Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alfat, amma ynx na dawo."
.
Abba ya tambaye shi.
.
"Abba zaka sake komawa?"
.
Khalifa ya dubi Abba, ya kasa bashi amsa. Hafsatu ta janye su daga jikin Khalifa, ya miqe tsaye ya kalleta cikin jin kunya.
.
"Anti."
.
"Na'am Khalifa, sannu da xuwa. Ya hanya?"
.
Khalifa ya ce.
.
"Lfy lau Anti."
Ya qanwata Sadiya?"
Ya yi murmushi sosai.
"Ta ce in gaishe ku, tana nan lfy."
.
Hafsat ta harare shi.
.
"Nayi fushi sosai Khalifa. Da kai da ita duk kun canza layin wayoyinku. Me yasa baku son muyi magana da ku?"
.
Khalifa ya ce da ita.
.
"ban san me ya faru da layin Sadiya ba, ni dai nawa faduwa yayi tun a ranar da naje."
.
Hafsatu ta sake harararsa ta ce.
.
"baka daina qarya ba har ynx Khalifa?"
.
Ya yi dariya ya kama hannun Alfat da Abba suka shiga cikin gida, Hafsatu ta biyo su a baya. A lkcn ne shima direba ya fitowa da Khalifa jakarsa ya biyo su da ita, ya nufi 6angaren da dakin Khalifa ya kai masa jakarsa.
.
Lkcn da Khalifa ya shiga gidan ne ya ji ya cika da qamshi an qawata ko'ina sai sheqi yake yi. Babu shakka Khalifa ya dawo gida.
.
Dakta Hamza ya fito daga cikin dakinsa, yana sanye da jaket mai ruwan qasa. Su ka yi arba shi da dan uwansa Khalifa suka kalli juna, suka matso kusa suka hadu. Hafsat da 'ya'yanta suka tsaya a baya suna kallon Dakta Hamza da Khalifa, har xuwa lkcn da kowa ya tsaya a gaban kowa. Dakta Hamza ya fara yi masa magana.
.
"Khalifa ka dawo?"
Ya ce da shi.
"Na dawo Dakta."
.
Suka kalli juna su dukan su sun rame. Kowa ya shiga damuwa da rashin jin dadin rabuwa da Dan uwansa. Dakta Hamza ya ce dashi.
.
"Ka yiwa xuciya rauni Khalifa. Ka jefa ni a cikin damuwa. Na san ka san haka.".
.
Khalifa ya ce dashi.
.
"Na san haka Dakta. Amma kana kallona na kwashe kayana na tafi. Da ace kana so in zauna tare da kai, ba zaka yarda in tafi in bar maka gidanka ba. Kai ka ce in tafi. Shi yasa na tafi."
.
Dakta Hamza ya sa hannu ya ture shi cikin fushi.
.
"Da ka fita me yasa baka dawo ba? Me yasa ka je ka yi zaman ka a can? Ni ba yayanka ba ne? Ba kai bane ke qasa da ni? Don nayi fushi sai kaima kayi fushi da ni? Ka yi min da'a kenan Khalifa?"
.
Khalifa ya yi ajiyar xuciya.
.
"Na dauka a lkcn ka tsane ni ne shi yasa na tafi. Bana son in tsaya in ga fushinka. Na bari ne sai sanda ka huce daga fushi da kayi sannan in dawo."
.
Dakta ya ce dashi.
.
"Duni yadda ka koma Khalifa. Dubi halin da ka jefa kanka a ciki. Lkcn da mahaifiyarmu zata rasu ta ce, in riqe ka amana. Kada in bari ka shiga cikin wahala, in dai ina da yadda zan yi. Nayi iya qoqarina wajen ganin na cika umarnin mahaifiyarmu. Amma baka bani hadin kai ba Khalifa. Ina son in gina rayuwarka ka zama abin alfahari, amma kai kana son ka jefa rayuwarka cikin tagayyara. Me yasa ka za6i kayi mani haka Khalifa?"
.
Ya ce da Dakta.
.
"Ba so nake in jefa rayuwata a cikin halaka baSADIYA
Page 57
.
.
.
"Ba so nake ba in jefa rayuwata a cikin halaka Dakta. Ni ne nake yunqurin in sami kwanciyar hankali, kai kuma kake son ka jeda ni cikin wahala. Ka san abin da xuciyata take so. Me yasa ba zaka bani hadin kai ba in cimma burina ba, in har kana sona da gaske?"
.
Dakta Hamza ya ce dashi.
.
"Sau da yawa Dan adam ya kan duqufa wajen neman abu wanda bai cancanta dashi ba. Ko ya samu ba zai amfaneshi da komai ba. Kamar yaro ne da yake qoqarin jefa hannunsa a cikin wuta. Bai san zafin wutar ba. Yana dai ganinta ne kawai a nesa tana bashi sha'awa. Ta yaya kuwa za a barshi ya jefa hannun nashi a cikin wutar ya qone? Duk irin son da yake yiwa wutar, dolene a kamo hannunsa a jawo shi baya."
.
Khalifa ya yi murmushi tunda ya san Dakta Hamza bai san abin dake a xuciyarsa ba. Bai san irin son da yake yiwa Sadiya ba. Hafsat tasa baki a cikin maganar su ta ce.
.
"Dama kai muke jira tun daxu, bamu karya kumallo ba. Mu je (Dinning room)."
.
Suka dunguma dukansu kamar yadda suka saba a lkcn baya, suka tafi dakin cin abinci.
.
.
**
.
.
Bayan Hafsatu ta hadawa kowa shayinsa, kowa ya amsa sun fara karyawa. Sai suka ci gaba da maganganunsu na cikin gida. Hafsatu ta kalli Khalifa ta ce dashi.
.
"Ka saki jiki ka ci abincinka. Ba irin shayin da wannan 'yar qauyen take hada maka bane."
.
Da yake ya san wasa take yi masa. Sai yayi dariya ya ce.
.
"Ai Anti idan kika sha shayin Sadiya, sai kin mance hanya don tsabar dadi."
.
Hafsat ta ce.
.
"To wa ya koya mata in ba ni ba?"
.
Suka yi dariya tare. Alfat ya ce da Khalifa.
.
"Abba idan zaka koma zan bika mu koma tare."
.
A lkcn ne Dakta Hamza yayi farat ya ce.
.
"Wa ya fada maka zai sake komawa? Abbanka ya dawo gida daga yau ba zai sake komawa ko'ina ba."
.
Khalifa ya yi dariya ya dafa kan Alfat ya ce dashi.
.
"Kada ka damu Alfat, in har lkcn tafiya ya sake xuwa zan tafi tare da kai."
.
Abba ya ce cikin shagwa6a.
.
"Nima zan bika muje tare Abba."
.
Khalifa ya ce dashi.
.
"Zan kwashe ku mu tafi tare ku duka, shi kenan?"
.
Dakta Hamza ya ture kofin dake a gabansa ya ce cikin damuwa.
.
"Ya isa haka nan."
.
Hafsatu ta tuntsire da dariya.
.
Bayan Khalifa ya huta ne, sai Hafsatu ta janye 'ya'yanta suka koma daki, ta bar Dakta suyi magana da dan uwansa. Akwai wani abu da yake bata tsoro ta kasa fahimtar ko mene ne a game da mijin nata Dakta Hamza. Bata san abin da ya qudure a game da qanin nasa Khalifa ba, amma dai ta fahimci idan har basu daidaita ba, babu shakka wani abu zai faru a gidan, domin kuwa ta tabbatar a wannan karon Dakta ba zai sake barin Khalifa ya tafi ba.
.
Dakta Hamza da Khalifa suka zauna a falo suna fuskantar juna, kowannen su a kan kujerarsa. Khalifa shi ya fara magana, bayan ya tattara hankalinsa waje guda.
.
"Na xo ne dama don in baka haquri akan abin daya faru tsakaninmu.
.
Da kuma abin da iyayen Sadiya suka yi maku kai da Anti. Mu dukaninmu mun yi kuskure muna roqonka kayi haquri. Da ace ka amince mu xo tare da iyayen Sadiya, da ka fahimci irin nadamar da suka yi. Mutanen kirki ne, wadanda suke karrama baqo. Kuskure aka samu har suka aikata abin da ya faru, amma sun ce kayi haquri."
.
Dakta ya yi murmushi.
.
"Ba komai Khalifa, na yafe musu. Ban riqi kowa a raina ba. Kaima na yafe maka. It's always my peasure to forgive."
.
Khalifa ya ce dashi.
.
"Na gode kuma naji dadi. Sai magana ta biyu wacce muka fara da kai jiya a waya. Ina roqonka da kayi haquri ka janye wadannan matakai da ka dauka, na kai iyayen Sadiya kotu. Da sauran laifukan da zaka ce sun yi, wanda kai kanka ka san idan aka yi haka to an zaluncesu. Bai kamata don sun yi kuskure daya, a ce an yi masu irin wannan horon ba. Kayi haquri ka janye niyyarka akan hakan."
.
Dakta Hamza ya ci gaba da murmushi.
.
"Nayi niyyar yin hakan. Ko ynx kana iya xuwa banki ka turo min da kudi milyan hamsin su dawo (account) dina. Na fasa duk abin dana fada maka zan yi jiya, dama nayi maka haka ne don ka dawo gida. Da ban fada maka haka ba, da ba zaka ji tsoro ka dawo kai kadai ba."
.
Khalifa ya ce dashi.
.
"Sai magana ta gaba. Wato maganar aurena. Yau saura kwana uku a daura auren. Iyayen Sadiya su suka yi komai, duk abin da iyaye ke yiwa dansu a harkar aure, iyayen Sadiya sun yi mani, sun daukeni tamkar dansu da suka haifa."
.
Dakta Hamza ya ce.
.
"ba wani abin mamaki bane don sun yi hakan,, ko nawa suka kashe sun san zasu ci riba a gaba. Sun san dan uwanka yana da dukiya mai yawa, idan ya mutu kai ne zaka kula da dukiyarsa sbd 'ya'yansa qanana ne. Idan dukiyarsa ta dawo hannunka kai ke da iko akanta, babu mamaki ka diba ka riqa kai musu. Duk abin da kaga dan Adam ya yi a duniya, to idan ka bishi a hankali zaka gano abin da yake son ya cimmawa a gaba."
.
Khalifa ya nuna damuwa a fuskarsa.
.
"Ba haka iyayen Sadiya suke ba Dakta. Iyayen Sadiya basu san komai ba a game da abin da ake cewa dukiya. Su a wajensu idan mutum ba manomi bane, basu dangantashi da wata dukiya. Mutane ne dake a cikin daji, basu san duk wani jin dadi da zamani ya xo dashi ba.SADIYA
Page 58
.
.
.
Ba haka iyayen Sadiya suke ba Dakta. Iyayenta basu san komai ba a game da abin da ake kira dukiya. Su a wajen su idan mutum ba manomi bane, basu danganta shi da wata dukiya. Mutane ne dake a cikin daji, basu san duk wani jin dadi da zamani yaxo dashi ba. Ta yaya zasu yi wannan tunanin da kake yi ynxn? Ba ruwansu da wannan kudin da kake dashi, basu san komenene ba."
.
Dakta Hamza ya gyara zama ya ce da Khalifs.
.
"Duk abin da ka yi a rayuwa Khalifa, ka fara tambayar kanka me nene ribar ka idan kayi a bin? Duk abin da ba zai amfana maka komai ba, babu dalilin da zai sa ka yi shi. Tunda ka je wannan qauyen wajen masoyiyarka mai ka qaru dashi a rayuwarka? Baka qaru da komai ba sai su da suka qaru da kai. Ka yi mu'amulla da mutanen da zaka qaru dasu a wani abu. Ka nemo muhimman mutane a rayuwa, kayi mu'amulla dasu, kayi la'akari da rayuwata Khalifa. A cikin abokaina akwai Gwamnoni da kwamishinoni. Ina da aboki Ambassada, ina da aboki sanata, ina da abokai a cikin manyan hafsoshi sojojin qasar nan. Matata Hafsat na aurota ne a babban gida. Tana da 'yan uwa a qauye, to amma iyayenta manyan mutane ne. Kafin mahaifinta ya rasu ya ta6a zama mataimakin babban alqalin kotun qoli na qasa. A dalilin mutanen da yayi aiki tare dasu, a ynx haka idan ina neman wata alfarma a sashin shari'a da gudu ake yi mani. Idan 'ya'yana suka taso, ko bani a raye akwai inda zasu je a basu aiki a kowacce ma'aikata ko gurbin dake a qasar nan.
.
To amma kai ynx idan ka auri wannan yarinyar wacce ke da irin wadannan iyayen, da irin wadannnan dangin da me zaka yi alfahari Khalifa? Me zasu qare ka dashi a duniya, wanda baka dashi? Sai dai su zame maka Parasites.... Liabities a rayuwarka. A lkcn da ta zauna a nan gidan, ban yi tsammanin irin wadannan mutanen sune danginta ba. Shi yasa har na barka ka shaqu da ita. Amma ynx bayan duk abubuwan da suka faru, wadanda na gansu da idona, ta yaya zan barka ka aureta? Idan aurenkas ya xo ina da muhimman mutane na wadanda zan gayyata, yawancinsu daga qasashen waje zasu xo, ta yaya zan kare kaina idan suka xo su ka ga inda zamu je daurin aurenka? Kowa zai qalubalanceni su ce ban riqeka irin riqon da nayi wa rayuwata ba. Kowa zai ce ina da dukiya amma na gaza taimakawa qanina. 'Yan jarida sun samu abin yayatawa a duniya. Na zama abin nunawa a cikin manyan abokaina, na yi abin da za a riqa yi mani gori har a gaba. Bayan kuma ba laifina bane kai ka jawo mani Khalifa, ta yaya zan bari ina kallo ka tarwatsa mani mutuncina da matsayina a qasar nan? Dole ne in hana ka ka auri Sadiya, koda kuwa hakan na nufin in dauki matakin da bana so."
.
Khalifa ya ji tsoro ya fara kama shi. Tabbas Dakta bai haqura ba. Kuma ba zai ta6a haqura ba. Ya yi masa dabara ne ya dawo gida don ya hana shi komawa.....don ya raba shi da Sadiya har abada....to amma ta wacce hanya zai iya tsare shi da girmasnshi da hankalin shi?
.
.
Tagwaye ne. Ci gaban shi na biye.SADIYA
Page 59
.
.
.
Yayi masa dabara ne don ya dawo gida ya hana shi komawa.....don ya samu damar raba shi da Sadiya har abada.....to amma ta wacce hanya zai iya tsare shi da girman shi da hankalinshi? Lallai ya kamata ya gaggauta barin wannan gidan ya nemi mota ya koma garin su Sadiya, don kada Dan uwansa ya shammace shi ya qulla masa wani makircin da zai sa dole ya zauna a gida. Khalifa ya tashi xumbur ya miqe tsaye ya ce da Dakta.
.
"Ban san abin da zan fada maka ba ka fahimce ni. Baka san soyayya ba Dakta. Kuma baka ta6a yin soyayya ba. Ita kanta Anti da ka aureta ba son ta kake yi ba. Ka aureta ne don nasabar mahaifinta, da kuma karatun da tayi. Baka ta6a son wata mace don Allah ba. Shi yasa ba zaka ta6a jin irin radadin da masoya suke ji ba a xuciyarsu. Sbd haka ni zan koma, saura kwana uku a daura aurena da Sadiya. Naxo ne in fada maka a matsayinka na dan uwana."
.
Khalifa yayi tsammanin Dakta zai nuna fushi, musamman da yaga ya miqe zai sake tafiya. Maimakon haka sai yaga Dakta yayi murmushi.
.
"Ba hanya Khalifa. Babu hanyar da zaka sake bi ko koma wajen Sadiya. Na toshe hanyar ba sake bin wannan hanyar ba. Idan har na sake bude maka wannan qofar a to sai na tabbatar Sadiya tayi aure ta haihu, a lkcn matar wani ce, zaka ce ne ta kashe aurenta ta xo ku yi wani auren?"
.
Dakta ya fara dariya kamar wanda ya sha giya. Khalifa ya sake jin tsoro ya kama shi. Yas waiga ko'ina a cikin falon bai ga wata qofa dake a rufe ba. Kowacce qofa a bude take har yana iya hangen waje. To wacce hanya ya ce ya toshe masa? Lallai ya kamata ya hanzarta ficewa daga gidan nan, sbd akwai babbar matsalar dake shirin faruwa. Akwai wani tarko da Dan uwansa yake qoqarin ya jefa masa.
.
Khalifa ya fita daga falon cikin sauri, ya ruga da gudu ya nufi waje. A lkcn ne ya jiyo muryar yayansa yana keta dariya. Sai da Khalifa ya fito farfajiyar gidanne inda suke ajiye motoci, sai ya ci karo da ma'aikata hudu sanye da kayan ma'aikatan asibitin nahaukata. A bayan su kums wani likita ne riqe da qaramar jakar xuba magani, yana sanye da fararen kaya.
.
Da fitowar Khalifa ma'aikatan suka cafe shi, su dukansu qatti ne majiya qarfi kamar 'yan lodin shanu a kara. Khalifa ya fara yi masu ihu yana tambayarsu.
.
"Me nayi maku? Me nayi maku da zaku kama ni?"
.
Likitan ya matso kusa da yaga sun danne Khalifa ya kasa motsi, yana 6urari a kwance. Ya ce da ma'aikatan.
.
"Ku riqe shi da kyau zan yi masa allura ne. Dan uwansa ya ce ciwon haukarsa yana da qarfi sosai, har kashe mutum ya ta6a yi. Kada ku barshi ya kufce!"
.
Da Khalifa ya ji abin da Likitan ya fada ne, sai ya fara hargowa yana cewa.
.
"Ni ba mahaukaci bane, qarya yake yi, ni ba mahaukaci bane! Ban ta6a kashe kowa ba. Wallahi ni ba mahaukaci bane."
.
Likitan bai saurari maganar da Khalifa yake yi ba. Ya ciro sirinji ya jawo wani magani a kwalba ya duqa ya tsirawa Khalifa allurar a hannunsa. Kafin ya zare allurar tuni har jikin Khalifa yayi sanyi, ko'ina a jikinsa ya mutu, ya kasa motsawa. Mutanen wadanda basu da wani aiki sai kamo mahaukata idan Likita zai fita aiki, suka saki Khalifa don kuwa sun san babu abin da zai iya tunda aka yi masa allura.
.
A lkcn ne Dakta Hamza ya fito gidan, ya samu mutanen, Likitan ya matso ya bashi hannu suka gaisa. Ya ce dashi.
.
"Mun yi masa allura, zamu tafi dashi asibiti ynxn, zamu bashi daki.".
.
Dakta Hamza ya ce da Likitan cikin damuwa.
.
"ka tabbatar ka samar masa wuri mai kyau. Ina son ku riqa kulawa dashi kamar yana gida. Duk wani abu na jin dadin rayuwa ku kai masa dakinsa. Zan biya komai zan xo gobe in ganshi."
.
Likitan ya ce da Dakta Hamza.
.
"Kada ka damu Dakta, za a yi masa duk yadda kake so. Mene ne amfanin zaman taren? Kada ka damu."
SADIYA
Page 60
.
.
"Ba komai Dakta, za a yi masa duk yadda kake so. Mene ne amfanin zaman tare? Kada ka damu."
.
Qartin hudu suka dauki Khalifa, jikinsa yayi sanyi, suka fita waje dashi inda suka ajiye motarsu ta asibitin mahaukata. Suka bude motar suka saka shi a ciki. A dai dai lkcn da likitan mahaukatan yake yiwa Dakta Hamza sallama zai tafi a lkcn ne Hafsatu ta fito ta rude tana kiran mijinta.
.
Dakta Hamza ya nufi inda matarsa, daya Likitan ya fice daga gidan ya shiga motarsa, suka tafi da Khalifa xuwa asibitin. Hafsatu ta fara yiwa Dakta Kwaratsi. Tana magana cikin fushi tana cewa.
.
"wannan wane irin abu ne Dakta? Akan me zaka yiwa dan uwanka haka? Ta yaya mutum da hankalinsa zaka kira asibitin mahaukata ka ce su xo su daukeshi bashi da hankali? Dama abin da kake shiryawa kenan tun jiya baka fada mani ba? Akan me zaka yi wannan danyen aikin? Akan me?"
.
Ta daka masa tsawa tana kuka. Dakta Hamza ya ce da matarsa.
.
"Nayi haka ne domin in nisanta shi da Sadiya, ta yadda har abada ba zai sake ganinta ba. Khalifa zai samu kulawa a asibiti kamar yada zai samu a nan gidan. Mun shirya wannan hikimar ne domin mu 6oye Khalifa. Ba kuma zai fito daga wannan asibitin ba sai Sadiya tayi aure ta haihu."
.
Hafsa ta ja baya cikin fushi ta nuna shi da yatsa.
.
"Wannan rashin tausayi ne, kuma rashin imani ne qarara. Idan har wannan abin da kayi shi ne qaunar da kake nunawa qaninka Khalifa, to tabbas bata da amfani. Baka qaunar Khalifa Dakta!!"
.
Dakta ya ce da matarsa.
.
"har ynx nafi kowa son sa a duniya. Ba abin kunya bane don mutane sun samu labarin qanina ya samu matsala a qwaqwalwarsa, an kai shi asibiti. Amma abin kunya ne a gare ni a samu labarin qanina ya auri Sadiya, ya hada xuri'a da danginta. Ban san iya lkcn da Khalifa zai yi ba a asibitin kafin ya fito. Zai yiwu ya kai shekara daya, ya danganta ga lkcn da Sadiya tayi aure. wataqila kuma ya kai shekara biyar ko goma. To amma ko yaushe zai kai na san wata rana zai fito, zai sabunta rayuwarsa......zai mance da Sadiya, zamu dawo mu sake zama tare....as a family. Kamar yadda muka saba. Damuwar da Khalifa zai yi a asibiti tana da iyaka, amma idan ya auri Sadiya yaushe zan samu kwanciyar hankali? Na fiki qaunar Khalifa, na fi ki jin tausayinsa. Amma ya zame mani dole in dauki wannan matakin domin in kare mutuncin wannan gida namu."
.
Hafsatu ta ci gaba da kuka, ta juya da sauri ta shiga tana share hawaye. Bata ta6a sanin tunda tayi aure da azzalumi take zaune ba, sai a wannan rana.
.
.
.
**
*
.
.
Bai farfado ba sai da ya kwana ya wuni a asibiti. Babban asibitin masu ta6in hankali ne, dake qunshe da kimanin mahaukata dari biyu da hamsin. Kowanne mahaukaci na a cikin dakinsa da aka yiwa qafar rodi kamar dakunan gidan (Zoo).
.
Sa6anin sauran dakunan dake a asibitin wadanda bab komai a ciki sai tabarmar kwanciya da robar cin abinci. Dakin da aka kawo Khalifa an qawata shi da kayan alatu, an ajiye masa lafiyayyiyar katifa da zanin gado mai laushi da taushi, akwai kayan kallo a dakin, da fanka da sauran tarkacen da mutum zai buqata kullum tun daga sabulun wanka da maya-mayan shafawa, man wanke haqora da burusan taje suma. Ba wani abu da Khalifa yake amfani da shi a gida wanda ba a kawo masa dakin dake a asibitin ba.
.
Lkcn da Khalifa ya fara bude fara bude idanunsa, bai tuno abin da ya faru dashi ba. Sai ya ji kansa yayi nauyi kamar an dora masa dutse.SADIYA
Page 61
.
.
.
Lkcn da Khalifa ya fara bude idanunsa ya farka, basi tuno abin da ya faru dashi ba, sai dai ya ji kansa yayi nauyi kamar an dora masa dutse. Ya ji ko'ina a jikinsa yana yi masa ciwo. Ya samu kansa kwance daki a kan katifa bai san ko'ina ne ba. Ya yunqura dakyar ya zauna akan katifar, ya fara waiga kowanne 6angare yana kallon dakin.
.
Sannu a hankali ya fara tuno abubuwan da suka faru. Tun barowarsa qauyen su Sadiya, da dawowar shi gida. Ya tuno maganganun da suka yi shi da yayansa Dakta Hamza. Da irin sa'insar da suka yi. A qarshe ne ya tuno lkcn da ya fito daga gidan zai gudu ya hadu da wasu mutane a waje wadanda suka kama shi da tsiya suka kayar dashi. Zai iya tuno lkcn da wani mutum dake tare dasu, ya ke cewa su riqe shi da kyau zai yi masa allura wai shi mahaukaci ne.
.
Daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba. Sai ynxn da ya farka ya samu kansa a wannan wuri. Abin ya zame masa kamar almara ko mafarki. Ta yaya haka kawai da hankalinsa da lfyrsa za a kama shi a yi masa allura a xo a kulle shi a wannan Daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba. Sai ynxn da ya farka ya samu kansa a wannan wuri. Abin ya zame masa kamar almara ko mafarki. Ta yaya haka kawai da hankalinsa da lfyrsa za a kama shi a yi masa allura a xo a kulle shi a wannan dakin?
.
Sai da Khalifa ya kasa kunne da kyau, sannan ya fara jiyo hayaniyar dake tasowa a cikin gidan. Ya jawo qafafuwansa ya sauke su qasa, ya dafa bangon qaramin dakin ya taka inda qofar dakin take, wacce daga ciki ana iya ganin duk wanda zai wuce ta gaban dakin, a sakamakon qarafan da aka jera a tsaitsaya a qofar dakin masu tazara.
.
Khalifa ya dafa rodikan qofar ya tsaya a lkcn ne ya hango mutanen dake a wasu dakunan. Dukkan su a hargitse suke, wadansu gashin kansu ya taru tsauni guda, kayan jikinsu a yayyage, wadansu suna ta qyalqyala dariya suna surutai. Khalifa ya ji gabansa ya fadi. Babu shakka gidan mahaukata aka kawo shi. Me ya same shi da za a kawo shi nan? Ya tabbatar lfyrsa qalau. Shin dama abin da Dakta ke nufi kenan da ya ce zai raba shi da Sadiya har abada? Ya sa an kawo shi gidan mahaukata kenan, don Sadiya ta samu labarin ya haukace, ta haqura dashi ta samu wani saurayin da zai aureta.
.
Khalifa ya fara ihu a cikin dakin, yana dukan qofar qarafan yana cewa.
.
"Ni ba mahaukaci bane! Ku xo ku bude ni. Ni ba mahaukaci bane sharri akayi mani."
.
Ya fara kuka, da yaji babu wanda yake sauraren shi, sauran mahaukatan suna ta haukarsu a dakunan su, basu san ma yana yi ba. Khalifa ya juya cikin dakin a fusace, ya fara yin fatali da kayan da aka xuba masa a dakin. Ya dauki tibinb ya buga shi da qasa ya fashe, ya riqa daukar duk wani abu da ya fado a hannunsa yana kwada shi da bango. Kwalabe suka farfashe. Yana lalata kayan dakin yana cewa da qarfi.
.
"Ni ba mahaukaci bane! Ku fita da ni, ni ba mahaukaci bane!!"
.
Khalifa yasa hannayensa biyu yana dukan qarafunan qofar yana kuka, har sai da hannayensa suka farfashe suna xubar da jini. Sai da ya ji ciwo sosai, sannan ya fadi qasa ya dora hannayensa akai yana kuka kamar ransa zai fita.. Ba zamansa a gidan mahaukatan yake yiwa kuka ba. Rabuwarsa da Sadiya yake yiwa kuka. Ynx har abada ba zai sake gabin Sadiya ba a rayuwarsa?
.
.
**
*
.
.
Kwana uku da tafiyar Khalifa ba amo ba labari. Hankalin Mai unguwa mahaifin Sadiya ya tashi. Ya kasa zaune ya kasa tsaye. Yaya Khalifa zai yi haka, daga kwana daya yaje yayi zamansa a gida? Ga ranar daurin aure ta xo, amma babu damar a daura tunda Khalifa bai dawo ba, babu wanda ya san me ya faru dashi da ya koma gida.
.
Sadiya tafi kowa rudewa da rashin dawowar Khalifa. Ta neme shi a waya, kullum ba dare ba rana. Amma bata same shi ba. Duk layikansa a rufe suke. Ta san indai qalau babu yadda za a yi Khalifa ya je gida yayi zamansa ya qi dawowa har a kawo wannan lkc, gashi ranar daurin auren Sadiya tafi

Please Login or Register in order to submit comment