Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa rudewa da rashin dawowar Khalifa. Ta neme shi a waya, kullum ba dare ba rana. Amma bata same shi ba. Duk layikansa a rufe suke. Ta san indai qalau babu yadda za a yi Khalifa ya je gida yayi zamansa ya qi dawowa har a kawo wannan lkc, gashi ranar daurin auren taxo.
.
Ta kasa samun sukuni a xuciyarta.SADIYA
Page 62
.
.
.
Ta kasa samun sukuni a xuciyarta kuka kullum. Idan ta kwanta a daki kuwa sai ta shiga neman lambar masoyinta. Ta san ba zata same shi ba, amma duk da haka ta kasa yin haquri ta jure, sai cajin wayarta ya qare. Ganin wannan al'amari ya qara dugunxuma xuciyar Mai unguwa tare da dukanin jama'ar gidan.
.
Bisa haka ne yasa a wani ganawa da Mai unguwa suka yi shi da amininsa Liman tare da qanin sa Mal. Buba. Sai ya bijiro da buqatarsa ta bin sawun Khalifa can birni gidan dan uwansa domin bin ba'asin dalilin da ya hana Khalifa komawa alhalin ya san da ranar daurin aure a Bisa haka ne yasa a wani ganawa da Mai unguwa suka yi shi da amininsa Liman tare da qanin sa Mal. Buba. Sai ya bijiro da buqatarsa ta bin sawun Khalifa can birni gidan dan uwansa domin bin ba'asin dalilin da ya hana Khalifa komawa alhalin ya san da ranar daurin aure a tsaye.
.
Suma dai shawarar da suka bashi kenan, cewar tunda dama tare suka so a yi tafiyar amma shi Khalifa ya canza salon tafiyar, to babu shakka ya kamata su bi sawu.
.
.
**
.
.
Kwana uku kenan Khalifa yana gidan mahaukata. Tunda aka kai shi gidan bai yi magana da kowa ba. Ma'aikatan dake shigowa lkc-lkc su duba marasa lafiyan, basu tsayawa. Idan sun duba kowanne daki sun tabbatar kowa yana nan ba wanda ya gudu sai su yi tafiyarsu..
.
Ma'aikatan dake cike da gidan sun riga sun saba, duk sanda suka ga wani daga cikin ma'aikatan ya shigo, sai su riqa miqo hannu suna son su ta6a su. Ba wani ma'aikaci da yake tsayawa kula mahaukatan idan ya shigo.
.
Wannan ne dalilin da yasa duk lkcn da wani ma'aikaci ya shigo sai Khalifa ya taso da sauri ya miqo masa hannu yana cewa.
.
"Ni ba mahaukaci bane.....ku xo ku gwada ni ku gani. Wlh lfyta qalau. Ni ba mahaukaci bane!"
.
Ba wanda ke tsayawa ya kalle shi, sbd akwai mahaukata da yawa da suke fadar haka idan sun ga ma'aikatan, amma kuma qarya suke yi, haukar suke yi aka kawo su asibitin.
.
Ko an kawowa Khalifa abinci baya iya ci. Tunasninsa a kodayaushe yana kan Sadiya. Ya tabbatar tana can tana kuka, kamar yadda shima yake nan yana kuka. Da ace wani zai taimakeshi ya saurare shi cikin ma'aikatan dake a asibitin, da ya roqe shi da yaje ya fadiwa masoyiyarshi Sadiya halin da yake ciki. Don kada ta zargeshi da laifin ya gudu ne ya barta....ya fasa aurenta.
.
To amma kuma a asibitin kowa yayi tsammanin Khalifa shima mahaukacin gaske ne. Babban Likitan asibitin ne kawai ya san gskyr abin dake faruwa. Shi kan sa yana tausayawa Khalifa, to amma ba zai iya yiwa Dakta Hamza jayayya ba a bisa wannan taimako da ya nema a wajensa. A kwana ukun da Khalifa yayi a asibitin sau biyu Dakta Hamza yana xuwa, amma bai iya xuwa dakin da Khalifa yake ya ganshi ba. Iyakarsa ofishin babban LikitanTo amma kuma a asibitin kowa yayi tsammanin Khalifa shima mahaukacin gaske ne. Babban Likitan asibitin ne kawai ya san gskyr abin dake faruwa. Shi kan sa yana tausayawa Khalifa, to amma ba zai iya yiwa Dakta Hamza jayayya ba a bisa wannan taimako da ya nema a wajensa. A kwana ukun da Khalifa yayi a asibitin sau biyu Dakta Hamza yana xuwa, amma bai iya xuwa dakin da Khalifa yake ya ganshi ba. Iyakarsa ofishin babban Likitan.
.
Da yaxo ne a xuwan farko Likitan ya sanar dashi yadda Khalifa ya lalata kayayyakin da aka xuba masa a dakinsa. Kai tsaye Dakta Hamza ya bayar da kudi ya ce a sake xuba masa sababbi. Sannan ya ce a tabbatar ana ba Khalifa irin abincin da yake so. Ko mene ne.
.
Babu wani abin jin dadi da za a yiwa Khalifa ya kwantar da hankalinsa a asibitin. Kullum bashi da wani aiki da ya wuce yiwa mutanen da suke shigewa magiya, yana cewa su taimake shi su bude masa qofa shi ba mahaukaci bane. Ya qosa ya fito ya je yaga Sadiya..... Ya qosa ya je su ga juna. Ya qosa ya je ya sake sauraren muryarta.
.
Idan mutanen da yake roqo su xo su bude masa qofa, suka tafi suka bar shi sai ya fashe da kuka.....sai ya fadi qasa ya kwanta a bakin qofar. Yana fatan samun wanda zai xo ya bude shi wata rana.
.
.
.
**
.
.
Washe gari tun da safe motar da zata kai su Mai unguwa Abuja ta shigo Turunkawa. Dama sun shirya direba suke zaman jira tun fitowa sallah. Masu tafiyar sun kai su shida. Bayan Mai unguwa da Mal. Buba da Liman, akwai Mal. Mamuda da Mal. Sunusi da kuma Alaramma Mal. Wada.
.
Kafin su shiga mota ne Mai unguwa ya shiga cikin gida ya kira Sadiya ta xo dakinsa, tun kafin ta durqusa ya ce da ita.
.
"Ga motar can ta xo zamu tafi, ki rubuta mana adireshin unguwar da sunan layin, da kuma duk inda zamu bi idan mun je, direba ya riqe a hannunsa.
.
Sadiya ta ce da mahaifinta.
.
"To, Baba bari in je daki in rubuto in kawo maka."
.
Ta koma daki da sauri ta dauki takarda da biro ta rubuto musu sunan unguwar, da sunan Dakta Hamza da inda zasu fara xuwa idan sun je Abuja. Ta kawowa mahaifinta ta miqa masa. Ya amsa ya ce Ta koma daki da sauri ta dauki takarda da biro ta rubuto musu sunan unguwar, da sunan Dakta Hamza da inda zasu fara xuwa idan sun je Abuja. Ta kawowa mahaifinta ta miqa masa. Ya amsa ya ce da ita.
.
"To Sadiya za mu je, sai mun dawo."
.
Sadiya ta ce da mahaifinta.
.
"Allah Ya kai ku lfy Ya dawo daku lfy."
.
Ta yi sauri ta koma dakinta don kada ta 6ata masa lkc.....ta qosa su yi sauri su tafi....su yi sauri su je su dawo mata da masoyinta Khalifa.SADIYA
Page 63
.
.
.
Ta qosa suyi sauri su tafi....su yi sauri sauri su je su dawo mata da saurayinta Khalifa.
.
Mai unguwa ya fita ya samu abokan tafiyarsa, suka shiga mota. Mutanen garin wadanda suka taru a gaban motar, suka yi musu addu'ar sauka lfy, da kuma addu'ar dawowa gida lfy, kowa yana cewa idan sun je su fadiwa Khalifa suna gaishe shi. Kuma don Allah ya dawo. Sbd ya barsu cikin kewar rabuwa. Direba ya ja motar suka tafi. Suka dauki hanya. Sai da suka yi awa hudu a hanya suna tafiya sannan suka shiga cikin birnin tarayya Abuja.
.
Basu sha wahalar gane gidan Dakta Hamza ba, kamar yadda Sadiya ta rubuta musu a takarda. Da tambaya tambaya aka nuna masu katafaren gidansa akan babban layinsu dake da qarancin mutane da ababen hawa. Da misalin qarfe tara da minti goma suka isa bakin qofar gidan. Direban ya kashe motar suka fir-fito.
.
Duk a cikin dattawan da suka yiwo tafiyar babu wanda ya ta6a xuwa Abuja, suna dai ganinta a hotuna. Kuma sna samun labarinta a wajen mutanen dake xuwa neman kudi. Da fitowarsu suka fara mayar da hankulansu akan dogayen gine-ginen da suka gani, kamar tsuntsaye suka hau kai suka gina ba mutane ba.
.
Mal. Mamuda ya daga kan shi ya nuna wani dogon qarfe da ya tafi cikin sararin samaniya ba a ganin iyakarsa. Ya yi salati ya ce.
.
"Ynx wancan qarfen mutum ya ta6a hawa kan "Ynx wancan qarfen mutum ya ta6a hawa kan shi?"
.
Direban da ya kai su ya ce dashi.
.
"Qwarai kuwa, mutane ke hawa kanshi su yi gyara idan wani abu ya lalace."
.
Mal. Buba ya bude baki ya ce.
.
"Lallai Yahudu da nasara sai dai a barsu da sha'aninsu."
.
Mai unguwa ya hango wasu motoci da suke tafiya akan wani bene na wani kamfani, ya riqe baki ya tambayi direban.
.
"Su wadancan motocin da suke tafiya akan gida, ba a tsoron su fado? Wannan ai sayar da rai ne da gangan."
.
Direban ya yi dariya ya ce.
.
"Ai titi ne a wajen, ba zasu fado ba."
.
Alaramma Mal. Wada yayi farat ya ce.
.
"Titi akan gida Mallam? Ta yaya aka yi shi?"
.
Mal. Sunusi ya lura da wasu ciyayi dake malale a jikin katangar tsakar gidan Dakta Hamza. Ya kasa yin haquri ya je ya ta6a su. Ya ji su da taushi har da 'yar laimar ruwa a jikin ganyayen, ya ce da sauran mutanen.
.
"Jama'a kun ga ikon Allah, ga rana ana yi ba ruwa ba ra6a amma ciyawa sharkaf da laima. To wannan nometa ake yi ko kuwa ya ake yi mata?"Jama'a kun ga ikon Allah, ga rana ana yi ba ruwa ba ra6a amma ciyawa sharkaf da laima. To wannan nometa ake yi ko kuwa ya ake yi mata?"
.
A dai-dai lkcn da suke ta xuba wannan tadin suna dararraku, a lkcn ne Dakta Hamza ya fito daga cikin gidan sanye da gajeren wando da singileti. Ya fito motsa jiki ne ya ji ana ta yi masa surutu a qofar gida. Ya tsaya yana kallon mutanen cikin mamaki ko su wanene haka duk a yamushe dasu. Basu ji fitowarsa ba sai da ya daga murya cikin fushi ya ce dasu.
.
"Kai ku su wane ne? Me kuka xo nema a nan kuka tarar mani a qofar gida?"
.
Mai unguwa da sauran mutanen suka mayar da hankalinsu akan Dakta Hamza. Ba wanda ya gane shi ne mutumin da yaxo qauyensu a watannin baya da suka dawo da Sadiya gida shi da matarsa. Ganinsa da suka yi da gajeren wando da singileti sun dauka Mai gadi ne. Mal. Buba ya ce dashi.
.
"Kai shiga ka yi mana sallama da Maigidan, ka ce yayi baqi daga qauye."
.
Dakta Hamza ya dube su nan take ya gane mutanen garin su Sadiya ne. Ya ji wani abu ya taso ya tsaya masa a wuya. Ya nuna musu yatsa ya ce.....
.SADIYA
Page 64
.
.
.
Dakta Hamza ya dube su da kyau, nan take ya gane mutanen garin su Sadiya ne. Ya ji wani abu ya taso ya tsaya masa a wuya. Ya nuna musu yatsa ya ce.
.
"Dama ku ne? Kun dauke mani qanina kun 6oye shi. Shi ne ynx kuka sake biyo shi kun dauka yana nan ko?"
.
Su Liman da Mai unguwa suka kalli juna.
.
"A'aha!!"
.
Mai unguwa ya ce cikin mamaki.
.
"Ashe kai ne Yalla6ai, ai bamu gane ka bane, a yi haquri. Mune iyayen Sadiya dake a qauyen Turunkawa."
.
Dakta Hamza ya ce dasu.
.
"Na gane ku ai Malam. To ya akayi kuma? Me kuka xo yi gidana, na aika ne nace ku xo? Ko kuwa yau ma kun biyo ni ne har gida kuyi min qauyancin da kuka saba?"
.
Mal. Mamuda ya ce dashi.
.
"Haba bawan Allah. Ko da muka xo daga qauye ai ka daure ka bamu wurin zama ko baka so xuwanmu ba. Ka duba awoyin da muka yi a mota mana kafin muxo nan."
.
Dakta Hamza ya juya kan shi.
.
"Kai Malam me ke tafe daku? Iyakar abin da nake son ku fada mani kenan. I don't have a time for all this nonsense. I want go to my work right now ok!"
.
Da Mai unguwa yaga mutumin yana neman ya ja su da rigima ne sai ya ce dashi.
.
"Mun xo wajen qaninka Khalifa ne. Yau kwanansa hudu da tahowa, shi ne muka xo mu ji ko lfy shiru bai koma "Mun xo wajen qaninka Khalifa ne. Yau kwanansa hudu da tahowa, shi ne muka xo mu ji ko lfy shiru bai koma ba?"
.
Dakta Hamza ya dubi Mai unguwa har cikin idonsa ya ce.
.
"Khalifa ya mutu yau kwana uku kenan."
.
Dattawan suka dauki salati baki daya. Wadansu suka dafe kai. Liman ya dubi Dakta Hamza.
.
"Amma yalla6ai shi ne ba a aika mana mu xo ba? Khalifa ya rasu amma ba a aika mana ba sai da muka biyo sawu?"
.
Dakta Hamza ya ce dasu cikin tsawa.
.
"Su wanene sanadiyyar mutuwarsa in ba ku ba? Ya dawo yana tafiya mota ta buge shi a bakin titi. Tunani yake yi. Wa ya jefa shi a cikin tunanin in baku ba? To ya mutu hankalinku ya kwanta, sai ku je ku koma kuyi (cellabration)".
.
Mai unguwa ya fara fashewa da kuka ya ce.
.
"Allah Sarki Khalifa. Ni dama na san in dai lfy-lfy ba zai qi komawa. Allah Ya jiqan Khalfa rayuwa kenan!!"
.
Liman ya ce.
.
"Qasa ta kira shi ya dawo. Ashe a nan turakarsa take ba a can ba. Allah Ya sa ya huta."
.
Mal. Buba ya fara kuka shima ya ce.
.
"To a ina ake zaman makokin muje muyi gaisuwa ganin har an yi sadakar uku "To a ina ake zaman makokin muje muyi gaisuwa ganin har an yi sadakar uku yau?"
.
Dakta Hamza ya dasu.
.
"Ku jirani in shiga gida in dauko bindiga, in kun isa ku tsaya in fito."
.
Ya koma cikin gidansa da sauri kamar da gaske. Alaramma Mal. Wada ya fara ankarar dasu Ya koma cikin gidansa da sauri kamar da gaske. Alaramma Mal. Wada ya fara ankarar dasu ya ce.
.
"kuna ji fa bindiga zai dauko, ku xo mu tafi wannan mutumin ba kirki gare shi ba."
.
Ko wannensu ya fara rige-rigen shiga motar. Direban wanda dama tuni yana ciki, ya tashi motar ya fuxgeta suka sheqa a guje. Dakta Hamza wanda ke 6oye daga cikin gidan yana kallon su ya fashe da dariya....."No body will find out the for Ko wannensu ya fara rige-rigen shiga motar. Direban wanda dama tuni yana ciki, ya tashi motar ya fuxgeta suka sheqa a guje. Dakta Hamza wanda ke 6oye daga cikin gidan yana kallon su ya fashe da dariya....."No body will find out the for ever."
.
Ya ce cikin daga murya.
.
Su Mai unguwa suka koma gida sharaf-sharaf da hawaye, da isar su suka fara fadawa mutane labarin mutuwar Khalifa. Garin ya rude da koke-koke, mutane suka rude, yara da manya babu wanda yake lallashin wani. A gidan Mai unguwa abin yafi tsananta sbd Khalifa ya zama dan cikin gida, kowa ya saba dashi. Da aka xo da labarin mutuwarshi, kowa Sadiya ya tsurawa idanu a cikin xullimi, kowa yana tsammanin zata fadi ta suma nan take. Wadansu kuma suna tsammanin idan ta fara kuka, zata dadai tana yi bata daina ba.
.
Sadiya bata yi duk wadannan abubuwan ba. Bata yi kuka ba, xuciyarta ta qeqashe. Tunannta ya daburce. Ta zauna tayi shiru ko qiftawa bata yi. Kishiyar mahaifiyarta taxo ta sameta tana bata haquri.
.
"Ki sanyawa xuciyarki dangana Sadiya. Duk mai rai mamaci ne. Kada ki sa kanki a cikin tashin hankali. Khalifa ba zai dawo ba sai dai kiyi masa addu'a."
.
Sadiya tayi murmushi wanda ya tsorata kishiyar mahaifiyarta. Tayi ajiyar xuciya ta ce.
.
"Mama ni na san Khalifa bai mutu ba, yana nan a raye a duniya. Da ace Khalifa ya mutu da gaske to da tun kafin ma a xo a fadi min, jikina ne zai fara fadi mani, xuciyata zata fara ankarar da ni. Khalifa yana nan a raye a duniya."
.
Matar dake sauraren Sadiya ta dubeta a kidime.
.
"Su Mai unguwa mahaifanki su xo da maganar ki ce baki yarda ba Sadiya? Da bai mutu ba za a ce ya mutu ne?"
.
Sadiya ta ce da ita.
.
"Mama na san an raba ni da Khalifa har abda. Na san yayi mani nisa, kuma da wahala mu qara haduwa. Amma ban yarda ya mutu ba. Idan akwai sauran haduwa wata qila a wani zamanin wani ya ganshi a wani garin yana rayuwarsa. Wata qila nima kafin in mutu in sake ganin shi. Zai iya kasancewa nan da shekaru goma ko ashirin. Wata qila ma sai mun tsufa mu duka ni dashi. To amma ko ma yaushe zamu kai inda rayuwa zamu sake ganawa, amma Khalifa bai mutu ba."
.
Sadiya ta fara xubar da hawaye a karon farko, tun sanda aka xo da labarin. Ta ce da kishiyar mahaifiyarta.
.
"Ni dama na san aurena da Khalifa abu ne mai wahala, sbd dan uwansa babban mutum ne, kuma zai iya yin komai a duniya, don ganin ya raba mu ni da Khalifa. Ban san ko wane hali Khalifa yake ciki ba ynx. Ina.....
SADIYA
Page 65
.
.
.
KAMMALAWA.
.
.
Ban san ko a wane hali yake ciki ba a ynx. Ina roqon Allah Ya kare shi a duk inda yake. Allah Ya hada shi da wata macen wacce ta fini son shi. Ina yi masa fatan alheri da zaman lfy har qarshen rayuwarsa."
.
Sai a lkcn Sadiya ta fashe da kuka.
.
.
.
***
.
.
Khalifa ya fara sabawa da rayuwarsa a gidan mahaukata. Ana kawo masa litattafan da yake so na karatu. Amma an hana kowa ya saba dashi a cikin ma'aikatan da ke kula da mahaukatan. Ya kai wata daya. Da ya tabbatar ya rasa Sadiya a duniya, sai ya gwammace ya yi ta yin rayuwa tare da mahaukatan har qarshen rayuwarsa. Ya qudurce a ransa ko yayansa ya sa a fito dashi ba zai fito ba.
.
Burin kowanne dan adam shi ne ya samu abin da yake so a rayuwarsa ta ainahi, me zai yi tunda ya san ynx iyayen Sadiya sun sake mata miji tunda shi ya qi dawowa? Wata qila ma ynx tayi aure. Don haka ynx bashi da wani sauran buri da ya rage masa a duniya. Babu sauran wani abu ynx da yake so ya samu.
.
A cikin watan shi na biyu ne da kawo shi gidan mahaukatan a cikin wani dare ya dauko takarda da biro ya fara rubuta duk wasu abubuwa da suka faru dashi a tsakaninsa da Sadiya da kuma dan uwansa. Yana fatan wata rana ko bashi a raye wani zai tsinci takardar, wata qila duniya ta samu labarin soyayyarsa da Sadiya. Inda rai da rabo, babu mamaki labarin ya je kunnen Sadiya ta fagimci gskyr abin da ya faru dashi. Ko bashi a raye ta san dai bai guje ta ba, kuma bai ci amanarta ba. Khalifa ya fara rubutunsa.....hawaye suka fara sartu a cikin idanunsa suna diga bisa farar takardar da ya tasa a gabansa.
.
.
......."SUNA NA KHALIFA. Kuma ina son ko bayan bani a raye duk wanda ya tsinci wannan takardar ya san cewar ni fa ba mahaukaci bane. An kawo ni wannan gidan ne an 6oye ni, an yi haka ne kawai don a raba ni da wata masoyiya tawa mai suna Sadiya, wacce nake sonta fiye da komai a duniya. Wacce dan uwana shi kuma yake qinta fiye da komai a rayuwarsa.
.
Na san a lkcn da wannan takardar zata bayyana wataqila na dade da mutuwa! Ina fatan duk wanda ya tsinci wannan takardar ya samu marubuta labarun soyayya ya basu takardar su karanta. Ina so marubuta su yada wannan labarin, suyi ta rubutu akan soyayyarmu ni da Sadiya. Na san ta haka idan nayi sa'a wata qila saqon zai isa gare ta. Na rabu da Sadiya a lkcn da take sa ran zan sake komawa gare ta...a lkcn da take da tabbacin ba zan gujeta ba.
.
Gashi na tafi ban dawo ba. Na san Sadiya tayi kuka mai yawa, kuma ta daukeni a matsayin masoyin qarya, wanda ya kasa cika mata alqawarin daya daukar mata. Mutanen da zasu samu wannan labarin zasu cika da takaicin yadda bamu cimma burinmu ba. To amma wannan dabi'ar soyayyar gsky ce. Fata na shi ne Sadiya ta samu kwanciyar hankali, ta samu wanda zai kula da ita ya yi mata adalci a rayuwarta. Ko bani a raye in har zata samu wani masoyin wanda ya fi ni, to nayi nasara kuma na cimma buri Gashi na tafi ban dawo ba. Na san Sadiya tayi kuka mai yawa, kuma ta daukeni a matsayin masoyin qarya, wanda ya kasa cika mata alqawarin daya daukar mata. Mutanen da zasu samu wannan labarin zasu cika da takaicin yadda bamu cimma burinmu ba. To amma wannan dabi'ar soyayyar gsky ce. Fata na shi ne Sadiya ta samu kwanciyar hankali, ta samu wanda zai kula da ita ya yi mata adalci a rayuwarta. Ko bani a raye in har zata samu wani masoyin wanda ya fi ni, to nayi nasara kuma na cimma buri na.
.
Inda rabo kuma wa ya sani ko mu sake haduwa da ita wata rana? Ban san ko sai yaushe zamu sake haduwa ba. To amma abin da zan tabbatarwa duniya shi ne, in har ina raye SADIYA nake so komai wahala ba zan canza ta ba. In har ni da ita muna Inda rabo kuma wa ya sani ko mu sake haduwa da ita wata rana? Ban san ko sai yaushe zamu sake haduwa ba. To amma abin da zan tabbatarwa duniya shi ne, in har ina raye SADIYA nake so komai wahala ba zan canza ta ba. In har ni da ita muna raye....
.
Soyayyarmu zata ci gaba da rayuwa. Wannan qauna daga Allah ce. Wannan SO NE HAR ABADA.
.
.
QARSHE.
.
SO HAR ABADA shi ne littafin dake qunshe da ci gaban labarin, sai dai kash! Har ynx littafin yana wurin aiki bai fita kasuwa ba. Muna baku haquri bisa rashin samun qarshen labarin a dunquSO HAR ABADA shi ne littafin dake qunshe da ci gaban labarin, sai dai kash! Har ynx littafin yana wurin aiki bai fita kasuwa ba. Muna baku haquri bisa rashin samun qarshen labarin a dunqule.
Naku
Iliyas Ishak Gundutse
.
Ke maku adabo a cikin wannan labarin sai mun hadu a daya cikin wadannan biyun.
(1)YARO BAI SAN WUTA BA....
(2) MUGUN ALBISHIR.
Na sadaukar da littafin ga kafatanin masoya GIDAN LITTAFI tare da mai gida SHAFI'U DAUDA GIWA.
Allah Ya bar qauna.
.
Har wayau na sadaukar da littafin gare ki sanyin idaniya burin rainaHar wayau na sadaukar da littafin gare ki sanyin idaniya burin raina.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment