Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a garin su, bai isa ya sa bulo daya a qasa ba sai sun yi yarjejrniya kan zai gina masu makarantu da hanyoyi, kuma zai dauki nauyin karatun 'ya'yansu. Idan za a gina banki a garin su, dole a dauki ma'aikata mafi yawa daga cikin su, ragowar ma'aikatan da bankin zai dauka sai sun bi diddigin sdunayensu sun ga ko su waye za a dauka, idan sun ga wani sunan wanda bai kwanta masu a rai ba na wata qabilar da basu so dole sai an canza shi."
¤
"Amma wadanda matasa suke iya bugun qirji a cikin matasan dake yankinmu na nan arewa suyi wa al'ummarsu wannan namijin qoqarin? Wane banki ne ka ta6a jin yaxo wani gari ko wani qauye a yankunanmu ya saurari muryar matasa ko al'umma? Suna xuwa ne kawai su yi abin da suke so, sbd sun san bamu da wadatar matasa masu karatu da suka san 'yancin su, wadanda suka san muhimmancin al'ummarsu, wadanda suke hasashe mai kyau akan abin da suke son su cimmawa.
¤
"A nan Arewa akwai manyan masu kudin da ana kallon su suna sayen kamfanoni suna rufewa, a dalilin haka mutane dubu nawa ne suka rasa ayyukan yi? Barayi nawa suka qaru? Wa ya san koma bayan da hakan yake jawowa? Kun ta6a cusawa yaranku irin wannan masaniyar sun farga da abin dake faruwa don su fito su nuna rashin amincewar su?"
¤
"Kuna ta 6ata tunanin 'ya'yanku wajen nuna masu hanyoyin rayuwa na da can...tsofaffin hanyoyin gudanar da rayuwa wadanda sun daina aiki a wannan zamanin. Yawanci ku da kuke a nan karkara har ynx kun kasa gane cewar a yau zaku iya sa yaranku a makarantar addini su samu karatu mai yawa a gida. Lkcn hijirar neman ilimi ya wuce. Waccan hijirar da aka yi ta neman ilimin addini ta sha banban da ta ynx.
¤
Ta yaya zaku dauke qananan 'ya'yanku 'yan shekara shida xuwa bakwai ku kai su wani gari da sunan neman ilimin addini, ba tare da kun san abin dake faruwa dasu ba? Yaran da kuke turawa birane ku kanku kun san ba karatu suke xuwa nema ba, sbd kodayaushe sune a tashoshin motoci suna bara, sun mayar da barar ta zama sana'a a wajen su, sun saba dole sai wani ya dauka ya basu sannan zasu ci sannan kuma a ce wadannan ne zasu amfani al'umma?
¤
Ta yaya kuke tunanin yaro zai yi tunanin bari ya tashi ya dogara da kan shi, ko kuma yayi tunanin yin wani abu da zai yi wa al'ummarsa garkuwa? Bayan ya taso xuciyarsa a makance baya iya neman na kansa? Ta yadda hatta abinci ba zai iya ci ba sai ya tsugunna wani ya ci ya rage masa?
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
26
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
Ta yadda hatta abincin da zai ci ya saba sai an ci an rage masa."
¤
Addini bai koyar damu irin wannan rayuwar ba ta barace-narace, kuna dai fakewa ne kawai da sunan addini kuna tura yaran ku wasu garuruwan don mutane su ciyar maku dasu, bayan kuma kun sani cewar iyaye Allah Ya dorawa nauyin tarbiyyar 'ya'yansu ba wata duniya ba. A yau ba wani gari komai qanqantarsa a garuruwan mu na musulmi da za a ce babu masu ilimin addinin da za su bude makaranta su koyar da yara su basu karatu mai kyau da tarbiyya.
¤
Amma sbd son rai da neman sauqi da rashin kulawar iyaye ga makomar rayuwar 'ya'yan su, sai kaga da an cire yaro daga nono sai a fara tunanin garin da za a kai shi yayi bara. Wasu sai su shekara biyar ba su je sun xiyarci 'ya'yansu sun ga halin da duke ciki ba. Kuma a haka har sai an kai lkcn da yaran ne zasu riqa sayo sutturu suna aikowa da iyayen, kuma suna amsa da murna. Kun mayar da 'ya'yanku na cikin ku sun zama bayi a wasu garuruwan, a haka wai har zaku iya fitowa ku ce Gwamnati azzaluma ce, shugabanni basu da adalci a haka zaku samu shugabanni masu tausayi bayan ku baku ji tausayin hatta 'ya'yanku na cikin ku ba?....(Please forgive me for using inpassioned tone in my speech.....I cant watch the destruction of our land without protesting)."
¤
Mal. Kalla da Liman wadanda jikinsu ya dade da mutuwa suka yi qarfin halin lallashin Dakta Hamza, wanda yayi shiru yana mayar da numfashi, suka bashi haquri har sai da ya fada da bakin sa ya yafe kuma komai ya wuce. Ya ce dasu.
¤
"Mu tafiya zamu yi ina fatan zaku jawo hankalin 'ya'yan ku, su canza yadda suke gudanar da tsarin ratywarsu."
¤
Ya miqe ya ce da Hafsatu ta taso su tafi, ta miqe cikin kasala da damuwa. Liman da Mal. Kalla suka tashi suma suka fita daga zauren, suka samu mutanen qauyen sun yi sansani a gefe guda ana ta mayar da zance ga wadanda basu xo da wuri ba. Wadanda ba a yi a gaban su ba.
¤
Mai unguwa Mal. Kalla ya daga murya ya dakawa samarin tsawa ya ce dasu.
¤
"Mun sallami kowa, duk ku bar nan wurin, mun warware wannan matsalar da ta faru mun fahimci juna, kada in bude ido in sake ganin wani a qofar gida na."
¤
Mutane suka fara darewa suna tafiya qofar gidajen su, wadanda kuma suke a gidan mai unguwa kuma suka shiga cikin gida yara da manya. Mal. Buba ne kawai da yake tsaye ya toge a waje daya yana ta harare-harare ya qi yin ko gezau daga inda yake.
¤
Dakta Hamza ya matsa wajen motarsa, ya dubi irin ta'adin da matasan suka yi masa, duk sun farfasa masa gilasai da fitilu, sun mokada bayan motar da duka, ya bude ba tare da ya nuna alhinin abin ba, yasa dan mabudi ya tayar, ganin haka sai Hafsatu matarsa ta zagaya daya 6angaren ta shiga ta zauna ita ma.
¤
Dakta Hamza ya tayar da motar ya tuqa suka yi kwana. Mal. Kalla da Liman da Mal. Buba suna tsaye suna kallon su. Kafin wani daga cikin su ya samu damar daga hannu yayi musu magana tuni har Dakta Hamza ya fige ta sun sheqa aguje. Duk da haka sai da Liman da Mal. Kalla suka dagawa motar hannu. Kafin su yi nisa ne Hafsatu ta juyo ta dubi mijin nata ta ce dashi.
¤
"Ya zaka tafi ba muyi ko sallama da Sadiya ba? Ai ba ita tayi mana laifi ba Iyayenta ne suka yi mana."
¤
Dakta Hamza ya dube ta shima ya ce da ita cikin fushi.
¤
"Na tsane ta kamar yadda na tsani kowa a cikin wadannan qauyawan iyayen nata. Bana son in sake jin kin ambaci sunan ta a gaba na daga ynx har abada."
¤
Hafsatu ta tambaye shi cikin karayya.
¤
"To amma yaya kake jin makomar soyayyarsu zata kasance ita da Khalifa?"
¤
Dakta Hamza ya fada da motar cikin wani dagwalon ta6o ya fantsama a jikin motar ya qara mata muni ya sake juyo ga Hafsatu ya ce da ita cikin gargadi.
¤
"Kada in sake jin kin hada qanina da wannan yarinyar wacce ta fito daga irin wannan qasqantacciyar xuri'ar, ba Khalifa ba auren wannan yarinyar har abada."
¤
Hafsatu ta ci gaba da kallon shi cikin kaduwar abin daya fada, ta san wannan hukuncin da ya yanke a ynx zai iya tarwatsa jin dadin Khalifa da Sadiya
¤
¤
Lp=27¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
27
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun Taska
¤
¤
Hafsatu ta ci gaba da kallon shi cikin kaduwar jin abin da ya fada, ta san wannan hukuncin da ya yanke ynxn zai iya sanadiyyar tarwatsa jin dadin Khalifa da Sadiya.
¤
¤
**
*
¤
¤
Da tafiyar Dakta Hamza a cikin fushi shi da matarsa, sai Mal. Kalla ya tasarwa Dan uwansa Mal. Buba dake tsaye gefe guda da fada, yana cewa.
¤
"Bai kamata kuyi irin wannan danyen aikin ba Buba, ynx ga irin abin daya jawo, mutanen nan basu da laifi, mutanen kirki ne, ba qaramin taimako suka yiwa Sadiya ba.
¤
Mal. Buba ya ce dashi.
¤
"To amma yaya ai dai a gabanka Inna taxo ta fada mana abin da aka fada mata a wajen aiki, ni mene ne laifina.?"
¤
Liman ya ce dasu.
¤
"Ya kamata ku shiga cikin gida ku daidaita al'amarin nan Mai unguwa. Wannan abu da akayi bai yi daidai ba, ni zan je masallaci lkcn sallah yayi, sai kun xo."
¤
ya tafi ya bar su a wajen, da tafiyarsa suka shiga gida. Suka samu mata sun zagaye Sadiya a tsakar gida an debo wuta a kasko, ana ta yi mata turare, tayi xufa tana ta xubar da hawaye, sun hana ta ko motsawa daga inda take.
¤
Mai unguwa ya daka wa matan tsawa ya kore su, ya ce da Sadiya ta xo daki ta same shi yana son ganin ta. Ta taso tana share hawaye, kafin su shiga turakar Mai unguwar ne. Inna Gaje ta fito daga cikin dakin da aka sauketa, tayi xufa tayi sharkaf ta fara kwaratsi tna cewa.
¤
"Wa ya ce ta tashi ana yi mata turare ba a gama ba? Musamman fa naxo dashi tun daga gida, maganin wadanda ba a gani ne, qawata Gude ta bani ta ce a tarbi hayaqin."
¤
Mal. Kalla da yake ya san halin tsohuwar, sai ya ce da ita cikin lallashi.
¤
"Ki yi haquri Inna, ynxn nan zata dawo."
¤
Tsohuwar tayi tsaki ta juya ta shiga daki, Sadiya ta bi mhaifinta suka shiga cikin dakin, da xuwan shi ya zauna akan buxun shi ita kuma ta zauna a qasa har ynx bata daina kukan da takr yi ba. Bayan ya tattara hankalinsa wuri guda ya ce da ita.
¤
"To Sadiya, wannan bala'i dai duk ke kika jawo shi, a ce ana zaune qalau ki tsallake kiyi tafiyarki babu amo babu labari? Mai ya kaiki yin wannan taqadarcin? Ke kina jin kin kyauta kenan?
¤
Sadiya ta share hawaye ta ce da mahaifinta.
¤
"Ka yi haquri Baba, ni kaina na san nayi kuskure, amma har ga Allab bana son mutumin nan da kuka bani, ba zan iya zama dashi ba, ban san lkcn da xuciyata ta jani har na gudu ba na fada cikin daji da daddare. Shi ne wadannan mutanen da ka fanni mun xo tare dasu suka tsinceni, tun lkcn ina hannun su, ba yawon dandi na fita ba, mutanen kirki ne, sun yi mani halacci mai yawa.
¤
¤
Lp=27part B¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
page
27part B
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
Mal. Kalla ya ce da ita.
¤
"Abu ne duk yaxo cikin rashin fahimta, kafin in xo shi Buba ya tasar masu da hauragiyarsa ya sa yara sun yi masu cin kashi yadda suke so, sai da muka zauna da shi wannan Dafta....yake ko? Sai na fahimci mutum ne sosai duk sai naji kunya da bayanin da yayi mani. Ita kuma Inna dana same ta da wannan magana sanda aka neme ki aka rasa, ita taxo da wannan bayanin ta ce taje wajen wata mata, an yi mata duba cewar wai mayune suka sace ki, da na san abin haka zai zama kin ga ba zan je in jajubo Inna ba muna zaman zaman mu lfy, gashi ynx taxo duk ta hautsina abu. To kuskure dai a nan dukanmu mun yi shi kowa yana da laifi, mu muna da laifi da muka tilasta aurenki alhalin mun san baki so. Ke kuma laifin ki da kika gudu aka rasa ki, ita kuma Inna Gaje da taje wajen bokarta suka yi ta surqullensu aka fadi mata qarya, taxo ta fadiwa mutane kowa ya zauna a kai."
¤
Mal. Kalla mai unguwa ya numfasa.
¤
"To amma tunda mun ga haka ba zamu sake yarda wannan matsalar ta kuma faruwa bam, dole ne miyi wa tufkar hanci, sji Sarkin noma bayan tafiyarki ya kawo takarda ya ce mana ya sake ki."
¤
Ya waiga wani 6angare daya tara irin masara a totuwa, ya tona qarqashin wata leda ya ciro takardar ya miqa mata, ta sa hannu ta amsa. Sadiya ta warware takardar ta karanta ta ga Sarkin noma ya sake ta saki daya, taji farin ciki ya cika xuciyarta, ta tuno qaryar da tayiwa su Hafsatu cewar mijinta ya sake ta a labarin da ta basu ashe abin ya tabbata da gaske, da ace ta san da wannan takardar da tuni ta dawo gida, dama qiyayyar da take yiwa Sarkin noma yasa ta gudu, kuma sbd ganin akwai aure akanta shi yasa ta qi sakin jiki da Khalifa, sai ynx da ta amshi takardar sakin daga hannun mahaifinta ta ji soyayyar Khalifa ta buwayi xuciyarta.
¤
Ta tuno yadda yake son ta kamar ya hadiye ta, da kalaman da yake furta mata masu sanyaya xuciya, ta tuno sanda yake koya mata mota, musamman yake xuwa da yamma idan ya dawo daga makaranta su shiga cikin wata unguwa mai qarancin jama'a da ababen hawa. A can yake bata kan motar yana nuna mata yadda zata yi, har ta iya, har ta fara hawa titi ita kadai ba tare dashi ba.
¤
Babu shakka ya cancanta taso Khalifa, ko ba komai ta san idan ta aureshi zata yi nisa da gida, ba zata riqa ganin irin wadannan ban haushin ba dake faruwa a qauyen su.
¤
Mai unguwa ya ce da ita ta tashi ta fita ya yafe mata, ta je samu sauran iyayen nata suma ta roqe su gafara, sbd kowa ya shiga damuwa a dalilin guduwarta.
¤
Sadiya ta shiga cikin gida ta samu mahaifiyarta da sauran kishiyoyinta ta gaishe su ta ce su yafe mata tayi kuskura. Tun kafin ta rufe baki suka ce da ita a tsorace sun yafe mata duniya da lahira, suka ce bata yi musu komai ba. Sbd har ynx a zaton su aljana ce ko mayu ne suka kama ta, kuma suna tsoron ko sun bata qanqara ne ta hadiya, ynx ita ma in taso zata iya kama mutum ta lashe shi ya mutu.
¤
Kowa ya riqa baya-baya da Sadiya suna jin tsoronta, amma fa ban da Inna Gaje wacce tace tana taqama da qawarta Gude mai bori, ta ce shege ka fasa, Dan halas sai yanka!"
¤
¤
**~**
¤
¤
Da komawar Dakta Hamza da Hafsatu gida qarfe biyar na yamma sai suka samu Khalifa zaune a qofar gida yana ta zaman jiran qarasowar su. Tunda yaga sun qaraso da fasasshiyar mota ya miqe cikin fargabar abin daya faru dasu, motar tayi haka.
¤
Suka qaraso Mai gadi ya bude masu qofa, Dakta Hamza ya cusa motar ba tare da ya waiwayi mai gadi ba wanda yake yi masa sannu da xuwa. Khalifa ya shigo gidan, ya biyo bayan su da sauri, da tsayiwarsu suka bude suka firfito.
¤
Tun kafin Khalifa yayi musu sannu da xuwa Dakta Hamza ya je har gaban sa ya fara gargadinsa a fusace.
¤
"Ka cire wannan yarinyar a xuciyarka, ba kai ba ita har abada, na fada maka ka cire ta a xuciyarka...."
¤
¤
Lp=28¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
28
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
"Ka cire wannan yarinyar a xuciyarka ba kai ba ita har abada, na fada maka ka cireta a xuciyarka."
¤
Dakta Hamza ya wuce cikin gida a fusace, Khalifa ya fara inda-indar rashin fahimtar abin daya faru, ya tsayar da Hafsatu wacce ita ma take qoqarin shiga gida.
¤
"Me ya faru Anti...me ya faru?...ina Sadiya take? Hafsatu ta ce dashi.
¤
"Khalifa iyayen yarinyar nan basu san mutunci ba, sun yi mana rashin mutunci. Sun zage mu ta uwa ta uba, dubi yadda suka yi mana da motar mu."
¤
Khalifa ya kalli yadda motar ta koma, ya sake kallon Hafsatu.
¤
"me ya faru suka yi maku haka Anti? Me ya hada ku dasu?"
¤
Hafsatu ta ce dashi.
¤
"Khalifa kada ka so kaga yadda suka yi mana, kawai abu mafi alheri a garemu baki daya shi ne ka rabu da Sadiya ka cire ta a xuciyarka."
¤
Hafsatu ta shige cikin gida, Khalifa ya bita cikin rudani, da suka je falo ne suka samu Dakta Hamza ya fara ciro wasu hotuna dake jikin bango wadanda suka yi tare da Sadiya lkcn zamanta a gidan, ya riqa daga hotunan yana maka su da qasa suna farfashewa.
¤
Khalifa ya tsaya a gefe guda yana kallon yayansa a tsorace. Bayan Dakta Hamza ya gama rorrotsa gotunan da suka yi tare da Sadiya ne ya juyo ya ce da matarsa Hafsatu.
¤
"Ki je dakinta ki kwaso duk wasu kaya da ta bari a kaisu bola a qona su, ki bincika ko ina a gidan nan kome ki ka gani nata, indai kin san idan na gan shi zai tuno mani da ita, ki yi waje dashi, bana son in ga komai da zai riqa sawa ina tunowa ta zauna a gidan nan. Zan yi wa (A and A motors) waya ynx, su xo su sayi motarta ko nawa ne an sayar masu, su dauke motar a yau din nan. Sannan kuma bana son in sake jin wani ya ambaci sunanta a cikin ku (Just forget her)."
¤
Dakta Hamza ya wuce dakinsa a fusace. Hafsatu ta tafi dakin da Sadiya ta zauna ta fara tattaro kayan da ta bari tana watso su waje don ta cika umarnin mijinta.
¤
Khalifa ya tafi dakinsa jikin sa ba qwari, da xuwan shi ya jingina a jikin qofa ya fara xubar da hawaye a lkcn guda yana tunanin Sadiya, masoyiyar da bashi da tamkarta a xuciyarsa. Har dare yayi bai daina kuka ba, ya debo hotunan shi da Sadiya ya xube su a gaban shi. Har dare yayi bai daina kuka ba. Yana kallon hotunan yana kukan baqin ciki.
¤
A lkcn ne ya tabbatarwa da kan shi cewar, ko zai rabu da kowa a duniya to ba zai rabu da Sadiya ba.
¤
¤
**
*
¤
Liman yasa aka kira Sadiya yayi mata fada sosai, ya ce bata kyauta ba. Gashi a dalilinta an ci mutuncin mutanen da basu ji ba basu gani ba, duk da taimakon da suka yi mata. Ya ce da ita.
¤
"Ynx tunda kin samu takardar sakin ki da tsohon mijinki Sakin noma ya kawo, sai ki fara yin Iddarki, idan kika gama sai ki fito da mijin da kike so a yi maki aure, ba zamu sake a maimita abin daya faru a baya ba, ynx auren soyayya za a yi maki Sadiya. Tashi ki tafi Allah Ya yi maki albarka."
¤
Sadiya ta tashi ta koma gida cike da farin cikin albishir din da aminin mahaifinta a qauyensu yayi mata. Duk da abubuwan da suka faru sai ta fara tunanin hanyar da zata bi ta kira su Anti Hafsatu da mijinta ta basu haquri ta fada musu albishir din da iyayenta su ka yi mata na bata wanda take so a halin ynx.
¤
Sadiya ta kira layin Dakta Hamza taji tun daga kamfanin ana yi mata gargadin idan ta sake kiran layinsa za a kulle mata layinta haihata-haihata,tayi mamakin jin faruwar haka, ta nemi lambar Antinta Hafsatu ta kira ta, ita ma ta ji an ce kada ta sake kira. Tsoro ya kama Sadiya, ta san indai ba fushi suka yi ba suka toshe layikansu, babu abin da zai sa haka ta faru. Tayi tunanin ta kira Khalifa amma ta fasa sbd dalilai biyu.
¤
Dalili na farko bata san abubuwan da suka faru ba da Dakta Hamza ya koma gida shi da matarsa bayan wulaqancin da 'yan uwanta suka yi masu. Na biyu kuma shi ne ynx ta shiga cikin Iddarta ta gsky. Bai kamata ta ci gaba da mu'amullar soyayya ba, har sai ta gama nan da jini uku.
¤
Sadiya ta kasa yin bacci a daren tana fargabar makomar soyayyarta da Khalifa a sakamakon sa6anin da ya faru tsakanin Yayansa da 'yan uwanta. A ynx idan har bata auri Khalifa ba, bata san gagarumin hadarin da zai faru ga rayuwarta ba.
¤
¤
**~**
¤
¤
A kwana daya kawai Khalifa ya rikice, ya kasa samun nutsuwa ya kasa cin abinci, ya daina yiwa kowa magana a gidan. Da Hafsatu ta je dakinsa ta same shi a cikin wannan mawuyacin halin. Sai ta ji tausayin shi ya kamata. Ta fara yi masa nasiha tana bashi haquri tana cewa.
¤
"Na san kana son Sadiya Khalifa, amma aureta da kai ba zai yiwu ba. Da a ce da kai muka je ka ganewa idanunka abin da muka gani, da tuni ka fahimci dalilin da yasa yayanka ya ce ka rabu da ita.
¤
Khalifa ya kawar da kan shi ya ce.
¤
"To amma Anti ita Sadiya mene ne laifinta, 'yan uwanta basu suka yi ko mene ne ba, ai ba laifinta bane."
¤
Hafsat ta ce dashi.
¤
"Akwai banbanci tsakanin soyayya da kuma maganar aure Khalifa. Da a ce ba aurenta kake son yi ba.
¤
¤
Lp=29¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
29
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu ihsaan
madugun taska
¤
¤
Akwai banbanci tsakanin maganar aure da maganar soyayya. Da a ce ba aurenta kake so kayi ba, ba zamu ta6a damuwa da abin da suka yi mana ba. To amma aure yana nufin hada xuri'armu ne da xuri'arsu. Kuma a zahiri ta kowacce fuska basu cancanta damu ba. Aure tsakaninka da Sadiya ba zai yiwu ba Khalifa. Ka haqura da ita mana!"
¤
Khalifa ya ce.
¤
"ko yaya xuri'arsu take ni ina sonta. Halinsu daban ita ma halinta daban. Kuma idan na aureta ba xuri'arsu baki daya na aura ba. Da ita kadai zan zauna a matsayin matata, don haka ni Sadiya bata yi min laifi ba.
¤
Hafsatu ta dubi qanin mijin nata, ta tabbatar yayi nisan da ba zai ji kira ba akan Sadiya ta tambaye shi.
¤
"To yayanka bai amince ba, kuma duk duniyar nan baka da kamar shi, ya zaka yi?"
¤
Khalifa ya ce a fusace.
¤
"kawai ki fada masa ya sauya ra'ayinsa muje a sami Iyayenta a sasanta wannan rigimar, idan kuma ba zai amince ba to ni gsky zan tafi garin su Sadiya da kaina in nemawa kaina aurenta."
¤
Hafsatu ta gargade shi.
¤
"Kai kanka ka san yin hakan ba qaramin sa6ani zai janyo maka ba tsakaninka da dan uwanka, kayi gaggawar sauya tunani akan wannan hukunci da kake so ka yanke."
¤
Khalifa ya kausasa murya ya ce.
¤
"Akan Sadiya ba wani abu da zan canza, ina sonta, kuma ba zan daina sonta ba, ko kuyi mani fatan alheri ku taimakeni in mallaketa, mu zauna tare, ko kuma idan kun qi amincewa, hakan ya zamo sanadiyyar rabuwata da ku."
¤
Hafsatu ta tashi a cikin sauri taje ta samu mijinta Dakta yana shirin fita xuwa asibiti. Ta ce dashi.
¤
"Dakta akwai qatuwar matsala da ta kunno kai a gidan nan, ya kamata mu zauna mu nemowa kanmu mafita mu maganceta tun kafin al'amarin ya fi qarfinmu."
¤
Dakta Hamza ya dubeta cikin rashin fahimta.
¤
"wacce irin matsala ce wannan?"
¤
Hafsatu ta ce dashi.
¤
"Akan al'amarin Khalifa da yarinyar nan ne, yana nan ya kafe wai shi lallai zai bita idan ba zamu je mu sasanta da iyayenta ba.
¤
Dakta Hamza bai dauki maganar da muhimmanci ba, ya ce.
¤
"To sai me idan ya bita garin nasu? (Let him go) in dai ina raye to ba zan ta6a sa hannu Khalifa qanina ya auri wannan yarinyar ba. Da in barshi ya auri wannan yarinyar wacce iyayenta basu san mutuncin mutane ba. Basu san darajar kowa ba sai qauyawa irin su, na gwammace ya rasa ranshi in haqura dashi har abada."
¤
Hafsatu ta tsaya tana kallon mijinta cikin xullumin abin da yake fada. Ta san shi wajen tsattsauran ra'ayi da kafewa akan abin da yasa a ranshi. Yadda ta tabbatar yana son Khalifa, tunda har ya iya yanke wannan hukuncin to ta san duk duniya babu mai iya sanya shi ya janye kalaman shi.
¤
Dakta Hamza ya ce da ita a fusace.
¤
"je ki ce da shi yaxo ina kiransa. Zan fada masa ni dashi don ya ji da kunnensa. In yaso duk abin da yaga yafi dacewa sai ya je yayi.
¤
¤
Lp=30¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
30
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
In yaso duk abin da yaga yafi dacewa yaje ya yi."
¤
Hafsatu ta tafi jikinta a sanyaye ta koma dakin Khalifa ta same shi a zaune ya kafa kan shi akan guiwar sa yayi shiru yana tunani.
¤
"Kaxo Dakta yana kiranka."
¤
Khalifa ya taso ranshi a 6ace, ya biyo matar Yayansa, suka nufi falon inda Dakta ya fito yana jiransu shi kadai sai zance xuci yake yi, ya kasa samun natsuwa. Da suka shigo ne Hafsatu ta koma gefe ta qura masu ido tana sauraren abin da zai biyo bayan wannan ganawa mai zafi da zasu yi wacce basu ta6a yin irinta ba a tarihin zamansu.
¤
Dakta Hamza ya ce da Khalifa qaninsa kai tsaye.
¤
"Tun jiya da muka dawo na baka umarnin ka rabu da wannan yarinyar, ka cireta a xuciyarka. Ina fatan kayi hakan?"
¤
Khalifa ya ce dashi.
¤
"Ba zan cireta a rai ba, ba zan iya cireta a raina ba. Ina son ta, kuma bana jin zan iya daina sonta."
¤
Dakta Hamza ya nuna masa yatsa cikin hargowa.
¤
"Kai qaramin yaro, baka da hankali, kuma baka san komai ba a game da duniya. Tun kana jariri nake kulawa da kai, ni na baka ingantaccen ilimi, ni na samar maka da duk wani jin dadin rayuwa da kake taqama dashi. Ashe har

Please Login or Register in order to submit comment