Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ci abinci da tsofaffi.
¤
Don kada Mai unguwa ya damu sai Khalifa ya tsaya, suka wanke hannuwansu suka ci danwaken da aka kawo Mai unguwa tare. Kafin wani lkc Khalifa ya fara sakin jikinsa a gidan. Da Balalle ya dawo daga gona, sai Mai unguwa ya kirawo shi ya ce ya gyarawa Khalifa wajen kwanciya su zauna tare. Ya sa aka kai masa jakarsa cikin dakin dake a qofar gida.
¤
¤
Lp=35¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
35
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
Balalle yayi wa Khalifa barka da xuwa, ya gyara masa daki. A ranar mai unguwa ya kira duk samarin gidan, da tsagerunsu da masu hankalinsu, ya gargadesu da kada wani ya kuskura ya ce za yi wa khalifa wauta. Inda samarin qauyen suke da ban sha'awa shi ne, duk maganar da manya suka fada, to magana ce mai muhimmanci. Don haka suka dauki Khalifa da muhimmanci kamar dan uwansu na jini. Aka manta da abin daya faru a baya. Mal. Buba ne kawai ya kusa yin halinsa daya saba, lkcn da yaga Khalifa ya sa wata 'yar qaramar riga da ta dage masa ta dame shi. Sai ya fara surutai yana qorafin Mai unguwa ya kawo masu yaro mara kunya gida zai 6ata musu tarbiyyar yara da shigar arna. To amma ko shi ba zai iya fadar maganar Mai unguwa ya ji ba, domin tun a lkcn da suka yi wautarsu shi da yara lkcn da Dakta yaxo ya 6atawa Mal. Kalla rai. Ynx bashi da ikon 6atawa Mai unguwa rai.
¤
¤
**
¤
¤
An kai sati daya da tafiyar Khalifa. Al'amarin gidan Dakta Hamza babu dadi.
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
36
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihasan.
Madugun taska
¤
¤
An kai sati daya da tafiyar Khalifa. Al'amarin gidan Dakta Hamza babu dadi. Sbd tun daga tafiyar Khalifa bai sake samun kwanciyar hankali ba. Dakta ya daina yin duk wasu abubuwan nishadi daya saba yi a gidan. Kullum idan ya dawo gida bashi da wani aiki sai dai ya zauna yayi tagumi yana tunanin yadda qaninsa Khalifa ya guje shi a dalilin soyayya. Duk shaquwar da yayi da Khalifa tun yana yaro, duk abubuwan alherin da yayi masa, soyayya tasa ya makance, ya daina ganin komai, ya dauki Dakta kamar wani abokin gabarsa. Sbd kawai ya hanashi abin da xuciyyarsa take so.
¤
Duk lkcn daya zauna yana tunanin rashin da'ar da Khalifa yayi masa, sai Hafsat taxo ta zauna kusa dashi tana bashi haquri. Ta ta6a nuna masa kuskuren da yayi, wajen hana qaninsa son Sadiya da yayi a kwana uku da tafiyarsa.
¤
"Idan Khalifa yana da laifi, kaima kana da naka laifin Dakta. Bai dace a ce ka hana shi ya auri wacce yake so ba, ka san shi so makaho ne, idan mutum ya kamu da so baya kallon komai sai gabansa, sai wannan abin da yake so...."
¤
Dakta ya juyo a fusace ya fara yi mata fada yana cewa.
¤
"A ina aka ce haska? A wanne shashan littafin kika karanta wannan shirmen? Kina nufin sbd soyayya sai mutum ya je ya hada xuriya da wasu qananan mutane wadanda basu san rayuwa ba, basu san inda komai ya dosa ba. Idan Khalifa ya auri wannan yarinyar yana nufin mun zama (Family) daya dasu kenan, ke kina fatan zama irin xuriyar da muka gani a wannan qauyen?"
¤
Aure yana nufin ka sami abokiyar zama wacce zata san aqidarka. Wacce zata san abin da kake son ka cimmawa a rayuwa. Wacce zata san martabar manufofinka, da kuma yadda zata dage wajen ganin ta kiyaye wadannan manufofin. Macen da koda baka a kusa zata iya tsayawa a dominka ba tare da wani xullumi ba. Macen da zata san halin da kake ciki koda baka fada mata ba, sannan ta shigo cikin gwagwarmayar da kake yi, ku fadi tare ku tashi tare."
¤
Amma ba haka kawai don mutum yaga mace ba....shi kenan don tana da wata siffa da yake so...farin ido ko wani dogon hanci ko wata murya mai dadi. Haka kawai sai mutum ya ce ya samu macen da zai aura, wannan wane irin shirme ne? Da Khalifa cewa yayi zai ci gaba da sonta, zai ci gaba da taimakonta, amma bisa la'akari da irin xuriyar da ta fito ya haqura da aurenta, zan amince da haka....becouse we are helping types."
¤
"Ke kanki kin san wannan gidan muna da tsare-tsare da muke yi don gina xuri'ar da muke son samu...We have our principles...we have our norms.....we have our own rules and behabious in this family..."
¤
Haka kawai sai in bar Khalifa ya tarwatsa mana wadannan tsare-tsaren? Idan yana son yayi aure ni ban hana shi yayi aure ba. Amma dolene ya samo mace ta gari wacce ta cancanta ya shigo mana da ita wannan gidan. Ba irin wannan yarinyar ba da yake so."
¤
Hafsat ta ce dashi cikin lallashi.
¤
"Duk na san da wadannan abubuwan Dakta, to amma don muna da wasu tsare-tsare da muka yiwa kanmu, wannan ba zai sa mu mance da yadda Ubangiji Shi kuma Ya tsara mana tamu rayuwar ba. Duk abin da ka fada haka ne, yana da kyau Khalifa ya samo yarinya ta gari wacce ta fito daga babban gida, a qarqashin manyan mutane, to amma kada ka mance da abin da Annabi (SAW) ya gargadi muninai dashi akan aure cewa,"Na umarceku da ma'abociyar addini." abubuwan da muka tsarawa kanmu Annabi (SAW) bai ce lallai sai dasu ba sannan za a auri mace, idan aka ce ma'abociyar addini ana nufin wacce ta san addinin Allah (SWT) Shi kadai. Wacce idan baka nan zata riqe maka amanar kanta da dukiyarka. Ita ce wacce zata tarbiyyantar da 'ya'yanka bisa rayuwa akan hanyar Allah miqaqqiya."
¤
Sadiya tana da waddanan halayen Dakta. Mun zauna da ita a nan gidan, kai kanka shaida ne, tana da kunya sannan kuma bata son duk wani abu da ya shafi sharholiya ko rashin tarbiyya. Ka duba irin shigar da take yi, bata rabuwa da lulli6i idan har akwai maza a gidan nan. Gata da riqon addini, komai yarinyar nan take yi idan lkcn Sallah yayi zata bari ta tashi taje tayi, gata da son karatun Alqur'ani, sai ta raba dare a dakinta kana jiyo muryarta tana karatu, in dai mace ta gari ake so a samu ni a ganina Sadiya tayi, a barshi kawai ya aureta mu kawo qarshen wannan tashin-tashinar hakanan."
¤
Dakta Hamza wanda duk maganar da take yi fuskarta yake kallo, ya bude baki yana maki ya ce da ita.
¤
"Hafsat har kin mance da duk abin da iyayen yarinyar nan suka yi mana? Tare da ke muka sha wahalar nan, har kin mance, har kina iya cewa da bakinki in bar qanina Khalifa ya asuri wannan yarinyar?"
¤
Hafsat ta ce dashi.
¤
"to ya za a yi laifin iyayenta ya shafeta? Ita menene laifinta a duk cikin abubuwan da suka faru? Basta san zasu i mana haka ba. Akan me zamu riqa danganta ta da abin da iyayenta suka yi mana Dakta? Wannan hukuncin yayi daidai kenan?"
¤
¤
Lp=37¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
37
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
¤
A kan me zamu danganta ta da abin da iyayenta suka yi mana Dakta? Wannan hukuncin yayi daidai kenan?"
¤
Dakta Hamza ya tashi ya ce da ita a fusacee.
¤
"Abin da nake tsoro shi ne mu hada aure dasu, gaba mu sami 'ya'ya masu hali irin nasu...I'am always afraid of the heredity problems...don haka nace ban yarda Khalifa ya auri wannan yarinyar ba, kuma ba zan ta6a yarda ba. This is all."
¤
Hafsat tayi ajiyar xuciya.
¤
"Allah Ya huci xuciyarka. Kayi haquri"
¤
¤
**
¤
¤
Khalifa ya zama dan gida a garin su Sadiya, sbd tsananin son da yake yi mata ya sa shi yake son kowa a garin, yara da manya kowa nasa ne. Bai dade da xuwa ba yayi abokai, idan zasu gona sai ya bisu su tafi tare. Khalifa ya fara koyon noma, tun yana yi ba daidai ba ana yi masa dariya har ya fara iyawa. Aikin da bai ta6a tsammanin zai yi shi ba a rayuwarsa. Sannu a hankali ya fahimci yadda rayuwar qauye take. Baya raina kowa, sannan kuma baya qyamar kowa, duk 'yan uwan Sadiya sun zama 'yan uwansa. Iyayenta sun zama nasa. Khalifa ya zama dan gida a garin su Sadiya.
¤
Da yamma su Balalle su kan tafi dashi harbin tsuntsaye a wani qaramin tsauni dake a bayan gari. Khalifa bai iya riqe gwafa ba. Ya ta6a yin harbi tsakuwar ta samu hannunsa ta ji masa rauni a dan yatsa. Yau da kullum da yake ya sawa xuciyarsa yana son ya koyi harbin, sannu a hankali ya fara qwarewa. Idan suka harbo tsuntsaye wani lkcn a daji suke hada wuta suna gasawa su ci, idan yamma tayi sanyi, babu abin da ya fi dadi irin zama a gindin bishiyun dake a saman tsaunin. A nan suke zama suna kallon gidajen qauyen dake a nesa kafin rana ta fadi su kama hanya su dawo gida.
¤
Duk sanda Mal. Kalla ya dawo gida tun kafin ya huta zai fara tambayar inda khalifa yake. Baya son yana yin nisa da gida. Haka kawai zai sa a kirawo shi su zauna suyi ta hira yana fadawa Khalifa labaran ban al'ajabi da suka ta6a faruwa a qauyen. Musamman a shekarun baya lkcn da kuraye ke gangarowa daga saman tsauni suna shigowa cikin garin suna daukar 'ya'yan awaki suna gudu. Da kuma lkcn da suke xuwa ko'ina a qasa, komai nisan tafiya babu hawa mota, sbd babu motoci a wancan lkcn. Khalifa ya riqa sanin abubuwan da bai sani ba a rayuwarsa. Abubuwan da bai ta6a sanin sun wanxu a duniya ba. Idan Mal. Kalla ya dawo gida tun kafin ya huta zai tambayi inda Khalifa yake?
¤
Da Khalifa yaga kusan duk samarin qauyen basu yi karatu ba sai ya jawo hankalinsu da samu lkc ya riqa koya musu, koda karatun hausa ne na yaqi da jahilci. Da mutum biyar ya fara, suka samu wani babban shago a qofar gidan Liman inda ake ajiye amfanin gona idan kaka tayi. Aka samo fitila, sannan akayi allo na baqin fenti. Khalifa ya fara koyar da karatu da daddare, da yake duk abokan sa ne, rabi wasa rabi karatu suke yi, sauran matasan qauyen suka fara turuwar xuwa yaqi da jahilci. Basu fi sati biyu da farawa ba, amma sai da duk matasan qauyen sama da hamsin suka shigo ajin yaqi da jahilcin, wurin ya cika maqil. Dole sai da Khalifa ya raba ajin gida biyu, sai wadansu sun gama sai wasu su shigo.
¤
Karatu ya kankama a qauyen su Sadiya, a sakamakon xuwan Khalifa. Da manyan gari suka ga yaran sun fara qaruwa, wadansu sun fara iya rubuta wasiqa, wadansu sun fara koyon karanta litattafi sai suka fara shawarar suma zasu bude ajinsu na manya tunda gemu baya hana neman ilimi. Suka samu Mai unguwa da maganar ya ce shima ya amince kuma zai shaidawa Khalifa. Sai suyi allon bango Khalifa ya riqa yi masu nasu da yamma. Da daddare kuma darasin matasa. Duk kusan dattawan qauyen ba a barsu a baya ba, kama daga kan Mai unguwa Mal. Kalla, da Liman da kuma Mal. Buba wanda Khalifa ya bashi muqamin shugaban aji sbd rashin haqurinsa. Yarima A Gangariya kuma mataimakinsa.
¤
¤
Lp=38¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
38
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
Mal. Buba wanda Khalifa ya baiwa muqamin shugaban aji sbd rashin haqurinsa. Karatu ya kankama a qauyens su Sadiya sbd xuwan Khalifa.
¤Khalifa ya samu kar6uwa a xuciyar duk wani wanda ke a qauyen. Duk inda yasa qafa matasa ne tare dashi. Sai da ya kasance baya aikin komai. Akwai wadanda ke daukar kayansa su wanke su goge masa. Idan zasu wani waje akwai wadanda ke daukarsa a babur su kai shi su jira ya gama abin da zai yi su dako shi su dawo dashi. Khalifa ya zama kamar shi ne Sarkin garin. Mai unguwa ya riqa alfahari dashi, ya qara riqe shi tamkar dan sa na cikinsa.
¤
¤
Na gode bisa kulawarku gaba daya ahalin Taska bisa kulawarku tun daga lkcn da na sanar da rashin lfy ta har xuwa ynx. Allah Ya bar xumunci¤<>¤<>¤<>¤ $@DIY@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
38part B
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
¤
Yara qanana basa xuwa makaranta a qauyen, da safiya tayi za a basu qananan shanu su tafi bayan gari kiwo. 'yanmata kuma sai a tura su cin tsintsiya ko kuma tsintar ta6o. Khalifa ya tuntu6i mai unguwa kan wannan matsalar ta rashin makaranta a qauyen. Mai unguwa Mal. Kalla ya ce da Khalifa.
¤
"to wannan matsala tafi qarfinmu Khalifa, mun samu Dagaci Sarkin noma, ya jagorancemu har xuwa fadar Hakimi dake a gari, mun je mun kai kukanmu wajen Ciyaman don a gina mana makaranta a wannan qauyen. Ya ce tuntuni ya fitar da kudin gina wannan makaranta da kudin filin da za a yi ginin, amma a tsakanin Kansilan wannan maza6ar da kuma dan kwangilar da zai yi aikin ginin, mun rasa wanda ya cinye kudin, shekara uku kenan muna jiro ko bulo bamu ga an kawo ba."
¤
maganar ta sosa xuciyar Khalifa, ya ce da Mai unguwa.
¤
"Ba komai Baba, in Allah Ya yarda duk inda makarantar nan ta shiga shekara uku da suka wuce, zan qwaqulota ta fito, kowa ya cinye dole ne ya amayo ta".
¤
Mai unguwa ya ce idan Khalifa yi yi masu haka ya taimakesu tare da duk wani wanda zai amfana da makarantar. Da daddare bayan an yi karatu an tashi.¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
¤
page
39
with
Iliyas Ishak Gundutse
Ix
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
Via comment
SADIYA Page 42
.
.
.
Khalifa babu wani abu da na iya wanda zan yi yayi kama da irin abin alkairin da kayi mana.
.
Khalifa yayi murmushi a taqaice, ya matso kusa da inda Sadiya take zaune tana xubar da hawaye, yasa hannuwansa biyu ya share mata hawayen dake a fuskarta.
.
"bana so in ga kina kuka Sadiya."
.
Ya ce da ita a sanyaye kamar yana yi mata rada a kunne.
.
"Duk lkcn da wani abu ya sa ki kuka, in har fuskarki ta canza komai na duniyar nan canzawa yake yi. Don haka ki kasance cikin farin ciki da murna akodayaushe."
.
Maganar da ya fada ita ce ta sanya ta murmushi cikin sauri Khalifa ya ce da ita.
.
"abin da nayi shi ne abin da ya kamata duk wani masoyi ya yiwa masoyiyarsa a duniya. Duk lkcn da masoyi ya nuna wata mace ya ce yana sonta, to ya zama wajibi ya so duk wani wanda ke tare da ita, in har soyayyar gsky yake yi mata. Tabbas ina son ki Sadiya, shi yasa na bar garin mu, na bar mutanen da nake zaune tare dasu tun ina yaro. Wataqila cikin mutanen da suka sanni idan wani yaxo ya ganni a nan ya ji tausayina sbd ya ganni a wahalar rayuwa, to amma ni bana jin wahalar komai Sadiya sbd ina tare da ke, ni bana jin tausayin kaina, tunda ina tare dake. Kullum na wayi gari ina yiwa kaina murna da samunki da kuma yadda kowa ya amince dani a gidanku. Babu wani dadin duniyar nan da zan ji in har bana tare da ke. Koda wata nahiyar za a kaini a duniya, sannan kuma babu wata wahala da zata dame ni, koda a cikin qaya zan zauna, in har zan bude ido in ganki, ba zan ta6a jin zafi ba Sadiya."
.
Sadiya ta lumshe idanunta na wani dan lkc, Khaliffa yana zaune a gabanta yana kallonta, lkcn da ta bude ido ne sai ta ce dashi.
.
"lkcn da na rasa Amir na tsammaci cewa masoya sun qare a duniya. Na dauka ba zan qara samun wani masoyin kamar Amir ba. To amma samunka da nayi ynx ya sa na fahimci soyayyar da nayi da Amir, tamkar sharar fage ce, tamkar wata qararrawa ce dake nuna mani cewar in shirya akwai wata gagarumar soyayya dake jira na. Soyayyar Amir tamkar iskar hadari ce dake sanar da ni cewar in nemi mafaka sbd alamun qaratowar ruwan sama. Tabbas ba zan yi butulci ba Khalifa, kai ne kafi kowa cancanta ya zama masoyina.SADIYA page 43
.
.
Kaine ka fi kowa cancanta ka zama masoyina a duniya. Kai ne kafi kowa cancanta da rayuwata. Babu abin da zan ce maka sai dai Allah Ya saka da alkairi. Na gode da wannan soyayya da kake yi mani Khalifa."
.
Ya ce da ita bayan ta kai qarshe.
.
"Ni ya cancanta in fara gode maki Sadiya, sbd kafin in hadu da ke a duniya ban san abin da xuciyata take so ba. Akwai 'yanmata biyu da na sanya su a xuciyata har in riqa fadawa mutane cewa masoyana ne, ban ta6a sanin kuskure nake yi ba sai da na hadu dake na fara sanin abin da xuciyata take so da gaske. Da acce ban hadu dake ba Sadiya, da a haka zan gama rayuwata har in bar duniya ba tare da na san abin da xuciyata take so ba. Da sai dai in zauna da wata mace daban cikin kuskuren rashin sanin ko menene soyayya. Don haka ni yafi kamata in yi maki gdy. Tabbas ynx na san abin da ban ta6a sani ba akan soyayya. Na san ko ni wanene ynx. Na shigo cikin wata sabuwar rayuwa ta musamman wacce na same ta a domin ki."
.
A nan masoyan suka dade suna ta hirar soyayya....sai ka ce yau suka fara ganin junan su a rayuwa. Su dukansu babu wani sauran abu da suke jira....su ke ta fatan gani a halin ynx da ya wuce ranar auren su. Khalifa da Sadiya sun kamo hanyar cimma burin su.
.
.
**
.
.
Kwana biyu da gama iddar Sadiya, sai Mai unguwa ya tara 'yan uwansa da sauran aminansa dake a qauyen ya tuntu6e su da zancen auren Sadiya da wannan yaro dan kirki Khalifa. Tun kafin Mai unguwa ya kai qarshe 'yan uwansa suka ce sun amince, sai a sa lkcn daurin aure kawai ba sai an jira wasu 'yan uwan yaron ba. Mal. Buba ya ce.
.
"Ai wannan yaro ya cika da, duk inda ake neman dan halak Khalifa ya wuce nan. Yaron nan baya qyamarmu ya dauke mu tamkar 'yan uwansa. Ni ne dai mai daurawa Sadiya aure, to na bashi.
.
Dattawn dake wajen suka tuntsire da dariya Mal. Kalla ya ce.
.
" To alhamdulillahi, ni kuma ni ne mahaifin Khalifa ni zan yi masa duk wani abu da uba ke yi wa da a wajen aure. Ni zan biya masa sadaki, ni zan yi kayan lefe, ni zan yi komai. Duk abin da ake buqata i zan yi."SADIYA page 44
.
.
Zan bada komai.
.
Liman ya yi gyaran murya ya ce.
.
"To alhamdulillahi, wannan sha'ani yayi dadi, tabbas wannan yaro ya cancanci mu saka masa da alkairin da yayi mana a wannan qauyen. Kun ga dai a da daidaikune a suka iya karatu da rubutun boko. Amma ynx gashi yara da manya ba wanda zai ce bai iya karatu da rubutu ba. Wasiqar nan za a iya rubutata, kun ga ada in aka rubuta mini takarda sai na nemo yara sun karanta, amma ynx ina gane komai. Ga Mal. Buba nan, jiya na same shi a Durumi ya bude wani wagegen littafi yana ta faman bita, har na wuce bai ganni ba, ina ta sannu amma ina. Yayi xurfi a kogon nazari."
.
Dattawan suka sake fashewa da dariya. Mal. Buba ya ce.
.
"Ina, ai ba zan ji ka ba Liman. Wani littafi na samo a gari da na je kasuwa wai shi MAGANA JARI CE: ai Malam idan ka ji abin al'ajabin dake a cikin littafin nan ba a mafana. Fasaha aka shirya gata nan a ciki. Kai wanda bai iya karatu ba an cuce shi.
.
Mal. Kalla ya ce.
.
"Tunda haka ne, zan ga shi yaron, zan fada masa duk abin da muka tattauna, bayan an yi bikin zamu hada kanmu qwai da kwarkwata mu je can garin su mu samu dan uwansa mu bashi haquri mu sasanta su, ya koma can su ci gaba da zama tare."
.
Liman ya tambayi Mal. Kalla.
.
"Wani hanzari ba gudu ba Mai unguwa. Me zai hana kafin a yi auren ba zamu fara xuwa mu sami dan uwan nasa ba mu bashi haquri. Sbd yaxo muyi komai tare dashi na bikin. Kuna jin zai haqura idan ya ji an ce an yi bikin qaninsa ba tare da an sanar dashi ba?"
.
Mai unguwa ya ce.
.
"A nan ma ka kawo shawara Liman, to amma abin da su yaran suke tsoro shi ne, kada a je a same shi kafin bikin ya qi amincewa kuma wata sabuwar rigimar ta sake tasowa. Sun fi son idan aka yi auren, to daga baya komai ya faru, an riga an yi an gama sai dai kuma a nemo hanyar sasantawa."
.
Mal. Buba ya numfasa sannan ya ce.
.
"Wannan matsala dai duk mu muka jawota, kuma babu wanda ya assasa ta sai Inna Gaje. Da bata xo da wannan maganar ba, mu ba zamu kama mu hau kai mu zauna ba, har mu xo muyi masu abin da bai kamata ba. Ynx dai kun ga duk da irin cin kashin da muka yiwa dan uwan wannan yaron, ku dubi abin da ya yi mana a wannan qauyen, bai dauki abin da zafi ba, sbd yana qaunar xcuriyarmu. To idan haka ne, ana iya sa ranar auren, idan ya rage saura sati daya sai mu dunguma mu je birni mu same shi mu bashi haquri, kun ga sai ayi biki tare dashi a yafewa juna, abin da ya wuce a bar shi ya wuce.SADIYA page 45
.
.
.
A yi komai tare dashi a yafewa juna, abin da ya wuce a barshi ya wuce."
.
Liman ya ce.
.
"Nima na goyu da bayan maganar Mal. Buba. Kafin a yi bikin a je a samu shi yayan nasa, hakan zai fi maimakon a ce sai dai kawai ya samu labarin mun ba qanin sa aure mun gama komai a nan bamu same shi ba. Gsky mai unguwa a duba wannan lamari a gani."
.
Mal. Kalla ya ce.
.
"Liman ai tunda kuna ganin hakan zai fi, dole a yi haka din. In lkcn bikin ya kusa, sai mu hadu mu tasa yaron mu je a zauna a sasanta shi da dan uwansa."
.
Da wannan yarjejeniyar suka tashi a zaman tattaunawar. Sun yi wannan zaman da kwana uku, mai unguwa ya sanarwa Khalifa da 'yan uwansa za a sa ranar auren Khalifa da Sadiya washe gari da safe. Aka tura Balalle ya hau keke ya je ya fadowa Inna Gaje don kada ta samu labari wani tashin hankalin ya kuma tasowa. A ranar da ta xo da daddare cikin sauri sai ta sa aka kirawo mata Mal. Kalla don ko wa za a bawa Sadiya.
.
.
**
.
.
Tunda Khalifa ya xo Turunkawa, ba wanda ya fadawa Inna Gaje labarinsa. Shi yasa bata san dalilin xuwansa garin ba har yake zaune a gidan su na gado, bata san shi ne qanin wannan mutumin da ya dawo da Sadiya gida ba, wanda Bokarta Gude ta fada mata maye ne.
.
Da ta xo ne ynx sai su Mai unguwa suka je dakin da take zama in ta xo garin, suka same ta shi da qaninsa Mal. Buba. Suka durqusa suka gaisheta, ta amsa da qyar a ciki tana hade rai. Bayan sun gama gaisawa ne ta ce dasu.
.
"Kun aiko Balalle daxu in xo za a sa ranar Sadiya. A ina ta samu mijin?"
.
Mai unguwa ya ce da ita.
.
"Wani yaro ne da ya xo daga birni, yake zaune a nan wajena, to gsky Inna mun yaba da hankalin yaron. Ki tambayi kowa a garin nan zai fada miki halin sa."
.
Inna GaJe ta harari Mai unguwa.
.
"Yaushe ya xo garin bani da labari? Dama akwai wani yaro da yake zaune a nan gidan amma ba a ta6a fada mini ba?"
.
Kafin Mal. Kalla ya bata amsa ne Mal. Buba ya riga shi.
.
"Ya dade a nan Inna. Tadin ne bai ta6a fadowa kan shi mun yi maganar ba amma ya dade. Yaron ya zama dan gida."
.
Inna Gaje ta ce dasu.
.
"To iyayensa da kakanninsa na nan ne, ko suma a can birnin suke?"
.
Mai unguwa ya bata amsa da cewa.
.
"A'a, duk a can birnin suke, amma sun xo mun yi magana, mutanen kirki ne dattawa."
.
Inna Gaje tayi shiru tana tattauna maganar, xuwa can ta sake tambayar su.
.
"A ina zai zauna da Sadiyar bayan sun yi aure? Yana da gida a nan ne?"
.
Mal. Buba ya ce da ita.
.
"A'a Inna garin su zai koma da ita. Ai ba dan nan bane, zama ya kawo shi nan garin, amma garin su zai koma in an yi auren.
.
Tsohuwar ta daga murya.
.
"To na gane! Ya xo nan ya zauna don ya yaudaremu mu bashi aure daga baya ya dauke matarrsa shi kenan ya gudu. Ai ni daga jin yadda kuka fada mani maganar na gano inda manufar take. Ku har ynx baku

Please Login or Register in order to submit comment