Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miji mai natsuwa da hankali wanda idan har baifi Auwal ba to sai dai suzo d'aya."

Dan shuru tayi sai kuma tace.."shikenan Allah shi zab'a abunda yafi alkhari,a dawo lafiya." Murmushi kawai yayi yana ficewarshi,zaune ya tadda shi a compound bisa rubber chair ya kurama waje d'aya ido.kallo daya zakayi mashi ka gane ba a cikin hankalinshi yake ba,hankalin ya tafi can wani wajen daban girgiza shi Yaya Muhd yayi yana cewa.."C'mon maiye kake haka kuma."?

Tashi yayi yana kallon Yaya Muhd,sai kuma ya langwabar da Kai yana cewa.."shikenan na rasa Hauwa kenan?wani ya rigani garin ya haka ta kasance Broth." Murmushi kawai Yaya Muhd yayi yana cewa.."kaji matsalarka saurin sarewa wallahi,muje ka rakani na maida mashi turarenshi,karka damu da wannan case din na Auwal dan ita Kulu ba sonshi take ba,ni nasa ma ta sallamaishi dan tun Ina level four yace yana sonta,ta kirani ta gaya man ita bata sonshi nace ta gaya mashi kawai a wuce wajen,amman ta kasa wai kunyarshi take ji"

Furzar da iska kawai yayi yana cewa.."Broth ba zaka gane yanda nike ba shiyasa,inason Kulu sosai ina kishin Kulu sosai bansan naji ko kallonta wani d'a namiji yayi Koda kuwa gaisawa ce zasuyi bani bukata wallahi,nidai ya dace ayi magana karda na tsaya kallon ruwa azo ayi ba dani ba,zan iya mutuwa gaskia inasonta inason na rayu da ita *DA'IMAN ABADAN*,Ina son ta zamo uwar 'yayana' Broth."

Tsaki kawai Yaya yayi yana cewa.."shin zaka zo mu tafi ko tsayawa zakayi ka kama gayaman abunda na haddace idan da sabo na saba da wanna surutun naka na son Jidda da kake,na haddace wallahi tunda ka dawo kasar ba sai ka gaya mata kana sonta ba tunda gaka ga ta"

Dan shafa kanshi yayi yana murmushi baice komai ba ya shiga drive seat key din Yaya ya bashi suka nufi office din Yaya Auwal dan maida mashi turarenshi .

"Nifa gaskiya sai naga kamar Jidda zata ce bata sona idan na gaya mata Ina sonta dan na lura ta man wani gani gani tayi man fassara ta daban Broth."

"Ba zatace bata sonka ba,amman tana maka kallon mai girman kai,da jiji da Kai harda miskilancin ma dai cewa take kana dasu." Murmushi yayi yana lumshe idonshi ya shafa kwantaicen sayen da ya kewaye fuskarshi ya k'ara fiddo mashi da zallar kyaunshi ma bahaushe na asali ma,bai dai ce komai na har suka iso wajen aikin Yaya Auwal,wajen da aka tanadar dan ajiye motoci yayi parking yana kallon Yaya Muhd yace.

"Idan ka shiga karda ka dade pls." Hararar wasa Yaya yayi mashi yana cewa."bangane karda na dad'e ba?kana nufin ba zaka shiga ku gaisa da Auwal ba? Auwal Ishaq fa ne ba wani ba."

"I know Auwal Ishaq ne,just kawai Ina jin haushinshi a yanzun shiyasa ba zan shiga ba that why."

Kallonshi kawai Yaya yayi yana cewa.."shikenan Broth yanda kace,amman ka sani ba zaiji dadi ba idan ya fito ya ganka dai ko."?shuru kawai yayi baice komai ba.shima Yaya Muhd baice komai ya shiga cikin ma'aikatar,ya dan jima a zauna a cikin motar sai da yaji zuciyarshi ta danyi sanyi kadan sannan ya fito,dan yasan waye Auwal Ishaq a wajen close friend din shi bai kama ace mace ta hadasu ba,duk da yanajin kishi akan turaren da ya kawo mata amman zai daure yaje su gaisa just ai gaisawa ce ba wani ba,da wanann tunanin ya fito Shima ya shiga cikin ma'aikatar ya doshi office din Auwal.

Nocking yayi yana tura door din ya shiga da sallama a bakinshi tashi Auwal yayi yana hunging din shi sai murmushi yake yace.

"Aliyu Sulaiman Jibir."

Dariya yayi yana mika mashi hannu yace.."My friend nayi missing dinka sosai,shikenan kawai ka boye ba'a ganinka sai dai aga posting dinka anya kuwa akwai amana Haidar ka yada zuminci kamar ba tare mukayi wasan kasa ba."

Murmushi kawai yaya Haidar yayi yana cewa.."Sorry Friend kana raina wallahi,ba zan iya mancewa dakai ba Koda Ina mantawa da kowa Auwal Ishaq believe me."

Wajen zama ya kaishi sai dadi yake ji ganin Haidar da yayi dan ya kusan shekara sama da goma rabon da ya saka shi a Ido tun suna a gusau kafin su koma Birnin kebbi d zama kuma baida number dinshi sai dai yaga posting din shi a IG,ruwa ya kawo masu da lemuka sai kuma ya kawo masu tea mai zafi sai sannu yake masu ya rasa a inda zai ajiye su.

Sun sha ruwan da tea sannan suka kara gaisawa, daurewa Yaya Muhd yayi ya fara gaya mashi abunda ya kawo su sai da ya gama gaya mashi,shuru Yaya Muhd yayi yana kallon Auwal sai kuma can ya furzar da iskan bakinshi yana yin kasa da murya cike da kunyarshi ya fara cewa.

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*EDITING NO❌*

*71-80*


"Auwal Ishaq." D'agowa kawai Yaya Auwal yayi yana kallon shi bai ce komai ba,amman kacokam ya maida hankalinshi wajenshi yasan magana ce zaiyi mashi mai mahinmamci tun da har ya kira full name dinshi to tabbas yasan magana ce zai mashi ba ta wasa ba,yana fatan yaji alkhari dan jikinshi har yayi sanyi ganin yanda Yaya yayi kasa da kanshi yak'i yarda su had'a Ido sam.

Katse shurun Yaya yayi da cewa.."Daman zuwa nayi da wata alfarma wajenka,duk da nasan ba'ayi maka adalci ba,sai dai inason ka sani komai ya faru daga Allah ne."

Shuru yayi yana maida ajiyar zuciya,ruwa Yaya Auwal ya dauka yasha yana goge zufar goshin shi,dan haka nan yaji maganar da Yaya zai gaya mashi ba dadinta zaiji ba dan gabanshi sai faduwa yake dam.sai kace wanda yayi gudun ceton rai murmushi ya kirk'ira yana cewa.

"Hakane kam Muhammad maganarka gaskiya ce komai nufi na Allah ne ba bawan da ya isa ya tsallake qaddararshi fatanmu Allah ya bamu ikon yarda da qaddararmu."

"Amin."

Tare suka ce Amin, duk su duka jikinsu yayi sanyi ba kamar Yaya Haidar da yake jin da ya san Muhammad zaiyi ma Auwal wanann maganar to da ba abunda zai shigo dashi office din Auwal da wani ido zai kalle Auwal,so yake ya tashi ya bar masu office din amman baisan wani excuse zai dauka ba,dubara ce ta fado mashi ya tashi yana cewa.

"Am Auwal ba toilet ne a office din nan."? Dan murmushi yayi yana cewa."eh akwai sai dai tap din kamar ya dan tsaya jiya kuma ba'a shigo an gyara ba har yanzun."

Nufar kofa yayi yana cema Yaya.."No problem bari na dan je na dauko ruwa a mota." Daga haka ya fita yana daukar wayarshi, murmushi Yaya kawai yayi yana maida hankalinshi wajen Yaya Auwal yace.

"Auwal nasan kasan matsayinka a wajena wallahi har gobe haka kake,kai ba iya abokina bane ka zama dan'uwa,ka gafarceni akan maganar da zan maka kuma inason ka fahimceni Ina fatan hakan."

Cigaba da cewa yayi.."Daman maganar ba ta kowa bace face Jiddarh,nazo ne muyi maganar Jidda dakai,maganar gaskiya Auwal anyi ma Jidda Miji tunin dadewa a birnin kebbi,sai yau naga turarukan da ka kawo mata nike tambayarta har yanzun kuna tare tace man eh,nace tana da interest akan aurenka ta nuna man A'a ni kuma ba zan zuba Ido ba nasan ba aurenka zatayi ta kama b'ata maka lokaci shiyasa nace zan gaya maka Ina fatan ka fahimceni dan Allah."

Kasa Yaya Auwal yayi da kanshi baice komai ba sai inalillahi wa'innalaihirajiun da yake ta maimaitawa sai yayi ya kusa sau biyar sai ya d'ago yana kallon Yaya idanunshi jajir harta jijiyoyin fuskarshi sun tashi tsabar shiga tashin hankali,AC ce kunne a office din tana buso masu sanyi,amman shi take yaji ya jike sarab da zufa ta ko Ina zufa keto mashi take,hawaye ne yaji suna zubowa a saman kyawkyawar fuskarshi,ya kasa tsadasu haka ya sake kallon Yaya yana cewa.

"Wallahi Muhd na fahimceka kuma na yarda da kaddarata daman banda rabon da rayu da Jiddah *DA'IMAN ABADAN*,haka Allah yaso kuma wallahi naji dadi ka gayaman matsayina a wajen Jiddarh duk da tuni naso na gano hakan,kuma wallahi na bar mata wanann turarukan da kazo dasu inace ko babu soyayya ni mai kawo ma turaruka ne saboda kanwarka kanwatace,kuma wallahi matsayinka yana nan yanda yake Muhd har abada Muna tare akan rashin samun Jidda ba zai taba shafar zumincinmu ba har *ABADAN*."

Rasa abun cewa Yaya yayi sai dai kallon Yaya Auwal da yake yana famar goge hawaye,tabbas yasan irin son da yake man amman mai ba yanda za'ayi gida bai koshi ba akai ma na waje,dama ace Ina sonshi da sauki to ban sonshi ya za'ayi a daura man aure da wanda zuciya ta bata so,sam hakan bai dace ba sauke ajiyar zuciya yayi yana dafa Yaya Auwal yace.

"Abokina na zan hanaka zubda hawayen nan ba,nasan rad'adin da kake ji na rabuwa da masoyi sai dai mai in shaa Allah sai Allah ya hadaka da wanda tafi Jiddarh kuma kamar yanda kace daman Allah yayi ba matarka bace,to in shaa Allah sai hakurinka ya zamai maka riba In shaa Allah sai kaci ribar hakuri Auwal Ina maka wanann fatan."

Murmushi Yaya Auwal yayi yana cewa.."to tunda kace Allah ka gama magana,kuma ka tayani da addu'a Allah ya cire man sonta a zuciyata dan son Jiddarh ba karamin kamu yayi man ba,Ina fatan Allah ya cire man sonta kodan gudan fatawa a halaka kana son matar wani kasan hakan ba daidai bane."

"In shaa Allah sai sonta ya fita daga zuciyarka karka damu ka cigaba da addu'a kawai,zan tafi Haidar na
cikin mota yana jira na."
Tashi yayi yana cewa.."ok bari na rakaka,amman yau inason nazo gida wajen Jiddarh zanyi wata magana da ita."

"Ok ba damuwa Allah ya kaimu anjimar,da kayi zamanka ba sai ka tashi ba,na barka lafiya sai ka shigo." Komawa yayi kawai ya zauna yana ma Yaya murmushi shi kadai yasan yanda yake ji a cikin zuciyarshi,shi kadai yasan irin son da yake ma Jidda amman na yanda zaiyi matar mutum.

Koda Yaya ya fito tadda shi yayi ya jingina da mota yana danna waya,Hy yayi mashi yana cewa.."Boss bude mana mota mu tafi." Harararshi kawai yayi yana unlock din motar suka shiga suka kama gabansu,ba wanda yayi wani magana a cikinsu har suka iso gida.

Suna shigowa Yaya ya kwala man kira Ina zuwa ya bani turaruka na yana cewa.."gasu nan yace ba zai ansa ba dan Allah ya baki sai ai ta fasawa." Girgiza kai nayi Ina cewa.

"Nidai Yaya A'a ba zan ansa ba ka tafi dashi room dinka ko kuma ka raba ma su Yaya Bash,ni Ina da turaruka ma." Na ida maganar inayin kasa da Kai ban yarda na kara gigin kallon Yaya Haidar ba,duba da wani kallon banza da dunga aika man da Yaya yace na anshi turare,kallona Yaya yayi yana cewa.."ki dauki ko biyu Kulu." Nidai shuru kawai nayi bance komai ba,da kanshi ya dauki guda ukku yace.."anshi wannan Kun Kara cikin naku and yace yau da anjima zai shigo zakuyi magana kisan mai zaki ce mashi dan na gaya mashi ba zaki samu damar aurenshi ba, dan haka daga yau ki dunga yi mashi kallon Yayanki ba masoyi ba hope kin gane."

Duk da ba son Yaya Auwal nike ba ,amman bansan sanda na d'aga kaina ba Ina kallon Yaya Muhd da yace ya gayama Auwal wai ba zan aureshi ba take naji zuciya ta ta karaya,ba abunda ya fado man a rai sai a wani hali bawan Allahn zai shiga akan sona,Allah ne sheda yana man son da yake bani tsoro , Yaya Auwal mutumin ne baicancanci haka daga gareni ba,amman Allah yasa haka yafi alkhari hawaye naji suna neman kubce man ansar turaren kawai nayi na juya da gudu Ina share hawayen da suke tarara a fuska ta.

Ina shiga room dinmu ajiye ma Meenat tururen nayi a saman cinyarta Ina hayewa saman gado na rushe da wani irin kuka tashi sukayi sukayo kaina suna tambayar lafiya.

Bance masu komai ba kukana kawai nike dan wani tausayin Yaya Auwal naji ya kamani bansan a wani hali zai shiga ba,nasan na cuci Yaya Auwal dan tun farko ban dakatar dashi ba, laifina ne da ban fitar dashi daga rayuwata ba.

Yana man son da shi kanshi baisan adadinshi ba,matsalarshi daya tak kallo daga baya kuma na gane kallon so da kauna ne yake man mai zan mashi na saka mashi da alkhari?mai zan mashi da zai wanke mashi tabon da na bar mashi a zuciya,sosai nike kuka kamar wanda aka gaya ma sokon uwarta ta mutu.

Wasi ce ta haye gadon tana girgiza ni tace.

"Hauwa."

Shuru nayi bance komai ba sai sauke ajiyar zuciya kawai nike,sai kuma hawaye da suka ki daina zuba a saman fuskata...cikin damuwa ta cigaba da jinjigani tana cewa.

"Hauwa,dan Allah maike faruwa kina tada mana hankali dan Allah ki gaya mana kukan mai kike."

Tashi nayi zaune Ina kallonta kama hannuwanta nayi Ina cewa.

"Wasi."

Kallona tayi tana cewa.

"Naam Hauwa gaya man maike damunki har ya saka ki kuka."

Murmushi nayi Ina mai kallonta sai kuma na Kara sakin wani murmushin a karo na biyu,sai da na Kara sauke ajiyar zuciya sau kusan biyar sannan na kalleta nace.

"Wata alfarma nike nema wajenki sau tak a duniya Wasi."

"Alfarma kuma Hauwa?wace irin alfarma ce wannan!?gaya man ita Allah ya bani ikon yi maki."

Da bayan hannuna na share hawayena Ina cewa.."tabbas kina da ikon yi man Wasi,sai dai indan bakiyi niya ba amman inason ki sani tunda nike dake ban tab'a tambayarki kiyi man wata alfarma ba sai yau,Ina fatan kuma kiyi man ita dan wannan ce ta farko kuma ta karshen alfarmar da zan tambayeki."

Kallona kawai take bata sake cewa komai ba,nima bani bukatar naji abunda zata ce shiyasa cigaba da cewa.

"Wasi inason kiyi man alfarma ki auri Yaya Auwal dan nasan ke kadai ce zaki kula da shi ki yaye mashi bakin cikin da na tusa mashi a zuciyarshi Wasi."

Shuru nayi sai kuma na rushe da kuka na cigaba da cewa.."Dan Allah kawata karda kice man A'a tabbas idan har kika ce man A'a kinyi man abunda har na mutu ba zan manta shi ba,kuma ki sani hankali na ba zai tab'a kwanciya ba mudun ban saka ma bawan Allah nan da hallaci ba,Wasi kinsan komai na sai na tsaya gaya maki ba,kinsan waye Yaya Auwal kinsan halinshi kamar yanda shima yasan naki halin na tabbata zaki kula dashi sosai zaki mantar dashi bakin cikin da yake cikin a yanzun."

Girgiza kai ta kamayi tana cewa

"Hauwa."

Dagowa nayi Ina kallonta Ina kukana,itama kukan ta fashe da shi tana cewa.

"Dan Allah Hauwa ki rufaman asiri karda ki jaman zagi a idon duniya,mai ya hadaku da Yaya Auwal din da har kike kokarin rabuwa dashi Hauwa ko har yanzun dai baki jin son nashi a zuciyarki."?

Rungumota nayi Ina kuka sosai nace.."Wasi ba mai zaginki ba mai maki kallon marar rike amana, sai ma jinjina maki da za'ayi na ceto rayuwar mutumin kirki Wasi,tabbas ban sonshi har yau har gobe sai dai Ina tsoron karda ya barni ga Allah akan yaudararshi da nayi."

D'agoni tayi tana share man hawayen fuskata tace.

"Kukan ya isa haka ,baki yaudareshi ba haka Allah ya kaddara babu rabon zaku rayu *DA'IMAN ABADAN* naji na kuma yarda zan auri Yaya Auwal sadaukarwa ga kawata rabin raina Hauwa, Allah ya bani ikon yi mashi biyaiya ke kuma Allah ya zab'a maki abunda yafi alkhari kukan ya isa haka."

Rungumota na karo yi Ina mata godiya sai da gama kukana sannan na gaya masu duk yanda akayi , addu'a sukayi mana Allah yasa haka shine alkhari....bayan mun gama maganarmu muka fito nida Wasi suka girki mashi abinci Muna cikin girkin Yaya Haidar ya shigo kitchen din kallona yayi yana cewa.

"Kin gama kukan."?

Kasa nidai nayi da kaina ban ce komai ba,furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa..."kinsan kina sonshi kika ce baki sonshi."? Sai anan na d'ago kaina kuma kallo d'aya nayi mashi na maida kaina kasa saboda kallon da yake jifata dashi ,dan karamin tsaki yayi yana cewa.

"Jiddarh."

D'ago kaina nayi Ina kallonshi sai can nace.

"Na'am."

Dan murmushi yayi ya kuma cewa again..."kinsan kina sonshi kika ce baki sonshi." Girgiza kai nayi Ina cewa.."ni har yanzun bani sonshi." Nan ma murmushin yayi yana cewa.

"To mai ya kawo kuka dan ance maki an rabaku."?goge hawayena nayi da bayan hannu ina sauke ajiyar zuciya ko kallonshi ban sake yi ba cigaba da yankan salad kawai nike nace mashi.."saboda ya bani tausayi sosai,dan son da yake man rabashi dani na tabbata zai shiga cikin wani hali kuma mutumin kirki ne."

Rasa abun ce man kawai yayi,amman yanayin shi kawai zaka kalla ka gane yaji maganar da nayi dan har idonshi sun nuna haka,saboda sun tashi daga farare sun koma jajaye,tsaki yaja mai tsawo yana fita daga kitchen din,abunda ya shigo dashi kitchen bai tsaya ya dauka ba tabe baki nayi Ina cewa.

"Can ta matse maka,kuma ta tsuke ka ba dai tsaki ba ko,naga dangin tsaka!mtss." Naja tsaki Ina bude tukunya naga ko shinkafar ta nuna na sauke ta ko na tafi nayi wanka dan zafi nike ji sosai, daman Wasi tun da ya shigo ya fara magana ta sulale ta bar kitchen din ta barni dashi,wani dogon tsakin na Kara ja Ina cewa.

"Ko Ina ruwanshi da rayuwata?Ina dalilin mutum yazo ya saka man Ido haka ma dazun da safe yai ta man bala'i kamar zai cizeni haka kawai mutum sai zafin zuciya da masifar tsiya matarka dai taga buni har ta ban tausayi dan zata ga mulkin mallaka a wajen ka kam."

Haka na kama fad'ana ni d'aya a kitchen har na ida kammala duk abunda muka fara shirya ma Yaya Auwal da Wasi kafin wannan mutumin yazo ya fidda ta, flakes na samu masu kyau na zuba abincin da jugs masu kyau na juye duk juices din da mukayi mashi na saka a freeze sanann na fito.

Zaune na taddasu a parlo shi da Yaya Muhd suna magana kasa kasa kamar wasu sabin munafikai,harararsu nayi a fakaice Ina cewa.

"A dai chanza sana'a gaskiya kam...dan gulma dai babu kyau da yi da wasu."

A kasa kasa nayi maganar Ina ida shigewa room din,wanka kawai na fada Ina fitowa na shafa cream dina sannan na zura katuwar hijab na kaffabara sallah Ina gama wa na samo wata atamfa ta silver ash mai gold na saka dinkin doguwar riga ce a shape,dinki yayi kyau dan ba karamin kyau dinkin yake man ba,ban shafa ma fuskata komai ba kawai dai na shafa ma bakina cheapest da daura dan kwali.

Turare na fesa Ina kallon Meenat nace.

"Ina Wasi ta tafi kuma."?

Tashi tayi zaune tana murmushi tace man.."Masha Allah Yaya Kulu kinyi kyau sosai wallahi kamar wata amarya."sai kuma tayi fuskar tausayi tana cewa."Allah sarki Yaya Auwal har ya ban tausayi,amman Allah yasa hakan yafi alkhari,na dai so ace shi zai samu wanann kyawkyawar budurwar Yaya ta."

Harararta nayi Ina cewa.."matsalar dan Nigeria kenan,ga tambayar da akayi mashi ya kama zuba yana kamo inda ba a aika shi ba." Mtss naji tsaki dan yau a wuya nike sosai duk Yaya Haidar ya b'ata man rai,dan banga dalilin da zai dunga shigar man hanci a kudundune na ma kosa ranar daurin auren Yaya Teemarh yazo ko ya tafi ya bar mana gida, thank God saura kwana biyu ai bikin Ina dalili harararta nayi Ina cewa.

"Nace maki Ina Wasi zaki wani cikani da surutu mararsa kan gado,ki fita idona na kulle tun ban b'ata maki rai ba na dai gaya maki ba."

Rike baki Meenat tayi tana kallona, abunda ban taba yi mata ba dan ni gidanmu kowa ya sheda sai ayi man laifi sau dubu ban d'aga Kai na kalli mai laifin ba,amman daga magana na hauta da fad'a kamar zan cizeta tsabar jaraba sauke ajiyar zuciya kawai tayi ta sauka daga saman gado ta bar man dakin bata ce man komai ba.

Ida hawa nayi wato ga sabon kaimu ina mata magana ta fita ta barni tsaye wato ga mahaukaciya ko kuma karya naita haushi na ni d'aya,bansan sanda na fito parlon ba dan ko dan kwali ban tsaya sakama gashi na ba nayi parlo ko mutunen cikin parlon ban kallesu ba wajen Meenat kawai nayi direct sai haki nike.

Ina zuwa ban tsaya jira ba na wanka mata wani lafiyaiyen mari,zan daura mata wani naji an rike hannuna kallon Yaya Bash nayi Ina kallon hannuna da ya rike bansan lokacin da na fashe da kuka ba ina fisge hannuna nayi hanyar room dinmu,nan ma rikoni akayi Ina kallona.

Kuka nidai kawai nike ban ce komai ba,sauke ajiyar zuciya yayi yana zaunar dani bisa kushun yana cewa.

"Jiddarh."

Nidai tunda na daura kaina a saman cinyarshi ban dauko ba,cigaba kawai nayi da kuka dan wani irin zafi naji zuciyata tana man, wai ni Meenat zatayi man haka Ina mata magana zata barni tsaye kamar wata kawarta,daga wani bangaren na zuciya ta kuma zafin Marin da nayi mata nike ji dan tunda nike ban tab'a d'aga hannu na doki kannena ba,balle Meenat da take kawata tare muke kwana daki d'aya yarinyar ta damu dani sosai tana son farinciki na,amman yau nice na d'aga hannu na sharara mata mari.

Bai hanani kukan ba,bai kuma zare kaina daga saman cinyarshi ba sai ma hura man iska da ya kamayi yana man magana a hankali dai dai sitin kunnena yake cewa.

"Sorry Babe,stop it please kukan ya isa haka."

Abunda ya kama ceman Kenan yana gaya man kalamai masu dadi a cikin kunne bai damu da su Mama da ke cikin parlon ba suna kallonmu.damuwarshi d'aya ce kawai nayi shuru dan bai son ya gani a cikin sad ko kadan,a hankali yace.."fushi bai maki kyau Kulu,ke din kyawkyawace komai naki mai kyau ne amman banda fushi da kuka please I beg kibar kukan haka kiji Beb."

sai da nayi kukana mai isata sannan na d'ago kaina ina kallon yaya haidar da ke ta aikin lailashi na, murmushi yayi man yana saka yatsenshi na tsakiya yana share man hawayen da ke shatatowa a fuskata girgiza kanshi yayi yana cewa.

"kukan ya isa haka karda hawayen su kara zubowa su b'ata maki kwaliya gashi guest dinki ya kusa isowa."

turo baki nayi ina sauke ajiyar zuciya na kusa minti biyar a saman shi sannan na fara kokarin zare jikina daga cikin jikinshi bai hanani ba sai ma bani space da yayi na zauna kusa dashi ina mai k'ara goge fuskata.

itama meenat din kukan take,amman kasa kasa ba kamar nawa ba,kasa nayi da kaina kawai yaya muhd ne ya katse shurun yana cewa.

"kulu."

d'agowa nayi ina kallonshi matsowa yayi kusa dani ya kama hannuna silently ya fara maganar.

"kulu mai kanwarki tayi maki zaki mareta bayan ban taba ganin haka ya faru tsakaninku ba."?

ajiyar zuciya na sauke ina cewa.."yaya magana nike mata a cikin room nace ina wasi sai ta kama yi man maganar shirme daga nayi mata fad'a nace ga tambayar da nayi maki zaki kama yi man shirmen banza shine kawai ta tashi ta bar man room wato ga mahaukaciya nai ta yi ni d'aya."

murmushi yayi yana cewa."bata kyauta ba,amman ina kika kai hakurinki kulu?haba kanwata ina son da kike ma kanwar taki dan tayi maki laifi ba sai yi mata nasiha ba."

nidai shuru kawai nayi ina wasa da zoben hannuna, bai sake ce man komai ba ya tashi ya koma wajen meenat kasa tayi da kanta bata yarda suka hadda ido ba harararta yayi yana cewa..

"yaushe kika sake hali ban sani ba."?

a hankali tace."kayi hakuri yaya."

tsaki yayi yana cewa.."sorry for yourself." dan shuru yayi sannan ya cigaba da cewa.."daga yau karda ki sake yi ma yayarki haka hope kin gane?bansan wawanci da rashin tunani da hankali maza tashi ki ban waje kiyi abunda ya dace stupid."

Tashi tayi tazo inda nike tana share hawayenta tace.."Yaya Kulu dan Allah ki yi hakuri ba zan sake ba ki yafe man." Kuka ta rushe dashi sauke ajiyar zuciya nayi Ina kamo ta na kama share mata hawayen Ina cewa.

"Kukan ya isa haka komai ya wuce nima kiyi hakuri akan abunda nayi maki ba sake ba."

Cikin kuka tace.."ai na cancanci kiyi man abunda yafi haka Yaya Kulu nima banji dadin abunda nayi maki ba,ki yafe man Yaya Jidda."

Dakyal na samu tayi shuru sai da komai ya koma normal sannan na tashi na shige room din

Please Login or Register in order to submit comment