Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan ta shigo yima su Mama sallama har kudi Baba ya bata Mama ta bata wata leda godiya tai masu baki ɗayan mu after dress ke jikin mu,haka muka fita har kofar gida Baban su yasamo mota yace akaimu a dawo damu nida kanwar ta Rahima,haka muka tafi har Umyuk.
Block A room 8 nan ne dakin ta muka tayata gyara kayanta da dakin saida muka kammala komai gaf da la'asar mukayi sallah sannan muka fito tare zamu dawo gida shiga mukayi mota,tace in rakata Student Center,wajene da keda tarin daliban iri daban daban da alama nan suke yan siye siyen su,kuma akwai Restuarant a ciki,haka mukaje wata super market ta siyo litattafai da biro,sannan muka fito sai fira mukeyi idona na kan Husna dake bani labarin tsaruwar makarantar su,domin nima idanuna ya gane mani hakan gaskia kam ta hadu sosai komai a tsare yake gwanin ban shi'awa,juyawar da zanyi ina kallan Cleanic dinsu dake cikin Center din kawai naji an bangajeni har saida books din Husna dake hannuna suka zube kasa nima din harna kusan kifewa Asma'u ta rikoni,wani irin tsoro ya kamani ganin wani saurayi tsaye yanata kallona kuma baida niyar yabani hakuri ,daga sama har kasa nike kallan shi dogone saidai baida jiki sanye da shadda brown fuskar shi dauke da murmushi,wani haushi yakara kamani zan duka in kwashe books din naga Husna harta kwashe jan hannun ta nayi nace.
"Mutafi kinsan wasu mutanen sai a hankali in suna abu basu san yakamata ba."
Na ida inajan guntun tsaki dan ya kulleni."
Ta gefen shi muka raba zamu wuce yace......



*Garabasa! Garabasa!! Garabasa!!!💃💃💃💃💃💃*

*Ga dama tasamu yar uwata karki bari wannan garabasar ta wuce na karanta littafin Daukat Fansar Budurcina,yar uwata idan kinsan baki soma karanta littafin fansar budurcina ba maza garzayo domin kada ayi babuke yar uwa,labari daya kunshi abubuwa iri iri ba rayuwa,musamman matsalolin mata yanda rape ya zama ruwan dare,kwantata da kanki* *ace kece yarinyar nan yar shekara goma a duniya wani gardi yai maki fyaɗe dan kawai kudin baku da galihu kuna aikin aikatau agidan su keda mahaifiyar ki,dan mahaifiyar ki takai koken ta wajen mahaifiyar shi,tasa ɗan nata yakara yi maki fyaɗe a idon mahaifiyar ki da tasa😭,turkashi wace irin cakwakiya ce ke cikin wannan labari,wace kalar Daukar Fansace Aisha zatayi akan Ahmad duk*
*wannan kulalliyar tana cikin wannan daddaɗan labarin mai taken DAUKAR FANSAR BUDURCINA na Jameey Yar Mutan Kankia, mai dauke da dinbin*
*darasi,ilimantarwa,fadakarwa,nishadantarwa,harma da wa'azantar wa, garzayo domin kar'ayi babu ke,zakisame shi*
*cikin sauki da rahusa.*
*Mai bukatar karanta* *wannan book ya tuntubi wannan number👇*
*08160508316 domin karin bayani*
*Yar uwa idan kinsan ba saye zakiba karkima wannan number magana nagode*

_Hausawa nacewa sayen nagari maida kudi gida🥰_


_Yar Mutan Kankia ce❣️_



share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*


*Sadaukarwa agareku Masoyana Allah yabar kauna💔*



S1/E47&48



"Haba yan mata miyayi zafi Allah yabaki hakuri duk irin ciwon da kikaji mani shine zakiji haushina bayan kin mani illah Allah ya huci ran gimbiya."


Wani wawan kallo na banka mashi.
Asma'u tace
Haba bawan Allah kana ganin ka bangaje ta baka bata hakuri ba shine harda wani korafi kaida ita waye zai jima wani ciwo.?"



"Ita mana gashi kuwa tai mani babbar illar da ba'ataba yimani irin taba."
Ya ida maganar yana murmushi,fisgo Husna nayi muka tafi kanmu na hayakin JJC na yan Jami'a ko takan zancen shi banbi ba bare musan inda ya dosa munafitowa nayi cikin mota harsu Rahima sun gaji da jiran mu,dan fuskar su ta bayyana hakan hakuri na basu,nan mukaima Husna ban kwana muka tafi gida.


Bamu isa gidaba sai biyar na yamma dan ba wani nisa sosai,ana ajeni ko gidan su ban shiga ba nayi gida saidai tun daga zauren gidan mu najiyo hayaniya na tashi har saida gabana ya yanke ya faɗi a hankali nike tako kamar barauniya jin bakuwar muryar dana gaza tina mai ita,ina isowa tsakar gida idanuna suka sauka kan Mami (Maman Samir) tanata zazzaga bala'i kamar gidan ta,itako Mama tayi shiru sai aikin bata hakuri takeyi,ko sallama banba dan bakina yai nauyi jin mugayen kalaman da take jifar Mama dasu koma ince take jifata dasu.



Zainab ta rigo da gudu ta kadaddabe ni tana cewa.
Anty kice tabar mana gidan mu bansan ta muguwa ce."
ta ida maganar tana gwadata da yatsa nikam kamar andasani na rungume Zainab jikina zuciya na halbawa a hankali ta sauya salon bugunta.
Kafin in ankara naji ta cacumoni da karfi ta kawoni gaban Mama tana gilgizani tana cewa.

"Badai akan wannan yar iskar yarba kika hana ɗana,kan wannan tsinanniyar har aka dukar mani kanwa ranar bikin ya'ta,bari kiji wlh billahi ai da kyaunta kuke gadara ko?indai nacika sunana Mufida na haihu ga jinin Alhaji Shehu indai Aminace tayi aure mugani duniyar nan,kuma ita da Taufiq basu ba aure har abada yanda Samir ya rasa Taufiq ma saida ya mutu bai aureba,alqawali nane wannan ni Mufida.!"


Ta ida maganar tana yakitar dani gefe daya kamar kyanwa, kannena ne suka taroni jikin su,nikam sai bugu zuciya ta ya ida rikicewa cikin kankanin lokaci kaina ya sara ganina ya nemi daukewa na rasa wace kalar musifa ke tunkaroni wai wane bala'i ne wannan,kenan ni iyayena basu da ikon hana Samir aurena koda ba Taufiq?mi suke gadara dashi arziki usuli mulki ko kuwa karfin iko dahar zasu tako gidan mu suci mana zarafi naga muma aiba matsiyata bane munada rufin asiri miyasa suke neman takamu son ransu.



Ji nayi ansake fincikoni abinka da ba katuwa ba saina koma kamar yar mage Wasila ta ɗagoni tana mikar dani tsaye tana gwadani da yatsa sama da ƙasa tana cewa.

"Baccin namiji na wawa mi Samir yagani jikin wannan abun yarinyar da bata jima da zama budurwa ba shine yake rawar kai akan ta,to kibar su Anty mudasu muzuba mugani shege kafasa dan halak sai yanka."


Ta kara tureni na koma gefe zuwa yanzun kuwa hawayen da bansan suna shida idona ba sun fara sauka masu dumi,gashi kamar ansama bakina kaca na gaza furta uffan dan takaici.



Maganar da mukaji anayi itace ta maida hankalin mu a kofa inda Mamar su Husna ta shigo danyi mani ban gajiya ta iske wannan tashin hankalin mamaki fal a fuskarta tace
"Haba bayin Allah har gidan matar aure zakuzo kuna mata ihu anya bakusa son zuciya ba.?"



Ke dallah malama ke asuwa?zakizo kina sakama mutane baki,inta isa ta rama,da wane bakin bayan sun taushe dukiyar ɗan mu,koda yake ai suna ikirarin sa ranar da Taufiq akayi amman ai tunda anfasa da sai amaido mana kayan mu,amman kwadayi yasa sun gaza zuciyar kaza ta sace ta dole suyi shiru mana da su tanka in sun isa.!"

Ai kamar an mani allura naja hannun Zainab sai gidan su Husna direct dakin Mama nashiga uwar ɗaka na jajibo katon zanin gado da kuloli Zainab ta dauko kafat din sallah da agogo harda botoci nasa kannen Husna dauko mani su goro da gishiri da sauran tarkacen kayan sa rana mukayo gida yan unguwa sai kallan mu suke domin dalla dallan motocin da suka gani guda biyu a kofar gidan mu ya shaida masu munyi baki kuma ana ɗan jiyo hayaniya a gidan mu,shiyasa kowa ya tsaya dan ganin kwam kotasu banbi ba muka shiga gidan na aje kafat din gaban Mami da karfi harsaida yayi kara tim haka kowa ya aje suka koma dan ida kwaso sauran tarkace muryata na shakewa nace.



"Mami muba matsiyata bane daman kayanku sunanan munajiran irin wannan ranar dan haka saiku kwashi arzikin ku,mu kubarmu da tsiyar mu.!"


Na ida maganar a zafafe,tas tas Wasila ta gaura mani mari har sau biyu.

The first history da zance hakanan a gidan mu an mareni tunda nai wayo a duniya,da yatsa ta nuni tace.


Dan ubanki ko uwarki bata isa ta maida wannan martanin ba bareke liddan kada miya,kuma inba makwadan tan bane ku,biscuit da chewgam da sweet ubanki ya tisa ya cinye eyeh.!"



Ke! karki kara zagar mani uba.!"
Wata ƙara na kwada na daga hannu zan shararama Wasila mari Mama ta rike hannuna ta watsar dashi gefe jikina na rawa.



Bansan na fashe da kukan takaici ba na fada daki inaji inama mutuwa nayi na huta.
Can naji tana cewa.
"Rabu da ita ta mararma kanta musiba dan ubanta,sannan sukace.



"Ke kuma tunda har kuka iya zuciyar dawo da kaya wa'anda aka cinye sai amaido a aiko dasu ko matsiya ta."
Haka suka karaci wulakancin su,suka tafi a fusace.


Zamewa kasa Mama tayi,Maman Asma'u taketa bata baki domin itama mamaki ya isheta da al'ajabi.



Nidai tinda na shigo daki bankara fitowa wajeba lamarin ya isheni ina mamakin dalilin shigowar Ya Samir da Ya Taufiq a cikin rayuwata wanda sukayi sanadiyar rabuwa da duk wani farin cikina na rayuwa musamman Ya Taufiq da akeshan mugayen kudure kudure akan alakar mu duk da ba wata soyayya ce ke tsakanin muba asalima ban taba son shi araina ba amman ana zuwa ana cimana zarafi ba dangi ba duk da ba kowa ke wulakanta muba,ba yan unguwa ba,gashi uwa uba har gida Mami tazo taci mana zarafi,raina ne yakara baci bansan na tashi ba naje falo wayar Mama na dauka na dauki numbar Ya Taufiq a cikin waya ta,sannan na koma daki.


Kiran su nayi saboda Baba yasaman kati kuma dayake sabon layine harda bonous suka bani,banda numbar Mama da Baba sai Husna number Ya Taufiq itace ta hudu data fara shiga a content dina.
Kaina ya dau zafi saboda na kira yakai sau biyar ba'a dagaba karshema rejecting yayi saida nakara kira ya dauka da kakkausar murya yai sallama harda gabana ya faɗi a hankali nafara rasa nutsuwata dan yanda naji muryar shi akwai sa fargaba a dake take alamun ba wasa kenan.



Who is on line.?"
Yai tambayar a takaice.
Muryata na rawa nace.
"Dan Allah ka aiko azo akwashe maka kayan sa ranar ka bamu so.!"


Minal.?"
Shine abinda naji ya iya furtawa cikin sanyin murya sabanin sallamar da yayi mani da farko.
Ban amsa ba,saboda kukan daya kwace mani.

"Daina kukan nan Minal miyafaru kayan sa rana kuma mizanyi dasu pls kiyi magana kanwata."

Muryata na rabewa nace.
Nidai ka aiko akwashe maka kayan ka ,banso kuma nace banson ka nafada dan Allah kace su kyalemu nidai ban sonka ban son k......
"Stop telling me nonsense,re u in ur sense Minal.?"


Kukan naci gaba dayi.
"Kina gaya mani magana mafi muni a cikin zuciya ta mike faruwa kuma abuna ai mallakin kine Minal kidaina fadar mugayen kalaman nan akaina.!"

Ya Taufiq.?"
Sainaji ta amsa da Na'am,dan banyi zatan zai amsaba.
Dan Allah katai maka mani wlh bazan iyaba zan iya mutuwa kace....
Sai kuma naci gaba da kukan.
Atakaice dai Ya Taufiq yai juyin duniya in gaya mashi suwane sukazo har na rude haka,kuma miye dalilin maganar kayan sa rana,bayan shi ya manta da sha'anin su,sam har dai na datse wayar ban iya yimashi bayani ba,har kirana ya kuma sau biyu naki dauka.
Can naji sallamar Baba fitowa nayi nai mashi barka da zuwa yanda ya ganmu a sanyeye hakan yasa ya gane gidan ba lafiya.

Zainab da Hauwa'u yar karamace suka rungume shi suna kuka kamar ransu zai fita,nima kamar an xugani naci gaba da kukan tambayar duniyar nan yai mana mun kasa magana har saida yafara fada musamman dayaga kayan sa ranar watse dai dai a tsakar gida.



"Khadija kan mi zaki daga mani hankali ke kuka ya'ya kuka har Hauwa'u,mike faruwa kuma bance maki na tsani ganin kayan nan a gidan nan ba,wai miyasa bakujin abinda nake ce maku miyakawo kayan nan gidana.!?"

Sai a lokacin Mama ta samu tafara magana.

Masu su aka fiddo mawa saidai sunce bazasu karba ba sai anhada da wa'anda akaci zasu aiko a ɗauka."


Dan danan ran Baba ya baci fuskar shi ta murtuke kamar bashi ba.
"Shi Major din yace haka.?"
"Aaa matar shi Mami da kanta tazo har gidan nan,nan ta kwashe komai ta gaya mashi harda mugayen kalamanta akaina duk ta gaya mashi.

Shiru yayi yana nazari sai kuma yace.
"Shikenan amman karku kuskura kusa furucin ta aranku ba abinda zai sameta sai alkhairi,maganar kayan sa rana kuwa zan siya kuma da kaina zansa amaidasu har Kaduna insha Allah gobe goben nan ku daina kuka Khadija,wannan yana cikin Qaddarar Amina kuma bakin ALQALAMI ya riga da ya bushe,sai hakuri ke kuma Amina sai kin sama ranki hakuri akan kalubalen da zakita fuskanta na rayuwa shiyasa banso aka samaki rana ba amman haka Allah yaso,ku tashi muje kowa yai alwalla muyi nafila."
Bayan shi mukabi kowa ranshi ba dadi,har da kowa ya kwanta.

Washe gari kamar yanda Baba yace haka yasa Baba Hassan ya dauki kaya yace yafara rakani makaranta wannan ya wuce Kaduna ya maida kayansa ranar kuma hannun shi hannun Abba ko Mami.



Abun daya faru sai naga kamar ina tafiya haka za'azo anacima Mama zarafi shiyasa naji ban daukin zuwa Makarantar sam daurewa kawai nayi ganin su Zainab suna kwalla yasani nafara hawaye a haka Baba Hassan yaja mota muka tafi,kamar yanda Baba yace saida yakaini har gaban Hostel,ya ajeni ya dauki kudi yabani,yaimani nasihohi sannan ya tafi.

Daukar kayana nayi nafara kaiwa gaban dakin mu,dauko wayata nayi na kira Fatash miscall biyu nai mata sannan ta daga itama yau da safe na dauki numbar ta a wayar Mama,tana ɗagawa nace
Gani nan a hostel naga room din ba kowa kixo ki tayani kwasar kayana."

Hakan yasa tagane nike magana.
"Yar rainin hankali kina nufin ni kadai zan zauna ina jiranki kamar marar aikin yi to ina gida wlh sai gobe zan shigo baki ɗaya."
Dafe kaina nayi nace.
"Haba Fatash miye laifi dan kinjirani ai kinsan hakanan bazanki dawowa ba to ina key.?"

Ki duba zakiga wani dutse babba yana nan kasa daga gefen wall na aje maki nakine nayi duplicate na dauki nawa."
To shikenan dan Allah gobe ki shigo da wuri.!"

Insha Allah Mrs Taufiq bye Allah huta gajiya."
Ta ida maganar da dariyar shakiyanci bansan na saka dogon tsaki ba nace
"Stupid."
Naji dai insha Allah raban Ya Taufiq ne."
Ɗit na yanke wayar raina na kuna dajin maganar Fatash da haka na kwashe kayana nafara gyarawa.



A Kaduna kuwa koda Baba Hassan ya isa gidan su Ya Taufiq,mai gadi yasa yakai mashi kayan har bakin kofar side din Abba,bayan ya tambaya ance mashi yana nan.


Waya ya kira shi,akai sa'a shine ya daga,nan yace yana bakin side dinshi yanasan ya gana dashi.
Cewa yayi ya shigo kai tsaye,saidai Baba Hassan ya musa hakan yace yana hanya daman sakone zai bashi sauri yake.

Abba ya fito compound din wanda security ke yawo jefi jefi as usual.
Yana kallan gefen bango yaga kaya aje,mamaki fal aranshi ya maida kallan shi ga Baba Hassan,bayan sunyi musabaha sun gaisa.


Fatash dake cikin garden taga Baba Hassan hakan yasa tazo ta gaida shi ya amsa ganin kaya dajin maganar da sukeyi yasa taje ta gayama Mum.



"Dan haka muna baka hakuri ba dan san ranmu muka dawo da kayan ba Aaaa dan samun masalaha da kwanciyar hankalin matar ka,kaga fitina kwance take Allah ya la'anci mai tadata,mun fison zumuntar mu ta daure kada shaidan yasa mufara samun sabani da fatan zakayi hakuri da wannan hukunci."


Kallan shi ya maida ga Mum dake tsaye tunfara maganar kanin nata jikinta a mace,dauke kanshi yayi ya sake kallan Baba Hassan yace.


"Nine zan baku hakuri Hassan kuyi hakuri dan Allah kan wannan cin zarafin da iyalina tai maku,kuma insha Allah zan dau mataki sannan bazan takura maku ku koma da kayan ba,amman komai kenan ku saurare ni nagode."


Sallama yai masu zai tafi duk yanda Mum taso ya tsaya ko abinci ne yaci amman yaki tsayawa duk da kuwa Yayar shi tasan yan uwanta nada zafi indai aka tabasu.
Waya Abba ya dauko yakira Mami yace.....




_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Comment
Pls
❣️




*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*



*Sadaukarwa agareku,kuyi yanda kukeso da page din nan Allah yabar kauna💓*

_*Muhammad Karem(MK)*_
_*Abbas*_
_*Yar gatan Mom Sultan*_
_*Prince Umar*_
_*Pharteemarh Kankia*_
_Fatan alkhairi agreku🤍_



S1/E49&50


_*End🖊️*_



"Kisameni Sashena yanzun yanzun nan.!"
Kashe wayar yayi yana fesar da huci mai zafi a bakin shi.
Yaje yadawo yana dukan hannun shi cikin tafin dayan hannun nashi.

Ganin kamar tana mashi nawa ya kira Fatash.
"Ke Fatima jeki kira mani Mamin ku,kice takara minti ukku ta kuka da kanta.!"


A sanyaye ta tafi kiran Mami itako cikin ta ya gama tsurewa daga ita har Wasila da tazama yar koren ta duk inda zasutafi suna tare,jiki mace ta fito daidai kofar fita part din nata ta hadu da Fatash,wani kallo ta aika mata tace.


"Wato dayake ba uwar ki,yakema wannan kiran farautan ba shine harda bin bayana ko?kunajin dadi kun samu abinda kukeso daga ke har munafukar uwar taki,wuce mutafi munafukai.!"
Yi hakuri Mami Abba ne...
Yiman shiru kada in kifa maki mari muje masu mugun hali,nan gani nan bari wlh.!"


Haka ta tisa keyar Fatash har sashen Abba can ta hangi tilin kaya kuma Abba yanata zirya tana ganin haka saida gabanta ya yanke ya faɗi dakewa kawai tayi ta isa wajen shi
Alhaji gani shine abinda tace.


Da yatsa manuniya Abba ya nunata a zafafe yace.
"Kinga tsiyar da kikaje har Caranci kika kulla dan haka nabaki nan da gobe wlh inhar baki koma da kankiba kika nemi afuwar tsiyar da kikayi ba ni kadai nasan hukuncin da zanyake maki,wanda zakiyi dana sani har karshen rayuwar ki Mufida,ni zaki maida shashasha ni dakaina nacema Yusuf yabar kayan angaya maki shi matsiyacine wato duk abinda na yanke maku bakubin umurnina ko,ni nasan yanda zanma duk wani gagararre sanann inajan kunnenki kafarki kafar tarkacen kayan nan,yanda kikai silar dawowa dasu haka zaki silar maidasu har gidan Alhaji Yusuf wlh muddin kika ki bin umurnina kijira sakamakon ki,shashasha dake.!"
Yana gama fadar haka ya faɗa side dinshi rai bace.



Sukuku Mami ke kallan kayan sannan tana juya maganar mijin nasu wane hukunci zai mata idan bata maida kayan ba?kaddai ace sakin ta zaiyi wani sanyi taji jikin ta yai mata,haka taita tunani iri iri, tana wurgama Mum harara tace.

"To makwadaita dan za'arasa dukiya harda tado miji ana zuga shi,ba'asaba ba dangin tsiya nasan in ba'a maida wannan kayan ba dagake har dangin naki baku ba kara sukuni duniya anji haushi matsiya ta.!"



Murmushi Mum tayi tace.
"Uhmm ko?ai ance daman tabarmar kunya da hauka ake kwasheta dole zaki kidime kina hakilo aikinga zahiri cewa yan uwana ba matsiyata bane tunda sun maido maki tsiyar ki,wa'anda suka gaji arziki basu wannan zuruftun kefa,dan Allah kwashe tsiyatakun ki,akai gida nasan tsohuwa na nema.!"

Ke Maryam! zan illataki.!"
Takaima Mum wani irin bugu ta rike hannun ta ta wullar dashi tace.
"Allah tsareni jikin ki ya hadu da nawa in kwashi kashin tsiya saidai kikarata yar bala'i.!"


Tana gama faɗar haka takama hannun Fatash sukayi side dinsu nan sukabar Mami tanata sababi Wasila na tayata sannan tasa ma'aikata suka kai mata kayan BQ din gidan.




*******Washe gari da safe kuwa ina tashi na shirya tsaf na tafi lecture inda aka fara mana da Chemistry,ranar farin cikin da nike ciki bai faduwa domin itace first lecture dina a jami'a sai murna nike kana ganina kasan Level One nike ga rawar kai inayi saidai duk abinda nike a nutse nikeyin shi wannan kuma nature dina ne,amman akwaini da arawar kafa danko lecture zamu mune farkon zuwa muna gaba gaba.


Doctor Gibrian shine ya dauke mu a ranar, mukafara kananun meanings da sunayen Acid iri iri,nan yake gaya mana hadaririkan su musamman Sulpuric Acid da Hydro Chloric Acid da sauran su haka yaita mana Explanation kuma muna fahimta sosai yanda ya kamata,bamu muka bar lecture room dinba sai 10am ana fitowa nayi Hostel.

Ina zuwa kwantawa kawai nayi banjima ba naji an kaiman duka a zarane na tashi Fatash ce keman dariyar mugunta wai na kwana hostel itako gida ta kwana nima murmushi kawai nai mata nan fa tafara bani labarin lecture dinsu da Physics suka fara kasancewar Enginearing take karanta,nima na bata labarin tawa,daga nan muka hau fira take bani labarin Baba Hassan ya maida kayan sa rana da yanda suka kwashe tsakanin Mami da Abba,murmushi kawai nayi nace.
Allah ya kyauta.


saidai ban bata labarin cin mutuncin da taje gidan mu tai mana ba nida mahaifiya.
Da haka mukahau labarai tsakanin mu na kawaye har muka fara girkin abinda zamuci wannan kenan.


********Caranci*******


"Assalamu alaikum,wai ance ana sallama da Amina kofar gida."
Cewar wani yaro dake tsaye bakin kofar shigowa cikin gida.
Mamar su Amina dake kitchen taji abinda yaron ke faɗa hakan yasa taji gabanta ya yanke ya faɗi,shiko Baba dake zaune a falon shi tareda Anty Hafsat dasu Umaima baisan ya fito ba da sauri zuwa zaure,dukawa yaron yayi ya gaida Baba ya sake jaddada masa abinda yace.

Bin bayan shi Baba yayi domin yagane ma idon shi wanda ke kiran Amina.



Yana fita yaga wani matashin saurayi jingeni a jikin motar shi,kusan a tare Baba da Ahmad suka isa wajen shi.
Yana ganin Baba ya duka yana gaishe shi,ba yabo ba fallasa Baba ya amsa sannan ya mike kanshi duke yace.

"Abba daman ina neman izinin ganawa da Amina ne.?"
Mamaki fal a fuskar Baba yace.
Bangane daga ina kake ba kuma daman kasan Amina.?"
Dan sosa keyar shi yayi alamun jin kunya yace.
"Sunana Ahmad Idris kuma ni haifaffen dan Katsina ne,Kofar Kaura."

Masha Allah cewar Baba sai kuma yace.
Miya hadaka da Aminatu.?"
Sake sosa keya yayi yace
"Makaranta naganta anan Umaru Musa shine nazo neman izinin aurenta."



Tabbas Baba ya shiga alhini najin wannan batu duk da yasan bai wuce ranar data raka Asma'u ne suka hadu ba,jinjina kai yayi yace.
"Ayyah saidai tana makaranta kuma level one take yanzun."
Eh Baba nasani nidai ina son kai mani izini zan iya jiranta tagama karatun ta sai iyayena suzo asa biki."

"Banki ta takaba saidai inason kabari karatun nata yai nisa bazanso tasa zancen soyayya a rantaba kaga yanayin karatun nata,wannan shine."
Sake dukawa yayi yaima Baba godiya sannan sukayi sallama ya hau motar shi ya tafi.

Baba nakomawa gida yace.
"Kinji wani yaro ne wai yazo neman auren Mamana."
Karaf Anty Hafsat tace.
"Ikon Allah shi kuma ina ta kwaso shi.?"
Wai jami'a data raka Asma'u ya ganta."
Budar bakin Hafsat cewa tayi.
"Tabdijam nifa shiyasa ban yarda da wannan jami'ar tsiyar ba ajecan a bata maka yaro kai kuma ka bashi tarbiya ga shegiyar karya samarin nan ke garesu Allah ya kyauta ya'ta tayi jami'a."
Kallan kallo akema juna tsakanin Baba da Mama,itako Mama tasaba jin wannan zancen marar dadinji a bakin yayar tata,amman saita nuna bata damuba.



"Maman Umaima kenan,ai idan kikaga mutun na tsoron kai dansa jami'a neman ilimi tabbas baiyarda da tarbiyar da yaima ɗansa bane,idan kasan waye danka kuma kasan a ranka Allah ya natare dashi wlh ba jami'a inda yafitama ni zan iyakai ɗana banjin komai nasan kullin addu'ar da muke masu tana tasiri da izinin Allah."


Uhmmm kawai Anty Hafsat tace amman ta ciki na ciki.
Itadai Mama tana mamakin yanda yar uwar ta,ta sauya halaye macen kirki maison zumunta amman yanzun ta zama mai yawan hassada da mugun kudiri cikin rai.


Da haka Mama ta gama girki sukaci sannan suka tafi gidan Yayar Baban su ganin kayan sa ranar Bilkisu da aka kawo shiyasa Anty ta biyoma Mama domin su wuce tare.




Amina Pov.


"Haba Husna miyasa zaki bashi address din gidan mu yanzun haka Ahmad yakirani wai har magana saida yayi da Baba ya kikeson inyi kin manta zuciyar Baba ko.?"

"Sorry Minal banyi ba dan nai hurting dinki ba wlh da gaske nike tun ranar duk inda ya ganni saiya tsaidani ko yabini har lecture kinsan shima lecturer ne kuma yana daukar mu Biology ya zanyi kullin ya matsamani saida na bashi sannan nasamu sa'ida a raina."

"Naji nidai Allah yasa Baba kada yai zargin kona taba magana dashi dan bansan ranshi ya baci wlh ko kadan kina ganin halin da nike ciki akan case din Ya Taufiq kema shaida ce tunda ban boye maki komai
Husna."


"Nasani Minal dan Allah kiyi hakuri kisan yanda zaki yakice shi."
Ai maganar yakicewa angama tunda Baba yagaya mashi karatu nikeyi."
Wai kina nufin bai kiraki waya ba.?"
Mamaki fal a raina na rasa mizancema Husna ta waya sai hello take cewa dakyal nace.
"Wato har number ta saida kika bashi kenan,wai miye haka Asma'u."

"Cool down duk labarin daya ne banda zabi amman kisamu ku rabu dan Allah kiman uzuri Amina."
"Okay nasan bazaki bada number ta da gayyaba Allah yasa kada ya kirani."
Ameen ya rabbi,ya lecture din.?"
Wlh lafiya lau banjima da dawo ba."
"Ina Fatash.?"
Har yanzun bata dawo ba sai takai 6 sannan."
Kice yau akwai kwasar gajiya Allah yabada sa'a."
Ameen ya rabbi.
Bye we talk later zanje lecture yanzun 4to6 ce."
A fito

Please Login or Register in order to submit comment