Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maki su cikinn sauki da wuri,ko kuma zaku iya hada team kuyi shipping kayan ku,suma zasu iso cikin aminci dajin dadi.

*Lallai kam kowa yasan inda ake nanaye nan keda armashi,iyayye masu aurarwa ku hanzatar domin wanke zukatan ya'yan ku abin kaunar ga mai bukatar yin shipping zai tuntubi wannan number*


08099219663

_Idan kuma kina bukatar kasancewa a cikin group din Deezatu Air and Sea ki danna wannan Blue din rubutun zaki ganki ciki tsundum_

https://chat.whatsapp.com/K0f79e9YCvbFQepkLETHse

*Hausawa nacewa sayen nagari maida kudi gida hanzarta kiyi order dinki batareda fargaba ba ko tsoro ba azo lafiya🥰*


****************
S1/E 27&28


Bayan kwana biyu da yima Mama maganar duk sai naga ta shiga damuwa da bata dauki lamarin da zafi ba amman tunda Anty tazo mata da zancen lamuran sukai mata tsaye a rai,haka nan take karfin hali tana danne damuwar ta,wani bi nike bata hakuri saboda nasan dalilin damuwar tata,yau tunda muka tashi ta tambayi Baba zamuje gidan su gaida kakanin namu,bai hanaba muka shirya mukaje gidan su Mama harda ita,tinda mukaje kakar mu Dada take murna da zuwan mu,haka muka gaishe da abokan zaman nata sai kakan namu namiji can mukabar Mama tana gaisawa da Baban su,mu kuma muka wuce dakin Dada muna hira da autar su Mama Anty Saudat duk da na girmeta saita zama karamar uwa haka muka zama,kawaye shiyasa koda mukazo da ita nike fira,Mama ce ta shigo samun waje tayi ta zauna nan Dada ke mata maganar auren da akace ana nema nawa labari ya kaure ita da mahaifiyar tata nikam Allah yasani duk sanda za'a tada zancen nakan rasa sukuni Dada ke cewa.

"Nikam dai Dije banga wani tashin hankali ba,in banda abin Yusuf taya zai hana dan yayar shi yaba ɗan kishiya ai duk wanda inuwar gemu taima dadi baiyi ya makogaro ba."

"Dada narasa yanda zanyi da lamarin nan nike kwana nike tashi ita kanta Amina tasa damuwa duk ta rame ga SSCE zasuyi fara bawani sukuni atare dani nagaji da wannan lamarin.

Addu'a kawai zakiyi itace mafita idan Samir shine alkhairi Allah ya tabbatar hakama idan shi Husseini shine alkhairi shima Allah yakawo,inma cikin su ba alkhairi Allah ya tabbatar mata dashi."

Ameen kinji zance Dada ai ba alkhairi a cikin su dan haka kubar zancen wadan nan mutanen, daka saida akuya ta dawo tana ci maka danga kawara kar asoma."
Cewar Anty Hafsat wadda shigowar ta kenan da ya'yan kamar sun san zamuzo gidan suma sukazo sai Anty Mubara ita da nata ya'yan atare suka shigo gidan.

Ke ko Hafsat miye ai addu'a itace takobin mumuni ko.?"
Dada tayi maganar cike da tuhuma.
Dada nidai inasan nusantar da iya kada su biyema dukiya azo ayi auren dana sani wannan shine abinda nike nufi dan haka a duba lamarin kwara mai karamar sana'a zaifi riketa da mutunci akan mai arziki.!"
Kinga malama bansan shashanci da mai arziki da talaka dukkan su akwai na kirki kuma akwai na banza fatana kaf ya'yana da jikokina Allah yaimasu zabin na kwarai kuma yabasu wanda zasu zauna lafiya kuma.asirin su ya rufu wannan shine dan haka idan akwai alkhairi Allah ya tabbtar dashi.
Cewar Dada.

Ameen suka amsa saidai kana ganin Anty zakasan ba haka tasoba.
Da haka Dada da Anty Mubara sukaita kwantarwa Mama da hankali.

''Ban gaya maku ba gaskia yarana akwai farin jiki ai Umaima karkuso kuga yanda samari ke kawo hari gaskia ina alfahari da farin jinin ya'yana."

Masha Allah,haka akeso Allah ya ida mana nufi yasa munada rabon gani masha Allah.
Cewar Mama.

Uhmmm.aikam kowa da kalar nashi farin jinin Allah yasa,alkhairi suma sauran Allah yatabbatar masu da alkhairi."
Inji Anty Mubara.

Ameen Dada ta amsa da haka,kuma sukaci gaba da tattauna matsalolin su na family nidai kamar ban wajen haka na koma maganar Umaima ta dawo dani hankalina.


"Inna Saudat aida kika ganni nan gab kike da ki samu suriki wasu kuwa saida akaje tallar kai da asiri aka samu aka kyasa muko daga Allah farin jinin mu yake."
Ta ida maganar a siffar jirwaye mai kamar wanka,nidai murmushi nayi masu dan batasu nike ba.

"Ke Umaima bansan kananun maganganu kaf dinmu kowa da nashi farin jinin fatan kin gane kisan kikeyi."

Kedai ai sha'ani Inna wasu fa saida sukaje tallar kai sannan suka samu masunsunai ko baki lura ba."

Zata kara magana nai mata wani razanannan kallo wanda har saida ta hadiye yawu kutt tsabar razanar da tayi,bance komai ba kowa yai shiru hatta Anty Saudat din.

Daman ni ban wasa da yaro kowa yasani ban daukar raini kaf zuriyar mu suna shayina musamman matasan yan matan dake tasowa wanda suke ganin dai dai suke da uban kowa,ko kanne na da muka,kwanta ciki daya dasu bana jan su da wasanni saida mukan yi fira ko wasan da ba arasa ba wanda bai kawo raini kuma kowa nasa abu baimini musu, yakeyin shi hatta Ahmad dake bina.
Hakama sauran ya'yan dangi Umaima ce kadai nike ganin zata kawo mani wargi kuma ni bansan inyi mata warning ta baki domin ina iya ina faɗa tana faɗa har raini ya samu damar shiga amman na kware wajen daukar mataki ta fuska ba kowa nikema dariya ba haka nike,shiyasa sai ya'yan dangi su dinga cewa ban dariya suna tsorona har iyayen su daga gaisuwa zan dauki mataki a fuskata dan bansan yan tsugunne tsugunne wannan nadauka halitta ta tane.

Anty Saudat ce zatayi magana wayar Mama ta hau ruri Samsung,open and close budewa nayi naga ansa Anty Maryam hakan yasa nagane Mum ce.
ganin su,Mama sun maida hankalin su akan matsalolin gidan su hakan yasa na dauka muryar danaji yasa nai mutuwar zaune!
"Aslm Umma ina yini Hussein ne."
Tarine ya sarkeni da kyal nace.
"Ya Taufiq bari inkai mata wayar."
Nai maganar murya a sarke gabana na faduwa."
Kokarin tashi nayi naji yace.
"Wait Minal inasan magana dake."
Wani ras haka naji, bakina na rawa nace.
"Inajinkaaa."
Naja maganar a tsora ce.
"Wai dagaske Samir kikeso?"

Sai naji maganar a bazata dan danan idanuna suka kaɗa suka canza launi bakina yai nauyi zuciyata na halbawa ga idanun su Umaima dako keftawa baiyi akaina tanasan taji mi muke tattaunawa akai ganin hakan yasa na maido jarumtata na mike ina maida kallan idona nayi waje nace.
"Aaa."
Wata iriyar ajiyar zuciya naji ya sauke da numfashi ya fesar abakin shi yace.
"Zaki aureni.?"

Hannuna yafara shabarin kai kace an saka mani shoking dan da nan naji kaina ya dauki zafi.
Minal zaki aureni?"

Yakara jefo mani tambaya nikam girgiza kaina nahau yi kamar yana ganina ga fitsari dake kokarin kubto mani koda Ya Samir yagaya mani sakon shi ido da ido ban rudeba da gigicewa kamar yanda Ya Taufiq ya gaya maniba wanda sautin shi ke barazana da numfashi na,na rasa dalilin haka miyasa akann Ya Taufiq nikejin wannan situation din shin mi hakan ke nufi tsoron shine dayai tasiri ajikina ko kuwa kwarjini yake mani,toh ai naga shi kwarjini sai kaga mutun sannan zakajin shi koma mene bansan ya zan saka maki lamarin ba domin ina shuga rudani da kidima a yanayin.

Baki sona ko Minal.?"
Eh,nasamu kaina da furtawa wanda bansan yanda akai kalmar ta fito a baki naba nidai naji nace Eh amman ban yarda ni na furta taba saida naji yace.

"Dagaske kike Minal.?"
Sai a lokacin na gasgata eh din dai nace mashi kokarin kashe wayar nike naji ance.

"Ya'ta ki nutsu ki zabama kanki abinda zai fisshe ki Mamana bazaki taba nadamar auren Taufiq ba dan uwanki ne kuma zai rike ki amana kada ki dauki bare kibar jinin ki,kinga ya jima bai aure ba ko yai budurwa sai akanki jinina dan Allah ki so dan uwanki Mamana kinji ya'ta.?"
Toh."
Kawai nace har saida na kalli wayar narasa gane kaina ilimi yaimin kadan dazan gane right way dina komai daida nike,ganin sa bare a level din da nike na,age of 16to17 ina cikin hatsari dan bansan miyai dai dai da rayuwa taba saboda kuruciya tunkan takara magana na yanke kiran jikina na rawa juyowa nayi da zummar in dauki buta inje kewaye domin juye lalurar fitsarin daya kamani ina juyowa naga Umaima tsaye bayana.

Wani kallan mamaki nike mata wanda yasa fitsarin yafara neman tafiya a jikina kamar an dauke mani shi, zata juya ta tafi na riko hannun ta na fisgota da karfi har numfashin mu na hadewa ina mata wani wahalallan kallo nace.

"Ke ni kawar kice.?"
Na jefa mata maganar ba alamun wasa a fuskata da tai niyar mani musu dan dole tace.
"Aaa!"
Uban mi kike nan."
Bakomai.?"
In baki amsa mani ba sainaci uban ki,uban mi kikeyi a bayana."
Saita fara kame kame.
Anty Amina fitowa kawai nayi zan dibi ruwa kuma...
"Kuma me zakici ubanki niba Antyn ki bace ki kiyayeni nafi karfin ki wuce ki bani waje kada in halbaki."
Na ingizata ina tandarar mata keya tayi ciki da gudu.

Tsaye nayi ina mamakin halin Umaima wai mi take nufi dani daman haka take yada mani magana na saka mata ido sai lokacin na dauki buta naje toilet ina mamaki araina.


Kaduna*****


Karka damu kanka Taufiq kaji yarinyar nan tace toh alamun zata aure ka."

"Mum Mum is not easy ke kike ganin lamarin da sauki karfa ki manta Abba baya tare dani yana bayan Ya Samir what i can do in this issue,Mum i love Minal, i swear.!"

Ya ida maganar idanun shi na kadawa kamar rushi.
"I belive u Hussein wlh i trust u,but bansan ya zanba ga Kawun naku yace shi bai magana biyu."
Haba Mum kanin kine fa mi zai hana ki forcing din shi.
Cewar Tariq da yakejin lamarin har zuciyar shi.
Dan ina Yayar shi bashi ke nuna cewa ni mahaifiyar shi bace nasan halin dan uwana amman zan gwada sa'a ta,ai duk kai ka jamana Taufiq da bakayi zurfin ciki ba da hakan bai faruba."

Zaiyi magana wayar shi ta shiga ringing,bai duba ba ya daga yasa ta handsfree.

Afternoon Sir today is swearing out in NDA."
Am busy,but talk to Major Sarki am not feeling better.!"
"Okay Sir wish u quick recovery."
Kashe wayar yayi Mum tace.

"Haba Hussein akan mi za'a kiraka wajen aiki kace baka lafiya wai saima kace a kira Abban ku."

"Mum nifa aikin nan bai gabana dan Allah forget about."
Shiru yayi kanshi na sarawa yace.
"Mum am not my fault duka duka nawa Minal take nayi hakuri harta gama karatun ta nasan lokacin ta kara girma zan jirata ban niyar falasa sirrin zuciya taba har sai lokaci yayi ammn yana iya,duk da haka Abba ke cewa wai bakin Alqalami ya bushe,Mum ya zanyi."

Addu'a zamu lazumta Taufiq itace mafita."
Hmmm sai anjima zan shiga ciki ina bukatar hutu.

*****Amina Pov*****

Haka Umaima duk ta sha jinin jikin ta har muka gama yinin mu sannan mukaima Dada sallama muka tafi gida.
Saidai koda safiya tayi saida Mama taima Baba maganar akan ranta bai kwantaba dasu Ya Taufiq ba duk ta kawo mashi dalilan ta kamar yanda yayarta ta daurata akai harda kukanta.

Tunda tafara magana Baba ke kallanta harta gama jawaban ta,wanda shi a wajen shi ba hujjoji bane saida ta gama kaf ya mike harta fidda rai daga samun amsar shi yace.

"Ki dauki Qaddara nima.ita na dauka dan haka ki rike wannan a ranki bakin ALQALAMI ya bushe ta Allah shine daidai mu luzumci addu'a haka Allah yaso kuma kisa aranki komai lokacine Khadija."

Dakin shi ya shiga bai jimaba kuma ya fita yabar gidan.
Haka Mama tagama jimamin ta dan dole tayi alwallah ta shiga daki dan gayama,Allah kukan ta.

Nikam haka nayi sakake kamar ba jini jikina haka rayuwa ta kasance a gidan mu ba dadi nidai jarabawa ta,ta farko a duniya akan so ne wanda bansan dadin shiba takamai mai bansan mi ake cewa so ba,saidai a furta shi agareni wanda hakan barazana ne agareni,musamman idan ya fito daga bakin Ya Taufiq wanda har yanzum bai furta mani shiba ido da ido wanda kullin addu'ata kenan kada Allah yasa ya furta mani shi ido na ganin ido ai kila sumewa zanyi dan firgita,haka na kasance har rama nayi sai nayi haske fayau dani.

Rayuwa taja hutu ya kare saura kwana ukku in koma makaranta daga komawar sainayi canday zan dawo wanda nikeji Baba nacewa wai za'a kawo kayan sa ranata da Ya Samir ina gamawa za'a daura mani aure dashi yanzun da Ya Tariq da Anty Fiddausi za'a fara nan da wata ɗaya,hakan yasa dan dole nayi kewaye na kece da zawo dan firgici haka naita zarya ina kuka ganin da gaske ake ashe lamarin bana wasa bane saida yamma likis bayan gidan nawa ya tsaya,ina zaune muna kallan Kuch Kuch Hotahe a Zee Aflam Baba ya shiga cikin unguwa Mama na dakin ta daga ni sai Zainab naji Sallama wadda tai sanadiyar tsayawar numfashina cikin kankanin lokaci da sauri na daga idanuna sai cikin.......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*


*Wannan page din nakune F.A.G&Bontel kuyi yanda kukeso dashi,hakika Comment dinku nasakani nishadi🥰*


S1/E 29&30



******Sai cikin na Ya Taufiq a razane na mike ina dafe kirjina kamar naga mala'ikan mutuwa shiko kafeni da ido yayi yana ganina yasan na gama tsorata dashi abin mamaki sai naga yai mani Murmushi har saida fararen hakoran sa suka bayyana,a hankali ya dinga matsawo,kusa dani wanda hakan yake daidai da fusgar numfashina harna koma na zauna bisa kushin,ina maida numfashi da sauri² cikina ya katsa da karfi har saida ya kallenj domin irin sautin daya bada,gani nayi ya gumtse murmushin bakin shi ko dariya oho amman ni nasa shi a murmushin dan bani tunanin Ya Taufiq yana dariya ji nayi yace.

"Minal wannan tsoron har haka mike faruwa pls calmdown."
Ya ida maganar dauke da fara'a.
A hankali nafara sauke ajiyar zuciya harna samu numfashina ya dai daita rufe idona nayi dan yaimani kwarjini, dayawa bansan yana kallona maganar da naji ta sauka cikin kunne na dan dole na ware duka idanuwa na,na zubasu akan shi a tsorace.


"Dagaske baki sona Ya Samir kike so.?"
Ko kaftawa banyi daga kallan shi nafara tambayar kaina a zuci waimi ke damun Ya Taufiq anya shine kodai Ya Tariq ne gashi yana Murmushi amman ai wannan muryar ta Ya Taufiq ce mike faruwa.?"

Sonki shine abinda ke faruwa Minal kina sona.?"
Sai lokacin na fahimci ashe tabaya ta raggo domin yaji abinda nace.
Girgiza kaina nayi dan bakina yai nauyi nakasa cewa ban son shi sabanin amsar dana ba Ya Samir."
Kiyi magana Minal."
Aaa."
Bugun zuciya ta naji nafia da sauri haka naji

Sai kuma nafara tambayar kaina mi Aaa na ke nufi ina son shi kenan a fili na girgiza kaina alamun banson shi,saidai nakasa furtawa daga Aaa din nan nagaza furta komai.
Jinina kai Yayi yace.
"Ki kwantar da hankalin ki Minal zan baki dama kiyi karatun da kikeso duk abinda kikeso zan maki kedai ki kasance dani sannan ki aje zancen soyayya gefe ki maida hankalin ki ga karatu kinji kuma,kada ki kula samari."

Mamakin yanda Ya Taufiq ke doguwar magana nikeyi sallamar Baba mukaji koda ban sani ba kila bazai rasajin kalaman Ya Taufiq na karshe ba,fuskar shi ba yabo ba fallasa ya shigo baki dayan mu muka gaida shi nikam saɗaf nai daki zama Baba yai ya fuskanci Ya Taufiq.

"Hussein nasan kaida mahaifiyar ka kunajin haushina kan nace Samir zanba Amina ko?
To banyi haka dan kuntata maku ba asalima kaine jinina saidai kannen mahaifin ka su sukazo nemawa dan uwanka wannan alfarmar wanda koda ace yanzun na dawo nace na hana shi to sudaine zasu dawo nema maka izinin domin daga tsatso ɗaya kuke kaida Samir.

Abinda nikeso kagane Taufiq ban hanaka Amina ba dan baka cancanta ba Aaa, asalima kaina nafiso ka mallake ta saidai abinda baka sani ba bakin alqalami ya bushe duba da wasu dalilai.

Nafarko mahaifin ku zai juya maka baya kuma bazai saka albarka a cikin auren ba, kuma kasan yanda hushin iyaye yake musamman a harkar neman aure.

Na biyu zai hana dangin sa suyi maka jagoranci a tafiyar ma'ana kowa ya fidda hannun shi Hussein ina kata ba ganin anyi neman aure ba dangin Uba?

Na ukku,koda kunyi auren kaida mahaifiyar ka ne kadai kukeso bazaka samu kwanciyar hankali ,dari bisa dari ba daga karshe ka dinga ganin tangarda kuma gashi kabata komai ba jituwar kirki kaida mahaifin ka.

Ni kuma bazanso rashin albarka ya wanzu a rayuwar auren kuba,kuma banso azo ana dana sani har zumuncin mu yasamu rauni tsakanina da yar uwata.

Shiko Samir na aminta saboda shiya fara neman izini kuma akan rashin sani muka amince mashi bamusan kai ɗan mu kana son yar uwar kaba.

Kuma mahaifiyar shi tana so ta goyi baya sannan uwa uba mahaifin ku yana goyon bayan shi kaga ta kowane fanni zai samu albarka a auren sa,sabanin kai daka rasa ta fanni uba kaji dalilina na kin amincewa ta, kamar yanda mahaifiyar ka ta nema dan haka ina sonka Hussein amman kaje kayi nazari akan maganganu na,yanzun kaje daki ka huta kafito kaci abinci Allah yai maka albarka.

Sauke ajiyar zuciya yayi yace.
"Ameen Abba amman dan Allah kaiman izini zanje mu sasanta nida mahaifina,na amince duk wanda Amina ta zaba tsakanina da ɗan uwana na aminta inta zabi Samir wlh nabar mashi fatana ya cika alqawali nabarin Amina tayi karatu dan cika burin ta haka idan ni Allah yace zan zama mijin ta zan barta ta nemi ilimi dan Allah Abba kaiman wannan alfarmar."

Shiru ne ya gauraye falon kafin nan yace
Shikenan Hussein na aminta kaje ku sasanta duk wanda ta zaba shikenan, kaje ka huta."

Nagode Baba saidai ina tare Soldiers kuma mun kama hotel a cikin Katsina sannan zanyi wata Seminar gobe zamu wuce nagode."

Shikenan da'na.

Mama takawo mashi ruwa suka gaisa yasha sannan yace akirani mu kara gaisawa koda nazo baice mani komai ba saidai ido dayake bina dashi sannan ya fiddo wani dan box karami yabani yace tsaraba yai mani.
Kwarjinin da yai mani yasa na amsa.
"Nagode Allah yakara budi."
Ameen ya amsa bisa lips dinshi yazo fita yaba Zainab kudi sannan yaima su Baba sallama ya tafi.

Koda nashiga daki ina budewa naga yan hannu ne sai zobe duk na azurfa na nunama Mama da Baba sukasa alkhairi nikan na saka zoben a yatsana,aje yan hannun nayi wannan kenan.


*****Nagama hada kayana na komawa School ban kara dawowa saina gama baki ɗaya saidai zullumina ɗaya kada inji labarin an saka mani rana abinda ke damuna kenan arayuwa ta,amman a haka naboye damuwa ta,na fito zan tafi Baba yabani kudi yace in kaima kanwata Hafsat (Yarinyar dana buga lokacin da muna shadows).

Haka natafi school wannan karan Ahmad ya rakani,Asma'u taje Kano sati biyu kenan da tafiyar ta,ina zuwa kuwa bakin gate na iske Hafsat saboda ni nakara sati ɗaya itako ka'ida ta koma da gudu tayi kaina muka rungume juna sannan suka daukar mani kayana har dakin mu,naji dadin yanda suka tareni haka mukaita fira duk da suna immediate dinmu saidai ba laifi shadows yai sanyi.
Inda a dane basu isa su shigo haka ba saidai in wani case ne ya kawo su,sallama sukai mani zasu tafi na bata sakon Baba godiya tayi da haka suka tafi.

Washe gari mukaje Class munfara Morning M.Bala Wada,ke samu saboda karatun Jarabawar gamawa,saidai duk wanda ya ganni sai ace na rame nayi haske amsa daya nike basu ciwo nayi da haka har nasamu aka daina tambaya ta,haka mukaci gaba da rayuwar mu hankali kwance saidai akai akai Ya Taufiq da Ya Samir na fado mani araina ya zanyi da soyayyar yan gida ɗaya kuma wa da ƙani wannan shine Qaddarata ni kuma haka tazo mani.

Wasa wasa lokuta sunaja muna karatu zuwa yanzun kowa ta kanshi yake ko prefect din masu zalinci yan kadan ne ansami Freedom.


******Kaduna


Kamar yanda Taufiq yaima Baban su Amina alqawali haka yaje ya sanar ma mahaifin nashi kuma lokacin kowa yana falon shi jira yake da ankai kayansa ranar Samir sati mai kamawa za'a daura auren su Tariq abinda ya rikeshi kenan akwai aikin da zaije yi abroad.

Jin zancen da Taufiq yai mashi ya fusata shi a tunanin shi sunkai karshen zancen wani kallo yakema mahaifiyar Taufiq a zaton shi duk shawarar tace.
karar da sukaji ta tashi itace ta dawo dasu hayyacin su

Abba ne ya wanke Taufiq da mummunan mari ya gwada shi da yatsa yace.
"Inbaka fita cikin zancen nan ba Hussein saina.....

A fusace Mum ta katse shi.
Dakata Alhaji Mukhtar kada son rai da bakin asiri dake dawainiya dakai wanda baka san kana wannan kaifi dayan ba yasa kaima dana baki ina dalili ai wannan shine mafita akira yarinya ta zabi wanda takeso shikenan ankawo karshen husuma amman tuggu yasa anjuye maka tunani ga gaskia kaki."

Kece yar asiri Maryam badai niba dan haka ki iya kalamanki."
Cewar Mami.

Shiko Abba jin kalaman hajia maryam sun fusata shi.
"Ni kike cema tuggu da bakin asiri ya tosheman kai wato ga mahaukaci kenan ko?ki shiga hankalin ki tunkan insaba maki ina ganin darajar ki a idona!

Kai kuma kajini da kyau tunda abin naka iskanci ne, gobe za'akai kayan sa ranar Samir inka tashi ka mutu,tunda son zuciya yasa kuna neman kawo mani yan ubanci cikin gida na.!"

"Allah ya huci zuciyar ka Abba,banso na fusata kaba."
Yana gama fadar haka ya fita.
Wani kallan tsana Mami tabi bayan Taufiq dashi ji take kamar ta halaka shi.
Fada yaitayi kamar zautacce ita kuwa Mum tace.
"Alhaji Gobe in Allah yakaimu zanje Abuja."

Allah yakaimu lfy."
ya tashi yai daki da haka kowa ya watse,rai ba dadi.


Alhaji Mukhtar ya kasance mai sanyin haline saidai yau da gobe yasa mugun tuggu da kudiri na Mami, yasa Alhaji ya koma mai zafi da saurin fushi,musamman idan tana kai mashi zigar yayan shi,gwana ce ta iya ziga zigi da tuggu.

Duk da haka son dayake ma Maryam yasa duk abinda zaiyi yakan daga mata ƙafa dan baso na wasa yake mataba ahakama an farraka tsakanin su dasu Taufiq da Tariq lokacin da aka haife su son daya nuna masu saiya kasance kamar ma ba'a taba yi mashi haihuwa ba a duniya,ya kasa boye farin cikin shi da suka fara girma kuwa sai ya kasance kamar su kadaine ya'ya komai su,hakan yasa Mami tayi yanda tayi saidai ta rage mashi son su aran shi damma su dukan su sunada tsayuwar dare da riko da addini hakan yasa suke samun sukuni.

Wannan karan tunda taga yama Alhaji Mukhtar,Samir nasan Amina ya kasa fahimtar gaskia, saboda Allah yaima Mami baki da iya tsara zance, indai ta furta mashi abu to haka yake duk wanda zai gaya mashi a banza ne bazai jiba,shiyasa yakasa tsayawa ya duba alakar dake tsakanin Amina da Taufiq,idon shi ya rufe shi kawai da Samir ta dace acewar shi ai shi yariga faɗa Amina zai aura.

******Washe gari Mum tabiyo jirgi sai Kano daga nan Driver dinsu ya daukota zuwa Caranci gidan kanin nata ta sauka aiko bata same shiba koda ya dawo ya iske yayar tashi cikin girmamawa ya gaidata ko amsawa batayi ba ta barke da kuka tana cewa
"Shikenan ni Mairo asirina ya tonu ɗan uwana uwa ɗaya uba ɗaya ya kasa rufa mani asiri ya zabi dan kishiya akan jinin shi Allah Sarki Hajia da kina da rai na tabbata da Yusuf bai wulakantani ba nashiga ukku ni Mairo mutuwa mai tonon asiri.!"

Haka Mum taita kuka wiwi cikeda tashin hankali

Dan danan hankalin Baba ya tashi indai kanasan kaga tashin hankalin tuno mashi da mahaifansa musamman mahaifiyar shi,duk yagama shiga damuwa.

"Kiyi hakuri dan Allah ke nike gani matsayin mahaifiyata inji dadi karki mani haka bansan ya zanba kun sani a sarka kiyawa ki daina kukan nan dan Allah.!"
Ya ida maganar a raunane,ganin kanin nata ya rude yahau hanya tace.


"Ba dole nayi kuka ba muddin ka yarda da auren Samir da Amina wlh ban komawa gidan mijina saidai ya aiko mani da takarda ta,kuma inanan gidan saidai mutuwa zata rabamu kaga kuwa nida ya'yana mune dolen ka ba Samir ba."

Shiru yayi kanshi nasara mashi kamar me yarasa,mafita murya na karewa yace.
"Ya isa ki daina kuka Samir dai ko nafasa bashi Amina shi shikenan tashi daina wannan halbe halben karki tona mana asiri Allah ya huci zuciyar ki."
Sai a lokacin taji dama dama tace.
"Taufiq zakaba ko.?"
"Dolena kuwa ai Hussein jinina ne."

Batasan ta riko hannun shi ba tace
"Ko kaifa Allah yai maka albarka Yusuf ka share mani hawayena."
Ameen ya rabbi,ya zakiyi da mahaifin su kina ganin zai amince.?"
"Insha Allah zai yarda gobe da sassafe zanbi jirgi in koma nasa Tariq ya saimani ticket na karfe takwas.
Allah yakaimu lafiya.
Ameen.
Da haka sukaita fira har abinci da kanin nata suka ci,washe gari da sassafe ta koma zuwa Kaduna.


Amina"""""""


Nikam kullin banda komai gaba sai karatu maganar Ya Taufiq ke dawo mani.
Ki aje soyayya kiyi karatu kinji Minal."
Da natuna kuwa zan hau karatuna kuma alhamdullh ina ganewa sosai

Washe gari Visting

Please Login or Register in order to submit comment