Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi dan harda jigira sai da nayi da yake na iya sosai makeup duk na iya har da kayan makeup din duk ina dasu yine banyi sai dai naita ma yan gidanmu da yan unguwa,amman ba kowa nike mawa ba sai na gadama,harda Jan baki na shafa,kallona Meenat tayi tana girgiza kai tace.

"Dan Allah Yaya Kulu ki goge red gloss din nan da kika shafa." Kallonta nayi Ina cewa."saboda." ", Saboda bai hau da lips dinki ba." Ni dariya ta bani wai bai hau da lips dina ba,daman kenan ba kowa color yake hawa da bakin mutane,kallonta nayi cewa." Maiye dalilinki na cewa bai hau da bakina ba."

"Haba Yaya Kulu kefe bakinki daman can jan bakinki aka haifeki,da Allah ya tashi sai ya baki pitch lips ma,wallahi duk wanda ya kalleki idan bai sanki ba sai yace pitch gloss kika shafa kuma yana kara fiddo da kyaunki sosai,pls Yaya Kulu ki goge kisa lips gloss kawai karda mu ki barshi shi d'aya zaune a parlo."

Girgiza kai kawai nayi Ina goge jan bakin na shafa lips gloss sannan na fito da sallama dauke a bakina.

Murmushi nayi inayin kasa da kaina dan wani irin kallo yake jefeta dashi mai ma'anoni daban daban,shi dai Yaya Auwal ya iya kallon kurila dan lokaci guda yake kalleka tas kafin ka farga da kallon da yake maka har ya gama sai ya nuna shi bai kalleka ba,haka yake da yake ni nasan waye shi a wajen kallo shiyasa da ya fara kallona sai na dunga turo mai baki Ina kwabe fuska sai kawai yayi murmushi ya girgiza kai sai ya sake salon kallon Wanda ba zan gane ba.

Zama nayi Ina cewa.

"Yaya Auwal Ina wuni." Baice komai ba sai ma kureni da Ido da yayi yana murmushi mun kusa 5min a haka sannan yace."kin hadu kinyi kyau Jiddarh komai naki yayi bari na gaya maki wata magana duk da nasan abokan karawata suna gaya maki ita nima zan gaya maki ke full option ce komai yayi,Allah dai ya bani ke a matsayin mata Jiddarh da nafi kowa dace." Murmushi kawai nayi Ina cewa.

"Yaya Auwal."Ina rufe fuskarta Shima murmushin yayi yana cewa "eh fah Jiddarh gaskiya ce na gaya maki kin hadu,fatan na samu Gimbiyata cikin koshin lafiya."?

"Lafiya lau Alhamdullahi,ya kuma kokari."?

"Da godiya Jiddarh myluv."

Murmushi kawai nayi ban sake ce mashi Komai ba,Meenat ce ta shigo da abincin da muka girka mashi tana gaisheshi,ansawa yayi yana jinjina mata murmushi kawai tayi tana bar mana waje,saukowa nayi na fara zuba mashi brown rice din na daura mashi chicken soup din a sama,sanann na ajiye a gabanshi wani plate din na dauko ma zuba bow tea meatballs sake dako cups nayi na zuba mashi mango juice da kuma watermelon lemonade na ajiye gabanshi Ina cewa.

"Sauko kaci abinci Yaya Auwal."

Kallon abincin yayi yana kallona sai kuma ya kalli cikinshi yana cewa."Babe duk a cikina zan duba wannan delicious din."?

Daga mashi Kai nayi Ina murmushi na tashi nace."kwarai kuwa Yaya bari ma na bar maka fili yanda zakaji dadin ci,dan ban yarda a barman saura ba duka za'a cin yeshi."

Shafa cikinshi yayi yana cewa."please Babe karda muyi haka dake, amman wallahi cikina bai anshe wannan kayan dadin ba."

Tashi nayi Ina turo baki nace."nidai ai na gama magana gaskya kuma itace ba chanzi." Inajin yana man magana ban waigo ba na shigewata.room dinmu,girgiza kai kawai yayi ya sauko ya fara cin abincin.

Ban dawo wajenshi ba sai da na bashi 20min sannan na fito Ina kallon plate din ba laifin dan yace ba kamar da ba idan yazo yaki cin abinci sosai,amman yanzun yaci ba laifin dan Brown rice sai da ya yafi rabi sai meatballs shima yaci ya kusa ukku da yake biyar na saka mashi sai ya bar biyu, juices kuma yasha duka bai rage ba har kasan raina naji dadin yanda yaci abincin amamn sai na shagwabe fuska Ina kallon plate din Ina kallonshi na cinno baki nace.

"Nidai nidai gaskiya ban yarda ba sai cinye duka."

Hada hannayenshi yayi waje daya ya langwabar da kanshi gefe yace.."Babe dan Allah ayi man afuwa na cika cikina har ba space idan kuwa na kuskura na k'ara Koda one spoon ne maybe fashewa cikin kawai zaiyi."

Zama nayi bance komai ba Ina ta kallon plate matso hawayen karya nayi Ina cewa.

"Shikenan tunda bakya ci nasan abincin bai maka dadi ba, shiyasa kaki ci."

Rufe baki yayi yana cewa."wallahi abincin nan yayi masifar dadi Babe,dadinshi ya fisgeni har nayi over feeding ban sani ba."

Turo baki kawai nayi ban sake cewa komai ba, murmushi yayi yana cewa."Babe rigima, rigimarki na tafiya dani Jiddarhna,komai naki special ne komai zakiyi sai na ganshi daban da na sauran pls ayi ma Yaya hakuri a bar yi mashi asarar wanann hawayen masu tsada."


Kara turo baki nayi Ina cewa.."yo ba Kai bane." Kama kunne yayi yana cewa.."nasan nine masoyiya,ayi man afuwa ba zan sake ma Rayuwata."

Murmushi kawai nayi ban sake cewa komai na Ina share hawayen,shima murmushin yayi yana lumshe yace.

"Jiddarh."

Dago Kai nayi Ina kallonshi bance komai ba, murmushi ya sakar Mani yana cewa.

"I love you Jiddah,Ina kaunarki sosai Jiddarh Ina fatan ki kasance tare dani har karshen rayuwata,dan kece rayuwata da gasken gaske."

Nan ma murmushi nayi ban ce mashi komai ba, cigaba da gayaman irin son da yake man da yanda yake jina a zuciyarshi,wani wajen na bashi ansa wani wajen kuma nayi.shuru mun dade muna fira sai tara da wani abu na dare sanann ya tashi yana ajiye man wata leda mai kyau a parlo ya tafi a bakin gate na rakashi Ina godiya na jiyo gida,Ina dawowa na dauki ledar na kaima Mama,nan Meenat ta fara fiddo abinda ke cikin ledar.


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or WHATSAPP

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*61-70*


Turaruka ne ciki masu kyau da tsada da kuma sanyaiyen kamshi sun Kai guda goma.fiddosu Meenat tayi tana jerawa d'aya bayan d'aya tana rike baki dan ba karamin kudi Yaya Auwal ya kashe ba wajen turaren dan ba na kasa da dubu dari,rasa abun cewa mukayi mu dukanmu sai dai kallo.

Rasa ta cewa nayi sai dai tashi kawai da nayi jin Mama na cewa Yaya Muhammad sun taso, Meenat ma had'a turarukan tayi waje d'aya tana cewa.."gaskiya Yaya Auwal ya kashe kudi da yawa kusan million daya da rabi ya kashe maki Yaya Kulu, wannan turare sunyi yawa a san dai yanda za'ayi."

Murmushi kawai nidai nayi na cigaba da gyaran parlo,haka ma Mama batayi magana ba sai Yaya Bash yace."zan mashi magana ya bar kashe mata kudi haka da yawa,kashe kudin sunyi yawa mai zatayi da turare har na kusan million biyu?haba mana ai ba'a haka gaskiya wato an hanashi kawo kudi sai ya koma kawo kaya ko?zan mashi magana ya rage ba'a hanashi yi mata kyauta ba,amman yayi wanda hankali zai dauka mana."

Anan Mama tayi magana tana cewa."ya dace dai kam ayi mashi magana,ya rage kashe kudi nan haka gaskiya, yarinyar da ba ma sonshi take ba yake ta yi ma barnar kudi haka,nidai ba ruwana idan Babanku ya dawo yaga wannan turarukan bansan wani irin fad'a zaiyi ba daman ya hana ana ansar mashi Koda naira biyar tunda ba'a tsada rana ba,akan mai zai kashe kudi har haka."?

"Nima abunda na gani kenan Mama,dama ace tana sonshi da sauki amman ita Jiddarh ta fito fili ta gaya mana gaskiyarta Kinga bai dace ba ta dunga ansar mashi abu idan ba son banza bane irin nata na bansani ba."

Turo baki nayi ina kallon Yaya Bash sai kuma nace."amman Yaya Bash ai bance ya kawo man ba ko?kuma sai da nace ban ansa ya ajiye ya tafi ya zanyi dashi?daman ai nema yake dole ya kashe kudi dan ya samu." Kama baki Yaya Bash yayi yana kallona sai da ya gama kallona sannan yace.

"Gaskiya ne Jiddarh kince wani abu,to dan ubanki idan kika cigaba da ansar mashi abu to wallahi sai ki aureshi ko kina so ko baki so,ki rubuta wannan ki ajiye."

Yanda yayi maganar with so serious sai na gama kaina ban yarda na sake cewa komai ba,dan nasan waye Yaya Bash ba sauki bane dashi ga saurin zuciya,nasan ba karamin aikinshi bane ya zuga Baba ya aura man Yaya Auwal ko Ina so kuwa ko ban so,dan Baba yana jin maganar Yaya Bash ,idan suka had'a Kai suna magana sai ka rantse kace mai tsabar yarda da juna da sukayi sun ma zama abokai.

Ina gama gyara parlon na dauko gyale na nabi Yaya Bash zuwa airport dauko Yaya Muhammad,Muna Isa jirginsu na sauka bamu dade ba suka fara saukowa da gudu naje na tareshi Ina cewa.

"Oyoyo Yaya Muhd welcome back." Murmushi yayi yana rikoni ya kalleni yace.."Masha Allah Kulu kice kika koma haka."? murmushi nayi Ina rufe fuskata dan rabon da ya ganni yanfi shekara Tara ta goma ake dan tunda ya tafi karatu bai dawo ba sai da ya gama sanann yau Allah yayi mashi dawowa,jan hancina yayi yana mikama Yaya Bash hannu suna hunging din juna, kallon shi Yaya Bash yayi yana cewa.

"Broth nayi missing dinka sosai da sosai."

Murmushi Yaya Muhd yayi yana cewa.."Nima Bash nayi kewarka har bansan ya zan kwatanta kewarka ba Ina Manu."?

Dariya yayi yana daukar jikarshi muka nufi mota yana cewa.."yana can yana ta tukuburi wai anbarshi ban taho dashi tararka ba."

Girgiza kai yayi yana cewa.."maiyasa baka taho dasu ba dukansu sai ka taho da Kulu kadai."?kallona Yaya Bash yayi yana cewa.."har ka manta wacece Kulu kenan?dan banzan naci ne da ita ka ganta ne,sai da nace ban zuwa da kowa in fito na ganta kofar gida tsaye tana jirana rashin abun ce mata nayi shiyasa kawai na bude mata ta shigo mu wuto karda ta mutu kafin mu dawo."

Dariya suka ansaya su duka Yaya Muhammad na cewa.."ai munyi waya da Haidar yace man gobe zai shigo Gusau sai bayan bikin Teemarh zai koma Birnin kebbi."

"Allah sarki Ina ruwan Yaya Haidar ai Muna gaisawa wani lokacin da yana Japan ni bansan ya dawo kasar ba sai shekaran jiya da naji yana waya da Baba nan nike jin dawowar tashi."

"Haka Haidar yake, nidai Ina rasa kanshi wata sa'in komai ke damunshi oho." Dariya Yaya Bash yayi yana cewa.."ba abunda ke damunshi Yaya Muhd sai dan banzan girman Kai da miskilancin tsiya da yayi mashi katutu a kahon zuci."

Kama baki Yaya Muhd yayi yana kallon Yaya Bash,kama mashi kunne yayi ya a cewa."yanzun Bash Haidar din kake ma wanann bakar shedar."?yar karamar k'ara Yaya Bash yayi yana cire kunnenshi a hannun Yaya Muhd yana turo baki yace." Ash Yaya Muhd zaka cire man kunne daga fadar gaskiya,ai halinshi ne na gaya idan kuma karya nayi mashi ai ga Kulu nan ka tambayeta."

Turo baki nayi gaba ban ce komai ba,daman tunda suka fara zance Haidar nidai bance komai ba,dan nasan halin Yaya Muhd baison laifin Yaya Haidar kuma ai halinshi ne komai Yaya Bash ya fad'a a kanshi bai mashi karya ba maike dawainiya dashi idan ba girma kan ba da miskilancin har da d'agawa dan yaga Babansu yafi kowa kudi a family,amman da yake besty din Yaya Muhd ne gaskya bata faduwa idan ma ka fadeta wahala zaka Sha,shiyasa na je bakina nayi shuru dan ni da zasu bi shawarata da sun chnza chapter dan ni bansan ana maganarshi a gabana baki d'aya.

Hararata Yaya Bash yayi ya mirror yana cewa."kika yi shuru kamar ruwa ya cinye ki,ba zaki fadi gaskiya ba?nace maki Yaya Haidar baida girman Kai ko kuwa."? Turo baki nayi Ina cewa.."to ni Ina ruwana da halinshi Yaya Bash,daman ai kowa yasan waye Yaya Haidar wajen girman kai,ni wallahi da za'abi tawa karda yazo mana gida,ya sauka gidansu tunda dai suna da gida a gusau ko kuma ya sauka a gidan Baba Bishir zaifi mana da yazo mana yana mana wani cize cize sai kace wani sarki dan yaga kawai suna da kudi shine fa."

Kama baki kawai Yaya Muhd yayi yana kallona baice man komai ba,alamu sun nuna na kasheshi da mamaki yanda yake ji da Yaya Haidar ai ko ni ila baiji dani haka,girgiza kai kawai yayi yace.

"Sai dai ke ki bar mashi gidan,amman gobe da safe ma zai durko garin gusau inga ta tsiya." Ban sake cewa komai ba sai dai turo baki da na kama yi ina kallon window,su kuma sai labarin halin Yaya Haidar Yaya Muhd yake ba Yaya Bash dole sai da ya fahimtar dashi yana da kirki sosai d sosai a haka har muka isa gida.

Koda muka isa gida sai ihu suke ga Yaya ga Yaya nidai tunda na sauko komai ban daukar masu ba na shigowata gida,ko parlo ban tsaya ba na shige bedroom dinmu dan sosai suka kaini bango sun wani damu mutane da maganar wani Yaya Haidar sai kace wani shelle.

Koda na shiga room dinmu wanka nayi na shirya cika halfgown na hayewata gado,nayi addu'a dan daman bacci nike ji daman rigima ce tasa ni na bi Yaya Bash daman,har na fara lumshe Ido wayata ta fara ringing dauko ta nayi Ina duba mai Kiran nawa Yaya Auwal ne,dan murmushi nayi daman Ina da niyar kiranshi gobe da safe sai gashi yanzun ya kira bari na dauka naji dalilin da yasa ya kashe kudinshi har haka wajen sawo turarukan nan.

Bayan na dauki wayar shuru nayi bance komai ba, murmushi yayi yana cewa.."Amincin Allah su tabbata a gareki yake sarauniyar mata hasken zuciya Rayuwata." Dan cinno baki nayi Ina cewa."barka da dare."

Murmushi yayi yana cewa.."barkanmu Amaryata,fatan Babban Yaya ya iso lafiya."

"Lafiya lau Alhamdullahi."

"Masha Allah ya shirin biki duk da biki gobe saura kwana ukku ko."?

Daga mashi Kai nayi kamar yana gabana bance mashi Komai ba, cigaba da cewa yayi.."ya zafi har anyi wanka nawa nasan ki da jin zafi Babe."

"Alhamdullahi,Amman nace ba."

"Uhmm!kika ce mai."?

"Yaya Auwal abunda kayi man yau ko kadan baiman dadi ba, fissabillahi Yaya Auwal mai Baba yace maka."

"Subuhanllh Babe wani abun kuma nayi."?

Cinno baki nayi Ina cewa."ai ka fini sanin abunda kayi Yaya Auwal,nidai ba anshi turarukan nan ba gobe zan ba Humaid ya kawo maka gaskiya,tun kafin Baba ya gani yayi man fad'a ma."

Shuru kawai yayi baice komai ba,Nima ban sake cewa komai ba amman da gaske nike ba zan ansa ba,akan mai zan ansa bayan nasan ni har yazun ba sonshi nike ba,ba zan ansa ba gaskiya kam.

Rasa abunda zance yayi kuma alamu sun nuna ranshi ya b'aci sai dai kawai ya furzar da iskan bakinshi yana cewa.

"Ok Babe duk yanda kikayi haka za'ayi,naga kamar kin kwanta bacci bari na barki sai da safe."

Bai jira yaji mai zance mashi ba ya kashe wayar,tabe baki nayi Ina maida wayar off nayi kwanciya ta,yaita jin haushinshi da Baba yayi man fad'a gwara yaji haushi ya huce daga baya, addu'a nayi nai kwanciya ta.

***Washe gari***

Koda na tashi nayi sallar asuba ban fito parlo ba balle nayi kitchen Ina gama azkar dina na hayewata gado na cigaba da bacci na,dan da nayi niyar shiga kitchen nayi ma Yaya Muhd breakfast da na tuna yau Yaya Haidar zaizo sai na fasa nayi kwanciya ta.

Ni Yaya Haidar ba abunda yayi man,dan ko magana bama hadani take dashi ba balle nace yayi man wani abu,kuma banjin tsanarshi a raina akan mai zan tsaneshi baiyi man komai ba.

Kawai dai wannan Karan naji zuciya ta bata bukatar zuwan nashi,duk daman nasan zaizo tunda yau saura kwana ukku bikin Yaya Teemarh nasan zaizo.baki amman nidai kam haka kawai sai naji gabana yana dan faduwa da an ambaci sunanshi haka kawai,kuma nasan bashi d'aya zaizo ba su duka gidan har da Yaya Teemarh ma zasu zo.

Baccin ma kasa zuwa yayi Ina ta juyi na sai ga Mama ta shigo dan tabani tayi tana cewa.

"Kulu tashi haka nan baccin ya isa tashi ki kwashe kayanki ki maidasu dakin da Babanku yace Kinga dai yau zamu fara baki ko."?

Tashi nayi Ina cewa."Toh Mama." Bayan ta fita na tashi na kwashe duk abunda nasan Muna so na maidasu bayan gida,ban bar komai a dakin ba sai da na cire komai ,na koma room din su Saddiqa suma nayi masu parking din komai na Isa room din Mama na kama mata muka ida had'a kayan room dinta muka kai.

Bayan mun gama muka gyara gidan muka kunna turaren wuta sannan muka yi wanka muka shirya bayan mun fito,muka zauna mukayi breakfast muka tashi muka tafi shagon dinki dan yau zamu anshi dinkunan mu.

Koda mukaje bamu dade ba muka anso dan har gogewa sai da sukayi kuma sukayi ma kowa parking din kayan shi a bag sannan suka bamu,muka shigo naped muka wuto gida.

Muna shigowa gida da sallamarmu fusksrmy dauke da fara'a bama kamar ni da na shigo Ina kwala ma Mama kira kina cewa.

"Mama fito kiga dinkunanmu sunyi kyau sosai kamar wasu amaren ma." Da dariya na ida shiga parlon Ina kallon Yaya Bash nace.."Yaya Bash Ina Mama wai." Hararata yayi yana cewa.."ban sani ba uwar mahaukata." Turo baki nayi ina cewa.."wayyo Allah nice uwar mahaukata kuma?Mai nayi maka zaka ce man uwar mahaukata." Waigawa nayi zan ma Yaya Muhammad magana crab na saka idona cikin nashi still nayi na kasa motsi Ina kallonshi na kasa Koda motsi yaushe ya iso?Daman da gaske Yaya Muhd yake da yace da safe zaizo rasa abun cewa nayi , magana Meenat ce ta dawo dani daga tunanin da na wulla tana cewa.

"Ina kwana Yaya Haidar sannu da zuwa." waigowa yayi yana dan murmushi yace ."lafiya lau." Dan sauke ajiyar zuciya nayi Ina cewa. "Barka da yau." Kureni yayi da Ido ya kusa minti goma yana kallona,sanann ya dauke kanshi baice komai ba,hararata Yaya Muhammad yayi yana cewa .

"Jiddarh."

Dagowa nayi Ina kallonshi na danyi murmushi nace ."Naam." Girgiza kai yayi yana surbar tea yace."ajiye bags din hannunki ki zo nan yanzun nan." Turo baki kawai nayi bance komai na samu wajen na ajiye bags din na nufi wajensu .

Koda na isa wajenshi na tsaya daga gefenshi yana cewa. "Gani Yaya." Ajiye cup din hannunshi yayi yana nuna man seat,zama nayi Ina yin kasa da kaina ganin irin kallon da yake man,wasa nike da zoben hannuna Ina jiran jin laifina irin kallon da yake man.

Dan karamin tsaki yayi yana cewa."yaushe kika zama sakara marar wayau ban sani ba."? Zaro Ido nayi Ina kallonshi sai kuma na cinno baki Ina cewa."wayyo Allah Yaya mai nayi kuma daga dawowa ta."? Buge man baki yayi yana cewa.."you are very stupid, useless ni zaki tambayi mai kike am ur mate."? girgiza kai nayi Ina goge hawayen da suka fara zuboman nace.

"Yi hakuri."

Tsaki ya kuma yi yana cewa."salon ki sake Kinga yanda zanyi maki sai na zaneki cikin gidan stupid zaki gaidashi ko sai nayi ball dake."

Cikin muryar kuka nace.."Yaya Haidar Ina kwana." Kallona yayi yana murmushi sai kuma yace.."Lafiya lau Hauwa'u,hope kina lafiya."? D'aga mashi Kai kawai nayi Ina kukana kasa kasa, girgiza kai yayi yana cewa.."stop it please,kukan ya isa haka tashi kije ki nuna ma Mama dinkin anjima ma zaki raka ni wani waje okay."

Nidai tashi kawai nayi bance komai ba,inajin yanda Yaya yaja tsaki yana cewa."na lura Kulu ta chanza Haidar,nama rasa mai ke damunta just ina kwana zatayi mata wuyar fad'a sai dai barka sai kace wani mate dinta anya kuwa"

Kallonshi yayi yana cewa."ni hakan ma da tayi ma dadi ya yayi,da nasan abunda zakayi mata kenan da ban barka ba,yanzun bakaji yanda nike ji ba wanann kukan da ka sata bayan kasan komai."

Tsaki kawai yayi yana cewa.."haka zaka aureta tana maka wanann fisge fisgen?to ni ba zan zuba Ido ba ubanta zanci kam."

Dafa Yaya Muhd yayi yana cewa.."matsalarka kenan M saurin fushi maiye dan Kulu tayi man fisge fisgen ai nasa girmanta ne." Kura mashi ido kawai yayi baice komai sai kuma can yace.

"Kana da aiki babba kuwa a gabanka indai kace zaka biye ma sonta ta kama wanann iskancin nan gaba baka isa ka sata tayi ba gwara tun wuri kayi ma tukar hanci Malan."

Murmushi yayi bai sake cewa komai ba sai ma maida hankalinshi kanmu da yayi Ina ta d'aga ma Mama Ina nuna mata sai murmushi nike,dan Ina kayan duk wani takaici da Yaya Muhd ya kunsa man na nemaishi na rasa ya cigaba da duba dinkuna ina jin dadi.

Bayan mun gama ganin kayan muka kwashe muka kaisu cikin bedroom,sannan muka fito har na zauna na tashi naje na dauko turarukan da Yaya Auwal ya kawo man ina ajiyesu a gaban Yaya Muhd,kallona yayi yana cewa.

"Wannan fa."?

Turo baki nayi Ina cewa."Yaya Auwal ya kawo man su jiya." Waigowa yayi yana kallon kayan yana kallona kamar wanda akayi ma dole yace.."waye Yaya Auwal kuma."? Cinno bakina kawai nayi Ina gunguni kallon da naga Yaya Muhd yana man nace.

"Wani abokin Yaya ne."

"Abokin Yaya kuma?wane Yayan?maiye alaqarku da har zai kawo maki wannan turarukan."? harfa hannu nayi Ina cewa."Yaya Auwal fa,Yaya Haidar har ka manta shi abokin Yaya Muhd fa."

Tsaki ya buga yana cewa.."Dan yana sonki sai aka ce mashi ya kawo maki turare?ko ke kika ce ya kawo maki turare tunda babu a gidan ku."?

Kuka na fashe da shi bance komai ba, tsaki yayi yana cewa.."maza kiyi man shuru ko na kwad'a maki mari yanzun nan wallahi,uban mai akayi maki da zaki saka mana kuka?okay dan Kinga banyi ball dake ba shiyasa kika samu chain din kuka ko."?

Goge hawayena nayi Ina kasa da kaina,ni tsoro ma ya bani yanda ya hakikance yana fad'a kamar zai cizeni,tsaki yayi yana tashi ya bar wajen bai sake cewa komai ba.

Ida durkushewa nayi wajen Ina rushewa da kuka,kuka nike sosai kamar wanda akayi man mugun bugu girgiza kai Yaya Muhd yayi yana dafani yace.

"Kukan ya isa haka Jidda,daman har yanzun kuna tare da Auwal?ba kince man baki sonshi ba."?

D'aga mashi Kai nayi Ina goge hawayena sai sauke ajiyar zuciya nike,cigaba da cewa yayi."baki sonshi maiyasa kike kulashi har yanzun Jidda?baki gudun Allah ya kamaki kina yaudarar bawan Allah mutumin kirki."

Cikin muryar kuka nace mashi.."ai bansan ya zanyi dashi ba shiyasa."

Furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa."wanann ba reason bane Jidda,kinsan son da Auwal yake maki kuwa?kinsan yanda yake jinki a zuciyarshi kuwa?baki kyautaman ba nasa tuni an wuce wajen kince baki sonshi dan ba'a dole sai ya sama ranshi hakuri Allah ya bashi wata,but kinata kulashi kina k'ara saka mashi sonki a zuciyarshi idan kuma kika auri wani bashi ba kin yaudareshi haka magana take."

Nidai shuru nayi bance komai ba dan banda ta cewa,tunda Yaya Muhd ya fini gaskiya tun wuri ya dace na gaya ma Yaya Auwal matsayinshi a wajena amman ai ba laifi na bane ni d'aya harda yan gidanmu da kullun maganarsu kenan na soshi mutumin kirki ne karda na sake shi,katse shurun Yya yayi yana cewa.

"Ki tabbatar da ki gaya mashi matsayin shi Jidda tun wuri.dan ni nayi maki miji kina karasa karatunki za'a sa maki ranar aure,karda ma ki sake kula kowa understand."?

D'aga mashi Kai kawai nayi bance komai ba,sai kuma yace.."saura wata nawa ki karasa karatunki." Dan shuru nayi sai kuma nace.."wata biyar in shaa Allah."

"Yauwa Allah ya kaimu,mijinki na nan yana jiranki tuni shekaru yake dakon sonki,baya da gurin da ya wuce yaga ya aureki,dan haka na hanaki sake sauraren kowa dan tuni na bashi ke tunda kika ce man baki son Auwal,Kinga kenan ba amfanin maido da hannun agogo baya,tashi tafiyarki bar turaren nan zan ba Auwal turaren da kaina."

Tashi nayi na shigewata room dinmu,na kwanta Ina matsar kwallah dan naji ciwon tsawar da Yaya Haidar ya zage yai ta zagga man kamar ya kamani da kwarto daga nace an kawo man turare ai naga bashi na gaya mawa ba da zai sakaman baki yana mai tsawa da hargagi kamar wani yunwataicen zaki.

Bayan shigata room da kallo Yaya Muhd ya bini yana girgiza kai,can ya dauki key din motarshi da kuma ledar turarukan yana ce ma Mama.."Mama zanje wajen Auwal na dawo ."

Tasowa Mama tayi tana cewa.."amman Muhd idan aka dakatar da Auwal zuwa wajen Kulu wa ake son Kulu ta aura mai hankali da natsuwa kamar Auwal."? Murmushi yayi yana shafa gefen fuskarta yace.."believe me Mama,Kulu ta samu

Please Login or Register in order to submit comment