Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in fada maka cewar....."
.
Dakta Hamza ya yi sa*rin dakatar dashi. Ya ce.
.
"Khalifa kada ka tsaya 6ata kudin wayarka, ni kaina ynx haka ina cikin aiki ne. Bari in fada maka abin da kake son fada mani (In brief). Iyayen Sadiya tare da kai, gobe zaku xo ku same ni ku sasanta da ni, sbd sauran kwana biyar a daura aurenka kai da ita. In dai wannan ne maganar na sani. Kada ka damu na san komai da yake faruwa Khalifa."SADIYA page 51
.
.
.
"Kada ka damu na san komai da yake faruwa Khalifa."
.
Khalifa ya yi tsammanin ko bayan sun gama waya ne da Hafsatu ta kira Dakta ta fada masa. Ya ce da Yayansa.
.
"Anti ta kira ka ta fada maka komai kenan?"
.
Dakta Hamza ya ce dashi.
.
"Ban yi magana da Antinka ba. (Spils) mutanen da na tura qauyen da kake zaune sune suka shaida mani. Kullum sai sun sanar da ni abin da yake faruwa da kai. Ka san su a fuska, kana tare dasu, kuma anan qauyen suke zaune. Amma baka san ko su wanene ba. Kadan daga cikin abubuwan da suka fada mani shi ne. An ce ka samar da ci gaba mai yawa a dalilin xuwanka qauyen. A dalilinka sun sami makaranta, sun samu ruwan sha, ga Asibiti za a fara ginawa kwanan nan. An ce kana koyar da karatu a garrin. (you gave them alot of improvement just becouse you want to marry their daughter. Khalifa you are the love philanthopist.)
.
Khalifa ya ji jikinsa yayi sanyi, koda yake bai kamata yayi mamakin jin hakan ba. Sbd ya tabbatar Dakta Hamza zai iya yin fiye da haka akan sa. Ya ce da shi bayan sun dauki gajeran lkc ba wanda yayi magana.
.
"Zamu xo gobe ni da iyayen Sadiya kamar yadda ka samu labari. Ka sauraremu."
.
Dakta Hamza ya ce dashi cikin sauri.
.
"No Khalifa you don't have to come) kada ku yi wahalar xuwa. Na san abin da zai kawo ku, in yi haquri in amince in barka ka auri Sadiya. (And I will not agree). Ba zan ta6a amincewa ba. Kafi kowa sanin dalilin da yasa bana son alaqarka da wannan yarinyar da Iyayenta, da ace (Friendship) ne kawai tsakaninka da ita. (I don't mind). Amma aure wani abu ne da yake da muhimmanci a rayuwa. Ta yadda dolene mutum ya san ko da wane irin mutum zai hada xuri'arsa. Wannan shi ne ra'ayina tun farko, kuma (Still) ina nan akan wannan ra'ayin. Na san zaka tambayi kanka cewar, da ace kayi shiru baka kira ni ba, me zan yi in hana ka ka auri Sadiya tunda saura kwana hudu a daura auren? Ina mai jaddada maka cewar ko ka sanar da ni ko baka sanar da ni ba. Ba zan yarda a daura wannan auren ba. (I knew you will ask me how)? Kadan daga cikin abin da zan fada maka shi ne, tuni na shigar da maganar aurenku a kotu. Ina tuhumar iyayen Sadiya. Na yiwa Lauyana bayanin komai. Tuntuni kotu ta bayar da jami'an tsaro damar da zarar an hadu don daura auren su kama duk wanda keda hannu a daurin auren. Zaka tambayeni da wacce hujja kotu zata qalubalanci daurin auren, tunda dai aure ba laifi bane? Da hujja daya kotu ta haramta daurin auren. Hujjar kuwa ita ce. Kana da ta6in hankali, kana da kudi a cikin (Account) dinka na banki har Nair milyan hamsin. Mutanen qauyen sun sace ka, sun yi maka siddabaru suna son su hada ka aure da 'yarsu don su qwace maka dukiyarka. Kaga kuwa sun zama masu laifi babba. Dole kotu ta hana a daura auren, akama iyayen Sadiya a dauresu, sbd 6arayin da suke qoqarin sace Naira milyan hamsin, kotu ba zata saurara masu ba.....manyan masu laifi ne musamman da aka ce kana da ta6in hankali."
.
Khalifa ya ji tsoro ya kama shi, ya tambayi yayan nasa.
.
"Dakta ban fahimci inda ka dosa ba. Bani da ko rabin milyan a (account) dina, duka kudin basu wuce naira dubu sittin ba, kuma da zarar an bincika accont dina za a gane gsky."
.
Dakta Hamza yayi dariya ya ce da qaninsa.
.
"Ka kai kwana biyar baka je banki ba Khalifa. Ka koma yau ka duba (Account) dinka zaka samu Naira milyan hamsin. Ni na xuba maka su don su zama hujjar zargin da muke wa iyayen Sadiya. Bai zama dole bankinka ya turo maka saqon shigowar kudin ba, sbd lambar wayarka da suke amfani da ita, ynx ba layin bane as wayarka.SADIYA page 52
.
.
.
Dakta Hamza yayi dariya ya ce da qanin sa.
.
"ka kai kwana biyar baka je banki ba Khalifa. Ka koma yau ka duba (Accont) dinka zaka sami naira milyan hamsin. Ni ne na xuba maka su. Na yi haka ne domin su zama shaidar da zamu baiwa kotu don kama iyayen Sadiya. Bai zama dole bankinka su turo maka da saqon shigowar kudin ba. Sbd lambar wayarka da suke amfani da ita, ynx ba ita ba ce a wayarka. Idan kana son Sadiya to abin daya dace kayi shi ne ka gaggauta janye wannan maganar auren, don kada ka jefata da iyayenta cikin tashin hankali. (leave that girl Khalifa....leave her and come back home). Na fada maka zan iya yin komai don ganin baka aureta ba. (And I mean it....)".
.
Khalifa ya ji xufa ta keto mashi a goshi. Tsoro da fargaba suka lulli6e xuciyar shi. Ya ce da Dakta Hamza cikin karaya.
.
"Bai kamata kayi haka ba Dakta. Ka tuna kai Dan uwana ne, bai kamata don kana da kudi kayi amfani dasu don tarwatsa jin dadin rayuwata ba. Na san nayi kuskure da na rabu da kai, to amma kaima kayi kuskure da ka dauki wannan matakin a kaina. Mu dukanmu mun yi kuskure. Kamata yayi ka jira mu idan muka xo gobe, zamu iya maganin wannan matsalar ta hanyar lumana a tsakaninmu. Kai ne kake fada mani cewar. Hanyar magani ita ce sahihiyar hanya da dan Adam zai bi ya warware matsalar dake tsakaninsa da wani Dan Adam irin sa, amma ba hanyar fito na fito ba. Bai kamata ka canza daga wannan ra'ayin ba. Kayi haquri ka bamu izini mu xo mu sameka gobe."
.
Dakta Hamza ya ce da Khalifa.
.
"Ba fito na fito nake son in yi da kai ba a rayuwa Khalifa. Tun kana yaro qarami ka san kullum sai mun yi wasa ni da kai, to wannan ma wani sabon wasan ne wanda kai ka xo dashi ka ce muyi. (this is a game) duk wasannin da muke yi da kai baka ta6a samun nasara akaina ba ko sau daya Khalifa. Duk sanda muka yi wasa ni ke samun nasara akan ka. Sbd haka ynx ma a wannan wasan ni zan yi nasara. Ba zaka auri Sadiya ba. Wannan shi ne sakamako na qarshe da zaka gani a wasan namu. (In the game of life. I defeat you permanently Khalifa)."
.
Dakta Hamza ya fashe da dariya cikin raha da farin ciki. Kafin Khalifa ya sake yi masa wata maganar ya kashe wayarsa a can 6angaren. Khalifa ya fara kiran sunan sa a rude.
.
"Hello...Dakta hello...kana ji na? Dakta...."
.
Khalifa ya kai kusan minti daya yana kwadawa yayansa kira. Kafin yayi tunanin Dakta ya kashe wayarsa ne.
.
.
**
.
.
Ba zai yiwu ba ya kwashi iyayen Sadiya ya tafi dasu wajen Dan uwansa a yi wata magana ta sasanci ba. In har wannan shi ne ra'ayin Dakta Hamza, kuma shi ne irin matakin daya dauka, to maganar xuwa da iyayen Sadiya, kamar ma sake saqa bakin wata sabuwar rigimar ne, tunda dai ba zai amshi uxurinsu ba. Ba zai ta6a amincewa ba.
.
Khalifa ya yanke shawarar zai sanarwa Mai unguwa cewar ya canza shawara. Zai je gida da kansa don ya sasanta shi da Dan uwansa ba tare da sun bi shi sun je tare ba. Xuwa dasu zai iya zama matsala don haka zai je shi kadai washe gari. Yana sa rai a kwana daya da zai yi a gida zai iya shawo kan Dan uwansa, ya janye adawarsa da iyayen Sadiya, yayi haquri a yi wannan auren tunda lkc ya yi.
.
Sai da daddare bayan Mai unguwa ya dawo daga masallaci, kafin ySADIYA page 52
.
.
.
Sai da daddare bayan Mai unguwa ya dawo daga masallaci, kafin ya ci abinci ya fita qofar gida inda suke hira shi da abokansa su Liman. Khalifa yayi sallama ya shiga dakin Mai unguwa ya same shi a zaune kamar yadda yake samun shi in ya shiga dakin sa.
.
"Khalifa dama ynxn nan na ke cewa a nemo mini kai, aka ce kana cikin gari."
.
Khalifa ya zauna jikinsa a sanyaye ya ce da Mai unguwa.
.
"Ban dade da fita ba, na jira ne a fito sallah dama in xo in same ka."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"Akan tafiyar za mu yi gobe, an sami mota. Wancan yaron dake a Rufeya mai farar motar nan, mun daidaita dashi ya ce zai xo da sassafe. Na fadawa su Buba da Liman, na ce su shirya da wuri gobe, don mu samu mu je da wuri mu dawo akan lkc."
.
Khalifa yayi ajiyar xuciya ya ce.
.
"Na kira yayana daxu mun yi magana. Ina ganin tafiyar nan ba sai mun yi tare ba Baba. Ko ni kadai na je zan shawo kan matsalar. Zan yi kwana daya kawai, ina sa ran xuwa lkcn zan shawo kan matsalar, zamu daidaita ni da dan uwana. A maganar da muka yi dashi daxu na fahimci matsalar bata kai yadda nake tsammani ba."
.
Mai unguwa ya kalli Khalifa cikin mamakin yadda ya canza maganar da suka yi."
.
"in har kana ganin akwai matsala ka fada mini in san abin da yake faruwa Khalifa.".
.
Ya ce dashi.
.
"Ba matsalar komai Baba. Ai rashin matsalar ce tasa na ce kuyi zaman ku, ba sai kun je ba. Ni kadai ma zan iya shawo kan matsalar, zamu dawo ni da yayana ba matsala Baba."
.
Mai unguwa ya saki ran shi ya ce da Khalifa.
.
"To ai ba komai, sai ka tafi gida goben, zamu sa idon dawowarka. Bari in aiki Balalle ya je can Rufeya ya fadawa direban mun fasa tafiyar kada ya xo. Tunda kana ganin kai kadai ma zaka iya gyara matsalar ya fahimceka, shi kenan ba sai mun je ba."
.
Khalifa ya ce da Mai unguwa a qarshe.
.
"Na gode Baba. Na gode da duk abubuwan alkairin da kuka yi mani tun xuwa na garin nan. Ba abin da zan ce daku sai Allah Ya saka maku da alkairi."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"Bamu yi maka komai ba Khalifa. Kai ne kayi mana abin da zamu gode maka, har jikokinmu zasu amfana da abin da ka bamu, ba zamu ta6a mantawa da abubuwan alherin da kayi mana ba a garin nan."
.
A nan Khalifa ya bar Mai unguwa. Ya sa aka kira masa Sadiya, suka zauna akan dutsen da suke hira da daddare. Da xuwanta Khalifa ya ce da ita.
.
"Sadiya gobe zan je gida, amma ni kadai zan je, ba kamar yadda kika sani cewar zamu je tare da su Baba ba."
.
Sadiya ta juyo a tsorace ta dubi Khalifa.
.
"Mai yasa ba zaka yarda ku je tare da su Baba ba? Me yasa ka canza shawarar xuwa kai kadai ynx?"
.
Khalifa ya numfasa ya ce.
.
"Zan iya daidaita matsalar da ta shiga tsakanina da Dan uwana ta hanyar da tafi dacewa Sadiya. Na san Dan uwana fiye da kowa a duniya. Bana raina yunqurin da Su baba suka yi bane. Nayi magana da Dakta daxu, abubuwan da muka tattauna su suka tabbatar mani zan iya shawo kansa ya yafe abubuwan da suka faru a baya. Ya xo ayi harkar bikinmu tare dashi."
.
Sadiya tayi shiru tana tunani. Bayan wani lkc da Khalifa ya ji bata ce komai bane, sai ya tambayeta.
.
"Naji kin yi shiru baki ce komai ba, me kike tunani ne Sadiya?"
.
Sai da tayi masa magana sannan ya fahimci kuka take yi.
.
"Wani abu a cikin xuciyata yana tsoratar da ni in har ka tafi kai kadai, zai yi wahala ka dawo wajena Khalifa. Nafi son ku tafi tare da su Baba, komai ya faru na san zaka biyo su ku dawo tare. Amma idan ka tafi kai kadai, da wahala in sake ganin ka. Dakta ba zai sake barin ka ka dawo garin nan ba. Duk hanyar da zai bi na tabbatar zai bi don ya hana ka sake dawowa."
.
Ta share hawayen farko da ya xubo mata. Khalifa ya ce da ita.
.
"Dakta ba zai raba ni dake ba Sadiya. Ba wanda zai iya raba ni dake a duniya sai mutuwa. Xuwa na gare shi a ynx shi ne damar da muke da ita wajen fahimtar irin yunqurin da Dakta yake shirin yi akan mu in har yana son raba mu. Ba zan ta6a barinsa yayi nasara ba Sadiya. Idan har zai bi kowacce irin hanya don ya raba soyayyarmu. To nima zan bi kowacce irin hanya don ganin bai yi nasara ba."
.
Sadiya ta girgiza kai cikin shakka da kokwanto.SADIYA Page 54
.
.
.
Sadiya ta girgiza kai cikin shakka da kokwanto.
.
"Dakta babban mutum ne wanda yake da qarfi. Yana da kudi yana da mutanen da zai nemi alfarma suyi masa abin duk da yake so a ko'ina a fadin qasar nan. Kai kanka ka san haka Khalifa. Don haka ni dai ina roqonka in har kana son ka je gida to ka saurara tukunna sai bayan an yi bikinmu, sai muje tare in taya ka aikin sasantawar."
.
Khalifa ya ce.
.
"ni kaina hakan naso ace mun yi. To amma kin ga su Baba sune suka ce bai kamata ayi haka ba. Sbd duk duniya a ynx bani da kowa sai Dakta, shi ne uwata shi ne ubana tun ina yaro. Shi ne tubalin da ya gina rayuwata, ba zai yiwu ba ace duk wani sa6ani da muka samu, ace an yi aurena Dakta bai sani ba sai dai ya ji lbari. Ba wani abu da zai faru don naje ni kadai Sadiya, ki kwantar da hankalin ki."
.
Sadiya tayi ajiyar xuciya
.
"Shi kenan tunda haka ne, sai dai in ce Allah Ya kai ka lfy. Allah Ya dawo mani da kai lfy. Ina son ka sani cewa ba zan iya jure rasa ka ba Khalifa. Komai ya faru ina fatan zaka dawo wajena."
.
Khalifa ya ce da ita.
.
"haka nima duk inda nake a duniya komai rintsi ba zan iya jurewa ba sai na dawo wajen ki. Yau saura kwana hudu ki zama matata. In sha Allahu ba wata masifa da zata fadowa ragowar kwanakin nan har mu samu matsala a soyayyarmu. Zan je gida gobe kuma ko nayi nasarar sasantawa da Dakta ko ban yi ba, nayi maki alqawarin zan dawo wajen ki."
.
Sadiya ta sake cewa.
.
"Allah Ya kai ka lfy. Idan ka je ka gaisar min da Anti da su Alfat."
.
Ta dan yi murmushin qarfin hali, da ta tuno irin zaman da suka yi tare. Khalifa da Sadiya suka yi bankwana tun a daren. Sbd ya ce da sassafe zai fita zai yi sammako, ba zasu hadu ba sai in ya dawo. Sadiya tayi kamar ba zata shiga gida ba....ta ji kamar ta tsaya da Khalifa kada su rabu. Tunda yaxo garin su bai ta6a yin nisa da ita ba, sai ynx a karo na farko gashi ya ce zai koma gida....zai koma wajen Dan uwansa.
.
A daren babu wanda yayi barci a cikin masoyan. Khalifa da Sadiya suka yi ta tunanin kwana hudu da suka rage musu kafin su cimma burikan su. Kwana hudun da komai zai iya faruwa a cikin su.
.
A daren Khalifa ya sanar da mutanen dake a qauyen cewar zai je gida washe gari, amma kwana daya kawai zai yi ya dawo. Da yake kowa ya saba dashi a qauyen, kullum ana tare dashi, ba wanda ya ji dadin tafiyar da Khalifa zai yi.
.
Kowa yayi ta roqon sa...."Dan Allah idan ya je kada ya wuce kwana daya."
.
Abin da yasa ya fada musu bai san me zai faru ba, ko ya dawo ko ba ya dawo ba. Sanin gaibu sai Allah. Shi yasa ya sanar dasu don kada a wayi gari su ji cewar ya tafi. Da sassafe ana fitowa daga sallar asubahi, ya dauko jakarsa, dama akwai wadanda suka ce zasu dauki babura su raka shi har bakin titi inda zai samu motar xuwa Zariya. Khalifa ya same su su biyar kowanne ya fito da babur. Balalle shima yana daga cikin 'yan rakiyar Khalifa.
.
Kafin ya hau daya daga cikin baburan ne, ya koma masallaci inda Mai unguwa ke laxumi tare da wadansu Dattawa su uku dukansu sun sha manyan riguna da rawani. Ya tsaya a bakin qofa ya ce da Mai unguwa.
.
"Baba na tafi sai na dawo goben in Allah Ya yarda.
.
Mai unguwa ya ce dashi.
.
"tunda sassafe zaka tafi haka? Ba zaka tsaya ka sa wani abu a cikinka ba?"
.
Khalifa ya ce.
.
"Ina son in je Zariya da wuri ne don in samu motocin safe dake xuwa Abuja. Tafiyar safe tafi sauri ne. Ba tsaye-tsaye a hanya."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"ka shiga gida kayi mata sallama?"
.
Khalifa ya san abin da Mai unguwa yake nufi. Yana tambayarsa ne ko ya je sun yi bankwana shi da Sadiya? Ya ce dashi.
.
"eh, na shiga na fada musu zan tafi."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"To a dawo lfy Allah Ya kiyaye hanya, ka gaishe da mutanen gidan naku. Sai ka dawo."
.
Sauran dattawan dake a masallacin suna jan carbi suka juyo suma su ma suka ce da Khalifa.
.
"A dawo lfy Allah Ya kiyaye."
.
Khalifa ya ce.
.
"To mdlh, na gode."
.
Ya juyo ya taho inda abokansa ke jiransa da babura. Ba zai iya xuwa sake yin bankwana da Sadiya ba. Don kada hankalinta ya tashi ta ga kamar ba zai dawo bane....ta ga kamar ya guje ta ne ya koma garin su...kamar ya fasa aurenta ne zai koma ya sami 'yar birni ya aura irin sa.
.
Khalifa ya kalli samarin da su ka xo da baburansu su biyar suna jiran sa, ya tambaye su.
.
"to wanne zan hau ne mu tafi?"
.
Wani da ake cewa Isa ya ce.
.
"Nawa zaka hau Mallam."
.
Wami mai suna Sani ya ce.
.
"Ni na far xuwa tun kafin ka xo, sbd haka mashin dina zai hau."
.
Jayayya ta 6arke a tsakanin su, kowa ya ce shi zai dauki Khalifa. Da yaga zasu 6ata lkc sai ya ce yana dariya.
.
"to ku tsaya. Ku tsaya. Tunda Sani ya ce shi ya fara xuwa ku tsaya in hau nashi ai duk daya ne, dukan ku na gode."
.
Khalifa ya hau babur din Sani. Balalle ya hau na abokinsa Badamasi. Suka tada suka tafi baki dayan su, suka dauki hanyar ficewa daga qauyen.
.
Duk wannan abin dake faruwa, Sadiya tana a 6oye a jikin kusurwar dangar dake fuskantar bayan gida, tana kallon ayarin baburan da suka yi wa Khalifa rakiya. Ta ganshi an goya shi ya sagala jakar shi a kafadarsa.
SADIYA page 55
.
.
.
Duk wannan abin dake faruwa Sadiya tana 6oye a jikin kusurwar dangar dake fuskantar bayan gidan su. Tana kallon ayarin baburan da zasu yiwa Khalifa rakiya. Ta han shi an goya shi. Ya sagala jakarshi a kafadarshi....
.
Wannan shi ne masoyina da yaxo garinmu yayi wata biyar ba tare da ya koma ba, sbd zunxurutun son da yake yi mani.
.
Wannan shi ne masoyin da ya share mani hawaye da duk wata damuwa dake a xuciyata. Shi ne wanda ya sa na fahimci ko mene ne so a rayuwa. Shi ne wanda ya fara koya mani yadda ake zamantakewar soyayya mai dadi. Wancan shi ne masoyin da ba zata sake samun kamar sa ba a duniya. Daga shi ba zata sake son kowa ba. Wancan shi ne masoyin da in har bata aure shi ba.....in har basu zauna tare dashi ba,,,bata san halin da zata sake tsintar rayuwarta ba a lkc na gaba....
.
Baburan suka yi nisa, Sadiya tana 6oye tana kallon su har suka 6ace. Ta share hawayen da ya xubo mata na bege, da takaicin rabuwa da masoyi. Tana fatan zai sake dawowa wajenta, domin ya aureta, domin ya aureta su zauna tare kamar yadda ya yi mata alqawari.
.
Samarin qauyen Turunkawa suka raka Khalifa har bakin titi, da xuwansu ya samu motar da zata wuce, suka tsayar da ita. Ya na saukowa suka fara rige-rigen ba shi hannu suna gaisawa, suna yi mashi fatan sauka lfy.
.
Balalle ya amshi jakarshi ya raka shi har qofar shiga motar. Sauran samarin suka riqa dago mashi hannu cike da farin ciki, da kuma damuwa da mutumin da ya xo garin su ya taimake su.
.
Khalif ya shiga motar. Balalle ya miqo masa jakarsa suka kalli juna, Khalifa ya ji hawaye ya taru a idanunsa. Tun xuwansa garin tare da Balalle suke kwana a daki daya. Komai yake so Balalle ke yi masa cikin hanzari. Ya aike shi ko'ina....komai nisa Balalle bai ta6a nuna damuwarsa ba.
.
"Sai ka dawo Khalifa. Allah Ya dawo da kai lfy."
.
Ya ce dashi yana murmushin qarfin hali.
.
"Na gode Balalle sai na dawo."
.
Motar ta tafi. Khalifa ya juyo yana kallon Balalle da abokansa da ya zauna tare dasu a Turunkawa. A da can bai san su ba. Bai ta6a zaton zai xo ya zauna tare dasu ba. Gashi ynx ya shaqu dasu, har rabuwa ta zame mu su wahala, babu shakka soyayya tana jawo soyayya, har so ya hadu kowa ya ji yana son kowa. Kowa ya ji baya son rabuwa da kowa.
.
Hawaye ya xubowa Khalifa da ya hangesu sun tsallaka titi da baburan su, zasu sake komawa qauyen don ci gaba da rayuwar da suka fi sabawa da ita. Khalifa ya ji dama tun farko tare dasu yake zaune. Ya ji kamar bai saba da kowa ba sai su a duniya.
.
Da qarfe bakwai ya isa Zariya, ya samu motar Abuja. Sun fara tafiya kenan sai ya kira yayansa Dakta Hamza ya ce dashi.
.
"Gani nan xuwa nan da qarfe goma in Allah Ya yarda. Kana gida ne ko har ka fita wajen aiki?"
.
Dakta Hamza ya ce da Khalifa.
.
"Ynxn dai nake shirin fita wajen aikin, amma na fasa xuwa. Yau ta zama ranar hutu, ba zan je ko'ina ba."
.
Khalifa ya tambayeshi dalili.
.
"Me yasa zaka fasa xuwa wajen aiki yau? Na san akwai (Patients) suna jiranka a halin ynxn, ka je ka sallame su kafin in xo na san ka kammala, sai in biyo ta asibitin in same ka mu taho gida tare."
.
Dakta Hamza ya ce.
.
"Ya za a yi in iya xuwa aiki yau, bayan dan uwan da yayi mani saura a duniya ya tuna da ni zai dawo gida a yau? Wannan damar tana da muhimmanci a gare ni."
.
Khalifa ya yi dariya. Ya san yayansa sarai.
.
"Dakta Hamza kenan."
ya ce a xuciyarsa.
.
.
.
**
.
.
Tun kafin motarsu ta isa Abuja, Dakta Hamza ya kirawo Khalifa ya ce zai turo a dauko shi a kawo shi gida. Da suka shiga Abuja ne, bayan Khalifa ya sauko daga motar da ya shigo sai ya hadu da direban yayansa, wanda yawanci yafi tuqa shi idan zasu yi doguwar tafiya mai nisa, ba a cikin gari ba. Suns haduwa da yake direban ya saba da Khalifa tun a shekarun baya, ya tarbeshi cikin girmamawa ya amsar masa jakarsa.
.
"Sannu da xuwa Khalifa. Ya hanya?"
.
"Lfy lau. Direba ya gari?"
.
Ya bashi amsa cikin girmamawa.
.
"Lfy lau. Ka dade baka nan. Kullum na tambayi Dakta sai ya ce ka tafi karatu ne amma zaka dawo."
.
Khalifa ya yi dariya ya dafa direban, ba tare da ya gasgata maganar da Dakta ya fadawa direban ba. Suka tafi inda direban ya ajiye motar da ya xo da ita. Wannan karon ma motar wani samfuri ce wacce Khalifa bai san ta ba. Daga dukkan alamu daga baya Dakta ya saye ta qirar (Road taurus) ruwan toka.
.
Suka shiga motar suka tafi gida. Direban yana tuqi yana jan Khalifa da surutu. Khalifa bai saurari maganganun da direban yake yi ba. Ya mai da hankalinsa wajen kallon garin, suka riqa wuce gine-ginen da ya shafe wata da watanni bai gansu ba. Yau ya sake shigowa cikin rayuwarsa ta farko. Yau ya sake dawowa cikin mutanen da ya rayu tare dasu.
.
Suka shiga gida. Da shigar su Hafsatu ta fito tare da yara Alfat da Abba, tun kafin su Khalifa su gama fitowa daga mota suka fara daga masu hannu, suna yi masu lale marhabin da xuwa. Khalifa ya bude qofar motar ya fito. Alfat da Abba suka rugo da gudu su duka, ya duqa ya bude hannuwansa, suka fada jikin sa.
.
"Sannu da xuwa Abba....sannu da xuwa.SADIYA.
Page 56
.
.
.
Sannu da xuwa Abba....sannu da xuwa."
.
Khalifa ya kira sunayen su.
.
Alfat ya tambayi Khalifa.
.
"Abba ina ka tafi tuntuni baka dawo ba? Muna ta nemanka."
.
Khalifa ya bashi amsa yana murmushi.
.
"Na je unguwa

Please Login or Register in order to submit comment