Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gefen bed din ita kuma KYAUTAR ALLAH tana kwance sanye da rigar bacci red ta amshi jikinta sosai, kallo daya ya mata yaji jarabarshi ta tashi. Karasowa yayi ya zauna kusa da anty Rukayya cikin sakin fuska yace "Sannu Mommy..." Cikin fara'arh Anty Rukayya ta amsa da "Yauwa kakah...ashe KYAUTAR bataji dadih ba..." RASLAN yace "Eah wallahi mommy nace mata muje asibiti Amma taki yarda, ulcer ce ke damunta kinsan batason cin abinci kwata-kwata..." Anty rukayya ta zuba masa ido harya gama maganar, a kalamansa ta gano be ganema kunshin daya kunsa mata ba kenan. "Gaskia wannan Ulcer Kam babba ce, ya kamata kuje asibiti.." RASLAN yace "Ai nima na gaya mata, bakiga yadda duk tabi ta rame ba, ss tayi ubab fari..." Anty Rukayya de ta zuba masa ido kana tace "Son harda kai kake ramar da ita, dannaga alamar ba bu wasa a lamarinka.." Tsaf ya fahimci me take nufi sosa keya yayi hadi da yin murmushi ya zubawa KYAUTAR ALLAH ido, itama shi din ta zubawa idon tin shigowarshi taji kamshin wani abu a cikin ledojin daya shigo dashi kamshin yayi mata dadih sosai dukta kagu taga ko meyeshi abunnan me kamshin dadih. "Ba haka bane mommy..." Ya fada still yana sosa keyarsa. Anty rukayya tayi Murmushi tace "in ba haka bane to yaya ne? Ya kamata ka rinka daga mata kafa plx da wanne zataji..., ga nauyinka ga kuma ulcer dake damunta..." Sosa keya yayi kmr muna fuki yace "tou mommy zan daure inyi yadda Kikace....kin desan ba lefina bane, bazan boye miki ba mommy yarinyarnan nada mugun dadih ne Wallahi.." Maganar setaso ta bama anty Rukayya daria da kunya ma baki daya, Shiru tayi bata kara Magana ba gudun kada ya fadi mgnr datafi karfin lissafinta, dan tasan halin RASLAN sarai ba kunya bace a idonsa. Taso da ita yayi ya tasa mata ledojin a gabanta ai kamar tana jira tashiga bubbude ledojin dukta kagara taga menene wanda kamshin shi keta kaiwa hancinta ziyara. Kayan makulashe ne da tande tande da ice cream dasu kaji e.t.c kwata kwata ko ganin ice cream ma batason yi a halin yanzu. Duk ta gama dube dubenta bataga abinda taji kamshin nashiba, komi ma ji tayi bata sonshi kawai ta fashe da kuka saboda ga abinci tana son taci Amma babu halin taci infect ma ko ganinsu batason yi.... Ba karamin rikicewa RASLAN yayiba ganin ta fashe da kuka kamar zararriya ya shiga tambayarta meya faru, babu amsa se kukan kawai...itama anty rukayya hankalinta ya tashi ta shiga tambayarta meya faru, duk bata tanka musuba haushima taji suna bata... RASLAN kamar wani zararre haka ya koma se bata hakuri yakeyi kmr ze zare shima, da kyar aka samu ta sassauta da kukanta, tace batama son ganin abinda RASLAN din ya siyo mata, jiki na rawa ya kwashi komi yasa a frij, se tambayarta yakeyi me takeso tayi bnza dashi ta koma ta kwanta tana ajiyar zucia se jero mata sannu sukeyi shida Anty Rukayya, batafi 10mnt da kwancia ba bacci me nauyi yayi awon gaba da Ita se ajiyar zucia kawai take saukewa a wahalce....RASLAN ya jima a dakin yana jira Anty Rukayya ta fita, Amma taki fita dole seshi ya gaji ya tashi ya fice a dakin bayan ya mata seda safe, da kewar matarsa ya nufa bedroom dinsa, zucia babu dadih, saboda yanada tabbacin yau baze rintsaba tinda babu gindin daza ayita caccaka.

Washe gari su Anty Fahima da fatima sukazo gidan, suna ganin KYAUTAR ALLAH seda duk sukayi mgnr ramarta amsarde dayace ulcer ce ke damunta, ...Anty Sadia ma datazo taga ramar da tayi seda tayima RASLAN magana yace mata ulcer ce ke damunta, Anty sadia ta shiga kare masa kallo tace "Ba wani ulcer son, kana takura wa yarinyar nan ne da sex gaskia, ya kamata ka rinka daga mata kafa, haba son bakaga karancin shekarun ta bane..." RASLAN ya sosa keya kawai ya amsa mata da to, domin shi kanshi yasan yana matukar takura mata, danma tanada juriya Sosai a kam jima'i. Ummih kam sam batama gantaba.

Sosai anty rukayya ke bata kulawa komi tace tanaso ita ke dafa mata wani taci wani kam tace bata iyaci,.. Anty rukayya ta kira dr hannatu ta tambayeta wani mgni mace me ciki ya kamata tasha wanda zataji karfin jikinta. Ba jimawa ta turo mata da sunan magungunan ta message . ta Kira Jummai ta aiketa ta siyo ta bata tasha, tin a ranar ta dan farajin karfin jikinta... Duk abubuwan nan dake gudana Annah bata saniba kullum cikin yin baki take tanaso ta hayo saman taga KYAUTAR ALLAH amma hakan beyuba ga ciwon kafarta daya sata a gaba, dan haka sede tasa jummai taje taganin mata ita, seta aiketa saman fin so goma tace aje a ganin mata lafiarta, sede jummai ta dawo tace mata lafiayarta lau, haka ma inta tambayi Anty Rukayya take ce mata lafia lau, a tunanin Annah ko tafison zama ne a nan saman shiyasa ta barta ba tare data takurata kan dole seta sauko kasanba. Kwana biyu sukayi kowa ya watse. Amma banda Anty Rukayya, wadda ta takurawa RASLAN ta hanashi rawar gaban hantsi ta kulle ko wacce kafa daze kadaice da ita, dan Anty Rukayya ta fara tunanin beda hankali ne, shi a hakan datakema da zata bashi gindin hayewa zeyi yayita ci. Duk yadda ya kaiga kwad'ayinta dole yayi haquri yasawa ranshi salama kullum cikin shan coffee yake kamar dan buzaye.

ganin Anty Rukayya kullum tana tare da kyautar Allah shiyasa Annah bata damuba dan tasan zata bata kulawa Tana nan de Ankare dasu but ba wani yadda ta bawa anty Rukayyarba 100%. Sosai Anty Rukayya ke bata kulawa har wani murmurewa tayi ta danyi yar qiba ta samu sassaucin laulayin sosai se abinda baza a rasaba sosai magungunan datakesha suke temaka mata, Tsakaninta Da RASLAN de ido... Satin Anty Rukayya daya a garin ta koma gidanta ta bar KYAUTAR ALLAH da kewarta, sam bata sanar da RASLAN cikine a jikin KYAUTAR ALLAH ba, ta bari cikin ya bayya knsa da kansa garesu tindashi bame boyuwa bane, sosai tayima RASLAN natsiha kan kada ya rinka takurawa KYAUTAR ALLAH da yawan sex, Amma ina ai tana tafiya, daren ranar ya lallabo yaci gaba da lafta mata bura, be bartaba seda Asubah aiko ta galabaita kwana biyu dabeyiba harta huta amma yanzu kam tasan ta shiga uku, inda abinda yafi uku ma ta shiga, gashi gabanta ya kara rufewa. Bayan Tafiyar Anty Rukayya da sati daya ya koma garin katsina da kewarta bayan ya barta da gajiyarsa, but a satin sam be daga mata kafa ba se yaje gareta sau uku a rana, daya dan faki ido shikenanfa seya nufa upstairs, ya dangana da gindi.. Washe garin ranar daya tafi taci gaba da zuwa isilamiyyarta da boko, daman an koma ita cede bata komaba. yanzu kullum se sun hadu da Annah, sede kullum cikin hijjabi take ganinta saboda Anty Rukayya ta mata wannan hudubar nasa hijjabi in zata sauka kasan, saboda inhar babu hijjabi a jikinta dole Annah Inta ganta ta gane akwai shigar sabon ciki jikinta, kullum cikin waya suke da RASLAN da Anty Rukayya ma wadda ke bata shawarwarin yadda zata kula da kanta.

Bayan tafiyarshi da kwana biyu ya kara dawowa yaci gaba da lafta mata bura, duk abinda yakeyi sam be bar kofar da Annah zata gane komiba... Wasu lokutan tana bukatarsa Amma wasu lokutan kawai yana cinta ne ba ason rantaba, inko bataso ta rinka masa bakin rai kenan ko yagama ranar wuni zeyi yana rarrashinta,... Kwana biyunnan kafar Annah ke matsa mata da ciwo dan haka sam batama wani cika zama a faloba doctor na zuwa yana dubata, kullum tana daki,.. Hakan ya bawa Raslan damar cin gindinta yadda ranshi keso, babu daga kafa, daomin ta kara masa dadih in yana cinta kmr zararre ko mahaukaci....satinshi daya a garin ya koma garin Abuja yaci gaba da aiyukansa , a halin yanzu bama su cika haduwa da ihsan ba, ta dawo da shegen yawon nata ita da qawatenta aminanta nimcyluv da maryam, sam RASLAN bema cika bi ta kantaba. Hajiya hadiza kam kullum cikin kawo mata kulle kulle takeyi wai tayi amfani dashi danta mallake mijinta, a tafin hannunta ta yadda baze auri wataba, tinda sun samu ya rabu da KYAUTAR ALLAH, a tunaninsu kenan,... A yan kwana kinnan nema take zuwa side dinsa saboda tanada bukatar kudi, sede yayi romancing dinta kawai ya barta ba tare da yayi sex da ita, romancing dinma dan jarabar tasa ta shahara ne, inde zega duwawu da kayan ruwa nonuwa bashi iya hakuri seya latsa, seya gama lallatsata ze bata abinda takeso sam be tunkarar gindinta zuciyarsa na kan gindin KYAUTAR ALLAH nan yake iya jin dadin na fitar hayyaci, saboda haka yasa baya tunanin gindin ko wacce mace a halin ynzu.

Yau gabaki daya ta tashi batajin dadih ne kwata-kwata, se amai taketayi dukda ba komi a cikin ta se ruwa, ko ruwan tasha se tayi amanshi, duk a galabaice take gashi tanada school, isilamiyya cede basu dashi, yau se hadda haddar kam bata wani cika zuwa ba ynzu. 7:57pm ta gama shiryawa da kyar, shirinta na zuwa school kallo daya zaka mata ka gane bata jin karfin jikinta kawai tana daurewa ne. Bag dinta ta dauko ta fara sakkowa a matattakalar a hankali a hankali taku uku hudu seta zauna ta huta tana maida numfashi se uwar zufa takeyi kmr wadda tayi karya aka kamata. A haka ta gama saukowa kasan a matukar galabaice Annah dake zaune kan kujerar 3sttr tin sakkowarta ta zubo mata ido, tana kallonta se zama takeyi tana hutawa harta karaso falon se nishi takeyi tana zufa ta karaso ta zauna kujerar dake facing Annah ta gaidata, Ansawa tayi idanuwanta na kan hannayenta dake bisa cinyoyinta. Sosai Annah ta kureta da ido musammanma yatsun hannunta dataga sun kara cika ba yadda tasansuba, kuma ita ta rame a jiki Amma yatsunta sunyi kiba, abinda yafi komi damunta yadda kullum take sanye da hijjabi kmr matar malam, tin bata tunanin tana boye mata wani abu ne, har a yau ta fara wannan tunanin. "Baki jin dadih ne yau ma?" Ta jefo mata tambayar, ... "Eah!" Ta bata amsa Se uban zufa takeyi har lokacin dukda sanyin a.c Dake falon, Amma sam bata jinsa wani irin zafi takeji na matsifa a yau din, tinda ta tashi take jin zafin. Annah tayi jim kawai tana kallonta tace "Wai wannan wani irin ciwo ne ke damunki? Se uban rama kikeyi kina kara haske wani irin ciwo ne wannan?" KYAUTAR ALLAH tayi shiru na yan wasu daki'qu kana ta miqe tsaye, hadi da miqa tayi hamma kana ltace "ulcer cefa .." Da ido Annah ta bita se miqa takeyi tana zabga hamma kmr wadda akawa duka. "Bazaki raka niba plx?'' Tayi mgnr tana marairaicewa . "baza kiyi karin kumallo bane?" Annah ta tambayeta. KYAUTAR Allah tace "Bana jin yunwa ..." Annah ta zuba mata ido kana tace "Bakijin yunwa...haka kike kullum babu ci babu sha... Wata rana zaki kashe kanki a banza..." KYAUTAR ALLAH da tini ta gaji da tsayuwa tace "Naji...nide taso muje ki rakani..." Miqewa Annah tayi ba tare datace mata komiba ta dauko sandarta ta fara takawa a hankali..KYAUTAR ALLAH na gaba ita kuma tana biye da ita a baya se karantarta takeyi har suka isa bakin car ta bude mata tayi ta shiga dreva yaja sukabar gidan. Komawa cikin gida Annah tayi zuciya cike da tunani hadi da nazarin KYAUTAR ALLAH.

yau kimanin satinshi daya da barin garin katsina, kullum suna manne a waya, sam sam bata kewarsa saboda a fari tanason sex din Amma ynzu kwata kwata ma bata kaunar jin kalmar sex...Yau ta kasance weekend ne, basuje isilamiyya ba saboda daya daga cikin malamansu ALLAH ya masa rasuwa, tin 12:20pm fatima tazo gidansu sunsha hira sosai, se kallonta fatima takeyi saboda ramar da tayi, ga hasken da tayi kullum kara karuwa yakeyi. "Frnd wai ko kin fara shafa cream ne na bleaching?" Fatima ta jefo mata tambayar. Girgiza kai KYAUTAR ALLAH tayi tace "Ah'ah bana shafa komi wlhy, ...haka ake cewa wai nayi haske kuma bana shafa komi..." Da mamaki Fatima taci gaba da kallonta tace "Kai! Kinko yi kyau kinyi fresh sosai, kamar me sabon ciki..." Jim KYAUTAR ALLAH tayi tace "waya gaya miki me ciki tanayin fari?" FATIMA tace "nasani mana, ai ina gani da sister din momy ta samu ciki haka tayi fari sol da ita tayi kyau abun sha'awah, shine su mommy keta cewa ciki ne da ita, ashe kuwa da gaske ne, bayan wasu lokuta ta haihu......" KYAUTAR ALLAH tayi jim tace "Uhum ni ai nayi karama ma da samun ciki ai kanana basa samun ciki..." Fatima tace "ta ina ma zaki samu ciki bayan baki da miji...kinsan dole se in kanada miji zaka samu ciki Ai..." KYAUTAR ALLAH tayi shiru tana tunanin kalaman fatima kana tace "Meyasa dole se da miji za a samu ciki?" Fatima ta jefeta da wani kallo na mara wayau kana tace "eah mana in babu miji ta yaya za a haihu..har yanzu frnd baki da wayau keda aka taba miki abinda miji da mata keyi Amma har yanzu bakiyi wayau ba. ." KYAUTAR ALLAH ta gallara mata harara kana tace "Wayace miki bnda wayau.." Fatima tayi Murmushi ganin ta gallara mata harara kmr kwayar idonta zasu fadi kasa, tasan ta shaqane. tace " Yi hakuri me wayau..." KYAUTAR ALLAH ta sakar mata murmushi, itama ta mayar mata da murmushi....haka suka cigaba da hira se 5:pm fatima ta bar gidan. Bayan ta dawo daga rakata, shaf tama manta bata sako hijjabi ba, sanye take da riga da zani na atamfa tuma tuman duwawuknta kmr zadu fasa zanin dake jikinta sun kara girma sosai haka ma kirjinta dukda cikin dake jikinta be gama kai 2 month ba, but ya kusa. Gyara dankwalin atamfar dake kanta tayi, dai-dai ta shigo falon... Idanuwanta dana Annah suka sarke cikin na juna, cikin lokaci kankani Annah ta shiga karewa kirar jikinta kallo, ji tayi gabanta ya yanke ya fadi, ta zabura ta miqe tsaye da yar sandarta ta gyara glass din dake idonta dan tabbatr da abinda idonta ke gane mata..."me nake gani haka KYAUTAR!!!" Annah ta fada da karfi kmr zata fasa falon.


*akwai kayan mata ingantattu, babu ne kawai babu....kude ku garzayo ku siya naku kada ku bari a baku labari 08136349646*
[8/24, 19:53] Sa'adatu Bintu Abdullahi: 🅿️55

*PAID BOOK...500 ONLY...08136349646*

*Tou! Readers mutanenmu... Wasu da dama suna canza lambobi suna zagina nida iyayena, suna cewa zan gani! Insha Allahu bazanga komi ba se alherih..! Bn muku mugun baki ba Amma na farku da fitar rana da faduwarta.*

SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽

Gaban KYAUTAR ALLAH ya yanke ya fadi saboda yadda Annah tayi maganar da karfi seda yan hanjin cikinta suka kad'a, tunani ta shigayi meyasa Annah ta jefeta da wannan kalmar, nan jikinta ya bata yau asirin dasuke kullewa ya budu. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Ta fada a ranta, yayin da zuciarta keta up up kamar zata fito fili, hnklinta in yafi dari hudu seda ya tashi. Jiki na rawa Annah ta karaso inda take ta kamo fingers dinta na hannun dama ta shiga binsu da izo a razane, taga sun ciccika sunyi aiba bul-bul dasu, har wani shinning sukeyi fiye da ada, ta kara kamo dayan hannunta na na hagu ta zuba ma fingers din nata ido, , gabanta ya kara yankewa ya fad'i zuciyarta kmr zata faso ta fito fili, har wani zazzabi taji yana neman rufeta. "Na shiga tara ni a'ee!! Dan ubanki bude bakinki in gani!" Ta daka mata tsawa, kyautar Allah kam tini jikinta ya hau rawa, tini jinin dake jikinta suka rikide, suka fara bata zafi a cikin jikinta, nan da nan zufa ta fara karyo mata. Jiki na rawa ta budewa Annah bakinta,... Annah ta lalleqa cikin bakin nata, ta dawo ta daga harshenta, ta lalleqa, ta gwale kwayar idonta kallo daya tawa kwayar idon nata jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta fara barazanar fitowa zahirin ALLAH ta'alah. "Haba! Wallahi ciki gareki!" Annah ta fada a razane Ba ita da tayi magabarba hatta KYAUTAR ALLAH seda hantar cikinta ta juya, ruwan dake yawo a jijiyoyin jininta suka birkice saura kadan su hade da jinin jikinta saboda tsabar firgici. Mamakin da Annah keyi shine ina ta samu ciki, bayan tayi period da RASLAN ya sadu da ita ballan tana tace cikin nashi ne, tana ma da tabbacin a lokacin da wuya in ciki ya shiga, kuma ma ai ita a ganinta RASLAN be haihuwa ta ina zema KYAUTAR ALLAH ciki, bayan matarsa da suke tare sunfi shekara da shekaru ko batan wata bata tabaji ance tayiba. "Na shiga tara! Na lalace! Na mutuh! Na tambad'e! Duniyata ta tankad'e da ni! Ni naga shiga uku takabar siriki! Wannan yarinya kin cuceni kin cuci rayuwata!" Annah ta fashe da matsananincin kuka rai a dagule, KYAUTAR ALLAH ma fashewa tayi da kukan cikin tsananin dimauta da dumbin tashin hankali. "Shegiya! Yar iska! Kukan uban me kikeyi! Dan kutmar ubanki ina kika samu ciki!!" Annah ta jefo mata tambayar cikin kuka da tsananin bacin rai. Kara fashewa da kuka KYAUTAR ALLAH tayi ta sauke idonta kasa, tana girgiza kai kawai fuskarta dauke da dumbin tashin hankali, hadi da rud'ani. se zufa kawai ke kwarara a goshinta, da duk sassan jikinta lungu ds saqo, zanin dake jikintama barazanar faduwa yakeyi ta kamoshi ta riqeshi gam a hannunta. Ran Annah ya kara baci matuka tinda take da KYAUTAR ALLAH bata taba bata mata rai ba irin na yau, ta riga ta gama sadaqarwa wani dan iskan ne ya lallabo yama KYAUTAR ALLAH ciki, da ace RASLAN na haihuwa ne dase tace shi ya zagaya ya narka mata ciki. "Na shigesu! Na bani! Dan kutmar ubanki baza ki bani amsaba! gidan durun uwar waye kika samo cikin shege! Wani la'anan nan ne ya miki ciki!" Annah ta fada zuciya cike da tsananin bacin ranta ji takeyi kmr ta kasheta da duka a lokacin. Zubewa kasa tayi hadi dayin kneel down a kan guiwowinta kawai ta kara fashewa da wani matsanancin kuka saboda batasan wacce iriyar amsa zata bawa Annah ba a kan tambayar datake mata. Annah ta kara fashewa da kuka har lokacin idanuwanta nata yawo a duk sassan jikin KYAUTAR ALLAH, ta riga ta gama tabbatrwa shigar sabon ciki gareta a jikinta, ga alamomi nan sun bayyaba, basema an gaya makaba, Fashewa ta karayi da kuka "kin cuceni! Kin cuceni! Asheke muna fuka ce bansaniba! Haba daushen goro yayi kama da goro! shine dalilin dayasa kullum kike kunshe da hijjabi! To yau dubunki ta cika! Kin cuceni kuma kin cuci kanki! Iya cutata kawai kikayi amma baki lalatamin rayuwaba! Ke ko kin cuci kanki kuma kin lalata rayuwarki a banza a hofi! Kin bawa wani katon banza al'aurarki ya lalataki a banza a hofi! ALLAH ya isa tsakanina dake rukayya!!" Zuciya ta debeta kawai ta shiga rada mata sandar karfen da take dogawara, sam bata gani saboda tsananin bacin rai, tana dukanta da sandar tana tambayarta "gidan ubanwa kima samu ciki!! Wani dan gaba da fatihar ne yayi miki cikin gaba da fatihah! Kin cuceni kin batamin zuri'ah! Kin dauko min dan shege! ALLAH ya isa tsakanina dake!!!" Annah ke fadi still se dukanta takeyi da sandar, sosai takejin zafin sandar nan ta shiga kurma ihu, kmr ranta ze fita, taba bawa Annah hakuri... Ihun nata ne ya ankarar dasu jummai da laraba dake kiching suna shirya abincin dare, dakatawa sukayi da aikace aikacen dasukeyi saboda kukan dasukejiyowa a falon Annah, ba wani bata lokaci suka nufo falon a guje, idanuwansu suka sauka a kan kyautar Allah Dake tsugunne se duka Kawai Annah ke kai mata da sandar karfen dake hannunta, sosai sukayi mamakin ganin Annah na dukan KYAUTAR ALLAH yau da kansu abinda basu taba ganiba tsawon zamansu a gidan se yau.... Jiki na rawa jummai ta karaso tana Bawa Annah hkri, Amma ina idanuwanta duksun rufe se kwala mata karfen takeyi, tini wasu sassa na jikinta suka fara fitar da jiki saboda azaba tanaso ta tashi ta gudu Amma ina ta gaza tashi ta gudun saboda kafafuwanta dasuka mata mugun nauyi. "Annah ki bari karki kasheta!!" Jummai ta fada kmr zata fashe da kukan tausayin KYAUTAR ALLAH, Annah na haki tana fadin "Ki barni in kasheta!!" Ta daga sandar da karfi ta rada mata a dai-dai saitin goshinta ai ba wani bata lokaci jini ya balle ya fara zuba saboda wawakeken ciwon dataji mata a goshinta ya shahara ... Azabar ciwon data ji mata a goshin ya gigitata, abinka da jikin yan hutu ba asaba da wahala ba, nan da nan ta gigice ta fice a hayyacinta, ta fashe da matsanancin kuka , bata masan sanda ta miqe ta a haukaceba ta dafe knta inda ke zubar da jinin ta ruga da gudu kmr mahaukaciya zata fice a falon, dai-dai ya sako kai sukaci karo da juna, ta juya zata fadi ya tarota da hannunsa na dama, ya zuba mata dara daran idanuwansa, meze gani! Jini yaga yana ambaliya a goshinta babu kakkautawa,,se fisge fisge takeyi sam bata hayyacinsa batamasan a hannunsa takeba, fadi takeyi. "dan ALLAH Annah karki kasheni! Ba lefina bane!! Wallahi bansan ina da cikiba!!" Kalaman dake fita daga bakinta kenan cikin fitar hayyaci. Sam be fahimci kan maganganun nataba yaji tausanta ya rufesa, again zuciarsa ta cika da mamakin wai yau Annah ce ke dukan KYAUTAR ALLAH da hannunta, daba dan yaxo yaganinma idanuwansaba da ko gaya masa akayi baze taba yadda ba . "meya samu goshinki plx?" A matukar razane ya tambayeta, idanuwansa duk a waje kmr zasu fito fili saboda tsabar tashin hankalin ganin jini na kwarara babu kakkautawa daga goshinta.. Dai-dai Annah ta karaso ta fisgota a hannunsa tana jijjigata tana fadin "zaki gayamin gidan ubanwa kika samu ciki ko senayi ajalinki yanzunnan...baza ki jawomin abin kunyaba da raina d lafia taba....kwara in kasheki in huta...!" Kalma daya ya iya riqewa a cikin kansa nan da nan ya shiga juya kalmar a cikin duniyar kwakwalwarsa, " ciki! Ciki! Ciki! Ciki kuma?" Ya jefawa kansa tambayar da bemasan meye amsar taba. Kara fashewa da kuka KYAUTAR ALLAH tayi hadda shasheqa kmr numfashinta ze dauke still ga jini nata kwarara ta goshinta, hatta fara ganin jiri,,, "dan ubanki baza ki gayamin wa yayi miki ciki ba!" Annah ta fadi da karfi, bata san sadda ta kufce a hannu taba tana saboda matsifa tana kokarin faduwa ta bugu da hannun kujera RASLAN dake tsaye ya karasa ya tallabota cikin dimauta hadi da tashin hankali,ya juyo da ita, yaga idanuwanta harasun fara kakkafewa saboda jinin daya zuba daga goshinta a kalla ze kai rabin leda. "KYAUTAR! KYAUTAR!!" Ya shiga kwalo mata Kira a razane amma ina tini ta sume , jiyowa yy da dubansa kan Annah, cikin kunar,rai hadi da gigita duk ya fice a hayyacinsa, ya fara magaba "Wallahi matata ta rasa ranta a kanki se kinci gidan yari!!" Be jira wata wataba ya ciccibeta suka fice a falon direct notar dasukazo dashi ya shiga, daman yusuf na ganinsa da ita a hannunsa ayi saurin karasowa yayima motar key suka fice a gidan,... Raslan na zaune a mazaunin baya yana rungume da ita a jikinsa se kiran sunanta yakeyi kamar wani zararre, ... Hkn ya bawa yusuf tabbacin asibiti zasuje, direct asibitin dasuke zuwa suka nufa daman shine asibiti mafi kusanci dasu suna isa ba wani bata lokaci aka nufa emergency da ita a kan gadon daukar mara lafia, wata nurse ke turo gadon, RASLAN na biye dasu , suna shiga emergency room din aka daketa aka daurata a kan gadon dake dakin, Har lokacin jini se kwarara yakeyi a goshinta,

2 Comments On KYAUTAR ALLAH
avatar
maryam-8-8-3

1 year ago

Reply

Aslm

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to maryam-8-8-3

Wslm

Please Login or Register in order to submit comment