Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan nasan kuna cike dajin haushina....sashi ya sakarmin jika!'' Ta karashe mgnr Tana directing daddyU. Ihsan tayi tsit tana jira kawai taji anyi sakin, se yanzu takejin zuciyarta fara sol saboda tanada Tabbacin yau insha Allah seya saki KYAUTAR ALLAH, kowama ya huta. Ummih ma tayi kasaqe tana jira taji me alhaji umar zece. Alhaji unar de shiru yy yayi kasaqe yama rasa mizece.

"Dan ubanka bada kai nake maganaba! Yau danka koda uwarsa yake kwana seya sakarmin jikata...." Annah tayi mgnr idonta na kn daddyU se umartarsa takeyi, ranta a matukar bace. "Wallahi ya sakarmin jikata ko ran uban kowa ya baci a dakin nan, kwara tin muna mu hakan mu ya saketan kawai! Kai yau ko tsirara yake yawo zigidir karshen iskanci da bura uba kenan kou, to seya sakarmin jikata dan bantan ubansa!"



*Wannan na 2 days kenan, dan darajar furfurar Annah kada wanda yace dani 44 please inba hkba zanyi tsalle in fada tekon maliya inyi wankan tsarki in lafta muku mutumci, lutsum lutsum*....... 😂

[8/4, 16:55] +234 913 133 0334: KYAUTAR ALLAH...🅿️44

*PAID BOOK..500 NAIRA ONLY.. 08136349646..*

*Bana edeting*....

SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏼

Alhaji umar ya kalli Raslan, yaga ya wanisha mur ya hade girar sama da kasa , dukda yana mahaifinsa Amma seyajima shakkar yace masa ya saki KYAUTAR ALLAH, saboda yadda ya hade rai fuskarnan babu Annuri seya zama kamar wani qasurgumin namijin zakin daya shekara dubu a jeji, yana farauta, irin wanda ya gagari duk wani me rai. "Bada kai nake maganaba!" Annah ta kara daka ma umar tsawa jin yayi shiru be zartarda abinda ta umurcesaba. Firgigit Alhaji umar yayi ya kalli Raslan cikin sanyi da san yayawa, yace "Ka saketa..."

Duk wata halitta dake dakin zubowa Raslan ido sukayi, wanda ya hade girar sama da kasa, kai kace mala'ikun mutuwa Aka Aika masa, ya harde hannayensa a kirji ya daura kafa daya bisa daya, yayinda bayansa ke jingine da bangon dakin har zuwa lokacin. Ihsan tayi shuru, hadi da yin kasaqe, dukta qosa taji meze fito daga bakin Raslan inda so samuntane kawai taji yace "Na saketa saki uku!" Har abadan kenan. Wata irin Ajiyar zuciya ta sauke,, hadi da dafe kirjinta tahau jero addu'ur'i kan taji ya furta wannan kalmar, da tunaninta ta bata.

Raslan yayi shiru kai kace badashi Daddynsa ke maganaba. "Dan kutmar ubanka bada kai ubanka ke maganaba! Ko rashin tarbiyar hadda ubanka zakayimawa, in ni ban isa dakaiba ai ubanka gashinan ya isa dakai, kamar yadda ya umurceka kawai ka sakarmin jikata, tinda ba jini kuke da hantaba, ballan tana ace ba a rabaku..." Annah ta fada tana jijjiga rai a bace, kawai so takeyi Raslan ya sakar mata jika, ita knta in za a ritseta a kan meyasa takeso Raslan ya saki KYAUTAR ALLAH hujjarta dayace zuwa biyu. Na daya saboda Ummih, na biyun saboda raslan dan iska ne, acewarta.

Raslan ya maida fuskarsa gefe guda kamar badashi ake maganarba, tin a nan ihsan ta sare dan tana hango Alamomin bedama niyar yin sakin, jikinta yayi sanyi. Ummih dake tsaye idonta tar a kan Raslan, harga Allah tanaso ya saketa kodan ta huta da matsalar Annah, hadda Auren dake tsakanin Raslan da kyautar Allah yakesa Annah kwata kwata bata sassautawa Ummih, kafin Auren tadanfi samun sassauci daga gareta, dukda ko babu auren na KYAUTAR ALLAH da raslan sam Annah ba ragawa Ummih takeyiba. Gaf ilahirin halittar dake dakin basuson rabuwar KYAUTAR ALLAH da Raslan, inka cire Annah da ihsan da ummih...Anty Rukayya tafi kowa son Auren KYAUTAR ALLAH da Raslan ya daure har Abadan. Haka itama Anty Sadia, da dukkanin mazan duk sunason Auren kodan kara karfafa zumuncinsu. kowa zuciyarsa cike takeda kunci saboda Annah ta matsa dole se Raslan ya saki KYAUTAR ALLAH, umarnin annah babu sha babu ketara ruwa. Abinda yasama tabar Auren ya jima dan basuyi ido biyu da Raslan bane.

A bangaren KYAUTAR ALLAH tini ta bude idonta a kan Raslan tana jira taji ko ze saketa, dukda da bacin ransa dake tattare da ita, wanda ya jawo tsanarsa ga zuciyarta seda taji bataji dadin yadda Annah tace dole ya saketaba, ba son Daddynta takeba tabbas tausayinsa take kuma tausayi yafi so daraja da kima ko a mizali, saboda so na gushewa Amma tausayi baya taba gushewa ga zuciyar dan Adam inhar jijiyoyin jikinsa na bayar da jini. Tausayi shine Ainihin soyayya ta gaskia. bason daddy takeyiba kaunarsa takeyi, kaunarce ta disashe a ranta Amma tausayinsa na cikin zuciyarta, kawai taji ta tsanesane saboda shi baya tausanta kamar yadda ita take tausansa. Rintse idanuwanta tayi gam, tunawa da tayi da azabar da yayi mata dukda dumbin magiyar data rinka masa amma sam be tausaya mataba, sema yayi biris da ita. Dan haka tafi tunanin sam Daddynta baya sonta. "Na tsaneka daddy saboda baka tausayina!" Ta furta a bayyane saboda disashewar muryarta, sam babu wanda ya samu danar jin me take cewa. hawaye ne ke zirya a gefe da gefen idanuwanta, sauri tayi ta kauda fuskarta gefe ta yadda babu wanda ze gane kwallar tata.

"Dan ubanka bada kai Ake maganaba!" Annah ta kara dakawa Raslan tsawa wanda yy gefe da fuskarsa, dukda yajita Amma ko juyo da fuskarsa beyiba, kai kace da gunki Ake magana. "Umaru kasa yaronnan ya sakarmin jikata, tinda ba tare uwarsa ta kawosu duniyaba, in kuma taren ta kawosu se inji...Kai yau ko tare uwarsa tsohuwar karuwarnan tayi naqudarsu zuwa duniya seya sakarmin jikata yau Yau dinnan babu ketarewa..." Annah ta fada fuska babu alamar wasa. Sam yaran nata basu taba ganin serious a kan fuskartaba kmr na yau, dan haka se jikin kowa yayi sanyi a dakin, tabbas babu makawa yau da wuya Raslan ya ketare,... "Ka saketa..." Daddy ya kara furta masa umarnin da mahaifiyarsa ta bashi, shima ya bawa nasa dan, a wannan karon babu sanyi a tattareda muryarsa.

Still raslan ko gezau beyiba, kai ka rantse da Allah ma badashi Ake magana, ko a hularsa. Ran Annah ya kara harzuqa ya baci ganin Raslan na neman maida ita yar iska, ta kudurta a ranta yau zata kawo karshen iskancinsa abinda yasa duk iskncin da yake mata ta rinka daga masa kafa kenan saboda tanada inda zata fanshe. "Wallahi na baku minti biyu kusa yaronnan ya sakarmin jika ko in tsine muku Albarka dukkaninku, inhar ni na haifeku kuna tsoron tsinuwata kawai kusa yaronnan ya sakarmin jika! " ta fada babu Alamar wasa, a tattare da ita, serious dintama yaci uwar nada, dan yanzu fito musu tayi a Ainihinta na Aishatu.

Hankalinsu duk ya tashi saboda jin ta Ambaci tsihuwa kuma babu Alamar wasa. Alhaji unar jikinsa har yana rawa ya kai dubansa ga Raslan yace cikin tsawa "A kan ka uwata bazata tsineminba...ka saketa nace ko in tsine maka!" Yayi directing dinsa babu Alamar wasa rai a bacr.

Juyowa Raslan yayi a matukar razane jin kalmar data fito daga bakin mahaifinsa da zafi zafi, na ze tsine masa, sam bega Alamun wasa a tattare da mahafin nasaba. Nan da hankalinsa ya tashi, ya gaskata cewar abun da gaskene dan ada ya dauka kawai zeyi wasa da hankalinsune yayi tafiyarsa, kuma a basa matarsa dole. Bashi kadaiba duk ilahirin halittar dake dakin seda hankalinsu ya tashi inka cire ihsan. Ummih knta tashiga damuwa ganin damuwa da tsantsar tashin hankali a tattareda dan nata, Amma ga fiti tafiso Raslan ya saki KYAUTAR ALLAH kowa ya huta ta gajida gutsiri tsoma. hatta na'im seda ya natsu yashiga taitayinsa, yayi shiru ya zubawa Raslan ido, cikeda tausayawa harga Allah duk fam dinsu yafison Raslan saboda beda damuwa gashi dason dan uwa a takaicede yanada zumunci sosai .... Haka kawai taji gabanta ya yanke ya fadi, dajin furucin Annah, tini ta goge hawayenta, ta dawo da dubanta Ga Raslan, wanda zuwa yanzu fuskarsa ta canza kala zuwa ta tausayi, da tsantsar tashin hankali... Girgiza kai kawai ya shigayi saboda harga Allah bakinsa baze iya furta mata kalmar sakiba, ya riga yakamu iya kamuwa, ji yakeyi a kan ya asashi ya saketa kwara kawai a kashesa Ya zamana baya numfashi a doron duniya, domin kuwa da ransa be taba iya sakinta, yana gani ta Aura wani yaje yayita cinta, Ai abindama baze taba yuwwaba kenan, inko ya saketa to tabbas macewa zeyi. Ihsan ta zuba masa ido tana murmushin mugunta a zuciyarta, ga dukkan alamu mijinta na gab da dawowa tafin hannunta, dan tanada tabbacin inde yana tareda KYAUTAR ALLAH sam bazatayi tasiri a garesaba, karshentama yazo, musammanma yadda taga Alamun gaban macen tasan mijinta dolema ya haukace a kn KYAUTAR ALLAH, saboda shi ya fara Amfani da ita a doron duniya, abinda yafi komi tsaya mata a rai kenan da ranta taga mijinta yayi Amfani da kishiyarta sannan babu wanda besan cewa shi ya fara Amfani da itaba, Itako a bayyane yake mijinta shida knsa yasan bashi ya fara Amfani da itaba, ko wannan ya isa ihsan ishara a doron duniya. Kafin taga gaban KYAUTAR ALLAH bataji zafi sosaiba bisa ga yanzu dataga gaban nata a memakon Abin ya damu KYAUTAR ALLAH a matsayinta na Kishiyarta se Abun ya tsayawa ihsan a rai, kuma tabbas ya tsaya mata a ran Ainun, kishiyartade kamilah ce ba kmr itaba ballagaza wannan kuwa a bayyane yake, kwad'o yafi gaya. "In be saketaba zan iya mutuwa!" Ihsan ta fada a ranta nan da nan wasu kwalla masu zafin rad'ad'i suka shiga zirya a kn kuncinta.

"Umaru!" Annah ta kira sunan Alhaji umar babu alamar wasa. Jiki na kakkarwa Alhaji umar ya Amsa da "Na am Annah...." "Kasa danka ya sakarmin jikata Nace, bazan kara maimaita makaba sede kaji tsinuwata a gareka..." Annah ta kara fadi babu wasa.

Hankalin Alhaji umar ya kara tashi dajin kalaman mahaifiyarsa a karo na biyu. "Ka saketa nace Muhammad!" Daddy ya kara fadi hadi da daka masa tsawa. Kawai se Raslan ya zube kasa still yana girgiza kai ba tare dayace komiba, se Aikin girgiza kai kawai yakeyi. Dakin ta dauki tsif yayibda kowa da abinda yake saqawa a cikin zuciyarsa, musammanma mazan da bakinsu ya mutu suka gaza mgna, jikinsu ya dauki sanyi.

"Ka sake ta dan ubanka!" muryar ummih ta karade dakin, yayinda muryarta tayi Amsa kuwwa a dakin , Kai dajin yadda tayi mgnr kasan *cikin zafin rai take Ainun* .
Kamar saukar aradu kowa yaji muryar ummihn. Ihsan kan tsabar farin ciki seda ta murmusa, ummih bata taba burgetaba kmr yau. KYAUTAR Allah kuwa a gigice ta dawo da dibanta daga knta Raslan zuwa kan Ummih...

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Itace kalmal data fito daga bakin Raslan murya na rawa, hankalinsa a matukar tashe, yayindayake zube bisa guiwowinsa, ya daura tafikan hannayensa kan cinyarsa, kawai seya fashe da wani matsakaicin kuka me cin rai, yana girgiza kai... Dole duk wani me imani ya tausa masa a dakin Amma banda ihsan, wadda bakin ciki ya rufeta, kawai seta fara ganin juwa dukda tana a zaune, ganin mijinta na kuka a kan wata banza karamar yarinya, yar da bata wuce yar cikinsaba ko wannan bacin cikin Allah ya batta dashi ya isheta isharah. Duk wani wanda yaji tausansa bayan KYAUTAR Allah yake, hatta ummih data haifesa KYAUTAR Allah tafita jin tausayinsa, musammanma dataga hawaye na zirya bisa kuncinsa yauce rana ta farko tin tadowarta data taba ganin hawaye a kan fuskar Raslan. Ba tare data Ankareba itama hawayen suka hau auna gudu daga kwayar idonta zuwa gefe da gefen idanuwan nata.

"Ko zaka mutu seka saketa!" Annah ta fada cikin dakiya dukda taji tausansa Amma san batajin zata hakura da mgnr ya saketan, dan sam KYAUTAR ALLAH bazata iya da raslan ba, sam Annah Batayi tsammanin Raslan ze iya kusantar kyautar Allah ba seda ya Aikata taga zahiri, shiyasa takeso tasashi ya saketa saboda bataso a kuma abinda ya Aikata tanada tabbacin aka kuma sede a dauki gawar KYAUTAR ALLAH, to tabbas aka dauki gawar KYAUTAR ALLAH zeyi dai-dai da rasa ran Annah ne, duk duniya babu wanda Annah takeso sama da kyautar Allah, dan hk duk wanda ze cutar da KYAUTAR ALLAH dai-dai yake daya cutar da ita, har kwarama a cutar da ita, zata iya yafewa, Amma sam bata yafiya ga wanda ya cutar mata da KYAUTAR ALLAH, shiyasa bazata taba yafewa Raslan Abibda ya aikatawa KYAUTAR ALLAH. "Dan iska kawai!" Ta fada a hasale.

"Kisa danki ya sakarmin jika inhar kinsan darajar uwarda ta haifoki, inde kin cika ke yar halak ce kisa danki ya sakarmin jika inde har ke ba yar titi bace...." Annah ta dawo kan ummih rai a zafafe take mgna. Mgnr tayima UMMIH zafi nan da nan ranta ya harzuqa zuciya bata da kashi kawai idonta ya rufe. Ta karasa ta cacumo Raslan ta hau sharara masa mari duka tako ta ina tana fadin "Ka saketa dan ubanka! Na gaji da mgnr da kake jawomin ka saketa nace ! Ka saketa dan bura uba kawai! dan kuka Mejawomin zagi dani da iyayena, saketa ko in tsine maka albarka! " kwata kwata idon UMMIH ya rufe se duka take kai masa tako ta ina Raslan dako gezau beyiba dukda dukan da ummih ke kai masa tin can karfin , Amma ko kadan bejin zafin dukan, pain din na kasan zuciyarsa. Zafin kalmar datace ya saketa kota tsine masa tafiye masa komi zafi a zuciyarsa. "Kiyi hkri ummih bazan saketaba!" Ya fada yayinda jini ke fita ta hancinsa, babu kakkautawa, saboda naushin da ummih takai masa ga hanci ya haifar masa da fitar jinin, abinka da jikin hutu. Ran ummih ne ya kara zafafa jin yace baze saketaba ta kara kai masa naushi a hanci saboda idonta ya rufe sam bata gani. Annah ta tsaya tana kallon ikon Allah,. Gaf ilahirin me ran dake dakin zuboma ummih ido sukayi wadda keta dukan Raslan kai dagani Kasan bata hayyacinta, ranta ya riga ya baci. Kowa nason dakatar da ita Amma yana tsoro. "Ki kasheshi! Kije gidan yari!" Annah ta fada cikin bacin rai, kai dajin yadda tayi maganar kasan ranta a bace yake da dukan da ummih keta yima jikan nata.

Sam UMMIH batamajin me take cewa se duka kawai take kaima Raslan tincan karfinta, cikin fitar hayyaci da bacin rai daman tanada zafinsa.

KYAUTAR ALLAH dakejin kmr ita ake duka duk hankalinta ya tashi, shi ake duka amma zafin ga jikinta take jinsa. Kawai seta fasheda wani irin mahaukacin kukan da batamasan sanda ta fashe dashiba tincan karfinta. "Dan Allah ummih kada ki kasheshi...Please! Wayyoo!! daddy narh!!! " ta fada cikin sarkewar murya irin na me kuka. Dukse kallo ya dawo gareta, ihsan kan ji takeyi kmr ta tashi taje ta shaqeta ta kasheta kowa ya huta, wani irin bnzan kallo ta gallarama KYAUTAR ALLAH, ita kam batamasan tanayiba. Raslan se yaji sanyi ga zuciyarsa ko yanzu ummih ta kasheshi zeyi mutuwar farin ciki, sannan ze mace da fara"arh a tattare dashi. "Ina sonki Rukayyah!" Ya fadi da karfi ta yadda kowa dake dakin seda yaji,....
Ran ummih ya kara baci a matukar harzuke ta kara daukesa da wani wawan mari, tana fadin "Ka saketa inba hkba wallahi tsinuwata ta tabbatr a gareka!'' Ta kara fada a zafafe.

Anty rukayya taga zafin da Ummih ta dauka yayi yawa, fushin uwa ba karamin Abu bane ga dan cikinta, darajar uwa ta wuce misali. kawai ta taso ta krso inda suke, ta tsugunna saitin Raslan tace "Raslan Saketa please sbda umarnin Ummihnka please...." Raslan ya dago red eyes dinsa ya kalli Anty Rukayya ya girgiza kai zuciyarsa na wani mummunan harbawa. "Anty inna saketa mutuwa zanyi!" Ummih ta amshe cikin kunar rai "ko zaka mutu ka saketa dan ubanka! In baka saketaba na tsine maka har Abadan...."

A matukar razane ya dago ya Kalli Ummih, yaga da gaske take sam babu alamar wasa a tare da ita. Maida dubansa yayi ga KYAUTAR ALLAH, wadda keta kuka har zuwa lokacin kawai ya maida knsa kasa had'i da fashewa da wani mahaukacin kuka kamar zararre. Cikin kuka ya fara magana, "Ummih zan saketa saboda bin umarninki, Amma badan inasoba, Wallahi inasonta itace Natsuwata, itace kwanciyar hankalina, na tabbatr inna saketa na rasa natsuwata har Abadan....." Ya yakara fashewa da kuka kamar ransa ze fita. Sosai kukan ke taba zuciyar ummih Amma ta danne saboda tafiso ya saketan kowa ya huta. Ita knta ta rasama Mike mata dadih a duniya.

Kawai Anty Rukayya ta fashe da kuka, saboda tausayi, duk wata halitta dake dakin seda suka tausaya masa Amma banda ihsan wadda zuciyarta ke cike da dumbin farin ciki. Annah kanta jikinta yayi sanyi, ta tsaya tayi shiru.

Yaci gaba da mgna hadi da kara rushewa da wani mahaukacin kuka, har numfashinsa na neman kwace masa. "Na....sa....ke.....ta......." Yana gama fadar hakan ya zube kasa hadi da jawo numfashi da Mugun karfi, tin daga haka numfashinsa be kara harbawaba.



*MANAGE NAYI BUSY WALLAHI BIKI MUKEYI.....* 😍
[8/4, 16:55] +234 913 133 0334: KYAUTAR ALLAH...🅿️45

*PAID BOOK...500 ONLY...08136349646*

*YA ARRAHAMANIRRAHIM*


"Wayyo Allahnah nashiga uku! Na bani! Wayyo daddy kar ka mutu ka barni! Dan Allah ka tashi daddyna!!" Shine Abinda ke fita daga bakin KYAUTAR ALLAH wadda duk tabi ta dimauce ta fita hayyacinta, saboda ganin daddynta a kasa warwas kamar gawa, ba karamin dimautar da ita yayiba nan da nan ta nemi yawo a bakinta ta rasa, ta hau kuka tana ihu . Yunkurin miqewa tsaye tashigayi dan tasamu ta karaso garesa, shap tama manta da ciwon dake kafarta, saboda ta shiga gigita iya gigita.... Jummaice ta taso a guje ganin tana neman tashi da ciwo a kafarta kowa be Ankaraba saboda hankalinsu ya koma kan RASLAN....da sauri jummai ta karaso ta riqeta tana fadin ki natsufa da ciwo a jikinki."ki barni inje gun daddy na please!" Shine abinda ya kara fitowa daga bakinta ba tare data masan waye me dannetanba, but idanuwanta duksun rufe.

"Yau kika kashemin jika Wallahi kema nice ajalinki zainabu! In bn zama ajalinkiba kice ni ba cikakkiyar yar katsinawa bace!!" Shine abinda ke fita daga bakin Annah rai a bace har tana buga kirji idonta na kan ummih wadda ke tsaye zuciya na tafarfasa, idonta na kan danta dake sume jin hawaye na neman kubucewa daga idanuwanta, kawai ta suri bag dinta dake kasa ta fice daga dakin hawaye na bin Kuncinta na tausan danta tilo daya duk duniya, takaicin kanta ne ya rufeta.

farin cikin, dake cike da zuciyar Ihsan baya misaltuwa ji takeyi kamar Anyi mata KYAUTAR Aljannar. Seta fashe da kukan munafurci hadda shasheqa, ganin mijinta a sume. Alhaji Abdullahi da na'im ne suka cincibesa suka fice dashi daga dakin, Anty rukayya and anty sadia maman na'im, DaddyU daddyH daddyM duk suka mara musu baya, kowannensu zuciya babu dadih. Na'im da Alhaji Abdullahi, su suke riqe da Raslan din, direct emergency room suka nufa dashi nan da nan likitoci suka dukufa a Kansa ganin baya numfashi. Nan wajen emergency din duk suka tsaitsaya kowannensu yanata adduarh Allah ya tashi kafadun RASLAN din.

Nan dakin suka bar Annah da jummai da KYAUTAR ALLAH, wadda har lokacin se kuka takeyi jummai na danneta tana yunkurin miqewa...Annahh se tsinewa Ummih takeyi. A karshede tace baza ayi kisan kai tana nanba, haka kawai yan sanda suzo su kamata, ta dauki mayafinta ta fice daga dakin tana fitowa ta hango umar da hanzari ya karaso inda take, "Annah ina zaku? Ko kunada bukatar wani abune?"

Haka kawai se Annah taji kunya ta rufeta na yadda umar be nuna komiba dukda itace silar komi daya samu dan nasa. Nan ta gaya masa so takeyi subar garin zuwa katsina yanzunnan,.. Umar yace su bari zuwa KYAUTAR ALLAH ta samu sauki mana, Annah ta daka tsalle tace Aah ai yau mutuwace kawai in tayi ze hanata zuwa garin katsina. Umar yace tou, ta koma ciki bari yaje ya samu doctor tace tou hadi da juyawa ta koma dakin, shi kuma ya nufa office din dr hannatu a bakin kofa sukaci karo tana sauri zata nufa emergency inda RASLAN yake kawai sukayi kicibus. Nan ya sanarda ita bukatar Annah dr tace bazeyuba inhar a mota zasu isa garin katsinar, umar yace ah'ah jirgi zasu hau.. Dr hannatu tace to bamuwa.amma ba hk tasoba, taso ace taci gaba da bawa KYAUTAR ALLAH kulawa har tasamu sauki. Komawa office tayi ta rubuta trnsper zuwa wani asibiti babba dake garin katsinar wanda takeda connecting dasu ta tura musu sauran byanan ta system. Ta bawa umar takaddar tareda ita dashi da wata nurse wadda ke daukeda wani basket suka nufo dakin, harma Annah da jummai sun gama shirya KYAUTAR ALLAH cikin doguwar riga an yane mata knta da dankwalin rigar, har lokacin se kuka takeyi, tana kiran sunan daddynta Annah batabi ta kantaba. Wasu allurori dr tayi kata kana ta bata wssu magun guna tasha da kyar tanayi tana kuka. Alhaji umar ya dauketa cir yasata a black car din dasukazo a ciki, se kuka takeyi Annah ta daka mata tsawa dole ta natsu... Annah da jummai suka shiga gidan baya Umar ya shiga front seat dreva yashiga yaja sukabar asibitin suka hau titi motar securities na biye dasu a baya. KYAUTAR ALLAH dake kan jikin Annah da jummai se hawaye takeyi me zafi harga ALLAH tanaso taga daddynta. Tin kafin su karasa airport din Alhaji umar yasaya muku ticket din zuwa katsinar Abinka da kudi sam babu bata lokaci suna isowa kawai suka shiga jirgin. da dabara Alhaji umar ya zaunar KYAUTAR ALLAH a kan seat din jirgin da kyar ta iya zaman amma taji sassaucin jikinta sosai. Alhaji umar yayima Annah Asauka lafia, ta amsa da Ameen, sukayi sallahmade, cikin ladabi. Yana gani har jirginsu ya tashi kana ya shiga mota suka koma zuwa asibitin. Har zuwa lokacin ba asamu RASLAN ya farkaba likitoci nata iyakacin bakin kokarinsu. Alhaji harun da alhaji musa suka tari dan uwansa da tambayar meyasa Annah suka nufa garin katsina yau ba taredamu sun saniba.." Alhaji umar yace "Saboda ita ta bukaci hakan naso sanar daku Amma duk tabi ta uzra.." Suka gamsu da mgnrsa, tareda mata fatan sauka lafia, time to time sunata kiran Annah a waya.

Tana fita daga asibitin, ta tari me adai-daita sahu, ta hau kawai ba tare datamasan inda zatajeba, se hawaye wani na bin wani a kuncinta, bude bag dinta tayi ta dauko tissue ta hau goge hawayen dake zirya kan kuncinta, ji takeyi kamar zuciyarta zata buga saboda tashin hankali da damuwa, gaf hankalinta yanaga danta data baro yashe a kasan tiles din dakin, bazata jure ganinsa bane shiyasa ta fice daga asibitib. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Shine abinda taketa maimaitawa a zuciyarta ko zata samu sassaucin radadi da azabtuwar da zuciyarta take ciki, bata taba nadamar Auren Alhaji umar ba se yau, haka kawai taji tanajin haushin kanta ba tare datasan dalilin hknba, tadesan silar tsanar Auren daddyn Raslan saboda Annah ne.

"Hajiya ina zan kaiki! Hajiya ina zan kaiki! Hajiya ina zan kaiki!!" Shine abinda me napep din keta fada Da dan daga sauti Amma sam bata jiba, ta riga da tayi zurfi a tunani,. Ta mirrow ya kalleta yaga se sharar kwalla takeyi da tissue haka kawai yaji tausanta ga zuciyarsa dan yasan ba karamin Abu bane yasata kuka saboda bega alamar wahala a tattareda itaba naira iya naira ta zauna ko daga fatar jikinta zuwa kayan dake jikinta ya isa ya yasashi gane hakan. Packing yayi a gefen hanya, ya juyo ya kalleta. "Hajiya nace ina zamuje!!!" Ya fada da karfi sosai. Firgigit ummih tayi ta dawo da dubanta garesa hadi da saurin share kwallarta tana kakalo murmushi dayafi kuka ciwo, ba tare datayi maganaba kawai ta kauda face dinta gefen titi... "Hajiya kin hau kuma baki gaya inda za a kaikiba, tin dazu se tafiya kawai mukeyi a kan titi...kuma inata magana baki jiniba..." Me napep din ya fadi hkn yana kallonta cikeda tausayawa. Ummih tace "Ayyah yi hkri banjika bane,....ina zuwa..." Ta

2 Comments On KYAUTAR ALLAH
avatar
maryam-8-8-3

1 year ago

Reply

Aslm

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryam-8-8-3

Wslm

Please Login or Register in order to submit comment