Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baka taba ganinshi ba sai kaje tashar zakaga anayi,wani yayi kyaun gani wani kuma sai a slow.

Mun jima a parlo Muna kallo Muna fira sai da lokacin sallah yayi sannan muka tashi dan yin sallah,kafin na fara yin sallar sai da nayi wanka dan Ina sane da Auwal yace zai shigo kuma tunda yace zaizo na kuma nace eh to babu fashi sai ya shigo tunda wannan damar yake nema kenan a wajena dan har Baba yasan yana sona tunda kafin ya tunkareni sai da ya aiko gidanmu aka nema mashi izini a wajen Baba sannan.

Wanka na karayi na dauro alwallah atamfa na fiddo wata marron mai toching din green na saka nayi sallah ,bayan na gama sallah nazauna na fara shiryawa kwaliya nayi dai doi gwargwado poder da kwali dai man baki da na shafa ma lips dina sannan na zauna daurin dan kwali,daman duk gidanmu na fisu iya daurin dankwali har mamaki suke a Ina na koyo,watarana ni ke masu daurin dan kwalin.

Ina cikin yi ya kirani waya ga shi nan a kofar gida,bayan na ajiye wayar na fito parlo Ina cema Saddiqa. "Kije ki shigo da Yaya Auwal yana kofar gida." Tashi tayi tana murmushi tace.."laaa Yaya Jidda ashe yau Yaya Auwal zaizo,shine baki gaya man ba nace ya taho man da doki."murmushi nayi Ina cewa.."Saddiqa kenan,ke damuwarki kenan doki ko.?" D'aga man kai tayi tana cewa."eh Yaya Jidda har da Zaki ma sai mota da jirgi." Lakutar hancinta nayi Ina cewa."karki damu zan sawo maki har da jirgin ruwa ma,je ki shigo dashi." Da gudu ta fita sai tsalle take zan saya mata harda jirgin ruwa.

Koma nayi ciki na dan fasa turare na kara gyara fuskarta sannan na fito,zaune na tadda su a parlo shi da Saddiqa da Rukky sai zuba suke,sai labari Saddiqa take bashi zan sawo mata doki da zaki harda jirgin ruwa dana sama,shi kuwa sai dariya yake yana tayasu Shima zai saya masu har da Yar Baby mai magana ma,amman idan suka kawo mashi na daya a wannan term din nasu,sai murna suke suna cewa zasu kawo mashi kuwa mudun zai saya masu, chocolate ya basu suna godiya suka bar parlon murmushi nayi Ina samun waje na zauna,gaidashi nayi Ina mai mashi sannu da zuwa Meenat ta shigo da abinci da ruwa sai lemu ta ajiye mashi,ta gaidashi ta koma room dinmu,saukowa nayi na zuba mashi abinci da ruwa na koma na zauna Ina mashi bissimllah.

Kallona yayi yana cewa."Gimbiyata ganinki kawai da nayi har naji cikin nawa ya cika babu wajen da wanann abincin zai samu shiga fa."langwabar da Kai gefe nayi Ina cewa.."nidai nidai gaskiya A'a Yaya Auwal sai kaci wanann abincin idan baka san Meenat taji ba dadi,tunda dai ita ta kawo maka bani ba." Kwafe yayi da Ido baice man komai ba,maida kaina kasa nayi Ina wasa da yatsen hannuna,dan jin idonunshi nike suna yawo a jikinta,takurewa nayi waje daya Ina dan turo baki gaba, girgiza kai yayi yana murmushi yace.

"JIDDA."

Dago kaina nayi Ina kallonshi baice komai ba,sai kuma na sauke kaina ina yar'karamar ajiyar zuciya, murmushi ya Kara yi a karo na biyu uana cewa."har ban san wani irin so nike maki ba Jidda,ban san ya zan kwatanta maki son nike maka ba,inasonki Ina kaunarki banda gurin da ya wuce na aureki kice rayuwata,karda ki juyaman baya karda kik'ini ,idan har kika zabi wani na ba bani ba ban san a wani hali zan shiga ba Jidda."

Ruwa ya dan kurbe ya ajiye ya cigaba da cewa.."zan zamai maki bango,zan zamai maki abun alfahari zan kula dake na tairairayaki kamar kwai ko kuma nace kamar tsoka daya a miya,zan baki duk wani jindadi dakike bukata a duniya zan nuna ma duniya kece sarauniyata zan nuna ma duniya cewa kece rayuwata,zan nuna ma duniya cewa kece dai Wanda ba zan iya yin komai ba idan baki a kusa dani,Ina sonki ina kaunarki Jidda."

Magangunanshi sunsa jikina yayi sanyi har ban san mai zance mashi ba,Ina mamakin wani irin so ne haka Yaya Auwal yake man?maiyasa zuciyata,ta kasa amincewa da son wanann bawan Allah?ta kasan ido na kare mashi kallo bai da makusa bai da aibu banga ta inda Allah ya rageshi ba,amman ban san hali ba maybe tana nan za'a ga nak'asun shi,amman dai yana da kyau daidai gwargwado yana da kudi yana da mota yana da kuma gida mai gate ma,ga kuma ilimin boko har da na isilamiya,amman ni ko daya ban jin sonshi a zuciyata ban jin shi ko kadan a raina,ya zanyi da wannan bawan Allah?tambayar da nayi ma kaina kenan, Ina cikin tunanin sai naji yana cewa.

"Jiddarnah."

Again dagowa nayi na kalleshi sai na sakar mashi murmushi Ina cewa."ba iya ruwa nike son ka sha ba,nidai har da abinci gaskiya nike son kaci." Lumshe idonshi yayi yana saukesu a kaina yace.."dagaske fa nike maki sonki ya cika man ciki babu waje a cikinshi." Maida kaina gefe nayi alamun nayi fushi,dan murmushi yayi mai sauti yana cewa.."Ina neman afuwa Gimbiyata zanci kadan yayi ko."? girgiza mashi Kai nayi Ina cewa.."aa baiyi ba,da yawa nike son kaci har sai ka cinye shi inba haka ba nayi maka kuka,kuma ba ruwana dakai."

Saukowa yayi yana zama kasa yace."kina son kenan yau na kwana a gadon asibiti ko.?"Dan kallonshi nayi ,sai nayi kasa da kaina ina cewa."kwana a gadon asibiti kuma Yaya Auwal.?" d'aga man kai yayi yana cewa."kwarai kuma Jidda,zan iya mutuwa ma idan har kika ce zakiyi fushi dani." Murmushi kawai nayi Ina cewa."nidai kaci kawai gaskiya Yaya Auwal." Spoon ya dauka ya fara tsokalar abincin yana ci, ya dan ci sosai sai da naga yaci yafi rabi sanann na hakura ya kyale abincin,goge bakinshi da tissue yayi yana cewa.

"Jidda cikina ya kusa fashewa fah,ga kuma abincin Masha Allah yayi dadi sosai." Murmushi nayi kawai bance mashi Komai ba,Rolex din hannun shi ya duba yana cewa. "Har Tara ta kusa Jidda ,dare nayi tafiya gida zanyi abunka da tuzuru na samu wajen da zan yada kwafaduna,amman Jidda har zan tafi baki ceman komai ba." Cikin muryar tausayi yayi maganar, tabbas Yaya Auwal mutumin ne mai hakuri da kawaici,wannan shine zuwanshi na uku a wajena da sunan zance,kuma duk zuwan da yake ban taba bashi ansar na yarda da soyayyar shi ba,sai dai nai ta yi mashi hanya hanya har ya tafi ,amman bai taba nunaman rashin jindadinshi ba,sai dai kullun ya dunga nunaman soyayyar da yake ma da nuna man girmanta a gareshi,ajiyar zuciya na sauke Ina cewa.

"Gaskiya kam dare yayi Yaya Auwal." Glass din idonshi ya cire yana goge zubar da ta dan kwanta mashi a gefen idon,goge glass din yayi ya maida yace. "Ai nasani dare yayi Jidda,abunda nike ce maki baki ce komai ba." Ni kunyar shi nike ji,dan har ga Allah ba zan iya ce mashi ban sonshi ba Kai tsaye,ba zan iya ba dan Yaya Auwal mutumin kirki ne ga shi kuma abokin Yaya Muhammad,da kunya na kalli tsabar idonshi na gaya mashi bani sonshi ,Ina ba zan iya ba bakina ba zai iya furta mashi wannan kalma mai nauyi haka ba,hakama bakina ba zai iya furta mashi Kalma so ba,dan nasan ko na fada karya nike mashi ba gaskiya bace kuma ni ban san yaudarar mutumin kirki kamar Yaya Auwal,gyara zamana nayi Ina cewa.

*Yanzun aka fara labarin JIDDH, Ina son kuyi man uzuri ku natsu ku karanta labarin BEAUTER ku kuma fahimce shi ku gaya man SANADIN WAYE? Inason ta hanyar comment ku gayaman WAYE SILAR,amman sai kunyi hakuri kun bini a yanda labarin yazo ngd*

*Jama'a ku dunga sayen data fa🤓*

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

Share ✓

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*21-30*

"Yaya Auwal kasan dai komai sai Allah ya nufa dai ko?Ina mana fatan kasancewa tare a inuwar aure idan Allah ya nufa,Allah ya tabbatar mana da alkhari yayi mana zabi na gari."

Shuru yayi yana kallona can kuma ya numfasa yace."Amin ya rabbi Jidda,sai dai kalamanki sun sanyaya man jiki sosai Jidda." Yanda yayi maganar a sanyaye yasa na d'ago Ina kallonshi Kara bani tausayi yayi dan ko bai fada ba jikinshi ya nuna haka,wani irin sone wanann har haka?haka ma bance mashi ban sonshi ba ya zama wani kalar tausayi Ina ga nace ban sonshi?ban san ya zata kasance ba kenan,cewa nayi.

"Kamar ya kenan Yaya Auwal."

Furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa."kamar yanda kika ji Jidda,jikina yana bani kamar baki sona Jidda." Lumshe idona nayi na bude Ina cewa."kamar ya jikina yana baka ban sonka Yaya Auwal."?wannan Karan murmushi yayi yana cewa.."Jidda wallahi idan na rasaki ban san a wani hali zan kasance ba,duk da kinyi magana ta hankali daman zabin Allah dai muke nema,amman Jidda ki sani ni kece zabin da Allah yayi man,Ina fatan watan watarana kema kiji sona a zuciyarki Koda rabin wanda nike maki ne,ke koda kwatan wanda nike maki ne nasan zai ishemu muyi rayuwar aurenmu cikin soyayya har *DA'IMAN ABADAN* "

Dan shuru yayi yana daukar kofin ruwa yasha ,ajiyewa yayi yana tashi tsaye yace."zan tafi gida,zan Kara jandada maki inasonki Ina kaunarki Jiddarh mysoulmate,ki kulaman da kanki Allah yayi maki albarka."

Tashi nima nayi Ina murmushi nace."kaima Allah yayi maka albarka Yaya Auwal,ya baka sa'ar rayuwa ya kare gabanka da bayanka.ya rabaka daga sherin mai sheri." Envelope ya fiddo yana ajiyewa bisa center table din parlo yace." AMIN MATATA,ki sani Ina alfahari dake,Ina son na tuna maki cewa ke haske ce ke Zara ce sai da safe Mysoulmate."

Murmushi kawai nayi bance mashi Komai ba,daga bakin parlo na tsaya nayi mashi sai da safe sannan na dawo ciki, envelope din da ya ajiye na dauka na shige ciki,zaune na tadda su Yaya Teemarh har da Mama suna ta firarsu zama nayi daga gefen Mama Ina ajiye envelope tsakiyarsu ,kallona Meenat tayi tana cewa.

"Yaya Jidda har Yaya Auwal din ya tafi.?"

D'aga mata kai nayi ina cewa."eh ya tafi,yace ince maki yana godiya abinci yayi dadi,Allah yayi maki albarka."murmushi Meenat tayi tana cewa."Allah sarki Yaya Auwal mutumin kirki shi dai bai da matsala."

Murmushi Yaya Teemah tayi tana cewa."tabbas bai da matsala ni ban taba jin ance ga abokin fadan shi ba, sai dai abokin arzikinshi kuma bai da son abun duniya komai nashi a kyauta yake karewa,haka Allah yayi shi yana da son mutane."

Kwarai kuwa Yaya Teemarh wallahi har ban son haduwa da bawan Allah nan a hanya ,Dan kunya nike ji idan ya ganka sai yace dole sai ya kaika idan zaka ,idan kuma kaki shiga sai ya baka nufin naped haduwa goma sai yayi maka haka, shiyasa watarana da na hango motarshi nike boyewa ko kuma na chanza hanya."

Cewar Meenat,sai anan Mama tayi magana tana cewa."Ina ruwan Auwalu,ai shi haka yake ,halinshi ne nima haka yayi man ya ganni na taho yaron nan ya kwafe akan dole sai na shigo ya kawo ni gida,ba yanda banyi dashi ba amman fir!yaki yarda ba yanda na iya sai da na shigo matar nan sanann hankalin yaron nan ya kwanta har kofar gida ya kawo ni ya kuma dauki ledojin da ya daukoni dasu ya shigo man dasu har cikin gida ga kuma sannu da yake ceman sai kace wanda tayi aikin wahala,gaskiya yana da kirki idan har Jidda kika aureshi kinyi dacen miji mai hankali da tarbiya,wanda yasan mutuncin iyayenki da na yan'uwanki irinsu ake son aure ai.

Murmushi kawai nayi Ina cewa."hakane gaskiya kuka fada yana da kirki da halaye masu kyau, ku tayi ni da addu'a idan alkhari ne aurena dashi Allah ya tabbatar ya kuma bamu da zaman lafiya mai daurewa."

Amin Yaya Jiddo,bari muga mai ke a cikin wannan envelope mai muka samu kuma." Cewar Meenat tana bude envelope,kudine yan dubu dubu a ciki,waro Ido tayi tana fiddo da kudin ta fara lissafawa sai da ta gama lissafa kudin ta kalli Yaya Teemarh tana mika mata kudin tana cewa.

"Allah dai ya ida nufi ya kuma saka albarka yasa abokan arzikine."

Da Amin Yaya Teemarh ta ansa tana ansar kudin ta lissafa tana cewa.."A'ah angode Allah ya Kara bude na alkhari,dubu dari ce ya baki Jidda."murmushi nayi Ina tashi nace.."angode duk da kudin sunyi yawa gaskiya,Ina lefen ya bada dubu ashirin nifa ban san saurayi yana kashe man kudi gaskiya duk da ba tambayarshi nayi ba."

"Gaskiya sunyi yawa sai kiyi mashi magana,kice karda ya Kara baki kudi masu yawa irin haka,kuma idan Babanku ya shigo sai a Kai mashi kudin sai Muji yanda zaice akan kudin." Cewar Mama tana saka kudin a cikin envelope suka cigaba da maganar Yaya Auwal,suna ta yabon halinshi suna man fatan aurenshi saboda mutumin kirki ne.

Nidai tashi nayi naje na cire kayan jikina dan sun isheni da dan banzan zafi,haddata breziya sai da na cire na fada toilet na watsa ruwa mai sanyi sosai,dan Ina watsashi ina sauke ajiyar zuciya sai da na gama watsawa na rage cikina sannan na dauro alwallah na fito,rigar bacci na dauko marar nauyi na saka sannan na dauko waya,nan na tadda tarin miscall kusan goma ciki har da na Yaya Auwal,sai da na gyara gadona sannan na kira Yaya Auwal dan misscall uku yayi man.

Bai dauka ba sai da ta zama misscall sannan ya kirani,sai da ta kusa tsinkewa sannan na dauka shuru nayi daga can bangaren yace."Amincin Allah da yardarshi su tabbata a gareki yake rayuwata."

Dan murmushi nayi Ina cewa."tare dakai Yaya Auwal fatan ka isa gida lafiya.?"

"Lafiya lau Alhamdullahi." Dan shuru nayi sai kuma nace.."Allah abun godiya,naga kudi nagode sai dai kudin sunyi yawa sosai gaskiya,mama tace nace maka karka sake kawo kudi masu iyawa irin wannan."

"Shikenan Jidda,amman gani nike ko nawa na baki ban fadi ba kefa ce mahadin rayuwata Jiddarh kece mafarkina kece tunanina Jiddarh kece farincikina Jiddarh,inasonki inasonki inasonki so marar adadi Jiddarh ki yarda dani ki kuma fahimceni wallahi ban dan wani abu nike sonki ba,inasonki dan Allah ne ba dan surarki ko kyaunki ba Ina maki son fissabillahi ne,amman kiba Mama hakuri in shaa Allah za'a kiyaye."

"Allah yasa Yaya Auwal,ya daren fatan yana maka dadi.?" Murmushi ya saki yana cewa."wani dadi Jiddarh?bayan baki a kusa dani,kawai dai ana maleji amman Ina dadi babu masoyiyata a gefena." Murmushi kawai nayi sai kuma nace."ka kira Ina wanka."

"Sarki wanka,ko kuma nace sarkin yan jin zafin gusau ba." Yar dariya nayi Ina cewa.."nidai ba sarkin masu jin zafi gusau bace." Shima dariyar yayi yana cewa.."to naji maiye labari."makale kafad'a nayi Ina cewa." Labari yana wajenka."

"Kin tabbata yana wajena.?"daga mashi Kai nayi kamar yana gabana ban ce komai ba, numfashi ya sakar man a kunne yana cewa."tabbas yana wajena sai dai labarin gizo baya wuce na koki Mysoulmate."

Dan shuru yayi sai kuma ya cigaba da cewa."a kullun sonki Kara karuwa yake a zuciyata,a kullun Kara gina babban gida kike a birnin zuciyata,yanzun haka baki ji yanda nike jin kewarki ba,banki ba gobe ace na dawo naga kyawkyawar fuskar nan taki mai sani natsuwa da manta wanene ni."

Murmushi nayi bance mashi Komai ba,bai damu da shurun da nayi ba dan yasan halina ba cika yawan magana mai tsawo nayi ba,shiyasa ya cigaba da cewa.

"Jidda kin gama mallaka zuciyar Auwalu,kin gama zama sarauniyar zuciyar Auwalu zan zamai maki bawa sai yanda kikayi dani,Ina tabbatar maki da cewa da sonki raina zai bar jikina Jidda."

"Yaya Auwal." Cikin kwatar da murya na ambaci sunanshi,dan kalaman da yake man suna saka man tausayinshi a zuciyata,kuma suna tsoratane ina rasa gane irin son da yake man,Ina ganin son ya girmama har ya wuce misali ma.jin yanda nayi shuru ya sake cewa."Jiddana kin kirani baki ce komai ba,Allah yasa lafiya ba dai wani laifin nayi ba.?"

Numfashi na furzar Ina cewa.."kawai dai ba komai." "Haba Mysoulmate kamar ya ba komai dan Allah gayaman maike damunki.?"Makale kafad'a nayi Ina cewa."Allah ko bakomai Yaya Auwal."

"Kina son yau nayi bacci kuwa Babe.?" Daga mashi Kai nayi kamar yana gabana sai kuma na turo baki Ina cewa.."Ina so mana Yaya Auwal." Furzar da iska yayi yana cewa."to indai kina son nayi bacci to ki gaya man damuwarki idan kuma baki son nayi bacci shikenan sai ki k'i gaya man."

Dan shuru nayi sai kuma nace."Inason kayi bacci zan gaya maka,duk da ba wani abu baine ba wanda zai zama damuwa ba fa." Nidai gaya man ko maiye Ina sauraren ki."

"Ina mamakin irin son da kake man Yayy Auwal har tsoro yake bani." Murmushi yayi yana cewa."sannu a hankali Zaki gane irin son da nike maki yanmatana kawai inason kisa a ranki Ina kaunarki."

Murmushi kawai nayi ban sake ce mashi komai ba,sai shi ya kama zubarshi sai da goma tayi sanann ya hakura ya barni ya kashe wayar ba dan yaso ba,dan na matsa akan bacci gobe Ina da lecture din safe.

Koda na gama waya da Yaya Auwal Ina kallon Ahmad yana kirana ban dauka ba,sai ma maida wayar silent da nayi na kwanciyata ,da yake ni surutu bai hanani bacci ba shiyasa duk wayar da su Yaya Teemarh suke da samarinsu bata hanani bacci ba ,Ina yin Addu'a bacci yayi awon gaba dani ban sake sanin Ina kaina yake ba sai da asuba tayi,shima Mama ta shigo ta taddamu yin sallar.

Kuma Koda nayi sallah komawata bacci nayi ,inajin su Meenat suna ta shirin tafiya school suna da 8,ga kuma shirya ma Saddiqa da Rukky ,duk surutun da suke bai hanani yin bacci na ba,dan ban san tafiyarsu ba,inata bacci na ban tashi ba sai goma na safe Ina tashi na shiga wanka na shirya cikin malarial light blue maikyau na dauki jikkata da gyale na fito parlo.

Zama nayi Ina kallon Baba sai kuma na marairaice fuska Ina cewa."shine jiya baka dawo da wuri ba har nayi bacci ban ganka da dare ba." Matsawa nayi kusa dashi Ina daura kaina a kafad'arshi na cigaba da cewa. "Ina missing dinka Baba,rabona da ganninka tun jiya da safe fa,nai ta jiranka da dare baka dawo ba har nayi bacci."

Murmushi yayi yana shafa kaina yace."Yi hakuri Kakata,aikine ya rikeni nima naso dawowa da wuri dan Ina kewarki,fatan babu wata matsala dai ko." Daga mashi Kai nayi Ina cewa.."babu ,banda matsala ina ma zan samu matsala ina da jarumin mahaifi, mahaifina yafi na kowa." Jan hancina yayi yana cewa.."Ina alfahari dake Jiddo,Allah yayi ma rayuwarku albarka baki dayanku,naga kudin da Auwal ya kawo maki sunyi yawa Jiddo,amman zan mashi magana ya rage kawo maki kudi masu yawa haka." Turo baki nayi Ina tashi na nufi kitchen Ina cewa."nima abunda nace mashi kenan,amman shi da anyi magana sai yace sone ya kawo haka." Da kallo kawai Baba ya bini yana girgiza kai sai kuma yayi murmushi yana tashi ya tafi wajen aiki,Koda na fito zama nayi naci abinci na koshi sannan na leka room din Mama nace mata na wuce school,addua tayi man sannan na fito Ina fitowa Ina hadewa da Wasila murmushi tayi tana cewa.."Allah dai yasa a daure a haka." Hararar wasa nayi mata Ina yin gaba nace."kindai gama ,amman Ina nan kan bakana sai na baki mamaki."dariya tayi tana cewa."Ina fatan haka." Daga nan bamu sake magana ba muka samu naped ta kaimu makaranta muka biyashi kudinshi, sannan muka nufa venue din da za'ayi mana lecture.

bayan mun gama lecture,muka tashi muka fito daga venue din lecture din,kallona Wasila tayi tana cewa."yanzun ina zamu kuma Hauwa?Kinga dai yanzun ba zamu sake shiga wata lecture din ba sai 4-6." dan furzar da iskan bakina nayi ina cewa."Nima wallahi bansan inda zamu ba,tunda dai ba wasu friend gare mu a hostel ba balle muje wajensu kafin time din yayi,Ina muka dosa nidai nan zama nike bukatar yi."

"kodai muje mosque mu zauna,kafin lokacin ya ida yi.?"dan shuru nayi sai kuma nace ."okay muje mosque din zai fi zaman wannan filin Allah." tafiya mukayi munayi muna fira,har muka isa massalacin muka samu gefe daga haraba muka dauko sallaya muka shimfida,zama mukayi Ina ce mata.

"kin san jiya sai da Yaya Auwal yazo gida."murmushi tayi tana cewa."Dan Allah.?"daga mata kai nayi Ina cewa."gaske kin san dai ba zan maki karya ba." fuskarta washe da murmushi tana gyara zama tace."har naji dadi wallahi,labarin yayi man dadi sosai Ina sonki da Yaya Auwal dan mutumin kirki ne gashi da sakin fuska da son mutane."

girgiza kai nayi ina cewa." kuna bani mamaki wallahi,haka jiya gida suka kama maganar yana da kirki yana da mutunci ga sanin girman mutane."dariya tayi tana cewa."kwarai kuwa gaskiya suka gaya maki,wallahi Yaya Auwal mutune har da rabin mutun,amman naga ke kamar baya gabanki sam." lumshe idona nayi Ina budewa sai kuma na saki murmushi Ina ce mata." ba dai bai gabana ba Wasi,kawai dai na kasa jinshi a cikin zuciyata inason na tusa sonshi kamar yanda kowa yake bukata amman wallahi zuciya ta ta kasa bani hadin Kai."

dafani tayi tana cewa."amman Hauwa kodai akwai wanda kike so nikam.!?"a tsorace tayi man tambayar tana kafeni da Ido,nima kallonta nike sai kuma can nayi dariya ina dan kai mata duka nace."wannan wata irin tambaya ce Wasi.?"

d'age gira tayi tana cewa."nifa ba wasa nike maki ba, serious magana dan Allah gaya man wa kike so,ni wallahi zan gaya mashi da kaina kina sonshi,shi kuma Yaya Auwal sai a bashi Meenat dan ba zai jira Saddiqa ba tunda yazun take primary three,ita kuma Yaya Teemarh Kinga an kusa bikinta ma."

bansan lokacin da na rushe da dariya ba,sai da nayi mai isata sannan na tsagaita ina cewa." ko daya ni ba wanda nike so,kawai dai ni har yanzun bani jin sonshi a raina,kuma itama Meenat ai ankawo kudin aurenta sai dai na bashi ke idan ma akwai wanda nike so." zaro Ido tayi waje tana cewa."rufaman asiri ai Yaya Auwal yafi karfina dake ya dace dai,dan Allah Hauwa ki rabu da wa'annan samarin yan karya ,yan soyayyar karya da karyaiyaki ki koma wajen gaskiya,Yaya Auwal dai shine gaskiya ki bashi dama shima ya aiko da kudi Kinga dai mun kusa gama wanann karatun Muna gamawa a saka ranar aure musha biki."

gyara zamana nayi Ina cewa."Wasi ya dace ace kinfi kowa fahimtata sama da yan gidanmu saboda ke kullun muna tare dake, faculty dinmu d'aya haka ma department dinmu daya Kinga kenan muna tare da juna a Koda yaushe,wallahi bani sonshi kuma ban tsaneshi ba wallahi Ina ganin girman shi da mutunci shi na rasa ya zanyi inason nima naga na aureshi dan kawai yanda yan'uwana dake kuke sonshi har da Baba ma,amman na kasa har sallar dare Ina tashi Ina gaya ma Allah ya saka man sonshi a zuciyata idan har alkhari ne ,idan kuma ba alkhari bane ya yi man zabin alkhari nida shi baki daya."

numfasawa tayi tana cewa."Hakan ma yayi,Allah ya zaba mana na gari da zuri'a daiyaba mai albarka." duba time nayi Ina cewa."Amin Amin tashi muyi sallah,mu koma wajen lecture kinga dai lokaci yayi." tashi tayi muka tafi mukayi alwallah bayan munyi sallah muka gyara fuskarmu muka koma wajen lecture,bamu dade da zama ba malamin ya shigo bai tsaya bata lokaci ba yayi mana abunda ya kawoshi da yake business muke karanta ,bai sake mu ba sai wajen 5:40 sannan.

Koda muka fito bamu tsaya wani jiran naped ba,muka fara takawa da kafafunmu dan wajen naped din cike yake da mutane dan har babu naped shiyasa bamu wani tsaya ba,muna cikin tafiya muka ji tsayuwar mota bayan mu bamu wani tsaya ganin waya ba ,horn aka dan yi mana nan ma bamu tsaya ba ji nayi wayata tana ringing ,har ta tsinke ban dauka ba sai da wani kiran ya shigo sannan na duba,dan gimtse fuska nayi Ina kallon Wasi nace.

"Wasi Ahmad ne fah." Dan bata fuska tayi tana cewa."ai tun tsayuwar motar na gane shine,nataice mai kuma yazo ya gaya maki.?" d'age kafad'a nayi Ina cewa."wa ya sanma sakaran!amman bari yau zamuyi ta ta kare nida shi bari ya iso." tabe baki tayi tana cewa."da dai zai fiye maki,ni ba zan tsaya ba dan haka gaba zanyi mun hadu gida."kama hannunta nayi Ina girgiza kai nace."haba Wasi ya zaki barni da wanann dan'iskan!bayan kinsan mugun abun da ake zuciyarshi a

Please Login or Register in order to submit comment