Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sadiya ita ce mai juriyar daukar kwaramniyar yara, Hafsatu ta bar mata yaran, koda yaushe ynx suna tare da Sadiya. Barci kawai yake raba su.
¤
Tun a ranar da Hafsatu ta gargadi Khalifa da kada ya kuskura ya yiwa Sadiya zancen soyayya, basi sake nuna mata ko a fuska cewa yana son ta ba. Idan ya je makaranta ya dawo baya yin nisa da gida. Yana xuwa ya zauna a falo su yi hira. Soyayyar Sadiya kullum tana sukar xuciyarsa. Haka nan yake haqura yana jurewa. A cikin littafi kullum yana rubuta yawan kwanakin da Sadiya tayi a gidan, don idan lkcn gama iddarta yayi ya fito ya sanar da ita. Ya bayyana mata aniyarsa a fili.
¤
A ranar da Sadiya ta kai kwana hudu da xuwanta gidan ne Dakta Hamza ya dawo....
¤
¤
Lp=11
¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
11
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
A ranar da Sadiya tayi kwana hudu da xuwanta gidan ne, Dakta Hamza ya dawo, Mai gadi ya bude faffadan gat din gidan da ya ji hon din motarsa, da bude qofar, sullu6e6iyar farar motar sa ta shigo, wacce keda duhun gilasa, ba a iya ganin abin dake ciki, mai gadin ya gaishe shi.
¤
Bayan ya kai motar inda suke ajiye motoci a gidan ne yayi saurin bude qofar motar ya fito.
¤
Dakta Hamza dogo ne fari wanda yake da qananan idanuwa dake a tsaye, yana da saurin magana da kuma yawan qorafi idan wani ya shiga lkcnsa.
¤
A wannan dawowar da yayi yana sanye da tsakatsakin wando, shi ba dogo ba shi ba gajere ba, tare da riga mai gajeren hannu, da hula hana sallah kalar takalmin dake a qafarsa (Canbas) yawanci irin wannan shigar yafi yinta ne idan yana hutu a gida kafin ya koma aiki.
¤
Da yake Hafsatu ta ji shigowar motarsa, nan da nan ta fadiwa Sadiya cewar ga mijinta nan ya dawo. Ta fadiwa Alfat wanda tun dawowarsu daga makaranta yake zaune a falo, Hafsatu da 'ya'yanta tare da Sadiya suka fita xuwa farfajiya gidan, a daidai lkcn da Dakta Hamza ya rufe qofar motar ya tunkari cikin gidan.
¤
Hafsatu wacce ke a gaba ita ta fara yi masa lale marhabin tana dariya, tayi sauri ta ja baya da taga ya nufo ta gadan-gadan yana qoqarin ya kamota ya rungume. Bata son yana yi mata haka a gaban 'ya'yanta, tana gargadin sa kullum kan ya riqa kulawa da mu'amullar soyayyarsu, sbd 'ya'yansu sun fara girma, yau kuma ba yaran kawai take jin kunya ba, har ma Sadiya baquwarsu, tunda yarinyar tana girmama ta, tana bin ta kamar mahaifiyarta.
¤
Hafsatu ta dakatar da mijinta ta hanyar mayar da hankalinta kan Sadiya.
¤
"Sadiya ku gaisa da mijina Dakta Hamza."
¤
A lkcn ne ya haqura da kamo matar tasa, ya kalli Sadiya da fuskar rashin fahimtar ko ita wace ce."
¤
"Sannun ki 'yanmata."
¤
Alfat ya rugo ya kaa hannun mahaifinsa, Abba wanda bacci bai gama sakin sa ba a lkcn da Hafsatu ta fito dashi daga falo bai yi yunqurin xuwa wajen mahaifinsa ba. Dakta Hamza yasa hannu ya lakaci kumatun Abba yana tambayarsa dalilin da yasa bai yi masa magana ba.
¤
Suka dunguma suka koma cikin gida tare, Dakta Hamza ya tambayi Hafsatu.
¤
"Khalifa ya je makaranta ne?"
¤
Hafsatu ta ce.
¤
"Daxun nan ya tafi, ya ce ba zai dade ba zai dawo, ya ce yau basu da lkc mai yawa."
¤
Bai jira sai sun shiga cikin daki ba ya tambayi Hafsatu.
¤
"Wannan wace ce naga kun saba da ita a cikin gidan nan? Ko a cikin 'yan uwanki ne dake a qauye kuka taho da ita?"
¤
Hafsatu ta ce dashi tana murmushi.
¤
"Abu na farko da zan fara fada maka kenan idan kayi haquri, amma sai bayan ka ci abinci ka huta."
¤
Hafsatu ta janye Alfat da Abba ta miqawa Sadiya su, ta ce da ita su tafi can dakinta kada ta barsu su xo su dame su. Ta shiga dakinta ita da mijinta Dakta Hamza. Sun shiga da awa daya, ya ci abinci, ta bashi laarin Sadiya tun daga farko har qarshe.
¤
Dakta Hamza bai nuna mata damuwarsa akan abin da tayi ba, yana bata cikakken 'yancin yin komai da take so a gidan. Tun kafin ta gama bashi dogon labarin, yana zaune yana cin abinci yana gyada kai cikin gamsuwa, ya ce da ita.
¤
"Na fahimci dai a taqaice yarinyar tana cikin matsalar rayuwa, kina son taxo ta zauna tare damu, wannan ba wani abu bane, yana faruwa a ko'ina."
¤
Hafsatu ta sake cewa da mijinta.
¤
"Kuma a yadda naga take-taken Khalifa yana son yarinyar nan, ni na dakatar dashi nace ya jira sai ta gama iddarta, sannan kome zai ce da ita sai ya fada."
¤
Dakta Hamza ya ce da matarsa.
¤
"Ba laifi bane, kowa zai iya za6ar macen da yake so a duniya, yana iya son ta ba laifi yayi ba."
¤
Hafsatu tayi dariya da ta ji yadda mijinta ya amince da Sadiya ba tare da wani dogon bincike ba. Bayan ya yi wanka ya huta, sai ya tara su a falo, Sadiya ta xo ta zauna ta sunkuyar da kanta tana jin kunya.
¤
Dakta Hamza ya ce da ita.
¤
"Na samu labarinki a wajen matata, kuma na tausaya maki....so....wannan ba wani abin damuwa bane, zamu taimake ki, kuma daga yau kin zamo daya daga cikinmu, kina da 'yancin yin komai a gidan nan kamar kowa, ki saki jikinki kada ki damu."
¤
Sadiya ta ce dashi a sanyaye.
¤
"Na gode Dakta, Allah Ya saka da alkairi."
¤
Dakta Hamza ya ce.
¤
"to Sadiya, a yadda muke zaune a gidan nan, kamar yadda kika xo kika same mu, kowa yana da 'yancin kansa wajen more rayuwa, kowa yana da motarsa, kowa yana da (Account) dinsa a bankin da yake so, ban yarda wani ya takurawa wani ba, ynx idan Khalifa ya dawo, anjima zaku je wajen da ake sayar da motoci, ki za6i irin motar da kike so a saya maki gobe kuma zaku je banki a bude maki naki (Account) din a xuba maki kudin kashewa, kome kike so ba sai kin tambayi kowa ba. Ina fatan kin fahimce me?"
¤
Sadiya ta yi masa godiyar wannan kyautar bazata da yayi mata, Dakta Hamza ya ce dasu.
¤
"idan ba sauran wani abu zan fita, tun daxu asibiti ke ta yi mani waya.
¤
Hafsatu ta ce.
¤
"Sai ka dawo."
¤
Dakta Hamza ya tashi ya barsu zaune, kafin ya fita daga falon ne faskekiyar tibinsa dake watso shirye-shirye...
¤
Lp=12¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
12
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
Madugun Taska
¤
¤
Dakta Hamza ya tashi ya barsu a zaune, kafin ya fita daga falon ne, faskeken tibinsa dake watso shirye-shiryen wata tashar yahudawa suka nuno wata matashiyar mawaqiya tana cashewa da daddadar waqarta hade da yin rawa.
¤
Dakta Hamza ya fara bin waqar wacce da alama ya dade da sanin ta, bayan sun kai kimanin daqiqa arba'in suna yi tare da mawaqiyar, sai ya tafa mata, sannan ya nuna ta da hannu ya ce cikin harshen turanci.
¤
"I like this song."
¤
Ya duba agogo sannan yayi saurin ficewa da gudu ya tafi wajen aikinsa. Sadiya wacce kunya ta sa tayi saurin duqar da kanta qasa ta kasa dagowa. Sai da ya fita ne Hafsatu ta dafa ta tana murmushi ta ce da ita.
¤
"Sadiya ki saki jikin ki daina jin kunya in dai Dakta ne to baki ga komai ba, sa'a aka ci bai tsaya yayi rawa ba. Haka yake, mu mun riga mun saba, komai yayi bama damuwa."
¤
Sadiya tayi murmushi ita ma, duk da haka kunyar bata sake ta ba. Sbd bata saba ganin manya suna haka ba a qauyensu, yaushe yara ma suka isa su zauna a kusa da manya, idan ba kirawo su akayi ba za a yi masu fada? Ta girgiza kai cikin mamaki, da su Mal. Kalla iyayenta zasu ga Dakta Hamza a cikin 'ya'yansa. Da babu abin da zai hana masu su yanke jiki su fadi. Don kuwa zasu ce qiyama ne ta tsaya.
¤
¤
HE! HE!! HE!!!
QAUYE GARIN SU KARE, KARA KUMA YA CE. A'A, BA GARINMU BANE, GARIN SU JAKI NE, SHIMA JAKI YA CE KAI SHI AKA YI."
¤
¤
------------------------------------------------------
¤
¤
DUK abin da ake yi har aka yi wata daya ana ta 6oye-6oye, ba a yarda Innan Gaje ta samu labarin 6acewar Sadiya ba.
¤
Inna Gaje qanwa ce ga mahaifin su Mal. Kalla, wacce ta rage ita kadai a raye a cikin iyayen su. Qaqqarfar tsohuwa ce 'yar kimanin shekara tamanin da biyu a duniya, wacce take zaune a qauyen Kufan qaura, bata da sauran wasu 'ya'ya a raye sai dai wasu jikokinta da suka yi aure suka hayayyafa, wannan yasa zama irin na qauye Inna gaje bata samu gatancin wanda zai riqe ta ba, har ynx wani tsoho take aure a qauyen Kufan qaura, wanda kullum da safe idan rana tayi, sai jikokin shi sun dauke shi sun fito dashi sun shanya shi a rana, idan hantsi ya daga jikin shi ya dan yi qarfi sai a mayar dashi inuwa, a lkcn ne kuma zai fara surqullensa na rudun tsufa, yana tuhumar yara kudin daya aikesu su sayo masa goro, ko kuma ya ce sun xo sun kwashe masa qosai ko daya bai ci ba, su kuma suna yi masa dariya don kuwa basu san da wannan lamari ba.
¤
Innan Gaje bata da sana'ar da ta wuce waina da miya a qauyen, idan aka ce kuma kaka tayi an fara fitar da amfanin gona to ita ce uwar tawagar aiki. Masu kudin qauyen ita suke xuwa su samu su roqeta ta hada masu xugar kawar da amfanin gona.
¤
Akwai dalilin da yasa duk wasu manoma manya da qanana suke bawa Inna Gaje ragamar aikin su idan ya taso. Tsohuwa ce wacce bata son wasa da kasala. Duk 'yanmatan dake qauyen sun san da haka. Idan yarinya tayo shirin aiki ta tambayeta ko za aje da ita. Innan Gaje sai ta ja mata kunne ba a yi mata iya ashege. Idan yarinya ta san ba aiki zai kaita ba, to tun wuri gara ta tsaya a gida uwarta ta more ta, kada ta bita aiki.
¤
Duk da yawan shekarun tsohuwar idan ta dauki sanda ta fara fyadi, to sai qato ya gaji ita tana yi wuni da kwana, ko a jikinta bata gajiya. Idan aiki yayi aiki. 'yanmata musamman irin wadanda aka sawa rana suka fara waqoqinsu na banza suna shewa, suna ganin su sun isa, sun kusa tafiya dakin aure. Inna Gaje dasu tafi tsama, da ta ji sun fara waqoqin au, zata rugo aguje da qaton iccenta, duk yarinyar da ta samu bata gudu ba sai ta barta kwance da duka.
¤
Idan ta tarwatsa su sai ta ja tunga ta fara aikinta na balbala ashariya, 'Yanmata suna a tsaye cirko-cirko sansani guda suna kallonta suna jira ta lafa kafin su dawo su ci gaba da aikinsu.
¤
Asalin tsohuwar dama tun kakanninsu maguzawa ne, ita kanta fuskarta cike take kwaya-kwayan tsage na maguzanci. Da yake baqa ce mai qatuwar fuska da qatuwar murya, ko rigima yara suke yi da ance ga Inna Gaje nan to sun daina kenan, yawanci da ace da yara gata nan har gara ace masu ga mai allura nan, ko kuma ga mai kaciya nan ya taho. Sbd idan yaro yayi laifi ta damqe shi ta fara casa shi, to ko uwar yaro bata isa ta amshe shi ba, sai ta gaji don kanta tayi haquri.
¤
'Yan uwanta su Mal. Buba da Mal. Kalla mahaifin Sadiya basa so take xuwa qauyen su, da wahala taxo tayi minti goma ba a san taxo ba. Mutum komai girmanshi zata fada shi da zagi a gaban yaran shi da jikoki, don tana ganin ita ce babba, kuma idan taxo ta samu labarin yaro yayi laifi a gidan, to kowanene idan ta tasa shi da zagi sai an bata haquri. Gata da ra'ayin gargajiya, kome za ayi sai an riqa tuna baya yadda suka yi a rayuwarsu.
¤
Idan taxo ta iske wani saurayi yaxo wurin wata budurwa suna zance da rana ko da yamma, to wadannan yara sun shiga uku a ranar, tafi son sai dare yayi. Kuma ita ma hirar kada su yi kusa da kusa, idan yarinya ta fito sai ta toge a qofar gidansu, shi kuma saurayin sai ya tsaya a nesa qofar wani gidan.
¤
lp13¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
13
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska
¤
¤
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. Yin hakan ha'inci ne. A kula.
¤
¤
Idan yarinya ta fito qofar gidansu ta toge jikin qofa ta tsaya, sai shi kuma saurayin ya tsaya can nesa a wani qofar gidan, a haka take so taga yara suna hira, kuma idan saurayin yana magana sai dai yarinya ta juya masa baya yayi hira da qeyarta kome ya ce ba zata ce masa uffan ba. Amma idan Inna Gaje ta kama yarinya tana washe baki tana dariya a gaban saurayi, to lallai kuwa a ranar sai ta karya yarinya don kuwa zata ce gidan su basu gaji irin wannan rashin ta idon ba.
¤
Kada mutum ya yi tsammanin idan tsohuwar ta tsaya akan wani ra'ayi za a iya shawo kanta ta sassauta ko janyewa. Ba a xuwa a ce za a lallashi Inna Gaje idan tayi fushi. Kuma ba a roqonta alfarma. Idan ta lashi yatsanta ta dangwala shi a qasa ta nuna sama ta ce ga abin da take so, to mutane su bi kawai su huta. Tunda ko mutuwa za a yi sai dai a mutu, ita dai ba zata canza ra'ayinta ba.
¤
Shi yasa duk badaqalar da akayi akan auren Sadiya ba a je qauyen an fadi mata ba. Ko sha'ani ba a son ta xo, idan aka je qauyen aka fadi mata ga hidindimu da aka yi na aure-aure, sai ta ce, ai don an san bata da komai da zata kawo shi yasa ba a xo an fadi mata ba. Amma da an ga ta rufa ta ta da kai da abin duniya ai da ba za a riqa yin sha'anin ba a xo an fadi mata ba, to amma ba haka bane, masifarta kowa yake tsoro, shi yasa ba a son xuwa wajenta.
¤
Sai da aka yi wata guda da 6acewar Sadiya sannan Mal. Kalla ya yanke shawarar zai je ya fadiwa Inna Gaje, don kada abin ya yi yawa, da ta ji an yi auren Sadiya ba a kai mata ko goro ba, babu wanda bai sha tsinuwarta ba. Don haka Mal. Kalla ya samu qanin sa Mal. Buba ya ce.
¤
"wannan tashin hankali yayi yawa Buba, a ce yarinyar nan wata guda kenan babu labarin ta. Wanda zai ce mana ma yaga Sadiya bamu ganshi ba, to ya zamu yi? Za je Kufen qaura in samu Inna Gajr in fada mata halin da ake ciki, a taru baki daya a tasarwa wannan matsala, in da wani taimako da za a samu daga wajenta sai mu ji ko me ke nan.
¤
"To ba matsala Mai unguwa, amma gsky ina jin tsoron fadan Inna, kana iya xuwa ta rufar ma da zagi, ka san halin ta."
¤
Mal Kalla ya ce.
¤
"to ya za a yi. Komai zata ce gara dai a je a fada mata, idan muka je muka fada mata duk zagin da zata yi a can mai sauqi ne, idan kuma muka jira sai ta xo nan to a gaban 'ya'ya da jikoki zata zazzagemu."
¤
"to ai shi kenan, sai ka dawo."
¤
Mai unguwa Kalla ya nemi allura da zare ya dinke wata 6araka dake a sabuwar babbar rigar shi wacce keken shi yayi mashi ta'adi a wani dawowa da yayi sadakar bakwai ta wani gidan fulani dake nan kusa dasu. Bayan ya shirya ne yasa matansa suka nemo leda ya yi mata guxurin furar da aka daka masa a gidan, ya daureta a bayan keken sa ya kama hanyar qauyen Kufen qaura.
¤
kafin a kira sallar axuhur ya kai quyen, ya iske Inna Gaje bata a gida, wai sun je tsinkar gyada amma gonar babu nisa. Wani matashin yaro da ya dawo kiwo ne ya raka Mal. Kalla gonar gyadar. Tun kafin su qarisa gonar gyadar ne Mal. Kalla ya ji muryar tsohuwar ta tasa wata budurwa a gaba tana kwashe mata albarka tana cewa.
¤
"tun safe aikin da kika yi kenan? Ko buhu daya baki cika ba don qaniyar ki? A haka za a tara kudin da za a saya maki kayan dakin? Ynx fa kuna ji samira ta tashi abar dari biyar ta koma dari bakwai da murtala biyu, shima an ce na bara murtala saiti daya murtala shida yake, amma bana sun koma murtala tara. A haka kike son a saya maki kayan dakin kina tsayawa wannan lalatar, tun safe wannan gyadar baki tsinki ko tiya ashirin ba? To zaki ci ubanki! Yarinya da ni kike magana, 'yar banza ana magana tana kallon mutane da shegun jajayen idanu kamar an taka kwado."
¤
Tsohuwar ta kai hannu ta kwashe budurwar da mari sai da yarinyar ta fadi qasa. Har zata sa qafa ta take ta, sai ta ji an ce mata tayi baqo. Ta daga kai ta hangi Kalla danta yana riqe da akwalarsa ya yi nadi akan sa, yana jiran ta gama yiwa yarinyar fada ta qaraso shima ya sha nasa, a ran sa bai fadda ran fushin yarinyar ya shafe shi ba. Da wahala idan ta ji dalilin xuwanshi in bata mare shi ba.
¤
Inna Gaje ta nufo inda yake tana balbala fada tana cewa.
¤
"Ina amfanin wadannan shegun yaran? Kowacce sai uwarta ta qura ido tana jiran yamma tayi a tashi daga aiki a basu lada su kai gida, da yaro ya koma bai tsinana komai ba ni suke jawowa baqin jini a ce ni ce ban matsa masu ba, to ni bana buqatar iya shege to kaji! In yarinya ta san ba zata zama jaruma ba ta riqa tsayawa a gida tana hucewa uwarta haushe ehe!!"
¤
Har ta kai wajen da Mal. Kalla yake bata yi shiru ba. Sai da ya kafe keke ya rage tsawo ya fara gaishe ta sannan ta dawo da hankalinta wajen shi ta ce dashi.
¤
"Kalla yau kai ne a garin namu, anga dama an waiwaye mu?"
¤
Mal. Kalla ya ce da ita cikin xullumi.
¤
"Ai da naje gidan ne aka ce kuna nan, Inna sannun ku."
¤
Ta tsaya qerere ranta a 6ace, shi kuma yana a durqushe ya dafa akwalar keken sa, ta....
¤
¤
Lp=14¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
14
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun Taska.
¤
¤
Ta tsaya qerere ranta a 6ace, shi kuma yana durqushe ya dafa akwalar kekensa, ta tambaye shi.
¤
"Wajen naku lfy lau ko?"
ya ce
¤
"Lfy lau Inna, duk sun ce a gaishe ku."
ta ce.
"Ya yaro mai quna da aka ce ya tsoma hannu a cikin talge, yaro na wajen Duduwa?
¤
Mal. Kalla Ya ce
¤
"Ya samu sauqi, an kai shi gari, ai har sau biyu uwar tana xuwa, sun yi mashi allura sun bashi magani."
¤
Tsohuwar ta riqe baki don mamaki.
¤
"Au ciwon har ya kai sai an yi allura? Ka ce quna ce ta uban gari yaro ya yi."
¤
Mal. Kalla ya ce.
¤
"kin san sha'anin asibiti ba irin namu na gida bane, su nasu da yake na turawa ne dole sai an bi qa'ida."
¤
Inna Gaje ta ce.
¤
"In banda sanaben tsiya da yin qunar da an je an nemi marke an daka an barbada mashi a hannun da tuni bai warke ba? Ni ban san irin wannan rashin jin magana naku ba Kalla, kuma kun fara biyewa 'yan zamani, in ban da haka a ce quna kawai sai an je asibitin gari, mu a zamaninmu me muke sha na bature? Ka dai ganni na ba shekara tamanin baya, amma qwayar bature daya bata ta6a shiga bakina ba, komai ya samu ga magunguna nan a kusa, ai ganewa ne ba a yi ba, shi maganin bature sai dai ya kwantar da cuta ta yi sauqi, amma a kawar da ciwo har abada sai gargajiya. To abu ne ya xo siyasar nan duk an xo, an watsar da komai na asali an koma na zamani. Ina amfanin wannan abu?"
¤
Mal. Kalla ya ce.
¤
"To Inna, ya za a yi? Sai haquri. Zamanin kenan ai."
¤
Bayan sun gama zantawa akan haka ne ya ce da ita. Inna na xo wajen ki ne kan wata matsala da ta same mu a nan gida."
¤
Mal. Kalla ya warware mata zare da abawar duk abubuwan da suka faru akan auren Sadiya da kuma guduwar da tayi, ya ce da ita a qarshe.
¤
"Yau kwanan wata daya kenan yarinyar nan bata ba labarinta, Inna mun rasa inda zamu sa kanmu muji dadi a duniyar nan, gashi mijin nata ya sake ta, ya kawo mana takardarta ya ce shi ba zai iya ba, mu je mu nemo 'yarmu, ba ruwan shi, mun yi neman duniya amma mun rasa ta har ynx ba dace ba."
¤
Inna Gaje ta murguza zagi sannan ta ce da Mal. Kalla a fusace.
¤
"Ai ba zaku dace ba dama, sbd baku kamo hanyar da zaku dace ba, dole ne ku riqa shan wahala Kalla."
¤
Sbd me kika ce haka Inna?"
¤
Tsohuwar ta daga murya kamar mai yi shela, ta ce.
¤
"Tuntuni me ya hana axo a fadi min ga halin da ake ciki? Da tuni ban je wajen aminiyata Gude mai bori ba? Duk halin da ake ciki a duniyar nan tana haska fitila a cikin qwarya za ta ganta. Ai Gude sha ynx ce magani ynx. Ni ba a ta6a ni sai dai kawai in naga dama in qyale mutum, ba irin aikin da Gude bata yi mani, kuma ina ganin nasara."
¤
"To Inna ai gani ynx nazo, mun bar komai a hannunki, wannan masifa ta ishe mu, ko barci bamu yi da ni da uwarta, yadda muka ga rana haka muke ganin dare."
¤
Inna Gaje ta numfasa ta ce.
¤
"Lallai Sadiya ta cika ta batse, ta nuna mana ta haifu, wato zaman da tayi a maraya shi ya 6ata ta haka? Ta yi mana wannan futsarar? To ku bar ni da ita zata dawo da qafarta za kuma ta hadu da ni, idan ta dawo zan xo in zauna a garin naku, a hannuna zata zauna, ni in ta isa tayi min iya shegen in gani, duk baku kuka saki yaran suka lalace ba?"
¤
Ta yiwa Mal. Kalla tatas, yana tsugunne yana saurarenta cikin ladabi, a qarshe ta ce dashi.
¤
"Tashi ka koma gida zan je wajen Gude anjima, kuma daina wahalar neman ta, zata dawo komin tsiyarta, tashi ka tafi abinka Kalla."
¤
Mal kalla ya kwance ledar furar da yaxo da ita ya daukota ya miqa mata.
¤
Inna ga fura kwa damawa yara."
¤
Ta amsa ba gdy bare na gode ta ce dashi.
¤
"Zan xo garin kome kenan zaku ji. Zan xo da daddawa wanda yake so sai ya tanadi kudi, na samu kalwa tiya uku mai kyau, duk zan dakata, in ka je ka fadiwa su Buba idan suna so."
¤
Mal. Kalla ya miqe tsaye.
¤
"zasu ji Inna, sai kin xo."
¤
Suka yi bankwana yayi kwana da kekensa ya na mai Allah-Allah kada ta tuno da wani laifin ta sake kirawo shhi. Inna Gaje ta koma kan yara da take shugabanta a gonar gyada, da xuwanta ta koma kan aikinta na fada. Kafin Mal. Kalla yayi nisa akan keken tsohuwar ta mangare yara uku suna kuka, sbd sun sa wasa a aiki don sun ga ta je wajen baqon da tayi.
¤
¤
**~**
¤
¤
A ranar da tashin su daga gonar Inna Gaje bata ko koma gida ba, ta dorawa yara kayanta suka tafi mata dashi. Ita kuma ta wuce wajen qawarta Gude mai bori wacce take a tsaunin Jan Baba.
¤
¤
Lp=15¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
¤
page
15
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsaan
madugun taska
¤
¤
Gude mai bori wata tsohuwar bafullatana ce, wacce take sa kayan maza, kuma a duk ranar lahadi take hawa borin ta, tun safe idan ta fara tsalle tana tuma a tsakar gida, sai ta kai yamma bata gaji ba, mutanen dake a qauyukan kusa da tsaunin Jan Baba sune kwastomominta, kome ta fada musu basa qetarewa kuma, tana samun gagarumin alheri dasu tun daga kan shanu da tumaki da kaji da kuma turamen zannuwa.
¤
Akwai wani ramammen dan korenta da take tare dashi a kodayaushe a tsangayarta yana kada mata garaya, duk borin da zata hau shi yake lalo mata taken shi, idan ta fito tsakar gida ko takalmi bata sawa a qafarta, sai ta fara rausaya, idan kida ya kaure kuma sai ta fara duduma har qasa na motsawa.
¤
A haka Inna Gaje taxo ta same su a gidan, siririn mutumin yana kada mata garaya tana zarya tana kaiwa da komowa, da ganin ta ya tsaya da kidan ya fara cewa.
¤
"Kunyi baqi, ku tsaya ku huta zamu sake dawowa anjima."
¤
Gude ta tsaya da zaryar, ta juyo suka yi ido hudu da qawarta Inna Gaje. Ta yi atishawa sau biyu sannan ta juya ta nufi dakinta da sauri.
¤
Dan koren Gude mai bori ya ce da Inna Gaje.
¤
"ki

Please Login or Register in order to submit comment