Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dariya kawai nayi mashi haka muka kama wayar mu sai da na tabbatar na cire shi daga situation din da yake ciki sannan muka kashe wayar.

Maida wayar flight mood nayi Ina mai tashi zauna na buga tagumi Ina tunanin rayuwa, komai yana neman ya juyeman na kasa fahimtar matsayin Yaya Auwal a raina,ga kuma tunanin Ahmad da ya makale man a zuciya,na rasa daina tunanin shi zuciyata ta karkata da son jin wani irin tuba yayi na gaske ne ko kuwa na karya ne,idan har da gaske ya tuba ya dawo hanyar gaskiya Mai yake nufi da ya hakura dani?yana nufin baya sona kenan?ai kuma yace daga mai kaunarki Ahmad,kenan har yazun yana kaunata kuma yace ya hakura dani? maiyasa zaiyi man haka?maiyasa zai zab'i rabuwa dani bayan kuma ni inasonshi tun farkon haduwarmu,tabbas idan har da gasken gaske yake ya tuba to ni kuma a shirye nike da aureshi dan ni zuciya ta da sonshi take rayuwa saboda da sonshi na kasa yarda na tusa son Yaya Auwal a zuciyata.(Toh jama'a wata sabuwa kuma anya kuwa Jidda ba zata aikata kuskure ba😢,son Ahmad fah?mutumin da yake kokarin cutarta mudai je zuwa Muji ya labarin zai kaya dan yanzun dai aka fara).

Ganin har daya na dare yayi na kasa bacci na tashi nayi alwallah na fara sallah Ina neman zabin Allah,sai da na gama sallah nayi karatun quri'ani sannan na kwanta zuciyata fal!da tunani iri iri wani bangaren soyayyar Ahmad wani bangaren soyayyar Yaya Auwal kuma ,fahimta nayi banda alqibila baki daya ma kam,salati na kamayi har na samu bacci yayi awon gaba dani.

*Washe gari*

Da wuri na tashi duk da bamu da lecture yau Yaya Teemarh zata tafu birnin kebbi kuma flight din 12 zata bi,Ina tashi wanka na shiga na shirya cikin wata light purple din atamfa ban tsaya daura dankwali ba na dauki hula kawai na saka sanann na fito parlo.

Koda na fito parlo ba kowa a cikin shuru yake sai tv da take aiki ita d'aya ,yan gidan ba duka suka tashi ba dan nidai a room dinmu na wanda ya tashi sai ni,shiga kitchen nayi nan ma babu kowa a cikin,alamu sun nuna nice na fara fitowa parlo ma.

Ida shigewa kitchen din nayi debo Irish na fere sai doya na daura doyar bisa wuta shi kuma Irish nan fara soyashi ,Ina gama soyashi na duba doyar naga ta nuna itama na sauko ta na yankata slide na soyata na duba a foodflake, ruwan zafi na dafa Wanda yasha kayan hadi sai da ya tafasa sannan na juye a flask naje na jerasu a dining na koma room dinmu.

Ina shiga na tadda Yaya Teemarh ta tashi har tayi wanka tana gaban mirror tana shiryawa,matsawa nayi a kusa da ita na daura kaina a saman kafadarta muna kallon juna ta cikin mirror Ina cewa.

"Morng Yaya Teemarh." Murmushi tayi tana shafa fuskata tace."Morng too Kulu,fatan kin tashi lafiya."? Komawa nayi gefen gado na zauna Ina cewa."lafiya lau Alhamdullahi,har na fara missing dinki Yaya Teemarh wallahi da ace Ina da yanda zanyi da baki zuwa wani birnin kebbi nidai idan na tashi aure ba zanje wani kebbi ba."

Murmushi tayi tana daura dankwali tana cewa. "Kulu kenan,ba zaki gane ba na fiki rashin son zuwa birnin kebbi dan mutanen gidan basu da kirki wallahi gwara ma Yaya Haidar yafi su mutunci,wallahi haka zanje naita rakubewa kamar maiya."

Tsaki nayi Ina cewa."Shima ai Yaya Haidar din watarana ba kirki ya cika ba,abunda yake bani haushi dashi d'aya ne ka gaidashi yana ji yayi maka banza,kamar kana gaida gunki." Mtsss na kara sakin wani tsakin, murmushi tayi tana cewa."wallahi gwara Yaya Haidar sau million akan sauran,shi dai barshi bai cika son yawan magana ba,amman Yaya Bilal shi ko murmushi baya yi ma mutane Koda mukaje bikin shi fa Allah yasa alkhari fa mukayi mashi idan zaki tuna bai ansa ba,ni wallahi dan ba yanda zanyi da ban zuwa."

Kaima Meenat duka nayi Ina cewa."tashi kwanan ya isa haka." Turo baki tayi tana cewa."idona biyu tun dazun inajin duk abunda kuke cewa, kudai kudaina yin haka wallahi suna da kirki sudai halinsu haka yake basu son yawan magana shine kawai muyi masu wannan uzurin please."

Tashi nayi Ina cewa."find kidai tashi ki shiga wanka dan goma ta wuce,kuma dai Yaya Teemarh 12 zata tashi." Ficewata nayi na koma parlo chanza channel nayi na maida Peace tv Ina kallon wa'azi.

Ban dade da zama ba su Mama suka fito,gaidasu nayi Ina cewa."yau dai na riga kowa tashi a gidan nan." Na ida maganar Ina dariya,murmushi Mama tayi tana cewa."gaskiya kam yau za'ayi ruwa har da kankara kuwa." Dariya mukayi mu dukanmu sanann muka wuce dinning danyin breakfast Muna gamawa Baba ya tashi yasa Yaya Teemarh ta dauko kayanta da ta hada suka tafi,har da kukanta dan har zuciyarta bata son zuwa birnin kebbi dan dai kawai bata da yanda zatayi.

Bayan tafiyarsu na shirya na tambayi Mama zani gidan su Wasi ,Dan inason na ganta zamuyi wata magana,da ta hanani dakyal na samu ta barni akan karda na jima,godia nayi mata na saka hijab dinta na fita.

Da sallama na shiga gidansu,da yake gidansu ba wani babban gida bane kuma flat bane gidane mai tsakar gida da toilet da kitchen sai ciki da parlo,Mami(mahaifiyarta) na tadda a tsakar gida tana tsintar shinkafa har kasa na duka na gaishe ta Ina cewa.

"Mami fatan na samaiku lafiya."? murmushi tayi tana cewa."lafiya lau Alhamdullahi,ya Mamarki."?tana lafiya tace na gaisheki."Ina ansawa tana ciki shiga."

Murmushi nayi Ina cewa."Allah yasa dai tana lafiya naga yau Keke aikin gidan."?dariya Mami tayi tana cewa."lafiya lau yanzun nan ta shiga ita ke tsintar tashinta na dauka Ina dan yi dan na gaji da zaman nan haka nan bani komai ai sai jiki yayi ciwo."

Amman Mami da kin bari mun fito mun ida kawai."girgiza kai tayi tana cewa."karki damu Allah yayi maku albarka." Amin nace Ina ida shigewa ciki,tas parlon yake yasha gyara sai kamshi turaren wuta yake ,ba kowa a parlorn sai na shiga uwar d'aka tsaye na taddata a gaban laka komai take nema oho,da sand'a na shiga Ina rungumota ta baya Ina cewa.

"Nayi fushi nikam."

Juyowa tayi tana sauke ajiyar numfashi tace."wallahi Hauwa kin tsoratani sosai!daman dazun na gama maganarki a cikin zuciya ta zan tambayi Mami anjima zan shiga na ganki rabona dake tun da na kaiki gida,inason nazo naji ya kuka k'are da wannan bunsurun dan iskan."

Dan b'ata fuska nayi Ina cewa.."wayyo Allah Wasi ki daina ce mashi bunsuru kuma harda dan iska ma." Tsaki tayi tana cewa."to ba dan iska bane?ko kuma bai cancanci da a kira shi da bunsuru ba?ke ni wallahi tsani gayen nan banson ko ganinshi ace mutun bai da hali Ina dalili,kullun addu'a nike Allah yayi mana tsari da irinsu haba."

Murmushi nayi Ina zama nace."daman ni magana nazo nayi dake kuma a kanshi ne fa da Yaya Auwal." Kallona tayi tana ajiye turaren da ake hannunta ta dawo gefena ta zauna tana cewa."wani abun ya sake faruwa ko."?

Girgiza mata kai nayi Ina cewa."ko d'aya Wasi ba abunda ya faru ,sai dai kinsan shekaran jiya Baba gidansu su Ahmad yaje ya gayama Babanshi abunda ke faruwa,nan Babanshi yayi mashi fada a gaban Baba har yaba Baba hakuri,shine fa ya turoman message akan na yafe mashi kuma ya hakura dani,shi kuma Yaya Auwal yace na bashi dama ya turo kudi kuma wallahi ni har yanzun ban sonshi Wasi,ni sai naga kamar ma Ahmad din nike so."



*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*EDITING ❌*

*31-40*


Itama Wasila tashi tayi tana cewa."Allah ya bada hakuri,Mama zan wuce gida." Kallonta Mama tayi tana cewa."Amin,Amman Wasila kunyi ganganci ai ba'a kin fadin wanann babbar matsalar,fadi ake da wuri dan ayi ma tukar hanci ba sai komai ya runceb'eba." Kallona Wasi tayi tana cewa."wallahi Mama bansan bata gaya maku ba,dan nasan bata boye maku komai nasa tuni Kun sani ai da nasan baku sani ba da ni da kaina zanzo na gaya maki dan ayi maganin matsalar."

Kwafah Mama tayi tana wurga man harara tace."Kulu ashe daman baki da wayau ban sani ba,ashe wayaunki na banza ne har da wofi?ina kika Kai hankalinki da tunaninki Kulu,to daga yau karda na sake ji balle gani karda ki sake boyeman komai naki,nice mahaifiyarki nice ya dace ki daya ma damuwarki,karda ki sake ko da wai ace kin boye man abunda ya shafeki dan nice nayi silar kawoki duniya."

Dan shuru tayi tana mai kallon Wasila tace."yi tafiyarki Wasila,Allah yayi maki albarka ya kareki a duk inda kike."Dan dukar da kai Wasi tayi tana cewa ."Amin ya Allah Mama na barku lafiya." Tafiya tayi bayan ta tafi Mama ta cigaba da cewa."duk duniya baki da kamata daga ni sai yan uwanki,ban hanaki.gayama Wasila damuwarki ba tunda itama tana gaya maki ta ta damuwar,amman kisan mai zaki ringa gaya mata,bai yuyuwa ace yanda tasan asirinki ni uwar da na mahaifeki ban sani ba,gaskiya ban yarda da wannan tsarin ba."

"Inason nida ku mu zama tsintsiya inason gidanmu mu zama abun kwatainci a wajen yan'uwa saboda hadin kanku, inason yarana su mana abun nunawa a wajen kowa saboda nastuwarku,dan haka karda ki sake rufemana damuwarki dan damuwarki tamu ce mu dukanmu,haka ma farincikinki namune mu dukanmu,mu hadu muyi murna tare idan a abun farinciki ya samu d'aya a cikinmu,sannan mu hadu muyi kuka tare idan wani abu ya samu wani a cikin shine ake kira da uwa daya uba daya."

Nidai bance komai ba,inajin yanda suke man fad'a dan sosai Mama tayi man fad'a kamar ba Mama ba mai saukin kai da raha maiwasa da yaranta,sai da suka gama na basu hakuri sannan na tashi na shiga room dinmu,wanka nike son nayi ga kuma kaina na ciwo saboda hayaniyar da nayi Ahmad ga kuma maganar su Mama, wani irin ciwon kai Nike sosai wanka na shiga dan na dade a toilet Ina watsa ma kaina ruwa Ina sauke ajiyar zuciya,sai da naji natsuwata ta dawo normal sanann na fito,doguwar rigar material na saka sanann nayi sallah na kwanta sai bacci duk da banyi isha'i ba, na gaji Ina bukatar hutu sosai.

★★★

Koda su Baba suka fita ba inda suka zarce sai gidan su Ahmad sallama Baba yayi ma mai gadin gidan yana ce mashi. Malan sannu da aiki."

"Yauwa sannu Alhaji,lafiya dai ko."?

Lafiya lau Alhamdullahi,nace Alhaji Bala mato yana ciki kuwa."? Dan shuru maigadi yayi yana kallon Baba sai kuma yace."yana ciki,amman baiyi dani yana da bak'i ba gaskiya." Murmushi Baba yayi yana cewa."eh gaskiya kam baisan da zuwana ba,amman dan Allah kayi man alfarma kayi man sallama dashi dan magana nike son nayi dashi mai mahinmamci."

A gaskiya Alhaji kayi hakuri dan baisan ana shiga ana kiranshi idan baiyi da kowa zasu hadu ba,dan shi Alhaji Bala ba mutumin da ake zuwa ana ma hawan kawaraba." Murmushi Baba yayi yana cewa."amman ai ban maka kama da mabaraci ba dai ko?tun daga kayan jikina zaka kalla har da motar da nazo da ita banyi kama da matsiyaci ba."

"Alhaji ai daman bakayi kama da matsiyaci ba,inason ka fahimci da wanann aikin nike ciyar da iyalaina,kuma miskila kadan za'a samu na rasa wannan aikin nawa bansan Ina zan saka kaina ba,shiyasa nike kiyaye dokar gidan nan dan a zauna lafiya." daga kai Baba yayi yana cewa.."na gane Malan karka damu,Allah yayi mana bude na kwarai." Da Amin ya ansa yana cewa.."nagode da ka fahimci ni."

Daukar wayarshi Baba yayi ya kira wani abokinshi ya turo mashi number Alhaji Bala mato,kira kusan biyar Baba yayi bai dauka ba sai a na shidda ya dauka ,ajiyar zuciya Baba ya sauke yana cewa.."Assalamualaikum." Daga can bangaren Alhaji Bala mato ya ansa yana cewa."Amin'walaikumus Salam."

"Alhaji fatan kana lafiya."?

"Lafiya lau Alhamdullahi."

"Kana magana da Alhaji Abdullahi Jibir."

"Alhaji Abdullahi Jibir mai campany A Jibir furniture."? Daga kai Baba yayi yana cewa.

"Eh Alhaji nine." Dariya Alhaji yayi yana cewa."Allah sarki Allah Abdullah ya kasuwa ya kuma hakuri da jama'a."? Girgiza kai Baba yayi yana cewa."Alhamdullahi Alhaji,Daman wajenka nazo sai mai gadi yace ba zan samu damar shiga ba,saboda ba'a gaya mashi zanzo ba shiyasa ya hanani."

"Hakane Alhaji Abdullahi nine na kafa mashi wannan dokar saboda idan na shigo gida mutane basu barina na huta sun dunga zuwa bara kenan bayan kuma na bude hanyar da za'a dunga neman taimako idan har rabonka ya rantse,amman ba'a zuwa wajen sai Azo nan kaji dalili."

"Allah sarki,yanzun ya za'ayi zan iya ganninka ko kuma sai gobe dan naga dare yayi har takwas tama wuce." Girgiza kai yayi yana cewa.."ba damuwa zamu iya haduwa ai Alhaji Abdullahi ai Kai dan gidane bani minti biyar gani nan fitowa."

Ba'a fi minti shidda ba Alhaji Bala ya fito sai murmushi yake gaisawa sukayi da Baba sannan ya shigo dasu cikin gida,wajen saukar baki ya kaisu sanann yasa a kawo masu ruwa mai sanyi da lemu, bayan sun dan sha sannan Baba ya numfasa ya kalli Alhaji ya fara cewa.

"Daman nazo ne akan maganar Ahmad dan wajenka." Murmushi Alhaji Bala mato yayi yana cewa "Allah sarki,Allah yasa dai lafiya Alhaji Abdullahi." Murmushi Shima Baba yake yana cewa.."lafiya ba lafiya lau ba dai Alhaji."

Dan gyara zamanshi yayi yana cewa.."Au ikon Allah,Allah dai ya shirya mana zuri'a Alhaji Abdullahi wani abu yayi kenan."? d'aga mashi yayi yana cewa.."Amin Amin!Daman yar'matsala ce ta hadasu da yarinyar wajena har ta kaisu da masayar baki har da da mare mare sukayi ma juna."

Girgiza kai yayi yana cewa.."Asha subuhanllh ,Allah ya sawaka ko mai ya hada su kuma."? komai Baba ya kwashe ya gaya mashi bai Kara ba bai kuma rage ba,sai da ya dan numfasa sannan kuma ya cigaba da cewa."da na tambayeta gidan wa yake sai tace man dan gidan ka ne,kuma da naji tace dan gidanka ne sai naga bai dace na Kai ga hukuma ba,gwara kawai nazo na gaya maka sai kayi ma tukar hanci."

Numfashi ya sauke yana cewa."nagode kwarai da karrancin da ka nuna man Alhaji Abdullahi,nagode da ka rufaman asiri dan wannan abun ashane ace musulmi yana cewa zaiyi fasikanci ko da tsiya bayan na tarbiyar da aka koya mashi kenan ba,daman ka haifi d'a baka haifi halinshi ba,in shaa Allah daga yau angama ko kallon inda Hauwa'u take ba zai sake ba indai na Isa dashi kuma ni na haifeshi." Dan shuru yayi ya cigaba da cewa.In shaa Allah ta kare yau dinan ba sai gobe ba komai zai zama tahiri,inajin bai Kai da shigowa gida ba dan banga motarshi ba,amman da ya dawo zaizo ya samaini har inda nike."

Kara ba juna hakuri sukayi sannan suka tashi zasu tafi,fitowa tare sukayi sai labari suke Baba yana bashi shawarar yanda zaiyi ma Ahmad karda yayi mashi zafi dan a wajen yi mashi fadan, sannu a hankali ya kuma dunga janshi a jiki har ya samu ya rabashi da abokan da yake tare dasu dan sune suke b'ata mashi tarbiya.

Suna fitowa yana shigowa,parka motarshi yayi yana isowa wajensu har kasa ya duka ya gaida Baba ya mika ma Bash hannu suka gaisa kallon Babanshi yayi yana cewa.

"Abba barka da dare."

Girgiza kai kawai Alhaji Bala yayi yana cewa.."yauwa sannu." Yanda Abban nashi ya ansa mashi gaisuwar sai jikinshi yayi sanyi,kasa hakuri yayi dan Ahmad a gidan mutumin kirki ne,ba wanda yasan yana da boyaiyen hali ko da kuwa matarshi ce ,yana kominshi a boye ba tare da kowa yasan mai yake shukawa ba.

Kasa yayi da kanshi yana cewa."Abba Allah yasa lafiya."?kallonshi yayi yana cewa."mai kagani Ahmad."?kasa yayi da kanshi yana cewa.

"Abba."

Daga mashi hannnu yayi yana cewa."Ahmad daman tarbiyar da na baka kenan."? Shuru yayi yana tunanin wani abu,sannan kuma yace.."Abba kayi hakuri dan Allah duk da bansan mai nayi ba."

"Hakane kuwa baka san mai kayi ba,amman yanzun zan gaya maka abunda kayi,ko kasan Hauwa'u Abdullah jibir Jiddarh."? Yanda ya dago kanshi fuskarshi ta nuna alamun rashin gaskiya tsintsa akan fuskarshi,kasa cewa komai yayi sai dai kafe Baba da yayi da Ido,sai da Abbanshi ya fadi sunana yaga kamata da Yaya Bash, sai kuma Baba da yake da dan yanayi nima,girgiza kai yayi yana cewa.

"Eh na santa Abba, school dinmu d'aya da ita." Murmushi Alhaji Bala yayi yana cewa."Daman ansar da nike son ji kenan,bayan ka santa mai kuma ke tsakaninku."?

Kawai rasa abun cewa yayi wato dai Jiddarh gayama Babanta abunda ke tsakaninsu tayi,tabbas idan har hakane tayi mashi abunda har ya mutu ba zai manta ba, zai kuma nuna masu kuskurensu daga ita har iyayenta yanda ta tona mashi asiri a wajen Abba,yanda suka saka zuciyar Abba yin baki shima sai ya sakasu nadama ta har abada,sai kuma ya yanke masu farinciki da walwala a gidansu ta har abada,sai ya dasa mata tabo a zuciyarta wanda har ta mutu ita da a halinta ba saeu manta ba. (Wata sabuwa kuma,sunzo dan gyara gashi sun b'ata goma daya bata gyaru ba,jama'a shin wani irin abu kuke tunanin Ahmad zai ma Jiddarh?)

Kukan munafinci ya barke da shi yana cewa."tabbas nayi nadama akan abunda nayi,kuma ban kyauta ba kuma wallahi ba hali bane Abba ka yarda nayi komai nace mata barazana nayi mata daman,Kuma ni tun dazun na yanke shawarar rabuwa da ita ta har *ABADAN* Abba."

Shuru Alhaji Bala yayi sai kuma yace."ka sani Ahmad komai kayi Allah yana kallonka idan har ni bani ganninka,kuma ka sani bani kadai zaka zubarma da mutunci ba har da kai da yaranka da kuma kannanka,dan haka dan Allah a kiyaye Ahmad abunda zance maka kenan nidai Allah ya sani mun baka tarbiya dai dai gwargwado."

Kuka ya fashe da shi yana basu hakuri sai da ya tabbatar da sun hakura har da raka su Baba bakin gate ya dawo gida,anan ma hakuri ya Kara ba Abbanshi sannan ya wuce part din shi.

Yana shiga part dinshi ya fada wanka, yana cikin wanka ya saki murmushi yana cewa.."wallahi!wallahi?wallahi! Jiddar sai na sakaku kuka daga ke har matsiyatan iyayenki,sai na yi maki abunda har ki mutu ki koma a wajen Allah ba zaki taba mantawa da fuskata ba,balle sunana wannan alwashine na dauka ma,yanda kika zubarman da mutunci a wajen mahaifina ni kuma zan zubar maki da naki mutuncin a idanun duniya,yanzun aka fara wasan nida ke, kinyi naki wasan ni kuma yanzun zan fara nawa cikin ruwan sanyi." Hhhhhhh Daria ya fashe da ita sai da yayi Mai isarshi sannan yace.

"Sai na zama ajalinki,daga ke har iyayen naki da suke nuna wani so ga gareki sai nasa son da suke maki ya rikid'a ya koma tsana."
Haka ya gama kudurinshi sannan ya fito yayi shirin kwanciya ya kanta da takaicina a zuciyarshi.

Koda su Baba suka dawo gida basu nemi a tadani ba,bayan sun huta ne suka gaya ma su Mama duk yanda sukayi da Alhaji Bala mato,sai da ya gama gaya masu duk abunda ya faru da fadan da Babanshi yayi da kuma hakurin da yaron ya bada sannan Mama tace.

"Wallahi har hankalina ya kwanta Baban Muhammad,karkaso kaga halin da na shiga da labarin nan yazo man na shiga damuwa marar musaltuwa,Allah ya Kara shirya mana zuri'a."da Amin Baba ya ansa yana cewa."karda kiso kiga yanda Alhaji Bala ya nuna damuwarshi,mutumin kirki, amman daga ganin wanann d'a nashi sai dai Addu'a yana da tsayaiyun idanu gaskiya kam."

"Hakane ai daman sai ka haifi d'a baka halinshi ba,Allah dai ya shirya mana."

"Amin ,yauwa na manta ban gaya maku ba,mun tsada ranar auren Fatima fa,dazun naje gidan Yaya Bishir yake gayaman an tsada rana jiya." Washe baki Mama tayi tana cewa."Masha Allah,wani wata aka kai sa bikin."? Murmushi Shima Baba yayi yana cewa.."nan da wata biyu masu zuwa haka yace man."

"Allah ya kaimu da rai da lafiya,amman naji dadi da ace itama Kulu ta gama nata karatun ba sai a hadasu ba ayi tare." Girgiza kai Baba yayi yana cewa."A'a Koda ta gama nata karatun ai bata shirya yin auren ba dan yanzun naga alamu." Gyara zama Mama tayi tana cewa."yanzun Baban Muhammad zuba mata ido zamuyi Kenan har sai randa ta shirya yin aure zamuyi mata."? daga mata kai yayi yana cewa.."kwarai kuwa." Kama baki tayi tana cewa."ko maiye dalilinka."?

Murmushi yayi yana cewa."yanzun kikayi magana,tabbas nima naso haka gaskiya kam na hadasu nayi masu aure tare na wuce wajen,amman sai na lura ita Kakata har yanzun bata da wanda ya kwanta a zuciyarta taji tana sonshi da aure a cikin masoyanta,kuma ni maganar gaskiya ba zan yi ma y'ay'ana auren dole ba wanann shine dalilina."

Yanzun shi Auwal kenan ba mijin da za'aji ana so bane?idan har bata son Auwal to bansan wani irin miji take son aure ba gaskiya,wata ila kyaun da take ganin Allah yayi mata yasa take raina arzikin duk wanda suke zuwa wajenta,ta fi son wanda zai bata mota da gida da kuma kaita aikin hajji."

B'ata fuska Baba yayi yana cewa."Kull!daga yau karda ki sake yin makanmanciyar wannan maganar,nama lura nuna wa kike yaran nan sun isheki fa,mai suka tare maki a gidan nike ciyar daku basu isheni ba sai ke haba dan Allah dan Maman Kulu banji dadin jin wanann maganar ba gaskiya,abunda nike son dake shine ki ta yi masu addu'a Allah ya kawo na gari ,amamn na tabbata babu wata manufa a zuciyar Kakata sai alkhari kuma muna ta fatan samun alkharin ita da yan'uwanta baki d'aya."

D'aga Kai kawai Mama tayi tana cewa."hakane amman banyi maganar da wata manufa ba,taya zan gaji da yaran da na haifa da cikina,nifa ce nayi nakudarsu ni kadai nasan wahalar da nasha kafin na haifesu tun daga wajen daukar cikin har rainonshi da kuma haihuwarshi,kawai dai bansan tayi sakin hannu kamun na guje,Ina mata sha'awar auren Auwal,ba dan komai ba sai dan tarbiyarshi da hankalinshi da kuma natsuwarshi sune kawai birgeni a wajen yaron ba komai ba."

Lura da ranta ya b'aci Baba yayi,sai ya saki murmushi yana cewa."na fahimceki yar albarka rayuwata,Allah yayi maku albarka ku dukanku,yanzun dai sai a fara shirin auren Fatima tunda shi Allah ya kawo lokacin damai damai ne baku ida saye ba wajen kayan kitchen."

Turo baki Mama tayi tana cewa."ai daman ka saba sai a daki mutun a hanashi kuka." Dariya yayi yana cewa."gayaman mana yanmatana damai damai ne baku gama saye ba." Dan shuru tayi tana cewa."eh to mun saye komai gas cooker ce da oven sai tested sune kawai suka rage."

Jinjina yayi mata da hannu yana cewa."a gaskiya ne Madam kina da kudi fa,su kenan abunda suka rage gaskiya kinyi kokari Allah yayi maki albarka,gobe in shaa Allah sai ku shiga kasuwa ku karasa sawo duk abunda kuke bukata 6m ta isheku ko."?

Daga mashi Kai tayi tana cewa.."eh sun Isa Allah ya Kara bude." Amin yace sai kuma yace.."kayan daki kuma idan kun samu lokaci sai kuje campany ku zabi wanda kuke so,daman jiya order da nayi a turkey da dubai suka iso,na manta ban gaya maki ba shiyasa ai nai dare ba ban dawo da wuri ba ranar."

Allah ya Kara bude maka mijina ya karemana kai Kaine rayuwarmu nida y'ay'ana Kaine komai namu Allah ya Kara tsawon rai." Murmushi yayi yana jin son matar tashi na Kara shigarshi,koya zai bata mata rai to bata fasa yi mashi addu'a,aikin Kenan kullun cikin yi mashi addu'a take,ko da kuwa a rana ya zuba mata ido bai bata kudin cefane ba zata dauka cikin kudinta kuma bata fasa yi mashi addu'a, wanann kyakyawan halin nata yasa baijin zai iya hadata da wata mace ,dan babu abunda ya nema a wajenta ya rasa.

★★★

Washe gari Koda na tashi Baba baiyi man maganar ba,kuma bai chanza man fuska ba mun gaisa kamar yanda muka saba gaisawa,haka ma Mama dan da kanta yau tama zubaman abinci Ina cikin ciki ta kalle ni tace.

"Kulu yau kina da lecture ne."? Girgiza mata kai nayi Ina Kai abinci a baki sai da na hadiye nace."A'a Mama bamu da lecture sai kuma Friday in shaa Allah." Tashi tayi tana cewa.."okay daman fita zamuyi nida Teemarh da Meenat ke kuma sai ki tsaya kiyi girki."turo baki nayi Ina tura plate din abincin da ke gabana nace." Mamana Ina zakuje kuma?sannan kuma

Please Login or Register in order to submit comment