Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fice daga gidan, bayan mai gadi ya bude masu qofa. Suka fice Khalifa yana daga masu hannu. Sadiya ta waigo tana kallon shi.
¤
Ta ji tausayinsa ya kamata kamar tayi kuka, sbd ta san da wahala yayansa da Hafsatu matarsa su dawo da labari mai dadi.
¤
Da qarfe sha daya da 'yan mintuna suka isa Turunkawa. Da shigarsu qauyen suka samu yara sun yi dafifi a wani dakin injin niqa. Wadansu suna ta 'yar gala-gala wadansu kuma suna ta meru, a lkcn da shi kuma injin yake ta aikin bulbular da bataliyar baqin hayaqi ta doguwar salansarsa da ta leqo waje tana tari kamar injin tsohuwar alaga.
¤
Yaran da suka kawo niqan duka bar wasanninsu suka mayar da hankalisu akan motar.
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
21
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
Suka mayar da hankalinsu akan motar, wadansu suka biyanta da gudu suna 6urari suna tsalle, da yawa a cikinsu basu ta6a ganin mota mai kyau kamar a mafarki irin wannan ba.
¤
Mutanen dake aiki a bayan gari suka fara tsayar da ayyukansu suna dawowa cikin gari don su ga ko a wanne gida motar zata ya da zango, kuma wanene yaxo da ita.
¤
Sa'ar da Dakta Hamza yayi fakin a qofar gidan su Sadiya, kamar yadda take nuna masa inda zai bi tun shigowarsa lardin, sai ya kashe motar suka fara bubbude qofofi suna firfitowa. Yaran da suka biyo bayan motar da kuma mutanen da suka baro gonakinsu suka dawo cikin gari suka yada sansani a gefe guda suna ba idanunsu abinci.
¤
Suka ga wasu mata biyu kamar an 6are su a leda, sun fito daga cikin motar, tare da wani mutum Dan birni. Babu wanda ya gane Sadiya da garaje. Sbd ta canza tayi qiba ta qara haske kamar sabuwar amarya a karkara, sai da ta jagoranci Hafsatu suka doshi zauren gidansu zasu shiga, kuma a hanyarsu ta hadu da wani matashi yayanta mai suna Baballe, ya fito daga gida babu riga a jikinsa, da Sadiya tayi masa sannu kowa ya ji muryarta sannan suka gane ta.
¤
Nan da nan mutane suka fara maganganun dawowarta, yara suka garzaya gidajensu suna fadin.
"Ga Sadiya nan ta dawo, 'yar gidan Mai unguwa Mal. Kalla tare da wata mata, an kawo ta a mota.
¤
Suka shiga gidan su kai tsaye, suka samu mata a zaune a baranda kowacce da zani iya qirji babu riga. Hafsatu ta saba xuwa qauye, bata yi mamakin komai ba. Da shigarsu matan gidan suka tashi a gigice, don kuwa sun gane Sadiya.
¤
Gidan ya hautsine da maganganu. Sbd Inna Gaje ta qauyen Kufen qaura taxo ta fadi cewar an yi mata duba an fada mata Sadiya tana garin aljanu sune suka sace ta. Don haka a ynx da matan ke yin baya-baya tsammaninsu aljanu ne suka shigo gidan.
¤
Mahaifiyar Sadiya ta fito daga dakinta da taji surutun da ake yi yayi yawa, da fitowarta ta ci karo da 'yarta tare da wata mata da basu santa ba. Sadiya ta doshi mahaifiyarta tana cewa.
¤
"Mama ni ce na dawo, nice...."
¤
Mahaifiyarta ta kaice a tsorace gefe guda, jikinta yana tsima ta fashe da kuka ta ce.
¤
"Sadiya basu cinye ki ba aljanun? Ya akayi ki ka gudo daga hannunsu? Ko kuwa sun ce ne ki xo ki tafi damu muma su cinye mu?"
¤
Sadiya ta cika da mamaki da tsoro da ta ga kowa ya tashi a kidime basa so ta matsa kusa dasu, hatta mahaifiyarta ma tsoronta take ji, ta tambayi mahaifiyarta.
¤
"Wadanne aljanu ne suka kama ni Mama?"
¤
Mahaifiyarta ta ci gaba da kuka tana cewa.
¤
"Sun hada baki da ke ne suxo su tafi da mu ne Sadiya? ita ma wannan matar a cikin su take? Ya akayi kika xo da ita nan taga inda muke? Muma sace mu zasu yi?"
¤
Hafsatu ta kalli Sadiya cikin rashin fahimtar abin dake faruw. Kafin kowa ya fahimci me kenan tuni maza sun fara fadowa cikin gidan, don jin hayaniyar da ake yi. Baballe wanda yaga shigowarsu ya fado cikin gidan. Da ganinsa mata suka fara dawowa wajen shi a tsorace tunda sun ga shi ne namiji. Mahaifiyarshi wacce ta kasance amaryar Mal. Buba ta ce dashi.
¤
"Baballe ku kira maza su yo mana dauki ga Sadiya ta dawo daga wajen aljanun da suka sace ta, bamu san wannan matar ba, don Allah ku kira maza su xo kada su sace mu muma."
¤
Kafin Baballe yayi wani yunquri sai ga Mal. Buba ya shigo aguke daga shi sai 'yar shara riqe da fatanya yayi futu-futu da qura. Da xuwanshi yaga Sadiya da wata mata wacce a tsammaninsa 'yar yankan kai ce. Ya nuna Hafsatu da yatsa ya ce da ita.
¤
"Asirinku ya tonu munafukai azzalumai, ai dama Inna ta ce mana muyi haquri har gida zaku dawo mana da 'yarmu, baku isa ku cinyeta ba."
¤
Hafsatu ta fara rudewa ta ce dasu.
¤
"Jama'a Assalamu alaikum, ni fa musulma ce 'yar uwarku, kuma ni mutum ce ba sace Sadiya muka yi ba, mun tsinceta ne muka taimaka mata...."
¤
bata kai qarshe Mal. Buba ya katseta ya ce.
¤
"Qaryar banza qaryar wofi, ai muna da labarinku."
¤
Ya ce da danshi Baballe.
¤
" Yi sauri ga babur can a waje, yi maza kaje Kufan qaura ka dauko Inna, ka ce aiki yayi kyau, azzaluman sun dawo da Sadiya. Ka goyota ku xo tare."
¤
Baballe ya bazama aguje. Sadiya ta ce da iyayenta itama.
¤
Ba sace ni suka yi ba, basu da laifi, taimakona suka yi, sun yi mani halacci tun tafiyata ina zaune a wajen su a Abuja mutanen kirki ne.
¤
Wata mata ta cire tsoro ta ce.
¤
"Ayya yarinya sun gama dake, sun gama sabautaki, dama ance haka suke yi, da sun baki wake da jini kin ci zasu rikide ki koma irin su, shikenan Sadiya ta zama mayya, jama'a mun shiga uku!
¤
Matar ta fashe da kuka, a sannan ne sauran matan suma suka dauki kururuwa.
¤
¤
Lp=20¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
22
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
Matar ta fashe da kuka a sannan ne suma sauran matan suka dauki kururuwa kamar an yi mutuwa a gidan. Mal. Buba ya ruga dakinsa jikinsa yana tsima, ya fito da wani qullin garin magani a leda yana cewa.
¤
"Haba, dolene su sake ta ta dawo daidai, ai bamu ake yiwa wannan tsiyar ba a kwana lfy."
¤
Ya fara waige-waige ya hango wani bokitin ruwa a bakin rijiya dake a tsakar gida cike maqil da ruwa, ya kwance ledar ya danqo maganin ya xuba a cikin ruwan yasa hannu ya motsa ya kinkimo bokitin ruwan a guje, da xuwanshi ya kwarawa Anti Hafsatu 'yar birni tun daga kanta har xuwa qafafunta yayi mata sharkaf tana tsaye a kidime ta kasa motsawa, yana gama watsa mata ruwan ya kama daka mata tsawa yana cewa.
¤
"Sakar mana 'yarmu ta dawo daidai yadda take da, muguwa sake ta."
¤
Hafsatu ta fara salati tana wayyo, don kuwa al'amarin ya wuce sawun hankali. Ta juya waje aguje har takalmanta suna faduwa, mutane suka dare a rude suka bata wuri, don kuwa a tsammaninsu aljana ce, ta nufi zaure aguje tana neman hanyar guduwa. Mal. Buba ya nunawa mutanen da suka shigo gidan ita da hannu.
¤
"Ku bita ku kamata, ku tsare su kada su gudu, yau sai mun kaisu gari wajen hakimi an kulle su."
¤
Hafsatu ta fita waje aguje ta samu mijinta Dakta Hamza a tsaye yana neman wata lamba zai kira a wayarsa. Yana dago kaine ya ci karo da matarsa Hafsatu ta fito aguje tana kuka tana salati, jikinta sharkaf da ruwa. Dakta Hamza ya tar6eta a rude yana tambayarta.
¤
"Ya aka yi...? wa yayi maki haka...me yake faruwa?"
¤
ta ce dashi bakinta na rawa.
¤
"Ba lfy Dakta, shiga mota mu gudu, wadannan mutanen halakamu zasu yi, shiga ka tada mota mu gudu kafin su kama mu."
¤
Tana cikin fada masa ne Mal. Buba ya fito aguje tare da sauran mutanen dake a cikin gidan, yana dauke da wani bokitin ruwan, da xuwanshi inda suke a jikin motar, bai jira komai ba, sai ya antayawa Dakta Hamza ruwan cikin bokiti, shima ya jiqashi sharkaf da ruwa. Dakta Hamza yayi tsalle gefe guda ya fara surutu a fusace yana cewa.
¤
"(What nonsense is this)....? Ku mahaukata ne, ya kuke yi mana haka Mallam... Me muka yi maku?"
¤
Mal. Buba yaja daga ya ce dashi.
¤
"kune mayun da kuka sace mana 'yarmu, mun samu labarin ku baki daya, dama tuntuni ku muke zaman jira, ance mana dama zaku xo ku kawo ta da qafarku, shegu azzalumai."
¤
Dakta Hamza ya fusata ya ciro wayar shi ya danna wasu lambobi yasa a kunne da sauri yana cewa.
¤
"Hello...police station. This is emergency....we are introuble...."
¤
kafin ya qarasa fadar abin da yake so ne, wani gabhehen qato baqi ya shawo kwana aguje riqe da fatanya, da xuwanshi tun kafin ya tambayi yadda al'amarin yake kasancewa, ya sa hannu ya mabgare Dakta Hamza wayarshi ta fadi qasa, ya dafe fuskarshi da hannu biyu. Hafsatu ta fara rafsa ihu tana neman a kawo masu dauki za a kashe su.
¤
Mal. Buba ya ce da wanda yayi dukan.
¤
"Tun daxu kuna ina Garba Sidi? Sai abu ya taso ayi ta neman ku a rasa inda kuke."
¤
qaton wanda yake ta kumbura yana sacewa, ya ce da Mal. Buba.
¤
"Kuyi haqiri Baba, ina can mashekari ne, ynx aka je aka fadi mani wai wadanda suka sace Sadiya sun dawo da ita gida, sune wadannan ko?"
¤
Mal. Buba ya ce a fusace.
¤
"sune mana marasa mutunci, har suna iya xuwa su kawo ta da kansu, kodayake ba yin kansu bane, dama Inna Gaje ta ce mu xuba ido da kansu zasu kawo ta."
¤
Garba Sidi wanda yake yaya a wajen Sadiya ya ce da sauran matasan dake a wajen tun daxu suna kallo.
¤
"ku mene ne amfaninku kuna kallo wasu zasu yi mana wannan wulaqancin, har su xo garinmu su tafi lfy, ku fara farfasa motarsu dama bata halas ba ce, ta yankan kai ce, ku farfasa shegiya."
¤
matasan qauyen suka farwa motar da bugu suna farfasa gilasanta da fartanyun aikin su da suka taho dasu daga gona. Dakta Hamza ya kama hannun matarsa suka fara yunqurin guduwa. Garba Sidi ya sha gaban su ya ce.
¤
"kuna guduwa zan sa a yi maku budu-budu a nan, ku tsaya kawai sai mai unguwa ya xo, yau sai mun kai ku gari wajen hakimi. Mayun banza mayun wofi."
¤
Dakta Hamza wanda ya rikice sosai. Har tabaronsa da wayarsa suka fadi bai san inda suke ba, ya ci gaba da qorafi cikin harshen turanci yana cewa.
¤
"I will report this kids to the commissioner of police as soon as we leave here."
¤
Garba Sidi ya tasowa Dakta Hamza yana zare idanu ya na cewa.
¤
"Naji kana cewa (Kill) da turanci, zaka kashe? Kana zaton mu jahilai ne bamu jin turanci ko? To naji abin da ka fada, ka ce (Kill) wato zaka kashe mu, to bari kafin ka kashemu bari in in kashe ka.
¤
Garba Sidi yayi kukan kura ya shaqare wuyan Dakta Hamza.
¤
¤
Lp=23¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
23
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska.
¤
¤
Yayi kukan kura ya shaqare Dakta Hamza suka fara juye-juye, Hafsatu ta dora hannu a ka tana faman kururuwa. Mal. Buba ya baro inda matasan suke rotsa kyakkyawar motar Dakta Hamza, yaxo inda Garba Sidi ke riqe da Dakta Hamza a lkcn tuni har ya kayar da dan birni ya haye kan ruwan cikinsa Mal. Buba ya ce dashi.
¤
"rabu dashi kai Garba, kada ya mutu ka ja a dora masa xunubinka duka, ai ba a kashe maye da mai cin mutane, sai ka ja xunubinsa ya dawo kanka ka rasa yadda zaka yi dashi ranar lahira, tashi haka nan."
¤
Garba Sidi ya tashi daga kan Dakta Hamza yana cewa.
¤
"Baba cewa yayi fa (Kill) kuma ni na san abin da yake nufi, turawan nan da suka yi mana aikin burtsatse sun ce idan ka ji bature ya ce (Kill) to ka nemi hanyar guduwa kashe ka zai yi. Kenan muma ynx kashe mu zai yi daya fadi haka Baba."
¤
Mal. Buba ya ce da Garba Sidi.
¤
"Rabu dashi yaxo ya kashemu idan ya isa, ai qaryarsu ta qare tunda suka kansu wajenmu bayan sun sace 'Yarmu."
¤
Dakta Hamza ya tashi yana tari, yasa hannu biyu ya gyara qashin wuyansa wanda Garba Sidi ya kusan karyawa. Dakta ya ce yana kukan takaici.
¤
"Ni ban ce zan kashe ka ba....(You peoples seems to misunderstand what I mean) na ce ne (kids) ku yara kuna wulaqantamu, bamu yi maku komai b. (I neaver kill any body anda i will neaver do it, to the rest of my life)"
¤
Garba Sidi ya sake yunqurowa ya ce a fusace.
¤
"Baba ka ji ya qara cewa ko? Ka barni in fara kashe shi tunda so yake ya kashe mu, nima fa turancin nan ba layance mini za a yi ba, ba abin da bana ji, shi yayi zaton ban ji abin da yake cewa bane, banza kawai bushman, kamon, gere, awut, faza, moza indiya."
¤
Mal. Buba yace da danshi xcikin lallashi.
¤
"Rabu dashi haka nan Garva, kayi qoqsri kuma ka wankemu tunda ka qwato mana 'yancinmu, ai ynx suma sun fahimci muna da masu jin turancin, basu kadai suka iya ba, ka rabu dasu tunda duk ta inda suka 6ullo ka san wajen."
¤
Hafsatu ta dawo wajen mijinta Dakta Hamza ta ce dashi.
¤
"Dakta qarar kwana ce ta kawo mu garin nan, sun kasa fahimtarmu, sun ce wai mu mayu ne, mu muka sace Sadiya."
¤
Dakta Hamza ya ce da ita yana share hawaye a fuskarsa.
¤
"Kada ki damu Maman Abba, komai zai wuce (We will survive)"
¤
A can cikin gidan su Sadiya kuma tana can matan gidan kishiyoyin mahaifiyarta da matan qannen mahaifinta, suna ta fitowa da gudunmawar jiqe-jiqe da qulle-qullen magunguna suna bata ta sha don ta dawo daidai yadda suka santa kafin ta 6ace, wata qanjamammiyar mata wacce ta debo toka tana watsawa a tsakar gidan tana surqullenta ta ce.
¤
"wannan qibar da tayi da wannan hasken ai bana lfy bane na ciewo ne. Sun lashe ta ne ta dawo haka dole sai an tashi da gaske, an ceto rayuwarta.
¤
Wata tsohuwa a gidan da suke cewa Haire ta fito daqyar daga cikin daki tana kyarmar tsufa, dusar goro na xuba daga wawulon bakinta. Ta xo ta samu matasan matan dake zagaye da Sadiya, tana kuka a tsakiyarsu ta rasa yadda zata yi.
¤
Haire tsohuwa ta yanke shawarar zata yiwa Sadiya addu' irin tasu ta tsofaffi, mutanen da. A cikin karatun da aka koya musu na yara, babu wanda tafi riqewa da kyau irin na jakar lahira. Wata malamarsu data mutu tun wajen shekara saba'in baya ita ce ta tabbatar masu da cewa. Duk laifin da mutum yayi kada ya damu akwai jakar da take yawo tana amsar alhaki tana xubawa a mangala. Idan taxo wajen mutum zata tambaye shi ta tsaya ne ko ta jirkice? Idan mutum yana da ilimi sai ya ce ta tsaya, sai ta amshi nashi alhakin ta qara gaba. Idan mutum jahili ne bai san karatun ba in ya ce ta girkiice, to duk alhakin da ta kwaso a baya ko na malala gashin tinkiya ne wai duk shi zata juye mawa. Sun zama xunubinsa tunda bai iya karatu ba.
¤
Haire tsohuwa wacce take ji da haddarta ta shekara saba'in taxo gaban Sadiya tana cewa.
¤
"Mu girkice ko mu dakace?"
¤
Wasu mata wadanda suma suna da ilimin wannan gur6ataccen karatun da tsohuwar tayi suka hada baki gaba daya suka ce.
¤
"Mu dakace haira haira. Haba mana Innan hajji!!"
¤
¤
**~**
¤
¤
Sai da Baballe yaxo da Inna Gaje a babur sannan al'amura suka dada lalacewa. Da sauketa a babur din a qofar gidan inda mutanen qauyen suka yi cincirindo ana ta hayaniya. Tsohuwar ta faso taron mutanen tan tambayar inda mutanen da suka kawo Sadiya suke.
¤
"Suna ina ne wai, ko baku jina ne....suna ina ne iyee?"
¤
A lkcn mutane sun zagaye Dakta Hamza da matarsa Hafsatu sun hana su guduwa, bayan sun gama farfasa motarsu ta dawo kamar wacce akayi karo da ita. Wani saurayi ya nunawa Inna Gaje inda suke, waje da mutane suka fi yin dandaxo.
¤
"Inna gasu can an tsare su an hana su guduwa.
¤
Inna Gaje ta garzaya wajen tana kumbura tana sacewa kamar asna sace tayar tantan.
¤
¤
Lp=24¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
24
with
Iliyas Ishak Gundutse
Ix
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
Inna Gaje ta garzaya wajen tana numfashi kamar ana sace tayar tantan. Da xuwanta ta ture mutane a hanyarta ta ce.
¤
"Ku bani wuri in kashe su in ga abin da za a yi."
¤
Kafin ta cafki wani daga cikin su ne wasu mutane masu dan hankali suka tarbeta suka fara lallashinta.
¤
"Ba za ayi haka ba Inna, wannan abu dai ya riga ya faru, kuma sun riga sun dawo da yarinyar nan gida, don haka komai zai xo da sauqi. Ki shiga gida Inna ku bar abin a hannun maza."
¤
Inna Gaje ta dubi Dakta Hamza da matarsa ta fara yi masu ruwan ashariya kamar wacce take bitar karatu. Ta ce dasu a qarshe.
¤
"qawata Gude ta fada mani komai. Me yasa baku cinye 'yar tamu ba kuka dawo da ita? Me yasa kuka fasa? Ku cinyeta mana in kun isa? Shegu...tsinannu matsiyata 'yan..."
¤
Mutane suka janye tsohuwar suka hana ta qarishe wani qaton ashar data mirgino, suka rakata ta shiga cikin gida. Inda abin yaxo da sauqi a lkcn da hakan ke faruwa shi ne, katsam! Sai ga Liman ya dawo daga gona. Ba a jima ba Mal. Kalla shima ya dawo. Da ya iske abin da ya faru ne sai Liman ya kirawo Mal. Kalla mahaifin Sadiya suka ke6e.
¤
Liman ya kori matasan da suka zagaye Dakta Hamza da matarsa, ya janyesu suka tafi zauren su su hudun. Da xuwansu suka tsugunna kamar wadanda zasu yi sasancin aure. Liman ya ce da Dakta Hamza.
¤
"Mallam mun dawo mika samu wannan rigima ta faru tsakaninku da wadannan yara namu da qannen mu. To shi dai wannan shi ne Mal. Kalla mahaifin Sadiya. Ni kuma ni ne Limamin wannan qauye namu. Bamu san ku ba an ce dai kune kuka dawo da Sadiya gida bayan tayi wata uku ana nemanta ba a ganta ba ba a san inda take ba. Muna son ka fada mana, mene ne hadin ku da ita? Kuma ya aka yi take tare daku tun lkcn baku nemi inda iyayenta suke kun dawo da ita ba?"
¤
Dakta Hamza ya numfasa zai yi magana kenan sai ya fashe da kuka ya kasa cewa komai, ganin haka sai itama Hafsatu ta fashe da kukan baqin ciki. Kukan da suke yi ne ya karya guiwar Liman da Mal. Kalla, suka ji tausayi ya kama su, Liman ya ce dasu.
¤
"Ku yi haquri, mun san cewar wadannan yara sun yi maku ta'annati, bamu san abin da ya faru ba, ku yi hquri, mu yi magana ta fahimta, ya aka yi?"
¤
Dakta Hamza ya share hawaye sannn ya girgiza kai.
¤
"Ba komai, na san cewar halin rayuwa ne yasa muka shiga wannan masifar ni da iyalina, kuma in ban da ina tunanin wani abu da kuma gudun kada in yi nadamar hukuncin da zai biyo baya ina tabbatar maku da duk wani mutum da kuka sani a qauyen nan sai an daure mani shi. Abin da yaran nan suka yi mana da wannan baqauyen mutumin mara hankali da tunani da yake qara iza su, wallahi da sai naje har wajen Kwamishinan 'yansanda na jihar nan nasa ya turo jami'an tsaro sama da hamsin sun xo sun kama duk wanda ke da hannu a wannan wulaqancin da aka yi mana.".
¤
Mal. Kalla mahaifin Sadiya da yaji ana maganar 'yansanda sai cikinsa ya duri ruwa, ya fara magana a sanyaye ya ce da Dakta Hamza.
¤
"Ba za a yi haka ba yalla6ai, kayi haquri, aiki ne na yara, ba hankali gare su ba, kayi haquri mun tuba."
¤
Ya dubi Liman wanda qaton rawanin sa ya sukurkuce kamar an dora masa buhun fulawa ya ce.
¤
"Ka basu haquri Liman, ka ce su yi mana afuwa."
¤
Liman ya ce da Dakta Hamza.
¤
"kuyi haquri, wannan al'amari sharrin shaidan ne, idan muka ce zamu ja wannan maganar ta je gaba, to ba dai kowa zai sha wahala ba, mu din ne dai. Yare daya ya hada mu kuma addini daya. Musulmi dan uwan musulmi ne duk inda yake, to ko don albarkacin wannan ina roqon ku kuyi haquri mu fahimci juna, mu yiwa juna maslaha."
¤
Dakta Hamza ya sake nmfasawa.
¤
"Haka ne...(Any way)...ni suna na Dakta Hamza, wannan kuma mata ta ce sunan ta Hafsat, muna zaune ne a cikin Abuja tare da 'ya'yanmu da wani qani na."
¤
Dakta Hamza ya basu labarin yadda aka yi har Hafsatu da qaninsa suka tsinci Sadiya a daji a wani hali mai cike da hadari, suka tafi da ita Abuja suka mayar da ita cikakkiyar 'yar gidan su.
¤
"Da na dawo gida na samu yarinyar a cikin iyalina, aka fada mani ga abin da ya faru da ita a dalilin auren dole da aka yi mata sai na basu goyon bayan taimakonta da suka yi,, sbd na san idan muka kore ta a wannan lkcn ba nan gidan zata dawo ba....(Her mind is far away from home that time, she might move to somewhere else...) kuma zata iya fadawa hannun miyagu ko a sace ta.....(Infact anything can happen to her) shi yasa na goyu bayan mu riqe ta har sai hankalinta ya kwanta ta dawo (normal) sannan sai mu dawo da ita wajen iyayenta mu fada musu abin da ya faru."
¤
Liman ya yi tagumi ya ce.
¤
"Ikon Allah, sannunku da qoqari."
¤
Dakta Hamza ya fadi musu kadan daga halaccin da suka yiwa Sadiya, da irin gatancin da suka nuna mata, kamar 'yarsu ta cikin su.
¤
"Sbd mata ta tana da 'yan uwa a qauye, wasu lokutan na kan je, na san wasu daga cikin matsalolin da suke faruwa a qauyukanmu, musamman a yankunan mu na hausawa a qasar nan, zaka ga mutane suna noma suna tara kudi, amma suna barin 'ya'yansu tsirara ba suttura.....
¤
¤
Lp=25¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
25
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
Madugun Taska
¤
¤
Zaka ga mutane suna noma suna da kudi sosai, amma suna barin 'ya'yansu tsirara babu sutura, suna barin su ba ilimi, basu sa 'ya'yansu a makaranta, suna barin iyalinsu da ciwo har su mutu a gida basu iya cire kudi su kai su asibiti, suna tara mata babu kulawa babu muhalli mai kyau, zaka ga yaro da mata hudu da 'ya'ya birjik, amma ba zai iya biya masu buqatun rayuwa ba....suna auren mata, suna sakin su su sake auro wasu kamar sayen kaji a kasuwa.
¤
Idan ka fito ka fadi wata illa akan haka sai al'umma su ra6e da addini su ce kai mai ra'ayin yahudawa ne, kana so ne ka hana tara xuriya mai yawa, bayan kuma irin xuriyar da al'ummar mu ke tarawa a yau, ba xuriya ce da za a yi alfahari da ita ba ta fannin ci gaban qasa, ko ta fuskar tattalin arxiqi, ko ta fuskar zaman lfy tare da juna, ko fannin dogaro da kai, xuriya ce wacce ba zamu ta6a kaiwa gaci da irin ta ba.
¤
Ba ga irinta nan ba? Ai gamu da yawan xuriyar, gashi nan mun cimma burin mu, mun fi kowacce qabila yawan xurya a qasar nan, amma me yawan namu ya haifar mana? Duk da yawan namu mune a baya ta 6angaren ilimi, mune kullum a baya ta 6angaren tallafawa juna,,, mune kullum a baya ta fuskar jami'an tsaro....ta fuskar Likitoci..ta fuskar Lauyoyi...ta duskar masana'antu da sha'anin banki...mune a baya ta fuskar mulki da ma'aikata a guraben gwamnati, kuma idan bamu dawo mun canza tsarin gina al'ummarmu ba, mun dawo mun zama masu kishin kai ta wajen bawa yaranmu ilimin addini mai kyau da na zamani ba, idan bamu dawo mun rungumi junanmu, mun zamo uwa daya uba daya ba, idan bamu kawar da banbancin aqida ba, wata rana sai mun wayi gari wasu qananun qabilu wadanda basu fi cikin cokali ba idan aka kwatantamu dasu. Sai mun dawo bamu iya hasala komai, sai mun dawo mune a qasa....(So every body know this). Babu wata qabila ko al'umma da ta ci gaba ta kan wannan hanyar da muka hau."
¤
Liman da Mal. Kalla suka girgiza kai suna jimamin maganar Dakta Hamza, duk da basa gane abin da yake cewa idan ya canja harshe, amma dai sun fahimci koma dai me yake cewa, yana nuna masu wasu matsaloli ne da suke faruwa a cikin al'ummar su.
¤
"Wadannan qartin 'ya'yan naku." Ya ce dasu. "Kamata yayi ku riqa amfani dasu wajen gina qauyukan ku da lardinan ku, maimakon ace kuna amfani dasu wajen ayyukan wauta da ta'addanci da kuma fadace-fadacenku na cikin gida wadanda ba zasu ta6a amfanar daku komai ba. Ku je ku ga yadda matasa ke taka rawar gani a duk wani sha'a da ya shafi ci gaban al'ummarsu a wasu yankunan na qasar nan.
¤
Idan wani mai kudi zai gina kamfani

Please Login or Register in order to submit comment