Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga, tun daxu dama ke take ta zaman jira, ai rauhanai sun fadi mata zaki xo."
¤
Inna Gaje tayi dariya ta ce.
¤
"Ai gani fa nazo dan tsito, a fadawa rauhanai naxo in gaishe su."
¤
Tsohuwar ta bi Gude mai bori har cikin dakin ta, ta same ta a hakimce akan baqin buxun kare, ta dauko qwarya ta ajiyeta a gabanta tana yawo da yatsun ta a ciki. Inna Gaje ta durqusa a gaban ta, kafin ta ce da ita wani abu ne, 'yar borin ta riga ta yin magana ta ce da ita.
¤
"kada ki fada min komai Gaje, ai muna da labarin matsalolin dake tafe dake, ynx dan qarin bayani kawai nake son ki yi mani, don daxu da Sarkin aljanu ya xo yana fada min labarin ki bai gama ba kuma aka gayyace shi bangon duniya, sai anjima zai dawo, qarishe mani in ji yadda aka yi."
¤
Inna Gaje ta ce da Inna Gaje ta ce da Gude mai bori.
¤
"To al'amarin ne dai na 'yarmu da ta 6ace, yarinya an yi mata aure kamar abin arziqi, ta kwashe kayanta ta gudu, wata guda kenan ba amo ba labari, shi ne naxo ki taimake ni mu ji inda take."
¤
Gude mai bori ta dauki qwaryar dake ganta ta jefata sama ta cafke, ta sake jefata ta cafe kamar wacce take wasan amada. A jefawa na uku ne tayi dariya ta ce da tsohuwar.
¤
"ki kwantar da hankalinki, 'yar ku tana nan a raye, ba a riga an kashe ta ba tukuna, amma da kin taushe hannu baki xo yau ba, to da lamari ya lalace, don kuwa gobe ake shirin za a cinyeta."
¤
Ta sake jefa qwaryar sama ta cafe ta. Inna Gaje ta rude ta fara yiwa Gude mai bori magiya.
¤
"ki taimake ni qawata, a ina take, su wa suka dauke mana Sadiya 'yarmu? Tana wane gari ne...?"
¤
Gude mai bori ta ce da ita.
¤
"Hannun wasu mayu ta fada, tana can wani gari ma nisa, a wani gida da ake sace mutane ana cinye su, ba a kusa aka ajiyeta ba."
¤
Inna Gaje ta ce
¤
"ta yaya za a yi ta fito daga can ta dawo gida kada su cinye ta?"
¤
Gude ta ce.
¤
"wannan aikin rauhanai ne, zamu tura su su bude mata qofa ta fito, ba wanda zai ce mata komai, zamu sa rauhanai su riqo hannun ta ta dawo gida da qafarta.
¤
Innan Gaje ta ce jikinta na tsuma.
¤
"A taimake mu a tura su ynx-ynx, a taimakemu ta dawo gida." 'Yar borin ta dubi idanun tsohuwar ta ce da ita. "Zan taimake ki Gaje, 'yar ku zata dawo gida, amma kin san bama tura rauhanai haka nan suyi mana aiki ba tare da mun basu tukuici ba. Ina fatan kin gane?" na gane ranki ya dade za a ka wo musa."
¤
Gude 'yar bori ta ce da Gaje.
¤
"To kin san dai tunda wannan aikin ki ne matsayinki na qawata dole sarkin aljanu zan tura, kuma shi gsky duk aikin da zamu tura shi sai mun bashi qaton sa da kuma tumaki guda uku, sannan kuma muna bashi turamen zannuwa hudu ya rabawa matansa, yana da wani qaramin yaro sarkin rigima wanda baya barin shi ya fita daga gida, to idan zamu tura uban shi aiki dole ne sai an baiwa yaron daqwalen zakaru guda shida matsayin toshiyar baki. To kin ji abin da kuke son ki kawo mu ba Sarkin aljanu, shi kenan sai tafiya zai je ya dawo muku da 'yarku."
¤
inna Gaje ta ce da Gude mai bori.
¤
¤
Lp=16¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
16
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
Inna Gaje ta ce da Guda mai bori.
¤
"Ba matsala ki lamunce ni nan da gobe, zan kawo maki duk wadannan abubuwan da za a kaiwa sarkin aljanu. Ai don irin haka muke tashi a tsaye muna nema kullum, don mu magancewa kanmu matsalar da ta taso mana, zan xo goben ki jira ni qawata."
¤
Gude mai bori ta sake jefa qwaryar ta cafketa.
¤
"Ni da ba ruwa na, idan ma kin 6ata lkc har aka cinyeta kafin sarkin aljanu ya je garin, idan kin xo da wuri shima ya tafi da wuri, idan baki xo da wuri ba to kome ya faru ni dai ba ruwana. Nima fada mani akayi in fada maki."
¤
Inna Gaje ta ce.
¤
"Ai ba 6ata lkc, zaki ganni, da an yi Assalatun fari."
¤
ta tashi ta fita da sauri, tana farin cikin xuwanta inda za a share mata hawayenta.
¤
A ranar da komawarta gida ta sa aka je wata ruga aka amso mata bujumin san ta, wanda ta bada shi kiwo tun shekara biyu da suka wuce, ta hada da tumakin ta da kajin da take kiwo a gida, tsohuwar ta yiwa kanta tatas, bata bari gari ya waye ba, a daren ta sa aka kaiwa 'yar borin duk wannan ganima, ta dawo bata da ko allura a hannun ta, duk neman da tayi na shekara da ashekaru, sai gashi nan take wata boka tayi awon gaba dashi a lkc daya.
¤
Abin da tsohuwar bata sani ba shi ne. Sadiya bata yi nisa ba, tana nan a birnin tarayya Abuja hankalinta a kwance tare da mutanen da suke son ta.
¤
A daidai lkcn da 'yar borin take qaryar wai za a cinye ta. Sadiya tana cikin sabuwar motarta wacce Dakta Hamza ya saya mata, tana yawon ta a cikin birni. Tare da Khalifa wanda ya koya mata motar a sati uku kacal, kuma yake burin ko ana ha-maza-ha-mata sai ya aure ta in dai suna raye.
¤
Khalifa bai san akwai Inna Gaje ba, wacce take nan tana jiran fitowarsu su fado hannunta.
¤
¤
BAYAN WATA UKU
¤
¤
kimanin wata uku cif-cif da tsintar Sadiya da suka yi. Da tashin Khalifa tun da sassafe ya fito dakinsa da gudu ya je dakin matar yayansa wato Hafsatu ya fara kiran ta yana cewa.
¤
"Anti lissafi ya cika yau, wata uku kenan da xuwan Sadiya gidan nan, don haka ta gama iddarta."
¤
Hafsatu ta taso cikin gajiya, ta fito falonta ta samu Khalifa fuskarshi cike da murna, yana riqe da qaramin littafi a hannunsa na lissafi.
¤
"Ya akayi ne Khalifa?" ta tambaye shi, akwai alamar ragowar barci a muryarta. Ya ce da ita.
¤
"Lissafin ne ya cika, yau wata uku kenan da xuwan Sadiya gidan nan, kin ce kada in furta mata komai na kalmar soyayya sai ta gama Iddarta, yau lissafin kwankin da nake yaxo qarshe, ta gama idda."
¤
Hafsatu ta ce dashi tana murmushi.
¤
Anya kuwa ta kai wata uku Khalifa? Na dauka da sauran lkc."
¤
Ya ce da ita.
¤
"ba sauran wani lkc, gashi ma ki gani, na rubuta ranar da muka tsinceta, duba ki gani ki lissafa, xuwa yau za ki ga an yi wata uku har da kwana biyar ma a sama."
¤
Hafsat ta amshi qaramin littafin ta duba rubutun da Khalifa ya yi, bayan ta gama sai ta dawo masa da littafin ta ce dashi.
¤
"ba laifi ynx don ka sameta ka fadi mata kana son ta, amma zan gargadeka, kada ka kuskura kayi nadamar aikata wani abu da zaska yi nadamarsa daga baya, ka tsaya a matsayinka na masoyinta kawai, idan ta amince shi kenan, idan kuma bata amince ba to dole ne ka dauki haquri, ka rabu da ita, rashin amicewarta ba zai canza matsayinta a wajenm ba, mun riqeta ne don mu taimake ta, ba don mu tilasta mata ta amshi soyayyarka ba."
¤
Khalifa ya tattara hankalinsa waje guda ya ce da ita.
¤
"Zan yi amfani da duk shawarar da kika bani Anti. Kuma zaki same ni mutum na gari a duk wata mu'amulla da zata shiga tsakanina da Sadiya."
¤
Hafsatu tayi masa murmushin fatan alheri.
¤
"ka je ka nemi soyayyar Sadiya. Allah Yasa ta amince ta amshi soyayyarka da hannu biyu."
¤
"Na gode anti."
¤
Khalifa ya fita da sauri ya garzaya dakin Sadiya, a lkcn tana kwance tana hutawa, bata koma barci ba tun sanda tayi sallar asubahi.
¤
Da ya je qofar dakin nata ne ya tsaya ya jingina da qofar, ya ji motsinta daga ciki sanda ta gyara kwanciya akan gado. A lkcn ne ya fara bude mata xuciyarsa a karo na farko a tarihin soyayyarsu. Ya yi mata sallama don ya tabbatar ba barci take yi ba. Ta amsa masa ba tare da ta taso ta bude masa qofar dakin ba.
¤
"Na dade ina zaman jiran xuwan wannan ranar, na zauna a cikin qosawa da xumudi ina qirga kwanaki, ina duba agogo, ina kallon fitowar rana da faduwarta, ba don komai ba sai don in furta abin da yake galabaitar da xuciyata dare da rana, xuwa ga wacce ta zama sanadiyyar faruwar duk wadannan abubuwan a gare ni."
¤
Sadiya ta ji jikinta yayi sanyi, don kuwa wannan muryar bata kowa ba ce a duniya, muryar Khalifa ce, shi ne yake yi mata magana da yaren Amir malamin soyayya. Tabbas tuntuni ta fahimci Khalifa ya yi nisa a fagen sonta, kuma ta tabbatar komai daren dadewa sai ya furta mata...don haka yau ga ranar taxo, Khalifa ya kasa jurewa gashi ya taso tunda sassafe yaxo har qofar dakinta yana bata labarin xuciyarsa.
¤
"tun ranar da idanuna suka fara ganinki xuciyata ta dimauce a wajen sonki. Ba qaramin qoqari nayi ba wajen bin umarnin soyayya.
¤
¤
Lp=17¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
17
with
Iliyas Ishak Gundutse
ix
Abu Ihsaan
madufun Taska
¤
¤
Ba qaramin qoqari nayi ba wajen bin umarnin soyayya, da aka tsawatar dani kada in fadi maki sai xuwa ynx, kuma na amince ba don zan iya ba. Ban ta6a zaton xuciyata zata iya jurewa ba, kamar yadda kowanne masoyi yake kwantar da kai don neman soyayya, nima ga nawa hannun na miqo don neman soyayyar ki tare da fatan kasancewata mijinki, ke kuma mata ta, don mu zauna tare a inuwar soyayya da qauna har qarshen rayuwa."
¤
Sadya ta kasa motsawa, ta ci gaba da kasancewa a kwance, qofar dakinta a rufe, tana sauraren saurayin da ta tabbatar idan bata amince ta amshi soyayyarshi ba rayuwarsa tana cikin mummunan hadari. Khalifa ya ci gaba da cewa.
¤
"kada ki wahal da kanki wajen furta mani amsar da nake nema a wajenki. Idan kin amince ina so ki bude qofar dakinki mu kalli juna a ynxn nan ni da ke, wannan ce alamar kin amshi soyayyata. Idan baki amince ba Sadiya ki yi zamanki kada ki bude qofar, idan har hakan ta kasance ina son ki sani, daga nan zan bar gidan nan, in shiga uwa duniya har ajalina ya xo. Idan har na rasa ki Sadiya, bana son komai a duniya, zan gujewa duk wani jin dadi da gatanci dana tsinci kaina a ciki tun ina yaro. Idan har na rasa ki a rayuwata zan za6i zama cikin qunci da yuwa a tsumma har mutuwata ta xo, samunki kawai shi ne jin dadin rayuwata kuma shi ne kadai cikar buri na, don haka ga makomar rayuwata nan na baki a hannunki, shin kin amince in dauwama a cikin farin cikin da nake ciki a ynx ko kuwa kin za6i in shiga uwa duniya in fada cikin mutanen da ba zan qara yin farin ciki ba har abada?"
¤
Sadiya ta taso da gudu ta bude qofar dakin don ta nuna masa ta amince ta amshi soyayyarsa, da budewarta suka kalli juna, hawaye suka fara gudanowa daga cikin idanuwanta, farin ciki ya cika xuciyar Khalifa, wannan kadai ya isa ya tabbatar masa Sadiya ta zama masoyiyarsa.
¤
"Kukan me ki ke yi Sadiya?"
¤
Ya tambayeta fuskarsa cike da murmushin samun nasara. Sadiya ta share hawayen da yake xubo mata. Ta koma cikin dakinta ta juyawa Khalifa baya, yayi saurin shiga ciki ya sake tarbar fuskarta ya tambayeta.
¤
"yau ba ranar kuka ba ce a gare mu, wannan ranar farin ciki ce, rana ce ta musamman a cikin kundin tarihin rayuwarmu. Yau ne muka qyanqyashe soyayyarmu wacce ta dade a cikin kwanso. Na baki labarin xuciyata, ina son ki bani labarin dake a cikin xuciyarki."
¤
Sadiya ta ce dashi.
¤
Tun sanda naxo gidan nan, na san kana sona Khalifa, sannan kuma a kwana a tashi na san wata rana zaka fito ka fada mani. Akwai abubuwa guda biyu a cikin xuciyata wadanda na kasa gane wanne yafi cancanta in bi, idan nayi la'akari da mu'amular dake tsakanina da kai, da sauran mutanen dake gidan nan. Kun yi mani halacci, sannan kun taimaki rayuwata a lkcn da nake cikin qunci da tashin hankali, tun sanda kuka tsinceni NAYI ALQAWARIN BA ZAN TABA YI MUKU BUTULCI BA. daga ynx har xuwa lkcn da Allah Ya qaddara iyakar zamana daku."
¤
¤
DA WANNAN HUJJAR TA SADIYA KADAI MA ZAN IYA CEWA HALACCI TASO YIWA KHALIFA BA SOYAYYA BA. AMMA AMIR SOYAYYA GANGARIYA TAYI MASA.
wannan nazarin Iliyas ne.
¤
¤
"A daya 6angaren kuma gsky tuntuni gsky nayi alqawarin ba zan sake yin soyayya ba daga nan har in bar duniya. Sbd naga tashin hankali da baqin ciki, naga xullumi naga duk wani abin tsoro da furgici da masoya suke gani. Khalifa ka tambayeni abin da ba zan iya baka ba, kuma ba zan iya hana ka ba, ka tambaye ni abin da zan iya yi a domin ka, kuma abin da ba zan iya yi ba a rayuwata. Ban san ya zan yi da raina ba akan maganar daka same ni da ita, idan har ban amshi soyayyarka ba na zama cikakkiyar butulu wacce bata iya maida alheri da alheri ba, idan kuma na amshi soyayyarka na sake jefa kaina a wani qangi da na ta6a fadawa a baya. Ka bani shawara Khalifa, me ya kamata in yi?"
¤
¤
DA NI NE KHALIFA, TUN DAGA NAN ZAN HAQURA IN BAR SADIYA. SBD BA SO NE TSANTSA TAKE MASA BA, ALHERIN DA AKA YI MATA TAKE DUBAWA. DA ACE ZATA SAMU DAMAR RAMA MUSU ALHERIN SHI KENAN TA SAMU 'YANCIN YIN WATSI DA KHALIFA.
har wa yau wannan ma ra'ayin Iliyas ne.
¤
Khalifa yayi ajiyar xuciya ya ce da ita.
¤
Bai kamata ki ba wannan hukuncin ba a hannuna Sadiya, sbd ba za ta6a yi maki adalci ba, idanuna sun makance basa iya ganin komai sai ke, xuciyata bata iya ganin komai sai burin in mallake ki, ki zama matata, ta yaya kuwa zaki tambaye ni abin da yafi cancanta kiyi a tsakanin so na da kuma sa6anin haka, ko wane hali zaki shiga idan kika tambaye ni me ya dace ki yi, amsa daya kawai zan baki...ki soni!...ki so ni!! Sadiya kin ga kuwa ba zan iya yi maki adalci ba, ke dai kawai ki za6awa kanki abin da kike ganin yafi dacewa da ke, kada ki yi la'akari da halin da zan shiga a sakamakon haka.
¤
Sadiya tayi tunani na wani taqaitaccen lkc. Khalifa yana tsaye yana kallonta. Ta girgiza kai kafin ta ce.
¤
"Akwai abin da nake tsoro ne Khalifa, shi yasa har kaji na dage ina ta wasi-wasi. Na rasa abin da har abada ba zan sake samun kwatankwacinsa ba a rayuwa, na rasa Amir, na rasa abubuwa da yawa
¤
¤
Lp=18¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
18
with
Iliyas Ishak Gunduts
ix
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
Na rasa abin da har abada ba zan sake mayar da kwatankwacin sa ba a rayuwa, na rasa abubuwa da yawa, na rasa masoyina Amir, tun ranar da ya rasu na sha alwashin ba zan qara son kowa ba, nayi alqawarin ba zan sake barin xuciyata ta sanya mani burin mallakar wani namiji ba a duniya. Kaima Khalifa ka haqura bana son in mallaki kowa, bana yanke wannan hukuncin bane don ina tsammanin ko ba zan sake samun wani bane. Na yanke wannan hukuncin ne sbd ina jin tsoron kada in sake sa raina akan mallakar wani daga baya shima in xo in rasa shi kamar yadda na rasa masoyina Amir. Ba wai bana sonka bane Khalifa, ka tattara duk wani abu da zai sa mace ta soka."
¤
"To amma ina jin tsoron kada in amshi soyayyarka daga baya in rasa ka.
¤
"ki daina jin tsoro Sadiya, in dai wannan ce kawai hujjarki ki kwantar da hankalinki, ya kamata komai ya same ki a rayuwa ki dauke shi matsayin qaddara kuma ki amshe shi mai kyau ne ko mara kyau, ba shakka rasa abin da mutum yake so a xiciya masifa ce babba, a cikin masifun da Allah Ya kan jarabci bayin Sa dasu. To amma ba shi zai sa ki sakankance cewa ba zaki ta6a samun wani abin a gaba ba, don kin rasa Amir wannan ba zai zama hujjar da zaki ce ba zaki sake samun kamar shi ba. Nayi maki alqawarin zan soki fiye da yadda Amir ya soki, zan kyautata maki fiye da yadda duk wani dan adam ya ta6a kyautata maki."
¤
"Sadiya ta sake numfasawa a karo na biyu.
¤
"Shi kenan Khalifa, na amince na kar6i soyayyarka. Amma kada ka ce na 6oye maka, da wahala ka same ni a matsayin matarka, ina son ka riqe wannan a xuciyarka!"
¤
Khalifa ya ce da ita yana murmushi.
¤
na gode da kika amince dani, dama wannan shi ne kawai abin da nake son in ji daga gare ki. Sauran abin kuma da zai biyo baya sai mu barwa Allah (SWT) Shi ne kadai yake da iko kan faruwar koma. Ba lallai bane abin da kike tsoro ya zama gsky, ban san me kike 6oye mani ba, ban san abin da yake baki tsoro ba, kuma bani son ki fada mani ko menene, sannan ina son kema ki cire shi daga xuciyarki. Tsoro da fargaba ba halayen masoya bane. Duk inda masoya suke a duniya zaki same su jarumai ne, wadanda suke iya tunkarar kowacce irin matsala ba tare da jin tsoro ba. Na sadaukar da rayuwata wajen fafutikar mallakarki Sadiya, ina son kema ki sadaukar da rayuwarki, In Allah Ya yarda zamu yi nasara."
¤
Khalifa ya fita daga dakin Sadiya xuciyarsa cike da farin ciki, ya bar Sadiya wacce ta ci gaba da kuka.¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
19
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
Ba wani abu take yiwa kuka ba tuntuni sai don sanin da tayi cewar akwai igiyar auren Sarkin noma akanta, Khalifa bai san matsalar dake tattare da ita ba. To amma lkcn da zai sani ya kusa. Gara da ya sadaukar da rayuwarsa akanta don kuwa tunkarar iyayenta da zancen auren ta a halin da ake cikin ynx ba qaramin tashin hankali bane ga wanda ya sa kanshi.
¤
¤
Tun daga ranar Khalifa ya rikice ya hana kowa sukuni a cikin mutanen da yake tare dasu, maganarsa a kodayaushe bata wuce Sadiya, a makaranta....a wajen abokanshi....a gida idan ya dawo baya iya yin daqiqa daya ba tare da yana ganinta a kusa dashi ba.
¤
Hafsatu ce take tsawatawa soyayyarsu idan taga zasu wuce gona da iri. Abinci ba zasu iya ci ba sai daya yana ganin daya. Ba za a ga suna yin sukuni da walwala ba sai in suna tare.
¤
Da Hafsatu taga abin nasu yayi yawa, sai ta samu mijinta Dakta Hamza a wani dare ta ce dashi.
¤
"Lkc yayi da ya kamata mu je mu samu iyayen yarinyar na, mu kaita gida mu basu haquri mu nemarwa Khalifa aurenta, a yadda suka shaqu da juna babu abin da yafi cancanta dasu irin suyi aure."
¤
Daktta Hamza ya ce da ita.
¤
"Shi kenan ki fadiwa yarinyar ta shirya zamu je da ita muga iyayenta muyi magana dasu. Nima ina da wannan tunanin kin riga ni magana ne, idan muka je qauyen muka fahimci juna, mu da iyayenta, sai su fadi mana lkcn da suke son a yi hidimar. Ni zan dauki nauyin komai, da Khalifa da Sadiya ynx duk nawa ne, duk abin da zan yiwa Khalifa zan yiwa Sadiya. Sbd yarinya ce mai ladabi. Naji dadi da zata zamo daya daga cikinmu."
¤
Washe gari da safe bayan sun kammala karin kumallo, kowa ya tashi ya shiga dakinsa, kafin Sadiya ta gama hada farantai da kofuna, sai Hafsatu ta ce da ita.
¤
"Sadiya akwai magana mai muhimmanci da muka yi ni da Dakta akan soyayyarki da Khalifa, ya ce in fadi maki ki shirya gobe zamu je can garin ku, mu samu iyayenki muyi maganar aurenku."
¤
Sadiya ta ji gabanta ya fadi, ta kalli Hafsatu a tsorace, domin kuwa ta san akwai qatuwar matsala dake shirin faruwa.¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
page
20
with
Iliyas Ishak Gundutse
ix
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
Ta kalli Hafsatu a tsorace, ta san akwai qatuwar matsala dake shirin faruwa da ita in har suka dauketa suka mayar da ita gida. Hafsatu wacce bata san abin dake a xuciyar Sadiya ba ta matso kusa da ita, ta dafa kafadarta ta ce da ita.
¤
"Kin kusan zama cikakkiyar 'yar wannan gida Sdiya, ina so tun ynx ki san cewa duk duniya mijina bashi da wani dan uwa kwatankwacin Khalifa, kansu a hade yake suna son junan su. Ina fatan ni dake muma zamu so junanmu."
¤
maimakon Sadiya tayi farin ciki sai ta fara xubar da hawaye. Ta san Hafsatu da 'ya'yanta da mijinta duk suna son su zauna tare da ita a rayuwarsu amma matsalar tana can qauyensu, ta san da sun je can komai zai lalace, za a riqe ta a raba ta dasu.
¤
wannan kukan da take yi bana komai bane, sai na kewar bankwana dasu, tana son zama tare dasu, amma ta san dole ne ta barsu ta sake komawa rayuwarta ta farko.
¤
¤
**~**
¤
¤
Da lkcn tafiyarsu ya yi, washe gari tun da qarfe takwas na safe Hafsatu da Dakta Hamza suka shirya. Ba tare da yara zasu je ba. Alfat da Abba a gida za a barsu tare da Khalifa.
¤
Khalifa ya kasa rufe baki, murna da farin ciki suka cika xuciyarsa, yayi ta kaiwa da komowa tsakanin dakin Sadiya da da-in Hafsatu yana ganin yanayin tafiyar tasu. Sadiya jikinta a sanyaye babu wani walwala a tare da ita. Tafiyar da zasu yi qauyensu ta san kamar sake komarta cikin wani tarko ne da ta ta6a fadawa a rayuwarta.
¤
Khalifa ya ce da ita.
¤
"Idan su Anti suka dawo yau, ni kuma jibi zan xo in gaisa dasu Mama da kowa da kowa a cikin 'yan uwanki."
¤
Sadiya ta dan yi murmushi bata ce dashi komai ba, ta xuba kayanta baki daya a cikin qaton akwatinta mai taya. Ta fito da mabudin motarta ta miqawa Khalifa ta ce dashi.
¤
"Ka bar wannan mabudin a hannun ka, na motata ne."
¤
Khalifa ya dubeta cikin rashin fahimta.
¤
"Ki ta fi da abinki mana, ba wanda zai buqaceta har ki dawo, kwana nawa duka-duka zaki yi a can ki dawo. Ko kina tsammanin za a sa lkcn bikinmu yayi tsawo ne?"
¤
Sadiya ta ce dashi.
"ban sani ba, amma ka bar makullin a wajenka babu matsala.
¤
Khalifa ya amsa ya dubi kayan da ta hada su baki daya ya ce da ita.
¤
"Kina abu kamar ba zaki sake dawowa gidan nan ba, Sadiya ynx nan ne wajen zamanki can sai dai xiyara daga lkc xuwa lkc idan wani abu ya taso."
¤
Sadiya ta sake yi masa murmushi kawai. Ta dauko cek dinta na banki tana shawarar tafiya dashi ko barin shi a wajen Khalifa. Da ya fahimci haka ne ya xe da ita.
¤
"Da cek din ki ya kamata ki tafi, kin san dole ne ki buqaci wani abu kafin ki dawo, sai ki je ki cir kudin ki a wani bankin mafi kusa.
¤
Sadiya ta....¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
20~partB
¤
¤
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
Sadiya tayi ajiyar xuciya ta cusa qaramin littafincek din a cikin qaramin aljihun wata jaka ta kafada wacce ita ma ta shaqareta da kaya, tana da kudi a cikin akawun dinta sun kai dubu dari biyu, wadanda Dakta Hamza ya xuba mata kamar yadda yake xubawa kowa kudi duk bayan sati uku, don biyan buqatun su, bata ta6a ciro ko naira daya ba, sbd rayuwarta ba irin tasu bace. Bata san abin da zata yi dasu ba. Sa6ani Hafsatu da Khalifa wadanda har qorafi suke yiwa Dakta su ce ya qara tura masu kudi sun kashe wandanda suke dashi.
¤
Bayan sun firfito sun hadu a falo Khalifa yana dauke da murgujejiyar akwatin Sadiya, ita kuma Hafsata bata dauki kayan komai ba sai qaramar jakarta tunda ba kwana zasu yi a can ba. Dakta ya sa Jacket mai ruwan qasa wacce ta dace da kalar fatarshi, ya sa farin tabarau akan dogon karan hancin shi. Wannan ce shiga mafi girma da yayi wacce a tsammaninsa tafi kowacce shiga da zai yi wajen tunkarar mutanen da yake ganin mutuncin su. Musamman daya kasance ynx neman auren qaninsa za shi.
¤
Suka shiga mota, Hafsatu tana gaba tare da mijinta, a yayin da Sadiya ta zauna a baya. Khalifa wanda har suka shiga mota yana tsaye a sautin gilashin bayan motar yana magana da Sadiya, ya yi mata a sauka lfy fiye da sau maitan.
¤
Hafsatu ta leqo da kanta ta ce dashi.
¤
"Ya isa haka nan (Romeo), ka barta haka nan ta huta, sauran maganar kwa yi ta a waya idan mun tafi."
¤
Khalifa da Sadiya suka yi dariya. Dakta Hamza ya tuqa motar yayi ribas

Please Login or Register in order to submit comment