Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne sai Alh. Mamuda ya fara magana.
¤
"ba wani abu ne ya kawoni wajenku ba sai don mu zauna mu fahimci juna kan lamarin matata Sadiya, daxu na aiko qanina ya xo ya gani ko nan taxo, ya dawo ya ce da ni bata xo ba, kuma wai basku ganta ba. To maganar gsky dai Sadiya ta gudu jiya da daddare, ta kwashe kayan sawarta, ko kallabi bata bari ba."
¤
Liman da Mal. Kalla suka hada baki wajen yin salati.
¤
¤
Lp=5¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
=5
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
Liman da Mal. Kalla suka hada baki wajen yin salati. Mal. Buba kuma firgita yayi ya ce.
¤
"Sadiyar ce ta gudu? Mu zata yiwa wannan lalatar kuma?"
¤
Sarkin noma ya ce.
¤
"A'a, wannan al'amari da ya faru gsky laifin mu ne, da ni daku mun yi kusjure, mun san cewar yarinyar nan bata son maganar nan, amma muka tsaya kai da fata sai an yi auren nan, ynx dai ni na gane gsky, na fahimci abin da yarinyar nan take ji a ranta. A gabana wannan yaron saurayin ta Amir dan birni ya rasu jiya da safe. Allah Ya jiqan shi. Ynx haka daga nan can Turunkawa zamu je wajen kakanshi inda ake amsar gaisuwa mu yi masu ta'aziyya suma akan wannan mummunan al'amari da ya faru."
¤
Sarkin noma ya ciro takarda daga cikin alhihun shi, ya ajiye a gaban iyayen Sadiya ya ce.
¤
"wannan takardar saki ce, na saki mata ta Sadiya saki daya, na tsame hannuwa na daga cikin wadannan rigingimu dake faruwa, ku je ku nemo 'yarku ku bata wanda take so, ina son in ja hankalinmu gabadaya akan sha'anin wannan auratayya da muke yi a wannan lardi namu, mu daina bin son xuciyarmu, mu riqa ba 'ya'yanmu wadanda suke so aure, sbd idan muka yi la'akari da irin abubuwan dake faruwa a ynx zamu ga cewar lifinmu ne, tun farko da mun kai hankalinmu nesa mun yi tunani mai kyau, da ynx Sadiya tana nan bata gudu ba, kuma da ynx yaron nan jikan Mutawakkilu bai mutu ba, to gsky mune sanadin faruwar duk wadannan al'amuran, don haka ni na gane gsky, ku je ku nemo 'yarku, tunda bata sona, wannan shi ne abin dake tafe dani wajen ku."
¤
Mal. Buba qanin mahaifin Sadiya ya yi farat ya ce da Alh. Mamuda.
¤
"kayi saurin yanke hukunci Sarkin noma, ya zaka yi mana haka? Yarinyar nan fa 'yar mu ce, mu ne iyayenta, ko'ina ta je zata dawo ta same mu, kuma dole ta bi umarnin mu, wannan takardar da ka kawo kayi haquri ka janye ta, duk abin bai kai ga haka ba, duk inda ta je zata dawo ta same mu don qaniyarta."
¤
Sarkin noma ya ce dashi.
¤
"A'a, na haqura, na kuma gode, a bar ta ta za6i wanda take so illa iyaka."
¤
Mal. Kalla ya dauki takardar ya ce.
¤
Allah Yasa haka shi yafi alkairi."
¤
Liman ya saka baki ya ce.
¤
"Haka ne...shikenan tunda haka lamarin ya kasance, sai muyi haquri baki dayanmu, mu mayar da hankali akan nemo ita yarinyar tunda ynx bamu san ko a wane hali take ba."
¤
Mal. Buba ya yi qwafa cikin fushi, sannan ya yi tagumi, ya gama sanya xuciyar sa kan kwadayin abin da ke biyowa ta hannunsa daga Sarkin noma. Abin da kawai yake rayawa a xuciyarsa shi ne, da ace Sadiya tayi haquri ta zauna tare da Sarkin noma, idan ta haifi 'ya'ya tare dashi, nan gaba idan Sarkin noma ya mutu, aka raba gado aka ba 'ya'yanta nasu manyan gonakin, sune zasu riqa nomawa kafin 'ya'yan su girma, tuntuni wannan burin yasa yake ta fadi-tashi, akan ganin auren Sadiya da Sarkin noma ya kankama. Ynx da wannan lamari ya faru sai yake jin kamar an aiko masa da ranar mutuwarsa.
¤
Sarkin noma yayi masu sallama ya tashi ya tafi tare da fadawanshi biyu da suka rako shi. Suka nufi Turunkawa gidan su Mai unguwa Mutawakkilu kakan Amir.
¤
¤
Lp=6
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
06
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
A ranar bayan sun dawo daga qauyen Gidan rijiya, sai Sarkin noma ya tara masu kudin dake qauyen Maqera yayi sanarwa da kakkausar murya, cewa a matsayinsa na Dagacin wannan lardi yana mai sanarwa da kakkausar murya cewa, daga ynx duk wani tsoho, in har ya san yana neman wata budurwa a qauyen kuma bata son shi ya rabu da ita kada ya saye iyayenta a tilasta mata dole sai an bashi ita.
¤
Ya ja hankalin dattawan garin wadanda auren qananan yara ya zame masu halayya cewa su kula da kansu, daga ynx baya goyon bayan auren dole na tsoho da yarinya, a bar samari suyi soyayya da 'yanmatansu ko basu da kudi, tsoho ya ja girmansa ya daina shiga sha'anin yara don yaga yana da kudi.
¤
Daga ynx duk wanda aka kama yana ba iyayen yarinya kudi don a bashi ita ko bata so, dashi da iyayen yarinyar za a kaisu gari wrin Hakimi ya hukunta su.
¤
Da samarin dake a lardin suka ji wannan sanarwa da Dagaci Sarkin noma ya yi suka fara murna suna tafa hannuwa. Don kuwa tsofaffin garin sun dade suna yi masu tsama, sai yaro ya fara soyayya da yarinya sai kuma tsoho ya fitar da hatsi buhu hamsin kasuwa, ya xo ya direwa iyayen yarinya ya sare duk wani saurayi dake son ta, dole a bashi ita, ko tana so ko bata so.
¤
Su kuma dattawan garin masu budurwar xuciya, wannasn gargadi na Dagaci ko kadan bai yi masu dadi ba, suka fara yin qus-qus su ya su, suna cewa ai wannan ana so ne haramta masu abin da shari'a ta halasta masu. Ta yaya don mutum ya tsufa ya kai shekara tamanin sai a ce za a hana shi ya dauki yarinya 'yar shekara sha uku? Tsoho da kudi ai yaro ne.
¤
Wannan shi ne ya kawo qarshen riginmu a kaf fadin lardin dake qarqashin jagorancin Sarkin noma. Don kuwa a da can kafin a yi haka akwai mutanen da duk bayan shekara idan amfanin gona yayi kyau qa'ida ne su yi ciro. A wata duniyar idan mutum ya ji an ce za a yi ciro, zai yi tsammanin wata shuka ko ciyawa za a cire wacce ta fito a inda ba a son ganinta. To amma a duniyar karkara, da wasu yankunan, ba wannan ne kadai ciro ba, ciron da suke yi duk shekara shi ne, duk matar da ta fara sukurkucewa a cikin matansu hudu, ma'ana ta fara tsufa, to a shekarar ita za a saka a je a auro qaramar yarinya mai jini a jika a cike gurbin wacce aka saki da ita.
¤
Idan shekara ta sake zagayowa dole a samu wacce wahala ta sa ta fara gajiya itama, to lkcn fitar yaxo, to amma idan amfanin shekarar bai yi kyau ba, akan haqura sai wata shekarar ta xo.
¤
Ko babu komai mutuwar AMIR ta kawo canji a rayuwar mutanen qauyen, tunda gashi Sarkin noma ya tsaya tsayin daka ya kowa gyara, sbd abin tausayin da ya gani da idanun sa.
¤
Ta yaya kuwa samarin Lardin Maqera zasu manta da Amir dan soyayya masoyin Sadiya?
¤
¤
**~**
¤
¤
Khalifa da matar yayansa Hafsatu suka tafi da Sadiya birnin tarayya Abuja, suka mayar da ita 'yar gidansu, wacce haka kawai suka ji ta shiga ransu. A ranar da suka tsinceta da daddare da xuwansu gidan Hafsatu ta bata wani daki wanda babu komai a cikin shi, ta nuna mata komai a cikin gidan ta ce ta saki jikinta.
¤
Sadiya tayi wanka ta canza kayan jikinta ta kwanta tayi barci hankalinta a kwance. Da safe lkcn karin kumallo Hafsatu ta xo ta jagoranceta xuwa teburin cin abinci, inda suke cin abinci ita da 'ya'yanta da mijinta idan yana nan, tare da Khalifa Sarkin gida kamar yadda take kiran sa.
¤
Khalifa ya baro dakinsa dake waje ya shifo cikin gidan ya samu Hafsatu da Sadiya sun zauna a kujerun cin abinci dake fuskantar teburi babba wanda ke dauke da tarin kayan karin kumallo. Khaliga ya ga Sadiya ta fito fes, ta sanya atamfa mai dauke da kalar fari da ruwan ganye, dinkin rigar doguwa ce har qasa, amma hannunta yankakkune iyakarsu kafadunta, da xuwanshi tun kafin ya zauna ta ce dashi cikin kunya.
¤
"Ina kwana?"
¤
Khalifa ya amsa mata yana kallon ta.
¤
"Lafiya lau Sadiya ya gajiyar tafiya?"
¤
Ta ce ba gajiya kanta a sunkuye tana duban yatsun hannunta wadanda ta dora su akan teburi tana motsa su. Khalifa ya gishe da matar yayansa ya tambayeta ina su Alfat da Abba? Ta ce dashi.
¤
"Basu tashi ba har ynx, wannan wahala da muka sha jiya da motar nan ai ba 'yar qarama ba ce, ni kaina barci bai ishe ni ba har ynx, da mun karya zan sake komawa daki in kwanta, na san kema kina jin barci har ynx ko Sadiya?"
¤
Sadiya tayi murmushi cikin kunya bata ce komai ba. Hafsatu ta fara hada shayi ta miqawa kowa nasa kofin, ta bude faffadan farantin dake dauke da soyayyen qwai da dankali, qamshi ya mamaye dakin cin abincin, suka fara shan shayi suna maganganu jefi-jefi, amma Sadiya bata sa baki ba a duk maganganun da suke yi, idan zata kur6i shayi sai ta tabbatar Khalifa baya kallonta. Tana jin kunyarsa fiye da yadda take jin kunyar Hafsatu.
¤
Lkc-lkc Khalifa ya kan saci kallon Sadiya, hankalinsa yana kan ta. Hafsatu ta dade da lura da yadda Khalifa yake kallon Sadiya, da kuma farin cikin da yake ji idan yana tare da ita, wannan kadai ya tabbatar mata cewar Khalifa son yarinyar yake yi.
¤
¤
Lp=7¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
08
with
Iliyas Ishak Gundutse
ix
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
wannan kadai yasa ta fahimci cewa Khalifa ya kamu da son wannan yarinya a dan qanqanin lkc da haduwar su.
¤
Bayan sun kammala karyawa ne sai Hafsatu ta tattara hankalinta waje guda ta dubi Sadiya ta ce.
¤
"to Sadiya, gaki a gidanmu, na san ynx hankalinki ya kwanta kin samu nutsuwa damu. Ina son ki fadi mana labarin ki, me ya faru dake? Kuma ina ne garin ku? Kada ki 6oye mana komai, kin ga mijina baya nan, ina son idan ya dawo ya same ki a nan gidan mu san abin da zamu fadi masa akan ki, kada ya ce mun yi kuskure mun daukoki bamu san ko ke wacece ba,.
¤
Sadiya ta ce.
¤
"haka ne Anti."
¤
Khalifa ya qura mata ido yana jira ta fara magana, lkc ya yi da ya kamata ya fara sanin wani abu a rayuwarta, sbd har ynx ita baquwace a wajensu. Sadiya ta yi ajiyar xuciya ta ci gaba da matsa yatsun hannunta, shirun da tayi ne suna saurarenta tayi tunani a gurguje, idan har zata bada labarin rayuwarta da gskyr abin daya faru, akwai abubuwa da yawa da suka faru da ita.
¤
Babban abin da ta tabbatar idan ta fada masu zai girgizasu shi ne, ynx haka ita matar aure ce. Ta gudo ne daga gidan mijinta Dagaci Sarkin noma wanda iyayenta suka cusa mashi ita, suka raba ta da masotinta AMIR a domin sa. Tabbas idan ta fadi masu haka ba zasu iya riqeta ba, zasu yi qoqarin mayar da ita gida ne, Sadiya bata son ta koma gida, tafi son tayi zamanta a wajen wadannan mutane da suka taimaketa. Tana son tayi nisa yadda babu wani mutum da zai xo kusa da inda take, ballantana har ya gane ta yaje ya fadiwa iyayenta inda take su xo su dauketa su mayar da ita wajen wannan tsohon mutumin, wanda take takaicin kasancewarsa mijinta.
¤
Hafsatu ta katsewa Sadiya tunaninta ta ce da ita.
¤
"muna jiran ki Sadiya, me ya faru dake? Mene ne dalilin gudewarki daga gida har muka same ki a cikin daji jiya da daddare?"
¤
Sadiya ta sunkuyar da kanta ta kalli teburin dake gabansu, ta fara yi masu magana a hankali kuma a sanyaye.
¤
¤
"An haifeni a wani qauye wanda bashi da nisa daga inda kuka tsince ni, amma ba a nan na girma ba, na zauna ne a wajen wata qanwar mahaifina dake a Zariya, a can na kammala karatuna na sakandire, kafin in ci gaba da karatuna ne mahaifina da 'yan uwanshi suka ce aure suke so su yi mani. suka dauko ni daga wajen Gwaggona suka mayar dani gida can qauyenmu suka yanke shawarar zasu bayar da ni sadaka."
¤
Sadiya ta dan saurara ta dago kanta kadan ta kalli Khalifa da Hafsatu wadanda suke kallonta cikin rashin fahimtar maganar da ta fada a qarshe, don haka sai ta warware masu zare da abawar bayanin don su fahimce ta.
¤
"Auren sadaka a qauyenmu ya zama kamar wani abin kwalliya, ko kuma abin burgewa,. Ana danganta wadanda suka bada auren 'ya'yansu matsayin manyan mutane, wadanda suke da rufin asiri. Lkcn da aka xo bayar da aurena, an samu tangarda, aka yi ta rikici a tsakanin 'yan uwan mahaifina. Daga baya don kada ya ba da aurena ga wani, wanda kuma ba a baiwa ba ya ji haushi, sai mahaifina ya bada aurena ga wani jikan abokin shi mai suna AMIR. Wanda ya kawo masu xiyara daga birni, Amir bai amshi aurena ba, bai ma yarda ya ganni ba, ko suna na bai tsaya ya ji ba, ya ce baya sona, baya son auren, ya zazzage kakanninsa da suka yi masa hanyar auren, ya kwashe kayansa ya koma birni inda yake makaranta cikin fushi."
¤
Khalifa ya yi tagumi yana jimamin maganar da Sadiya take fada musu. Hafsatu tayi xugum, ko qiftawa bata yi tana kallon Sadiya, wacce ta ci gaba da basu labarin ta.
¤
"Da qanwar mahaifina wato Gwaggona Haj. Uwani taga abin da ya faru sai ta ba sauran 'yan uwanta iyayena shawarar, a bar zancen auren nan haka, tunda wanda aka baiwa ya ce baya so, zata sake daukata mu koma birni in ci gaba da karatu, tunda dama ni a ra'ayina nafi son in yi karatu a lkcn. Basu yi mata musu ba, suka amince ta sake tafiya da ni Zaria, na zauna a wajenta na fara yin karatun Diploma a Jami'a. Abin da kowa bai sani ba shi ne. Ashe Amir din nan da aka bashi aurena ya ce baya sona, shima a nan Jami'ar yake karatu, wata rana sai muka hadu a dakin karatu, yayi ta kallona, a taqaice dai ya kamu da sona fiye da yadda zan fada maku, ni ban san shi ba, shima kuma bai sanni ba. Naqi in amshi soyayyarsa, sbd a lkcn soyayya ta fita a raina, daqyar qawayena suka shawo kaina na amshi soyayyarsa muka fahimci juna sosai ni da Amir, shi bai san ni ce Sadiyar da aka bashi ya ce baya sona ba, nima kuma ban san shi ne Amir din da aka bashi aurena a baya ba."
¤
Hafsatu ta ja numfashi ta ce.
"Ikon Allah kenan."
¤
Khalifa ya canza hannun tagumin da ya yi na mamakin duk abubuwan da Sadiya take fada kamar aikin mafarki ba da gaske ba.
¤
"Bamu dade da fara soyayya da Amir ba, sai qnin mahaifina yaxo daga qauye ya ce sun yi mani miji zasu sake yi mani aure. Ya xo ne ya tafi da ni. Dole na bi shi muka koma qauye ba don ina so ba, kuma a wannan lkcn hatta Gwaggona Haj. Uwani bata so ba. Da na koma ne naga mijin da suka za6a mani ashe wani tsohon najadu ne.
¤
¤
Lp=9¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
09
with
Iliyas Ishak Gundutse
ix
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
Suka za6a mani wani tsohon najadu wai shi Sarkin noma, ya girmi mahaifina nesa ba kusa ba. Babu yadda za a yi in zauna dashi, sbd rayuwata tare dashi ba qaramar cutarwa ba ce a gare nim kafin a daura auren ne Amir ya jji labarin abin dake faruwa, sai ya biyo ni, tun kafin yaxo qauyenmu ya fahimci ni ce Sadiya da aka bashi a baya yace baya so. Amir yayi kuka mai yawa, ya yi nadama a lkcn da bata da amfani, sbd bakin alqalami ya riga ya bushe, iyayena sun yi mani miji. Da yaxo qauyenmu ne iyayena suka gane shi, suka sa yayyena suka yi ta dukan shi kamar zasu kashe shi, suka kore shi ya bar garin jina-jina, ni kuma suka sa mani takunkumin ba shiga ba fita, a haka har aka daura aurena da Sarkin noma."
¤
Khalifa ya fara tsorata da abin da Sadiya ke fada, ya dubeta a furgice. Hafsatu ma ta kalle ta. Bata ta6a zaton Sadiya ta ta6a yin aure ba.
¤
"Aurena da Sarkin noma bai zauna ba, sbd babu wata alaqa mai kyau ta soyayya da qauna tsakani na da shi. Baya iya sakin jikinsa ya xo kusa da ni, sbd ya san bana son shi kuma na tsane shi. Muna zaune a haka rayuwata cikin qunci da baqin ciki, wata rana Amir ya biyo ni har qauyen da nayi aure, a sannan xuciyarsa ta kamu da matsanancin ciwo. Amir ya sha wahala sosai ya yi qoqarin xuwa inda nake, don ya sake gani na, muyi bankwana tunda ya san ciwo ya ci qarfin jikinsa, rayuwarsa ta xo qarshe."
¤
Sadiya a fara kuka, ta tsaya da basu labarin, ta fara share hawayen da yake xubo mata. Khalifa ya ji xuciyarsa ta buga da qarfi, Hafsatu ita ma ta ji hawaye ya ya fara sartu a idanunta. Sadiya ta ci gaba da fada masu cewa.
¤
"Da na samu labarin cewa Amir ya biyo ni, amma ya fadi a bayan gari ya kasa takowa ya xo qofar gidan mijina, sai na miqe na fita da gudu don in je in same shi. Wannan shi ne abin da ya 6atawa mijina rai, ya ba mutanen garin damar su kama ni, kuma su kashe Amir, ya ce babu abin da zai faru, tunda shi ne Dagaci, to amma har naje wajen da Amir yake babu wanda yayi nasarar kama ni a cikin mutanen dake biye da ni, na durqusa a gaban shi ina kuka a daidai lkcn da yake qoqarin bude baki yayi magana. Amir ya fara neman afuwata, ya ce in yafe masa laifin da yayi mani a baya, ya ce duk abin da ya faru shi ya jawo, na ce na yafe masa duniya da lahira, nayi kuka kamar raina zai fita, sbd halin da naga Amir masoyina a ciki, duk maganar nan da muke yi da Amir a kwance yake baya ko iya bude idanun shi. Ga jini ya xuba ta baki da hancin shi, sbd xuciyarsa ta kumbura tuntuni. A haka mijina da mutanen shi suka xo suka same ni da Amir."
¤
Khalifa ya yi saurin tambayar ta cikin xullumi.
¤
"A haka duk da halin da Amir yake ciki suka kashe shi da hannun su?"
¤
Sadiya ta girgiza kan ta, hawaye ya xubo daga cikin idanunta, ya sauka akan teburin dake tsakiyarsu..
¤
"A'a, basu yi masa komai ba, nima ba wanda ya ce da ni komai. Duk mutanen da abin ya faru akan idonsu suka tsaya suna kallonmu, shi kanshi mijin nawa a lkcn yayi saranda, ya fahimci kuskuren da yayi na qwallafa ranshi a kaina. A nan Amir ya rasu a gaba na....a gaban mijina...a gaban kowa."
¤
Sadiya ta dora kanta akan teburin ta ci gaba da kuka. Irin kukan da suka same ta tana yi a daren da ya gabata, lkcn farko da suka fara ganinta, Hafsatu taji hawaye yana xubo mata akan kumatunta. Bata san ita ma kuka take yi ba, sai da taji sanyi tafiyar hawaye akan kumatunta, ta share hawayen da hannayenta biyu. Khalifa ya kasa ko motsawa akan kujerarsa. Bai ta6a jin irin abin da yake ji ba a xuciyarsa a halin ynxn.
¤
Masoyina Amir rasu, wannan ce rabuwata dashi ta qarshe, aka je garin Kakanin sa aka sanar dasu suka xo suka yi masa sutura. Sarkin noma kuma da yaga haka sai ya sauwaqe min. Ya sake ni ya ce in koma gidan iyayena. Na san idan na koma gidan iyayena, zasu yi qoqarin mayar dani gidansa, tunda ya riga ya saye su, ya tula masu kudi. Wannan ne dalilin da yasa na gudu na gwammace in shiga duniya ko na samu sauqin wannan musiba da ta addabi rayuwa ta. Bana sha'awar gida, nafi son in nisanta da duk wanda ya sanni a da, ina so ne in sake sabuwar rayuwa, na gaji da zama a cikin takaici da baqin ciki, da na taho ne cikin dare na gaji da tafiya na fadi a hanya, ku kuma kuka xo kuka same ni, kun ji labarina a taqaice."
¤
Sadiya ta ci gaba da kukan da take yi kanta a sunkuye bisa teburin. Khalifa da matar yayansa Hafsatu, suka kasa yin magana har wani lkc, sai daga baya ne Hafsatu ta yi ajiyar xuciya, ta share hawayen dake cikin idanunta ta ce da Sadiya.
¤
"Rayuwa kenan, ki yi haquri ki daina kuka Sadiya, mun tausaya maki matuqa akan wadannan abubuwan da suka faru dake, kuma mun yi alqawarin zamu taimake ki, zamu riqe ki bisa amana kamar yadda kika ga kowanne yaro a gidan nasn, kwantar da hankalinki ki zauna tare damu, har xuwa lkcn da zamu ga abin da zai faru kuma, kada ki damu Sadiya."
¤
Sadiya ta tashi daga kan kujerar kanta a sunkuye, tana qoqarin tsayar da kukan da ya sake taso mata, ta ce dasu.
¤
"Na gode da taimakon ku gare ni...
¤
Lp=10¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
10
with
Iliyas Ishak Gundutse
Ix
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
¤
¤
"Na gode da taimakon ku gare ni, Allah Ya saka maku da alkairi, ina son zan koma daki kuyi mani uxuri."
¤
Sadiya tayi sauri ta bar dakin cin abincin. Khalifa ya bita da kallo bakin sa a bude ya kasa ce mata komai, sai da ta fita ne ta nufi dakin ta, sannan ya ja doguwar ajiyar xuciya ya ce da Hafsatu.
¤
"Sadiya ta sha wahalar soyayya, ko kuma in ce ta sha wahalar rayuwa, amma na dauki alqawarin zan share mata hawayenta, zan maye mata gurbin Amir tsohon masoyinta."
¤
Hafsatu ta juya ta dube shi sosai ta ce dashi.
¤
"Me ka ke nufi da zaka maye gurbin tsohon masoyinta Amir? Khalifa tun jiya naga alamar kana yiwa yarinyar nan wani iri kallo wanda ban gane masa ba, me kake nufi?"
¤
Khalifa ya dubi fuskarta sannan ya ce da ita.
¤
"Anti ba zan cuci kaina ba, gsky ina son yarinyar nan fiye da duk yadda zan fada maki, na kamu da son ta, kuma ba zan iya daina son ta ba, in dai ina raye a duniyar nan."
¤
Hafsatu ta ce.
¤
"Gareje ga dami! Daga xuwanta har zata qwace min kai, a haka za'ayi zaman dama? A'a, ban yarda ba, ynxn nan zan je in koreta ta koma qauyensu, ba zai yiwu ina zaman zamana lfy na in jawo wata taxo ta qwace min miji."
¤
Da yake Khalifa ya san wasa take yi masa sai ya yi dariya duk da damuwar dake a xuciyarsa. Hafsatu ita ma ta saki ranta ta ce dashi.
¤
"Ko baka fada ba na san kana son Sadiya Khalifa, na fahimci haka tun jiya, to amma ba zai yiwu kayi mata zancen soyayya ba tun ynx, ka bari sai nan gaba."
¤
Khalifa ya kalli Hafsatu cikin rashin fahimta.
¤
"Me zai sa in 6oye mata abin dake a xuciyata Anti?"
¤
Hafsatu ta ce dashi.
¤
"Baka ji ta ce mijinta ya sake ta ba a labarin da ta bamu? Ba damar ka ce kana son ta ynx, dole sai tayi Iddah ta gama, ka bar abin a xuciyarka, idan lkc yayi ni da kaina zan same ta muyi maganar, ka kwantar da hankalinka Khalifa, ni naji a jikina wannan yarinyar ita ce matarka."
¤
Khalifa ya yi dariyar farin ciki. Ya dade bai ji wata magana kwatankwacin wannan ba.
¤
¤
-------------------------------------------------------
¤
Sadiya ta zama 'yar gida a wajen su, ta saki jikinta suna zaune tare. Tana girmama Hafsatu, komai taga ta tashi zata yi sai ta tashi ta amshe tayi mata, tana taimakonta a wajen duk aikace-aikacen gida, tare suke shiga Kicin suyi aikin abinci, idan sun gama Sadiya ke xubawa kowa nasa, sannan ta tattare farantai da kwanoni ta wanke idan sun gama.
¤
Kafin Hafsatu ta tashi a inda take zaune Sadiya ta gyara mata dakin ta da falo, bata da kasala, a koda yaushe bata zaunawa sai taga ta kammala duk wani aiki da yayi saura a gidan.
¤
A kwanaki hudun da Sadiya tayi a gidan ta saba sosai da 'ya'yan Hafsat, da sun dawo daga makaranta zasu yi dakin ta, sbd tana sakar masu fuska, tana sauraren duk wani abu da zasu fada mata.
¤
Idan suka fito da kayan wasannin su waje, suka barbazar dasu, ita zata tattara su ta adana kafin su sake waiwayarsu. Babu ma kamar Abba wanda duk lkcn da Alfat ya zalunce shi wajen Sadiya ynx yake kai kukansa maimakon mahaifiyarsu Hafsatu, wacce bata da juriyar daukar qorafin yara, da sun isheta da surutu zata kore su waje,

Please Login or Register in order to submit comment