannunsa, ko ɗaga kai bai ba balle ya kalleta.
Duk da ƙaramar waya ce amma Alqura'ani ne a kai yake karantawa.

Zama tayi a kusa da shi "Wai yau ma azumin maganar ka ke yi?".

Kashingiɗa yayi da jikin bencin, ya ware mata idanunsa a kanta, still bai ce komai ba.
Da sauri ta janye nata idanun, jin tsigar jikinta na tashi, ga wani gumi da bata san na menene ba yana tsatsafo mata a goshi, ta kasa tashi ta kasa komai, shi kuma ya cigaba da kallonta, kamar ya samu majigi.

Samun kanta tayi da miƙewa tsaye, tana ƙoƙarin barin wurin, amma cikin shammata ya janyo hannunta wanda hakan ya tilasta mata zama jikinsu na daf da haɗewa har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskarta, Allah yasa ajin babu mutane, kowa sabgar gabansa yake yi.

Sosai jikinta yake rawa, kamar wadda ake yiwa gangi, ga idanun Yazid da suka dasa mata wani shocking da yake tsirga mata tun daga kanta har yatsun ƙafarta, yawun bakinta har wani bushewa ya yi.

Bakinta ya dinga bi da kallo, ɗan madaidaici a kyakykyawar fuskarta, da ya ƙware a wurin iya tsiwa da masifa.

"Bani wayata" ya furta yana sake ƙoƙarin sanya idonsa a nata, amma ta hana hakan, ta hanyar sunkuyar da kanta.

"Bani mana" ya sake maimaitawa, amma ta kasa motsi, sai jujjuya idanunta da take yi.

Hnnunsa ya sa ya zare wayarsa daga hannunta.

Mafarkan da take da shine suka dinga dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, maganar Yusra ce ta dawo mata 'Wataran sai kin rungumeshi a zahiri'

Firgigit ta dawo hayyacinta, daga duniyar da ta lula, har ta kasa gane mafarkan da ta saba yi ne, ko kuma zahiri ne, dan wani irin yanayi ta shiga wanda da ta kasa fassarawa kanta wane irin yanayi ne haka.

Miƙewa tsaye tayi, ta bar wurin da sauri, tana ta sauke numfashi a jejjere.

Yazid kuwa binta yayi da kallo, yana kallon yadda ta birkice a lokaci ɗaya, duk taurin kan Fadila, ba wuya ya sa ta shiga taitayinta.

Fadila ta cigaba da rarraba idanu, tana jin yadda halin da ta shiga ya kasa barinta haryanzu.

A hankali ɗalibai suka cigaba da dawowa ajin, saboda shiga lectures ɗin su ta ƙarshe, wadda daga ita kowa zai tafi gida, kuma wadda a ita ne, zasu gabatar da presentation ɗinsu.

Lokaci na cika malamin ya shigo ajin, kasancewar mutum nai kiyaye lokaci, kowa ya nutsu ya shiga taitayinsa, kasancewar malamin ba shi da wasa Sam.

Kowane 'yan group sun nutsu, sun haɗu wuri guda, suna tattauna yadda za su gudanar da presentation ɗin su, banda 'yan group ɗin su Fadila, ita tana nata wuri, Yazida ma haka, sauran 'yan group ɗin ma haka.

Aka dinga kiran groups ɗaya bayan ɗaya, suna gabatar da presentation ɗinsu, duk karsashin group idan lecturer da 'yan bani na iyan aji suka fara suburbuɗo tambaya, duk karsashin 'yan group ɗin, sai sun karaya.

Da haka aka zo kan group ɗin su Fadila, aka kira su, suka fito ɗaya bayan ɗaya, suka jeru a gaban aji, sai dai Yazid bai fito ba, sai da suka gama fita gaba ɗaya sannan Yazid ya fito, yana zuwa ya tsaya a kusa da Fadila, suna fuskantar 'yan aji.
Ji tayi tana neman diriricewa, a hankali ya furta mata "Ki nutsu mana, you are facing the class"

Suka fara gabatar da presentation, aka zo kan Wanda Fadila za tayi, gaba ɗaya ba ta da confidence, saboda a halin da Yazid ya sakata, sai dai yadda take zuba turancin ne zaka san ya zauna sosai a bakinta.
Suka gama gudanar da presentation, aka zo fannin amsa tambayoyi, lecturer ya fara yi musu tambaya, Yazid ke da karsashin amsa tambayoyin, tun da shi ya yi Assignment ɗin, sai dai ba ya iya public speaking da harshen turancin yadda yakamata, a rubuce ne dai ba laifi, amma banda a baki.
Yana ƙoƙarin bada amsar, sai larabci ya suɓuce masa, ya dinga haɗawa da hausa yana bayani.

"Kai Malam, bafa ajin larabci bane, ba nahawu muke yi ba, da turanci zaka mana bayani" cewar wani ɗalibi.

Yazid ƙoƙari yake ya kuma gudanar da bayanin, amma turancin yaƙi fita yadda yakamata.

Ana haka, Amra ta kuma yankowa Yazid wata tambayar.

Ƙoƙarin amsawa yake, gashi ya san amsar, amma bisa kuskure sai ya dinga haɗawa da larabci, babban abin da ya ƙonawa Fadila rai, bai wuce yadda wasu daga 'yan ajin ke masa dariya ba, ba ita ake yiwa dariyar ba amma abin ya ƙular da ita sosai.

Shi dariyar da suke masa, bata dameshi ba, ganin turancin ya ƙi yiwuwa kawai ya juya harshe zuwa larabci, ya dinga zuba bayani, wanda ya tilastawa 'yan ajin yin shiru suna kallonsa, ba zaka taɓa cewa ya jii hausa ba.

Fadila ce ta fara yi masa tafi, 'yan group ɗin ma suka ɗau tafi, lecturer kam zuba musu ido yayi yana kallon ikon Allah, ya miƙe tsaye ya ce "Kai Sheikh haka za muyi da kai, wa zai fassara mana me kace mu da bama jin larabci?"

Yazid ya ce "Sir, ban iya turanci ba, kuma na ji sun ce ba sa so da Hausa".

Lecturer ya dafa kafaɗar Yazid ya ce "Ka burgeni sosai, Allah ya ƙara hazaƙa, ina ɗan jin larabci kaɗan, na kuma fahimta, and you zaki zo mini da abin da kika fahimta a bayanin da yayi a next lectures" lecturer yayi maganar yana kallon Amra.

Lecturer yayi nasiha sosai, da nuna musu kuskuren abin da suka yi, na son ƙure Yazid dan bai iya turanci ba.

Fitar lecturer babu daɗewa, class rep ya fita gaban allo, ya dinga faɗa a kan abin da Amra da wasu 'yan ajin suka yiwa Yazid, duk da irin taimakon da yake musu, a kan koya musu wasu abubuwan da ya shige musu duhu.

Amrah ta ce "Nifa bana son raini, ai naga Fadila ce ta fara yi masa dariya a ajin nan a kan bai iya turanci ba, amma ba wanda ya ce mata komai dan ana tsoron ta sai ni"

"Kar ki ƙara saka sunana a shirmenki, ni ba sa'ar yinki bace wallahi" Fadila ta faɗa daga wurin da take tsaye, tana ƙoƙarin haɗa jakarta ta fice.

Hayaniya ce ta nemi ɓallewa a ajin, Yazid kuwa tuni ya sulale yayi tafiyarsa.

Saura ƙiris Fadila ta tsinke Amra da mari, da ƙyar aka lallaɓata aka sallameta ta tafi, dan Fadila ba ta fiye shiga harkar mutane ba, amma idan ama taɓata ta ƙware a masifa, bata ragawa kowa.


Kusan ƙarefe goma saura na dare, Mummy ta shiga in da su Amina suke, ta ƙwanƙwasawa Hajara ƙofa, Hajara ta buɗe ta fito tana mutstsuka ido, alamun ta fara bacci.
Hajiya Zainab ta kalli Hajara a yatsune ta ce "Ki dafawa baban su Fadila tea, ki ajiye masa a dining, zai fito ya sha" Hajara ta risuna ta amsa da to.

Haka ta shiga kitchen, kamar tayi kuka, dan taji daɗin baccin da ta fara yi.

Ta kammala dafa shayin, ta fita falo, ta tarar da Alhaji Ahmad a zaune a falon.

Ta risuna ta ajiye masa shayin, ya miƙe tsaye, ba tare da ya kalli Hajara ba ya ce "Ajiye a nan, ki turo Amina ta kai mini falona" daga haka ya wuce ya barta saroro tana binsa da kallo.



Hurry up and subsribe the VIP GROUP
at affordable price.
08081012143
07063065680
GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


35

"Too wai meke faruwa a gidan nan ne?" Hajara ta faɗa a fili, sai da ta gama surutanta da mamaki, sannan ta tashi ta tafi kiran Amina"

Amina na zaune a tsakiyar katifarta, ta baje litattafanta, tana ta aikin nata na karatu.

Hajara ta ɗaga labulen ɗakin Amina, ta kalleta, ita lamarin Amina ya fara bata tsoro, kullum tana nace da littafi kamar masifa, har aiki idan tana yi, tana kallon littafi, saboda tsananin saka boko a ranta.

Amina da bata son Hajara ta shigo ɗakin ba sai yanzu da ta ɗago kai, ta ganta a tsaye tana kallonta.

"Lafiya kuwa?"

Hajara ta ɗan geɓare baki ta ce "Maigidan nan ya ce ki kai masa shayi falonsa, yana son ganinki"

"Ni kuma? Ba ke na jiyo Hajiya tana cewa ki dafa masa shayin ki kai masa ba?"

"Na dafa masa, amma ya ce ki kai masa" Hajara ta faɗa a hasale.

Haɗe rai Amina tayi tana ɗan tura baki, ganin Hajara ta zuba mata ido, tana nazartar action ɗinta ya sanya Amina ta ce "Ina shayin ya ke?"

"Mhmm yana falo"

"To zan kai masa, ina ga zai mini maganar tafiyar mu Abuja ne, wurin competition, ina ga makarantarmu sun masa magana" tayi maganar cike da son kawar da mugun tunani da mummunan zargi a zuciyar Hajara.

Amina ta ɗan buɗe baki ta ce "Au Wai dagaske Habujar zaki?"

Amina ta ce "Ai ban sani ba, sun ce zasu kira shi a waya ne su sanar masa, ina ga shi yasa ya ce in kai masa shayin, bari in je" Amina ta miƙe ta zura dogon hijjabi, a kan kayan da ke jikinta na bacci.

Hajara tabi bayanta da kallo ta ce "Lallai yarinya, ni zaki rainawa hankali, zan zuba ido dai in ta bibiya"

Amina ta ɗau kayan tea ɗin, ta tafi falon Daddy, tana fatan Allah yasa idon Hajiya Zainab biyu, kuma ya sanya tana ɗakin, yadda tana ajiye masa tea ɗin zata dawo ta cigaba da sabgarta, dan bata son wani abu ya sake haɗata da Daddy.

Da sallama ta shiga falon, yana sanye da jallabiyya fara ƙal, hannunsa riƙe da remote. Ya amsa mata ba tare da ya waiwayo ya kalleta ba.
Ta zo gabansa ta ajiye tea ɗin a kan center table. Ta juya zata tafi ta tsinkayi muryarsa yana faɗin "Sai yanzu kika ga damar zuwa?"
Tsayawa tayi cak tana kallonsa, tayi masa shiru tana kallon gefe guda.

"Zo nan" ya faɗa cikin command.

Ta juyo ta dawo ta tsaya a gabansa tana kallon ƙasa.

"Zaki saka kaina yayi ciwo, kin tsaya mini a ka kamar sa'anki"

Ta nemi wuri a ƙasa ta zauna, tana cukuikuye hannunta a hijjabinta, kamar mara gaskiya.

Ya ɗan kalleta ya kallia shayin ya ce "Haɗa mini tea"

Ba musu ta matsa gaban teburin, ta fara haɗa tea, tana tunanin ina Hajiya Zainab take, a irin wannan lokacin da har Daddy ke samun damar keɓewa da ita? Zancen zucin da take, ya bata damar antaya sugar da yawa a cikin shayin.

Sai da ta gama haɗa tea ɗin nan, sannan ya kalleta ya ce "Amma bani kika haɗawa ba ko?" Yayi Maganar yana tsareta da ido. Ta ɗago da sauri ta kalleshi.

Ya ce "Eh mana, wannan kan ki kika haɗawa, wannan sukarin da kika zuba, idan na sha ai sai in rasa raina, kodayake dama haka kike so ko? Oya  Sake haɗa mini wani ki shanye wannan da kika cika sugan"

A raunane ta ce "Ni na ƙoshi"

"Ai kuwa sai kin sha, haɗa mini wani"

Haka ta sake haɗa masa wani, ba tare da ta zuba sugar sosai ba, ta ajiye masa.

Ta tsaya jiran ya bata umarnin tafiya.

"Ki ɗauki shayin nan ki shanye na ce"

"Wallahi na ƙoshi" tayi maganar kamar za tayi kuka.

"Sai fa kin sha" Amina tayi shiru tana mamakin wannan takura haka.

Ya cigaba da shan shayinsa, kamar ya manta da ita a wurin, can har ta fidda ran zai magana ya ce "Meyasa na bada abu a baki, dan kin raina ni kika dawo mini da shi ko? Kuma kika daina gaisheni, gani ga ki idan muka haɗu, sai kiyi fuska ki ƙi gaisheni, meye dalili?"

Tuni ƙwalla ta taru a idon Amina, ta ce "Bakomai"

"Akwai ko mai, sai kin gayamini dalili, ko mu kwana a nan tare"

Ɗan waro idanunta tayi, amma ba ta iya cewa komai ba.

"Wallahi idan na rufe ƙofar falon nan da mukulli, sai kin kwana a falon nan, kuma kin San halin Zainab ni ba ƙwatar ki zan yi ba a wurinta"

Cikin marairaicwa Amina ta ce "Dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban rainaka ba Daddy"

"To menene idan ba raini ba" ya faɗa yana zuƙar tea hankalinsa kwance.

"Ba kai ne ba" sai kuma tayi shiru, saboda kukan da ya ƙwace mata.

Daddy ya ce "Ikon Allah, to gama kukan sai ki mini bayani, kafin ki gama ma na gama shan shayin nawa"

Aikuwa Amina ta gyara zama, ta dinga kuka, sai da tayi mai isarta ba tare da Daddy ya ce tayi shiru ba, tana yi ta goge hawaye da hijjabinta.

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Kinga ga tissue nan, ki dinga goge hawayen da majinar da ke ƙoƙarin zubowa, kar ki mini ƙazanta ina cin Abinci" aikuwa sai ta ƙaro sautin kukan nata, jin ya jefeta da kalmar ƙazanta.

Ya ce "Cigaba da ɗaga murya, Allah yasa ta jiyo ki, ta zo ta tarar da ke kin saka mijinta a gaba kina kallonsa"
Ba shiri Amina ta fara ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Shi kuma ya dinga murmushin gefe ɗaya, yadda ba zata gani ba.

Sai da ta gama kukan, sannan ya ce "Masha Allah, in kin gama ina jinki"

"Ba kaine Kai mini gori ba, shi yasa na dawo maka da wayar ka"

Dariya yayi ya ce "Subhanallah, Ohh ni Ahmad, to mai yasa kika daina gaishe ni"

"Daina amsawa kayi, idan na gaisheka sai ka harareni"

Sosai Alhaji Ahmad yayi dariya da jin abin da Aminar ta faɗa cike da wauta da ƙuruciya.

"Ni Ahmad naga ta kaina, na yi miki gori nace me?"

"Cewa kayi gidanka ba wurin tara maza bane, kuma ni Bakomai tsakanina da shi, ranar da ka ajiyeni a hanya ne, ya kawoni gida sai gaisawa da muke da shi shikenan"

"Saboda na ce Kar ki sake kawo wani gidan nan shine kike jin haushina? Amina na fiki shekaru, hankali da kuma gwagwarmayar rayuwa, muddin kika haɗa karatunki da shirmen samarin zamanin nan, to ba zaki mayar da hankali ba, idan ki ka biyewa samarin zamani da soyayya karatunma sai ya gagareki, soyayya ba abin da ba ta sakawa. kuma ni idan kin gaisheni ba hararki nake ba, bana amsawa ne saboda ki fahimci kin mini laifi, ki bani haƙuri amma ki kayi mirsisi ashe ke nan fushi kike dani ne ko? Wace irin 'ya ce haka mai fushi da babanta har ta daina kula shi, ya bata abu ta mayar masa anya kuwa kina Baban da ni?"
Amina tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Shikenan, ni bari in sauko in baki haƙuri"

Da sauri ta ce "A'a kayi haƙuri dan Allah kar ka bani haƙuri"

"To tunda fushi kike, har da cewa na miki gori gara in bada haƙuri ai"

"Kayi haƙuri dan Allah, bana fushi da kai"

"To sai kuma me nayi miki?"

"Kace mini ƙazama" ta faɗa har cikin ranta.

"Yaushe kuma na ce miki ƙazama?"

"Yanzu" ta faɗa tana tura baki.

"Eh ai ƙazamar ce, kalli yadda kika ɓata hijjabinki da hawaye, kuma haka kike mana girki, kina mana ƙazanta, shi yasa Abincin yake daɗi ashe".

"Mhmm ka daina ce mini ƙazama"

"To ki daina goge hawaye da hijjabinki"

Ya ɗan tsura mata ido, sannan ya ce "Jeki janyo drower can, wayarki na ciki, ki ɗauko ki haɗo mini da abin gwajin suga na" tamkar wata kurma haka ta tashi, taje ta ɗauko abin da ya sakata, ta dawo ta zauna, ya sauko daga kan kujerar ya zauna a kusa da ita, hakan ya sa ta sake takurewa.
Ya fito da kayan gwajin, ya yi gwajin sugan nasa, ya kalleta ya ce "Kin gani sakamakon daina kula dani, suga na ya hau duk abin da kika ga dama, dafawa kike ki bani, suga na ya hau ya kai sha biyu da ɗigo uku"

Ita dai ba tace masa komai ba, sai sunkuyar da kai, kamar mara gaskiya.

A ranta ta ce 'Hakkin azababbiyar matarka ne ai bani ba, abin da aka ce in dafa ai shi zan dafa'

Ya miƙa mata wayar ya ce "gata nan, lokaci lokaci, zan dinga karɓa ina dubawa"

Ta Sanya hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi, naga takalmi da jaka ma, Baba ya bani Allah ya ƙara buɗi"

"Amin rigimammiya, mutanen nan ma da kika mini Maganana akan su an biya musu kuɗin shekara biyu, na bawa Maigidan fili ya gina kamar yadda kika nema"

A gigice Amina ta kalleshi ta rasa me zata ce masa sai ta sake fashe masa da kuka.

"Ke wai komai ma kuka kike masa, tashi ki tafi Allah ya bamu alheri"

"Allah ya biyaka da Aljanna Daddy"

Yayi murmushi ya ce 'Ameen, tare da ke da kika ankarar da ni nayi aikin alkhairi. To Yanzu mu shirya ko?" Yayi Maganar ƙasa-ƙasa.

Ta ɗaga masa kai alamar eh.

"Bana son ɗaga kai, amsa mini zaki"

"Eh mun shirya" ta faɗa cikin jin kunyar abin da tayi.

"To shikenan, tashi muje in rakaki bakin ƙofa" ta miƙe tsaye hannunta riƙe da kwalin wayarta.

"Kun koma makaranta yau ko?"

Tace "Eh Daddy. kayi magana da Baban kuwa a kan tafiyar?"

"Kar ki damu, zamu yi maganar in sha Allah, ke dai ki cigaba da karatu"

"Ina nan ina yi, ka dinga yi mini addu'a"

"Sai kin biya tukuna, kawo abin sadaka, ai miki Adduar" dariya Amina tayi ta ce "Zan kawo, idan kai mini addu'ar na ci"

"To shikenan, kije ki duba wayar, abin da baki gane a ciki ba, sai ki mini magana"

"To Daddy na gode" ta juya ta fice, Daddy ya tsaya yana binta da kallo, harta ɓacewa ganinsa, sannan ya koma ciki, yana shafa gemunsa.

Hajar kuwa tun da Amina ta tafi wurin Daddy take yi tana leƙa falo zuwa kitchen, dan taga dawowar Amina, amma shiru babu Amina babu dalilinta, ji take tamkar ta zama tururuwa ta rarrafa taje ɗakin Alhaji Ahmad, ta gano meke faruwa Amina ta zauna haka? Tun tana zuba ido taga dawowar Amina har ta gaji, ta tafi ɗakinta ta zauna tayi shiru tana tunani, tashi ta kuma yi ta leƙa ɗakin Amina, ta tarar da ita a tsakiyar katfarta tana kunna sabuwar waya.

"Amina ashe kin dawo, naga kin daɗe daga kai shayi, ki kayi wannan zaman?"

"Kai Hajara, ban gane me kike nufi ba, da na kai masa shayin fa suna tare da Hajiya, na ajiye musu na tafi baranda na cigaba da karatuna, me zai zaunar da ni kuma?"

Sai kuma cikin borin kunya Hajara ta ce "Au, na zata wani laifin ki kayi ai, duk hankalina ya tashi, wannan sabuwar wayar fa" Amina ji tayi kamar ta zagi Hajara, amma idan ba ta bi Hajara a sannu ba, zata sanya kwaɓarta tayi ruwa, dan haka ta ce "A makaranta ne aka bamu, saboda mu dinga amfani da ita wurin karatu"

"Allah sarki, lallai wannan makaranta taku ana ji daku, lallai da safe na shigo a bani in gani" Amina tayi murmushin yaƙe, ta cigaba da kunna wayarta, bayan Hajara ta fita Amina ta raka bayanta da harara, cike da jin haushin saka idon da take mata.

Hafsa na cikin bargo ta ƙule, ta saka wayarta a silent, tare da rage mata haske, suna chatting da Khalil, sai su daɗe suna chatting basu san dare ya yi ba, ita kanta tana mamakin kanta yadda ta yi wani irin sabo da Khalil, wanda har ya kai idan Khalil baya son abu, har rawar jiki take ta daina, duk abin da ta san zata yi yayi farin ciki tana masa. Haka shima ɓangaren sa tattalata yake tamkar ɗanyen ƙwai a kan dutse, shima yana kaucewa duk wani abu da zai sanya ta ɓacin rai ko damuwa, yana matuƙar tausayinta, hakan ya sanya yake tattalinta yake gudun abin da zai ɓata mata rai ko tayi fushi.

A Hanyar Yazid ta tahowa makaranta, suka haɗu da class Captain ɗinsu, ya ɗauko Yazid a babur ɗinsa, suna tafe yana bashi labarin faɗan da Amra da Fadila suka kusa yi jiya, a kan abin da Amran tayi masa.
Yazid dai bece komai ba, sai ɗan murmushi da yayi, Captain ya cigaba da bashi haƙuri, a kan irin abubuwan da wasu daga cikin 'yan ajin suke masa.
Zuwansu yayi dai-dai da tsayuwar motar Fadila.

"Ahh Yazid ga Bestynka nan ta ƙaraso"

"Wace kuma Besty na?" Yazid yayi maganar cikin ko in kula.

"Fadila mana"

Ta rufe motar ta ɗan tsaya tana jiran ƙarasowarsu.

"Captain" ta faɗa tana ɗan murmushi.

Captain ya ce "Na'am tsigai, sarkin tsiwa"

"Kaga ka kiyayeni bana so"

Yazid yaƙi ko kallon in da Fadila take.

Ya yin da ita kuma take satar kallonsa, Captain ya ce "Bari in yi gaba ku gama ganawa, dama zan karɓo mana Assignment, sai kun taho" yayi gaba ya bar su a tsaye.

Captain na barin wurin, Yazid shima ya yi tafiyarsa ya barta a wurin, gaba ɗaya sai taji babu daɗi shareta da ya yi, ko dai Kankiya ya kira shi ya yi masa warning ne a kanta, shi ya sanya ya daina kulata?.
Ɗan taɓe baki tayi, ita ma ta nufi aji tana cigaba da zancen zuci.

Sai yau Azima ta dawo daga hutu, suka rungume juna ita da Amina suna ta murna. "Azima shi ne kika ƙi dawowa sai yau?"

"Ke bari, munje hutu da Mummy ne, sai jiya muka dawo"

Amina ta ce "Masha Allah, ya Mummyn?"

"Mummy na nan lafiya, ya Baba da mutanen gidanku marasa mutunci"

Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Meye haka?"

"Ba dole in faɗa ba, mutuncin ne da su? Wallahi matar nan ta bani mamaki Amina, a gaskiya kina haƙuri sosai, Allah ya ƙara miki haƙuri"

"To Azima idan ban yi haƙuri ba yaya zan yi? Tun da karatu nake son nayi"

"Ke zan yiwa Mummy magana, wallahi da zaki yadda ki dawo gidanmu, ki daina wannan aikin, Mummy zata dinga biya miki kuɗin makaranta, meye dubu sittin Allah na tuba, Mummy zata biya miki"

Waro ido Amina tayi ta ce "Azima dubu sittin kuma? Dubu sittin ne kuɗin makarantar?"

"Au ke da baki sani ba? Dubu sittin ne fa kawai duk term, sai sauran abin da ba a rasa ba, Mummy tana da kuɗi sosai, ga shi Daddynmu ya mutu ya bar mana kuɗi, ni da Yaya Sagir da nake gaya miki, wallahi da zaki yadda Mummy cewa tayi zata ɗauke ki ki dawo gidanmu, ita tana sonki"

Shiru Amina tayi tana tunani, Yanzu duk term naira dubu sittin Alhaji Ahmad yake biya mata na makaranta, kuma gashi ance na shekara ya biya mata, ga kuɗin litattafai da sauransu.

"Ya naji kin yi shiru? Zaki yadda ki dawo gidanmu?"

Firgigit Amina ta dawo daga tunanin da ta tafi, ta ce "Azima Baba ba zai yarda in nisa da shi ba, nima ba zan so hakan ba, amma naji daɗi da ƙauna da karamcin da Mummy take nuna mini, shi wannan aikin da nake na lokaci ne, watarana sai labari. Kuma in Allah ya kaimu next year fa zamu gama, da

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment