Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka hada ido dashi duk da daman inajin jikina kallona yake dan gangar jiki ta sanar dani,dan murmushi kawai nayi shima murmushin yayi yana man sign da na daina damuwa karda shima na sashi a damuwa.

Murmushi kawai na kuma sakar mashi Ina duba time 3 har tayi harda wani abu mean sauran yan minti fa ya rage ya tafi ya barni nidai kam bansan ya zanyi ba..cigaba da firarsu kawai sukayi sai 3:30 sanann ya tashi ya tafi dan ya shirya nima tashin nayi na shiga room dinmu.

Sai da na dan matse kwalla na sannan na shiga wanka cikin yolk din laces na shriya dinkin coke shape ne sosai rigar tabi jikina ta fiddo man da shape dina ,ganin 3 harda minti 55 na tashi nayi sallah first sannan na shirya wayata naga tayi haske na duba murmushi kawai nayi na dan fasa turare sannan na dako gyalena na fito.

Har airport muka rakashi da ni da Yaya Muhd kawai muka tafi..Muna zuwa airport din Yaya Muhd ta fita motar yana answering din waya,Shima Yaya Haidar fitowa yayi ya dawo baya yana kallona sai kuma ya kamo hannuna yana kissing din kumshin hannun, shafa fuskata yayi a hankali yace.

"Zanyi kewarki Babe,zanyi kewar wannan kyaun naki Babe da komai naki take care take care take care please and please Babe I love you muah." Ya sakarman kiss a lips lumshe idona kawai nayi Ina murmushi mun dade a cikin mota muna jimamin tafiyar da zaiyi sai da aka fara announcement din za'a fara tafiya ya fiddo wasu kudi masu yawa ya damka man a hannu yana cewa.

"Ki fara manage da wannan 200k ce kafin na dawo."

Kallon kudin nayi Ina kallonshi sai kuma na girgiza kai Ina cewa.

"Yaya sunyi yawa sosai."

Dan daure fuska yayi yana cewa.

"Nine nan nike da hakin yi maki komai Jidda saboda an bani ke iyaye sun gama magana karatunki kawai ake jira ki karasa na dan watan ni ke ida zama tawa,dan haka karda ki sake ki sake yi man haka karda ki sake ki tambayi Baba kudi ko Mama ko kuma su Muhammad komai kike so ni zaki tambaya a shirye nike nayi maki komai kike so a duniya Ina sonki inasonki Ina kaunarki Jiddarh."

Fadawa nayi jikinshi Ina kuka Ina cewa Ina kaunarshi sosai Nima dakyal ya rairasheni ya fito Ina kallo ya shiga jirgi nan na Kara sakin wani sabon kuka Muna tsaye suka tashi suka tafi,nan na Kara volume din kukana har muka iso gida Ina kuka tun Yaya na lailashina nayi shuru har ya fara yi man fad'a akan na isheshi da yankoke koke.

Koda muka dawo gida ban tsaya sauraren kowa ba na shige room Ina kukana ban bar kuka ba sai da ya kirani ya gayaman har ya sauka sanann yace na bar kukan hakanan ya isa haka ..lokacin Sallah yayi muka kashe wayar bayan isha'i ya kirani muka sha wayarmu sai wajen sha biyu muka ajiye wayar cike da kewar juna.


*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Editing❌*

*101-110*


Yau da wuri na tashi da yake Ina da lecture ten,lokacin da na gama hada mana breakfast takwai ta wuce wanka na shiga na sa kaya sanann na fito na zauna na fara breakfast Ina cikin yin breakfast Meenat ta fito itama cikin shiri kallonta nayi Ina cewa.
"Daman kina da lecture yau."?
Zama tayi tana hada tea, murmushi tayi tana cewa.."Ina kwana Yaya Jidda." Hadiye abincin bakina nayi Ina ansa gaisuwarta time ta kalla tana cewa.
"Wallahi fixing din lecture din akayi mana daga dawowa har an fara had'a mana zafi."
Murmushi nayi Ina cewa.."ai daman ku manya ne barrister ce fa nan da kanta."
"Amman kafin na zama Barrister din ansha wuya ko Yaya Jidda? daga wannan sai wanann har na gaji da karatun nan wallahi Wanda bai karewa."
Dariya nayi Ina tashi nace.."Daman aiki idan yazo gaban goshi ai yafi zafi duka duka baifi yan shekaru ki gama ba."

Itama tashi tayi tana daukar back bag dinta tace..."amman kafin yan shekarun suzo ansha wuya sosai Yaya Jidda." Har na nufi kofa na waigo Ina kallonta dan waro idona nayi ina cewa.."ya da tsayuwa kuma?ko ba ten kike da ita ba."? Kallon time tayi tana cewa ."ten gareni mana,wai Baba ya fito ya bamu kudin transport ko."?

"Okay taho mu tafi akwai kudi a wajena."

Tahowa tayi muka tafi muna fitowa muka tadda Wasi tsaye tana waya sai murmushi take ga dukan alamu da Yaya Auwal take waya dan daganin wanann wayar ta masoya ce murmushi nayi Ina cewa.

"Morning yanmata."

Waigowa tayi tana cewa.."ai yanzun nike shirin shiga na fito dake." Turo baki nayi Ina cewa.."duka duka yazun 9:30 tayi har na makara kuma."

"Kwarai kuma kina da tabbata cin zamu samu naped kan lokaci."? gaba nayi ina cewa.."ai yanzun gashi nan zaki sa muyi lating din mai hujja ba." Bayana tabi tana cewa.."Meenat wanann semester kenan kina da lecture din safe kema." Murmushi tayi tana cewa.."aikuwa rabin lecture din wanann na safe ne amman bamu da lecture yau ma kawai dai fixing akayi mana."

"iKon Allah har an fara fixing kenan daga dawowa hutu to Allah dai ya bamu sa'a baki d'aya."

Da Amin muka ansa muna ta famar tsada naped amman shuru bamu samu ba,cikin ikon Allah sai ga Yaya Auwal ya tsaya yana cewa.

"sannunku iyayen yan makara ."

Tare mukayi dariya Ina cewa.."Laaa Yaya Auwal wallahi Wasi ce ta jamana wanann makarar." Kallon Wasi yayi yana murmushi langwabar mashi da Kai tayi tana turo baki tace.."amman Babe ai kasan komai tunda kana jinmu a waya ko."

Gira d'aya ta dage mata yana cewa.."amman ai waya kika tsaya da tsigumi ko Sweetheart."

Turo baki kawai tayi tana harfe hannu,fakaitar idon Yaya Auwal nayi Ina mata gwalo,kukan banza ta barke dashi tana cewa.."Babe ka ganta ko."?

Dariya nayi Ina bude baya na shiga nida Meenat,itama ta shiga gaba sai zabga mashi shagwabe yake shi kuma yana ta lailashi yana maida laifin a wajena.

Bayan ya saukemu ya wuce wajen aiki,da yake ba wata lecture bace mai tsawo zamuyi one hour ce ,ana gamawa muka je wajen project supervisor dinmu muka anso gyaran chapters din akayi mana sannan muka fito bamu tsaya bata lokaci ba muka dawo gida.

Tunda Yaya Haidar ya tafi kullun cikin waya muke bamu da aiki sai zafin waya kamar baya tausayin katin da yake lodawa a wayarshi..idan kuma muna bukatar ganin juna sai muyi video call aikin Kenan...idan kuma Ina da test da shi nike karatun dare yana nuna man wani wajen duk da ba bangare d'aya muke karantawa ba amman haka zai koyaman har na gane ni har mamaki yake bani ba.

Shakuwa mai karfi da soyayya ta Kara kullewa ban iya yin Koda 2mn ban jin muryarshi ba,idan har na wuce 5mn bamuyi waya ba har wani malaria malaria nike ji sai na koma sukuku gani nan kamar ni kamar ba ni ba wata walwala haka zan kasance..har mamaki nike ba yan gidanmu yanda muke soyayya da Yaya Haidar kamar bani ba shima kamar ba shi ba mun wani zama chimgem ko wani lokaci muna manne a waya.

Kallon yanda ya tsare parlon nayi da yanda na cika dinning da iyayen warmers sai jugs kamar zan tarbi mutun goma dasu..boner na kunne sanann na wuce room dan shiryawa nasan sun kusa isowa gida yanzun tunda tun dazun Yaya Bash ya tafi daukoshi a airport.

Kayan da zan sa na dauka na kaima hancina kamshi suke kamar mai dan cikin kamshi yau suka wuni,zama nayi bisa kambasa sai da kamshi ya gama turnike ko Ina a jikina sanann na tashi na fara shafa humra mai kyau da kamshi na bata lokaci sosai wajen shafa kayan kamshi sanann kuma nayi zaman kwaliya.

Zaunawa nayi na dandasama kaina kwaliyar yar'ubansu daman na iya makeup sosai kuma shi Yaya Haidar mutane mai bala'in son yaga mace na kwaliya banjin komai ya kashe maki ko wane indai zakiyi kwaliya..da ban damu da wata kwaliya ba amman tunda na lura Yaya Haidar yana son kwaliya dole na daura ma kaina sonta nima dan Ina son duk abunda yake so.

Bayan na gama na samu sweet mai dadi da dadin kamshi na fara tsotsa Ina lumshe Ido dan kamshin mint flavor take har wani sanye kasan makoshi yake..sai da nasha kusan biyar sannan na gama na tashi zan tafi parlon dan tun Ina daura dankwali naji shigowarshi.

Zaune yake yana danna waya da yake ba kowa parlon tunda suka gaisa da Mama ta koma room dinta daman Meenat tana school dan tana yin lecture din Friday Saddiqa da Rukky da Manu da Usman da Hamid kuma suna isilamiya.

Cikin takona mai daukar hankali na fito Ina jefarshi da murmushin da ni kaina nasan idan nayi mashi shi yana rasa control din Kansa a kaina,tunda ya d'aga Kai yana kallona bai kauda kanshi ba har na iso gabanshi..nan ma bai fasa ba sai da nayi weaving din fuskarshi Ina yin farrr da Ido na wani juya gabanshi nace.

"Welcome PP."

Dukawa nayi kasa a gabanshi Ina kama hannunshi na cigaba da cewa.

"Ina wuni ya hanya."

Kissing din hannun kawai yayi yana sauke ajiyar zuciya yana kuma kallon kumshin da nayi a saman hannun,duk da nike brown skin amman black henna din yayi kyau sosai ga kuma ja da nayi a cikin tafin hannunna ya dad'e yana kallon kumshin yana shafa hannun kissing din hannun yayi yana murmushi sai kuma ya kalleni ya sakarman murmushi.

Kissing din koshi na yayi yana magana a hankali kamar yana rada yace.."Allah yayi maki albarka Babe..kinyi kyau sosai I love you and I miss you."

Kwantar da kaina nayi a saman hannunshi ina a yanda nike a tsugune sai kuma ya lushe idona sai murmushi kawai nike shafa gefen fuskana yayi yana d'agoni ya kalleni yace.

"SP maiye sirrin."?

Harfe hannu nayi Ina langwabar da Kai gefe nace.

"Namai kenan PP."

Dan jan hancina yayi yana cewa .

"Na komai ma,SP kin chanza just two month nayi ban ganki ba,amman kin chanza sosai."

Kashe man ido yayi yana dan daura hannunshi saman boobs dina yana cewa.."haddata My friends sun Kara girma fa sosai SP gayaman maiye sirrin."

Rufe fuskata nayi Ina murmushi tashi nayi Ina cewa.

"Babu wani sirrin PP ai kaine sirrin idan ma haka yanda kike kula dani ai dole kwanciyar hankali ta baibayeni banda damuwar komai tunda Allah ya mallaka man kai na fi ko wace mace sa'a da na samaika Ina kaunarka PP."

Kissing din bakina yayi yana dan tura hancinshi kadai a bakin ya shako kamshin mint din da bakina yake ya lumshe Ido yace.

"Ina kaunar kamshinki Babe komai naki daban yake da sauran ai ni nafi kowa sa'a da na samaiki a matsayin wanda zata san sirrina SP."

Murmushi kawai nayi na kama hannunshi muka je dinning naja kujera na zaunar dashi,da kaina na zuba mashi farfesun kaji da Irish na ajiye gabanshi sai na tsiyaya mashi lemun mint...zaman nayi Ina kallonshi nace..."Dan sauraniya ga fa abinci aci abinci sai aje anyi wanka a huta."

Turo baki yayi yana cewa.."Nidai Babe sai dai ki bani da kanki hannuna ya gaji sosai."

Hura mashi iskan bakina nayi Ina cewa.

"I love you."

Lumshe Ido yayi yanaman murmushi kawai ya langwabar da Kai alamun dan Allah shi dai na bashi..gyara zama nayi na fara bashi da kaina yana ci yana lumshe Ido tsabar dadin da abincin yayi sai da na tabbatar da ya koshi sosai sanann na kawo mashi Loma ta karshe ya rike yatsun a cikin bakinshi yana wani tsotsa kamar ya samu chocolate or sweet lumshe idona ina cewa.

"Ashhhh PP."

Bai sakin hannun ba sai da ya tabbatar da ya tsotse yatsun tas sannan ya sake shi murmushi na sakar mashi Ina daura mashi cup din juice din a hannu,makale kafad'a yayi yana cewa..."Nidai A'a SP." Zaro Ido nayi Ina cewa.."please kasha ko kadan ne mana PP kaifa nayi mashi nasan kana son mint juice."

Langwabar man da Kai yayi cikin shagwabe yace.."zan sha amman sai ki dunga zubashi a bakinki ki saman a bakina idan kuma ba haka ba nidai na koshi kawai."

Zaro Ido nayi Ina kallon parlon Ina kallonshi ,Shima zaro Ido yayi yana kuma turo baki gaba yace.

"Ai shikenan tunda daman ba so ake nasha ba nagode."

Dafashi nayi Ina cewa.."Ayyya PP kaga a gida muke taya zan iya feeding dinka mouth to mouth idan wani ya shigo ya ga bakina cikin baka Ina dura maka juice kasan za'a samu matsala."

Kureni da Ido yayi sai can muka yace.."ai nafi son a samu matsalar SP,C'mon taho ki bani yanda nace idan aka gani Kinga sai ayi aurenmu gobe gobe ni hakan ma zaifi yi man dadi."

Dan shuru yayi sannan ya cigaba da cewa.."wallahi Jidda a matse nike sosai aure nike so yanda baki tunani tsoro nike karda hakuri yazo karshe bansan barnar da zan tabbka ba shiyasa nike son yau nayi magana da Baba ansan yanda za'ayi nidai na kusa mutuwa akan bukatar aure."

Marairaice fuska nayi Ina cewa.."Mahakurci mawadaci PP saura wata d'aya fa mu gama exams Muna gamawa na yarda ko da kwana d'aya ne a daura mana aure kuma zan baka duk farincikin da kike bukata myluv."

Kallona ya dunga yi can ya furzar da iskan bakinshi yana cewa..Allah ya k'ara man hakuri Babe yanzun dai a bani lemu ko kuma nace na koshi kuma nayi fushi."

Wayyo Allah na PP wallahi nidai tsoro nike ji sosai fa." Nayi maganar Ina Kara matsawa a jikinshi Ina kallon idonshi, Shima kallon idon yayi cikin nawa yana cewa.

"Okay shikenan a barshi na koshi hakan yayi maki ko."?

Girgiza kai nayi Ina tashi zaune daga jikinshi na janyo glass cup din da na zuba juice din ciki kallonshi nayi sai kuma na kalle juice din shima ni yake kallo yana jiran yaga shin zanyi abunda ya sani ko kuwa ba zanyi ba.

Kwafa juice din nayi a bakina na surbe na hadiye yayi man dadi sosai dan sai da na lumshe Ido kuma sanyin yayi man yanda nike son shi dan nasan Babyna baya son sanyi sosai.

Matsawa nayi sosai a jikinshi yana gyaraman zamana a saman cinyarshi na daura bakina saman bakinshi budewa yayi ya tura bakin cikin ina dura mashi mint din a hankali sai ansa yake yana lumshe Ido yana shafa bayana.

Haka na dunga bashi mint din yana sha har sai da ya kusa anshe fiye da rabin juice din sannan yace ya koshi,amman bai bari na ciro bakina ba daga cikin nashi ya cigaba da tsotsa yana lumshe Ido,ni kuma nayi lamo a jikinshi Ina ansar sako dan shap na manta a wani waje muke bani ganin komai sai PP banjin komai sai PP,karar bude kofar parlo da akayi ya dawo damu da ga duniyar da muka lula zaro Ido nayi Ina kallon kofar kamar yanda shima Yaya yake kallon kofar..

Kallon kofa kawai yake yana Sosa kanshi ni kuma rasa yanda zanyi da raina nayi ga wata kunya da ta rufe ni,ida shigowa tayi cikin parlon tana murmushi tace.."sannu da zuwa Haidar." Murmushi yayi yana cewa.."Yauwa Meenat yan makaranta ya karatun?hope kina maida hankali sosai." Itama murmushin tayi tana cewa.."Alhamdullahi Ina maidawa sosai ma Yaya." .

"Okay Allah ya baku sa'a baki dayanku." Da Amin ta ansa tana wucewa ciki,sauke ajiyar zuciya nayi Ina k'ara godema Allah da Meenat bata iskeni saman cinyar Yaya ba yana tsotsar bakina , k'ara godema Allah nayi da yake parlonmu idan aka shigo ba'a hangen dinning har sai an shigo ciki sosai to tana bude kofar kafin ta ida shigowa na sauka jikinshi na koma saman kujera na zauna shi kuma ya samu ya saita natsuwarshi yana kurbe juice a hankali a hankali.

Jan hancina yayi yana cewa.."sannu to matsoraciya." Lumshe Ido kawai nayi ina Kara sauke ajiyar zuciya dan na tsorata sosai Allah yasa ni,da ta ganni bansan da wani ido zan kalli Meenat ba,nasan take mutuncina zai zube a idonta da na bani.

Hararar wasa kawai nayi mashi Ina tashi nace.."Naji bakomai ai tsoro halak ne, yanzun kaje kayi wanka ka huta ko kafin Yaya Muhd ya dawo daga wajen aiki ya kuma hanaka hutawa."

Langwabar da Kai yayi yana cewa.."angama ranki yadade abunda kikace ai haka za'ayi Babe." Tashi yayi ya tafi bangaren maza har bakin kofa na rakashi na juyo ban yarda na kara fita waje ba nasan Muna shan kwanar da zata sadamu da bangaren su Yaya sai ya matse ni a bango ya cakula shiyasa na tsaya a bakin kofa duk da ba haka yaso ba,ban yarda na kalli fuskarshi ba balle har naji tsausayinshi na bishi.

Bayan na dawo gyara parlon nayi da dinning area din na wuce room dinmu zauna na tadda Meenat tana duba wata handout da yake ankusa fara exams.

Kallona tayi tana murmushi tace.."kinyi bala'in kyau Yaya Kulu ba karamin dacewa kukayi ba da juna keda Yaya Haidar Allah ya kaimu lokacin bikin nan naku lafiya musha shagalin baki."

Dariya kawai nayi Ina cewa.."Amin Amin barrister Aminatu Abdullah jibir." Girgiza kai kawai tayi ta cigaba da karatunta nima tashi nayi na shiga nayi wanka na fito na sake shiryawa cikin wata atamfa dinkin riga da sakit sai dai banyi kwaliya irin ta dazun ba cheap kawai na shafa ma lips dina na daura dan kwali na fito na fada kitchen dan girka mana abincin dare.

Tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa nayi mana taji ganda da kafar sa..bayan na gama nayi mana papaya juice na saka a freeze sannan na fito na koma room Ina yin alwallah nayi sallar mangariba ban tashi ba sai da nayi isha'i sannan na shiga wanka bayan na fito na shirya cikin material marar nauyi na fita parlo.

Zaune na tadda duka gidan a dinning suna cin tuwo harda Yaya Haidar din,nima ida karasawa nayi na zauna Ina gaishesu,kulli daya na zuba sai uwar miyar da na zubga dan ni gwanace a wajen shan miya ni kaina na sani.

Bissimllah nayi na fara cin ta gefen Ido na lura da irin kallon da Yaya take man yana wani murmushi,dan turo baki nayi na cigaba da cin tuwona, murmushi yayi yana mai dan harboni da kafarshi ta kasan dinning nima rama nayi Ina mai mashi gwalo kasa kasa, murmushi yayi yana girgiza kai.

Nunawa nayi bansan yana yi ba na cigaba da cin tuwona..haka dai muka cigaba da soyayyarmu a boye ba tare da yan wajen sun gane abunda muke yi ba dan a natse muke cikin abincin gabanmu ba mai cewa muna tsokallar kafar juna ta kalkashin taburin cin abinci.

Kwanan Yaya Haidar biyu a gusau sannan ya koma Birnin kebbi sai da na kuka da zai tafi dan yan kwanan biyun da yayi wani sabon shafin soyayya muka bude mai tsayawa a zuciya.

Ba inda ya manta baije dani ba a yan kwanakin da yayi sai da muka kusan zagaye gusau dan ma ana matsalar tsoro shiyasa bamu Kai dare da mangariba ta gabato muke dawowa gida,saboda da lokacin aka fara wani abu wai shi kidnapped a gusau sanda akayi abun kusan kwana nayi Ina mamaki dan abunda muke ji na faruwa a kasasen waje sai gashi yazo a kasarmu a kasarmunma jaharmu a jaharmun ba bayan gidanmu na tsorota sosai a kan lamarin ainun.

Shiyasa ban yarda na biye ma Yaya Haidar muna kai mangarib waje ba,yau da ya yafi sai naji gani nan dai na zama wata irin duk wani jindadin rayuwa sai naga kamar ya janyesu ta tafi dasu ya barni cikin kunshi da dacin rayuwa.

Haka na cigaba da zuwa makaranta har aka fara yin covering din lecturer..har time table yan manna mana ko wane dallibi yasan randa zai fara exams da kuma randa zai gama exams naji dadi sosai naga timetable dan a cikin sati daya jal zamu gama exams dinmu mun zama guarantee student daman na gama projet dina tuni har banding duk nayi.

Randa muka fara exams a rana aka kawo kudin auren Wasi da Yaya Auwal har ranar auren yan tsada wata hudu ba karamar murna nayi ba da jin wannan labarin maidadi.

Dan yanzun soyayya suke kamar sun cinye juna baka cewa hadasu akayi dan kallo daya zakayi masu kaji sun burgeka soyayya suke maitsafa mai daukar hankali.

Daman Yaya Auwal professional ne akan soyayya sai kuma ya samu Wasi ita kuma Dr ce a fanni soyayya kuma sun fahimci juna ra'ayinsu daya ba mai jin kansu.

Nayi murna sosai hakama Yaya Haidar da na gaya mashi yayi murna sosai sai a sannan naki jin yana cewa anyi bakinmu da sati biyu za'ayi na su Wasi,nasha mamaki sosai dan ni banma san an tsada ranar aurena ba na dai sannan ankawo kudi.

Cigaba da exams mukayi kuma munata preparation din programs din da zamuyi na kammala jami'a sai Yaya Haidar ya bulla daga gefe yace bai yarda na je ko wane ba indai ya isa to babu wani program da zanyi attending ko ya yake.

Ba yanda banyi dashi ba amman yaki yarda daga karshe sai da rai ya b'aci akan na naci sai nayi da naga karamar magana zata koma babba sai na bashi hakuri nace na fasa zuwa event din.

Sai da nasha wuya sanann na samu ya sauko amman nasha jaraba da ace Ina kusa dashi maybe sai ya zaneni yanda yake balbalaman bala'i yana cewa.

"Da yake ni sakarai ne ko Jiddarh da zan barki kije wajen taron da za'ayi mata da maza kattin Allah su kama kalleman ke kinsan yanda nike kishinki kuwa?na lura har ynzun baki san ya nike jinki a raina ba haka kuma ya nike kishinki ba dan haka ki ajiye maganar zuwa wani partyn banza da wofi fatana Allah ya baki sa'ar exams ki gama lafiya ba tare da wani spillover ba shine yanzun fatana a kanki Babe."

Nidai shuru kawai nayi sai da ya balbala masifar shi sannan na bashi hakuri ya sauko muka cigaba da soyayyarmu.. dalilin kin zuwa itama Wasi tace ta fasa zuwa amman ita Yaya Auwal ya barta har kudin da ake bukata duk ya bata,Koda ta gaya mashi ta fasa sai da yayi mamaki ya San yanda ta sa abun a rainta da ya tambayeta dalilin fasawarta.

Sai ta ce mashi saboda dani ba zan samu damar zuwa ba,again mamaki yayi dan yasan lokacin da muna tare na tabba gaya mashi idan zamu gama degree ba events din da ba zanyi attending ba har ya kama yi man dariya ma.

Nan ta gaya mashi Yaya Haidar ne ya hanani zuwa murmushi kawai yayi dan yasan halin Haidar yasan waye Haidar tabbas duk cikin abokansu yafi kowa nuna zafin kishi,shi bai iya boye kishin shi a fili yana danne komai amman banda kishi balle kuma ni yasan son da Haidar yake man ko shi baiyi man rabinshi ba cewa yayi.

Shikenan ai tunda ya hana kawarki zuwa sai ku yi pictures dinku a gida idan kun dawo daga school kun huta."

"In shaa Allah haka nike son muyi Sweety."

Da yake mun samu interval din kwana biyu bayan mun dawo daga school ko kayan jikina ban cire ba na fad'a saman gado na kwanta sai bacci dan na gaji sosai da sosai da yake exams din 8 ce shiyasa banyi wani bacci ba cikin dare.

Dan wajen 2:30 na dare Yaya Haidar ya tadani dole sai da na tashi na yi karatu harda kuka nayi mashi ya barni na dan kara samun baccin zuwa hudu sai na tashi amman yak'i sai da na tashi na fara karatun.

Ga inajin bacci banda damar kwanciya dan Shima idonshi biyu inayin motsin shi da yake ba kashe wayar yayi a kunne a barta dan yasan hali yana kashewa zan koma baccina.

Ban kwanta ba a daren Ina dai zaune Ina karatu wajen karfe hudu da rabi yace na tashi nayi alwallah Ina yowa yace ayi sallah bayan na gama sallah na zauna ina lazimi da addu'a can aka kira sallahe asuba na tashi nayi.

Bayan nayi naso na kwanta yace a'a sai fa nayi azkar sai da nayi shi kuwa yace na shiga wanka Ina fitowa wanka nan ya barni na kwanta wajejen six thirty bakwai kuma ya tadani nayo brush sanann na saka kayana ma dauki kayan exmas na fito parlo na hada tea nasha lokacin 7:40 har tayi Ina fitowa naga motar Yaya

Please Login or Register in order to submit comment