Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Ammie suka shigo da amare,Mom ta kamo Zubaida da Moha sai kuma Ammie ta kamo Zulaihat da Najeeb sai suka saka Hajja a tsakiya.yanda sukayi tsarin dole sai sun baka sha'awa gwanin burgewa,dole kaji family din sun birgewa yanda suke rayuwarsu babu nuna banbanci,Dan ko su iyayen suna mutunta juna tsakanin Mom da Ammie suna ganin girman juna babu nuna mijina tafi mijinki, rayuwa suke Mai kyau abar koyi dan basuyin wasa da zamuncinsu ba, wannan aiki kuma na Hajja ne da ta tsaya tsayin daka ta hada kan zur'arta,bata yarda aka shigo mata da kabilanci ba a cikin zuri'a,dan da ta ga ana neman kawo mata shirme zata taka burki take.

Har wajen zamansu suka rakasu sannan suka jiyo daga dan bangarensu kadan suma suka samu wajensu suka zauna.tunda aka taho dasu har suka zauna bata daga kai ba ta kalli ko inda yake ba,haka zalika shima kallo daya yayi mata ya dauke kai bai kuma kallonta ba,daman bata gaidashi ba yana rike da ita dan ko dazun da yazo akan yi mata kwaliya bata gaidashi ba , yanzun ma haka ta kasa gaidashi,yaji haushi sosai akan rashin gaisuwar da tayi mashi shiyasa bai yarda ya kara kallon inda take ba,duk da zuciyarshi na ingizashi akan ya kara kallonta dan tayi mashi kyau sosai kwaliyarta ta tafi da Imaninshi,baiki ta tsaya a haka ba, amman hakan bai zaisa ya kama kallon yarinya ba tazo ta raina mashi wayau,dan ya lura da taketakenta wani raini raini take nuna tazo mashi dashi kuma shirye yake da yayi maganinta.

Itama a tata zuciyar haushinshi take ji, ji take kamar ta kama masga mashi maruka ko ta danji sauki a zuciyarta,tana bakincikin nuna ko in kula da yake mata a rayuwa,ba abunda tafi tsana a taitare da shi sai I don't care attitude da yake nuna mata.kuma a haka ake cewa yana sonta,Ina son yake?daman haka ake so?indai haka ake so to ashe shi son ma suna ya tara,dan turo baki tayi tana harararshi ta kasan ido,tanan taga kwaliyarshi ba laifi kam yayi mata kyau,bata taba sanin kyaunshi ya kai kyau ba sai yau dan wata farar shadda gizina yasa ,sai ya daura hula ash da takalmi ba karamin kyau dressing din yayi mashi ba,kamar wani shuwa tsabar kyau,a ranta take tunanin anya bai hada jini da shuwa ba?sai dai shi bai da haskensu sosai bakayi mashi kallo daya ka gane shi wani tribe ne sai kaga kamar fulani kamar shuwa kuma kamar buzu,a hankali ta dauke idonta ganin yana shirin kamota,kuma bata san yaga tana kallonshi dan karda ya dauka ta damu dashi ko kuma tana sonshi ya rainata.

Murmushin gefen baki yayi yana kwafah dan shi kadan yasan abunda ke cikin ranshi gamai da ita,shi kad'a yasan irin hukuncin da zaiyi mata idan aka barsu daga shi sai ita, dole ya cire raina da yake gani a cikin idonta,kuma tabi shi ko tana so ko bata so,dan ba zai dauki shashanci ba a wajenta kuma ba zai dauki yarinta ba dan ya lura yarinta tanan dawainiya da ita.
Bude taron da akayi da addua ne ya maido dasu daga duniyar tunanin da suka wulla ,su duka maida hankalinsu wajen addu'ar da ake sukayi,ana gama addu'ar kowa ya shafa sannan matar da tayi addu'ar ta koma ta zauna,Mc ya tashi ya gabatar da Malama Zainaba Jafar za tayi wa'azi na 30min,take wajen ya kara yin shuru nan ta tashi ta dawo inda aka tanadar mata ta zauna ta fara wa'azi akan zamantakewar aure,maiye aure,Mai shi kanshi auren ya kunsa ,aikuwa sunsha wa'azi dan ba inda bata tabo ba tun daga kan hakuri biyaiya da kuma bin miji da kuma mutunta kowa nashi,da kuma kara tuna ma ma'aurata da su bi mazajensu idan suna son shiga aljana banda yi ma miji gardama,kuma banda yana fada kina fada,take jikin kowa yayi sanyi zuciyar kowa na wajen sai da tayi lakas,bayan ta gama malama Juwairiya ta ansa ita kuma tayi magana akan kwaliyar mace a gidan miji,da tsafa da kuma iya girki da iya magana da kuma gyara jiki karda kije ma miji jiki duk wari karda kuma ki bar makwancinku da daud'a itama.30min tayi sanann Mom ta tashi itama tayi tata nasihar haka ma Ammie sannan ka fara bada abinci.

*FRIED JALLOF RICE WITH CABBAGE* suka girka da *BEEF SAUCE* sai kuma *EGG PUFF PASTRY* da ake daurawa saman fried jallof,sai kuma aka daura ma kowa juice different flavors haka aka bi kowa da shi,bayan angama ci ansha ankoshi aka fara raba dubai abaya da takalmi da turare haka aka gama komai cikin tsari ba'a gama walima ba sai kunsan tara na dare nan aka kai amare part din Hajja,anan su Dad suka zo da su Ammie aka hada harda su Najeeb din akayi masu wa'azi dan ba komai suka tsaya ce masu ba,dan komai zasu gaya masu to su Malama Zainab sun gaya masu a wajen walima,tuni dai suka kara yi masu sannan suka saka masu albarka suka ce ko wane ya dauki matarshi ya tafi da abunshi gidansu Allah ya basu zaman lafiya,nan fa Zulaihat ta fashe da kuka tana daura kanta saman Ammie,rairashinta Ammie ta kamayi amman takiyin shuru,itama Zubaida kukan take amman nata bai kai na Zulaihat ba dan bamai ihu take ba,sabanin Zulaihat da har take ta bani dan kuka take sosai har Ammie ta sakata a gaban motar Najeeb kuka take sai da akayi dakyal ta shiga motar ma,da bissimllah ya tada motar bayan ya samu ya kulle motar dakyal, weaving yayi ma yan gidan yana danna horn gateman ya bude masu gate suka fita.
Tunda suka kama hanya take kuka tana ta bani ta shiga ukku,taka birkin motar yayi yana kallonta can kuma ya girgiza kai yana dafe kanshi saboda da ciwon da yake mashi,tsaki yayi yana ce mata.."yi man shuru tun da ba kashe ki nayi ba." Yanda yayi maganar ne yasa ta kama bakin ta tana hawaye nan yasa hannu yana share mata hawayen da kanshi yana jan tsaki yayi ma motar key..

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba! yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Wanna page din naku ne masoyana a duk inda kuke🫂*

*11-20*

*UKRAINE🥀*
*Wacece Hauwa'u Abdullah jibir (Beauter)*

Sunana Hauwa'u Abdullah jibir kamar yanda na gaya maku,asilina yar Nigeria ce a jahar Zamfara muna zaune a cikin birnin gusau .unguwar tunda wada unguwace wanda ta hada mutane kala kala tun daga kan tallakawa tsaka tsakiya da kuma masu arziki.

A unguwarmu mahaifina ba'a kiranshi mai arziki kuma ba'a kiranshi tallaka tsaka tsikiya dai ,kuma yana cikin wanda suke fada aji a cikin unguwa. dan mahaifina shi mutumin ne wanda bai da wasa ko kadan a wajen bada tarbiya! ba ruwanshi da bashi bane ya haifeka ba idan har yaro ya aikata ba daidai ba har gida zaije ya hukunta yaron dai dai laifinshi.

Shiyasa kowa ke bashi girma a unguwar dan ya dauki ragamar unguwar ya daura ma kanshi,dan kuwa yaran da ya dauki nauyin karatunsu a unguwarmu yawa ne da su tun daga kan boko har isilamiya,dan ko abinci za'ayi ayi a gidanmu ba a dafashi dai dai cikin yan gida,dan gidanmu gidan mutane ne kullun cikin shigo mana ake dan baka raba gidan da mutane haka gidan yake.

Gidan mu babban gida ne kuma ginin zamani ne mai tsikiya babban parlo ne mai dauke da dakuna hudu ko wane daki yana da bathroom sai kitchen da store sai kuma toilet din tsakar gida,da kuma filin da mota daya zuwa biyu zasu samu masauki.

Mu goma ne mamarmu ta haifa maza biyar mata biyar, Muhammad ne babba sai Fatima sai Bishir sai Hauwa'u sai Sulaiman sai Aminatu sai Humaid sai Saddiqa sai Usman sai kuma Auta Rukayya...mun taso cikin gata da kuma kulawa dan babu abunda muka nema muka rasa a rayuwa duk da muna da yawa gidanmu,amman hakan bai sa muka taso cikin rashin tarbiya ba ko kuma rashin mutunta na sama da damu.

Daman na gaya maku Babanmu bai da sauki a wajen tarbiya shiyasa bamu taso mararsa ji ba a unguwa dan bai barinmu muna fita bama kamar mu matan idan har kaga mun fito waje bai wuce dayan biyu isilamiya zamu ko kuma boko!abunda ke fidda damu waje kenan,kuma bai cika barin muna hudda ko wasu kawaye ba,bama mu mata ba hatta suma mazan bai basu wannan damar ba,balle kuma mu mata da daman koda yaushe muna gida ,kuma a gidan ba zaman banza muke ba,idan bamu karatu to muna taya Mama aikin gida,idan kuma ba aikin gida muna kan keken muna koyan dinki da yake Mama taila ce ta iya dinki sosai,amman ba kowa take ma wa ba daga mu sai yaran yan uwanta mu kenan take ma wa ,da tana sana'ar dinkin sosai tunda aka taba yin dambe a gidanmu akan dinki daga ranar ya hana yace andaina yi mashi wannan sana'ar a gida sai dai a chanza wata.

Ba yanda Mama batayi dashi ba wajen bashi hakuri amman fir!yaki yarda yace ya gama magana sana'ar dinki dai ba'a gidanshi ba,dan ba zai zuba ba ido ba yana ji yana gani a maida mashi gida madaldalar fadace fadace,tun tana bashi hakuri akan ya barta har tazo da ta hakura ta koma sana'ar takalmi da jikkuna.

Gidanmu gidan boko ne haka ma isilamiyar duka anayi dan Baba yana da ra'ayin baiyi ma yaranshi aure har sai sun kammala karatu,shiyasa ma bai ba matansan unguwar fuska fara zuwa zance wajen yaranshi ba,bai kuma yarda da zance ba a kofar gida bai kuma lamince ka fara tsada yarinyarshi ba, ba tare da ka aiko manyanka sun nema maka izinin nema ba.wannan shine ra'ayin shi akan yaranshi mata.

Cikin sa'a mu ukku mata muka taso kai daya duk da ba aji daya muke a makaranta ba,amman tare muka taso kanmu daya Yaya Teemarh sai ni ana ceman Jidda ko Kulu sai kuma Meenat,haka muka taso kanmu daya dan banbanci kadan ne,Yaya Teemarh tana 400l ni kuma ina 300l sai Meenat tana 200l a nan FUG.

Ko wane da course din da yake karanta dan ba faculty dinmu daya ba, Teemarh tana humanities sai ni ina polic science sai kuma Meenat tana low shiyasa tafiyarmu take da banbanci kowa da lokacin da yake tafiya.

Tunda na taso samari sukayi man ca!kowa ka gani yazo gidanmu sai yace ni yake so da yake daman nafi duka yan gidanmu kyau bani kama da kowa sai dai kamar jini amman komai nawa daban yake akan rasa wa na biyo a cikin dangin Baba da Mama nidai gani nan kama ta daban da ta kawo..ni kuma tunda Allah yasa na taso bani kula kowa duk wanda zaice yana sona to yayi aikin banza har da wofi ma dan kayi ka gama ka kama gabanta ba lokacinka zanyi ba.

Yau tunda na tashi na fara shirin zuwa school dan muna da lecture 8,shiyasa tunda na tashi asuba ban koma bacci ba dan nasan halin Wasila da shigen nacin bala'i dan da na kuskure na ja mana makara ta dunga mita kenan har sai na bani da mitarta... shiryawa nayi cikin wata atamfa purple dinkin riga da siket ni na dinka kayana da kaina dan gidanmu ba wanda bai iya dinki ba sai dai idan baka sa kanka koya ba,size bag dina na dauka na fito parlo na tadda Mama tana hada ma Baba break zama nayi Ina cewa.."Mama Ina kwana." Kallona tayi fuskarta dauke da murmushi tace.."lafiya lau Kulu,fatan dai babu wata matsala dai ko.?"

Girgiza kai nayi na tashi na hada tea na dauki bread Ina cewa.."babu sai dai kudin hannuna sun kusa karewa fa." Murmushi tayi tana cewa."Kulu ba dai kashe kudi ba,ai Babanki bai Kai da fita ba idan ya fito sai ki gaya mashi,amman duka duka yaushe Babanku ya baki duba biyar har kin kusa ganin bayanta?kuma bayan na hanaku yawan kashe kudi kamar ba gobe."

Turo baki gaba nayi Ina cewa.."amman Mama ai nayi kokari yau fa sati da bani 5k din da kike magana,kinga dai kudin naped kanshi ya karu ga kuma handout banda abinci ai Ina ma yin maleji sosai gaskiya nidai." Har zatayi magana Baba ya fito yana cewa."sai kuta yin addua Allah ya kara budi,ya bude hanyar samu sai ai ta baku yanzun bayan kudin babu wata matsalar ko.?" Dariya nayi Ina kurbe shayi nace.."Allah ya barmana kai Babanmu,Babanmu maganin kukanmu." Dakuwa yayi man yana murmushi yace.

"Ai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,nidai fatana Allah yayi maku albarka ya kuma kareku da kariyarsa ya bani hanyar da zan baku halak malak."
Dan marairaice fuska nayi Ina cewa.."Allah dai ya kara maka tsawon rai Baba,banda wata matsala bayan ta kudin." Da Amin ya ansa yana cigaba da yin break dinshi na rigashi tashi,dakatar da ni yayi yana cewa.."tsaya na dauko maki kudin ko Jiddo." Murmushi nayi kawai Ina ce ma Mama."yau mai zaku girka mana da rana.?"harararta tayi tana cewa.."abunda kika nemo kika bamu mijina." Dirdira kafafu nayi Ina cewa.."wayyo Allah Mama daga tambaya." Itama yin yanda nayi maganar tayi tana cewa.."wayyo Kulu daga baki ansa." A tare mukayi dariya Ina rungumai bayanta nace.."inasonki Mama sosai,Allah yasa ki gama da duniya lafiya." Lakutar man hanci tayi tana cewa.."Nima inasonku Kullu,Allah yayi maku albarka keda yan'uwanki baki daya,ya kareku da karewarshi."

Fitowa Baba yayi yana cewa.."to masoya kun fara ko?yanzun zaku fara nunaman banbanci." Rufe baki nayi Ina cewa.."ai bamu Isa ba Baba kaima ai kasan kaine mai babbar fada a birnin Zuciyar Hauwa'u Kullu Jidda Abdullah jibir."murmushi kawai yayi yana girgiza kai ya mikoman kudi yace.."gasu nan sai a jallallauta kinji Kakata Kinga dai Baban nan naki ba kudi ne dashi ba." Ansa nayi Ina lissafawa naira dubu goma ne murmushi nayi nace.."nagode Babana Allah ya Kara bude ya Kara tsawon rai,Ina kaunarka Babana." Murmushi yayi yana cewa."ki kula kinji Kakata ,Allah yayi maku albarka." Da Amin na ansa na fito waje Ina duba time dan nasan halin Wasila ila tana kofar gida tana jira sai cika take tana batsewa.

Koda na fito cikin sa'a ban tadda Wasila ba tsaya sai na sauke ajiyar zuciya Ina mai nufar gidansu da yake unguwarmu d'aya,duk da ba jikin gidanmu gidansu yake ba amman tafiya kadan zakayi ka iso gidansu daga gidanmu.

Kafin na ida Isa gidansu Wasila ta fito tana kama baki tana cewa.."A'a yau kuwa za'ayi ruwa har da kankara Hauwa kice da kanki?." Murmushi nayi Ina cewa.."ya son ran yanmatan zuciyarki?ai nayi fushi nima ba zaki kara jirana ba sai dai ni na dunga jiranki daga yau dan na gaji da gorin da ake man kusan kullun." Dariya tayi tana kallona sai kuma tace..."tabbb mu gani kasa ke din? da dai baki dan banzan bacci dai,amman na baki kwana biyu kadai kafin angulu ta koma gidanta na tsamiya."daure fuska nayi Ina cewa.."wato haka ma kika ce ko.?" murmushi tayi tana yin gaba tace."eh ke din ai halinki na sani shiyasa." Bin bayanta nayi Ina cewa.."ni din dai ko.?"Daga man kai tayi tana cewa.."eh." Shikenan ni kuwa in shaa Allah sai na baki mamaki yanmata." Dariya kawai tayi muka cigaba da tafiya har muka iso bakin titi,muna isowa Yaya Auwal ya tsaya gabanmu da mota yana zuge glass din motarshi yace.."Jidda sai Ina da safenan sarauniyar mata.?" Dan karamin tsaki nayi Ina dan yin murmushi nace."Ina kwana." Da yake Ina dan jin nauyinshin abokin Yaya Muhammad ne tare sukayi karatu sai dai shi Yaya Muhammad yana ingila can yake karatun likita ya samu scholarship,amman duk tare suka taso a cikin unguwa.

Kureni da Ido yayi yana cewa.."lafiya qlau yanmata nace Ina zuwa kuma.?" Ya sake maimata tambayar dan kallon Wasila nayi da ta maida hankalinta kan wayarta,dan gyara tsiyuwa nayi Ina gyara hijab dina dan kallonshi ya fara takura ni,na tsani kallo shi kuma al'adarshi kenan kallon tsiya da kurulla,cewa nayi.."makaranta." Fitowa yayi yana cewa.."ok ku taho na saukeku mana tunda nima hanyar nayi." Girgiza kai nayi Ina cewa."mungode Allah ya bar zuminci,amman ka barshi." Ba yanda baiyi da mu ba amman muka ki shiga sai dai ya dauko dubu biyu ya bamu yace mun hau naped anjima munyi waya sannan ya wuce,yana wucewa muka tari naped muka gaya mashi inda zai kaimu.

Koda muka isa school samun waje mukayi muka zauna sannan na fiddo dubu d'aya na bata nace.,"gashi ki kara cikin kudinki." Ansa tayi tana cewa."nagode,amman Ina mamaki nikam dai."kallonta nayi ina cewa.."mamaki kuma?mamakin Mai.?" Dan murmushi tayi tana cewa."Ina mamakin yanda kike ma masoyanki abunda kika gadama Hauwa,ki gode ma Allah ke kina da samarin ma,ki godema Allah ke kina da masu sonki ma Hauwa,mu kuwa nan mun rasa masoya ba dan bamu da kyau ba kuma ba dan bamu da farinjini ba,kawai dai haka kaddararta take,amman ke kin samu kina dasu maimakon ki kama su ki rike amman sai ki kama yi masu rikon sakainai kasa,haba Hauwa wallahi banjin dadin haka."

Dan shuru tayi tana cigaba da cewa..,"kuma ni Hauwa banga aibun Auwal ba,Auwal Kinga dai yana da ilimi kuma yana da aikin yi ga kuma kasuwa har da gidan kanshi ya mallaka ke harda motar nan dai ta zamani yana da ita banga makusar Auwal ba da har zaki ringa nuna mashi baki sonshi."

Dafa ta nayi Ina cewa.."komai kika lissafo akan Auwal gaskiya ne,tabbas Auwal baida makusa kuma Auwal mutumin kirki ne sai dai kinsan shi so ba ruwanshi da mai mutum ya mallaka kuma ba ruwanshi da kyau ko na saba,nidai kawai ban sonshi nayi nayi na saka sonshi a raina na kasa Wasi."

Dan Jim tayi sai kuma tace.."kema kinyi magana Hauwa,amman dan Allah ki daina yi mashi abunda kike mashi,ki dan dunga kulashi kina Addu'a sannu a hankali idan da rabon da shi za'ayi sai kiga kun sasanta."

Nidai ban sake ce mata komai ba,dan ni abunda na sani bani sonshi amman zan dunga kulashi ko dan na faranta ma kawata Wasi rai,dan nasan Wasi tana sona kuma tana son cigabana ,zaman tsakani ga Allah muke da ita,babu bakincikin balle maku hassada,bata boyeman komai nata kamar yanda nima bani boye mata komai nawa,Ina sonta kamar yanda take sona itama,kuma tafi karfin komai a wajena,dan furzar da iskan bakina nayi Ina cewa

"In shaa Allah zanyi yanda kika ce Wasi,Allah dai ya zaba mana abunda yafi alkhari,Allah ya bamu mazaje na gari wanda zasu somu ba dan wani abu na jikinmu ba."murmushi tayi tana cewa.."Amin ya Allah,ai ni duniyar nan tsoro take bani Hauwa,lamarin mazan ne babu tabbas dan rabin mazan yanzun ba dan Allah suke zuwa ba da wata manufa ta daban suke zuwa,abun dai sai dai addua kawai itace gaba."

"Hakane kuma Allah dai ya zab'a mana na kwarai." Da Amin ta ansa nan lecturer ya shigo mukayi lecture sanann mukaje entery muka samu abunda muka sakama cikinmu sannan muka dawo muka sake daukar wata lecture din sanann muka nufo hanyar gida.

Koda na koma gida,taddawa nayi anyi abinci ban tsaya yin komai ba na fada wanka dan wani irin zafi ake kwalawa a gusau a ranar, gashi kuma ni ba ma'abociyar son zafi bace fada nike dashi sosai,ina fitowa wanka na samu wata halfgown na saka na saka hula na fito parlo.

Zaune suke su dukansu a parlo ana kallon fastx duk sun natsu dan tsaki na danja kadan Ina wucewa kitchen dan ni haushi suka bani yanda suka natsu suna kallon film din da babu abunda ake yi a cikinshi sai zallar karya wanda hankali baya dauka,su kuma har burgesu karyar take,abinci na zubo na dauko purewater daya na dawo parlorn samun waje nayi na zauna Ina kallonsu nace.

"Dan Allah dubi yanda kuka natsu sai kace bitar karatu ake maku,maiye dadin kallo ga karya dan Allah nidai ku chanza mana channel ku maida mana African action na tabbata suna can suna dafama recipe mai dadi ko kuma gaskiya plus." Na ida maganar Ina sunburo baki.

Dakuwa Yaya Bash yayi man yana cewa.."gidanku nace Jidda kinji,yaushe muka zama abokinki.?kwabe mashi fuska nayi Ina marairaicewa dan nasan halin yan kayana bai da sauki watarana kuma yafi ruwan sanyi , sanyi dan ba Koda yaushe ake wasa dashi ba tuni ya gama karatu shi dan ya riga Yaya Teemarh ta shiga university shi yanzun haka aiki yake a gidan nepa.

Maida kallona wajen Mama nayi Ina turo baki gaba nace.."Mamana kiyi masu magana a chanza mana wanann film din ni baiyi man kyau ba,kuma Kinga fa ina koyan girki a African action fa,kuma time din da zasu saka yayi."

Dukansu zuba ma Mama Ido sukayi suga mai zatace ,dan tama fisu son kallon fastx din tunda akace ya fito take maganarshi ayi download a kalla dan mu gidanmu fast and fesbriou baya wucesu,da an saki suke kallo har da Baba shima kallo yake dan suna son film din sosai,saboda yanda suke rairen motoci shine yake daukar hankalinsu a kallon film din.

Kallon Sule Mama tayi tana cewa.."Sule mai da mata ta kalli African action din tana gama kallon recipe's din tunda mu nan a cikin flash yake da ta gama sai mu maida mu cigaba daga inda muka tsaya."

"Daman nasan Allah cewa Mama zatayi a maida mata ,bayan kuma muma muna son kallon fastx dina fa Mama,kuma ya dauko dadin kallo dan Allah Yaya Jidda kiyi hakuri ki barmana mu kalla anjima sai ki bi maimaici haba please mana." Cewar Humaid yana yin fuskar tausayi,harararshi nayi zanyi magana Yaya Bash ya tsadani yana cewa.

"Idan har kika kuskura na taso sai ranki yayi bala'in b'aci Jidda,ya za'ayi kin taddamu muna kallo kice ke sai an Kai maki wani waje?haka ake rayuwa nifa banson son zuciya fa."

Kasa nayi da kaina bance mashi komai ba,sai dai har na fara tara hawaye,ni a dole sai an Kai man African action kuma nasan sun fini gaskiya kawai fastx din ne bani son kallo kuma,banji zan iya zaman daki ba saboda kallon da suke gyran murya Mama tayi tana cewa.

"Yanzun har ni zance a maida mata inda take so Ku tsaya fadin abunda ke ranku ko?kenan ban Isa da ku ba?ban Isa nace eh ba ta zauna ko?ku dukanku nagode tunda ban Isa ba bari na barku kuyi abunda kuke so,tunda yar'uwarku bata da alfarma a wajenku har da ke Teemarh da kuma Bash a matsayinku na manya a wajen nan,amman Kai Bash kama fi kowa nuna rashin amincewarka a umirnin da na bada duk nagode."

Tasowa Yaya Bash yayi ya tsuguna a gaban Mama yana kamo hannunta yana cewa.."Dan Allah Mama ki yafemana amman wallahi banyi haka dan bijirewa umirninki ba,nayi haka dan na nuna mata kuskurenta amman kiyi hakuri haka ba zata sake faruwa ba in shaa Allah Mamana,dan Allah ki daina fushin nan kin san dai inasonki kice rayuwata ban son naganki a cikin fushi Mamana."

Shafa kanshi Mama tayi tana murmushi,mu duka ta kalla a parlorn tana cewa."ku dukanku Ina sonku Ina kaunarku kuma ba wanda na fiso a cikinku dukanku so iri daya da kauna daya nike maku,Ina jinku har cikin raina yarana,Inason ku hada kanku ku mazo tsintsiya madaurinki daya,Inason ku so junanku wanda son zai kai ku sadaurkawa dan farincikin dayanku." Dan shuru tayi ta maida numfashi sannan ta cigaba da cewa.."Ina da dalili da yasa nace a maida mata ,naga mu namu kallon yana a flash.ita ko nata sai ta kunna stalitile sannan idan kuma ya wuce tayi missing dan bai zama dole tana gida ba sanda zasu maimaita kuma gashi abu mai amfani zata kalla tana karuwa sosai da kallon recipes din da suke nasan nan gaba zasuyi mata rana."

"Hakane Mama muma munsan ai kina sonmu kuma baki nuna mana banbanci daga ke har Baba,tabbas munyi dacen iyayen Allah ya Kara maku tsawon rai da lafiya mai amfani,mu da muke manya Allah ya Kara bude mana mu taimaki kannenmu da kuma iyayen da yanuwa da mabukata." Cewar Teemarh da Amin muka ansa mu dukanmu sanann kuma aka maida mana African action,cikin ikon Allah muna zuwa muka tadda ana girke girke nan muka natsu Muna kallo.

Inason kallon tashar saboda Ina karuwa da abubuwa da yawa,bama kamar wajen recipe wani abun

Please Login or Register in order to submit comment