Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na daura dankwali na wanko fuskata ban sake shafa mata komai ba,daga cikin room dinmu Ina jiyo muryar Yaya Auwal yana gaisawa da mutanen parlon bayan sun gama gaisawa su Yaya Bash suka fita suka bar masu parlon,magana sukayi sosai da su Yaya sannan Yaya ya leko room dinmu yana ce man.

"Jiddarh Auwal yana jiranki a parlo."

Kallonshi nayi Ina cewa.."Yaya ni har bansan mai zance mashi ba wallahi kunyar shi nike." Murmushi yayi yana cewa."ki natsu sosai Kulu karda ki damu shi Auwal baida damuwar komai kuma ya fahimci abunda muke nufi and ko yanzun sai da muka Kara bashi hakuri nida Haidar dan haka feel free Baby."

Murmushi kawai nayi na dauko hijab dina na saka na fito a hankali nike tafiya cike da natsuwa kamar banson taka kasa,kaina kasa ban yarda na had'a Ido da kowa ba sai da na zauna sannan Yaya Haidar ya tashi yana ba Yaya Auwal hannu yace.

"Broth a fito lafiya."

Murmushi yayi yana cewa."Ina godiya Broth."

Shuru mukayi a parlon can nayi keeping silent din ina cewa.."Ina wuni Yaya Auwal." Murmushi yayi yana cewa.."lafiya lau Jiddarh fatan na samaiki lafiya ya kuma shirin biki."?

Murmushi kawai nayi bance komai ba sai wasa da nike da kasan hijab dina..murmushi yayi yana cewa.."karda ki damu Jidda komai mukardarine daga Allah,haka Allah ya qaddara bamu da rabon kasancewa a inuwar aure dan haka wallahi ban rikeki ba har yau har gobe Ina maki kallon kanwa,Ina fatan kema ki dunga yi man kallon Yaya kamar yanda kike man a baya."

"Nagode sosai Yaya Auwal,Allah ya bar zuminci amman Yaya Auwal dan Allah Ina son na nemai wata alfarma a wajenka."

Gyara zamanshi yayi yana kallona sosai yace.

"Alfarma."?

D'aga mashi kai nayi ina cewa.

"Eh Yaya Auwal."

Murmushi yayi yana cewa."Allah ya bani ikon yi maki wanann alfarmar Jiddarh. "

"Amin."

Shuru nayi sai kuma na cigaba da cewa.

"Daman ce maka zanyi idan babu damuwa dan Allah Yaya mai zai hana ka auri kawata Wasi."

Kasa motsi yayi sai kafeni da yayi da ido furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa.

"Wasi kuma Jiddarh."?

D'aga mashi kai nayi ina cewa.

"Eh."

Uhm!yace yana mai cigaba da cewa.

"Amman maiye dalilinki na cewa na auri Wasi Jiddarh."?

Murmushi nayi kawai Ina cewa.

"Saboda hankalinta da natsuwarta kuma nasan zata kula da kai yanda kike tunanin zaka samu farinciki a wajena haka itama zaka samu sama da yanda kake tunani dan nasan wacece Wasi,nasan abunda zata iya da wanda ba zata iya ba shiyasa nayi maka sha'awar ta zama matarka na tabbata watan watarana zaka gode man kuma fatana kenan na saka maka da alkhari kamar yanda kike man fatan alkhari a Koda yaushe."

Murmushi yayi yana tashi tsaye yana duba time yace.

"Shikenan Jidda na yarda da bukatarki dan kinfi karfin komai a wajena,Allah yasa hakan ya kasance alkhari a garemu baki d'aya we are the best Jiddah."

Murmushi nayi ina mashi godiya har bakin gate na rakashi sai da naga ya bar unguwar na dawo cikin gida a compound na hadu da Yaya Haidar saman rubber chair yana danna wayarshi kallona yayi yana ce man.

"Zo Jiddah."

Nufarshi nayi Ina dan sakin murmushi dan maganar da nayi da Yaya Auwal ta wanke man damuwa da kuncin da naji zuciyata tana man,balle ma da ya yarda da batun auren aminiyata kuma yar'uwata Wasi sai naji zuciyata ta komai watsai babu digon komai a samanta samun waje nayi na zauna Ina cewa.

"Gani Yaya Haidar."

Murmushi yayi yana cewa.."ya kukayi da shi Auwal Ishaq din."?

Kallonshi nayi sai kuma na sakar mashi wani killer smile Ina boye fuskata da hannuna,shima murmushin yayi yana cire hannuna daga fuskata yana cewa.

"Uhmm!tell me mai yace maki haka wanda ya saki happy har haka Jidda."

Dariya nayi Ina kallonshi nace.."ba abunda yace man Yaya Haidar sai dai wata alfarma yayi man wanda ta sani a cikin wannan farincikin."

Murmushi yayi yana cewa.

"Wace irin alfarma ce wannan Jidda."

Gaya mashi duk yanda mukayi dashi nayi Ina gaya mashi ina dariya ,sakale yayi yana kallona sai murmushi yake ni kuwa sai gaya mashi nike daga karshe nace.

"Yaya."

Shuru yayi sai kallona yake yana ta sakin wani killer smile,sake kiranshi nayi kusan sau ukku bai motsa ba kuma bai fasa kallona ba, weaving nayi mashi a fuskarshi Ina turo baki nace .

"Yaya Haidar."

Sauke ajiyar zuciya yayi yana kamo hannuna ya rike yana kallona sai kuma yayi ma hannun nawa kiss,da sauri na janye hannun Ina mai mikewa zan bar wajen kamoni yayi ya maidoni kusa dashi yana rike da hannun nawa can ya manna bakinshi saman..


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*, *AIRTEL*,*GLO* price din su d'aya yanzun masu *9MOBILE* sunyi magana azo dai a sai data

500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*EDITING WALA ❌*

*81-90*


Saukar bakinshi naji a saman kumatu na na sakar mani wani zaizafar french kiss,bansan lokacin da nayi baya ba na tafi tangal tangal zai kefe a kasa,taro ni yayi na fado a saman ingarmar kirjinshi masauki yayi man a saman kirjin nashi yana hura man iskan bakinshi a saman fuskata,boye fuskar tawa nayi Ina sauke ajiyar zuciya.

Mutsu mutsu na fara yi ina neman sauka a saman shi yaki bani damar sai ka kara matse ni da yayi a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya a jere jere,mun fi minti goma a haka sai da ya gadama dan kanshi sannan ya sake ni ya kureni da ido.

Kin yarda nayi mu hada ido duk da kuwa kokarin da yake kenan,naki bashi dama dan a kunyace nike kuma a takure nike dan tunda nike a rayuwata ban taba zama akan namijin da ba maharramina ba sai yau ba d'a namijin da ya tab'a yi man kiss a rayuwata sai shi.

Hannu yasa ya d'ago kaina yana hura ma idanuna da lumshe iska,kifkif na fara yi da idanun saboda iskan da yake hura man a sama turo baki nayi ina son sauka.

Murmushi yayi yana daura bakinshi saman nawan bakin yace.

"Zaki bude idon nan ko sai na sanye bakin tsiwar."?

Da sauri na bude idon ina mai marairaice mashi fuska na koma kallar tausayi,jan hancina yayi yana cewa.

"I love you Babe."

Wata irin zabura nayi sosai wuntsulawa nayi kasa Ina neman hanyar da zata sadani cikin gida, murmushi yayi mai sauti yana cewa.

"Ke tawa ce ni d'aya Jidda take care and sweet dreams."

Nidai har hardewa nike a wajen tafiya tsabar sauri,zuciyata sai bugun tara tara take ikon Allah ne kawai ya shigo dani parlo,kallon na tadda Yaya Bash d Yaya Muhd suna yi su kadai ne a cikin parlorn kenan har su Mama sun shiga dakunansu sun kwanta.

Da kallo kawai suka bini basu ce komai ba,ban yarda na had'a Ido dasu ba dan hawayene kawai naji suna zubo man a saman fuska,Koda na shiga room dinmu zauna na tadda Meenat tana operation din laptop dinta tana kuma waya,alamu sun nuna koya mata wani abu ake hakan ya bani dama Ina shiga na shige toilet na kullo.

Famfo na kunna ina mai rushewa da wani irin kuka,sosai nike kuka nama rasa kukan mai naki idan za'a tsiyani ace kukan mai nice to sai dai ayi man duk abunda za'ayi man dan har ga Allah bansan mai nike ma kuka ba.

Ban daina kuka ba sai da naji Meenat nayi nocking din kofar toilet tana cewa.

"Yaya Kulu are you okay?kina lafiya kuwa."!?gyaran murya nayi mata sannan na hau wanke fuskata,goge fuskar nayi bayan na wanka Ina kallon mirror cikin toilet din,idanuwa har sun kunbura tsabar kuka nasan mudun Meenat taga yanda idanuna sukayi sai ta tambayeni abunda ya sani kuka,kuma ni bansan abunda zan ce mata ba nidai kawai naji Ina kuka amman bansan dalilin kukan ba,dan banji haushi da yace yana sona ba kamar yanda nike ji idan Yaya Auwal yace yana sona ko wani,banji ko wani irin symbol ba a zuciyata ko na tsanarshi or something like that.

Ruwa na watsa na kara wanke fuskar sosai sannan na fito,tsaye na tadda Meenat bakin toilet ta bugu abun tagumi,Ina fitowa ta kamoni cikin damuwa take cewa.

"Subuhanllh!Yaya Jidda dan Allah mai akayi maki kike kuka?kodai Yaya Auwal dine bai yarda da tayin auren Yaya Wasi da zakiyi mashi."

Kamar jira Kara rushewa nayi kuka Ina daura kaina samanta,lailashi na ta dunga yi tana bani hakuri mun fi minti goma a haka sannan nayi shuru dan kaina ina mai share hawayena na kalleta sai kuma nayi murmushi Ina cewa.

"A'a Meenat ya yarda da auren nata kuma naji dadin haka sosai finally kawata ta samu miji na gari mutumin kirki in shaa Allah."

Itama murmushin tayi tana cewa.."In shaa Allah." Nufar wardrobe dina tayi ta fiddo man kayan bacci tana kallona tace.."Amman mai ya saki kuka har haka Yaya Kulu."?

Ansar kayan nayi Ina sawa na dan fesa turare na kama hannunta muka zauna bakin gado, murmushi nayi Ina jan hancinta nace.

"Yaya Haidar ne."

Tashi tayi tana kallona sai kuma tace.."Yaya Haidar kuma?keko Yaya Mai ya hadaki da Yaya Haidar da har zai saki kuka."? Hawaye kawai na share ban ce mata komai ba,dan bansan mai zance mata ba,mai kuwa zai hadani da shi mutumin da ko dariya bayi yake ba,idan har kaga dariyar shi to da Yaya Muhd suke magana anan ne zaiyi dariya har ta kusa kulle mashi ciki.

Ni tunda nike bansan yana ma murmushi ba sai da yazo bikin Yaya Teemarh naga yana yi, mutumin da rabon na ganshi anfi shekara shidda ma dan tunda ya tafi Cairo karatun likita ban sake saka shi a Ido ba sai wannan zuwan da yayi bikin Yaya Teemarh,Shima naji Baba yace ya gama karatun intership kawai ya rage yayi shima kamar dai Yaya.

Taya haka zata kasance duk manyan matan da ke cikin garin birnin kebbi da gusau amman ya rasa wa zai so sai ni? never ai nasan yaudarar kaina ne kawai zanyi ba son aure yake man ba,wata ila yana nufin kaf yan gidanmu yafi ji dani ba wai so na auri ba,yin wanann tunanin sai naji sauki sauki sai kuma na kalli Meenat da ta saki baki tana kallona murmushi nayi nace mata.

"Wai cewa yayi yana sona,but nasan wasa yake ai ni ba class dinshi bace,shi babban yarone dan maikudi shima da kudinshi Kinga kyaun shi sai dai yar'maikudi kamar shi amman ba ni ba."

"Yana sonki fa kika ce Yaya Jidda."?

D'aga mata kai nayi Ina tabe baki nace.."wai ba." Murmushi tayi tana cewa."kenan wai ne Yaya Jidda." Tabe baki nayi Ina gyara gadon baccinmu nace.."kwarai kuwa wai ne." Ajiye wayar hannunta tayi tana cewa.."But maiyasa kika ce wai ne?ko shima baki sonshi kamar yanda baki son Yaya Auwal."?

Kallonta nayi sai kuma nayi murmushi nace.."Taya za'i nace banson shi."?Dan shuru nayi sai kuma na cigaba da cewa.."ni bansan matsayinshi a zuciyata ba,just yace I love you abunda yace kenan Kinga kenan ba yana nufin I love you zan aureki Hauwa'u Abdullah jibir,just abunda na fahimta a wajenshi yana nufin kawai yana yina mean maybe yafi ji dani akan ku ko."?

Dariya kawai tayi tana kallona sai kuma ta Kara barkewa da dariya tana dauko wayarta tace..."Allah yasa mu dace to Yaya Jidda." Kwanciyata kawai nayi bance mata komai ba,wayarta ta cigaba dayi da Umar inajin yanda suke ta shan soyayyarsu kamar zasu cinye juna tun ina jinta sama sama har bacci yayi gaba dani.

Bangaren Yaya Haidar tunda na gudu na barshi yake murmushi yana shafa bakinshi da yayi kissing dina dashi, lumshe idonshi yayi yana mai k'ara bude kofofin hancinshi yana zuko kamshi na da na bar mashi,shafa chest din shi sai kuma ya girgiza kai yana cewa.

"I love you Jiddah,Ina kaunarki with all my heart Babe."

Shi d'aya yake ta surutunshi sai da ya duba time yaga har goma ya wuce sannan ya tashi ya shigo parlo ,kallon Yaya Muhd yayi sai kawai yayi murmushi yace.." Oga baka kwanta ba har yanzun."? Harararshi Yaya yayi yana cewa.."Oga na kwanta har na tashi ai." Dariya yayi yana ida shigowa yana cewa.."kodai wayar ake da Madam."? Dariya shima Yaya Muhd yayi yana cewa.."kamar yanda kaima ka gama da taka madam din ba."

Murmushi yayi yana yin kasa da kanshi sai kuma ya kalli Yaya yana cewa.."Sorry Yaya." Wata dariya Yaya ta barke da ita yana cewa.."kenan har na zama Yaya."? d'aga mashi kai yayi yana cewa.."ba dole na ba." Zama yayi yana cewa.."yau na fara fallasa sirrin da ke raina." Koma yayi serious yana kallon Yaya ya cigaba da cewa.."sai dai ina tsoro karda aki ansar kokan barar tawa,duk da na danga alamun nasara."

Dafashi Yaya yayi yana cewa..."kwantar da hankalinka Oga,kadai kawai ka iya takonka kasan hanyar da zaka bi cikin sauki ka mallake zuciyar mace haba mana be a men."

Langwabar da kanshi yayi yana zukar black tea yace..."in shaa Allah Hauwa tawa ce ni d'aya mallakina ce."

"Allah yasa."

"Amin Amin."

Tashi yayi yana cewa.."12 ta kusa bari naje na kwanta bacci nike ji." Dariya Yaya yayi yana cewa.."Kai saurin bacci ita saurin bacci idan kuka yi aure ba'a san wa zai chanza wani ba."

Shima dariyar yayi yana cewa.."ni zan chanza ta ta koma yin bacci 12 nasan yanzun tayi nisa a bacci."

"Kwarai kuwa ai matan gidan nan akwai su da saurin bacci kamar kasaye." Sai a lokacin Yaya Bash yayi magana yana cewa.."bama kamar Jidda,dakyal a kasamu ta koma yin bacci karfe tara fa,da takwai nayi tayi bacci dakyal take sallah,amman yanzun ai an samu cigaba tana kaiwa goma wani lokacin."

Murmushi kawai Yaya Haidar yayi yana cewa.."soon zata koma bacci 12 or 1 ma dan dolenta muyi firar soyayya kafin mu kwanta." Harararshi Yaya yayi yana cewa.."ko kunyarmu babu." Dariya yayi yana cewa.."kunya uhm!kaifa Bestyna idan naji kunyarka da wa zanyi labarin sarauniyar zuciyata."? Girgiza kai Yaya Muhd yayi yana cewa .."aikuwa zan hana mutun kanwata." Dariya kawai yayi ya tafi room dinsu dan kuwa da gaske bacci yake ji sosai.

Washe gari

Sai wajen karfi Sha biyun rana na fito parlo a shirye na fito sanye da hijab dinta iyakar gwiwa ta tsaya Koda na fito ban kalli inda yake ba na dai gaidasu a jimlace nace wajen Mama na duka Ina cewa.

"Ina wuni Mama."

"Lafiya lau Kulu,sai yanzun ake ganinki yau kuma."?

Dariya nayi Ina cewa.."wallahi ko Mama da yake nayi wani abu a dakin shiyasa." Dan shuru nayi sai kuma nayi gyaran murya Ina cewa..."Daman gidan su Wasi nike son zuwa zanyi maganar nan da ita."

"Shi Auwal din ya yarda da auren Wasilar ko."? D'aga mata kai nayi Ina cewa.."wallahi ko Mama ya yarda ai shi ya sanya nike son naje nayi maganar da ita."

"Shikenan Jidda,Allah ya kiyaye hanya ki dai kula sosai."

Tashi nayi Ina cewa.."Yauwa Mama sai na dawo." Na nufi kofa tana cewa a dawo lafiya har na Kai bakin kofa naji Yaya Haidar yana cewa.."Take care Jidda." Turo baki nayi gaba Ina mai tafiya ta murmushi kawai yayi ya cigaba da danna wayarshi,Koda na fita ban tsaya bata lokaci ba na fada gidan su Wasi,Mami ce zaune tsakar gida tana karatun alquri'ani har kasa na duka na gaida ta sannan na ida shiga cikin parlorn.

Zaune na tadda ta tana gyaran kumba bayan na zauna na dan harareta Ina cewa.."shine jiya kika tafi babu ko sallama Wasi har kika ja na buga Meenat akan na tambayeta kina ina tayi man shuru."

Ida gyaran kumbar tayi ta gyara wajen ta dawo tana cewa.." wallahi naso nace maki na tafi sai naga har lokacin Yaya Haidar bai bar kitchen din ba ni kuma bansan na katse maku firar da kuke shiyasa kawai na wuto daman Kinga mangariba ta wuce har sai da Mami tayi man fad'a nayi dare fa."

Turo baki kawai nayi Ina cewa.."Dan saboda da wani Yaya Haidar zaka tafi babu sallama nidai banji dadi ba karda ki sake yi man haka idan ba haka ba wallahi sai nayi maki kuka."

Dariya tayi tana lakutar kumatuna tace.."to Kulun Mama ayi hakuri ba zan sake na shikenan ko."? D'aga mata kai nayi ina gyara zamana na kalleta sosai Ina cewa.

"Jiya Yaya Auwal yazo din kuma munyi magana dashi sosai."

"Okay mai kuka ce."?

Duk yanda mukayi dashi sai da na gayaman tas, rungume juna mukayi sai muka rushe da kuka a tare sai da mukayi mai isarmu sannan muka ba juna hakuri,kallona kawai take tana jinjina irin kaunar da nike mata kamar yanda nima a Koda yaushe nike jinjina kaunar da take man,bayan mun gama tautaunawa akan Yaya Auwal na kiranshi waya suka gaisa na tura mashi number dinta itama na bata number shi.

Ban bar gidan ba sai da nayi sallar la'asar sannan na tashi nace ni zan tafi gida,saboda yau gidan namu cike da yake mutane yan zuwa biki dan har Amarya sun iso daga birnin kebbi amman a gidansu na nan Gusau suka sauka shiyasa bata shigo ba,a hankali nike tafiya har na iso cikin compound din gida ban lura dashi ba sai dai kawai nayi an kamoni anyi wajen motoci dani sosai na tsorata na bude baki zan kurma ihu yayi saurin had'a bakinmu waje d'aya ya fara tsotsa kamar ya samu sweet ,rudewa nayi ina fis fisgewa Kara rungumoni yayi yana tura hannunshi a cikin.

Tura hannunshi yayi cikin hijab dina yana shafar wuyana fikefike na kama yi da ido,zuciyata ba abunda take sai bugawa fat fat zabar tsoro,so nike na ciro bakina a cikin nashi yaki bani damar hakan...hawaye naji suna zubowa a saman fuskata tsotsar man baki yake kamar wanda ya samu chocolate ga zafi da lip dina suka fara yi man.. bansan lokacin da nayi hugging din shi ba Ina manna kirjina a saman kirjinshi Ina sauke wani numfashi mai karfe.

K'ara gyaraman kwanciya yayi a jikinshi yana zare bakinshi daga cikin nawa,kafeni yayi da ido yana sauke ajiyar zuciya sai kace wanda yayi gudun ceton rai, shuru kawai yayi yana maida numfashi yana shafa bayana a hankali a hankali.

D'agoni yayi yana sakar man kiss a saman baki yace.."Oya Babe shiga moto muje kiji wata magana." Turo baki nayi Ina kallon motar naki shiga,ganin banda niyar shiga ya kama hannuna ya zagaya dani seat din mai zaman banza ya bude ya sani da kanshi ,yana manna man bakinshi saman goshina yace

"I love you."

Kullewa yayi ya zagaya drive seat ya shiga ya kulle yayi bissimllah yayi ma mota key ya bude gate ya fita da motar ya kulle gate din ya dawo muka dauki hanya..inda yake ban kalla ba dan haushin shi nike ji ace mutun sai jarabar tsiya bai da aiki sai tabe tabe da tsotse tsotse kamar dai mayunwaci.

Kamo hannuna yayi ya had'a da nashi ya cigaba da driving din hankalinshi kwance kamar yanda banyi mashi magana ba kuma ban kalle shi ba ,Shima haka baiyi man magana ba amman yana dan kallona jefi jefi sai kuma ya saki murmushi haka ya kamayi har muka iso wani babban park a cikin Gusau dan ni ban ma san da zamanshi ba nida nike zaune a cikin gusau din,samu waje yayi inda aka tanadar dan ajiye motoci yayi parking yana kashe motar.

Waigowa yayi yana kallona sai kuma yayi ma hannun nawa kissing yana dan lasarshi kadan a hankali bansan sanda na lumshe idona ba ana budewa a kanshi, murmushi yayi yana cewa.

"Kin san mai Jidda."?

Nidai shuru kawai nayi bance mashi Komai ba,ya kusa minti uku yana jiran yaji feedback dina amman shuru, girgiza kai yayi ya kwantar da seat din da nike zaune yana cewa.

"Okay baki gaji ba kenan,to bari nasha wanna twins din daman sunfi tsokaleman ido,dan cuta idan kina tafiya kika gama turo man su kina man kwalele." Sauri nayi zan tashi ya maidani yana cire hijab din ya ajiye gefe yana kokarin zuge zip din rigata na fashe mashi da kuka Ina cewa.

"Wallahi Yaya Haidar kaji tsoro,Allah dai yana kallonka kuma ka tuna duk abunda kayi ma wani sai anyi ma naka." Murmushi yayi yana kissing din bakina yace.."okay bari nasha mana Kinga sai ayi ma nawa da hujja ko."

Girgiza kai na nike ina cewa.."Dan Allah kayi hakuri karda kayi man haka,ka tuna nifa kanwarka ce kake neman yi ma fyade."

Daura bakinshi yayi saman kunnena yana tsotsa dan cizawa yayi kadan yana cewa.."Jidda komai kika Ina maki sonki ne sila,Ina sonki sosai kuma inason jikinki sosai komai naki sonshi nike Jidda,ba zan tab'a yi maki fyade ni ba mazinaci bane asali ma ban taba tab'a macen da ba maharamata ba sai ke kema din sonki ne sila."

Dan shuru yayi sai kuma ya cigaba da cewa.."inasonki inasonki sosai Jidda Ina son muyi rayuwa a inuwar aure har *DA'IMAN ABADAN*,ke nike son ki zamo uwar 'yayana' banda gurin da ya wuce wannan Jidda ki barni nasha nidai na sama raina ne pls Luv."

Yanda ya ida maganar a cikin kunne na na sauke man numfashi a hankali a ciki,bansan lokacin da na makwalkwaleshi Ina hawaye ina girgiza kai,shima girgiza man kai yayi yana cewa.

"Please ki barni nasha sau tak zance ba zan sake shansu ba sai na bada sadaki believe me Sweety."

Nidai ban sake ce mashi komai ba sai ma hawaye da nike ta zubarwa, murmushi yayi yana share hawayen yana sauka kaina ya d'agoni yana goge man fuskata yana cewa.

"Na fasa sha,amman ki sani bayan bakin Teemarh za'a sa bakinmu dan ba haka ba da matsala gaskiya Jidda,dan a matse nike hakurina yazo karshe gaskiya."

Kara goge fuskata nayi Ina kokarin maida hijabi na da ya cire man,ansar hijab din yayi yana saman da kanshi sanann ya bude kofa ya fita,ya fiddo ni ya kulle motar yana kama hannuna muka shiga cikin entery din.

Samun waje mukayi muka zauna yayi mana order shawarma da meatpie sai kuma kuma five alive na roba,bayan ya ankawo mana da kanshi ya dunga bani a baki tun Ina nokewa har da na saki jikina naci shawarma din yanda ya kamata sai da ya gama bani sanann shima na ya matsa man sai da na fara feeding dinshi sai wani shagwabe yake man yana man tabara ko mutane da ke bai nuna yasan da zamansu ba,duk da wasu suna kallonmu.

Ina cikin bashi na dan b'ata mashi baki da bama,waigawa nayi zan dauko tissue dan goge mashi inda bama din ya tab'a mukayi Ido biyu da Ahmad da yake zauna kamar an dassashi yana man wani irin kallon,sai da gabana ya fada da naga Ahmad dan har na manta da shi a rayuwata,kauda kaina nayi ina mai daukar tissue din na goge mashi wajen sanann na cigaba da bashi meatpie din.

Sai da ya koshi ya rike hannuna yana shafa cikinshi yace.."Oya Babe fasa man ciki zakiyi ko."?

Murmushi nayi Ina mai kauda kaina gefe kama hannuna yayi yana mikewa tsaye dani yace.." Oya Babe tashi muje mu karasa maganar aurenmu dan nidai gaskiya aure nike so,idan kuma kika ki zaki Sha matse ne a wajena ko wace rana dan ba zan yarda Ina da ke na tsaya sha'awa ta kashe ni."

Nidai rasa ta cewa nayi dan wata irin kunya ta kamani,shi ko a jikinshi tafiya muke a hankali sai wani shagwabe yake man wai shidai na daukeshi na Kai shi a motar kafafunshi sun gaji da tafiya,nidai ba abunda nike sai murmushi yana boye fuskata a hannu,waigawa nayi naga Ahmad Shima ya taso yana biye damu a bayanmu.

Maida kaina kawai nayi a wajen Yaya Ina cewa.

"Yaya."

Waigowa yayi yana kama hancina yace.

"What wrong Babe."

Turo baki nayi Ina cewa.

"Nidai muyi sauri mubar wajen nan baiyi man ba."

Murmushi yayi yana daukata kamar wata Babe, bansan sanda na zagayo da hannuna a wuyashi ba Ina boye fuskata a saman kirjinshi,har bakin mota ya saukeni yana budewa ya saka budewa ya sakani ya zagaya drive seat ya yi ma motar key muka tafi.

Tunda ya daukeni ban sake yarda na kalleshi ba, murmushi yayi bayan ya parka motar a wani wajen shakatawa yace..

"Bake kika ce muyi sauri ba."

Cinno baki nayi Ina cewa.

"Ai bance kuma ka daukeni ba ko."

Jan hancina yayi yana cewa.

"Babe ai kece daman baki yin sauri da na daukeki ba gashi har munzo nan ba."

Murmushi kawai nayi ina yin shuru nidai,dariya shima yayi yana cewa.

"Babe kinsan mai."?

D'aga mashi kai nayi kawai nayi, cigaba da cewa yayi.

"Inasonki kefa kina sona."?

Shuru sai kuma na maida kaina gefe ina murmushi, maida da kaina yayi direction din da yake ya kafe idonshi cikin nawa ya sake cewa.

"Babe Ina sonki

Please Login or Register in order to submit comment