Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Auwal kofar gidansu Wasi shiga nayi baya Ina gaidashi yayi man ya karatu nace Alhmdulh can ta fito ya kaimu school dawowarmu kenan kuma na kwanta ina ramuwar baccin da banyi ba daman ma exams din tayi dadi sosai ba abunda ban sani ba a questions din da aka fiddo.

Ban tashi daga bacci ba sai wajen karfe hudu Ina tashi naga tarin miscall din Yaya Haidar ya kusa kai goma.. murmushi kawai nayi dan nasan zai kirani ya hanani bacci shiyasa na maida wayar silent wanka nayi nayi sallah sanann na shirya na fito parlo abinci na zauna naci na koshi sannan na koma na wanke bakina na saka hijab.

Zaune na tadda Mama a parlo nan nike ce mata na wuce Allah ya tsare tayi man da na kula da kaina to nace mata Ina ida ficewa tsaye na tadda Wasi kofar gida tana waya.

Wucewa kawai mukayi da yake wajen tela dinmu zamu da kafafu ma zuwa ake tunda ba wani nisa garemu sosai dashi ba ,in minutes muka isa shagon tela din muna tafiya muna firarmu bayan mun gaisa ya bamu dinkinmu muka ida bashi balance dinshi sanann muka jiyo nan ma bamu wani dad'e ba muka iso dan Ina cikin parlon gidanmu Ina nuna ma su dunkuna aka kira sallar mangariba bayan sun gama gani na kwashi kayana na shige dasu.

Bayan na gama sallah na koma saman gado muka fara waya da Yaya bayan ya gama yi man ya exams da tambayar fatan exams din tayi dadi Ina nashi ansa bamu ajiye wayar ba sai da aka kira sallah sannan na tashi nayi alwallah nayi sallar isha'i Ina gamawa na fito parlo nayi dinner sannan na koma muka cigaba da wayarmu true out ranar banyi karatu ba Ina hutawa da yake saura daya mu gama kuma mun samu two days interval.

Washe gari Yaya Auwal yazo ya daukemu ya kaimu wani studio akayi mana makeup muka wuce wani kuma akayi mana pictures din guarantee hadda gown sai da yazo mana da ita bama musan ya dinka mana ita ba.

Bayan yan gama muka dawo gida ban tsaya wasa ba na dauko course din da zamuyi gobe na fara revision din shi daman already na karantashi ,sai karfe biyun dare na kwanta ban dad'e da kwanciya ba Yaya ya tadani karfe hudu sallah nayi na dan k'ara dubawa bayan na gama sallah Ina cikin karatun lokacin sallah yayi.


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*111-120*

Bayan na gama sallah na bude data ta na dan duba whatsapp nan naga Wasi ta turoman pictures din da akayi mana jiya,duba pictures din nayi naga muyi kyau sosai ba wanda bamuyi kyau ta bayan nagama yi mata godiya nayi ma Yaya Haidar forwarded dinsu da su Yaya Teemarh ya Muhd da dai duka yan gidanmu masu yin whatsapp harda freind dina mata na primary dana unguwa da kuma yan course mate dinmu.

Bayan na gama tura masu na kashe data na na dan kwanta dan baki d'aya ni jina nike wani iri duk da Ina cikin farinciki yau zan kammala karatuna na degree amman lokaci lokaci Ina jin gaba na faduwa tun jiya Koda na gaya ma Wasi cewa tayi naita inalillahi karda na sama kaina damuwa..ko yanzun da na gama shiryawa na fito parlo danyi breakfast na dan k'ara duba karatuna da yake sai 2pm muke da exams din again gabana faduwa kawai yake.

Daurewa kawai nayi Ina bin kowa da Ido yana ta rayuwarshi hankali kwance cikin walwala..ni kuwa tawa zuciyar bansan abunda ya samaita ba sai karaya take kuma ba abunda akayi man ba fad'a nayi da Yaya ba balle ba abunda aka man ban ma kowa laifi ba amman sai faduwa gaba nike fama dashi tun jiya.

Jin karatun ya fice a raina yasa na ture littafin gefe muka cigaba da fira da su Yaya Bash da yake kowa na gida banda Yaya Teemarh da take gidan miji,ita kuma Meenat bata da exams sai next week dan wani irin interval suke samu a wannan semester din.

Kallonsu ina murmushi na kamo hannun Autarmu Rukky nace.."inasonki Rukky." Murmushi Rukky tayi tana jan kumatuna tace.."Nima Ina kaunarki Yaya Jiddarh." Dariya akayi duka parlon sai kowa ya koma yana cewa inasonki wance haka muka kama Mama sai dariya take mana sai a lokacin na danji saukin faduwar gaban da nike fama da ita,suma sunji dadi da sukaga na sake na koma kamar yanda nike a da dan na gaya masu faduwar gaba nike ji tun jiya,suma addu'a sukace nayi karfe Sha biyun rana Yaya Bash yace na tashi na koma room dinmu na dan k'ara duba karatuna kafin one tayi sai na fara shirin tafiya school din.

Tashi nayi banyi mashi gardama ba duk da banso ba,naso ya barni a karasa firar dani sanin hali yasa na mike cikin mutunci da sallama na shige room dinmu Ina shiga na dauko waya na kira Yaya haka kawai naji inason jin muryarshi dan tunda mukayi waya da asuba bamu sake ba,sai dai munyi chating da na tura mashi pictures din da mukayo jiya nida Wasi.

Sau biyu Ina karanshi bai dauka ba nasan bai kusa ko yana theater ila ya bar wayar a office cigaba nayi da kallon peper ban dan ina ganewa ba haka dai nai ta dubawa har lokacin sallah yayi nayi sallah na kuma yi wanka na shirya fitowa nayi na dan zuba jallop rice din kadan sai uban salad da na zuba mai yawa na kuma Kara bama a sama ma zauna na cinye duka nasha zobo sannan naje nace ma Mama ma tafi.

Har gida na tadda Wasi muka gaisa da Mami sannan ta saka hijab dinta muka tafi yau Yaya Auwal bai samu damar zuwa kaimu ba saboda wani aiki da aka tureshi a lagos a wajen aikinsu.

Cikin ikon Allah sanda Daya da minti hamsin zatayi muna cikin exams hall,kowa ka kalla fuskarshi kumshe take annuri banda ni da yanzun naji gabana ya dawo da faduwa faye da ma sai da na dafe kirjin Ina inalillahi idan ta lafa na cigaba da karatuna.

Biyu daidai invigilator suka shigo nan aka fara raba answer sheet muka fara last exams Alhmdulh duk da ba wani karatun natse nayi ma course din ba saboda yanayin da nike ciki ya ansa duka da yake answer three questions ne cikin question biyar na samu masu sauki wanda na iya nayi answering three hour ne da yake three credit unit ne course bamu fito ba exmas ba sai 5pm.

Har mun dauki hanya nace ma Wasi ta fara zuwa mosques muyi sallah sannan karda mu had'a sallah tunda dai biyar tayi,duk da ta gaji haka ta biye man bata yi man gardama ba muka wuce massalaci makuyi sallah bayan mun gama muka fito nan muka rasa naped ganin babu naped a cikin makaranta muka fara takawa da kafafunmu dan zuwa bakin gate ko zamu samu.

Muna cikin tafiya munyi rabin tafiya dan da nisa daga bakin gate zuwa cikin makaranta gashi daman marece yayi babu mutane sosai a school daman makarantar a wajen garin gusau take.

Kallon Wasi nayi Ina cewa .

"Wasi."

Kallona tayi tana.."Na'am nasan kin gaji dan k'ara hakuri madam ai mun kusa isowa."

Murmushi nayi Ina girgiza mata kai nace.."ba wanann ba Wasi har yanzun ji nike kamar wani abu marar kyau zai faru dani dan har yanzun gabana faduwa yake man."

Dafani tayi muna cigaba da tafiya tace.."haba mana Jiddarh ki bar cewa haka in shaa Allah ba abunda zai faru dake sai alkhari ki ma bar sama ranki haka please kiyi ta inalillahi."

Lumshe Ido kawai nayi ban sake ce mata komai ba sai kuma can nace.."gashi na baro wayata gida,nasan Yaya Haidar nacan yana ta kirana." Murmushi tayi tana cewa.."iyayen soyayya ai dai angama karatun yanzun sai ayi aure ayi mai dalili." Nidai murmushi kawai nayi mata,mun fito cikin makarantar da yake ba'a tsayawa a bakin gate shiyasa muka dan tafi gefen gate din muka tsaya.

Kamar anyi ruwa an dauke tunda muka tsaya bamu ga naped ba gashi wasa wasa har shidda ta wuce har da minti goma, inalillahi kawai dai muke bama kamar ni da nike jin zuciyata na bugawa da sauri da sauri kamar mai daurewa kawai nike ban sake yi ma Wasi maganar ba.

Muna tsaye wata mota ta taho da gudun bala'i taja burki gabanmu wasu maza ne suka fito daga bayan fuskarsu boye da wani bakin abu sai bindugu a hannunsu baya muka ja muna salati,wani ya kamo hannuna yana wurga ni a cikin mota ya shiga ko gama kulle motar basuyi ba sukayi reverse da ita.

Da gudu Wasi tabi motar tana kuka tana a taimaka mata sun dauke mata yar'uwa hawa saman titi kawai tayi tana zunduma ihu tana an dauke mata yar'uwa..k'ikkkk haka ya taka burki yana gangarawa bakin titi dakyal ya samu ya tsada motar yana fitowa yayi kanta,kamota yayi yana yin gefen titi da ita yana duba gefe da gefe dan har duhu yayi ba kowa a wajen,kallonta yayi yana cewa.

"Ke Wasila lafiya maiyafaru?maikikeyi wajen nan a wannan lokacin.!?"

A tsorace yayi mata tambayar kuka kawai take tana nuna mashi inda motar tayi da hannu ta kasa magana can kuma ta sulale a jikinshi sumai..tsorata yayi yana cewa.."subuhanllh inalillahi wa'innalaihirajiun." Cabcabarta yayi ya saka cikin mota ya tsala titi ya dauko mata jikkunan da ya gani yasha a bakin titi yasan nata ne,yana shiga da gudu ya ba motar wuta ya wuce cikin gari,yana driving yana waigawa baya yana addu'a Allah ya rufa mashi asiri karda yarinyar mutane ta mutu a motarshi.

A faderal hospital Gusau yayi leading da ita ko tsayawa kulle motar baiyi ba bayan ya daukota yayi cikin asibitin da ita,da sauri nurse suka anshesu aka shiga emergency da ita rai hannu ga Allah dan ko numfashi bata yi kallon d'aya zaka yi mata kace babu rai a jikinta.

Tsaye yayi bakin kofa yama rasa mai zaiyi jingina kanshi jikin bango yayi yana addu'ar Allah ya tadi kafad'ar Wasi,tambayar kanshi ya faru ya firgitata har haka? daga gani daga makaranta take to ya akayi ta Kai har dare bata koma gida ba? tsoro ne ya k'ara kamashi Allah yasa ba wani abu akayi mata yaga kuma tana nuna mashi hanyar daji,sauke ajiyar zuciya Alhaji Kabir yayi yana mai kallon nurse da fitowarta kenan daga emergency zata dauko wani abu bin ta yayi yana cewa.

"Nurse ya ake ciki?ya jikin nata ta farfado ko.?"

D'aga mashi kai kawai tayi tana wucewa dan zuwa dauko abunda Dector ya sakata... inalillahi wa'innalaihirajiun" abunda yace kenan dan yama rasa abunda zaiyi sam.

★★

A gida ganin har bakwai na dare ya wuce ban dawo ba Mama ta fara tambayar Meenat tana cewa.."Meenat." Dagowa Meenat tayi tana kallon Mama can tace.."Na'am Mama." Dan shuru Mama tayi tana furzar da iskan bakinta tace.." wai ba Haidar yace karda taje wajen da za'ayi events ba.?" Girgiza kai Meenat tayi tana cewa.."wallahi Mama ba zataje ba kuma ai ba yau suke dinner din ba sai gobe ko jibi kuma nasan ba zasu biye su tsaya yin pictures ba tunda marece yayi kuma Kinga ai ynzun hanyar ba lafiya gareta ba inajin tana gidan su Wasi suna hira ko."

"Maza kira man ita waya ta dawo gida haka nan,haka ake takwai har tayi na dare bata dawo gida ba idan Babanku ya dawo yayi fad'a kenan ko.?"

"Mama ai nan gida ta bar wayarta fa,tun dazun Yaya Haidar ke kiranta da naga kiran yayi yawa sai na dauka nace mashi bata Kai da dawowa ba ya kira Yaya Wasi tunda nasan suna tare shima sai da yayi fad'a duk mai take waje da bata dawo gida ba har yanzun."

Shuru Mama tayi tana yin jigum da ita,ita dai duk hankalinta bai kwanta ba sam kallon Meenat tayi tana cewa.."kiraman Wasilar ki bani ita tunda basu da hankali." Daukar wayarta Meenat tayi ta kira Wasi har sau hudu bata dauka ba ga waya tana ringing amman no answer gaya ma Mama tayi bata dauka tsaki Mama tayi tana cewa.

"Zaki tashi kisa hijab ki duboman ko lafiya ko ni zanje da kaina Aminatu.?"

Itama Meenat duk jikinta yayi sanyi da ta kira Wasi bata dauka ba to lafiya muke kuwa abunda take sakama kanta kenan,a sanyaye ta tashi ta dauko hijab dinta ta shiga gidan su Wasi,Zaune ta tadda Mami ta bugu abun tagumi tasa abinci gaba ta kasa ci bayan ta gaida Mami take ce mata.

"Mami su Yaya Wasi suna cikine.?"Girgiza kai Mami tayi tana cewa.."wallahi nima zaman da nayi kenan ace har taran dare ya kusa Wasila bata shigo gida ba wanann shurun ba na lafiya ba yanzun nike shirin tashi naje gidanku ko tana can ashe kuma Hauwa'u bata dawo ba.?"

D'aga mata kawai kai Meenat tayi tana barin gidan,Koda ta koma gida zaune ta tadda Mama ita da Yaya Bash da Yaya Muhd sai Sulaiman da Manu da Hamid da Saddiqa da Rukky Babane kawai babu a cikinsu.

Tana shigowa duk suka taso suna cewa.." Ina Kulu din take."? K'asa tayi da kanta tana cewa.."Basu gidan su Wasi itama Mami neman Wasilar take tasa ma tana nan gidanmu."

Kamar ya bata gidan su Wasi kira man wayar Wasin Muji suna Ina mararsa hankali kawai."cewar Yaya Bash daman yafi Yaya Muhd zafi shi Yaya Muhd bai dai ce komai ba sai kallonsu da Ido kawai yana kuma saurarensu.

Tsaye tsaye cirko cirko Baba ya iskesu ajiye ledar apple din hannunshi yayi yana kallonsu yace.."ya dai? lafiya naga ganku haka.?"

"Kulu ce har yanzun bata dawo ba."

Agogo Baba ya duba yana cewa.."iKon Allah bata dawo ba?har Tara na dare Mai take yi haka a waje ankirata ne.?"

Girgiza kai Sulaiman yayi yana cewa.."nan gida ta bar wayar tata,kuma anata Kiran wayar Wasi ita kuma No answer."

Zama Baba yayi yana cewa.."a k'ara gwada kiran Wasilar dai mu gani."

Kara trying din number Wasi Meenat tayi sai da ta kusa daukewa sannan aka dauka ana dauka ta mika ma Baba wayar tana cewa.."An dauka Baba." Ansa Baba yayi yana cewa.."Assalamualaikum Wasila kuna ina."? Ansa sallamar Alhaji Kabir yayi yana cewa.."wa'laikumus Salam,Alhaji Abdullahi." Tashi Baba yayi yana cewa.."Aaaha Alhaji Kabir Kaine da kanka Inasu Wasilar suke."? Dan Jim kadan yayi sai kuma yace masu.."yanzun dai muna asibiti." Inalillahi wa'innalaihirajiun wane asibiti." Cewar Baba gaya mashi asibitin Alhaji Kabir yayi yana kashe wayar dan tunda ya kawota bai sake komawa cikin motar ba sai yanzun da ya anfito da ita daga emergency an wuce da ita rest room fuskarta dauke da na'ura mai taima kama mutun wajen yin numfashi wato oxygen.

Kallonsu Baba yayi yana cewa.."Bash Kai da Muhd ku taso mu tafi asibitin muga a wani hali suke ciki,Kai kuma Humaid da su Manu ku zauna ku kula da su Mamarku kafin Allah yayi mana dawowa.".."A'a nima inason na biku Alhaji naga a wani hali suke ciki ko."? Cewar Mama idonta na matsar da kwalla,ganin yanayin da ta ciki yasa Baba baice komai ba sai ma gaba da yayi suka bishi a baya,Meenat kamar ta kurma ihu haka take ji,tana Kallo suka shiga mota suka tafi suka barta.

Dawowa tayi tana mai buga tagumi tana ta hawaye addu'ar samun lafiya tayi mana sannan a matsayinta na babba a wajen ta samu ta lailashi su Saddiqa da Rukky har sukayi dakyal ta samu suka ci abinci har da su Manu ma Humaid ne kawai baice Komai ba sai Meenat da suka gama ta samu sukaje suka kwanta tace su kwanta idan su Mama sun dawo zata taddasu suga yanda nike tasan dani za'a dawo.

★★

A asibiti kuwa Koda su Mama suka Isa Kiran Alhaji Kabir sukayi ya gaya masu word din da suke nan suka nufa jiki a sake bama kamar Mama da Mami dan sai da suka tsaya ta gidan Mama ta shiga ta fito da ita ta gaya mata halin da ake ciki.

Tsaye suka taddashi ya tarbesu ya ida yi masu jagora har dakin da aka kwantar da Wasi,kwance take babu rauni ko digo a jikinta,amman ta firgita sosai wanda har firgita cin ya jefa ta a wani condition marar dadin ji,dan tunda aka kawo ta asabitin sau d'aya ta farfado kuma da sumbatu ta tashi tana fisge na'urar da aka makala mata a hanci ganin haka yasa akayi mata allura akan ba zata farfado ba sai washe gari kuma anan fatan Allah yasa abunda ta gani bai shafi kwakwalwarta ba.

Bayan sun shigo suka samu waje suka tsaitsaya duk da kujerun da ke a dakin,nuna masu kujerar Alhaji Kabir yayi yana cewa.

"Alhaji Abdullahi ga waje ku zauna."

Dan murmushin karfin hali kawai Baba yayi yana ba su Mama umirnin zama duk zama sukayi suna kallon Wasi yanda take bacci daga ganin ba baccin dadi take ba,dan datse shurun yayi yana cewa.

"Wallahi dawowa ta kenan daga sokoto Ina cikin tafiyata naga yarinya saman titi ta nufi mota ta zubga uban ihu,dakyal na samu da taimakon Allah nayi da motar bakin titi wallahi da ace gudu nike da mota ba abunda zai hana ban taka Wasila ba."

Dan shuru yayi sai kuma ya cigaba da cewa.."ni da farko ban gane ta ba,bayan na samu na tsada motata sai na fito duk da a tsorace nike duhu ya fara kuma wajen yanzun bai da kyau ko kadan na rashin tsaro to Ina fitowa sai naga ashe ma yarinyar nan ce Wasila a gidan maraganyi Isihu,kamota nayi Ina tambayar ta lafiya wani waje ta kama nuna man da hannu can kuma ta yanke jiki ta fadi sumaimiya, shine nayo da ita asibiti ban bi ta kan na kira kowa ba saboda a hirgice nike sai naga a fito da ita daga emergency kuma wai na gama waya dakai sai ta farka tana farkawa sai ta fara da ihu tana cewa ko sun dauketa ba dai mu fahimci zancenta likita yayi mata allura fitar likita shigowarku."

Kuka Mama ta fashe dashi tana cewa.."innalillahi wa'innalaihirajiun Allah ya kawo mana dauki kayi mana maganin wanann masifar da take shirin tunkaromu,wallahi Alhaji sun dauke Kulu su waye wa'annan da zasu dauke ta? Mai tayi masu Mai ya tare masu."

Dan Jim Baba yayi sai kuma ya kalleta yace.."yaushe aka ce maki Hauwa'u ce aka dauke Aisha?haka kawai zaki saka mana kuka akan abunda baki da tabbacin faruwarshi?idan ma da gaske dauke Jidda akayi ba sai kiyi mata addu'ar Allah ya tsare ta a duk inda take a matsayinki na mahaifiyarta amman sai ki kama yi mana kuka haka kawai." Kallon Mami yayi da itama kukan take amman ta toshe bakinta da hijab girgiza kai kawai Baba yayi yana cewa.

"Shiyasa tun farko ban niyar zuwa da ku ba abunda na gudu kenan kema kin biye mata Halimatu kina ta kuka haka ake fissabillahi ai addu'a ya dace da kuyi ba wannan ya koken ba."

Su dai basu sake cewa komai ba ya suka cigaba da kukansu shuru Alhaji Kabir yayi sai can kuma yace.

"Wai kana nufin tare suke da yar gidanka Jidda."?

D'aga mashi kai Baba yayi yana cewa.

"Wallahi ko tare suke da yake yau suka gama final din su da marecen nan suka gama ta,shuru shuru basu dawo ba har dai yanzun da mukaji kace kuna asibiti kuma munzo kaga iKon Allah d'aya aka gani ba'a ga d'aya ba, d'ayar ma kaga a yanayin da muka isketa balle mu tambayeta a wani hali kawar tata take."

"Inalillahi wa'innalaihirajiun."

Abunda iya cewa kenan sai kuma ya cigaba da yin addu'a a tare suka dauka kowa yana ta yin kallar tashi..ganin dare nayi Baba yace su tashi su tafi gida sai abar Mama da Mami su kula da Wasi,haka suka tafi jiki sake dan dakyal Yaya Bash ya iya tuka motarsu yana tukawa yana share hawaye har suka iso gida, karfe biyun dare suka dawo gida a lokacin da suka shigo cikin gida zaune suka tadda Meenat da Humaid sai Sulaiman a parlo sun buga abun tagumi sun zararama kofa Ido suna jiran shigowar su Mama.

Suna shigowa suka taso suka taresu a tare suka ce.

"Baba Ina Yaya Kulu din."!?

Kallon su Baba yayi yana kallon yanda suke a tsorace kuma a rude jarumta ya aro ma kanshi yana shafa kan Meenat yace.

"Tana asibiti kuje ku kwanta tana lafiya Mamarku ma na wajenta gobe da safe sai kuje ku gano ta okay."?

Share hawayenta Meenat tayi tana cewa.."to Baba Allah ya bata lafiya..Allah kuma ya kaimu goben lafiya."

Da Amin suka ansa mata sannan tayi masu sai da safe ta shige room Koda ta shiga k'asa kwantawa tayi saman gado sai dai ta shimfidar devut ta kwanta kasa nan ma ba baccin tayi ba cigaba tayi da kuka yanda taga rana haka taga dare.

A bangaren su Baba bayan Meenat ta shiga daki ya samu waje ya zauna yana kallon silin duk abun duniya ya taru yayi mashi yawa,maike shirin faruwa ne su waye suka dauke Jiddarh mai suke nema a wajenshi shi dai bai fad'a da kowa tsakanin shi da mutune sai da mutunci da mutunta juna,ita kuma Jidda Ina ma take zuwa balle har tayi ma wani laifin ko wani abu balle Mama da fita sam bata damaita ba bata gabanta.

Furzar da iskan bakinshi yayi yana kallon su Yaya yace.."kuje ku kwanta munyi magana gobe."

Tashi kawai sukayi basu ce mashi Komai ba Koda suka koma wajensu basu rintse ba Yaya Bash yake cewa.

"Allah ka kawo mana sauki a cikin lamarinmu,ni Yaya lamarin tsoro ya bani kamar wasa ko kuma film ace an dauke mutu anya kuwa Alhaji Kabir yaji yanda Wasila tace sosai kuwa."?

"Nima mamakin da nike kenan Bash,Allah dai ya tsare ta idan ma dauketa akayi Allah ta kare mana ita fatanmu kenan amman Ina cikin jimami da aihini nidai kam lamarin kasar nan ya fara bani tsoro."

"Yaya wai ba'a Yaya Kulu ba."?

Cewar Humaid yana kure su Yaya da Ido, d'aga mashi kai kawai Yaya Bash yayi yana cewa .

"Eh Humaid ba'a ganta ba,amman in shaa Allah duk inda take Allah zai kareta da karewarshi dan addu'a take bukata a wajenmu."

Hawaye kawai suka cigaba da sharewa ba wanda ya sake cewa tak a cikin su har lokacin sallah yayi suna dawowa daga sallah suka wuce asibiti ko cikin gida basu shiga ba balle Meenat tace masu da ita zasu dan sun san target dinta kenan.

Sanda suka isa asibitin a sallamai sallah a massalacin asibitin room din suka shiga da sallama zaune suka taddasu saman abun sallah,kallo d'aya sukayi ma Mama suka gane kwana tayi kuka dan idonunta sun kunbura suyi jawar dasu Koda su Muhd suka gaisheta dakyal suka ji mai tace dan muryarta ta shake ta dakushe.

Samun waje Baba yayi ya zauna yana tambayar jikin Wasi da sauki suka ansa mashi sannan kowa ya kama bakinshi yayi jigum yana kallon Wasi da ke kwance tana bacci kamar gawa.

Wajen karfe shidda da rabi na safe Alhaji Kabir yazo shida matarshi da basket din breakfast,bayan sun gaisa tayi masu ya mai jiki ta kuma yi ma su Mama jaje zuba masu abincin da ta girka tayi tana had'a masu tea din,yanda ta basu ba wanda ya tab'a abincin a cikinsu dakyal ta samu suka sanye tea din da ta hada masu.

Karfe bakwi daidai Wasi ta farka da inalillahi wa'innalaihirajiun ta farka tana salati can ta bude idonta tana k'arema masu kallo,kallon wajen da take tayi da dakin da take sai kuma ta kalli hannunta taga ruwan da aka k'ara mata har an cire shi ma ,kuka ta fashe dashi kawai tana girgiza kanta can tace.

"Inalillahi wa'innalaihirajiun Baba wallahi wasu mutane ne suka saka Jidda mota suka tafi da ita." Kara rushewa kawai tayi da kuka tana daura kanta saman gwuwowinta sai kuka take.

Itama Mama kuka ta rushe dashi tana kama Wasi tace.."Wasila gaya man su waye su?kuma mai tayi masu a Ina suka dauketa."? A jera ta jero mata tambayar tana kuka can kuma ta tafi luuuuu ta zube a wajen,da gudu Manu ya tafi ya kira likita gado aka bata aka saka mata ruwa aka duba ta likita yace karda su damu stress ne kawai amman yayi mata alluran bacci da ta tashi zata tashi normal godiya sukayi mashi kawai.

Bayan fitar likita Baba

Please Login or Register in order to submit comment