Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an gano hankalin gidan, dan gidan ba kyaun gani wata biyu har da sati biyu ba'a yi mopping ba balle wani sharar yana.

Bayan sun gama aka je bayan gida aka daura katuwar tukunyar da ake dafa abincin saraka duk rana ana rabama almajirai da mabukata,bayan angama girkawa su Yaya Bash suka raba ma duk wanda rabonshi ya tsaga sannan kuma aka raba dabino ga kananun yara da kulikuli.

Bayan kuma angama sallar isha'i aka zauna kofar gida dasu Yaya aka raba quri'ani aka hadu aka sauke sai karfe dayan dare har da rabi sannan aka kammala akayi addu'a sannan kowa ya tafi gidansu.

Daman abunda sukeyi kenan kullun sai an sauke a unguwar suna dawowa suka dan kwanta wajen karfe uku kuma aka tashi aka cigaba da salla har asuba.

Ana dawowa sallar asuba aka yi kallacin safe aka raba sanann aka daura na rana,kullun sai Momy ta kira Mama waya daga birnin kebbi tana tambayar ko an kira waya amman ansar d'aya ce A'a.

Hakama Yaya Teemarh da bata da aiki sai Kiran waya tana tambayar ya ake ciki,kuka kuwa ta shashi kamar ba gobe dan ma Mama tana mata fad'a akan tabi sannu karda wani abu ya shafi abunda ke a cikinta sannan ta dan rage.

Shima Yaya Haidar yana zuwa duk bayan sati a gusau yayi kwana biyu zuwa ukku ko da yazo ba zama yake ba baya police station baya gidajen malaman da ke da almajirai yana Kai masu abinci da kudi ayi mashi addu'a Allah ya bai yana ni.

Baba Bashir pictures dina yasa a baza a media tun daga kan Facebook, Twitter Instagram telegram tiktok da duk wata kafar yad'a labarai sai da ya bada cigiyata.

BBC, LIBERTY,NTA,TVC,KSMC,TAURARUWA,GASKIA TV DA Duk wajen da ake watsa labarai ya bada pictures dina da kyauta mai tsoka ga duk wanda ya gano labarina...nan duniya ta Kara dauka kowa da abunda yake cewa wasu na cewa su daina wahalar da kaina saurayina nabi muna can muna holewarmu dan kaina zan dawo gida wasu kuma na Allah ya kyauta ya maidoni lafiya ya kuma kareni.



*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ


*131-140*

Wani haske ya gauraye man Ido, bansan lokacin da na saka hannu ba na k'are haske Ina mai rintse idona sosai,dan rabon da naga haske ko ya yake har mantuwata ta manta dan ban san ta ko wace hanya aka biyo aka shigo dani dakin da aka ajiye ni dakine mai dahun bala'i....Tun a cikin motar suka daureman hannu da Ido ba abunda nike gani,dan a rana d'aya sau d'aya tak ake bani ruwa shima ba dan na koshi ba dan ana bani na fara sha bani makalwa biyu zuwa ukku za'a anshe ruwan kafin kuma mai kawo man ruwan ya fita sai ya watsa man ruwan sanyi mai masifar sanyi inajin har da kankara a jikinshi haka zai watsaman sanann ya ficewarshi.

Ba dai a tab'a buguna ba tunda aka kawo ni kuma ba wanda ya tab'a kama Koda da hannuna ne amman kullun rana sai an watsaman ruwan kankara sau hudu a rana duk mura tabi ta kamani ga ba abinci dan sau biyu ake bani abinci a sati.

Cire hannuna akayi daga saman fuskarta ana haskeman fuska da wata irin fitila mai bala'in hasken tsiya cikin wata irin kaukausar murya mutumin da ke tsaye gabana yace.."maza taso."

Tasowa nay Ina mai yin kasa da kaina dan ko kallonshi bani son nayi saboda wani irin basamudan gardi ne gashi baki jikinshi ba ya wuce tunanin mai tunani sai kace ana shafa mashi bakin mai tsabar baki...Tsaki yayi yana yin gaba,tsaye nayi ban dai bin shi ba kuma ban motsa daga tsaguwar da nike ba,waigowa yayi yana buga man wata muguwar tsawa yana cewa.

"Idan har kika kuskura nazo wajen nan sai nayi kuli kuli dake a wajen nan."

Da sauri nabi bayanshi ina mai dode kunnena haka na kama bin bayanshi wasu kofofi ne muka kama fitowa Ina lissafawa sai da muka wuto kofar tara a ta gomance na ganni cikin wani katon parlo cike yake da kujeru royals sai kuma wata katuwar plasma da take manne a bango tana aiki ita d'aya...Shuru parlon yake ba abunda ke tashi sai sanyi Ac da kuma karar Tv,wata kofa ya nuna man yana cewa.

"Bayi ne maza shiga kiyi wanka minti goma na baki."

Ya ida maganar yana duba agogon hannunshi ba,da sauri na nufi kofar da yake nuna man na tura na shiga a hankali babban toilet ne wanda ba abunda babu na amfanin toilet a ciki kayana na cire Ina had'a ruwan zafi na fara gasa jikina dan wani irin sanyi nike ji ga kuma mara da nike fama da ita.

Ido k'afe yake babu hawaye ko d'aya,dan nayi kukan har na daina na bar ma Allah lamarina,brush na gani sabo fal aikuwa na dauka na matsa makali na wanke bakina tas sanann nayi wanka na wanke jikina tas sai kamshi nike.

Wani irin dadi naji ya mamaye ni da nayi wanka kayana ma maida Ina fitowa,ko kallona baiyi ba yayi gaba Ina binshi a baya wata hanya ta daban ya bi dani nidai nawa Ido Ina addu'a a zuciyata,dai dai wata kofa ya tsaya yana cewa.

"Maza shiga zaki ga kaya da mai harda kayan kwaliya ki shirya minti goma na baki idan har kika kuskura na shigo baki shirya ba sai nayi gunduwa gunduwa na tsokar jikinki."

Shiga nayi bance mashi Komai ba, bedroom ne babba wanda yasha gado madaidaici mai daukar hankali kaya na gani an ajiye gefen gadon,zama nayi saman stool na shafa mai na dan shafa hoda ban kalli jan bakin da suke jere a saman mirrorn ba na tashi na dauko breziya na saka da pant.

Sakin baki nayi Ina kallon rigar da aka ajiye man da sunan wai na saka tabbas ba zan iya saka wanann rigar ba da ita ai gwara babu dan rigace yar'karama duk tsawonta ba zata rufe duwawuna ba haka gaban rigar wayam yake babu komai a gabanta sai wasu igiyoyi da ba zasu wuce biyu ba anyi crossing dasu.

Ajiye rigar nayi Ina zama bakin gado na rakka abun tagumi komai na duniya yayi man zafi ya tsaya man cak,mai haka ke nufi wani salo ne wanann suke kirkiro man dashi kuma?Ina zaune naji an bango kofar an shigo babu Sallama balle neman izini,dukewa nayi kasa Ina kare kirjina da hannuwa na,tsaye akayi a gabana sai can kuma aka d'agoni rintse idona nayi sai hawaye ke malala a saman fuskata.

Ba abunda aka ce man sai naji ana saka man rigar sanann naji ana fesa man turare kamar mai fesa man turaren kawai ake sai da aka kusan bulbular da turaren ajikina sanann yace.

"Taho muje."

Tsaye nayi ban motsa ba kuma ban bude idona ba,maganar da yayi na gane wanda ya fiddo ni daga cikin wanann kurkunki ne.

Saukar wani wawan mari naji a saman fuskata sai da naga tartsatsin wuta wani jam da dam haka naji kunuwana suna ansa man tsabar masifa da azabar marin da wanka man a fuska.

"Taho muje."

Ya sake maimaitawa ai kafin ya d'aga kafarshi har na d'aga tawa jikina sai kirma yake dan tunda nike a duniya ba'a tab'a yi man irin marin da yayi man ba har lokacin kaina ciwo yake kunnuwa na suke dam haka suke ta yi man.

Tafiya kawai muke wata hanya kuma ya sake bi dani sab'ani ta farko bainan kasa muka hau sai ga a gidan kasa, tsorata nayi dan tunda nike ban tab'a shiga ginin k'asa ba sai a lokacin a tsorace nike sosai dan bani cikin haiyacina bin bayanshi kawai nike kamar yanda ya umirceni.

Tafiyar kusa minti uku mukayi muka iso wani babban parlo wanda ya take na sama haduwa,tsayawa fadin tsaruwar parlon da dukiyar da aka kashe ma parlon b'ata lokacine a tskiyar parlon ya tsaya nima na tsaya kaina kasa.

Dan durkusa yayi yana cewa.

"An kammala komai yanda kace Oga,Umirninka kawai muke jira."

Nidai banji abunda Ogan nashi yace mashi ba naji kawai an kama hannuna anyi dani cikin wani daki a ajiye ni saman gado sannan mutumin ya fita ya sayo dakin,kuka na fashe da shi ina cewa.

"Inalillahi wa'innalaihirajiun!na shiga ukku ni Kulu wai maike shirin faruwa dani."

Had'a kaina nayi da gwiwar kafa ta ina mai rushewa da wani irin kuka,na rasa gane mai ke shirin faruwa dani wata qaddarace wanann take neman kutsoman a cikin rayuwata ta wargaza man farinciki da duk wani dan uwana wanda yake da alaqa dani.

Su waye wa'annan mutanen mai nayi masu?maiye tsakanina dasu da suka daukoni suka kawo ni nan,babu Imani babu tausayi a wani hali su Mama suke bama kamar Yaya Haidar da yake bala'in sona nasan yana can cikin wani hali na rashina da yayi,sake rushewa nayi da sabon kuka Ina cewa.

"Allah ka taimakeni."

★★

"Aisha har sau nawa zan ce maki ki rage ma kanki wanann damuwar?damuwa ba zata amfanemu da komai ba ya kama ki gane inda na dosa addu'a dai itace mafita a garemu ba abunda Hauwa'u take bukata a wajenmu sama da addu'a amman wanann koke koken ba mafita bane Kinga yanzun abunda kika jawo ma kanki da wane zanji da b'atan Kakata ko kuma da ciwon zuciyar da ke damunki yanzun yana hanaki bacci."?

Ita dai Mama batace komai ba tunda Baba ya fara magana,hawaye ne kawai take sharewa ita mamaki suke bata idan suka ce ya daina kuka idan batayi kuka mai ake son tayi?ita fa uwa ce ita kadai tasan irin zafi da rad'adin da zuciyarta take mata,rabon da tayi bacci tun bacewata yanzun kuwa watana hudu da sacewa.

Bacci yayi kaura a idonunta addu'a yi yake da ace bata kukan da suke hanata da yanzun bata san a wani station take ba,kukan shi ne yake rage nata zafin da zuciyarta take mata,da sun san yanda kukan yake taka rawa waje rage mata rad'adin zuciya tabbas da basu matsa mata akan ta daina yin shi ba.

Taya za'ayi ace danka na cikinka wanda kasha wahala wajen daukar cikinshi kayi rainon cikinshi kazo kuma kayi nakuda wajen haihuwarshi kasha wahala sosai kafin Allah ya nufa ka haifoshi kuma kazo ka shayar dashi har na tsawon shekara biyu banda hidimar kashinshi fitsarinshi da kuma kula da lafiyarshi.

Idan bai lafiya kaima baka da ita baka da gurin da ya wuce kaga danka a cikin walwala da farinciki,kasha wahala matuka wajen kula da tarbiyar shi azo rana daya lokacin d'aya wasu mugaye wanda ba'asan su waye ba su dauke maka danka kuma a hanaka kuka ai abunda ba zai tab'a yuyuwa bane,dole tayi kuka kuma dole ta kasance a cikin damuwa mai tarin yawa,dole hawan jini da ciwon zuciya su samu mazauni a cikin jikinta ita da fita damuwa kuma sai Jidda ta dawo gareta taga lafiyarta taga ba abunda akayi mata sannan zata natsu,amman mudun ace gudun jininta na wani waje cikin halin k'ak'anikayi kuma ace karda tayi kuka ba wannan maganar.

Shima Baba bai sake ce mata komai ba har suka iso gida da kanshi ya bude mata mota ta fito ya dauko magungunanta suka shigo gida tare,sannu da zuwa Meenat tayi masu da yauwa suka ansa sannan suka samu waje suka zauna abinci Meenat ta kawo masu sannan ta bar parlon.

Baba da kanshi ya zuba ma Mama abinci sai da ya matsa ma Mama taci abincin ba laifi sannan ya bata magani tasha saukowa yayi yana zama kasa yana kamo hannunta yace

"Duk tsanani yana tare sauki,in shaa Allah komai zai zama tahiri Allah ya baiyana mana ita sannan kuma mu musulmaine ya kamata muyi Imani da qaddara maikyau ko mararkyau Imani ba zai cika ba sai kayi Imani da qaddara wanann kuma qaddararmu ce kuma jarabawa ce sai muyi addu'a Allah ya bamu ikon cinye jarabawa."

Share hawayenta kawai tayi yana cewa.." in shaa Allah zanyi kokari naga na bar shiga damuwa, amman kubar cewa na bar kuka dan Allah,dan kukan yana rage man rad'adi sosai akan wanann lamarin dan Allah."

Murmushi Baba yayi yana cewa.."shikenan hakan ma yayi nidai fatana ki daina wannan damuwar."....."zan daina damuwa kamar yanda kaima nike son ka daina taka damuwar."

Shafa fuskarta yayi yana murmushi yace.."In shaa Allah ranki ya dad'e."

★★

Durkushe nike ina kuka,banji budewar kofar ba sai dai kawai nayi an rungumaini tsam ana sinsinar man wuya,firgigi nayi Ina mai kokarin ture wanda yayi hunging din nan, kasa tureshi nayi dan ba rikon wasa yayi man ba.

Kuka kawai na fashe dashi Ina girgiza kai,d'agoni daga jikinshi yayi yana kure ni da Ido murmushi yayi yana mai bin jikina da kallo,dago kaina nayi Ina saukewa a saman fuskarshi zaro Ido nayi Ina rushewa da sabon kuka nace.

"Ahmad."

Dariya ya fashe da ita yana cewa.

"Tabbas nine nan Jiddah."

Shuru yayi yana mai ingizani saman gado ya fadawa ya haiye kaina kuka na fashe da shi ina bugunshi nace.

"Kaji tsoron Allah Ahmad mai nayi maka mai yasa kake son keta man hadi ka tuna abunda kayi sai anyi maka baka gudun kaima ayi ma naka."

Buge man baki yayi yana cewa.

"Yi man shuru munafika ke nan har ta Allah ce?wato ni zakiyi ma wa'azinki na banza ko?kin manta nasha ganinki a saman kato,nasha ganin kina tsotsar bakin Kato amman da an tab'a sai ki fara cewa Allah ya hana to wallahi ba abunda zai hanani dandanaki."

Tura bakinshi yayi cikin bakina yana tsotsa dan kanshi ya fiddo bakinshi yana cewa..."har kin manta da wuri haka Jiddah?okay soyayya ta rufe maki Ido kin manta da alkwarin da nayi maki a baya ba ko?to bari kiji ni Ahmad bani yafiya kuma bani manta ranar ramuwa."

Kiss ya manna man a baki yana lasar gefen kunnena ya cigaba da cewa.

"Daman ai na gaya maki Koda tsiya ko da arziki sai na cima manufa ta a kanki Kai kuma kince kin gani to gashi kin gani yar'karamar karuwa."

Kuka nike ina bashi hakuri shi kuma sai dariya yake kyalkyalawa can yayi shuru yana cewa.

"Yanda Babanki da Yayanki suzo suka zubar man da mutunci da kima a idon mahaifina suka sa na zubar da hawayena, wallahi nima sai nasa sun zubar da hawayensu sai na sakasu bakin cikin da har abada ba zasu daina yin shi ba."

Hade hannuna nayi waje d'aya Ina cewa.

"Dan Allah kayi hakuri karda ka keta man hadi na yarda ka zaneni kasa a cigaba da watsaman ruwan sanyi mai kankara amamn banda abunda kake kokarin aikatawa a gareni Ahmad na tuba ka yafe man ba zan sake ba."

Bugu hannuna yayi yana fisgar hannun rigata take ya balle daman ba wata rigar arziki bace kuka na sake rushewa dashi Ina bashi hakuri Ina k'are kaina,wasga man wani mari yayi da na hana ya balle man breziya duk da zafin da marin yayi man amman ban daina kokarin kare kaina daga Ahmad ba.

Da karfi da bala'i ya cire duk kayan dake jikina ya barni tir haihuwar uwarta hannu nasa Ina kare kirjina Ina mai bashi hakuri,Mari kuwa nasha ba adadi babu Imani babu tausayi a lokacin a ranar Ahmad ya rabani da *BUDURCINA* Ina ji Ina gani Koda ya tashi hakeman bai bini a hankali ba haka ya hakeman babu tausayawa kamar ya samu tsohuwar mace wanda ta kware a fanni saduwa,ban sake sani inda kaina yake ba sai da na naji saukar ruwan mai bala'in sanyi firgigi nayi na farka Ina sakin kuka.

Kuka nike cin karfina amman saboda nayi kukan har muryata ta dose ko sautin kukan bai fita a makoshi kawai yake tsayawa sai hawayen da ke zuba.. k'ara watsaman wani yayi kasa Koda motsi nayi sai zuba mashi ido da nayi ina hawaye,motsi mai karfi bani son nayi saboda wani irin rad'adi ba na wasa ba k'asa na yake man.

Ina kallon yanda Ahmad yake watsaman ruwan kankara sai da ya watsaman kusan sau biyu sannan yayi man tsaye sai da na shiga cikin wani ruwa.. dakyal na tashi Ina shiga ruwan rintse idona nayi ina karkawa dan ba ruwan komai bane yasa na shiga sai ruwan sanyi ga ronikan da yaji man kacakaca.

Ina shiga ruwan ya koma kallar jini yana tsaye kaina a cikin toilet din fuskarshi murtuke take babu annuri a samanta haka ya dunga sa Ina shiga ruwan sanyi da masifa sai da jinin da ke fitowa daga k'asa ya daina fita sannan yace na fito girgiza mashi Kai nayi Ina cewa.

"Inason nayi wanka tsarki nayi sallah."

Dariya ya fashe da ita yana cewa."wanka tsarki da sallah ko?to ba zakiyi su ko kinsan na gama dake Jiddarh?ai yanzun aka fara wasan ba'ayi komai ba Jiddah mai na dandana da har zan barki kiyi wani wanka to bari kiji yanzun nan a bakin aiki zamu koma."

Girgiza mashi kai nike ina had'a mashi hannu waje d'aya alamar roko nace.."na tuba Ahmad kayi man rai,wallahi mutuwa zanyi idan ka sake hakeman ka barni haka ka maidani wajen iyayena tunda burinka ya cika ka samu abunda kake so."

Janyo gashi na yayi yana fito dani a cikin toilet din yana cewa.."kinsan yanda kike da dadi kuwa Jiddah?kinsan yanda najiki kuwa Jiddarh? kin taba ganin inda aka raba shazimami da sugar?karda kisa ran zaki koma gida anan kusa sai na gama fansar rashin kunyar da kikayi man, sannan kuma na fansar rashin kunyar da wannan shashashan saurayinki yayi a kanki."

Jafeni yayi saman gado yana hayewa kaina ya fara tsotsar boobs dina kamar ya samu alawa ga wani irin zafi da suke man ji nike kamar zasu tsinke dan zafi,kuka nike ina had'a shi da Allah yayi hakuri ya kyaleni zan mutu zafi...amman yayi burus dani ya cigaba da cin karenshi babu banbaka a kaina sai da yayi round yafi ukku a kaina sannan ya sauka bansan sanda ya sauka a kaina ba na dai ji yana watsaman ruwan kankara kamar yanda yayi man da farko.

Yana ganin na farfado ya ficewarshi daga toilet din, had'a kaina nayi da gwiwa Ina kuka ji nike daman na mutu addu'a nike a lokacin Allah ya kawo mutuwa ta tafi dani in huta,dan komai na duniya fice man yayi a rai nasan ni tawa tazo karshe tunda har Ahmad yayi man wannan torzarcin tabbas banda saurin wani hope a rayuwata ya rabani da martabata ta 'yamace.

Rayuwa tayi man cak sai da nasha kukana sanann na rairafa na had'a ruwa again ruwan sanyi ne dan babu ruwan zafi a toilet din duk wata na'ura da take fitar da ruwan zafi na gwada kunnata a toilet din bata aiki.

Ga gabana yana man wani irin zafi kamar ana watsaman dakaken barkono haka nike ji,dan har wani kaikayi naji yana man abunda ban tab'a ji ba kenan a tare dani a yau ,ba yanda na iya haka nayi wanka tsarki na samu towel na dauro na fito Ina jan kafa.

A hankali a hankali nike tafiyar dakyal dakyal dan duk motsawa sai na saki Kara Ina harfa hannu a haka da taimakon Allah na samu na fito daga bathroom din.

Wata fisgaigas rigace na gani shararar amman har kasa take sai dai sunan kawai ka saya jikinka da kaya amman babu tsiyarcin da zata boye saka rigar nayi nasan nidai aka ajiye mawa,babu pant balle breziya ita kadai ce zilinta.

Da rairafe na Kara'sa bakin dirowar da ke a cikin dakin duk wanda na buda a kulle take sai ta karshen na tadda a bude hijab ce kwaya d'aya jal daga ita babu komai a cikinta.

Dauko hijab din nayi na saka daga zaune sanann na kalli gaba na kabbara sallah ina sallah Ina kuka Ina makarkarwar sanyi dan zaizabi nike ba na wasa ba,daga zaune na samu na gama sallolin da nasan suna kaina sannan na kama kuka ina kaima Allah kukuna.

Wata irin yunwa nike ji ba ta wasa ba,daman daga ruwa ba abunda ake bani tunda nazo gidan,sai kuma abincin da ko loma ukku ba'a barina nayi ake anshewa kuma sau biyu a sati ake bani abincin.

Nabi na rame na lalace babu abunda yake yawa a fuskarta sai dogon hanci da daradaren idanu kamar wata mujiya,kwantawa nayi a saman tiles din Ina hawaye ina gaya ma Allah damuwata...kuka na fashe dashi Ina shafa cikina da yake man kugi ga kuma zafin da kasana yake har yanzun dan zafin baya ragewa sai ma gaba yake.

Ina kwance naji an bude kofar an shigo,zama yayi gefen gado yana kallona yace.."ke taso kizo nan,ki tabbatar kin cire wannan hijab din kin maidata inda kika ganta munafika."

Rintse idona nayi inajin yanda Ahmad yake zagina hawayena na share ina tashi zaune dakyal na cire hijab din na saka a laka sannan na tashi Ina jin kafa har na iso gabanshi na tsaya,kafa yasa yana tadiyeni na fadi rijab a gabanshi Kara na saki Ina cewa.

"Allah ya isa tsakani na dakai in shaa Allah ba zaka gama da duniya lafiya ba kuma tun anan duniya sai Allah yayi man sakayya Allah ya isa fasiqi mazinaci."

Wani wawan mari ya wanka man kafin na dawo ya sake daura man wani sanda zai Kara dauraman na ukku take jini ya balle a hanci kamar an kunna famfo.haka jini ke zuba abunda ban tab'a yi ba a rayuwata wato habo bai damu da jinin da ke zuba daga hancina ya cigaba da wanka man maruka kamar ya samu jakka ba dan adam ba.

Luuuu na tafi na fad'i sumaimiya tashi yayi ya zare belt din kufunshi yana ajiyewa gefe ya shiga toilet da ruwa ya fito yana kwarara man shi daga tsaye sai da ya juya ruwa jugs biyu ban farfado ba ana ukku na sauke ajiyar zuciya Ina rushewa da kuka.

Wurgar da Jugs din yayi ya cigaba da labtaman belt ko ina daman ba wata suturar kirki bace a jikina kuma ya watsaman ruwa rigar ta lafe a jikina haka yai ta labtaman belt ta ko Ina nidai idonuna sun bushe babu ko digon hawaye a samansu sai dai boye fuskata da nayi dan karda ya bugarman ido,sai da yayi man jinajina sanann ya yarda belt din yana sa hannu ya keta rigar jikina biyu yayi wurgi da ita Ina a cikin halin rai ko mutuwa Ahmad ya k'ara hakeman yanda ranshi yaso ya gadama yake sukuwa a kaina.

★★★

Zama Baba yayi saman kujera shigowarshi kenan sauke ajiyar zuciya yayi yana kallon Mama yace.."kin san waye yayi sallama dani."? Girgiza kai Mama tayi tana kawo mashi ruwa mai sanyi ansa yayi sai da ya shanye ya ajiye kofin yana cewa.

"Alhaji Bala Mato ne."

"Allah sarki mutumin kirki shidai ba ruwanshi bai da kyamar tallaka."

Murmushi Baba yayi yana cewa.."kwarai kuwa ai Alhaji Bala Mato ba abunda zance dashi sai Allah ya saka mashi da alkhari ya biya mashi bukatu na alkhari tunda Kakata ta tab'a yake nuna damuwarshi kusan kullun sai munyi waya yaji ya ake ciki haka ma d'anshi Ahmad wallahi yaron nan da ya ganni zaizo ya duka har kasa ya gasheni yayi ma Jidda addu'ar Allah ya baiyanata ai yaron kirki ne shima."

"Hakane kam nima nan ya kawo matarshi har cikin parlon nan tayi man jaje ni banma ganeshi ba sai da na tambaya yace ai Ahmad dan gidan Alhaji Bala Mato nace Allah sarki nagode sosai sau biyu yana kawota wallahi."

"Ai mutanen kirki ne gaskya Allah dai ya baiyanata a duk inda take ya kuma Kareta."

Dan shuru Mama tayi sai kuma ta goge hawayenta tana ce ma Baba.."Alhaji wallahi kwanan nan gaba sai faduwa yake dan kuwa yau sai da nayi mafarkin Kulu tana kuka tana cewa nazo na taimaketa wallahi nidai mafarkin nan ya tsayaman rai dan ban tab'a yin mafarkin Kulu ba tunda aka saceta sai yau Alhaji."

Shuru Baba yayi yana kallonta can ya furzar da iska yana cewa.."ki kwantar da hankalinki in shaa Allah ba abunda zai samaita sanann kuma ai mafarki ba gaskiya bane sai ayi addu'a fatan kinyi addu'ar mafarki da kikayi mafarkin ko.?"

Girgiza kai tayi tana cewa.."wallahi Alhaji banyi ba,kawai dai na tashi Ina innalillahi wa'innalaihirajiun abunda nace kenan sai na yo alwallah nayi sallah."

"Ba laifi ai tunda kince innalillahi ai kin gama fadin komai Madam,ai matsalar rashin yin addu'ar duk da mafarki ai ba gaskiya bane."

"Hakane kuma Allah yayi mana da kyau ya baiyanata Ina lissafi wata shidda kenan da sacewarta shuru ba

Please Login or Register in order to submit comment