Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saku farinciki kamar yadda ku ka sani" ta ƙarasa maganar har da hawaye a idonta, dan ba zata iya misalta farincikin da take ciki ba.

Abdul ya yi murmushi ya amsa da "Ameen, ki dage kiyi karatu da kyau Allah ya bada sa'a, ga wannan in an fito break ki sayi wani abun" yayi Maganar yana bata ɗari biyar.

Girgiza masa kai ta yi ta ce "A'a na gode zan iya zama har a tashi ban ci komai ba, a ƙoshe nake" tayi gaba tana ɗaga musu hannu. Wani irin murmushi ne ya suɓucewa Abdul, yarinyar ta burge shi, duk da ɗan karen surutunta, amma acting ɗinta zai tabattar maka da ga gidan tarbiyya take.
Tsakin Khalil ne ya dawo da shi daga tunanin da yake, ya bi bayansa zuwa mota, suna tafe Abdul na yiwa Khalil hirar Amina da yadda ta burge shi. Banza Khalil ya yi masa, dan tun haɗuwar sa farko yarinyar ta yi masa tsiwa yake jin haushinta, ga ta da shegen surutu da iyayi kamar jefaffiya.



An samu numfashin Yazeed ya daidaita, sai bacci da yake yi, saboda allurar da aka yi masa, har azahar Fadila ta je ta yi salla ta dawo bai farka ba, tana nan zaune taga ya fara motsawa a hankali, ta zuba masa dukkanin idanunta, dan babban fatanta dama shi ne taga ya tashi ya warware. Captain ya kira Fadila a waya cewar 'yan ajinsu zasu zo duba Yazeed, amma tace ya ware an sallame shi, saboda bata son ƙananan maganganu.

A hankali ya buɗe idanunsa, yana ƙarewa ɗakin kallo, ya kalli hannunsa dake ɗauke da canular anyi hanging ɗin drip.
A hankali ya juya ɗaya ɓangaren, ya yi tozali da fuskar Fadila, sai da gabansa ya faɗi, ƙoƙari yake ya gane, zahiri ne ko mafarki.
"Sannu" ta furta kamar an mata dole.
Ya jinjina mata kai alamar yauwa.
"Ina ne nan?" Ya yi maganar yana kallonta.
"Da ina ya yi maka kama?"
"Yi haƙuri gani na yi ban san environment ɗin ba, dan Allah zan sha ruwa" ya ƙarasa maganar da sigar magiya, tare da tashi zaune ya jingina.
Kamar ya yi mata dole, ta tashi ta buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ɗakin, ta ɗauko ruwan roba mai sanyi ta miƙa masa. Ruwan sanyi ƙarara dan haka ya karɓa ya ajiye a gefe.
"Ba zaka sha ba ka sa na ɗauko?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
"Yayi mini sanyi da yawa"
Doctor Aliyu ne ya shigo ɗakin, ya tarar da Yazeed a zaune "Masha Allah, Alhamdilillah ka farfaɗo kenan?" Ganin farar riga a jikin Aliyu ya sanya Yazeed gane cewa likita ne.

"Eh doctor".
"To yaya kake jin jikin yanzu?"
"Alhamdilillah, bana jin ciwon komai, sai rashin ƙwarin jiki".
"Ok, shima insha Allah zai ware, for how long kake da Asma?"
Yazeed ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Gaskiya an jima, da farko pnuemonina ne, sai ya koma asma, to daga baya ya zama chronic, a hankali kuma da na ƙara girma, sai na rage samun attack ɗin, dan har ina aiki a cikin hayaƙi, ƙura idan ba tayi yawa ba ba ta damuna, rabona da ciwon ya tashi nafi shekara huɗu, sai yau na sheƙi hayaƙi da ƙura, na fara tari kuma daga nan ban san abinda ya sake faruwa ba"
Haka kurum Yazeed ya bawa Fadila tausayi, ya sha wahala sosai daga ɗazu zuwa yanzu. Nan Aliyu yayi ta bawa Yazeed shawarwari tare da rubuta masa wasu magungunan, ya ce a sayo masa wani abun ya ci.
Fadila ta fita ta bawa security Asibitin kuɗi, dan ya siyo wa Yazeed Abinci.
Mamaki ne fal da tambayoyi a cikin ran Yazeed, amma ya san idan ya tambaya ba zai samu gamshashiyar amsa ba, sai ma dai baƙar Magana.

Sallamar Yusra ce ta katse masa tunaninsa, Fadila na ganin Yusra ta miƙe tana faɗin "Beb sai da ki ka zo?"

"Na kasa jurewa ne, na ce gara in zo in ga mai jikin, kuma naga Alhamdilillah shi ne a zaune ko?"

Fadila ta ɗan taɓe baki ta ce "Sannu bawan Allah"
Yazeed ya ce "Yauwa sannu da zuwa"
"Allah ya sa kaffara ne"
Ya amsa da Ameen.
Security ne ya shigo da ledar wani restuarant, ya miƙawa Fadila ta sa hannu ta karɓa ta ciro dubu ɗaya ta bashi, ta fito da takeaway ɗin, ta buɗe dankali da miyar jajjage sai uban yankan naman kaji a kai, ta ajiye wa Yazeed ta ce "Gashi nan kaci, Aliyu ya rubuta maka sallama, in ka gama sai in ajiyeka a gida in wuce gida".

Yazeed ya ƙurawa Abincin ido, amma yaƙi ko motsawa balle ta sa ran zai ci.
"Magana fa nake maka kai mini banza"
"Alhamdilillah na ƙoshi" ya furta yana kaucewa haɗa ido da ita.
"Ban gane ka ƙoshi ba, amma a gabanka ya ce a samo maka Abinci ko?"
Yusra ta ce "Kai kuwa ka daure ka ci mana, ko baka cin irin wannan?".
Yazeed ya ce "Wannan ba cimata bace ta ɗan talaka, ba zan iya cin Abincin nan ba, Na gode sosai da kulawarki a gareni Fadila, ba zan manta ba har abada, amma wannan cimar ku ce ba irin tawa ba, zan ƙarasa gida na samu abin da zan ci a can"
Tsaki Fadila ta yi ta miƙe tsaye, ta kalli Yazeed cike da masifa "Ni zaka rainawa hankali ka gayawa baƙar magana, in wuni a Asibitin nan saboda kai, na san silata ciwonka ya tashi amma ka raina mini hankali, tun safe nake Asibitin nan saboda kai, ko ruwa ban kai cikina saboda zullumi, amma daga tashin ka ka fara ɓata mini rai" ta cillo masa ledar magungunan da aka kawo daga Pharmacy ta ce "Gashi nan, idan ka ga dama ka ɗauka shima idan ba ka ga dama ba ka barshi a wurin aikin banza kawai"
Yusra ta riƙota tana faɗin 'Haba Fadila ba a haka, ai sai ki zobe ladan ki, baki ga ba shi da lafiya ba, ki dinga haƙuri dan Allah"
"Dalla sakar mini hannuna, ba za ai haƙurin ba" ta figi jakarta tayi waje fuuu.
Yazeed kam murmushin gefen baki yayi, ya sauko daga kan gadon a hankali, Yusra tayi ta bashi haƙuri ya ce "Bakomai kar ki damu" sun kai ruwa rana da Yusra kafin ya yarda ya karɓi maganin, shima mutuncin yarinyar ya gani ya karɓa.
Ya shafa aljihunsa ya ji babu komai, dan haka ya sadaƙar jotter sa, da hamsin ɗin jikinsa sun zube, a halin da yake ciki ya fara daɓawa da ƙafafuwan sa dan tafiya gida, ya samu masallaci ya rama sallolin da bai yi ba, daga nan ya wuce gida.


Ƙarfe biyu Abdul ya addabawa Khalil a kan su koma su ɗauko Amina, ko da suka koma tana in da Abdul ya ce ta tsaya, goye da ƙatuwar jakarta ta makaranta.
Tana ganin motarsu ta faɗaɗa fara'arta, ta ƙarasa ta buɗe motar ta shiga, wannan karon Khalil ne yake tuƙi dan a motarsa suka zo, ta gaishe su Abdul ya amsa, amma Khalil ya yi mata banza.

"Amina 'yan makaranta, ya makarantar ya baƙunta?".

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, bari in nuna maka litattafaina an cika mini jakata da litatafai, gobe in Allah ya kaimu za a bani Uniform, Baba ya sai mini takalmi da safa"
Ta zuge jakar tana nuna masa, yace "Masha Allah, Allah ya sa a amfana, bari da yamma zanje da kaina in sayo miki takalmin".
Amina ta girgiza kai ta ce "A'a Baba fa zai saya mini, kar ka damu, sai daɗi nake ji na koma Makaranta".
Abdul ya ce "Sai kice Alhamdilillah, wai ni kuwa ya aka yi kika iya turanci haka?".
"Malaman mu ne suke koya mini, a makarantar mu ana zuwa da ni debate ko quiz, su suke koya mini, kaga kuma muna da ƙaton Library, amma babu ɗalibai sosai 'yan garinmu ba su damu da karatun ba, akwai litattafai sosai a ciki, kuma ina da dictionary da nake duba Words, mu uku ni da wasu ƙawayena ake mana extra lessons a ƙauyenmu"
Abdul ya jinjina kai ya ce "Lallai ashe gifted ce?"
"A'a ni ba gifted ba ce, dagiya nake yi in gaya maka"
"To ya aka yi ki ke son cigaba da karatu a nan? Ko can babu senior secondary School".
Yamutsa fuska ta yi, ta tura baki sannan ta ce "Ƙannen Baba ne za su yu mini Aure, wai ba sa son ina zuwa boko, ni kuma na gudo wurin Baba"
"Da an yi asarar talent, wannan ƙwaƙwalwar ta ki atleast yakamata ko secondary ki kammala ai"
Amina ta sake ta dinga bawa Abdul labarin yadda tai karatu a ƙauyensu faɗi ba a tambayeka iri iri.
"Ke shut up dalla!" Khalil ya buga mata wata uwar tsawa, da sai da cikinta ya kaɗa.
Abdul ya ɓata fuska ya ce "Khalil ya haka?, Ya muna hira da yarinya zaka yi mata tsawa?".
"Duk ta bi ta cikawa mutane kunne, ko haɗiyar yawu ba ta yi, i hate nonsense, ta kuma magana Wallahi sai ta sauka".

"Khalil waye ya gaya maka irin wannan yaran ana katse musu hanzari? A irin wannan surutun nasu ba sa na banza, kuma ba a kan karatu take Magana ba?" Khalil yai wa Abdul banza ya cigaba da tuƙi. Tun da Amina ta firgita da tsawar da Khalil ya yi nata kasa magana ta yi, sai jikinta da ke ta tsuma.

A ƙofar gida suka sauketa, ta yiwa Abdul godiya ta shiga gidan. Khalil ya wuce kai Abdul gida, suna tafe suna faɗa. Abdul ya ce "Kana hantarar 'yar mutane ba abin da tayi maka, ƙila ma ita zaka saka a wannan gidan da kake ta ƙerawa"
Khalil ya ce "Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, da Mummy kaɗai ta isheni, kai idan aka ce zan auri wannan yarinyar sai ka yadda?"
"Eh mana ba mace ba ce? Meye aibunta 'yar duma duma black beauty"
"Yawwa an zo wurin, sai kace mini sonta ka ke yi"
Abdul ya ce "Ai ni ka san wadda nake so, kuma alamu sun nuna ba za ka bani ba"
Kalil Yayi guntun tsaki ya ce "Kai ka fiye shirme Wallahi" daga haka ya basar da zancen ya kai Abdul gida ya sauke shi yayi gaba.
Wata hanya ya biyo, domin ya yi yanke, ya samu sauƙin go slow.
A ƙofar wani kanti yayi parking, dan ya sai ruwan roba, na motarsa ya ƙare, ya miƙawa wani yaro kuɗin ya ce ya karɓo masa.
Ya gyara zamansa, ya kashingiɗa da seat ɗin motar, ya ɗan waige ya hango wata matashiyar budurwa tana juya awara a cikin mai, tana sanye cikin gogaggen hijjabi ash, sai dai fuskar nan tata a ɗaure tamau, wani matashi na gefenta a kan babur, da alama tsarata yake yi, amma ko sau ɗaya ba ta ɗaga kai ba, balle ta kalle shi!.


Follow my Arewabooks Account
Ayshercool7724
Watpad
Ayshercool7724
08081012143

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


Domin samun update a kan lokaci, ko samun book ɗin daga farko
Follow me on
Watpad Ayshercool7724
Arewabooks Ayshercool 77724
What's app
08081012143



P11



Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda take gabatar da sana'ar ta ta cikin nutsuwa, ba hayaniya ko ƙazanta komai nata a nutse, amma mamaki ne ya biyo bayan tunanin da yake yi, me wannan budurwa take haka a titi? Yafi dacewa ace  tana gidan Aure, ko kuma tana makaranta, amma kalleta a titi tana suya.
Yaron da ya aika ne ya kawo masa ruwan, ya barwa yaron sauran canjin, ya cigaba da kallon in da Hafsa take, sai dai yadda take gudanar da lamarin nata ne, da gani ka san za ta yi izza, saboda sai shan ƙamshi take, tare da haɗe rai dan kar ma wani ya kawo wargi. A hankali Khalil ya yi you tune, ya koma hannun da Hafsat ke zaune tana gudanar da sana'ar ta. Parking ya yi a gefenta, ya fito daga motar, ya ƙaraso in da take suyar awarar ya kalleta ya ce "Sannu dai" ba tare da ta ɗago ba ta amsa masa ƙasa ƙasa da 'Yawwa".

Ya miƙo mata dubu biyu ya ce "Zuba mini abin nan na 2k" wani irin kallo Hafsa ta yiwa Khalil, irin kallon ka raina mini hankali ma, ba ta ce masa uffan ba, ta cigaba da sallamar yaran da ke gabanta.
Khalil gani ya yi ba ta da niyyar sake ko ɗaga kai ta kalleshi, ya kuma matsawa ya ce "Magana fa nake yi, ki sa mini na 2k"

"Ka bari idan ka san sunan abin da nake sayarwa, sai ka dawo in sayar maka" ta bashi amsa.

Khalil ya ce "To, ikon Allah am serious ki karɓa ki bani".

"Malam nace ka bari ka san sunan abin da nake sayarwar sai ka siya".

Yaron da ke tsaye zai sayi awara ya ce wa Khalil, "Sunan abinda take sayarwa Awara".

Khalil ya ce "Ok na gode sosai, ki bani awara ta dubu biyu".

Ba tare da kalleshi ba ta ce "Ni awarata ba ta kai ta dubu biyu ba, ta ɗari biyar kawai za ka iya samu".

"To bani ta ɗari biyar ɗin, sai ki riƙe canjin"

Hafsat ta ɗago idanunta ta harari Khalil ta ce "Malam ba fa bara nake ba, sana'a nake yi".

"Ai nima bance bara kike ba, kyauta ce kawai na baki, ta ɗari biyar ɗin ki rabawa yara sadaka, sai ki riƙe canjin".

Ba ta kuma tankawa Khalil ba, ta cigaba da iza wutarta, ya tsaya ya zuba mata ido, ta gama soya awarar dake cikin mai, ta zuba masa a leda ta miƙa masa .

Khalil ya ce "Ai ba ni zaki bawa ba, sadaka zaki bayar".

Hafsa ta ce "Ai kai ma kana da hannu, zai fi kyau ace kai ka raba musu da kanka" Nan Khalil ya shiga jinjina halin yarinyar, ana mata abin Arziƙi amma ba ta gani, sai jin kai da tsabar taƙama.

Ya sa hannu ya karɓi ledar awarar, ya miƙa mata dubu biyun, ta kalli hannunsa da yake riƙe da dubu biyun, ta ɗauke kanta ta cigaba da sabgar gabanta.

"Ikon Allah, yau Allah ya haɗani da gamona, to ga dubu ɗaya tun da ba zaki karɓi dubu biyu ba".

Nan ma ɗauke kai ta yi, ta ƙi kallon in da Khalil ya ke.

"Idan ba zaki karɓa ba zan tafi da awarar ba tare da na biya ba".

"Ka daɗe baka tafi ba" ta furta a hankali.

Khalil ya durƙusa ya sa mata dubu ɗayan, a gefenta sannan ya juya ya fara tafiya.
Ko ɗago kanta ba tayi ba, balle ta dubeshi, fifita wutar ta kawai take yi.
Yayi gaba ya bawa wasu almajirai awarar, ya kuma waiwayawa yana kallon Hafsa, cike da mamakin wannan tsatstsauran ra'ayi nata.




Amina kuwa tana shiga gida, ta tarar da Baba ya dawo daga ƙauye, wurinsa ta nufa cikin fara'a, shima ya tareta da murmushi yana faɗin "Alhamdilillah".

"Baba an kai ni Makaranta, na zama 'yar Makaranta".

"Alhamdilillah, Allah yayi miki Albarka ya cika miki burinki 'ya ta".

Amina ta ce "Ameen, ka san wani abu Baba?".

"A'a sai kin faɗa uwata".

"Baba sufa wannan makarantar a aji biyar ake gamawa, babu aji shida, zuwa baɗi ta gaba insha Allah zan gama sakandare".

Baba ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya baki miji na gari a birni kiyi Aure, wanda zai kula da cigaban karatunki" Jikin Amina yayi sanyi ta ɗan yi shiru tana nazari.

Baba ya ce "Ya kika yi shiru, ko kin fi son ki koma ƙauye ki auri Jarmai?" Da sauri ta ɗago ta kalli Baba ta ce "A'a Baba, nifa ko sunan Mutumin nan bana ƙaunar ji, ni ban tambayeka ya hanya bama, ya ka baro  Inno?".

"Duk suna lafiya sunce a gaishe ki, Jarmai kuma ya sa su Yaya Bala a gaba a kan lallai su biya shi kayan Auren da ya kai, yazo ya sameni wai nima saina biya shi, ni kuwa nace masa sisinsa ban gani ba balle in ci, dan haka yaje can wurinsu ya karɓa, amma da ina da kuɗi da na rage masa wani abun".

Amina ta kalli Baba ta ce "Ka jika Baba, Mutanen da ba tare da kai suka ci kuɗin ba, akan ne za ka biya abinda ba kai ka ci ba, banda asarar da suka yi maka ma. Baba kalli litattafaina fa, wai duk wannan litattfan nawa ne" tayi maganar tana nuna masa cikin jakarta.
Baba ya buɗe baki, text books kawai sun kai goma sha shida, banda na rubutu, ga math set, da calculator komai akwai, shi kansa Baba ya san wannan kayan sun fi ƙarfin kuɗin aikin da Amina take yi musu.
Baba ya ce "Uwata mutanen nan sun mana karamci, duk na san kina da ƙwazo, amma ki ƙara sannan ki ƙara yi musu godiya, idan mai gidan ya dawo, ki kuma yi masa godiya".

"Insha Allahu Baba zan masa, idan na yi salla fa har Addu'a nake masa, Allah ya ƙara masa Arziƙi da lafiya, ba zan manta alkhairinsa ba"

"Yauwa uwata, har 'ya'yansa ma da matarsa da ahalinsa duk ki dinga saka su a Addu'a".

Amina ta ɗan tura baki ta ce "wannan 'ya'yan nasa da basu da kirki".

"A'a fa uwata, yanzu ba Makaranta ɗansa ya kai ki ba? Idan mutum ya miki ba daidai ba, ki bishi da alkhairi albarkacin addu'a da kike musu, sai Allah ya miki abin da ba ki zata ba"

"To Baba zan dinga yi musu insha Allah, bari in je in wanka nayi salla, ka ci Abinci kuwa?"

"Eh naci, Hajara ta kawo mini, maza kije ki yi salla"

Ta amsa da to Baba, ta miƙe ta shiga cikin gidan, cike da fara'a da jin daɗi.

Kallo ɗaya Mummy ta yi mata tare da kwaɓe baki, ganin yadda ta goyo uwar jakar Makaranta tana washe baki.
Amina tayi mata sannu da gida, amma da ƙyar ta iya amsa mata. Hajara ma tsokanar Amina ta dinga yi, tare da tayata murnar samun cigaba da zuwa makaranta.

Fadila ba ta dawo gida daga Asibiti ba, sai bayan biyar na yamma, ta dawo a gajiye matuƙa, kuma rai a ɓace saboda abin da Yazeed ya yi mata, kai tsaye sashenta ta wuce, ba tare da ta nemi ko in da Mummy take ba, dan ba abin da take son yi, banda ta yi wanka tai salla ta ci Abinci.
Duk da ranta a ɓace yake, amma abin da ta tarar a part ɗinta, yayi mata daɗi sosai. Tayi wanka tayi salla, ta fito ta nufi kitchen da kanta, a kitchen ta tarar da Hajar da Amina na ƙoƙarin ɗora girkin dare, sai bawa Hajara labarin makarantarsu Amina take yi.

"Wacece ta gyara mini ɗaki a cikin ku yau?".

Amina ta ce "Nice".

"Biyoni" ta yi maganar cikin bada umarni. Bayan Fadila Amina ta bi, tana fargabar kar abin Arziƙi ya zama na tsiya.
Da suka ƙarasa ɗakin Fadila, Fadila ta ƙare wa ɗakin kallo sannan ta ce "Naga aikin da ki ka yiwa ɗakin nan, kin canzan labulaye kin wanke waɗancan, kin ɗaga gado da wardrobe kin gyara kin canza musu fasali, na ji daɗin hakan, keep it up Ina son sauye sauyen Abubuwa lokaci zuwa lokaci".

Amina ta ce "To insha Allah"

Fadila ta ce "ɗan tsaya" ta ƙarasa ta ɗakko wata babbar ledar siyayya ta store, ta sakawa Amina turamen atamfa uku, da dogayen riguna, sai hoda da turare ta ce "Gashi nan kije kya saka" Amina ta karɓa cikin fara'a ta ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi" ta amsa da Ameen.

Sai da Amina ta fara zuwa ta nunawa Baba kayan, sannan ta je tana nunawa Hajara, sai dai ran Hajara ya sosu, dan tun da take ba'a taɓa bata makancin wannan kyautar ba a gidan.

Amina ta ce "Yaya Hajaru, ki ɗau doguwar riga ɗaya, zan ɗinka atamfa biyu in ajiyewa Inno ɗaya".

A fuska Hajara ta ce "An gode madalla" amma a zuciyarta kuwa sam ba ta ji daɗin hakan ba.

Tun da Khalil ya baro wurin Hafsa yake tunanin mai ya fito da ita zaman titi da irin wannan sana'ar haka? Gashi ita ba gwanar fara'a ba, balle ya samu ya tambaye ta, to matar da ko fara'a ba ta yiwa kwastomominta, ga taƙamar tsiya ina zata saki jiki har kayi mata wasu tambayoyi?
Duk yadda ya so ya manta da batun Hafsa, ya cigaba da sabgarsa, amma ya kasa, duk in da ya motsa tunaninta kawai yake yi, har haskowa yake irin kyan da zata yi, idan har tayi dariya ko murmushi.


Bala'in Jarmai ya sanya su Bala a uku, dan duk in da ya tsuguna zaginsu yake a garin nan, kuma duk inda ya gansu ya dinga yi musu tijara kenan a kan kuɗin aurensa.
Haka suka ƙuƙuta, suka mayarwa da dillaliya kayan gadon da suka saiwa Amina, amma tayi musu sayen wulaƙanci, suka tattara dubu talatin da ƙyar suka kai masa, a wulaƙance Jarmai ya karɓa sannan ya kalli Kawu Bala ya ce "Amma dai ka san na baku kuɗi sun kai dubu tamanin ko?"

Bala ya ce "Haka ne"
"To banci nanin ba, nanin ba zata ci ni ba, ba ƙira ba abin da zai ci gawayi, ina ganin mutuncinku ne shi yasa ban kai ku ƙara birni ba, kuma wannan dubu talatin na karɓeta ne dan kar nayi biyu babu, amma daga nan zan fara wucewa wurin mai gari, in fara kai masa ƙarar".

Kawu Lawan ya ce "Haba Jarmai, dan Allah kar mu yi haka da kai mana, insha Allah zamu ciko maka sauran kuɗinka, kayi haƙuri".

Jarmai ya gyara wata daƙalƙalalliyar babbar rigarsa ya ce "Ai haƙuri shi ne kawai in ga uwar kuɗina a hannuna".

Kawu Bala ya ce "Insha Allah, zamu cigaba da lalubawa zamu baka sauran kuɗinka" da ƙyar suka lallaɓa Jarmai, ya haƙura bai kai su ƙara ba.


Washegari da Fadila ta koma Makaranta, Captain ya tambayeta ya mai jiki, ta sanar da shi tun a jiyan aka sallame shi ya tafi gida, 'yan aji suna son suyi tsurku su ji yadda abubuwa suka wakana, amma sanin halin Fadila ya sanya ba wanda ya tanka mata.
Ta dinga zuba ido, ta ga ta ina Yazeed zai shigo aji, amma babu Yazeed babu alamar sa, har aka yi lectures ɗin ranar aka gama.
Nan cikin Fadila ya sake ɗurar ruwa, ta san ba zai wuce ace jikin ne ya hana shi zuwa Makaranta ba, nan zuciyarta ta dinga saƙa mata abubuwa daban daban, ciki har da tunanin ko jikin ne ya tayar masa ya mutu? Nan da nan ta yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranta.
Da aka tashi daga Makaranta ta samu Captain ta ce "Musa, kun yi waya da gayen nan ne?"

Captain ya ce "Wa kenan?".

"Wanda muka kai Asibiti jiya"

Murmushi ya yi ya ce "Hajiya Fadila ta mu, sunan nasa ne ma ba za a iya faɗa ba. Wallahi tun jiya nake kiran wayarsa, amma ba ta shiga, kuma ina kyautata zaton jikin ne ya hana shi zuwa yau" Fadila ta ce "Ok shikenan"

Daga haka ta wuce ta nufi motarta, tana cigaba da tunani.

A kwanakin nan kowa da abin da ya dame shi a jama'ar gidan, Khalil ya kasa sukuni saboda tunanin Hafsat, gashi ya kuma komawa amma bata nan bai sameta ba.
Fadila kuwa gaba ɗaya tunanin halin da Yazeed yake ciki ne ya dame ta, dan a rayuwarta bata taɓa aikata abin da ya dameta ba kamar abin da ta yiwa Yazeed ba, saboda ta tsorata da irin yanayin ciwonsa.  Bata taɓa ganin mutum a mawuyacin yanayi na ciwo kamar Yazeed ba.
Tana zaune a aji, tana ƙoƙarin ɗauko littafi tayi rubutu, ta ga jotter Yazeed, ta ɗauko jotter ta fara bubbuɗewa, rubutunsa a tsare yake kamar musamman yake shirya rubutun, sai dai fahimtar abinda ya rubuta ɗin sai ƙwaro ko kuma shi kansa da ya rubuta abin sa.
Rubutu ne na turanci, jotting ɗin lectures ɗin da ake yi ne, sai yayi sentence ɗaya biyu ya gauraya su da rubutun larabci, ga wasu irin manyan Words na turanci, da bata taɓa jinsu ba.
To ya akai ya iya turanci a rubuce, amma bai iya a baki ba? 'Maybe yana da matsalar public speaking ne' ta bawa kanta amsa.
Bakomai ta iya ganewa a jotting ɗin nasa ba, saboda yadda yake rubutun larabci kamar rubutun yarensa na haihuwa.
Ɗan taɓe baki tayi, ta ajiye jotter, tana fatan Allah ya sa dai ba jikinsa ne ya hana shi zuwa Makaranta ba.


Khalil musamman sai ya shirya ya tafi unguwar su Abdul, yayi shawagi domin kawai ya ga Hafsat, cikin ikon Allah yau yayi sa'a ya tarar da ita a bakin kaskonta bayan magariba, tana ta harhaɗa kayanta ta tashi.
Parking ɗin motarsa ya yi, ya fito da sauri ya ƙarasa in da take. "Sannu dai"
Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce "Yawwa".

"Ba dai har kin tashi ba?"
"Me kaga ina yi?"
"Oh sorry haka ne, na gani haɗa kaya ki ke yi, yanzu ba zan samu ba?".
"Eh ta ƙare".
"Kwana biyu na zo ba na ganinki, meyasa ba kya fitowa?"
Hafsa ta ce "Eh da yake ai ba aikin gwamnati

1 Comments On GABA DA GABANTA
avatar
shemau-shafiu

11 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment