Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

washe da safe muka shirya mukayi portion as usual sannan muka tafi morning daganan muka tafi Assembly ana gamawa kowa ya tafi Class domin daukar lesson......


_Yar Mutan Kankia ce❣️_

Share
Comment


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


S1/E 5&6


******Haka akaita yimana lesson Uncle Kaka shi ne yaimana lesson din Biology akan what's Biology and Brenches of Biology har akayi break fast mukaje muka karbi tea and bread sannan muka dawo Class mai intergrated Science Uncle Isa ya shigo shima yaimana lesson,dayake lokacin Basic Science na yanuzun shine Intergrated Science ba kadan ya koyar damu ba,haka malamai sukaita shigowa last period dinmu mai Bussiness ya shigo malam Bala Umar Sayaya ya koya mana Demand ana wasa ana dariya har akayi ringing kowa yayi hostel saidai kowa yana ɗar ɗar kada atare shi daukar haya lokacin G.G Kankia akwai dalibai sosai kuma manya ne nagank na faɗa lokacin mune kanana shiyasa ba maison a tare shi (Haya) ma'ana daukar ruwan da seniors ke sawa koda Allah yasa muka wuce ba'a taremuba ba inda muka wuce sai Mosque akai mana jam'in sallah Baba mai Jam'i yajamu sallah shida Malan Bala Wada har aka gama sannan muka koma hostel dinmu kowa yafara shiri,daukar botikina nayi na tafi tankin Malan Bala dibo ruwa,dayake mu Hostel dinmu gab yake da Area Class kuma nan duk seniors sunfi yawa musamman *Hassun Mono da Hassun Yan Kankia sai Delu Doguwa da Delu Gajera* daman *Hassun Yan Katsina* shine House dinmu saiya kasance kamar ansaka mu tsakiya ne,da kafito za'ayi ram dakai abaka wanki ko kuma dibo ruwa.
tafiya nike da ruwa a saman kaina amman kirjina na bugawa fas fas dan tsoro ina shakkar kada akirani a juye mani ruwana ko kuma a kwashe mani kafin inkai Hostel dinmu aiki ban gama fargabar da nike ba naji wata Senior tace.

"Ke ke ke!!!."
Yanda take kwala mani kira kai kasan lamarin ba dadi duk da nasan dani take sainayi uwar shaggu da ita saima kara bazama sauri nikeyi inata addu'a ji nayi tace.
"Ke dan ubanki kika bari na taddaki wajen nan saina illataki ke JS1 mai cotten house were.!"
Wani daram daram haka naji,ba yanda na iya dole na juya na tafi wajen ta,tana tsaye baki house din *Hassun Mono* aikuwa tun kafin in tsaya naji ta kwaɗa mani mari duk da ruwan dake kaina,ina shirin saukewa ta sake ɗaura mani wani gigitaccen mari har saida botikin kaina ya faɗo ƙasa aiko ya dagargaje jaking dina tayi gashi duk jikina ya jike da ruwa amman haka matar nan taita dukana da hannu tana marina waini yar iska takirani zan tsere nikam sai aikin bata hakuri nikeyi dan naji marin da take mani tun ina iya dauka har saida nafara kuka wiwi ga zugi da kuncina ke mani amman haka wannan senior din tai mani dukan tsiya sannan ta bani consumer botikin fenti na elephant na dibo mata ruwa nai mata wanki da wanke wanke sannan tasani nacigaba da lining cikin rana har aka fara kiraye kirayen sallar la'asar batace intafi ba,hartayi wanka ta gana shiryawa cikin House were dinta Brown color sai taunar chewgam takeyi,cigaba da zagina tayi can mukaji haya gagar Malan Bala Wada yana cewa.
"Kutubur zalincin ne ya motsa sai naci ubanki Hafsat daman ke muguwa ce,ke tashi kijr ki shirya yanzun za'a tafi evening.!"
Ita wadda ya kira da Hafsat ganin Malan Bala ya nufota da icce ba shiri ta gudu tana gunguni,niko kasa tashi nayi sai kuka nikeyi daka mani tsawa yayi na mike a razane ina kuka yanda ya ganni jikina duk kasa ya baci take na bashi tausayi dayake Allah yaima Malan Bala tausayi ga jinkan Juniors kirana yayi na bishi tanki yafara tambayar abinda ya hadani da ita ina kuka na gaya mashi,bude wani daki yayi ya bani botikin karfe yana bani hakuri yace.
"Daina kuka Amina sai taci ubanta kuma saita biya maki bucket dinki data fasa dibi ruwanki ki tafi duk wadda ta tareki kice mata ni Bala Wada na hana kina jina.?"
Eh nace mashi sannan nai mashi godiya haka natafi nafara shiryawa a cikin ɗan lokacin daya rage mani wannan kenan.
******akwana atashi a sarar mai rai zuwa yanzun G.G Kankia takara tsamari lamuran ta tunda Ya Salma tayi Candy na kara shiga cikin maraici,yanzun an sauya mana Principal an kawo mana Hajia Rabi Bara'u Moh'd itace PC dinmu,ta kasance macece mai kamar maza kwarine babu kallabi tsakanin rauwuna kenan,jaruma ce ta gani ta fada kuma batasan sakarci daga teachers har students ba wanda ta ragamawa danko tunda aka kawota in har kaga daliba taje admin saidai in nemanta akai kowa ya kama kanshi haka malaman mu,kowa na tsoron disgi na Pc in dalibace kina tsoron hukuncin da zatai maki,wajen 2005 ta dawo G.G Kankia daga G.G kai kai,itace ta dauki yan last JS1 dinmu wanda daga su ba'a kuma daukar yan boarding ba a G.G sune suka gama a 2011.
Bayan an sake mana PC batai sati biyu ba aka bada shadows na 2006 lokacin ina JSS3 tunda aka fara lissafo sabbin Prefect yan School kowa yai tsit dan tsoro musamman da aka ambaci labor Prefect ya faɗa akan Murja Abu Cika dan ansan ba sauki kenan musamman a wajen yan SS2 haka aka gama aka tafi Class saidai ko wulgin blue baka gani kowa ya nutsu bamai yawo a tsakar makaranta saidai Shadows Prefect da kake gani wulgi wulgi sai kuma malama dake roaming about tsakanin Classes dan bad Lesson har kayai Break tunda aka bugu bell kowa ya balle da gudu zuwa dining sai bugun mutane sukeyi haka suka tare rabi da kwatar yan SS2 da coroling zaka iso ka amshi Alala da kunu haka suka kowa ya siga line kamar an mutu,Baba Hashimu dattijon kirki dashi da Umarun dining sai Yan lalo su suka kama bahon alala aka fara rabo lokacin Malan Isiyaku shine Kitchen Master haka aka gama rabama abinci akasa muka cinye shi gaya ko hadi babu danko SS2 cikin minti ukku akace su cinye shi ga zafi amman kamar mayu haka suke lunkumar Alala da kunu sannan aka bisu da ruwan bulalai lamarin dai ba dadi har lokacin break ya wuce suka sake kora kowa aka koma Class,akaci gaba da karatu.
After School hours angama Jam'i yan makaranta ne fululu a filin Kanya ana mana general Cleaning ana binmu da bulalai Labor da sauran Prefect masu zafi suke cewa.
"Yan makarantar nan!."
Baki ɗaya sai mu dauka muna cewa Na'am.!
Bakujin mu.?"
"Muna jinku."
Dan ubanku baku jinmu.!"
Muna jinku!!."
Haka sukaita yi mana suna dukan mu kamar jakai suna hawa bisan mu sannan sukara koramu cikin makaranta ba jimaw su maido mu filin kanya haka sukaita yi mana saida suka tare rabi da kwatar Makarantar sannan suka tada Yan JS1 sune yan Fresh Nana sukace su tafi hostel suyi C-ester haka kuwa akayi,daga JS2 yan Bount Nana sai mu JS3 Yan Ramat House sai yan SS1 yan Daurama House sai SS2 sune yan Amina House,mu kadai suka bari suna mana tsarki da bulalai musamman yan SS2 sai kaji tausayin su,sai duk dukan da sukeyi SP dinsu Samira Aliyu ko bulala bata daukaba hakama ASP Samira kwarama DSP tana dan bugu amman kadan dayake shekarar Simira³ duk sukejan ragamar makarantar G.G Kankia haka aka fara checking duk wanda baida roba da cup da takalmin yan maradi kalar kayan ka, ka shiga matsala uwa uba tsitsinya wadda ta zama wajibi ga duk wani ɗalibi,muda aka saka c-ester tadomu akayi aka hadamu mukaci gaba da gyaran makaranta cikin kankanin lokaci angyara G.G kwal baka ganin datti sannan aka koramu C-ester duka school din saidai yan Set dinsu suke yawo,har akaje evening kowa kaca kaca rabi da kwata duk uniform ke jikin mu,da haka akayi evening aka dawo aka wuce kitchen aka anshi tuwo miyat taushe su Babu da Saude sai Hajia da Rayya su Ramun dining da sauran yan dining suke mana abinci,sai Baba Hashimu shike mana Nika yana tai makama Students sosai sannan ya samana ruwa a tukunya ruwa ya tafasa ya zuba mana ajikon abincin mu haka yakema dalibai dattijon kirki kenan mai zuciyar alkhairi.
Koda muka gama ana gama sallar isha'i akayi Light up haka kowa ya kwanta kamar anmutu.

********ba'ajima da bada shadows ba,aka bamu hutu muka koma gida koda na koma gida ba kadan nafara kukaba tunkan hutun yai nisa nacema Babana nifa ban komawa makaranta so ake a kashemu da duka,ba kadan Baba ya tausaya mani ba haka ya dinga bani baki yana bani hakuri sosai da hikima harya samu ba hakura,haka Mama taci gaba da kwantar mani da hankali har nasaki jikina nafara hutuna cikeda farin ciki danko harna fara sauyawa ba abinda ke damuna.
Bayan kwana biyu da yamma nasamu Baba na tambaye shi zanje gidan su Asma'u bai min musuba yace saina dawo hka naje wajen aminiyar tawa muka bude babin fira iri iri cikin kulawa tace.
"Amina wai baki ganin komawar mu School ba ƙura ni wlh tafitar mani akai jibi kiga yanda aka fasa mani hannu dan zalinci wlh saida nayi jinya."
Murmushi nayi nace.
"Ke Husna miye abin damuwa yanzun SS2 sucemi bakiga yanda aka maida suba gwanin tausayi ba.?"
Keni kyaleni kowa kanshi ya sani jiya Ya Ali yazo gidan nan wlh yana ganina yace kamar mai ciwon ƙanjamau duk na lalace gaskia kilan bazan koma ba ina dalili."
Dan danan naji damuwa ta dirar mani zuciya idan Amina tace bazata koma ba ya zanyi da raina bayan nasan halin Babana zaice saina koma langabar da kaina nayi abar tausayi nace.
"Haba Asma'u karkice haka dan Allah kikoma kinsan Baba bazai sauya mani school ba,kuma kinga ke nike gani inji dadi araina."
Haka naita beging Asma'u har mamar su ta shigo ta hau yimata fada tace.
"Kibar wani lallashin ta itama tasan bata yuyuwa saita koma dan Baban su bazai maidota Day ba da take ikirarin dawowa."
Da haka naji sanyi a raina itaki ta cukule fuska kamar zatayi kuka cigaba da bata hakuri nayi da haka muka hau firarmu ta saki ranta bani nabar gidan su sai kusan magrib haka tai mani rakiya na dawo gida,salla kawai nayi na zauna da kannena muna fira sannan muka hau kallan film din hausa irin nada dinnan haka mukaci gaba rayuwar mu cikin farin ciki da anna shuwa.
*********hutu yai hutu lokaci nata kurewa abubuwa nata wanzuwa wani kaji dadi wani kuma akasin haka yau takama lahadi ranar ake komawa School as usual muna zaune da Mama a tsakar gida da sauran kannena tace.
"Yau sai makaranta aje aita karatu banda wasa."
Ai kamar jira nafara kuka ina cewa haba Mama zanje a kasheni ku kunanan kuna cin dadi ga nama ga shinkafa da miya banda abubuwa masu dadi nidai bazan koma ba.!"
Murmushi tayi mani tace.
"Nidai ba ruwana kadama kibari Baban ki yaji kuma kema kinsan yau dinnan zaki koma ba fashi."
Kukan naci gaba dayi itako daki ta shige tabarni ina aikin ibadar tawa,saida na gaji sannan na tashi na shiga toilet na watsa ruwa alwalla nayo na saka kaya nayi sallah,koda Baba ya dawo gaidashi nayi ba yabo ba fallasa ya amsani yaci gaba da duba Jaridar hannun shi cewa nayi.
"Baba dan Allah kayi hakuri nidai bansan komawa G.G ka maidoni Day dan al......
Wani wawan kallo da Baba ya aika mani ba shiri nayi shiru dan na tsorata da al'amarin shi,a sabule na mike na koma daki shigewa nayi dakin mu na afka bisa gado na hau kuka kamar raina zan fita daga jikina ba wanda yabani hakuri dan karin kaina na hakura har dare banji Baba yace inzo intafi School ba nima haka nai zamana ban fito na shirya ba,har dare ba wanda yai mani magana,ni daman haka nafiso nai zamana wasa wasa saida na kara kwana goma sannan na shirya nacema Baba zan tafi,ba tareda yace mani komai ba yabani focket money sannan yai mani addu'a ya saka kai zai tafi kallan mama nayi da mamaki ita kallan mamakin take mani da sauri tace.
"Baban Amina tagama shiri fa kai take jira ka maidata."
"Ki maidata da kanki mana ni ban maidata."
Yana ida fadar haka yabar gidan,zugum mukayi nida Mama kowa yai shiru faɗa tafara yimani.
"Kingani ko kibi abinda Babanki yace kinki gashi yace insan yanda zanyi dake yanzun ya kikeso ayi.!?"
"Mama dan Allah kiyi hakuri bazan kuma ba."
"Naji yanzun jeki gidan su Asma'u in bata tafiba kibita Baban su ya maidaku."
Toh nacewa mahaifiya ta,aiko ina zuwa na isake Baban su zai maidata gaida shi nayi yafara tsokanata yana cewa.
"Amaryata ba'a komaba kenan."
"Eh daman Mama tace zan bika saika maidamu nida Asma'u."
"Shikenan je kidauko kayan ki mutafi."
Da haka yaita jana dayake Kawun Mama ne,ni kuma nazama jikar shi,haka nagayama Mama taji dadi sosai fiddo mani da kayana akayi muka kama hanyar tafiya makaranta cikeda zullumi.
********washe gari Monday mun hallara gaban Assembly Pc tagama jawabin ta inda ta rufe da kiran yan karin hutu haka akaita kiran mu from JS1 to SS3 sai kafito gaban kowa zatasa Malan Abubakar Shekare yai maka bulala dai dai Class dinka labor nai mata dauraya haka Displine Master dinmu na time Ɗan Banye shima suka dukemu sannan duk ta koramu gida ranar kuka wajena ba abin misaltawa bane,haka shakku da tsoron Baba ya dirsar mani a zuciya tafiya mukayi har muka isa gida da kyal na samu nazo zauren gidan mu na tsaya har yamma Baba ne ya dawo ya ganni rabube jikin bango kallo ɗaya yai mani ya kauda kai yace.
"Wuto cikin gida."
Bin bayan shi nayi na wuce daki,koda Mama taganni ba kadan ta shiga rudani ba,saidai ta gaza magana shima Baba baice mana komai ba ranar haka na wuni a sussuce saidai mukasamu Baba yadan fita waje sannan Mama ta samu hope din yimani magana tace.
"Amina koreki akayi ya zamuyi kuma kinga ba fuska balle aima Baban ki wannan zancen."
Kuka na rushe dashi nace.
"Ai Mama harda ke da kika biyeni na kara hutu yanzun gashi ankoroni ya zanyi."
Bakadan na dinga kukaba,fada sosai mama tabani sannan ta nemi numbar wayar kanin ta lokacin farkon shigowar waya tanada Motorolla yana dauka tagaya mashi komai yace zuwa gobe zaizo ya maidani haka kuwa akayi har kagara nayi gari ya waye. Haka Kawu Umar yazo ya maidani ranar ahaka akaita dawowa da Students sai Pc tagama warning kasa hannu sannan zata anshi yarinya,da haka aka ansheni,sannan yai mani sallama na wuce hostel.
Haka washe gari aka kara taramu aka raba mana funishment ba kadan nayi dana sanin karin hutuba a rayuwata daga ranar ban kara gigin wani karin hutuba domin na gwagwatu kuma naga bacin ran mahaifina.

Akwai wata ranar alhamis da marece gaba da kiran magariba kowace yarinya na dakin ta tana shirin zuwa masallaci prefect suka fara hura usur ana kora zuwa compound ana dukan mu aranar kuwa harda Displine Master dinmu Ɗan banye haka yasa Prefect suka dinga dukan yan makaranta from JS1toSS2 sai gudu akayi kamar na tashin ƙasa dan bala'i haka akaita gudu kamar dabbobi wasu ka faduwa kasa ana takasu amman hakan bai hana ankyale muba saida aka hadamu wani babban fili bakin Chemistry Lab aka bazamu sannan.......


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


S1/E 7&8



"""""""Sannan Prefect suka fara takamu kamar ba mutane ba suna mana ruwan bulalai Despline na kara sasu wai munbar makaranta da datti saida akai mana ligib sannan yasa aka koramu sharar area classes ga magarib tayi ranar ce ta kasance bakar rana ga Yan G.G Kankia saboda ranar akayi gamo da katar ga duk wani mai tsautsayi dake cikin G.G aka kama kwasar aljanu yaran makaranta sai zubewa sukeyi kamar ba gobe a ciki kuwa harda masoyiyata kuma aminiyata Asma'u saida suka shige a sume ta fadi haka sauran yan makaranta ba abarmu sai gaf da isha'i sannan haka aka kwashi students sai filin masallaci Amirar lokacin da sauran official suka fara yin karatun alqur'ani harda Baba mai Jam'i haka aka tsaya ka'in da na'in anata rukiya saidai kamar ana kara ingizo su sai kada zubewa akeyi ,intakaice maku ranar dai sam lamarin bai dadiba haka washe gari akaje Assembly da anfara Prayers Aljanu zasu fara tashi aita zubewa haka filin Assembly ya koma filin yan bori tabbas PC ta nuna rashin jin dadin ta akan faruwar lamarin haka tasa Malan Abubakar Boyi da sauran malaman addini suka fara bada addu'oi ana koyawa mana.
Bayan kwana biyu jikin Asma'u sai kamari akeyi ba shiri aka aikama iyayen ta sukazo suka tafi da ita gida dan neman guduwa takeyi haka rayuwa taci gaba da wanzuwa saidai inyi kuka idan kewar Asma'u ta kamani domin ita kadai ke gareni haka na dangana na dauki Qaddara domin nasan komai ne ya rigada ya wanzu sannan kuma Bakin *ALQALAMI* ya rigada ya bushe kuma *Haka Allah Yaso* Sannan kuma Komai *Lokacine* da haka naci gaba da rayuwa ba dadi komai ba zuwa a dai dai.
Wata rana da daddare ana zaune a masallaci aljanu na tashi sai ihu ake kwadawa haka Baba mai jam'i zai tsaya har kusan tara ya zauna damu yana bamu addu'a,mutumin kirki Malan Magaji Allah yajikan rai yai mashi rahama yasa mutuwa hutuce agare shi🙏
Dayake ya rasu a halin yanzun,haka zai tsaya yana bamu karatu da azkar shida Amira da sauran official ba JS1 ba SS3 lokacin jinni sun tisomu gaba addu'ar da aka bamu ta _Lau'anzalna harzal qur'ani aka jabalillara aitahu kashi'a kashi'an mutasaddi'an min kashyatillah_ ......zuwa karshe haka zamuyi tayi kamar ba gobe saida ta zama abinci kuma abin sha ga yan G.G Kankia saida kowa ya iyata da Qul'auzai haka mukaitayi da Ayatul-kursiyyu koda Assembly idan zamuyi prayers su mukeyi sai gashi cikin yardar Allah aljanu suka lafa suka daina tashi hakanan sai inda kwakkwaran dalili.
Bayan sati ukku kawata ta dawo ranar murnar da nayi bata misaltuwa haka mukaci gaba da rayuwar mu gwanin ban shi'awa saidai ko sati ukku bata cikaba ciwonta ya tashi harta neman guduwa suna cewa basu san boarding ba shiri aka kira Baban su inaji inagani aka dauke mani kawata akaro na biyu saidai wannan tafiyar bata dawowa bace ga Asma'u ba nayi kuka marar kyaun gani haka nazama kamar wata marainiya haka nakoma wannan tana ɗaya daga cikin ranakun da bazan taba mantawa da itaba a cikin rayuwata ta G.G wannan lalurar da tasamu kawata mafi kauna da soyuwa agareni yau gashi ta tafi tabarni duk da nasan *haka Allah yaso* sannan kuma komai rubutaccen al'amari ne domin komai ya wanzu ta hanyar *ALQALAMI* Wannan kenan.
"""""""""""Haka rayuwa ta kasance ba dadi a wajena kullin ina kan tunanin kadaicin daya gama addabar rayuwata ga fargaba da kusan kowane ɗan boarding ke fuskan a cikin zuciyar shi na shigowar da katti keyi duk dare haka suke round ɗaki ɗaki haka yan makaranta zasuita ihu ƙato ana gudu kamar me wata ma take gamuwa da ciwon jinni wata kuma tafadi abi ta kanta ataka a wuce da dama mukanji mugun ciwuka ajikin mu duk ta sanadiyar gudu da muke kwasa akan katti da suke shigomana a cikin school.

Akwana a tashi ba wuya wajen lillahi gab muke da fara zana JSC sai murna mukeyi kowa yanaji da kanshi dan gani mukeyi har munfi masu SSCE matsayi da ganin mudin wasu ne zuwa lokacin duk wani walahala ta shadows takare saidai abinda ba'arasaba haka muka dukufa karatu har mukazo mukayi JSCE murna wajen mu bata faɗo haka mukaira bankwana da kawayen mu,wasu nacewa basu kara dawowa transfer zasuyi wasu nacewa sudai zasu dawo nikam bance komai ba,ranar da mukayi final exam ranar Asma'u tazo daukata ina fitowa ta kadaddabeni ta anshi kayana muka shiga mota sai gida Charanci duk da itama d alama daga jarabawar take dan dai ita takoma Day tun amota take mani fira nikam saijin dadi nikeyi kamar anabani kyautar mota ganin kawar tawa ta warke kamar ba itaba,baifi minti sha biyar ba muka iso gida,tara ta musamman na samu daga makota har zuwa yan uwa da abokan arziki haka akaita zuwa ana mana murna kai jace Candy nayi mai baki ɗaya saijin dadi Mama takeyi koda Baba ya dawo saida yaimani kyauta ta musamman kaya ya siyamani after dress sai dinki shadda mai kyaun gaske yaimani nida Asma'u gift na JSCE sannan yai mani alqawalin zai barni inje hutun da nike kwakwar zuwa wajen Yayar Babana dake Kaduna ranar ji jike nafi kowa gata dan murna ko godiyar kwarao nagazayi saidai kana ganin fuskana kasan najin dadin wannan albishir na mahaifina.
***********bayan kwana biyu da gama jarabawar mu aranar ne nacema mahaifina zanje gidan su ganin kakanina duk ni kakata tarasu da kakana namiji amman Step grand fa dina tananan da ranta,bai min musuba haka muka shirya nida kanwata Zainab mukayima Mama sallama mukatafi direct Asma'u na biya mawa bamu jimaba ta shirya muka tafi har munfito soro muka hadu da Baban su gaidashi mukayi nan yafara tsokanar mu yana cewa.
"Inyeh Yan' matana an girma angama jarabawa Allah yaima rayuwa albarka ina zakuje har haka.?"
Murmushi nayi nace.
"Zamuje gidan su Anty Hadiza."
Shima murmushin yayi yace.
"Shine kuketa wannan dauki harka da wannan gayu kamar zakubar gari,to kigama yawan naki kinga wancan dakin nan zaki shiga."
Ya ida maganar yana nuna mani wani daki dake gefe,nima murmushin nayi dan nasaba da jan dayake mani na kaka da jika nima cikin zolaya nace.
"Haba ni mizanyi da tsoho aini sai saurayi."
Dariya yayi yace.
"Shikenan nagani ai Allah yadawo daku lafiya."
"Ameen muka amsa taro kudi yayi dari Ukku yace muhau mashin godiya mukayi mashi muka tafi muna yar firar mu har muka isa gidan kakannin nawa haka muka zauna saijin dadin ganin mu sukeyi ranar acan muka wuni mukayi zumunci da sauran dangi har gidan Yayan Babana saida naje mun jima sosai acan sannan mukayi masu sallama muka fito,a kafa muka tako muna fira muka yanko ta kofar fada zuwa gida kallan kawar tawa nayi nace.
"Gaskia muhau mashin harna fara gajiya da wannan tafiyar akafa."
Murmushi tayi mani tace.
"Kinga ko ragganci da ace a school kike kinsan kilo meter nawa kike kwashema kina tafiya akafa dayake andawo gida jiko ya mutu ko.?"
Dariya maganarta ta bani har saida ba dara nace.
Wlh kuwa kinsan ai munsaba da aikin wahala shiyasa bamu ganewa kuma kingafa har mun kusa isowa baifi minti goma ba cikin munjima."
Aikuwa dai ashe kema kin fahimta kinga kwara kawai mu ida ko kanwata."
ta ida maganar tana kallan Zainab wadda batace mana uffan ba saidai in munyi abin dariya tayi kotayi murmushi jinjina kai tayi tace.
"Nima dai abinda nagani kenan Anty Asma'u mu ida kawai tinda mundawo gida."
Kallan su kawai nayi da haka muka idasa gida,gidan su Asma'u nan muka sauka muka baje a falon mamarsu muka hau labarai ina bata labarina da kuncin dana shiga bayan ta barni a school,itama ta fada mani kalat missing dina da tayi lokacin data dawo gida ba kawa,hakadai mukaita yar firar mu saida mukayi magarib sannan muka shiga gida,daki na wuce na kwanta kafin zuwa isha'i.
Sallamar Baba najiyo koda ya zauna haka mukaje munai mashi barka da wowa yawwa ya amsamu baijima da zamaba aka kawo mashi abincin dare sunata fira da kanina Ahmad nikam ina falo wajen Mama muna tamu firar sallama muka jiyo bada jimawa saiga wani matashin yaro ɗan makota ya duka ya gaida Baba sannan yace ance ana sallama a waje."
To cewar Babana.
Bai jimaba ya fita wani saurayine ya gani sanye da kaya masu mutinci da ƙima na hausawa yana ganin Baba da sauri ya duƙa kasa ya gaida shi,amsawa yayi cikin girmamawa kallan da Baba ke mashi hakan ya tabbatar ma saurayin tambayar shi yake,sosa keya yayi yace
"Baba daman nazone neman wata alfarma wajenka inbadamuwa."
"Inajinka fadi alfarmarka."
Baba ya ida maganar ba yabo ba fallasa."
Sake sunkuyar dakan shi yayi yace.
"Nazo neman izinin auren Amina dakai mani izini inyi magana da ita."
Jinjia kai Baba yayi sannan yace
"Alhmdullh naji dadin hakan saidai kasani Amina kankanuwar yarinya ce duka duka shekarar ta sha biyar a duniya sannan kuma karatu takeyi JSCE tayi amman minene sunanka.?"
Sunkuyar da kanshi yayi yace.
"Sunana Mustapha Hashim Bakin kasuwa."
Nana yaima Baba bayanin nasabar shi sosai

Please Login or Register in order to submit comment