Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haifeta tafita sonka... Ynzu ta dawo ta gnka a hk Ai inajin itama seta kwanta ciwon dayafi nakama.."

Duk Abinda take fada Raslan nji, gashi azaba ta isheshi domin zazzabine me zafi ya rufeshi, numfashinsa da kyar yke fita, ga haqoransa na kakkarwa..

Nan hnklin Annah ya kara tashi duk tabi ta kid'ime, ta rasa ina zatasa rnta, bata tabbtr tnason raslan ba se yau data gnshi a wannan halin... "tau kai babana dmn bkada lafiane kuma kaxo hk...sekace dole..koude so kk ka kullamin kullallah kazo ka macemin ne A nan kou.." Annah ta fadi hkn a gigice, yynda idonta ke knshi...

Sosai zazzabin dake jikinsa ya tsananta yayinda har jikinsa ya fara rawa..

Hnklin Annah ne ya kara tashi ganin yadda jikinsa ke rawa kai ka rantse da Allah girgizashi akeyi.... "Subhanallahi ni indo do..yazanyi da rayuwata, Wannan wacce iriyar bkar ranace yau zan gani...dan Allah babana kada Ka mutum min a gida, kajamin bakin jini a gun ummaruru da wannan uwar taka zainabubuwalle..."

"Annah..pls...ki kawomin blanket...sanyi nkeji..." Ya fadi hkn da kyar yynda yke krajin sanyi, a jikinshi..

"Yoooohhh! Ni akace mka nji me kacene. " Annah tyi mgnr tana matso da kunnenta saitin bakinsa... "Me kace newai..mezan kawo mka..."

"Blanket..." Ya kra fadin hkn still muryarsa na kakkarwar sanyi..

"Menene blontiti...kou brodi kake nufi..tou a hado mka da shayine.." Cewar Annah.

Bkramin haushi ta bawa Raslan ba, Dmn da haushinta ya shigo gidan...Runtse idonshi yy gam yna Ambato sunan Allah sbda yadda yaji Cikinshi na murd'a masa... "Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un.." Ya fadi hkn da karfi sbda yadda yji cikinsa na yamutsawa...

Hannu Annah ta dora A kai ta kwantsama wata uwar kara, Ita a zatonta ya mutune... "Wayyihuuuhuuuu!!! Nashiga uku! Shikenan ubana ya mutu...Allah yasonima ya cika da kalmar shahada!" Annah ta kara fasa wani uban ihun daseda duk masu Aikin suka hallara falon gidan suna tambayar mike faruwa,... Dai-dai KYAUTAR ALLAH ta shigo falon sanyeda kayan school dinta se yar jakarta me kyau goye a bynta, Tnata raye raye..da sauri sauri ta krso falon cikeda murna sbda taga motar babanta a compound... Dan hk ta shigo tna rera waka tna murna tna rawa tna fadin "oyoyo daddyna..oyoyo daddyna...dmn zakazo yau bka gyaminba..shine ka bari nje school dana sanima da bnjeba.." Ta fadi hkn tna shigowa tsakiyar falon

Annah tayi saurin kwabarta dacewa "Dan ubanki kiyi shiru Anyi mutuwa yau A gidannan...zaki shigowa mutane kina rawa ..da dan guntun skeet dinki sekace siyar kafurai..." Se kuma Annah ta qara fasa ihu "wayyo Allahnah ni A'ee Allah yasa ka huta babana..." Allah ta fadi hkn tna fyace majina da gefen zaninta..

Kallon rashin fahinta KYAUTAR Allah Tashiga bin Annah dashi.... "Annah mutuwa kuma waya mutu...uhm Allh ya jikanshi...ni ina daddyna.."

Annah ta qara fasa wani uban ihun har masu Aikin na rirriqeta domin shirin kwancia take tyi birgima A kasan.."ku kyaleni in kwanta A kasan sanyi sanyinnan kou zanji sanyi A raina...wayyooooohhhhh!! Nashiga uku ni A"eee wayyoo rayuwata..Allah sarki ubana..Dan ubanki gashican shine ya rasu daddyn naki.."Annah ta qarashe mgnr tna nunawa KYAUTAR Allah raslan dake kwance kn 3 sttr, idonshi A rufe, duk Abinda Annah keyi ynajinta, Sede beda karfin yin mgna sbda yadda jikinsa keta kakjarwa, yynda haqoransa wani ke kaiwa wani guga, sbda azabar zazzabi...

Nayi nan...

Team Annah ku fafata...
[8/4, 16:55] +234 913 133 0334: KYAUTAR ALLAH...🅿️16

*PAID BOOK..500 NAIRA ONLY.. 08136349646..*

*YAA WADUDU!* 👏🏼

hnkli a matukar tashe kyautar Allah tabi Inda Annah ta nuna mata da dara daran idanuwanta.. Ganinshi a kwance kmr ya mutunne ya kara tayar mata da hnkli ta wurgarda jakar dake goye A bayanta, Yayinda gaf ilahirin jikinta ke rawa, da gudu ta isa inda yake kwance, yna kakkarwaR zazzabi..girgizashi tashigayi A kid'ime tna fadin, "daddy Da gaskene ka mutu..pls bamuyi hk dakaiba, bkacemin zaka mutuba..wayyo Annah dan Allah kada ki kara gyamin Wannan mummunar mgnr.." Ta fada a matukar gigice yayindakou cikakken gani batayi, kwallah kam wata nabin wata a kuncinta.

Annah ta kara fasa ihu, ta dora Hannu A kai, tna fadin "Ni wlhy babban tashin hnklina daya mutum min a gida, Sirikai ba a iya musu ynzu se uwarsa tace wani Abu na bashi yaci ya mutu..Wayyo Allahna! nashiga uku na bani na lalace ni A'ee.."

KYAUTAR ALLAH ta kra fashewa da kuka, yynda kirjinta yahau mta ciwo, zuciarta kmr zata fatso ta fito fili..Kifa knta tyi a kn jikinsa, tsabar tashin hnkli batamaji yna motsiba, saboda idonta ya rufe da tashin hnkli..shafo knta yy cikin karfin hali.. "Bbyna, ban mutuba..kndesan halin tsohuwarnan..bande da lafia ne..."ya daure yy mgnr ne danya kwantr mtada hnkli

nan da nan mgnrsa ta samar mata da natsuwa, a cikin zuciarta, kn kace kwabo ta nemi ciwon ds kirjinTa keyi ta rasa,
Dagowa tyi yynda idanuwanta sukayi jawur kai kace ta shafe awanni ne tana kukan. Haushin Annah ne yabi ya tokare mata kirji. Kara Kwancia tyi a kn jikinsa tana sauke ajiyar zucia ta rugumesa da duk ilahirin jikinta da rayuwarta. nan zafin zazzabin jikinsa ya fara bugunta. "Daddy fever ne kou...sowie bari in kira family doctor kou.." Tyi mgnr tna miqewa, da kyar sbda knta harya buga, tsabar tashin hnklin da Annah tasata a ciki.

"Pls fara kawomn blanket ki lullubeni.." Yy mgnr still yna rawar sanyi, yynda hatta muryarsama rawa takeyi.. Da hanzari ta miqe ta nufa bedroom din Annah dan dauko masa blanket din..

Annah kam tna gefe ta saki baki, ta zubawa Raslan ido, "ashe bka mutuba.." Ta fadi hkn da mamaki a fuskarta.

Ma"aikatan gidan kam maidata sukayi kmr t.v, duk suka tsaya cirko cirko suna kallonta.. masu daria a boye nyi masu jin haushin Annah Naji, basude da yadda zasuyi da ita ... One bye one annah tashiga binsu da kallo tna yamutsa fuska "Uban meye zakuzo ku zubamin ido kmr mayu...kou dannace mutuwa, mutuwarce baku taba ganiba, kou kumade dmn kuna fatane jikannawa ya mutu..shegu yan iska zaku Aikata, dan halin mutum se shi.. Amma kuwa yanda mutuminnan ke baku dukiyarsa kmr ba nemowa yakeyiba be kmata ku masa wannan mummunar sakayyarba,..kouda yke ba lefinku bne ai ba yau Aka fara mutum yy maka ranaba kai kyi masa dare..."

Dukkaninsu suka saki baki suna mamakin klmin Annah, jummai tace "Hba Annah ai ba a murnar mutuwa sbda kou Anyi murnar bnzane tinda yna kn kowa.."

Wata uwar tsawa Annah ta daka mata "Dallah rufemin baki!, shegiya yar iska mebin maza! se wani raftako zance kkeyi, yaaan! Yaan!! Yaan! Dan kan bura ubaki ni zakiyiwa wa'azi Tou tin kafin A haifa uwarki nake zuwa mkrntar Allow..in takai mikima mijina malamine izifinsa dari da hudu.."

Duk suka zaro ido, dan liti me wankin mota yace "Dari da hudu kuma Annah.." Damnshi bakinshi be shiru..

Harara Annah ta gallara masa kna tace "Karya nkeyi dan ubanka, ka ajiye Katon kai kmr dan ruwa..kai Anyama kai ba dan ruwa bne..gaskia kwara uwarka ta maidaka bakin kogi nafi tunanin kai dan ruwane..sbda halittartaka ba irinta mutane bace..wannan halittar taka sede in a dunjar aljanu.."

Ma'aikatan gidan suka kwasheda daria jin An kira dan liti da dan ruwa..

Annah ta daka musu tsawa, "yan iskan bnza da hofi kawai..ku ficemin a falo tin ban hadaku na rufeku da dukaba..."
Sumimi-sumimi dukkanninsu suka fara qoqarin barin falon, suna daria ..."shegiya duba kafafuwanta kmr sauro, da duwawu a shafe...ke kamde lantana kou irin dirinnan baki dashi na mata, a hk ubanwa zaki samu ya Aureki.." Annah ta fadi hkn tna kallon lantana wadda take yar siririyace.. A dunia lantana ta tsani a mata gorin kiba, dan hk rai A baci ta karasa fita daga falon.

Zuwa Lokacin KYAUTAR ALLAH harta kawo bargon ta lulkubeshi, Amma still be dena rawar Sanyiba, Wayarta ta dauko tyi dealing num din Doctor Ahamad, wanda shine family doctor dinsu. Bugu dya biyu ya dauka nan ta sanar dashi yaxo sbda daddynta bb lafia, doctor Ahamad yace subhanallahi! Gani nan zuwa...kna ya katse wayar, komawa tayi ta kwanta gabaki dynta a jikinsa, Shikam se maida numfashi ykeyi, se yji dadin kwanciarta A jikinsa, sbda dmn gaf jikinsa ciwo ykeyi masa..

Krsowa Annah tyi tna dogaro sandarta,.. "Amma wannan shegiyar yarinya bakida tausai..duba kiga yadda Yke qoqarin mutuwa, Amma a hk duk kikabi kika dora masa uban nauyinki gaki Daya ..duba kiganifa kou wadannan uban duwawukan naki Ai nauyine.."

Dagowa,KYAUTAR ALLAH tayi ta gallarawa Annah harara zucia fal haushinta, "Ina ruwanki...gaskia Annah ki dena wannan rayuwar, kawai kn kma ihu, kina fadin daddyna ya mutu,..insha Allahu bashi ze mutuba.." KYAUTAR ALLAH ta fada cikeda haushi.

"Sede ubanki ya mutu kou..shegiyar yarinya da ido sekace yar mayu..so kike kawai kice sede ni in mutu to sede shi uban nki ya mutu bade niba, Dan ubanki, ni nan naci dubu se ceto..yar bura uba kai, wai harni kike cewa indena irin wannan rayuwar, se inyi rayuwar ubanki kou.." Annah tahau mita.

"Uhm,pls kirinka mgna a hnkli, bakiga daddyna bb lafia bne, kna damunsafa.." Tayi mgnr tna qara lafewa a jikinsa, wai incase in mutuwa taxo ta daukesu su duka

."Allah yasa mutuwa yy, se nyi mgnr da karfi..kawai Allah ya tsagamin bakin mgna a hana ni mgna..toukou ubansane zezo nan be isa ya hna ni mgnaba Ehhheeeh!.."

Turo baki KYAUTAR Allah tyi cikeda takaici. "To ki zauna mna.." Kyautar Allah ta fadi hkn ganin ta tsaya tsaye a knsu qiqam

"Bazan zaunaba dayake A knki nake tsayen kou.." Se kuma ta zaunadin domin ta gaji da tsayuwar.."Allah ya isa ihun da nyi A bnza Ashe shegenma be mutuba..tou ynzu ya jikin nka Babana..😂"

Raslan dake lullube yna rawar sanyi yna jinta, Shima takaicin ya rufesa, Wai a hk se ace Akwai cikakken hnkli a tareda Annah ... Doctor Ahamad ne yayi sallahma falon tareda neman izinin shigowa, Annahce ta Amsa da karfi tace "Shigo mna.." Doctor Ahamad ya shigo sanyeda qana nan kya, gajereneshi kou ince wadane.sannan shi baki Wuluq se uban shekaru, a gaskia shidin mummuna ne sosai ga katon kai ga sanqo. , hannunshi rike da kyn Aikinsa. Krsowa yy ya rissina a gaban Annah yace "Ina wuni Hajiya. "

Annah ta washe baki tna kallon sanqon Ahamad kna ta Amsa da "Lafia lau Dannan..gakade dan wada dakai.. Kai kam bkajin kunyar yadda Kake dinnan...."

Doctor Ahamad yasabada Halin Annah dan ba yau suke tareba. Murmshi kawai yy ...KYAUTAR ALLAH ta gaidasa, ya Amsa ckin sakin fuska. "Yakike bby.."

"Lafia lau doctor..

Murmushi ya sakar mta kna yace "Yame jikin?"

"Alhmdllh doctor dan Allah ka dubashi bnaso ya mutu pls.." Ta marairaice masa..

Anbah ta tabe baki tace "Inya tashi mutuwa, seki hnashi koushi likitan ya hanashi ya mutu.."

KYAUTAR ALLAH ta gallah mata harara.. "Kin harari wannan uban nki dan buzu.." Cewar Annah.

Turo baki KYAUTAR ALLAH tyi cikeda shagwaba,..doctor Ahamad kam daria yy ciki ciki... " yar kan uban kai da baki kmr gidan tsutsa..zaki dagashi a dubashi kou kumade, yayane mayyar maza.." Cewar Annah.

Turo baki tayi cikedajin haushin Annah ta kirata da mayyar maza..Dagashi Tayi Amma tana nan gaf dashi, har doctor din ya bude bargon dya rufa dashi ya taba jikinshi yji kmr wuta.. "Ai ba a lullubewa in ana zaxzabi..sbda lullubarma kra zazzabin takeyi...Kaci abnci.." doctor din, Ya krshe mgnr zuwa tambya.

Girgizaasa kai Raslan yy Alamar ah'ah. "Okay..da ina da ina ke mka ciwo"

Raslan yace "Kaina ke ciwo sosai..se zazzabi, Da ciwon ciki.."

"Okay..Kou Abunne ze tashi.." Doctor din ya tambayi Raslan.

"Aah bna tunanin hakan, but Ummihnarh tayimin treatment dinshi,.." Yana mgnr ne da kyar.

Girgiza kai doctor din yy kna ya gwada masa BP nan da nan yaga jininsa ya hau.. Da matukar mamaki yake tambayrsa "dmn knada BP ne?"

Gaban KYAUTAR ALLAH ne ya ynke ya fadi, jin Ance BP,cikeda tausayawa ta zubawa Daddyn nata ido..

Girgiza masa kai Raslan yy.. Shi knshi doctor din yy mamaki, sbda a iya saninsa da Raslan besan ynada hawan jininba.. "Okay . kna tunani ne sir.."

Raslan ya girgiza masa kai hadi da fadin "nop.."

Jinjina kai doctor din yy "in knayi pls ka dena. Kaga ynzu yahau kadanne, bamaso kuma yy gaba, sede ya Sauka pls.."

Raslan yayi shiru yna kallon doctor din tare maimaita abinda yace masa wai BP.. A rnshi yace "Uhm koudan rashin gindi Ai dole in kamu da BP.." Yata allaqa ciwon nasa da hkn..

Annah data zubawa likitan ido taji yace hawan jini, nan tahau salallami, tana tafa hannu "hawan jini kuma..oh ni A'ee.tou ba dole ka kamu da hawan jiniba, koudan wannan shegiyar matar taka,,wlhy dmn sakinta kyi ka huta..kaima kaine kajawa knka, duk matan garinnan ka rasa wazaka Aura se karuwa..Allah ma ya qara, gashinan Ai tna neman kasheka kowa ya huta..su zainabu kuwa Aise Anyi hauka dmn d'ane daya kmr rai..Danma an samu ta haifadin, Allah yaso bata zubar da yayanba A titi..Wannan tsinnniarde matarka itace ta zubarda yayan a titi, dan wannan da ganinta ta zubar da ciki kafin tyi Aure yafi sau dari hudu.."

Raslan ya dafe koshi cikeda takaici.. KYAUTAR ALLAH ma taji takaici tace "Annah waike bakya shirune.."

"Bazanyiba dan ubanki..in ina mgnata badake nkeyiba bnaso kinasamin baki knajina kou.." Annah ta hayyaqo mata.

"Allah ya baki hkri.." Cewar KYAUTAR ALLAH.

Murguda baki Annah tayi tace "Ameen inda zucia daya kk fada, jikar mayu.."

Doctor din ya jinjina kai yyndayaketa kallon Annah kmr comedy ji ykeyi a ranshi dmn A gidansu take da babu ruwansu da kallon t.v...
Nan take doctor Ahamad ya fara dubashi, Allurori yy masa, KYAUTAR ALLAH kam se Runtse ido takeyi kai kacema ita akewa Allurar, ganin Anyi masa Allurori har hudu, a bom bom, Amma doctor din ya kakkare ta yadda ba wanda zega bom bom dinnasa.. KYAUTAR ALLAH kam Har kuka tayi, sbda Tausayinsa... Nan da nan Zazzabin jikinsa ya fara sauka... Drib doctor din yasa masa saboda yasamu karfin jikinsa, doctor din na masa treatment ammashi idonsa na kn KYAUTAR ALLAH cikedaso da kauna yke kallonta, Se ykejin sassauci A zuciarsa Amma inya tuna cewar zatayi Aurene ze dena ganinta se yji wani bakin ciki yazo masa kahon zuciarsa ya tokaresa.. Zancen zuci ya farayi "Ina Baze yuba!" Ya fadi hkn yna lumshe ido.

Doctor din ya bawa KYAUTAR ALLAH magungunan da Raslan din ze sha, nan ya kwatanta mata duk yadda za ayi da maganin, kna yy masa fatan samun sauki, Sannan yace ynzu ze samu bacci Amma inya tashi A tabbatr yaci Abinci...doctor Ahamad ya kwashetarkacensa kna yyma Annah sallama ze wuce ...Annah ta kalli sankwansa ta kwasheda daria.. Doctors Ahamad ya rasa me takewa daria a jikinsa, seyahau dube dube,... "Amma wannan kan naka kwal kwabo kakeyi kou..rantalilis kenan..kai kaga kai tal sekace za a duba madubi.. " Annah tayi mgnr tana qara bushewa da daria.. Ba itaba hatta KYAUTAR ALLAH Abun ya bata daria shi knshi Raslan mara lafia Abun ya basa daria, girgiza kai yy a rnshi yace "kai wannan tsohuwa Akwai fitina.."

Doctor kam murmushi yy yace "Aah ba Aski nkeyiba Sanqone, hk Allah yayini.."

Annah ta qara kwashewa da daria tna gyara glashin idonta danshi da da kyau.. "Wai! Amma kou knada katon sanqo! Sekace dan matsafa..Ga muni sekace a ynka ka a boye wuqar.." Ta kra fashewa da daria.. KYAUTAR ALLAH kam bakinta ta rufeda hannunta, sbda itama ji takeyi kmrta kyakyata..

Doctor Ahamad kam dariar yy yace "Hajia kenan..ai hk Aka haifeni.."

Annah ta riqe haba tace "Wai! Ammakou Allah yy halitta A nan, uwarka tasha whlr haihuwar wannan katon kan naka,..tabdijan! Allah me halittah.." Ta kara kwashewa da daria.

Raslan ya girgiza kai cikeda uban takaici yace " sorry doctor pls...ngde semunyi waya. "

Doctor ahamad yy yar daria kna yace "Bkm sir..Ai gobema zan dawo in mka injection.."

"Okay tnks.."

"No problem sir..Allah yasa kaffarace.."

"Ameen.." Raslan ya Amsa yna lumshe ido, sbda baccin dayakeji.

Doctor ya juya ze fice Annah ta kira sunansa. "ahamad.."

Ya juyo tareda amsawa fuska sake "Na'am Hajia.."

"Dafatanede bkji haushiba kou..uhm tou inma kji haushin yaza kyi, ngde Ai hkn kke..kirarka Abun daria..gaka dan wada dakai.." ta kara kyalkyalewa da daria..

Doctor yace "bkm Annah ngde.." Inda sabo ya saba inde yazo seta samu wata halitta tashi ta sokeshi da ita.juyawa yy yabar falon yabar Annah nata daria, gashi bb halin a mata mgna..

Kunya kmr ta kashe Raslan...KYAUTAR ALLAH ta kwanta jikinsa, tna masa Sannu har bacci ya kwasheshi, me matukar nauyi.. Annah kam data kallesu setayi uban tsuki "Tou Ande kusa dena wannan iskncin..kwana nawane maye yy Amarya ya lashe.." Annah ke fadar hkn itakam KYAUTAR ALLAH tanajiintane kawai Amma btsan me mgnr tata take nufiba.

Kwanansa biyu yasamu sauki ba lefi, KYAUTAR ALLAH na basa kulawa ta musamman, mkrntarma dena zuwa tayi, kullum suna maqaleda juna,..Raslan ya bugawa Annah wani jahilin Gargadi, kan kadata kuskura ta kira wani a kn bashi da lafia,...Annah ta haushi da zagi, ta uwa ta uba..Amma kuwa tji gargadi sbda tasan halin Raslan..

Packing car dinta tyi kirar corollah, red color, cikin isa da kasaita ta ziro kafafuwanta wadanda suke sanyeda red din shoe kasancewar less din dake jikinta red and mint color ne.., dinkin doguwar rigace A jikinta, dinkin ya matseta gam-gam, fans babbar mace cefa domin takai 50yrs, Hajiya Hadiza kenan.. fuskarnan tayi ja jawur saboda tsabar bleaching, gabobin hannunta kam kmr kyi Amai,yayi baki kirin dashi, bleaching kawai ke mgna a fatar jikinta wai a hknma da Akwai hutu da kwanciar hnkli a tareda ita. Hannunta riqeda hand bag red sbda red dinne beda yawa sosai a jikin lace din. Handle din car din ta mayar ta rufe kna tyiwa motar key tna tafe da kyar sbda ga tsawon takalmin again kuma ga kyn sun matseta. Nanko gani takeyi bb wani shege a garin Abuja se ita.

Ma'aikatan gidan se koro mata gaisuwa sukeyi tna Amsawa a yatsine kai kace gidan na ubantane, ko kuma itace matar gidan. Direct ta nufa falon gidan da sallahma tasa kai cikin falon.

Ummih na gishin gide tna kallon tv ta tashigo, da sallama. Jin sallamarta yasa ummih tashi zaune cikeda murna da farin ciki ta Amsa sallamarh.. "Ah'ah aminiyars kece ke tafe kenan lallai yau za ayi ruwa da qamqara.."

Guri ta samu ta zauna hadi da washe baki haqorin makan dake bakinta har guda hudu biyu sama biyu qasa suka bayyana. "Aida nyi fushi dake nace bazan qara zuwa gidankiba..hba hajia ace kullum niketa zirya a hnyr zuwa gidanki Amke kam sam bakison zuwa, se inzo gidanki so hudu , sannan ke zakizo so dya..ai mutumcinmu ya wuce hk Hajia munfa zama kmr jini daya.."

Ummih ta marairaice kna tace "Yi hkri hajia hadiza kemade knsan ba lefina bne wlhy..Alhajine uban yan kishi sam beson ina fita sekace ni kadaice mace a dunia..ko ince sekace wata yar sha bakwai.."

Hajia hadiza tayi yar daria kna tace "Bnga lefinsaba ta wani fannin..Ammande Ai alhaji yasan yadda nke dake, uhm an rigafa An zama dya.."

Ummih tace "hkne kam..ai Danma gidankine yke barina na fita..ya iyalin naki?"

"Alhamdulillahi, ya Nki iyalin.." Cewar hajia hadiza

"Alhmdllh.." Ummih ta kira laraba tace a kawo mta abun motsa baki, Aiba jimawa Aka cika mata canter table din dke gabanta da kayan dadih. Nan ta fara tabawa sannan suna taba hira. "Hajia yaya yaran nkine knsan kjn fimu kusa dasu.."hadiza ke tambayar Ummih.

Ummih tace "suna nan lafia lau, hajia...dmn inaso in sameki muyi wata mgna.."

.hadiza ta kara gyara zama kna tace "tou ina jnki qawata.."

"Kan yaran nan ne namu..nace wai yan magun gunan nan baki batane?" Ummih ta tmbya Aminiyar tata, ta gugar jigida..

Hadiza ta tabe fuska kna tace " wlhy ina iya qoqarina, Amma sam batasha, se isknci iri iri, mijinne yy complain kou?" Hadiza tyi mgnr cikin kissa.

Ummih tace "Ah'ah wlhy, ni sam be taba kawomin karartaba.."

Hadiza tace "Allah sarki, yaronne ba ruwanshi wlhy..matsalarde dyace Wannan Abun nashi knsn yaranmu na yanzu sam basuda juria.."

Ummih tace "Ai tnama qoqari wlhy..sede a kara mata natsihade knsan yaranmu na yanzu se hkri.."

cikin kissa da kisisina hadiza tace "hkne kam hajia..Amma gyaran Ai kou kece kikayi bkm,ai duk Anzama daya.."

Sosai ummih taji dadin magar tata tace "Tou shinenan hajia..ngde da karamci Allah ya kara hada kn yaran namu kada su lalata mna zumuncinmu.."

Hadiza tayi carab tace "Hba hajja Aikou bb yara muna tare, Insha Allahu yara bazasu lalata mna zumunciba..Allah na tubama ga yaron nga ba ruwanshi, sam beda yan hange hange.."

Ummih tace "gaskia kam..Allahde ya shirya mna zuri'arh.."

Ummih ta Amsa da "Ameen ya rabbih.." Nan suka cigaba da hira irin tasu ta manyan mata. Se yammaci ta wuce byn ummih ta cikata da kayan arziki, Hadiza ta Amshe tnata koro godia, dmn hknne ya kawota, don hadiza tanada kwadayi ba lefi dukda mijinta nada rufin Asiri.

Byn kwana biyu Ummih da knta ta kira Gimbiya Ihsan gidanta, aikou ba jimawa tazo sanyeda doguwar riga me hannun best irin me kwancia a jikinnan bb inda Ba a gani a jikinta, seta sako wani gyale wanda dashi da babu bambamcinsu kadanne, ta ratayo bag dinta irinta yammatar, wannan karon plat shoe tasaka, ta zauna a falon Ummih ta hakimce tna cin Cake din da ummih tyi me mugun dadih tna korawa da exotic drink, me mugun sanyi, ,. Ummih dake zaune kn kujerar dake facing dinta ta zuba mata ido,cikeda mamaki take kallonta, irin wannan shigar nata na firgita Ummih, kyaun wannan shigar Ai kayiwa mijinka shi kaidai a daki..

"Waini shin bakijin kunyar yawo da wannan kyn na jikinki ne inlow.." Ummih ta tambayi ihsan knta daure.

Tsagaitawa ihsan tyi dacin cake din ta tsaya karewa knta kallo,kna tace "Me shigata tyi ummih? Sbdafa knayimin fadane shiyasa nasa wannan kyn masu mutumci dazanzo nan, bnso ki gni kiyimin fada.."

Wani mamakinne ya kara baibaye Ummih tace "ai hkn masu mutumcine? .."

"Eh ummih.." Ihsan ta fada tna qarewa knta kallo.

"To wai bakida Atanfofine da lace, nadesan kinada dogayen riguna .." Sbda tna aika mata da kusan kla goma sha a lokaci dya.

Ihan tace "inadasu sosai Ummih.."

"Metasa bakya sawa?" Ummih ta tambayeta.

Dan guntun tsuki ihsan tyi kna tace "mtws! Ina zan iya da wannan kyn zafin, nifa na riga na saba da wadannan kyn Ummih sunfimin dadih wlhy... "

Ummih tji jim hadi dayin murmushi tace "kai yarinta na damunki inlow..tou ynzude ba wannanba na kirakine inaso muyi mgna bnaso ki daukeni a matsayin sirikarki, aah ki daukeni kmr qawarkice ko yayarki.. "

Ihsan tace "tou UMMIH.."

"Inaso ki gyamin yaushe rabonki da mijinki tsakaninki da Allah.." Ummih ta jefo mata tambayarnan.

Jim ihsan tyi tna naxarin tmbyrta gareta "wato ya kawo karata kou..shi uban yanson gindi.." Ta fada a rnta amma a fili se tace "An dade gaskia.." ta fada idonta tsaye

"Meyasa an dade.."

"Ummih sbda be nemeniba..kullumma yna ziryar zuwa katsina ina ma yga lokacin daze nemeni.."ta karashe mgnr cikeda kishi.

Seta bawa Ummih tausai sbda da zafi ace mijinka be kulaka "okay yi hkri kinji kou my doter karki damu time na zuwa ze dena..Abindama yarinyar ta kusa Aure kowa ya huta.."

"Dan Allah fa ummih? Da gaske ta kusan Aure? Amma kuwa da nafi kiwa farin ciki da murna.." Ihsan ta fada cikin murna.

Ummih tace "Kwanan nan ma kuwa zaki huta doter..Amma ykmata ki rinka neman mijinki base ya nemekiba, sbda hkn na qara miki qima a gun miji.."

Zaro ido ihsan tayi tace "wai! Ummih wlhy bazan iyaba, wai! Bnma nemeshiba ya aka kare ina mgna na nemeshi,..ummih kullumfa inya kusanceni se Anyimin dinki..gaskia ni yafi karfina.." Ta fadi hkn gatsal.

Se ummih tji tausayinta domin tasan tnada juria a hknma "Ina magungunan da nake baki?"

Ihsan tace "inasha ummih..amma wlhy indeze kusanceni seya kureni koumi nasha ...nifa tsorinshima nkeji gaskia Ummih dade kawai inasonshine nke zaune dashi. "

Ummih tayi shiru tnajin klmn Ihsan "Kishiya kikeso a miki?"

Cikeda firgice tace "Allah ya kiyaye! Nida kishiya Aikou a lahira! Hba UMMIH meyasa kkemin fatannan, wlhy har knsa gabana ya fadi.." Ta karashe mgnr tna dafe kirji.

Ummih tyi shiru tna nazarinta, ga azabar kishin tsiya Amma kuma ba asan me za awa miji yaji ddhb. "Aiba fata nke mikiba my doter..nima nan bazanso A miki kishiyaba,..."

Ajiyar zucia ta sauke se ynzu taji sanyi sanyi A ranta..

"Ki kama kanki kinji my doter ki kula da mijinki, sbda mazan ynzu ba irin nada bne,..."UMMIH ta fara mata natsiha.

Yatsina fuska ihsan tyi kna tace "Ummih inafayi masa komi...nifa UMMIH kawai, dande Abun nasane yayimin girma,..Kuma ina iya qoqarina dashi.."

Ummih tace "nasani wlhy doter..Inade miki natsihace kan ki qara kaimi..sannan ki qara Kaimi gunsha magungunan da nake

2 Comments On KYAUTAR ALLAH
avatar
maryam-8-8-3

1 year ago

Reply

Aslm

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryam-8-8-3

Wslm

Please Login or Register in order to submit comment