Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wayau.SADIYA page 46
.
.
.
Ku har ynx baku da wayau, baku san inda kanku yake ciwo ba. Haka kawai ku dauki aure ku ba dan birni, ya tafi da yarinya wata uwa duniya, idan ma yankata zai yi baku sani ba, shi yasa dama na ce da Balalle ya fada maku ku jira ni komin dare zan xo. Ba zan yarda akai Sadiya wani Birni ba, ga yaranmu nan a gida jarumai a tsallake su a kai yarinya dawa. Buhu nawa yake nomawa a shekara? Kun san ba su xuwa gona, sai qaryar banza da doro, amma ko qwaryar hatsi basu iya nomawa a shekara."
.
Mal. Kalla ya ji jikinsa yayi sanyi. Matsalar da suke tsoro kenan, aqi fada mata sha'ani ta xo ta shiga tsinewa mutane. A fada mata kuma ta ce bata yarda ba. Ya ce da ita.
.
"Inna in haka ne sai a fada masa in ya amince zai zauna a nan tare damu sai a bashi ita, tunda yana son ta ita ma tana son shi.
.
Tsohuwar ta kumbura fuska ta ce.
.
"Ni shi yasa bana iya zama a nan, sbd ba zan iya tsayawa ina kallon irin wannan lalacewar da kuka bar yaranku suka yi ba. Kullum idsn naxo garin nan sai an ce min Gaje ki baro Kufen kaura ki dawo gida, ina son zaman nan din, amma dole nake yin haquri in zauna a can. Ynx kamar Sadiya har sai ta ga wani da take so? Aure wai ba zaku yiwa yarinya aure ba sai ta ce ga wanda take so? Kun saki yaranku sun 6aci da rashin kunyar banza. Mu a zamaninmu game da aure yaushe yarinya ta isa a ji bakinta? Komai manya suke yi. Har aka yi mani aure ban ta6a ganin irin fuskar Tanko ba. Kai mun fi wata daya a dakin aure, amma in kashe ni za a yi ba zan ce ga irin fuskarsa ba. A haka muka haifi 'ya'ya bakwai kafin ya rasu. Kuma da wuya ka ji aure ya mutu a lkcn mu. Ba kotu, a ina ma za a ga kotu? Amma ynx da ka je kotu kaffin gari ya waye zaka ga yaran mata qanana sun xo kawo qara a raba aure iyayensu suna kallo sun qyale su. Wannan lalacewa da me za a kwatanta?"
.
Mai unguwa ya lallasheta ya ce.
.
"To Inna kin san zamani ne ya canza, in ba a tuntu6i yaran an ji wanda suke so ba, ko an yi auren ba zaman lafiya suke yi ba, idanun yara ynx sun bude, basu son auren dole, shi yasa muke basu dama kowa ya za6i wacce yake so don a zauna lfy.".
.
Inna Gaje ta tasowa Mai unguwa da fada.
.
"Kai bana son zancen banza ka ji ko Kalla? Ana maganar auren zaka ce sai an tambayi yarinya wanda take so sannan zata zauna a daki. Ni ku barni da duk wata shedaniya, ban ce ku tambaye su ba, ku basu duk wanda kuke so, in ji shedaniyar da za a ce ga wani iya shege da take yi a daki, ku bar ni in je in gauraya ni da ita
SADIYA page 45
.
.
Khalifa dake a baya ya ja rigar Balalle cikin rada ya ce dashi.
.
"balalle zo mu koma tukunna, idan ta haqura in anjima sai mu dawo."
.
Balalle ya juya shima cikin rada ya ce da Khalifa.
.
"Ai a irin wannan lkcn tafi sauqin sha'ani Khalifa. A haka din nan shi ne lkcn haqurinta, idan aka jima rana ta yi, to babu wanda yake iya xuwa inda take."
.
Khalifa yayi ajiyar xuciya. Balalle ya ce da Inna Gaje.
.
"bari mu shigo dama mun xo gaishe ki ne, ni da Khalifa wanda zai auri Sadiya."
.
Ya ja hannun Khalifa suka shiga cikin dakin, suka yi saurin durqusawa sbd hayaqin dake cunkushe a dakin. I qa'ida idan mutum zai shiga dakin tsohuwar to tun daga qofa zai rage tsayi, in fa mutum yana so ya fita lfy kada ya sha zagi ta uwa ta uba.
.
Tsohuwar ta bude idanunta dake tsiyayar da hawaye sbd zafin hayaqi, ta kalli samarin biyu dake durqushe a gabanta. Khalifa yana sanye da dogayen kaya da hula. Gargadin da Balalle yayi masa kenan a jiya, ya ce dashi. Akan rashin hula kawai maganar aurensa da Sadiya zata iya watsewa a gaban Inna Gaje.
.
Khalifa ya fara gaishe ta.
.
"Ina kwana Inna?"
.
Ta kawar da kanta gefe gefe guda ba tare da ta amsa masa ba. Balalle ya sake yiwa Khalifa rada a kunne ya ce dashi cikin sauri.
.
"kada ka damu ba fushi take yi da kai ba, ka san idan suriki yayi magana wasu ba su amsawa a nan, kunyarka take ji, ka yi shiru kada ka sake yin magana, ka duqar da kanka kada ka riqa yarda kuna hada ido."
.
Khalifa yayi saurin sauke kansa qasa yayi hiru. Balalle ya gaisheta.
.
"Ina kwana Inna?"
ta juya a fadace.
"lfy lau."
"Ya gajiyar hanya?"
"Gajiya ta bi lfy."
.
"dama na rako Khalifa ne....ke kadaice dama bai sani ba a cikin 'yan uwa. Shi ne su Baba suka ce ya xo ya gaishe ki."
.
Sai a lkcn tsohuwar tayi masa magana. Ta ce.
.
"kai na nan ne ko kuwa a nesa kake?"
.
Har Khalifa ya bude baki zai yi magana, sai Balalle yayi sauri ya mintsile shi a qafa ya yi masa inkiya da yayi shiru, balalle ya bata amsa da cewa.
.
"A'a, a birni yake Inna. Amma ynx ya zama dan nan. Tunda a nan muke tare dashi, mun zama daya."
.
Inna Gaje ta sake tambaya.
.
To an ce bai kai shekara daya da xuwa nan din ba. Ya yi noman ne an ga abin daya samu? Ko kuwa a haka da xuwan shi za a bashi auren bashi da abin da zai ci da matar?"
.
Balalle ya ce da tsohuwar.
.
"Ai yayi karatu Inna. Idan an yi auren sai su koma can birni da zama. Kin ga zai sami aijin Gwamnati ya riqa daukar albashi duk wata....."
.
Kamar Balalle ya watsawa tsohuwar wuta. Yana gama fadar haka ta tasar masa da zagi, sai da ya ja da baya har suna yin karo da Khalifa.
.SADIYA page 46
.
.
.
Yana gama fadar haka ta tasar masa da zagi, sai da ya ja da baya, a garin haka har suna yin karo da Khalifa.
.
"Qaniyarka Balalle, sakarai dan jakin uba. Kai ma ashe ka lalace ka zama dan iska ban sani ba? Ana maganar arziqi shi ne zaka riqa kawowa mutane tadin wani Birni da Gwamnati? Don ubanka Sadiyar ce za a dauka a kai ta birni? To sai dai in bani a raye. Ko a da da ta zauna a birni a wajen Uwani, ai ba yadda na sani ba. Da na san birnin da kaina zan je in dawo da ita. Don haka ba zan yadda ba. Duk wanda zai auri yaranmu to ya zauna a nan yayi noma mu gani. Ba wanda zai dauki yarinya daga nan ya tafi da ita can wata uwa duniya, ya je ya sayar da ita a fille mata kai a banza. Ana magana shi ne zaka yi mana tadin wata Gwamnati, mu bamu da wasu 'yan uwa a gwamnati, duk danginmu suna nan, kaburburan iyayenmu suna nan. Ban yadda Sadiya ta je ko'ina ba daga nan."
.
Ta fara zazzaro idanu tana huci. Khalifa da yaga hanyar auren sa ta kamo hanyar watsewa. Sai ya ta6a kafadar Balalle yayi masa rada.
.
"Ka ce mata na yarda zan zauna a nan har abada. Ka taimaka Balalle ka ce mata a nan zan zauna in yi noima da kiwo."
.
Balalle ya ce da kakar tasu.
.
"Ba komai Inna zai zauna a nan din, ba zai tafi da Sadiya ko'ina ba. Ya haqura yin aikin Gwamnati, ya ce shi dama tunda ya gama karatunsa na boko, ana bashi takardun ya kyakketa su ya watsar, ya ce shi noma da kiwo zai koma. Ba ruwan shi da aikin Gwamnati."
.
Tsohuwar ta sauko daga fushin da ta yi, ta ce da Balalle.
.
"to kaga da yayi haka ai ya nemarwa kansa mutunci da arziqi. Yaro in baya xuwa gona ai ya zama lalatacce ko a ina yake. Ba har a rediyo mun ji ana fada ba, an ce Sarki lanjeriya ya ce kowa ya koma noma. Ni komai yaro zai yi bana damuwa in har zai je gona wallahi, ba ya 6ata mani rai. Amma in har yaro yana so yga masifa ta da ake cewa ina yi to ya zama malalaci, in ga baya son aiki, to fa zamu qulla gaba."
.
Ta sa hannu ta matso da kaskon wutar, da yake toka ta fara taruwa. Ta kalli Khalifa da gefen idonta ta ce dashi.
.
"idan kana son Sadiya, to sai dai ka haqura da garin ku,ka dawo nan cikin garinmu kayi irin rayuwar da muke yi. Ba zamu yarda mu dauki 'yarmu mu kaita wata uwa duniya da sunan aure ba. Ka ci gaba da zamanka a nan qauyenmu, na amince za a baka Sadiya. Da dai ban yi niyyar zan amince ba, to amma tunda naji ka fasa aikin Gwamnati, kuma har ka yayyaga takardar makarantar boko, ka ce zaka yi noma to ni ka faranta raina sau dubu. Tashi ka tafi ku bani wuri. Allah Ya yi maka albarka. Kai kuma Balalle mara kunya, ka dwo anjima zan aike ka gida ka kwaso mani wasu kaya na da na mance dasu jiya ban taho dasu ba.SADIYA page 47
.
.
Kai kuma mara kunya Balalle ka dawo anjima zan aike ka can gida ka dauko mani wasu kaya na da na mance dasu jiya.
.
Khalifa yayi murmushin jin dadi. Ya ce da tsohuwar.
.
"na gode Inna, na gode Allah Ya saka da alkairi..."
.
Balalle yayi saurin bugun shi da hannu. Inna Gaje ta harari Khalifa ta ce dashi.
.
"Kai bana son rashin ta ido, kaima zaka koyi halin Balalle ne? Cewa akayi ana gdy? Marasa kunya ku tashi ku bani wuri."
.
Balalle yayi saurin jan shi suka tashi da gudu-gudu suka fita daga dakin Inna Gaje. Suka yi qofar gida suna dariya, da shigar su daki sai Balalle ya ce da Khalifa.
.
"Saura qiris ka 6ata shiri. Ai da bamu yi sauri mun fito, da cewa zata yi ta fasa amincewa, ba zaka auri Sadiya ba."
.
Khalifa ya bude baki yana mamaki..
"Sbd me Balalle? Laifin me nayi kuma?"
.
Balalle ya ce dashi.
.
"to ya zaka ce mata ka gode? Ai shiru ake yi idan manya suna maganar aure. Kamata yi yi da kaji ta ce ta amince za a baka Sadiya, tana gama fada sai ka tashi ka rugo da gudu ka fito daga dakin sbd kunya. Amma kai baka gudu ba, maimakon haka ma sai ka tsaya kana yi mata dariya kana gdy. Aure fa kake nema, an ce an baka kuma kaine zaka yi gdy Khalifa? Ai iyayenka ne masu yin gdy. Inna bata daukar irin wannan rashin kunyar."
.
Khalifa ya ji tsoro ya kama shi ya ce da Balalle.
.
"mu kuwa a can Birni, kakar yarinyar da mutum zai aura, kamar kakarsa take, zaka ga ana wasa sosai irin na jika da kaka. Akwai wata 'yar makarantarmu dana ta6a so a baya. Na ta6a xuwa gidan su ta kaini wajen Kakarsu wacce ta haifi Babanta. Mun je mun same ta tana cin abinci, da xuwanmu ta ce mu sa hannu mu ci tare, kuma muka sa hannu muna cin abincin muna hira, har muka gama. muna ci muna hira, ina ce mata matata tana ce mani mijinta."
.
Balalle ya dafe kansa yana mamaki ya ce da Khalifa.
.
"Idan Innan Gaje ta ji wannan labarin sai ta suma. Ynx haka da muka je dakinta da ace abincin take ci ka sa hannu, aka ce mata kai ne zaka auri Sadiya, ai in fadi maka ba kai ba, kai hatta su Baba da suka yarda da zancen auren in ba sa'a ba sai ta kore su daga gidan nan, balle kuma ni dana rako ka, kajin gidan nan, shanu da awaki babu wanda zai tsira daga tsinuwarta.".
.
.
**
.
.
Tunda Inna ta amince da batun auren Khalifa da Sadiya kuma shi kenan, babu abin da za a tsaya jira, don haka sai Mai unguwa ya tara 'yan uwansa aka sa ranar auren Khalifa da Sadiya. Wata biyu kawai aka sa wato sha uku ga watan qaramar sallah. Khalifa da Sadiya don farin ciki kamar su hadiye kan su. Kowa a cikin su yana murnar burinsa zai cika. Khalifa ya samu matar da yake ta fafutikar nema.....matar da a dominta ya baro garin su ya dawo da take ya zauna tare da iyayenta da 'yan uwanta.
.
Sadiya ta samu mijin da take so, wanda a domin shi ta fara sanin ko menene so a rayuwa. Su dukan su sun yi nasara, tabbas burin masoya ya cika. Tunda kowa ya amince me kuma za a tsaya jira?
.
.
**
.
.
Saura kwana biyar a daura auren Khalifa da Sadiya. Mutane suna ta cewa lkcn yayi saurin xuwa. Wa yake tsammanin Sadiya da Khalifa zasu ce haka? Su a ganin su lkcn tamkar shekara ne, abu kullum lissafi suke yi amma ya qi yaxo. Mai unguwa ya ke6ewa Khalifa sashin da zasu zauna shi da Sadiya. Iyayn Sadiya ne suka yi komai, dama sun ce ynx sune iyayen Khalifa.SADIYA page 48
.
.
Mai unguwa ya ke6ewa Khalifa da Sadiya sashin da zasu zauna. Ya fitar masu da qofar gidan su. Iyayen Sadiya su suka yi komai dama sun ce ynx sune iyayen Khalifa. Dama Mai unguwa ya ta6a fada masa cewa, sun gode da abin alherin da ya yiwa 'yarsu Sadiya, kuma suma zasu nuna masa godiyarsu ta hanyar da zai fahimci babu shakka sun gode. Gashi ynx sun bashi mata....sun bashi muhalli. Kuma tabbas zasu bashi duk wani abu da zai nema wanda zai zame masa abin dogaro. Khalifa bai damu da yanayin bikin, da yadda ya kamata ace ya kasance ba, ya san cewar da ace suna tare da yayansa ba a irin wannan gidan za a saka amaryarsa ba. Kuma ya san cewar da ace da yawun yayansa ba irin wannan shagalin za a yi ba a bikinsa. Sai dai kuma yana ganin tunda har ya yi nasarar mallakar Sadiya to babu wani sauran shagali da zai dame shi.
.
.
**
.
.
Mai unguwa ya kira Khalifa ya ce dashi, ya kira dan uwansa a waya ya fada masa cewar gobe zasu xo su same shi. Kamar yadda suka yi alqawari kafin ranar daurin auren taxo zasu je su same shi su bashi haquri, domin a yafewa juna. Khalifa ya ce da Mai unguwa.
.
"Baba ko dai za a bari sai bayan bikin sai a je tunda ynx lkcn ya qure?"
.
Mai unguwa ya ce da Khalifa.
.
"A'a, gobe da sassafe zamu je tare da kai Khalifa. Idan aka yi wannan daurin aure ba tare da an shaidawa dan uwanka ba, ba a kyauta masa ba. Kuma ba zai yafe maka ba, sannan ba zai fahimcemu ba, yana da kyau a same shi a fada masa."
.
Khalifa ya ce da Mai unguwa.
.
"to Baba, zan sanar dasu in Allah Ya yarda."
.
Khalifa ya koma daki yayi shiru yana tunanin yadda zai fara tunkarar yayansa Dakta Hamza, tun ranar da ya rabu dasu ya dawo garin su Sadiya ya cire layinsa ya canza sabo, don kada ma su kira shi su fada masa wata magana. Shi kuma ko sau daya bai ta6a kiran su ba. Bai san halin da suke ciki ba. Ya san in dai da rayuwa wata rana zai sasanta shi da dan uwansa, amma yafi son tukuna sai ya auri Sadiya, sannan ya neme shi da kansa su sasanta. Amma in har bai auri Sadiya ba ya sake komawa gida to akwai matsala. Bai san me zai faru ba, baya son wata matsala ta sake tasowa kafin ya auri Sadiya. Ya fi son idan ya aureta, komai za a yi a yi ta yi, tunda dai burinsa ya cika. To sai dai tunda Mai unguwa ne ya ce ya nemi Dan uwansa a waya suyi maganar za su he gobe. Dole ne ya fada masa. Ba zai iya kiransa yayi masa maganar ba. Hafsat zai kira ya fada mata cewar suna nan xuwa gobe shi da iyayen Sadiya..SADIYA page 49
.
.
.
Hafsa zai kira ya fadi mata cewar suna nan xuwa gobe shi da iyayen Sadiya.
.
Khalifa ya shigar da lambar wayar Hafsa a wayarsa, ya kira ta xuciyarsa na bugawa da sauri a lkcn da wayar ta shiga. Ya ji ta dauka tayi sallama, da yake bata san lambar da Khalifa ya kirawo ta da ita ba. Ya ce da ita a hankali.
.
"Sannu Anti ya gida?"
.
Hafsat ta riqe numfashinta cikin kaduwa.
.
"Khalifa...Khalifa ashe baka mance damu ba a rayuwarka? Ashe zaka sake tunawa damu kayi mana magana?q
.
Khalifa yayi ajiyar xuciya.
.
"Anti idan nace zan iya mantawa daku a rayuwata babu shakka ni yafi cancanta a nadawa sarautar wanda yafi kowa iya butulci a duniya. Idan na ce na ji dadin rabuwata daku, to ba shakka na yaudari kaina. Ban ta6a yin sa'a daya ban tuna daku ba."
.
Hafsat ta numfasa ita ma ta ce dashi.
.
"To ya Sadiyar take? Mun ji an ce biki ya qarato saura kwana biyar a daura aure. Allah Shi tabbatar da alheri."
.
Khalifa ya ji gabansa ya fadi, saura kadan wayar ta su6uce ta fadi daga hannun sa.
.
"Anti wa ya fada muku? Ya aka yi ku ka san wannan labarin?"
.
Hafsat ta ce dashi kai tsaye.
.
"Khalifa kana son Sadiya sosai. Tabbas kana baiwa soyayya muhimmanci a rayuwarka fiye da komai. Sai dai duk da haka akwai wata soyayya guda daya wacce ka kasa bata muhimmanci. Wannan soyayyar kuwa ita ce wacce ke tsakaninka da dan uwanka. Ina son ka sani cewar, tun san da ka saka qafarka ka fita ka bar gidan nan Dan uwanka bai sake samun kwanciyar hankali ba. Ya shiga damuwa ta yadda hatta al'amuran aikinsa komai ya tsaya.kai dai ka san duk irin maganganun da ya fada maka, yana sonka fiye da kowa a duniya, kuma ba zai ta6a canza wannan soyayyar da wata soyayyar ba. Tun sanda ka tafi ya haqura da kai, ya san cewar ya rasa ka tunda ka za6i Sadiya, ka bita garin su, mu kuma ka barmu. Duk da haka hankalin Dakta bai kwanta ba, akwai mutanen da ya samu suke samo masa rahoto akan ka, suna gano masa halin da kake ciki, suna fada masa yana biyan su, duk da ka tafi ka barmu. Hankalin Dakta baya kwanciya har sai an xo an fada masa cewar kana cikin qoshin lfy. Kada kayi mamaki don mun san zaka auri Sadiya ba tare da ka sanar damu ba. Mun san komai a game da kai, tun daga ranar da ka tafi har xuwa yau din nan."
.
Khalifa ya ji hawaye sun tarar masa a idanunsa. Ya tambayi Hafsatu.
.
"Anti kina so ki ce Dakta bai yi fushi da ni ba? Kuma har ynx yana daukata a matsayin Dan uwansa kamar yadda ya dauke ni a da?"
.
Hafssat ta ce da Khalifa.
.
"Yayanka har ynx yana daukarka amatsayin Dan uwansa, amma baya danganta ka a matsayin Dan uwa na gari wanda yake qaunarsa. Yana dangantaka ne a matsayin wani irin dan uwa mai son kansa, wanda baka damu da irin halin da zai iya fadawa ba. Wanda baka damu da makomar 'ya'yansa da xuri'arsa ba. Yayanka yana cewa ynx abu daya ne yake xullumi ynx a duniya. Ynx idan ya mutu wa zai riqe masa 'ya'yan sa da gidansa da dukiyarsa? Wannan tunani yana sa shi kukan tafiyarka Khalifa."
.
Khalifa ya fashe da kuka yana riqe da wayar. Hafsat ba ta ce yayi shiru ba, ta bar shi har sai da ya saurara don kan shi, ya tambayeta.
.
"kina jin Dan uwana zai yafe mani laifin da nayi masa in dawo mu sake zama tare?.
SADIYA page 50
.
.
"Kina jin dan uwana zai iya yafe mani laifin da nayi masa in dawo mu ci gaba da zama tare?"
.
"Qwarai kuwa zai iya yafe maka, amma sai ka tabbatar masa ka haqura da wannan yarinyar wato Sadiya. In har ka haqura ka fasa yin wannan auren ka baro garin su ka dawo gida, na tabbatar dan uwanka a shirye yake da ya amshe ka. Amma in har kana tare da Sadiya, to har abada dan uwanka ba zai ta6a yafe maka ba. Kada ma ka 6atawa kanka lkc wajen xuwa ka ce zaka bashi haquri, sbd ba zai ta6a haqura ba.".
.
Khalifa ya ce da Hafsatu.
.
"Anti sanin kanki ne Sadiya ita ce rayuwata. Ban san yadda rayuwata zata kasance idan bani tare da Sadiya ba. Ta yaya zan iya rabuwa da rayuwata Anti?"
.
Ta ce dashi.
.
"Haka kaima kamar rayuwa kake a wajen dan uwanka. Dakta bai san yadda rayuwarsa zata kasance ba idan bashi tare da kai. Ta yaya zaka raba shi da rayuwarsa Khalifa?"
.
Khalifa ya kasa cewa komai. Tabbas Hafsatu tayi gsky. Soyayyar Sadiya ita ce ta shiga tsakanin sa da Dan uwansa. Da ace bai kamu da sonta ba, da ynx yana can tare da Dan uwansa hankalinsu a kwance. Yana son Sadiya, sannan kuma yana son Dan uwansa. Soyayya ce ta shiga tsakaninsa da wata soyayyar. Gashi su duka biyun ba zai iya rabuwa dasu ba.
.
Khalifa ya sake yin ajiyar xuciya ya ce da Hafsat.
.
"Zamu xo gobe da safe ni da iyayen Sadiya. Ina son ki fadawa Dakta zamu xo mu fahimci juna. Iyayen Sadiya za su xo su bashi haquri."
.
Hafsat ta ce dashi.
.
"Duk abin da zan fada maka ynx ba zaka fahimci abin da nake qoqarin nuna maka ba Khalifa. Amma abin da nake son kayi shi ne, ka kira wayar Dakta kayi magana dashi, ka fada masa cewa zaku xo kai da iyayen Sadiya. Duk abin da ya fada maka, kada ka yi masa jayayya, sbd ba zai ta6a canza ra'ayinsa akan haka ba."
.
Khalifa ya ce da ita.
.
"Zan kira shi ynxn nan. Yana gida ne?"
.
Ta ce dashi.
.
A'a, yana wajen aiki, sai anjima zai dawo."
.
Khalifa ya ce da ita.
.
"Ki ta6a mani kan 'ya'yana idan suna kusa da ke. Ki ce da su ina gaishe su, in Allah Ya yarda wata rana zan dawo in sake zama tare dasu."
.
Hafsat ta ce dashi.
.
"Bayan na ta6a masu kai a lkc gud kuma zan share masu hawayen dake a idanun su. Domin kuwa tun tafiyarka kullum sai sun yi kuka a gidan nan suna tambayata in fada masu ranar da zaka dawo. Ban san me zan fada masu ba....."
.
Hafsatu ta fashe da kuka. Ta kashe wayar da sauri. Khalifa shima ya ci gaba da kuka, ya kwanta tsawon lkc yana tunanin mutanen da duk duniya bashi da kamar su, mutanen da ya zauna tare dasu, kuma ya rabu dasu a lkcn da suke tsananin buqatarsa a rayuwa.
.
.
**
*
.
.
Sai da ya gama kukan da yake yi tsawon lkc, sannan ya yanke shawarar zai kira yayan sa. Babu shakka yau zai yi magana da dan uwansa a karo na farko tun barin sa gida. Lkc yayi da ya kamata ya fara fahimtar matsalar da ta shiga tsakaninsa da Dan uwansa, wanda ya jawo sanadiyyar rabuwar su. Lkc yayi da ya kamata ya koyi yadda zai zauna tare da Dan uwansa wanda baya son ganin sa tare da ita.
.
Khalifa ya kira wayar Dan uwansa ya same shi a dai-dai lkcn da yake duba marasa lfy a can Asibitinsa. Yayi tsammanin lkcn da Dakta Hamza ya dauki wayar zai tsayar da hankalinsa ya nuna yana fushi ko mamaki idan ya fahimci shi ne ya kirawo wayar. Amma sa6anin haka sai ya ji ya ci gaba da dariyar da yake yi. Yana magana shi da wani mara lfy, yana yi masa wasa. Har xuwa lkcn da Khalifa yayi masa sallama, ya ce dashi.
.
"Khalifa ne yake magana."
.
Dakta Hamza ya ce dashi cikin harshen da ya saba yi masa magana.
.
("I knew it's Khalifa. How could possibly failed to recognise your voice?") Na san kai ne kake maga Khalifa. Ya kake?"
.
Khalifa ya ce dashi.
.
"Ina lfy Dakta. Ya aiki?"
.
Dakta Hamza ya ce dashi cikin farin ciki.
.
"komai lfy a nan gida, ina fatan kana jin dadin rayuwarka a nan inda kake a halin ynxn?"
.
Khalifa ya ce dashi.
.
"Ina lfy Dakta, ba wata matsala."
.
Ya yi dariya ya sake tambayarsa.
.
"Ya masoyiyarka ina fatan tana kulawa da kai?"
.
Khalifa ya saba da irin wannan barkwancin na Dakta Hamza, komai fushin da yake yi in dai zai yi magana sai ya sa raha da wasa a ciki. Khalifa ya ce dashi.
.
"Sadiya tana lfy Dakta. Ta ce in gaisheka."
.
Dakta Hamza ya ce.
.
"This is my girl; She respect me always. I hope she is putting asense in to her typical parent?"
.
Khalifa ya dan ji nauyin maganar. Ya ce
.
"Dama na kira ka ne

Please Login or Register in order to submit comment