Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaina so yake yayi raping dina fa."

zatayi magana sai kuma tayi shuru tana mai Kara kama kanta kamar yanda Nima nayi,shi kuwa murmushi yayi yana cewa."Myluv ya Ina maku horn Kun gyale ni kamar ma bakuji tsayuwar motar nawa ba,kuma na kira wayarki bakiyi picking ba.?"harararshi nayi Ina cewa."har sau yaushe zan gaya maka ka fita a sabgata Ahmad?maiyasa kake son matsama rayuwata ka isheni ka damaini ka maitsa mani."

Dan shuru nayi sai kuma na cigaba da cewa."Ina dalili haba mana Ahmad ya kamata ka rabu dani haka nan mana,Kai ba aurena zakayi ba Kai kawai soyayya kazo muyi soyayyarma wanda ta sab'ama addini, kuma tin farko nace maka ni bani da ra'ayin yin soyayya irin taka ba shikenan ba,sai ka samo wata ba,tunda bani d'aya bace ba akwai mata da yawa a garin gusau iri iri haba mana."

tunda na fara maganata ya kafe ni da ido yana kallo sai lashe baki yake,kamar wani tsohon maye,gashi idonshi akan boss dina ya saukesu kamar zai kai hannu ya cabkosu haka yake ji, murmushi yayi yana cewa."wallahi wallahi Jidda tunda har na kwalafa ma raina ke to ko kiso ko karda ki so sai na kashe ishir ruwana a kanki,karda kiga Ina binki ta laluma kina man wanann haukan banzan kinyi aikin banza har da na wofi dan limit na baki akwai lokacin da na dauka wanda zan kashe kishiruwana a kanki ki rike wannan."

harararshi nayi Ina nuna shi da yatsa nace."idan ka fasa baka hauhu da jini ba Ahmad,idan ka isa Kai dan iska ne to ka daina bani limit kazo kayi zina dani,Kai idan ma ka tashi dan Allah kayi ta a saman gadon uwarka anan zan tabbatar da kai jakkin dan iska ne,anan zan gane ka ansa sunanka bunsuru jakki marar kwalkwalwa da ilimi kuma jahili wan...Jidda." ya katseni ya kawo man mari a fuska sai dai bai sauke hannunshi a saman fuskata ba,daga ni har Wasi rintse Ido mukayi,ni kuwa jira nayi naji saukar belt ko kuma maruka dogon tsaki yaja yana mai cewa.

"Matsala ta dake dan banzan tsoro daga ke har masu zugaki,inba kina sakara ba wanda bata waye ba ,banga amfanin sakoki university ba tunda har yanzun kanki a tukunya yake,nida nazo maki da harkar arziki harkar da zakiyi kudi harkar nan fa idan kika shigota riba biyu zakiyi ga kudi ga kuma dadi da zan shayar dake Jidda,zan biyaki ko nawane zan baki ko million nawa kike bukata kwanciya daya kawai zanyi dake fa,na tabbata ta biyun da kanki zaki kawo man kanki na kara sosa maki inda na tabo maki amm...sauka mari yaji a fuskarshi wanda ya hanashi karasa maganar,Ina kuka Ina cewa.

"Allah yayi man tsari dakai fasik'i mazinaci ,Allah ya shiga tsakanina dakai in shaa Allah sai Allah ya shiga tsakani dakai,Kai bani ba duk wata mace kammila sai Allah ya shiga tsakaninmu da irinku bata gari wanda suke bata tarbiyar yaran mutane,kuma in shaa Allah sai anyi ma y'ayanka ko kuma k'annanka Kai in shaa Allah sai anyi ma uwarka fyade a gaban idonka anyi mata kaca-kaca,kuma in shaa Allah...wata uwar Kara na saki Ina cewa.."Allah ya isa tsakanina da Kai kuma wallahi baka mari banza ba,ba dai takamarka kudi ba to ni zan nuna maka ba komai kudi keyi ba kuma wallahi ban yafe ba nafi karfinka nafi karfin duk wani mai mugun halin irin naka."

Janyo ni yayi yana cewa.."duk rashin kunyarki da tabbatarki da zakiyi karda ki sake ki sako a halina a ciki,dan duk iskacina ban hada uwata da kowa ba haka ma kanena balle kuma yarana na gaya maki."

cigaba da cewa yayi."kuma wallahi sai nayi maganinki sai na nuna maki kudi suna da rana ki rubuta ki aje."karza mashi cizo nayi Ina cewa."ni kuma zan nuna maka kudi basu maganin komai." tafiyata nayi dan daman ita Wasi ba a wajenku ta tsaya ba,dan nisa kadan da mu ta tsaya sai dai tana kallonmu ba dai taji abunda muke cewa,Ina isowa nace mata tashi muje yanda taga raina a bace yake bata ce man komai ba sai ma naped da ta samo mana muka hau,bata ce man komai ba nima haka sai ma gefe da na kalla Ina goge hawayen da ke zuboman saman fuskarta.

Koda muka iso unguwarmu a kofar gidanmu tasa a sauke mu ta fiddo kudinta ta biya ta kama hannuna muka shiga cikin gida,a parlo muka tadda duka yan gidanmu har da Baba dan yau da wuri ya dawo a wajen aiki, kallonta Baba yayi yana cewa."Wasila Mai ya samu kawar taki ko bata lafiya ne.?"a tsorace Baba yayi maganar,girgiza kai Wasila tayi tana cewa."Aa Baba lafiyarta qalau,haduwa sukayi dai da Ahmad yau sukayi magana sai naga kamar harda fada sukayi dan harda marinta naga yayi."

Tashi Yaya Bash yayi yana cewa."what?Mari fa kika ce Wasila?waye shi?waye Ahmad kuma?da har zai d'aga hannu ya mari mace."kasa tayi da kanta tana kallona,nidai daura kaina nayi bisa cinyar Mama Ina ta hawaye,buga mata tsawa Baba yayi yana cewa.."Wasila ba dake ake magana ba?akace maki waye Ahmad.?"Dan dabarbarcewa tayi dan batayi tunanin ban gaya ma yan gidanmu issues dina da Ahmad ba,kuma taga gangancina tasa tun attack din farko da ya kawo man na gaya ma Baba,sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa.

"Baba wani saurayinta ne dan school dinmu, department dinmu daya dashi shine yake sonta kuma tace ai bata sonshi amman yaki yarda." kallo daya Baba yayi mata ya gane akwai wata a kasa,dan murmushi Baba yayi yana cewa."daga nan sai akayi yaya?Ina ganin mutuncinki karda kiyi man karya idan nayi bincike na gano kinyi man karya wallahi sai na sab'a maki Wasila." zufa ta share dan tana tsoron lamarin Baba tasan halinshi yana da wasa amman bai daukar shirme ko kadan,dan rage murya tayi ta fara gaya mashi.

"Tun muna level one shi kuma yana level two a lokacin yace yana son Hauwa,ita kuma a lokacin ta gaya mashi role din gidansu akan sai yazo wajenka sannan kuma ya taro iyayenshi sun nema mashi izini,anan aka fara samun matsala dan shi yace bai dade da yin aure ba matarshi haihuwarta biyu duka duka ba zaice zaiyi mata kishiya ba duka duka ko shekara hudu basuyi da aure ba."

"Anan ita kuma tace gaskiya yayi hakuri,dan ita gaskiya bata auren mai mata ma yayi hakuri,anan ne aka samu matsala sai ya fito mata da abunda ya kawoshi wajenta wato kawai sunyi soyayya, soyayyarma irin wanda ta sab'ama addini ,anan tace ita bata yarda bata da ra'ayi shi kuma yace zai bata ko nawane idan zata amince da bukatarshi anan taki yarda."

Dan shuru tayi sai kuma ta cigaba da cewa." haka dai yake ta fama da ita, akan ta amince da bukatarshi amman dai ita taki yarda , da yaga bata yarda ba sai ya biyo mata ta bayan fage ko ta tsiya tsiya sai yayi abunda ya gadama da ita ko tana so bata so,haka dai take fama dashi yayi kwana biyu bai shigo school ba saboda sun gama yanzun muke a level 4,sai kawai yau ya shigo muna tafiya ya tsadamu amman ni yau bansan mai yace mata ba,ta dai taho wajena tana kuka."


kallona Baba yayi yana cewa."da kuka hadu yau mai yace maki."? ban boye masu duk yanda mukayi dashi ba ,sai da na gaya masu da kuma alwashin da ya dauka a kaina,sosai ran Baba ya baci yayi fada sosai dan ta inda yake shiga ba tana yake fita ba,sai da nima yayi man fada akan maiyasa ban gaya mashi na duk tsawon shekarun da muka dauka muna tare,sosai yayi man fada sannan ya tambayen na gaya mashi full name dinshi ya tashi fuu ya fita,Yaya Bash da Sule suka bi bayanshi.

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Editing❌*

*41-50*


Ina mai neman afuwarki da yafiyarki akan abunda nayi maki a school Hauwa,nayi nadama sosai marar adadi ni yanzun har bansan da wani ido zan kalleki ba akan wanann lamarin,sai dai kawai nace kiyi hakuri Ina mai k'ara baki hakuri dan ni mai laifi ne a wajenki ba zan tab'a gajiyawa ba wajen baki hakuri Hauwa,daga karshe zan ce maki Allah ya zab'a maki da abunda yafi alkhari ya baki miji na gari Jidda dan ni ban cancanci na zamo miji a gareki ba,kamillar mace kamar ki sai kamilin namiji na barki lafiya daga mai kaunarki Ahmad Bala mato Gusau.

Na dad'e Ina sake maimata karanta message din Ahmad,ni tsoro ma ya kamani mai ya faru mai zafi haka da har Ahmad yayi sauri saukowa daga alkwashin da ya dauka?Anya kuwa ba wata gadar zare yake kullaman ba?nasan halinshi fah nasan waye Ahmad ko kadan bai da kirki ban dauka kowa da mutunci inba iyayenshi ba,tabbas ruwa baya tsami banza ban yarda da tuban ba,wannan ba tuban Allah na Annabi bane nasan haka kawai ba zai yadda makaman yak'inshi ba dan kawai Baba sunje gidansu.

Wata zuciyar kuma raya man tayi ai yana jin maganar iyayenshi kuma baison b'acin rainsu,maybe sune suka nuna mashi fushinsu shiyasa yayi nadamar abunda yayi kamar yanda yake fadi,Indai na shiga kokanto komai tsayaman cak!yayi da na saka wanann sai na kaucen na kulla wanann.

Ina a cikin jimamin message din Ahmad su Mama suka dawo nik'i nik'i da kaya,dan sayaiya sukayi ba karama ba kudi suka kashe iya kashewa kamar ba'a so,sannu da zuwa nayi masu Ina shiga kitchen na kawo masu ruwa mai sanyi,na zuba ma kowa a cup na mika masu,ansa sukayi suna sha,sai da suka gama sha Yaya Teemarh ta kalli tace.

"Allah yayi maki albarka Jiddah." Murmushi nayi Ina cewa."Amin Amarya ko a k'ara zubo maki."d'aga man kai tayi tana sauke ajiyar zuciya, murmushi nayi kawai na k'ara zuba mata wani nan ma na zuba ma Mama k'ari sai da suka sha cup biyu na ruwa sannan suka dawo dai dai.

Dukawa nayi wajen kayan Ina kallo sai na kallesu nace."gaskiya kunsha kasuwa tun safe." Murmushi Meenat tayi tana cewa."ai dole mu jima a kasuwa Yaya Jidda,karki so kiga yawan da mukayi sai da muka kewaye kasuwar nan dukanta Ina jin,sai da muka saya komai sauran kayan ai suna dakunan baya ai Mama tasa aka kaisu."

Daga kayan nayi Ina kallon wasu glass cup da sukayi man kyau sosai,gaskiya kam sun kashe kudi abunda ke kudi,sai da na gama ganin kayan na gama yabawa sannan na tashi na shiga kitchen na dauko masu abinci na ajiye masu gaban su a tsiyar Parlo dan ko dinning ban nufa dashi ba,saboda nasan ba zasu iya hawa dinning ba Koda na Kai masu dan a gajiye suke sosai.

Kallon Abincin Mama tayi tana cewa."ajiye abincin nan gefe Kulu bari mu dan watsa ruwa mai maido karfin jikinmu mu kuma yi sallah sai mu dawo ma abincin,dan muna iya ci kuma jikinmu ya mutu mu kasa tashi muyi wanka da sallar kuma."

Daga Kai nayi Ina cewa."hakane kuma , ku tashi to kuje ku kintsi yummy better na jiranku." Kallon food flasks din Meenat tayi tana cewa."gaskiya kam Yummy na jiranmu wannan iyayen flasks din duk abinci ke ciki."? d'aga mata kai nayi Ina cewa."sai ma kin dawo idonki zai gane maki dadinki da ke ciki." Dariya tayi tana bin bayan su Mama da sukayi gaba,gyara kayan nayi na kaisu dakin Baba na ajiye sannan na fito ya kulle dakin na kunna kallo,ganin waka aka saka a channel din da ake kallo na maida wata tasa suna haska wildlife nan na zauna na fara kallo dan bani gajiya da kallon wild bama kamar a saka na zagikuna da giwaye to ban sanin iya adadin da zan bata a wajen kallonsu.

Bayan sun fito suka zauna suka ci abinci suka koshi,sai yabon abincin suke dan Meenat da take zagewa ban iya girki ba rasa bakin magana tayi,sai da taci ta koshi sannan ta kalleni tana cewa.."Yaya Kulu dan Allah wannan wani irin abinci ne mai dan banzan dadi haka,baka cewa coconutrice ce ga kuma wannan abun da kika daura mana sama shi ba wainar kwai ba kuma ba wainar fulawa ba,gaya man ya akeyinshi."?

K'ara daukar *EGG OMELETTE ROLE* tayi ta tauna tana lumshe Ido ta saukesu a kaina tace. "Kamar pizza ga dai shine dan Allah maiye damai kika yi shi."fir nayi da Ido Ina cewa."cheif Meenat,kune fa kitchen ai nasa kallo d'aya zakiyi mashi zaki gane maiye." Dariya tayi tana cewa."Dan Allah Yaya Kulu,na bar maki kin fini iyawa,daman ai fini yawan kallon recipes taya zan hada kaina dake pls ki koya man." Sai da na mula nasha iska sanann nace mata."baki da case Beb,randa muka samu time kalar wannan zanyi gabanki sai kiga yanda ake yi." Dan kwabe fuska tayi tana cewa."nasa yanzun zakiyi man bayanin yanda ake yi duka minti nawa ne luv." Hararar wasa nayi mata Ina cewa."koba luv ba, yanzun dai wani irin shiri kika yi ma biki kanwar amarya."?Dan shuru tayi tana cewa .

"Ni da cewa nayi mai zai hana Dani da ke da Saddiqa sai Rukky muyi lace iri daya a samu color din da zatayi ma kowa kyau Kinga dai mu farare ne ke kuma brown skin gareki dama ace black skin ce sai muyi nervy blue amman sai muyi choosing din color mai kyau sai kuma muyi material dan nasan har da dinner za'ayi sai kuma muyi atamfa wanda zamu saka a ranar daurin aure."

Murmushi nayi Ina cewa."kin dan dauko hanya sai kuma kika dan kauce."turo baki tayi tana cewa." Kamar ya kenan Yaya Kulu."dariya nayi Ina cewa."kamar yanda kika ga na fadi,naji muyi lace iri daya mu saka ranar daurin da rana sai kuma atamfa mu sakata da safe sai kuma idan marece yayi lokacin mutane sunzo sosai sai mu sake saka wani laces din wand yafi na farko,muyi kwaliya wajen makeup washe gari kuma ranar walima mu saka atamfa da safe sai da marece idan za'a fara walimar mu laces dinmu,idan kuma za'ayi dinner din sai mu samu laces dinmu shima maikyau da tsari mu saka zaifi material Kinga shi material daga ranar maybe ba zamu sake sakashi ba,laces fah?shi baida matsala zamu saka kayanmu randa muka gadama."

Kallon Yaya Teemarh nayi Ina cewa."wai Yaya Teemarh zakuyi dinner din ne."? D'aga man kai tayi tana cewa."dazun a kasuwa munyi waya dashi yace man da dinner da kamu wani nike so,nace mashi dinner."

Allah sarki Yaya Sadiq,shidai bai da matsala daman." Cewar Meenat tana washe baki taji ance za'ayi dinner daman ita ba daga baya ba wajen son harka tana son taga ana event a biki bata san biki salat babu ko dan Dj.

Waya Mama ta gama yi sannan ta kalle mu tace." Wai kunsan Yayanku jibi zai dawo ya gama karatu shi." Ihun dadi muka dauka muna cewa."Dan Allah Mama." Kama gemu Mama tayi tana cewa."Dan gidanku da karya nike maku, yanzun nan dashi na gama waya fa."dariya nayi Ina cewa."Allah sarki Yaya Muhammad daman munata kewarka ,Ashe da rabon ayi bikin Yaya Teemarh yana nan." Murmushi Mama tayi tana cewa."aikuwa Kinga abun Allah." Kallon Teemarh Mama tayi tana cewa." Ya dace fa kije birnin keffi Teemarh gidan Babanku kiyi masu sallama." Turo baki tayi tana cewa."A'a dan Allah Mama,wallahi kinsan ni ba son zuwa birnin keffi nike ba."

Harararta Mama tayi tana cewa."aikuwa zuwa birnin kebbi ya zamai maki dole,dan da gobe Babanku yace zaki je nice nace ya bari sai jibi sai a gaya masu su san da zuwan naki." Kuka ta fashe dashi tana cewa ."Amman tsakani ga Allah Mama kinsan dai halin matar nan ba mutunci bane da ita,gashi ba son mutune gidan suke ba haka zanje na kama rakubewa kamar wata aljana." Dakuwa Mama tayi mata tana cewa."Teemarh yaushe kika taci har haka?gidan Baban naki kuka kina baki son zuwa?ke zakiji dadi yaran Kulu suce basu zuwa gidanki?ni ba ruwana wallahi tun wuri ki dawo a cikin haiyacinki,Allah yaso ba'a gaban Babanku kika nuna baki son zuwa gidan Yayanshi ba da sai yau ranki ya b'aci kinsan dai bai had'a yan uwanshi da kowa ba,kuma uwa d'aya uba d'aya ya wuce wasa."

"Amman Mama..Amman mai?yi man shuru ko na buge bakinki nidai ban yarda kuyi wasa da zuminci ba dan haka gobe ma zaki tafi bari yanzun na kira Hajia Aisha na gaya mata zuwan naki."

Kasa tayi da kanta bata sake cewa komai ba,kiran Momy Mama tayi ta sheda mata da zuwan Teemarh sannan ta kashe wayar tana cewa. "Maza tashi ki hada kayanki ba zaki dawo ba sai ana saura sati biyu bikinki haka Babanku yace." Da to ta tashi ta wuce room dan had'a kayanta,kallon Mama nayi Ina girgiza kai nace.

"Allah ko Mama koni nan banson zuwa gidan su Yaya Haidar,ko kadan Momynsu bata da kirki dan kawai taga mijinta yafi su Babanmu kudi shiyasa take mana d'agin Kai ita da yaranta bama kamar Yaya Haidar da ko gaidashi kayi bai ansawa sai ya gadama sai kace zasu baka aljana."

Murtuke fuska Mama tayi tana cewa."ko bayan rai kuka yarda zumincin Allah nidai ban yafe ba,Ina ruwanku da girman kansu kudai ba zumunci kuka je ba?balle ma nasan Hajia Aisha bata yi maku komai barta dai da rashin son magana,amman ba daga nan ni banga aibunta ba haba mana jama'a idan ana biyewa ai ba za'ayi zuminci ba kuwa." Nidai hakuri kawai na ba Mama ban sake cewa komai ba.

Koda Baba ya dawo Mama yake sanar dashi tafiyar Teemarh ta dawo gobe dan har sunyi waya da Hajia Aisha ma,sosai Baba yaji dadin haka flight yayi ma Yaya Teemarh take yana cewa."ba zata bi hanyar birnin kebbi ba ita d'aya,yanzun hanyar a bace take wannan rashin tsaron da yake son kunno mana Kai kafin ma ta isa sokoto aiki ne balle kuma birnin kebbi."

Gyara zamanta Mama tayi tana cewa."gaskiya kam,Allah dai yayi mana maganin wanann masifa,naji ance jiya an shiga tsafe ni wai wannan wasu irin mutane ne mararsa Imani haka." Jinjina Kai Baba yayi yana cewa ."Allah dai ya tsare wai kidnapped ni abun har mamaki yake bani muna jin abu a kudu sai gashi yanzun yazo gida nan ma Gusau abunda ake kenan,Allah dai ya tsare mu." Da anub muka ansa mu dukanmu sannan muka taba fira lokacin sallar isha'i yayi muka tashi dan zuwa yin sallah.

Bayan na gama sallah nayi shirin kwanciya,sai ga Yaya Auwal ya kirani waya, murmushi nayi Ina daukar wayar,inajin saukar numfashin shi a cikin kunnena sai da ya sauke ajiyar zuciya sau ukku sannan yace.

"Soulmate wallahi zuciya ta kusa bugawa kiris ya rage da sai dai na tsinci kaina a gadon asibiti." Waro Ido nayi waje Ina cewa."subuhanllh Yaya Auwal wani abu ne ya kusa da kai."!? A tsorace nayi mashi tambayar,dan murmushi yayi yana cewa."kusan haka Jiddarhna,Mai ya faru dake kika kashe wayar ki tun daren jiya har zuwa marecen yau."?Dan turo baki nayi dan ni nasa wani abu ne ya kusa samunshi na tashin hankali,kinyin magana nayi da ya gaji da jiran ansa ya cigaba da cewa."hope kina lafiya dai ko."? D'aga mashi Kai nayi kamar Ina gabanshi nace."lafiya lau Alhamdullahi Kai fa.?

Humm!sai kuma yace."dasauki dai Jiddah." Sake cewa nayi."wani abu ke damunka."? "Eh mana Jiddarh wani abu yake damuna babu dare babu rana, ya tsayaman a zuciya." Zaro Ido nayi Ina cewa."innalillahi Yaya Auwal maiye wannan abun haka."

"Sonki ne Jiddarh."

Dan shuru yayi sanann ya cigaba da cewa ."Jidda da gaske nike maki sonki ya kusa zama ajalina Jiddarh,Ina sonki ina sonki Jiddarh dan Allah ki soni ki yarda ki aureni zan kula dake Jiddarh myluv."

Lumshe idona nayi Ina budewa nace."Yaya Auwal." Dan shuru nayi sai kuma nace.."ai bance ba zan aureka ba,dan Allah ka daina zafafa sona haka a zuciyarka dan bansan mai gobe zata haifar ba,kuma ni har ga Allah banson wani abu ya samaika saboda ni dan ba zan yafe ma kaina ba har abada."

Na kusa minti uku da gama maganar,baice komai ba dan nasan maganar yake aunawa ko kuma haka yayi shuru saboda jin dadi nidai ban sani ba sai da fidda rai da zai bani ansa yace.

"Jidda." Rintse idona nayi dan yanda ya kira suna har cikin kaina haka naji sunan, kuma yanda sautin muryarshi ta fito yana cikin damuwa,Ina mamakin irin son da yake man nidai zan gaya mashi iyakar gaskiya ta ko da ba zata yi mashi dadi ba kam,zan gaya mashi nidai kam.

"Baki sona ko."

Kamar saukar aradu haka naji tambayar, kamar yana gabana haka na kama girgiza kai ,shafa fuskata nayi Ina cewa."ko d'aya Yaya Auwal." Murmushi yayi mai sauti yana cewa.

"Jidda baki bani ansata ba,kina sona eh ko A'a."?

Dan turo baki nayi Ina cewa."Dan Allah Yaya Auwal ka daina yi man irin wannan tambayar nikam,har bansan mai zance maka ba taya ma za'ayi nace bani sonka bayan Kai yayana ne ,ai Kai mijin da ko wace take fatan samu ne Yaya Auwal kana da kyaun hali ga kirki da hankali da ilimi taya zan ki son mutun mai ilimi irinka."

"Uhmm! Jiddarh Ina tsoron randa zan wayi gari naga kin zama mallakin wani *DA'IMAN ABADAN* ,ba ni ba, Jidda ni musulmi ne inason na zama cikaiken Muslim,amman inajin ba zan tab'a yarda da qassarar rashinkin ba Jiddah,ki taimakeni ki tausayaman zuciyata tana cikin halin sonki da begenki,zuciyata bata da abunda take son kasancewa dashi sama dake Jiddarh,wallahi Jiddarh baki ba zai iya fasalta maki dumbun son da take maki ba."

Dan shuru yayi sai kuma yace ."Allah ya sani Jidda,Allah ne shaida banda gurin cutar dake sonki nike kaunarki nike Jiddah,fatana na rayu dake *DA'IMAN ABADAN* fatana ki zama uwar y'ay'ana Jidda, fatana ki zamaiman inuwa inason ki zamaiman natsuwata Jidda,mai kike jira Jiddarh finally year kike fa Jiddarh ki bani dama manya su kawo kudin na gani Ina so,ni idan na kawo kudin aurenki hankali sai yafi kwanciya Jiddarh,amman yanzun hankalina a tashe yake Ina tsoron karda wani yazo ya kwaceman ke Jiddarh da gaske nike maki bansan ya zanyi ba,akwai matsala babba Jidda ya kamata ki fahimci inda nike son ki dosa Jiddarh."

Dan jum!nayi Ina tunanin maganarshi tabbas da gaske yake mai nike jira?idan har Ina sonshi dagaske ya dace na bashi dama kamar yanda ya bukata,to ni ya zanyi?haka zan aureshi bani sonshi?banfa sonshi dagaske nike maku bani son Yaya Auwal ko kadan a rai na,kuma idan har nace zan dunga binshi a haka yana mashi hanya hanya watarana fa zan aure wanda naji inaso, na yaudareshi kenan? Hakan na nufin mutuwa zaiyi kenan?nice sila fa , nice akaina ne son da yake man ne yaja haka fa,ni kuma idan na aureshi zan cuci kaina da kaina zama aure fa ,aure fa ba wasa bane taya zanyi rayuwar aure da wanda banso?gaskiya da sake ya kamata nasan abun yi tun kafin dare ya kure man,dole nasan abun yi gaskiya kam,furzar da iskan bakina nayi Ina cewa.

"Yaya Auwal,in shaa Allah zamuyi wannan maganar bayan bikin Yaya Teemarh,kasan dai ansa bikinta ko."? Murmushi yayi yana cewa."eh Soulmate,ai Sadiq ya gaya man next month ake yin bikinsu ko."? D'aga mashi Kai nayi Ina cewa ."eh in shaa Allah." Furzar da iska yayi yana cewa."Allah ya kaimu, amman wannan ba zai hanamu magana ba tunda bikin bai Kai da matsowa ba."

"Hakane amman inason natsuwa ne shiyasa Yaya Auwal."

Shafa kanshi yayi yana cewa." Okay yayi,yanzun nawa kike bukata wajen hidimar bikin." Girgiza kai nayi Ina cewa."bakomai Yaya Auwal Allah ya Kara bude da kuma girma."

"Amin Soulmate,yanzun yaushe zan zo kinsan nayi missing din beautiful face dinki Babe ya kamata a saka man rana dai nazo." Turo baki nayi Ina cewa. "Yaya Auwal duka duka yaushe kazo yau fa kwananka biyu da zuwa."

Murmushi yayi yana cewa." Luv kenan ba zaki gane yanda nike ji ba,ni ji nike kamar anyi shekara dubu biyu haka nike ji dan baki san yanda nike jin sonki a raina ba shiyasa,a taimakeni nidai a saka man rana Tawan."

Murmushi nayi Ina cewa."okay kazo jibi dan gobe Yaya Teemarh zatayi tafiya jibi sai ka shigo ko."?

"Yes My Beb luv uh,har naji hankali ya dan kwanta zanga beautiful face din nan mai neman hanani bacci a Koda yaushe." Nidai

Please Login or Register in order to submit comment