Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saka Wasila gaba yana ce mata.."Wasila." D'agowa tayi tana kallonshi sai hawaye take kamar ankunna famfo, girgiza kai Baba yayi yana cewa.."goge fuskarki kukan ya isa haka Ina son yi maki tambayoyi."

Goge hawayen tayi tana kallon Baba,gyara zama Baba yayi yana cewa.

"A Ina mutanen suka dauke Hauwa'u."?

Cikin muryar kuka tace.."Baba a bakin gate din school dinmu mune neman naped."

"Mai ya fiddo ku waje neman Naped babu naped ne a school."?

D'aga mashi kai tayi tana sauke numfashin kuka tace.."lokacin da muka fito exams biyar tayi sai muka tsaya a massalaci mukayi sallah sannan muka fito sanda zamuje bus stop babu naped kuma babu bus, mun tsaya shuru basu dawo ba sai muka tako zuwa bakin gate zamu taresu a bakin gate shine muna tsayawa bamu dade da tsayuwa ba suka zo da bindugu suka tafi da Jidda."

Shuru Baba yayi yana kallonta yama rasa mai zaice kenan dai daman already Hauwa'u kawai sukayi niyar dauka idan da ace ba ita sukayi niyar daukata ba da su duka zasu dauke harda ita Wasilar,zufar da ke keto mashi a goshi yayi yana ce mata.

"Amman maiyasa baku jira naped din a cikin makaranta har ta dawo ta daukeku."

"Ai Baba ana haka daman kafin muje wasu sunje Koda muka fito naga wata naped ta dauki wasu ta wuce dasu ,idan bamu fito ba ba zamu samu ba shiyasa muka fito."

"Allah ya kyauta."

Cewar Baba yana tashi ya kalli Yaya Muhd yace.

"Muhd taso muje police station mu shigar da case din."

Tashi Yaya yayi yabi bayan Baba,Koda suka je Police suka shigar da case din tambayar a Ina aka dauketa sukayi masu nan suka basu ansa a bakin makaranta tambaya ta biyu a gaban wa aka dauketa suka ce Wasila yanzun haka tana asibiti ma,tare da yan sanda Baba suka dawo asibitin lokacin Mama ta farfado sai kuka take ana bata hakuri Usman da Sulaiman na tayata kukan,Humaid da yake ya girmaisu shi ke badu Manu hakuri da yake shi level one yake Huda.

Bayan sun dawo Yan sanda sukayi ma Wasi tambayoyi sannan suka tafi nan likita ya sallamaisu suka tafi kamar an hura wisil unguwa har labari yazo yan dauke Jidda ba'a san suwa suka dauketa ba a wajensu ta kwana ma jiya.

Bayan sun dawo Baba ya kira Baba Bishir ya gaya mashi halin da ake ciki,sannan ya kira Baba Usman Baban su Yaya Haidar kenan duk ya gaya masu halin da ake ciki.


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp


*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*121-130*

Zaune suke a cikin parlo sunyi jigum ba mai ma wani magana ba sautin da ake tashi a parlon sai sautin kukan Haidar tun ana bashi hakuri har an daina an saka mashi Ido,kuka yake kamar karamin yaro tunda Muhd ya kirashi waya ya gaya mashi halin da ake ciki ya nemi ticket ya duro a gusau yake kuka..kowa ka kalla fuskarshi a parlon ba annuri a cikinta sai tarin damuwa...damuwar d'aya ce har yanzun basu kira waya ba wanda suka dauketa takaimaimai ba'a ma asan shin waye suka dauketa tunda ba a gida bane balle ace kidnappes ne.

Mutanen unguwa da mutanen gari sai zuwa suke jaje,sallamar da akayi ce ta tada su Yaya daga parlon suka koma bangarensu har lokacin kuka Yaya Haidar yake dafa shi Yaya Muhd yayi yana cewa.

"Haba Broth kukan nan ya isa haka karda ka jawo ma kanka ciwon kai addu'a zamu cigaba da yi mata Allah ya tsare ta a duk inda take shine yanzun fatanmu ba wanann kukan ba, banjin dadi idan Ina kallonka kana wanann kukan da wane zani ji dan Allah."

Cikin kuka Yaya Haidar yace.."Broth kenan duk yanda zan gaya maka yanda zuciyata take man akan wanann b'atan na Jidda ba zaka fahimceni ba,yanzun ace mace tana hannun wasu gardawan banza tun jiya gashi yau din ma dare yayi Ina hankalina zai kwanta ba zai tab'a kwanciya ba wallahi inason Jiddah kuma Kai kasan yanda nike da kishi akan abunda nike so nike kauna ba zan iya yafe masu ba hannunta da kuka kama da shigar da ita a cikin motar balle kuma yanzun da take a wajensu sai kalleta suke taya zuciya zatayi dadi."

Dafashi Yaya yayi yana cewa.."naji na kuma fahimceka na gane abunda kake nufi amman dan Allah kayi hakuri ka daina wanann kukan,kayi mata addu'ar Allah ya Kareta daga sherinsu,mu zage muyi addu'a Allah ya shiga tsakaninta dasu ba wannan kukan ba wallahi rabona da bacci tun shekaran jiya haka abinci mai nauyi sai da tea Kulu ce kawai a raina baiwar Allah."

Shidai shuru kawai yayi yana share hawayen shi bai son yawan magana daman ya lafiyar kura balle,daman can Yaya Haidar bai da yawan magana idan anga yayi magana mai tsawo to ina tare dashi ne amman family kowa yayi mashi shidar shi din missikilne na karshe nima da kallon da nike mashi kenan ya cika miskilancin banzan da kuma girman kai da jiji da Kai kamar wani basarake.

Amman tunda muka fara soyayya dashi na gane ba haka bane shi mutumin so simple yana da dadin zama da dadin hulda bai da damuwa ko kadan sai da yana zafin zuciya da saurin daukar fushi kuma ni sheda ce yana da zafin kishi..kishinshi ya wuce duk yanda zan gaya maku shi ance maza sunfi mata kishi ada ban yarda da wanann maganar ba sai da Allah ya hadani da Yaya Haidar anan na yarda dan shi Yaya Haidar ko a cikin maza samun mai irin kishinshi sai an tona ko antona din dakyal a samu biyu a cikin goma.

Idan yana nuna kishin shi watarana har tsoro nike ji ina jin anya zan iya aurenshi ba?ba dan komai na nike wannan tunanin sai yanda yake da zafin kishi irin masu kishinshi basu cika zaman aure da matansu ba...abunda yasa nace haka suna da saurin zargi magana zakayi da wani namijin zasu aiyana ma kansu wani abu daban to shima haka yake.

Dan sai da nayi da gaske dashi sannan ya hakura ya barni ina cigaba da gaisawa da Yaya Auwal sai da yaga da gaske akan hakan zan iya hakura dashi sanann ya barni ba dan yaso ba,amman idan har yaga muna magana da takai minti biyar sai yayi tsugumi yace har yanzun Ina son Yaya Auwal ai da nasan Ina sonshi da na aureshi haka nike fama dashi akan Yaya Auwal.

Lura da bakin kishinshi da nayi na yanke duk wata hulda da nike da maza wanda ba yan'uwa ba kamar su course mate yan unguwa har da primary school mate dina sai da na datse alaqa ta da su sanann aka zauna lafiya aka cigaba da soyayyar.

Tashi yayi ganin har sha biyu na dare yayi ya shiga toilet yayo alwallah ya fara salloli suma su Yaya Muhd tashi sukayi kuka jona suka cigaba dayi suna Kai kukansu ga Allah Dan shine mai kowa mai kowa ba mai taimakawa sai shi gafurin rahimn.

Basu ne suka bar yin sallar ba sai da aka kira asuba sannan suka tafi massalaci bayan sun dawo suka zauna yin azkar tun da safe wajen karfe bakwai da rabi Yaya Haidar ya tashi ya fito ya tsaya bakin kofar gida duk yaron da yazo wuce sai ya kira shi ya bashi kudi naira goma yana cewa.

"Kayi man addu'a Allah ya fiddo man da matata lafiya ya Kareta ya shiga tsakaninta da wanda suka dauketa dan su cutar da ita."

Haka ya kamayi bai bar raba kudi ba sai da tara na safe yayi sannan ya shigo gida ya bada kudi bai san adadinsu ba,Koda ya koma bayan ya gaisa da su Yaya Muhd bai sake ce masu komai ba ya dauko key din motar Yaya ya fita ba inda ya nufa sai shopping store ya sayi buhunan shinkafa da su macaroni da taliya jarkan manja da farin mai dasu maggi star da dai different campany,haka ya hado iyayeyen kayan abinci aka loda mashi a mota ya tafi.

Bai zarce ko Ina ba sai wata babbar makarantar tsingaya(makarantar allo),bayan ya gaisa da malamin makaranta yasa almajiran malamin suka sauko da duka kayan abincin da ya sawo yace.

"Allah ya taimaki Malan,daman na kawo wanann kayan abincin dan a dunga dafama dallibai kuma ana sakani addu'a wasu yan iska suka dauke wanda zan aura tana wajensu yanzun haka bamu san a wani hali take ciki ba dan har yanzun basu kira waya ba."

Ya ida maganar yana share hawayen da suke zubo mashi a fuska,girgiza kai Malan yayi yana cewa.

"Inalillahi wa'innalaihirajiun!Ya Allah ya toni asirin ko su waye suka dauke wanann baiwar Allah,Allah kuma ya baiyanata cikin koshin lafiya...in shaa Allah yau din nan ba sai gobe ba zamu sauke mata alquri'ani kuma haka gobe sai munyi sati muna mata sauka zata fito in shaa Allah kuma lafiya zata dawo da yarda Allah,kuma ka daina wannan kukan da damuwa yarinyar zata fito Kai dai kawai ka gaya man sunanta dana Babanta."

Dan murmushi yayi dan har yaji dan sanyi kadan da Malan yace zasu sauke alquri'ani mai girma akan b'atan Kulu,sauke ajiyar zuciya yayi yana cewa.

"Sunanta Hauwa'u Abdullah jibir."

Kallonshi Malan yayi yana cewa.

"Wai yar'gidan Alhaji Abdullahi Jibir mai campany din kayan daki aka dauke."

D'aga mashi kai yayi yana cewa..."Eh Malan itace ni kuma kanin Babana ne da Babana da shi uwa d'aya uba d'aya kuma ni zan auri ita Kulu din."

Kama baki Malan yayi yana jimamin abun yana cewa.."Allah sarki Kai dan gidan Bishir ne ko Usman.?"

"Usman."

Kallonshi sosai Malan yayi yana cewa.."Allah sarki rayuwa kenan,iyayenku mutanen kirki duk shekara sai Alhaji Usman ya kawo taimako a wannan makarantar haka ma Abdullahi da Bishir suma suna kawo dai dai karfinsu taimakon in shaa Allah sai mun saka masu da alkhari muma ga ranar da nike tazo kullun Ina rokan Allah ya bani ikon na saka ma bayin nan nashi da alkhari kamar yanda suke taimakon marayu dan haka yi tafiyarka zamu kwana muna nata addu'a Allah ya baiyanata."

Godiya yayi ma Malan yana tashi ya tafi,ba gida ya nufa ba sake komawa yayi shopping store din ya Kara lodar kayan abinci har da kayan tea da su pampers su biro da pencil da books ,ba inda yayi ma tsinke sai gidan marayu,haka aka lode kayan a cikin store din gidan marayu daman gidan ba bakonshi bane yana yawan Kai masu ziyara an saba dashi shiyasa bai Sha wahala ba yana Kai kayan basu wani tsaya bincike ba aka kai su ma'ajiya aka had'a marayu yara yan shekara ukku zuwa goma suka karanta fatiha dasu falaqi kafa ukku ukku aka yi addu'a.

Ba shine ya bar gidan ba sai wajen jen la'asar sannan ya fito ya samu wani waje ya tsaya yana raba hamsin dari da duk wanda rabonshi ya tsaga bai bar rabon kudi ba sai da aka kira sallah yayi alwallah ya shiga wani massalaci da ake wajen da ya tsaya bayan ya gama sallah ya fito yana shirin shiga mota yaji an rikoshi,juyowa yayi fuskarnan turnike idanunshi jajir tsabar kukan da yasha , kallon Wanda ya tabashi yake yana mashi kallon lafiya? murmushi wanda ya tabashin yayi yana cewa.

"Sunana Ahmad Bala mato."

Haidar baice mashi Komai ba sai dai kallonshi da yake yana jiran yaji mai zaice mashi,duk da yasan sunan Babanshi tunda babban mutune a cikin garin gusau yana da kudi iya kudi amman baisan yaranshi ba tunda bai da business dasu,wani killer smile Ahmad yayi yana cewa.

Haidar Usman Jibir."

Dan shuru yayi sai ya cigaba da cewa.."Allah sarki naji labarin daukewar da akayi ma budurwarka Hauwa'u Abdullah jibir shine da na ganka nan arear nace ya dace nayi maka jaje tunda dai Kai ba sani na kayi ba amman ni na sanka sannan kuma yan gidan su Jidda sun sani amman a da,anyway Allah ya baiyanata a duk inda take fatanmu kenan,duk dai takini taki ta soni amman hakan bai sa naji dadin bacewarta ba sai ma shiga damuwa da alhini da na shiga da naji cigiyar b'atanta a gidan tv munata addu'a kamar yanda kike ta sawa muma muna sawa Allah ya bai yana ta."

Da ya dan sakar mashi fuska da yaji yana mashi jaje amman tunda yace shima ya b'ata cewa yana son jiddarshi sai ya nemi fara'ar fuskar shi ya rasa take yaji ya tsani Ahmad baison ganin Koda fuskarshi,balle yaji muryarshi cire hannun Ahmad yayi daga jikinshi yana bude mota ya shiga ya dan kalle shi yace.

"Thank."

Kulle motar yayi ya bata wuta yana bad'a mashi kasa da kura ya barshi nan tsaye sake da baki,iska Ahmad ya Kai ma naushi yana huce kamar wani ingarman zaki,take kalar idanunshi suka sauya tsabar b'acin rai ,kamar shi Ahmad Bala mato wani zai bade da kura da tarin kasa a Ido,tabbas zai ya sa shi kukan da har ya mutu ba zai daina yin shi ba, murmushin gefe baki kuma yayi yana cewa.

"Kishinka na banza ne harda wofi kuma zanyi maganinka yanda ba zan aureta ba haka kaima ba zaka tab'a aurenta ba."

Dariya ya fashe da ita sai da yayi mai isarshi sannan ya dauko waya ya kira wata number bayan an dauka yace.."a tabbatar da ajiyar nan an daureta sosai sanann a watsa mata ruwan sanyi ruwan ma na freeze."

Yana gama fadin haka ya datse wayar yana kara rushewa da dariya ya bude motarshi ya shiga ya wucewarshi gida sai murmushi yake dan shi kadai yasan abunda ke a cikin zuciyarshi.

Sosai yake sakar ma motar wuta yana yi yana sakin tsaki,ba abunda take tafasa mashi zuciya sai maganar Ahmad da yace wai shima saurayin Jidda ne,wato amanarshi Kulu take kenan idan ya koma Birnin kebbi tana da samarin da take soyayya dasu tana rage zafi shi kuwa yana can bai kula kowa bai kallon kowa duk da tarin matan da suke kawo mashi kansu amamn duk yaki ya kulasu saboda son da yake mata,ita kuma tana can tana kula duk wanda ta gadama tana raina mashi wayau.

Hawaye ne kawai yaji suna zubo mashi gefen hannunshi yasa ya gogesu yana fitowa cikin mota ya bude gate ya shiga da mota ko cikin gida bai nufa ba dan yasan gidan cike yake da mutane yan jaje, direct part din maza ya nufa ya zuwa ko sallama baiyi ba ya tsaya gaban Yaya Muhd sai huci yake yace.

"Daman Hauwa'u tana da wani saurayin bayan ni."? Kallonshi suka kama yi yanda yake huci yana Zara Ido yana wani kank'anci Ido rashin mutunci fal a cikin idonshi.

"Kamar ya kenan."

Tambayar da Yaya Muhd yayi mashi kenan yana kafeshi da Ido,cikin bala'i da bakar zuciya ya cigaba da cewa.

"Malan kamar yanda kaji nace,karda ka maida yaro Wanda baisan abunda yake ba Muhammad,taya za'ayi da baikona a kanta tana soyayya da katon banza Kuma kuna sane Kun sa mata ido kuma ka ce man kamar ya bayan kasan komai."

Murmushi kawai Yaya yana kallon Yaya Auwal da bai dade da shigowa gidan ba ,daga lagos yake tun yana Lagos yaji wannan mumunainan labarin yaso ya biyo flight din safe bai samu ba sai wajen ukku ya samu flight yana sauka airport direct gidanmu ya nufa yana zama ya fara yi ma Yaya jaje ya shigo yana masu huci.

Dafashi Yaya Auwal yayi yana cewa.."haba Haidar Kai kuwa maike damunka taya ana cikin jaje da alhini zaka shigo ka kawo wata magana marar tushe da kan gado."

Buge hannun Yaya Auwal yayi daga jikinshi yana nuna shi da yatsa yace.

"Dakata Malan ban sakoka a cikin magana ta ba,ka bari sai na kasa da Kai sai ka kwasa, daman kallonka nike duk wani munafircinka da tsugunne tsugunnenka duk Ina sane da Kai zuba maka Ido nayi naga gudun ruwanka ba dan Ina tsoronka ba, kana wani sunsunna Kai kamar wani na Allah."

Tasowa Yaya Bash yayi yana cewa.." wai maiye kake yi Yaya Haidar tarzoma kake son tada mana a gida ko mai.?"

Matsawa kusa da Bash yayi yana cewa.."Eh tarzomar nike son na tada maku sai ka dauki mataki karamin marar kunya,ko rashin kunya zaka yi man ?da ka taso kana d'aga man murya,ba dole nayi magana ba kuna yan'uwana amman da ku ake cuta ta."

Dafa Yaya Bash Yaya Muhd yayi yana cewa.

"Bash fita kabar dakin nan idan kasan ba zaka sa ido ba a wanann maganar shi Haidar din mate dinka ne da zaka nemi gaya mashi magana.?"

Kasa kawai Yaya Bash yayi da kai bai sake cewa komai ba,amman kallo d'aya zakayi mai ka gane ya Kai kololuwa a b'acin rai,daman shima zuciyar gareshi kamar kuturu dan Ina iya cewa yama fi Yaya Haidar zuciya ko kuma su zo daya.

Kallon Yaya Haidar Yaya yayi yana cewa.

"Zaka iya zama ko Malan."?

Hararar Yaya yayi yana wucewa wajen kayanshi ya fara hadasu cikin trolly din da yazo da ita, kallonshi kawai suke har ya gama ya janyota ya nufi kofar fita,rike trolly din Yaya yayi yana cewa.

"Yanzun Haidar akan kishinka na banza da wofi da ya rufe maka ido kake neman zagina har da had'a kaya da ka had'a Ina zaka da kayan."

Bai ce mashi komai ba sai sakar mashi trolly din da yayi zai bar masu room din, rikishi again Yaya yayi yana cewa.." to ni waye wanann saurayin kuma was ya gaya maka ta na kula wani bayan Kai."

Waigowa yayi yana kallon Yaya idonshi cike tab da kwallah girgiza kai kawai yayi ya kasa magana dan zuciyarshi a wuya take kiris ya rage ya fashe kuka ga wani zafi da zuciyar take mashi kamar ana diga mashi darma haka yake ji,so yake ya fisge daga rikon da Yaya yayi mashi amman ya k'asa.

Hawaye kawai suka fara zubowa a saman fuskarshi hunging dinshi kawai Yaya yayi yana bubuga bayanshi a hankali yake cewa.

"Reliex."

Can kuma ya cigaba da cewa.."be a men my friend." Haka Yaya ya kama lailashinshi sun fi minti goma a haka sanann ya d'ago kanshi daga jikin Yaya,kallonshi Yaya yayi sai suka sakar ma juna murmushi sake komawa yayi jikin Yaya yana cewa.

"Am so sorry Broth."

Sauke ajiyar zuciya yayi sannan kuma ya cigaba da cewa.

"Bansan wani irin so nike mata ba,naji zuciyata tana zafi sosai da ya gaya man wai shi boyfriend dinta ne naji kamar na kashe kaina in huta ,na tsaneshi ban kaunarshi da ace zan ganshi da sai na kashe shi akan Jidda, cike da gadara yake gaya man wai shi boyfriend dinta ne taya zuciyata zatayi dadi wannan gardin Allah ya na kiran Jiddah budurwar shi a gabana."

"Gaskiya ba dadi,amman wanann waye nidai ban san Kulu na kula kowa ba."

Dan shuru yayi kamar yana tunanin wani abu can kuma yace.." I think yace man sunanshi ko Ahmad Bala mato,Ina jin hakane."

Tabe baki Yaya Bash yayi yana gaya masu waye Ahmad da irin case din da akayi dashi sai da ya gaya masu can kuma ya daura da cewa.

"Babban dan iska ne maiyasa baka zubda mashi hakoran gaba ba da yayi naka maganar wannan banzar maganar."
Zama kawai yayi bai ce komai ba yana dafe kanshi,shuru suma sukayi suna jiran tsanmanin.

Bayan wata ukku

Abubuwa da dama sun faru mararsa dadi a family dinmu dan ba za'a kirashi mai dadi ba,dan tunda aka daukeni ba'a sake jin duriyata ba anyi kukan anyi addu'ar amman abun dai ba'a magana sai dai a godema Allah.

Dakyal aka samu Yaya Haidar ya koma Birnin kebbi ya cigaba da zuwa intership din shi amman kallo d'aya zakayi mashi sai ya baka tausayi dan yabi ya rame ya jemai ya lalace ya fita haiyacinshi ya zama wani sususu ba komai yake gane ba kawai rayuwa yake a doran kasa kamar ba Haidar ba dan kwalisa dan gayu celebrities a social media dan rabon da ya shiga wani abu wai shi IG ko Twitter yayi posting har ya manta.

Ya zama wani so silent duk zuciyar nan ta zama tarihi dan sai ayi masu abu sau biyar ko goma bai d'aga kai ya kalli mutun ba,ko a wajen aiki idan yaje ba abunda ke had'a shi da mutane sai gaisuwa daga gaisuwa ba abunda zai sake shiga tsakaninku har a tashi.

A Gusau kuwa kawai rayuwa ake yi a cikin gidanmu amman duk wani farinciki yayi kaura a zuciyoyinsu ko magana mai tsawo gidan basu yi abinci kuwa sai da aka kai ruwa rana sannan suka fara tsakurarshi ba dan dadi ba.

Ba ranar da Meenat bata kuka dan yanzun tabar kwana room dinmu hatta kayanta ta kwasosu ta maidosu room din su Saddiqa kulle room din tayi dan idan zata shiga room din sau dubu sai tayi kuka sau dubu.

Haka ma bangaren Wasi ita dai gata nan dai ga bikinta ya matso saura sati d'aya babu shirin da take ma bikin dan ko gyaran jiki sai da Mami tayi mata jan Ido sannan ta yarda aka fara yi mata shi.

Koda aka kawo lefenta bata bude ta kalleshi ba,dan ranar da aka kawo lefen kwana tayi tana kuka tun Yaya Auwal yana bata hakuri har ya hakura ya kyaleta dan yasan bayan iyayena da yan uwana da Yaya Haidar to ba wanda zai kaita jin zafin b'ata nan nawa, balle ita da aka daukeni a gabanta abun kamar a mafarki ko kuma wasan kwaikwayo.

Babu abunda za'ayi a bakin bayan daurin aure dan bata da yanda zatayi amman har tagawa sai da tayi akan a d'aga bikin sai Allah yayi na dawo ,amman iyaye suka nuna aa addu'a kawai nike bukata a wajenta ta cigaba da yi man.

Sai da Mama tazo tayi mata fad'a sosai sannan ta yarda akayi mata kunshi da kitso na biki,biki ake amman kamar ba biki ake a unguwar ba,dan unguwar yanzun ta koma shuru dan bacewata ba yan gidanmu kawai suke a cikin damuwa.kusan rabin unguwar ne dan kullun idan aka gama sallah a massalacin unguwarmu sai anyi addu'a Allah ya baiyanani a cikin aminci da lafiya.

Ranar juma'a aka daura auren Auwal Ishaq da Wasila Yusuf akan sadaki naira dubu dari,Koda aka gama daurin auren sai da akayi addu'a a wajen daurin auren akan Allah ya baiyanani ya kuma kareni daga duk sherin wanda suka dauke ni.

A ranar wajajen biyar na yamma aka kai Wasi gidanta da ake a GRA ,gidan yayi kyau sosai kuma dangin Babanta sunyi kokari dan sunyi mata kayan daki dai dai karfinsu haka ma kayan kitchen Mami ta cika mata kitchen da kayan kitchen na zamani.

Bayan an gama ganin gidan amarya yan kawo amarya suka watse suka barta daga ita sai halinta,tayi kuka sosai ita har yanzun gani take kamar bacci take za'a tasheta ace ta tashi daga baccin da yake tana fatan taga abun da yake faruwa ya kasance a mafarki ne.take ganinshi ba a zahiri ba,bayan sallar isha'i ango ya shigo shi d'aya dan cewa yayi ya gode ba sai an rakoshi ba.

Da yake squad dinsu d'aya da Yaya Muhd shiyasa basu wani matsa ba akan sai sun rakashi saboda suna cikin hali da alhini na b'atan nawa..Dan sai da Yaya Muhd yayi tsaye sannan aka daura auren a yau,dan shima Yaya Auwal da ya kafe akan a d'aga bikin har sai Allah ya baiyanani,Yaya ne ya nuna rashin amincewarshi da kuma su Baba shiyasa aka daura.

Koda ya shiga daki kwance ya taddata kan gado tana aikin kuka ,ida hayewa yayi saman gadon yana mirginota jikinshi ya share mata hawayen da suke zubawa a saman fuskata can yace a hankali.

"Kukan ya isa haka,ayi hakuri karda ciwon kai ya kama ki."

Rintse idonta kawai tayi bata daina matsar hawaye ba sai da yayi dakyal sannan ya samu tayi shuru da kanshi ya taimaka mata tayi wanka shima yayi sannan suka ci abinci suka wanko baki sannan sukayo alkwallah sukayi sallah suka kwanta.

Washe gari haka dai ta tashi ga ciwon jiki ga kuma damuwar dake a cikin zuciyarta na b'ata na,da hira ya kama janta tun tana maida mashi da uhm da ko har dai ta saki jikinta suka cigaba da shurunsu .

★★

Yau su Meenat suka tashi da aikin gida dan tunda aka daukeni gidan bai sake ganin gyara ba sai dai kaskarima da yake tiles din parlon farine yayi duhu yayi masifar daud'a ga kuma uwar yana da ta kusa Kona gidan tsabar yawanta.

Harda su Yaya suka taimaka wajen ganin

Please Login or Register in order to submit comment