Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai wani zamani da zai xo in ce da kai ga abin da nake so, kayi mani jayayya ka ce ban isa ba? To qarya kake yi yaro. Dolene ka bi umarni na.ka qyale wannan 'yar qananun mutanen....'yar qauyen da iyayenta basu isa mu hada xuri'a dasu ba."
¤
Khalifa ya ce dashi.
¤
"Zamana a qarqashinka tun ina yaro har xuwa ynx, ba shi ne zai sa kayi imanin har abada ni ba zan ta6a zama mutum in kai ka ba. Don ina zaune a qarqashinka ba shi ne zai sa ka mayar dani bawa a rayuwa ba, haka kamar yadda kake baiwa xuciyarka abin da take so. Dole ne nima in baiwa xuciyata abin da take so. Ka sani xuciyata Sadiya take so, kuma nayi alqawarin komai wahala, komai rintsi ita ce matata."
¤
Dakta Hamza ya tasar masa kafin Hafsatu ta riqe shi ya shara masa mari, har sai da falon ya amsa kuwwar marin. Hafsatu ta dakawa mijinta tsawa cikin kuka da damuwa. Ta shiga tsakaninsa da qaninsa.
¤
Dakta Hamza ya sake nuna shi da hannu.
¤
"Qarya kake qaramin mutum. Ni ne gaba da kai, kuma har abada haka Allah Ya tsara. Ni ne zan ci gaba da zama a gaba kai kuma kana biye da ni a baya ko kana so ko baka so. Ba ka kai matsayin da za kayi sa'insa da ni ba, kuma ba zaka ta6a kaiwa wannan matakin ba qaramin yaro!"
¤
Khalifa ya ce dashi cikin qunan rai.
¤
"Taqamarka daya ce, ina zaune a gidanka kuma a qarqashinka. Bani da komai, kuma bana iya neman komai, sai kayi mini. To zan tafi garin su Sadiya, zan yi duk wani aikin wahala da 'yan uwanta suke yi, na gwammace in je in yi raywata tare dasu duk da qauyancinsu, da in zauna tare da dan uwan da ba zai iya magance mani baqin cikin xuciyata ba, wanda yake iqirarin shine wayayye dan birni."
¤
Khalifa yana gama fadar haka ya juya ya fice daga falon a fusace. Hafsatu ta garzaya ta bishi. Tana kiranshi tana kuka tana bashi haquri. Dakta Hamza ya kirata yana yi mata fada.
¤
"Ki rabu dashi (Leave him alone...let him go.) ya tafi mana....idan yana ganin ya isa ya yiwa kansa abin da bana so, ya je yayi mu gani."
¤
Hayaniyar da suke yi ce ta tayar da yaransu daga barci. Alfat da Abba suka fito, suka tsaya suna kallon mahaifinsu yana fada a falo. Khalifa ya shiga dakinsa ya dauko jakarsa ya bude ya fara xuba kayansa. Hafsat ta biyo shi tana tayi mashi magiya yayi haquri. Bai saurareta ba har xuwa sa'ar da ya gama cusa kayayyakin nasa a cikin jaka.
¤
ZAN TAFI anti, na sani baki yi mani laifin komai ba, na gode da qaunar da kika nuna mani na tsawon lkc a zamana tare dake.
¤
Hafsat ta ce dashi tana kuka.
¤
Ka tsaya Khalifa...don Allah ka tsaya muyi magana duk abin bai kaimu ga haka ba. Ka tsaya in je in samu Dakta. Kada ka tafi.
¤
Khalifa bai ko tsaya ya saurareta ba.
¤
¤
Lp=31
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
31
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan.
Madugun taska
¤
¤
Khalifa ya wuce ta bai ko tsaya ya saurari abin da take fadi masa ba. Ta sake biyo shi tana kuka, da suka fito waje ne ta tarar da Dakta Hamza, ya fusata ya biyota yana cewa da ita.
¤
"Na fadi maki ki dawo, ki rabu dashi ko? Ba ruwanki a cikin wannan magana, ki tafi daki na fada miki!"
¤
A lkcn da Hafsatu ta ja baya tana kuka ne 'ya'yanta suka fara kuka suma ganin mahaifiyarsu tana kuka. Alfat ya garzaya ya riqewa Khalifa riga yana cewa.
¤
"Abba kada ka tafi, ka tsaya Abba."
¤
Khalifa ya dafa kanshi ya ce dashi.
¤
"kayi haquri Alfat lkcn rabuwata da ku ne yayi."
¤
Ya 6an6are hannun yaron daga jikin shi yayi ficewarsa dauke da qatuwar jaka. Ko waigowa bai sake yi ba. Da fitarsa Dakta Hamza ya ce cikin qunan rai.
¤
"ba dai akan wannan yarinyar ya yi min wannan tirjiyar ba? Ki bar shi ya je ya aureta in ya isa. Zan je qauyen tare da jami'an tsaro, sai na sa an kama yarinyar da iyayenta tare da danginsu baki daya an kulle mani su. Ki rabu dashi ya koma qauyen, in dai ina raye ba zai ta6a auren wannan yarinyar ba.!"
¤
Hafsatu ta kama hannu 'ya'yanta ta rarrashe su suka yi shiru, duk da yake ita bata daina xubar da hawaye ba. Bata ta6a zaton soyayya zata iya raba dan uwa da dan uwansa ba sai a wannan rana, da soyayyar Sadiya ta raba Khalifa da dan uwansa Dakta Hamza.
¤
¤
**~**
¤
¤
Khalifa bai sha wahala wajen gane Turunkawa ba. Duk tsawon tafiya daga bakin titi xuwa qauyen a qasa yayi ta, sakamakon qarancin masu babura a ranar, kuma qarin rashin jin dadinsa shi ne, ko ya kira wayar Sadiya baya samunta, ko wane lkc wayarta a kashe take.
¤
Duk da yake da safe ya baro Abuja ya shigo motar haya, sai da kusan la'asr ya isa qauyen su Sadiya. Da xuwanshi ya tambayi gidan Mai unguwa mahaifinta, kamar yadda ta sha fadi masa cewar babanta shi ne mai unguwar qauyensu.
¤
Mutanen qauyen wadanda basu je yammaci ba, suka riqa kallon Khalifa wanda ba sai an tambaya ba, da ganin sa sun san daga maraya ya fito. Da Khalifa ya je qofar gidan ne ya samu qanana yara dake gara tayoyin babura, ya samu wani ya aika daga cikinsu ya ce dashi.
¤
"Ka je ka ce da Sadiya wai tayi baqo daga Abuja."
¤
Yaron ya garzaya da tayarshi ya shiga cikin gidan, ya samu Sadiya tana wankewa mahaifiyarta kayan sawarta.
¤
Sadiya wani yana kiran ki a waje, ya ce wai daga Abuja yake."
¤
Sadiya ta tsaya da wankin da take yi, ta ji gabanta ya fadi ras! Wani yaxo daga Abuja yana son ganinta. Nan take ta fahimci Khalifa ne. Sadiya ta dabuce. Tayi saurin dauraye hannuwanta wadanda kumfar wanki ta baibaye su. Ta ce da yaron wanda yake tsaye yana jiran amsar da zata bashi.
¤
"Ka ce dashi ina xuwa ynxn nan."
¤
Yaro ya koma ya fadiwa Khalifa saqon Sadiya, ya sake fadawa cikin sauran yaran daje guje-guje da tayoyin su. Khalifa ya dubi tsarin gidajen qauyen da korayen shuke-shuke a ko'ina. Ga kaji nan suna yawo da 'ya'yansu suna neman abinci, da kuma qananun Awaki da Tumaki wadanda basu isa daurewa ba.
¤
Sadiya ta jawo hijabinta ta fita waje, ta dafa qofa ta leqa kanta waje, taga Khalifa a tsaye ya jingina da katangar zauren, yana sanye da shudin wando da farar riga mai kwala, qatuwar jakarsa ta 'yan makaranta cike da kaya saqale a bayansa.
¤
"Khalifa."
¤
Ta kira sunansa cikin kaduwa da mamaki. Ya juyo yana murmushin farin cikin ganinta.
¤
"Na'am Sadiya."
¤
"kai ne Khalifa...ya akayi ka gane garinmu?"
¤
"Baki ta6a jin karin maganar da aka ce garin masoyi baya nisa bane?"
¤
Sadiya ta ji duk ya dora mata nauyi, ta ji duk ta kasa samun natsuwa, don kuwa yaxo ya sameta a garin su wandda ya sha ban-ban da inda yake zaune. Ya xo ya same ta a gidansu na qauye, ba irin gidan da yake zaune ba a can birni Abuja. Ta ji kunyarsa ta kama ta. Ta rasa inda zata kai shi, don kuwa tana ganin duk inda ta ce ya tsaya bata karrama shi ba. Wane irin ruwa zata debo masa ya sha?
¤
"naga kamar kin yi mamaki da gani na ko?"
¤
Sadiya tayi ajiyar xuciya.
¤
"Ba wani mamaki.....ya su Anti suka koma gida jiya?"
¤
Ya ce da ita.
¤
"Sun koma gida lfy."
¤
Sadiya ta tambayeshi da sauri.
¤
Khalifa sun san zaka xo kuwa?"
¤
Khalifa ya ce da ita.¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
32
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
¤
"Khalifa sun san zako xo kuwa?"
¤
Ya ce da ita kai tsaye.
¤
"Sun sani mana, idan ban fadi musu ba wa zan fadawa?"
¤
Sadiya ta tuno cin mutuncin da 'yan uwanta suka yi musu da suka xo, ta sake tambayar Khalifa.
¤
"Basu fada maka komai ba a game da abubuwan da suka faru?"
¤
Khalifa ya amsa mata.
¤
"Sun fada mani komai Sadiya, sun ce iyayenki sun wulaqantassu, sun sa an farfasa motar Dakta, duk abin daya faru na sani.
¤
Sadiya ta ce dashi.
¤
"Bayan ka san an yi haka kaima ka xo Khalifa? Kana nufin ka ce har ynx baka tsane ni ba? Kuma baka mance dani ba kamar yadda na tabbatar Yayanka da matarsa sun tsane ni a halin ynxn?"
¤
Khalifa ya ce
¤
"Babu dalilin da zai sa in tsane ki, sbd na san ba laifinki bane Sadiya. Idan har za a samu gidanku da wani hali, in har ke baki da wannan halin, babu wani dalili kuma da zai sa a ga laifinki in har za ayi maki adalci."
¤
Sadiya ta kalli Khalifa sosai, ta san duk abin da yake fada mata shine har cikin xuciyarsa, abin da yake nufi kenan. Bata san lkcn da hawaye ya xubo mata ba. Ta sa hannu ta share sannan ta ce.
¤
"Naji kunyarka Khalifa...kuma har ynx ina jin kunyarka. Ka nuna mini so da qauna, kuma kayi min halacci, a qarshe sakamakon da na baka ban mayar maka da alkairi ba, 'yan uwana sun wulaqanta Yayanka da matarsa. Sannan kuma nima nayi maka qarya a tarihin rayuwata da na baka. Na fada muku mijina ya sake ni a wancan lkcn farko da kuka tsinceni. Amma a zahiri abin ba haka yake ba. Gsky a wancan lkcn da aurena na gudu, duk zaman da nayi daku ina da aurena."
¤
Khalifa ya kusa faduwa daga tsaye. Ya tambayeta a rude.
¤
"kina nufin har ynx ke matar aure ce?"
¤
Sadiya ta girgiza kai.
¤
"Bani da aure ynx. Da na dawo gida jiya na samu mijina ya bar takardar saki a ajiye mini. Ynx ina cikin Idda ne, waccan Iddar da nayi a baya ba gsky bane sai na sake yin sabuwa ynx."
¤
Khalifa ya ji duniyar tayi masa nauyi ynx, don kuwa da ya dauro aniyar da yaxo zai tuntu6i iyayen Sadiya maganar aurensu. Gashi kuma sai nan da wata uku. Bai san cewar mijinta sai ynx ya saketa ba. Suka yi shiru shi da ita...suka yi jugum-jugum a bakin zauren gidan kowa yana tunani. Khalifa yayi ajiyar xuciya ya ce da ita
#
"Ba komai Sadiya, ban san haka abin yake ba, idan ba zaki damu ba zan roqe ki wata alfarma."
¤
Sadiya tayi saurin tambayarsa.
¤
"wacce irin alfarma kake so in yi maka Khalifa?"
¤
Ya ce da ita.
¤
"Ina son ki roqeni ki kaini wajen mahaifinki in roqe shi wajen zama. Na dawo nan garinku da zama ynx."
¤
¤
GASKIYA KHALIFA BUTULU NE, KUMA MARA HANGEN NESA. HAR YANA IYA BUDAR BAKI YA CE YA BARO YAYANSA SABODA BUDURWA? YAYANSA SHINE UWARSA KUMA UBANSA, SBD DUK DAWAINIYAR IYAYE DAKTA NE YAYI MASA, AMMA YA BIJIRE MASA. TABBAS IDAN HAKA NE BABU TUNANIN SAKAWA DAKTA DA IRIN GUDUNMWAR DA YAYI MASA A RAYUWA.
¤
¤
sadiya ta kalleshi a rikice.
¤
"Ban gane abin da kake nufi ba Khalifa."
¤
Ya sake maimaita mata.
¤
"Ina son in zama dan garinku, ina son in zauna tare da 'yan uwanki, ki kaini wajensu, ki roqar mani wajen kwana."
¤
Sadiya ta girgiza kai cikin jimami da rashin amincewa.
¤
Khaliffa nasan akwai wani abu da ya faru tsakaninka da Yayanka. Na san da ya koma gida ya kira ka ya gargadeka cewar ka rabu dani. Kai kuma ka nuna ba zaka iya rabuwa da ni ba, don haka kuka samu sa6ani ka bar gidan, ynx ka xo nan garinmu don ka ganni."
#
Khalifa ya ce da ita.
¤
"gsky ne Sadiya haka ne....gani naxo garinku, naxo wajenki. Ynx a duk duniyar nan ban san kowa ba sai ke. Na taso tare da Yayana, muna cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Yau wani zamani ya xo wanda zamana dashi ba zai ta6a yiwuwa ba. A da ra'ayinmu daya, muna fahimtar juna, amma ynx ra'ayinmu da fahimtarmu duk sun banbanta, ya zamo mani wani baqon mutum a rayuwa wanda ban san ko wanene ba."
¤
¤
KO KUMA KAI KA CANZA MASA BA? KAI NE BUTULU KHALIFA. YA KAMATA KA TSAYA DA DAKTA KO DON QAUNAR DA KA ZAMO SHAIDAR YANA YI MAKA.
ra'ayin Iliyas
¤
Sadiya tace dashi kai tsaye
¤
"kayi kuskure Khalifa, Dakta bai cancanci haka daga gareka ba. Ka fini sanin matsayin Dakta da kuma irin amfaanin da yake yiwa rayuwarka.
¤
¤
Lp=33¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
33
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska.
¤
¤
"Kayi kuskure Khalifa. Bai kamata ka yiwa Dakta haka ba. Ka fi ni sanin matsayin Dakta da kuma amfanin da yake yi maka a rayuwa. Idan har zaka gudu ka bar shi sbd ya hana ka soyayya da ni, gsky kayi masa butulci mai yawa. Sbd amfanin da Dakta yayi maka a duniya, ba zan ta6a yi maka koda kwatankwacinsa ba, kayi haquri ka koma ka sasanta da dan uwanka. Zamanku tare yafi soyayyarmu muhimmanci."
¤
Khalifa ya numfasa sannan ya ce da ita.
¤
"idan har zaki iya fadar wannan maganar a gabana ya nuna cewar tabbas soyayyar da nake tsammanin kina yi mini ba ta kai ko'ina ba. Ban ta6a zaton nine kawai nake sonki ba ashe ke ba kya sona ba, ban ta6a zaton zan xo garinku ki kore ni ba. Ki tuna a ynx bani da sauran masoyn da zan iya zama tare dashi a duniyar nan in samu nutsuwa sai ke kadai. Ni maraya ne bani da iyaye, bani da wurin zama. Bani da wanda zai nuna min qauna. Ke kadai nake son ki amince da ni a matsayin abokin rayuwarki....A FAHIMTA TA MAGANAR AUREN SADIYA DA KHALIFA YA LALACE, DOMIN KUWA WANNAN ZANCEN SOYAYYAR DA YAKE YI MATA TANA CIKIN IDDA YANA HANA AUREN MACE HAR ABADA BISA KOYARWAR MALAMAI MASU YAWA.....Ko da dadi ko banu dadi Sadiya, ashe dama bani da wannan matsayin a xuciyarki?q
¤
hawaye ya fara xubowa daga cikin idanunta.
¤
"kada ka ce haka Khalifa. Har abada ba zan ta6a mancewa da abin da kayi mani ba. Kai ne ka tallafa mani a lkcn da rayuwata ta fada cikin tagayyara. Kaine wanda ya dawo mini da farin cikina bayan tuni ya salwanta. Amma a dalilin xuwanka cikin rayuwata komai ya sauya a gare ni, na samu sauqi. A halin ynx da nake tsaye a gabanka Khalifa, a ynx haka wannan numfashin da nake shaqa, duk a dalilin sabuwar rayuwar da na samu ne a dominka bayan ka fitar dani daga qangin rayuwar dana fada a van baya.
¤
idan har zaka yi mini irin wannan halaccin dole ne in saka maka da wani abu da na san kaima zai amfani rayuwarka. Shi yasa nace ka koma gida ka sasanta da dan uwanka. Shi ne wanda zai yi maka abin da babu wanda zai iya yi maka irin sa a duk fadin duniyar nan. Dakta yana sonka fiye dani,,,fiye da yadda kai kanka kake son kanka. Na zauna tare daku naga komai da idanuna. Idan har ina sonka da gaske to wannan shi ne abin da ya cancanta in fada maka."
¤
¤
Lp=33 partB
is comming soon¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
33 part B
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
¤
Khalifa ya dakatar da Sadiya ya ce da ita.
¤
"idan xuciya ta kamu da ciwon son abu, babu wani sauran abu mai kyau ko mara kyau da zata gani balle har ta gani abin da ya fi cancanta tayi. Samun abin da xuciya take so shine kawai magani, Sadiya a wajenki kawai zan samu wannan maganin, naxo ki bani maganin abin da yake damun xuciyata."
¤
Tayi shiru tana tunani xuwa can ta share hawayen daya fara xubo mata ta ce dashi.
¤
"Babu wani abu da zaka xo nema wajena in hana ka Khalifa. Komai kake so a wajena zaka samu, amma ka sani ba lallai abin da kaxo nema a wajena ynx samunsa ya zama mafi alheri a gareka ba. Zan roqi iyayena su baka wajen zama a fidanmu, amma kada ka ta6a zaton zamanka a gidan nan shi ne abin da yafi dacewa kayi, idan na gama iddar da nake yi zan amshi soyayyarka, kuma zan amince ka zama mijina. Amma bayan duk wadannan abubuwan, kada ka ta6a zaton wannan hanyar da ka hau ita ya dace ka bi. Ynx ba lallai bane ka fahimci duk abubuwan da nake fada maka, amma ina da tabbacin wata rana zaka fahimci abubuwan da nake nuna maka."
¤
Khalifa yayi murmushin jin dadi ya ce da Sadiya.
¤
"Ni kuma zan tabbatar maki da cewar wannan ce hanya mafi dacewa a gare ni. Ban ta6a zaton akwai wata hanya da tafi dacewa da dan Adam ba, fiye da hanyar da zai bi wajen ceto rayuwarsa, da kuma samarwa kansa abin da xuciyarsa ke so ba....KHALIFA KAYI KUSKURE. SADIYA TAFI KA HANGEN NESA......ban ta6a yadda akwai wani jin dadi da ya wuce mutum ya zauna tare da abin da xuciyarsa ke so ba. Babu wata qasaitacciyar wahala mai azabtar da xuciya a kullum da ta wuce dan Adam ya rayu cikin rashin cimma burin abin da yake son ya mallaka a xuciyarsa.
¤
¤
**~**
¤
¤
Mallam Kalla ya dawo daga gona lkcn da rana ta daga, ya saqalo qaramar fatanyarsa a kafada, ya gunguro kekensa wanda ya dorawa ciyawar harqiya tari guda. Da yaxo zai shiga gida ne yaga khalifa a zaune kan gungume yayi masa sallama. Khalifa ya amsa yayi masa sannu da xuwa, yana qoqarin fahimtar ko wanne saurayine wannan? Ya san dai ba a cikin yaransu bane na karkarar, bai ta6a ganin Khalifa ba a garin.
¤
¤
Lp=34
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
34
with
Iliyas Ishak Gundutse
Ix
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
Da shigarsa gida bayan ya jingine keke ya shiga dakinsa, sai amarya ta debo ruwa a kofi ta durqusa ta bashi ya amsa. Bayan ta fito sai Sadiya ta shiga dakin itama ta durqusa tayi masa sannu da xuwa. Mai unguwa ya amsa sannan ya tambayeta.
¤
"Wanne yaro na gani ynxn nan a qofar gida?"
¤
Sadiya ta sunkuyar da kanta qasa ta ce da mahaifinta.
¤
"Khalifa ne, shi ne qanin Dakta wanda na zauna a wajensu, yayansa ne wanda muka xo dashi jiya."
¤
Mai unguwa ya gyara zama cikin rashin fahimta.
¤
"Shi kuma mai yaxo yi nan garin, bayan abubuwan da suka faru tsakaninmu dasu?"
¤
Sadiya ta ce da mahaifinta.
¤
"Ya samu sa6ani da yayansa ne bayan ya koma gida jiya, ya fada masa duk abubuwan da suka faru jiya, shi ne ina jin ya ce ya rabu dani, shi kuma yaqi amincewa da haka. Shi ne dalilin xuwansa, ya ce yana son a taimakeshi a bashi wajen zama, yana son ya zauna tare damu, sbd bashi da kowa a duniya sai yayansa. Iyayensu sun dade da rasuwa. Shi maraya ne."
¤
Mal. Kalla ya fahimci yadda Sadiya take jin kunyar fada masa maganar. A nan take ya gano abin dake tsakaninta da Khalifa. Duk da haka sai ya tambayeta.
¤
"A taqaice dai in na fahimceki ynx, a zaman da kika yi a gidansu kika saba dashi, ko kuma in ce kuke son juna ke dashi."
¤
Sadiya ta gyada kanta cikin kunya ba tare da tayi magana ba. Mal. Kalla ya sake gyara zama sannan ya ce da ita.
¤
"to ba komai Sadiya, wadannan mutane sun taimake ki, kuma muma sun taimakemu, sun yi abin da muka kasa yi maki a matsayinmu na iyayenki, don haka zamu riqe wannan yaron muma, zamu mayar dashi kamar dan da muka haifa a nan gidan. Za mu nuna Dafta godiyarmu ta hanyar da tafi cancanta ya gane tabbas mun ji dadin abin da suka yi maki. Bamu sani ba wataqila a sakamakon haka Dafta ya fahimcemu, ya gane muma mutane ne, bai kamata mu bari su riqa kallon mu har abada amatsayin wasu mutane wadanda basu da kyautatawa ba. Mu mutanen qauye mu aka fi sani da kara, mu aka fi sani da xumunci da nuna qaunar huna, idan har akwai hanyoyin da zamu bi mu nuna masu muna da wadannan halaye, babu shakka zamu yi shi. Don haka ki je ki shigo dashi ki ce ina son ganinshi."
¤
Sadiya ta tashi xuciyarta cike da farin ciki ta nufi qofar gida, da xuwanta ta samu khalifa a zaune.
¤
"Baba ya ce ka shigo yana son ganinka.
¤
Khalifa ya dago kansa yana murmushi.
¤
"Kin fada masa dalilin xuwana kuwa Sadiya?"
¤
Ta ce dashi.
¤
"Shine ma dalilin da yasa ya ce in shiga da kai ciki.
¤
Khalifa ya tashi ya bi Sadiya suka shiga cikin gidan, ya gaishe da mutanen da ya samu a tsakar gidan, Sadiya ta jagoranceshi suka shiga dakin mahaifinta, suka same shi yana jiran shigowarsu, Khalifa ya toge daga baya har ya durqusa zai zauna a bakin qofa Mal. Kalla ya ce dashi.
¤
"Shigo ciki mana, xo nan kusa dani."
¤
Ya nuna masa dardumar da yake sallah akanta.
¤
¤
Page 34 part B maybe continued after break meals.¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
34 part B
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
Khalifa ya gaishe da Mai unguwa cikin girmamawa. Bayan sun gama gaisawa ne sai Mal. Kalla ya ce da Shi.
¤
"Sadiya ta fada mimi ko kai wanene. Ta fada mini duk irin abin alherin da kuka yi mata. Mun gode Allah Ya saka maku da alheri."
¤
Khalifa bai ce komai ba ya na mamakin yadda mahaifin Sadiya ya karrama shi. Bayan kuma Dakta Hamza ya fada masa cewa 'yan uwanta basu san mutumci ba. Mai unguwa ya yi gyaran murya ya ce.
¤
"Na samu labarin rashin jituwarka da dan uwanka. A sakamakon irin abin da akayi musu jiya da suka xo. Na san dolene dan uwanka yayi maka gargadi da kakkausar murya akan ka qauracewa Sadiya. Wataqila ya fadi maka mu din nan bamu san mutunci ba. Kada ka ga laifin dan uwanka game duk abubuwan daya fada akanmu. Tabbas mun yi kuskure, abin da muka yiwa Dan uwanka da matarsa jiya bai dace ba."
¤
Mai unguwa ya gyara zama sannan ya ci gaba da cewa Khalifa.
¤
"Duk wadannan abubuwan da suka faru an yi su ne bisa kuskure. Ni kaina bani nan lkcn da suka xo, ina gona a wajen aiki. To ka san sha'ani idan aka ce maka an hada da mata, sune suka fara dagula wannan al'amarin. Wai suna tsammanin sace Sadiya akayi, shi ne kuma wadanda suka saceta suka dawo da ita. Kafin muxo mu iske abin dake faruwa qanina Mal. Buba da sauran yaranmu dake a nan sun yi 6an6arma da yawa. To amma daga baya shi kanshi Yayan naka mun zauna dashi mun bashi haquri akan abin da akayi masa. Su kuma wadanda suka yi wannan wautar na nuna masu rashin jin dadina, don kuwa har akwai wata Innarmu da taxo akan haka, don nace basu kyauta ba tayi fushi ta koma gida. Ban ji dadi ba, da ace muna gida ta yaya zamu bari haka ta faru?......KUN JI SHI...KAMAR BA A GABANSHI AKA RIQA TURMUZA AMIR MALAMIN SOYAYYA BA....ai ba a mayar da alheri da mugunta. Wlh ban ji dadin wannan abu ba."
¤
Khalifa ya yi ajiyar xuciya ya ce da Mai unguwa.
¤
"Na fahimci duk irin abin daya faru Baba, ni kaina na san kuskure aka samu. Nayi qoqari wajen bawa Yayana haquri, amma ya qi ya fahimceni. Ni kuma gsky Baba ina son Sadiya, ba zan iya daina sonta ba akan wannan abin daya faru. Wannan dalilin yasa muka samu sa6ani. Na bar masa gidansa na dawo zan zauna nan tare daku."
¤
Mai unguwa ya ce dashi.
¤
"Bai kamata ka 6ata da dan uwanka ba akan ya ce ka rabu da Sadiya, sbd yana da hujjar da zai ce haka, to amma zamu zauna da kai Khalifa, sai dai akwai abin da zan tunatar da kai. Ka san mu talakawa ne, kuma duk abin da zamu yi muna yin sa ne daidai da tunaninmu na mutanen dake qauye. Bamu da wata sana'a da ta wuce noma da kiwo, wadannan sune abubuwan da muka gada tun kaka da kakanninmu, gashi kuma kai mutumin maraya ne, baka saba da yin rayuwa irin tamu ba.
¤
Khalifa yayi murmushi.
¤
"Baba zan iya yin duk abin da kuke yi a nan, kuma zan iya zama tare daku, in dai kun amince mani in zauna.
¤
Mal. Kalla ya ce dashi.
¤
"Sai abu na biyu, kaga ynx Sadiya tana cikin Idda ne, bata gama ba, kada ku riqa shigewa juna da maganganu, wadanda suka shafi alaqar dake tsakaninku, a bari har sai lkcn da ta gama Iddarta. Na maka alqawarin zan baka Sadiya! Kuma zan sasanta ka da kai da dan uwanka. Wannan shi ne abin da zan yi in nuna muku godiyata akan abin da kuka yiwa Sadiya.
¤
Khalifa ya ci gaba da murmushi, bai san da abin da zai kwatanta jin dadinsa da wannan maganar ba.
¤
A qarshe Mal. Kalla ya ce dashi.
¤
"Ka jira yaranmu su dawo daga gona mu hadaka dasu. Ina ganin Baballe shi kadai ne a dakinsa dake a waje, sai ka kai kayanka ku zauna tare, ka saki jikinka da kowa, daga yau ka zama dan cikin gidan nan."
¤
Khalifa yayi wa Mai unguwa gdy, har yana xubar da qwalla. Suna nan a zaune aka turo wata yarinya ta kawo abinci a kwano. Har Khalifa zai fita Mai unguwa ya dakatar dashi.
¤
"Yau sai

Please Login or Register in order to submit comment