Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nasu insha Allah banda Taufiq da ya hade rai kamar banda shi ake maganar Abba ne yace.
"Kaifa Taufiq kayi shiru ko bakajiba."
"Aini na fidda Abba."
Baki ɗayan mu muka kalle shi kowa yana mamaki hattani dake bakuwa nayi mamaki domin inaji Mum na masu fada ko budurwa basu da ita amman wai shi yace harya fidda ban gama sakon zucin da nike ba naji Abba yace.
"Ina take wacece ita.?"
Duk yai mashi wannan tambayar.
Dagowar da zanyi idanun mu suka sarke dana juna wani ras ras haka naji still ni yake kallo yake ba mahaifin nashi amsa.
"Time will tell Abba,kaimin uzuri,zanje office."
Yana gama fadar haka ya mike cikin uniform dinshi jinjina kai Abban su yayi baice ma dan nashi komai ba sanin miskilancin shi yai gaba abin shi.
"Haba Alhaji akanmi zaka biyema Taufiq tunda ya samu ai saiya fada mana kowa yaji."
Cewar Mami ɗaga mata hannu yayi baice komai ba.
"Eh gaskiar Abba abari lokaci zai fada mana komai muyi masu fatan alkhairi."
Cewar Fiddausi.
Kallanta Abba yayi yace.
"Including U Fiddausi kema ki fiddo miji understood."
Gyada kai kawai tayi hakan yasa muka murmusa danji tayi dama batayi magana ba.
Haka rayuwa ta kasance a Kaduna komai yana tafiya normal dan ba kadan Mami ke mani gataba haka Mum danko Ya Samir kamar ya goyani dan mutunci banda Ya Taufiq dake bani tsoro shiyasa nike shayin sa wannan kenan.
******Bayan wata ɗaya baifi sati biyu ba inkoma gida saboda jarabawar mu ta fito kuma munci saidai G.G Kankia zan kara komawa.
Muna zaune a falon Mum,nida Fatima munayin game a tv aikam nacita fasa ihu tayi tana cewa ita bata yardaba itace tai wining nikam naki yarda akan itace taci aikam haka mukahau musu muna rigima akan game,bamuyi auneba mukaji an daka mana uwar tsawa,Ya Taufiq ne tsaye cikin jins and t-shart a razane kuma naba'a hade rai ya kumayi yace.
"Ke Fatima bakida wayo ko?bazaka ki bar mataba.?"
"Ya Taufiq aini nai wining fa ba ita.....
"Shut up u re very stupid ina fada kina faɗa i will deal with u nonsense.!"
dan danan idanun Fatima sunkawo ruwa nikam kamar ruwa ya cinyeni sai faman raba ido nikeyi dan nagama tsorata da alamarin Ya Taufiq.
"Kutashi kubar falon."
Har rige rige mukeyi dan mun firgita,da sassarfa na fara hawan stairs maganar da yai manice ta daki dodon kunnena har saida jina yadan dishe na wucin gadi saboda abin yazo mani a bazata.
"Minal.''
Cak na tsaya koda bansan sunan da yakirani dashi ba ainasan ma'anar sa dai Amina yake nufi,tsaye nike u nakasa waigowa bare inzo kiran dayake mani.
"Minal."
Sai a lokacin na juye yanda ya kafeni da shanyayyun idanun shi mai saka mutun razana haka na tako kamar wadda kwai yafashe mawa a cikin ciki har na iso wajen shi dukawa zanyi ya ɗaga mani hannu.
"Wai kin kusa tafiya dagaske ne.?"
Da sauri na ɗaga kaina nace Eh.
"Kicema Mum ina jiranta a falo."
"Toh."
Juyawa nayi ina sauri amman tafiyana na hardewa still nafara hawan bene yace.
"Minaal."
Ya ida kiran sunan nawa yanajan karshe tsaye nayi dan har nafara kawo kwalla bansan ko second ɗayane inyi da Ya Taufiq,Na'am na iya furtawa dawowa nayi bance komai ba sai faman wasa da nikeyi da yatsuna nakasa kallan shi,shima din baice mani komai ba saidai jikina yabani ni yake kallo ta gefen ido na saci kallansa karaf idanun mu suka sarke ji nayi kamar inyi fitsari sai naga kamar yana hararata duk saina tsargu shiru mukayi kamar wasu kurame
"Kidawo wajen Mum da zama."
Kamar aradu naji zancen shi,hakan yasa na kalle shi amman baki taba cewa shiyai maganar yanda ya murtuke ba alamun annuri,sadda kaina nayi nace.
"Baba bazai bari ba."
"Uhmmm jeki."
Bance komai ba na tafi ina addu'ar kada ya kuma kirana a karo na ukku,direct dakin Mum na isa,lokacin tana waya,saida najira tagama nagaya mata sakon Ya Taufiq,to tace mani nazo fitowa bedroom dinta zuwa karamin falon ta daya gaji da haduwa mukayi taho mugama da mutun dagowar d zanyi naji hanjina sun kada garda kululu haka yabada sauti Ya Taufiq ne saidai kuma naga alamun annuri a fuskar shi tsoro yabani a raina nace kaga mutun kamar mai jinni harya saki ranshi,dariya naga ya kece mani da ita yace.
"Trouble so kike ki karya yayan naki ko?kema kin zama sholi kenan."
Nikam dai al'ajabin shi nike zancen Mum ne ya katse mani nazarina akan Ya Taufiq tace.
"Haba Tariq taya zaka bige mani Ya' sannan kaxo kana cewa zata karya ka miye haka.?"
"Sorry Mum ban kulaba ai bamu yar haka da darling ko besty."
Sai a lokacin nayi sirriyar ajiyar zuciya na kirkiro murmushi ganin Ya Tariq ne ba Ya Taufiq ba nace.
"Eh yi hakuri Ya Tariq ban kula ba."
Bakomai besty."
Fita nayi naji yana cewa.
"Mum kefa muke jira miskilin dan ki na falon kasa."
To cewar Mum,aiko ina sane na leko shi daga saman bene yana zaune bis kushion ya harde kafa ɗaya bisa ɗaya yana latsa wayar shi ashe kaya iri daya suka saka shiyasa nakasa gane su.
a hankali na zame jin maganar su Mum nayi dakin mu.
Aiko haka Mum taje itada ya'yan nata sunjima suna tattauna muhimmin abu a tsakanin nidai bansan abinda suke tattaunawa ba saidai naga fuskar Mum cikeda annuri,har aka fara kiran sallah hakan yasa nida kawar fadana Fatima bayan mun shirya muka fito zamuje garden anan muka iske Mum dasu Ya Taufiq sunyi abin dariya suna dariya shikam gogon naku saidai murmusawa da yayi har saida hakoran sa suka fito the first time da naga murmushin Ya Taufiq.
Haka muka shigo ta falon zuwa waje sannu da hutawa mukai masu Ya Tariq ne ya amsa Mum tace.
"Ina zaku kuka sha dogayen wanduna har haka."
"Garden zamu Mum."
Wani kallo Ya Taufiq ya watsa mana,nida Fatima ba shiri muka kama kammu,ganin munyi tsaye mu bamu tafiba kuma mu bamu koma ciki ba,a fusace yace.
"Badaku nike ba.?"
Da gudu Fatima tayi sama tana kuka,nikam bangane yaran saba,dan jikina yai sanyi,rakani da kallan ke bakiji abunda nace ba."
Yanda Mum taga bangane manufar saba yasa tace.
"Mamana kikoma daki ku sauya kaya kinji."
"Da kin barta na ballata.!"
Haba Taufiq miye haka bata gane manufar kaba,kabita a hankali."
Mtsw shine abinda ya iya ja,nikam kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki haka naji a sannu nike tafiya harna isa dakin mu.
"Mum kidaina daka ta yaran nan,taya zasu fita waje duk garada suna ganin jikin su,jibi kiga Minal yanda jikinta ya fito haba wannan sakarci ne.!"
Kallan mamaki Mum tabi Ya Taufiq dashi ganin yanda ya hakikan ce har da nuna bacin rai.
"Cool down Taufiq yarane zasu bari karka bata ranka wannan irin dogon zance duk kai keyin shi."
"Forget about Mum."
Hmm Allah ya kyauta."
Ameen cewar Tariq
"Tariq muje in raka ka dan wlh idan ka kara 5mint kayi loosing.!"
"Eyeeh da kyau rashin mutunci zakai mani ko Hussain.?"
"Haba Hassan sorry wlh wannan Minal din nan ce ta bata mani rai.!"
"Wai wacece Minal.?"
Cewar Mum.
"Aminar Baba Yusuf mana."
"Okay na fahimta."
Kutashi kuje Allah ya tsare."
Ameen ya rabbi."
Haka suka fita komai nasu gwanin birgewa tsawon su daya haka kayan jikin su iri dayane da haka suka shiga mota,Tariq ya jasu zuwa Malali.
*******wani katon gidane na fadi da busa suna isa aka bude masu gate suka shiga cikin compound din wani saurayine ya fito yai masu iso zuwa cikin falon gidan wanda ake saukar da baki,zama sukayi saman ƙawatattun kujerun falon bada jimawa ba wata kyakkyawar budurwa ta fito sanye cikin maroon din atamfa da sallama abakin ta,wadda ta kasa idata sabanin ganin su Ya Taufiq da tayi kamar anyi kaki tsabar kamar da sukeyi,tunda Ya Taufiq ya dago ya kalleta ya maida kallan shi kan wayar shi ya Tariq ne yace......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


S1/E 13&14


"Ranki shidade,bissimillah."
Kallan su kawai takeyi sai alokacin ta iso ta zauna tana facing din Taufiq a tunanin ta shine bakon nata cewa tayi.
"Yawwa,ya naga ba'asan yi mani magana nagane ko kake ka baddani kenan dan in kasa ganeka ko.?"
Ko kallan ta Taufiq bai kuma saidai smile da yayi yaci gaba da latsa wayar shi wadda ta zama abokiyar firar shi.
Taufiq kenan haka yake karki damu da yanayin sa,kuma bashi bane wanda kike tsammani nine."
Kallan shi tayi tana al'ajabi sannan tace.
"Allah mai iko sannun ku da zuwa ya hanya."
"Alhmdullh,mun sameku lafiya.?"
Cewar Taufiq.
"Lafiya lau alhmdullh."
Da haka sukaita firar su,shidai baice masu komai ba saidai aikin latsa waya da yakeyi,suko sai soyayar su sukeyi Aisha Manga kenan cikakkakiyar Doctor ta mata wato Gaconagy sun hadu da Ya Tariq wajen aikin su,duk da department dinsu dayaba,amman suna haduwa a wajen aiki,shi Doctor ne na kowane fanni irin su Theater Surgery d.s
Aisha Manga ta mutu kan son Ya Tariq duk da suna asibiti daya kuma suna gaisawa amman shi baitaba sonta ba saida mahaifin su yace su fiddo da matar aure shine ya amshi tayin soyayar ta.
Sosai suke fira da Tariq,shiko gogon naku sai lokacin ya dauki ruwa ya zuba cikin cup ya kurba ya kalle su yace.
"Romio and Juliet it's time."
Ya ida maganar yana mikewa tsaye,wani kallo Tariq yabi shi dashi na ka kyauta yace.
"Bari muje sai munyi waya."
"Tom tunda kanin namu ya matsa mana ai shikenan."
Kallan kin rai nani Taufiq yai mata yai gaba abin shi,saida suka kara gaisawa sannan tai mashi rakiya already Taufiq ya shige cikin mota driver sit shiga Tariq yayi, Taufiq yajasu suka tafi gida wannan kenan.

*******Bayan sati ɗaya nafara parking kayana domin komawa gida,gajiya nayi na kwanta cikin kankanin lokaci kuwa bacci gai gaba dani ban farkaba saida naji yunwa na dawainiya dani,tashi nayi nai wanka sannan nayi walla sallah nayi na fito cikin riga da wanko da fakistan saidai basu kama mani jikiba sosai, gyalen su kawai na yafa nasaka turare nayo falo tamkam na iske su zaune sunata fira Ya Samir kebada labari da Mum da Tariq sai Taufiq,su Fatima da Aisha sai Zakiyya sunata lido as usual.
tafiya nike kamar ina sanɗa kai kace zasu kamani dan bansan suji takona bare su kalleni Fatima ce tafara ganina murmushi ta sakar mani taci gaba da game dinsu ta lido,Aisha ce tace.
"Lah Anty Amina sai yanzun kika tashi ko lunch fa bakiyi ba,mukam har mun gama namu."
Murmushi na kirkiro a fuskata,kallona sukayi su dukan su tinda Ya Taufiq yai mani kallo daya ya dauke idan shi akaina,ya cigaba da duba jaridar hannun shi,hakama Ya Tariq Murmushi kawai yai mani Mum tace.
"Kije kiyi lunch Mamana."
Tom Mum barkan ku da hutawa."
Yawwa.
Kama hanya nayi a nitse nayi dining Ya Samir yace
"Kanwata ba gaisuwa."
Sosa keyata nayi alamun jin kunya nace.
"Ina wuni Ya Samir."
"Lfy lau Yan mata."
Kallona Ya Taufiq yayi idan mu na hadewa na sauke nawa,nafara zuba pride rice sai paper chicken take nakara nin yunwa ta yun kuro mani diba nayi nafaraci ji nayi yace.
"Minal save me."
Baki daya sukabi shi da kallo wanda yake bude jarida kamar bashi yai maganar ba,ko ajikin shi,Ya Samir yace.
"Dazun ba yanda ba'ai dakaiba kace bakaci lafiyan ka Taufiq."
"Normal yanzun nikeda ra'ayin ci."
Sake maida kanshi yayi a jarida,nikam jin abinda yace hakan yas na zuba mashi kima.
Dago kai nayi nace.
"Ya Taufiq nazuba."
Jinjina kai yayi nikam cigaba da cin abincina nayi,banyi auneba naji yaja kujera yana facing dina a hankali na janyo mashi flat din kallona yayi ya kalli abincin yace.
"Nidawa.?"
Aje spoon din hannuna nayi nace.
"Nakane kai kadai."
"Uhmmm."
Cigaba dacin abinci nayi amman kadan kadan nikeci sabanin da danike buga uwar lomata,amman yanzun dole na koma yar gayu irinsu.
Fidda spoon din yayi yasaka fork da shi yafara tsokalar abincin yanaci kamar baiso, saidai kadan kadan idanun mu na haduwa hakan yasa natashi dan jinayi harna koshi duk da nasan ba koshin bane,juyawa zanyi intafi na tsaya cak.
"Sit down."
Komawa nayi nazauna bance komai ba abincin gaban shi ya turo mani yace.
"Maza within a 5mint ki cinye shi naci nawa saura naki."
rau rau idanuna suka ciko da kwalla waigawa nayi na kalle wajen su Mum amman batamu sukeba kowa da abinda yakeyi ganin bamai kawo mani dauki hakan yasa nafara cin abincin kamar inyi kuka saukina ma wayar shi yake latsawa alamun hankalin shi baikaina ina ganin haka nafara saka lemo dan in sauri intafi,haka naitayi ganin cin abinci da fork zai bata mani lokaci ba arziki nasa spoon na ciko katuwar loma saida nakai bakina nasaka kenan ya kalleni gashi nasakata cikin bakina da sauri na guntse dimple dinshi kawai naga ya lotsa alamun murmusawa yayi.
Ji mukayi Ya Samir ya zauna gefen mu yace.
"Major nifa ina ciki da kanwar nan taka kaimani iso wajen Baba."
da sauri naga ya aje wayar shi,yana kallan Samir nikam yinayi kamar bansan takan zancen ba.
"She's SS1 karatu takeyi."
"I know ta ida gidana."
"Look Ya Samir we talk later Minal jeki ciki."
Mikewa nayi na tafi shima Ya Taufiq mikewa yayi yace.
"Nagaji dayawa shiyasa bye."
Jinjina kai Ya Samir yayi shima tashi yayi ya tafi side dinsu.
Kayan mune muka zuba cikin boot inda drivern Mum ya shiga cikin mota yai mana hone muna ciki nida Fatima,Mum da autar ta suna cikin mota,tareda Fatima muka sakko kasa duk munsha after dresses a jikin mu,a falo muka taddasu Ya Tariq kowan su yana aiki a system gaidasu mukayi duk da ban kallesu amman naji sanyayyar muryar Ya Tariq shine ya amsa mana,saidai ba wanda ya damu da halin ko in kula irin na Ya Taufiq,wucewar mu,mukayi har munzo bakin fita part din mukaji yace.
"Minal,Fatima kuzo nan."
Jim kadan mukayi sannan muka juwo muna zuwa muka tsaya,nikam kaina na kasa kallan mu yayi yace.
"Look at me Minal."
Dago idona nayi na aza a kanshi kamar yanda ya umurce ni.
"Zakuje Abuja kuyi one week na kuskura naji kunyi wani misbehave ko fita yawan banza ko kuwa kula samari ni kadan abinda zan maku saina ballaku understood.!"
Jinjina kai mukayi,Eh Yaya cewar Fatima.
Nikam nakasaa magana saida ɗaga mashi kai da nayi dan yaimani kwarjini da yawa kuma kallan dayake mana sainaga kamar ni kadai yake kallo cos ranshi a hade yake.
Juyawa mukayi zamu tafi jin baikuma cewa komai ba.
"Minal."
shine abinda kunnuwa na suka jiye mani itako Fatima ganin bai kira da sunan taba ai da sauri tayi waje nikam kamar in kurma ihu haka nikeji a raina dawowa nayi nace.
"Gani Yaya."
Nakai sakon goma kafin yace.
"Bakiji me nace maku ba.?"
Shiru nayi har saida Ya Tariq ya dago daga aikin da yakeyi ya kalleni,sadda kaina nayi dan nagane manufarsa a hankali nace.
Naji insha Allah zamu kiyaye.
"Good."
Jin kadan nayi ganin bai sallameni ba nikam ina tsoron kada in tafi nayi wani laifin,shikam fita yayi safgata yaci gaba da operating system din shi.
"Amina jeki kinji Allah ya tsare."
Cewar Ya Tariq,ai sa sauri na juya ina cewa ameen.
A mota na taddasu shiga nayi ina zama Fatima tace.
"Mi wannan dan sa ciwon kan yace maki.?"
Yace ban amsa abinda ya gaya mana bane,shine na amsa.
Dafe goshinta tayi tace.
"Ya Taufiq problem miskili kafi mahaukaci ban Allah ya kyauta."
Ke Fatima yayan naku kike cewa haka kisa a ranki kamar a gaban shi kikace hakan."
Ai dan danan Fatima ta shiga damuwa tafara ba Mum hakuri kamar zatayi kuka ni dariya taso bani na guntse abuna.
Mum kiyi mata hakuri cewata.
Shikenan Mamana.
Da haka Sojan dake gabam motar yajamu zuea birnin tarayya.
Koda muka isa Abuja a unguwar Maitama muka nufa cikin wani daular gida mai ban mamaki,ya hadu ya haduwa.
Kamar yanda kowa ya sani unguwar Maitama unguwace data hada jibga jibgan masu kudi masu fada aji tun duniya na kwance,haka muka shiga katon compound din gidan mai part ukku na gefe gefen iri dayane saina tsakiyar kalar tsaruwar shi daban ne akalla parking space din shi mota kusan ashirin suna iya parking,koda muka isa duk tamu motar motoci guda goma ne a compound din,kamar ansan da zuwan mu ma'aikata suka fito tararmu har side din dake ta bangaren dama nan mukayi,saidai abinda yabani al'ajabi muna shiga ciki wani sanyin Ac da kamshi ya daki hancin mu,maimakon mu tsaya falo kafin matar gidan ta fito mu gaisa sai naga Fatima ta kama hannuna munyi wani corridor dakuna ne guda ukku a jere sai biyu na kallan ukkun cikin na jeren naga ta murza handle muna shiga nayi tozali da wani hadadden gado,zare dress din jikinta tayi ta fada bathroom.
Kafim ta fito wanka har an shigo mana da troly dinmu,tana fitowa naga ta bude wardrope ta dauko wata doguwar riga ta zira nikam ce mata nayi.
Kekma baki zake ba Fatash."
Dariya tayi tace.
"Ikon Allah daga baki labari Ya Bash jiya harkin hada sunan mu waje ɗaya amman fa yaimani suger sosai."
Ya Bashir ɗan kanin Baban sune shine suke soyayyaa boye saboda ƙa'idar gidan su Fatima baki isa kice xakiyi aure ba saikin hada master s degree dinku a mace namiji kuwa saikayi Phd sannan saboda baban su cikakken dan boko ne na fadi da busa.
Eh mana ai sunan yai dadi,amman ina matar gidan nan ke daga zuwa kinhau sauya kaya."
Dariya ta kece dashi harda rike ciki tace.
Malama tashi kije kiyi wanka Minal."
Murmushi nayi nace wato kema kinzama Ya Taufiq kenan ko?
Yes nice name yai dadi ai."
ɗage kafada nayi bance komai ba,can kuma nace baki bani amsa ba wai ina mai gidan nan."
Mum dinki itace mai gidan."
Bangane ba,kamarya.?"
OMG Minal gidan mune fa na Abuja wannan side din na Mum na tsakiya kuwa part din Dad,a cikin shi side hudune first&second apartment na Ya Hassan ne da Ya Hussan sai third na Abba ne sai fouth shine na Ya Samir,sai kuma wancan dayan part din irin wannan na Mami ne kinji dan haka shiga wanka malama ta,yunwa nikeji naga an hada mana lunch."
To shine abinda na iya furtawa na tashi na fada wanka banjima ba na fito nima rigar na saka ta atamfa aikam tai mani kyau sadda muka fita har Mum da autar ta sungama lunch muma zama mukayi muka fara,Mum ce ke waya da alama da Ya Taufiq take magana dan naji tana cewa angama Major Hussain ba inda zasuje."
Da haka naga tabar dining area din gaba ɗaya.
Haka rayuwar mu taimana dadi a birnin tarayya,munyi yawan bude ido kusan kullin sai mun fita da Mum daga Maitama among the park muka fara,munyi yawo haka cikin soldiers aka ware mai mana hoto, the next day mukaje Wonderline haka dai muka warwasa sosai naji dadin hutun sai nakara sakewa da banganin su Ya Taufiq musamman ma shi,haka ana gobe zamu dawo Mum takaimu Sahad mukayi shopping kowa ya dauki abinda yake bukata a cikin mu sannan mukadawo gida muna gama dinner muka kwanta nida Fatash,bacci yi gaba damu saida akai asuba muka farka ana azuhur muka shirya muka kama hanyar dawowa Kaduna ji nayi kamar kada mudawo dan nasan yanzun Ya Taufiq zai hanamu sakat duk da bai cika magana ba amman yanada tsanani koda yake ba abin mamaki bane kasancewar Soja,aikam sadda za'ayi la'asar muka iso har gida ana parking dai dai da leda bamu daukaba mukayi daki,masu aiki suka kawo mana kayan mu daki,suka maida komai muhallin shi,tunda muka dawo gidan tsit haka muka huta gajiyar mu da daddare Ya Tariq ya shigo yaima Mum barka da wowa haka ma Ya Samir saidai yan kwana kinnan naga wani kallo na musamman Ya Samir yake bina dashi ga mutuncin shi ya waita agareni komai yace ni,nikam murmushi shine abinda nike iyawa Mum da Ya Tariq sun dauka mutunci da kara yakemin nikam nasan bakin zaren tunda naji yacem Ya Taufiq yana sona duk da gabana yafada amman ban nuna mashi cewa ilimina yakai nan ba duk da kuwa inajin dadin haka ace a sona musamman da mutun mai class kamar Ya Samir wai yace yana sona wadda ko a jerin mata ban cikin sahun mace ta goma da za'a zaba dududu shekarana shabiyar yan budircina ma baikaiga wanke mani kyauna ba bare in zama babbar budurwa.
"Amina ya hanya."
Lfy lau Ya Samir,ya muka sameku.?"
Alhmdullh."
Da haka yaima Mum sallama ta tafi.
*****Yau kimamin kwana biyu da dawowar mu amman ba keyar Ya Taufiq ba alamun shi,ni kaina nayi mamaki amman ban wani damuba dan daman ni haka nafi so,auta ce tace.
"Mum koya Taufiq bai kasar ne,naga ban ganin shi kuma ko gaidaki yadaina zuwa."
"Karki damu auta ta,yana cikin gidan nan ba inda yaje yana part dinsu,kinsan halin botsewar Yayan naku saidai kullin yakirani waya."
"Uhmmm wlh matar Ya Taufiq tabani wannan hali ai sai mai hakuri zata dauke shi,ni gwarama da Abba yace duk su fiddo mata yai masu aure suje subamu waje ko mun huta."
"Auta ba ruwa in suka jiki ki kama bakin ki,mi ruwanki samanki suke kai Allah ya shirya mana zuciya."
Ameen na amsa a hankali.
Maganar da auta zatayi mukaji ana cewa
"Yes sir afito lafiya."
Ai saida kowa ya nutsu hatta Sholi dake kwance bisa cinyar Mum saida ta tashi zaune Fatash dake kallo a waya ta datse kallon tana gyara zaman ta,nikam tunda naga Ya Taufiq cikin dakekiyar shadda milk na maida kallona bisa tiles,cikeda da takun kasaita ya karaso yana zuwa naga ya sunkuyo kusa da fuskar Mum yaimata kiss a kumatu sannan ya zauna gefenta yana rike hannyen ta,kasa Auta ta sakko ba shiri cikeda so irin na ɗa da mahaifiya yace.
"Afternoon first lady how was ur journey.?"
Alhmdullh son shine sai yau zan ganka.?"
"Sorry Mum aiki ya rikeni sunan ina zaune gida amman banda time kaina Mum thank god yau nagama mission din kuma munci nasara."
Masha Allah,Allah yasa albarka ya taimaka."
"Ameen."
Ina zuwa har haka naga kasha manyan kaya.?"
Hmm wlh kuwa Mum kema kya fada yanzun abinda Abba yace danaje gaida shi,bikin abokin mu zamuje daurin aure Zaria."
Sallamar Ya Tariq mukaji shima cikin thesame shadda ya shigo sai baza kamshi yake gaida Mum yayi ko zama baiba yace.
"Hussein it's time."
Fiddo ambulan yayi yace.
"Minal ga pictures dinku ki zabi wanda zaki tafi dasu gida,ki ajeman sauran."
"Tom Yaya mungode."
Jinjina kai yayi yace.
"Weldone hope kinji dadin Abuja."
"Eh akwai dadi,ko Fatash?"
Na ida maganar ina kallan Fatima duk suka kalleta eh tace cikin sauri nima sai yanzun na fahimci suna mamakin sunan dana bata,Ya Tariq ne ya maimaita Fatash saman labban sa sai kuma yace.
"Wow nice name."
Shikam Ya Taufiq harya kusan barin falon baki dayan shi.
Sai a lokacin Fatima ta dalla mani harara tana cewa.
"Da gaban Ya Samir kikace Fatash din nan sai yabi diddiki ya gano ma'anar sa,saukin wajen yan i dont care kika fada."
Murmushi nayi nace.
"Yo miye dan ya sani."
Sorry Minal mu canza chanza chapter wai wace tsaraba zaki kaima Husna aminiyar ki.?"
Murmushi nayi nace in mun koma daki zan gwada maki."
Shikenan Minal.
Da haka mukaita fira aikam haka na zauna na ware pictures masu yawa kuma sunyi masifar kyau,na aje mashi sauran ashe shi yasa Sojan nan yimana hoto kuma sainaji dadin hakan sosai a raina.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
Na
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


S1/E 15&16


"""""Yau takama gobe zan koma gida bakadan nayi murna ba badan nagajinda hutun ba aa saidai ina daukin zanje inga Mamana da kannena sai kuma sauran yan uwana,haka na dukufa parking harna gama.
Kiyi sauri Minal Ya Taufiq yana jiran mufa."
Tom nagama muje.
haka muka fito har parking space Ya Taufiq ne da kanshi a driver sit sanye yake da kananan kaya sai t-shart maroom ba kadan sukayi mashi kyauba abinka da farar fata,masha Allah.
Muna zuwa mu dukan mu harda auta muka zauna baya,gaida shi mukayi ta mirrowa yake kallan mu saidai bai amsa mana ba.
Mumkai minti biyar ta cikin mirrowa yace.
"Who was ur driver.?"
Yana fadan haka jikin auta na bari ta fito zata komo gaba ta cikin mirrow din ya kallemu yace.
"Minal dawo gaba."
Daram na tsinci kaina da faduwar gaba gani nike ban iya jimawa tareda Ya Taufiq bare har in zauna gaba hakanma duk na takura inaga na koma gaba,amman banda zabi haka na koma gaba na zauna,banjima da zama yaja mota muka fita,saidai Soldiers ke sarama motar mu har muka fita muka kama hanya cikeda nutsuwa yake driven ba hayaniya waigowa yai ya kalleni kamar baisan magana yace.
"Put ur sit belt Minal."
Sanya sit belt dina nayi bance komai ba,ba inda ya tsaya sai bakin wani katoon saloon waya ya kira saiga wata mata tafito tana zuwa naga ta sara mashi kamar wani Laptanar Genaral na kasa,shiko bai damuba sai jinayi suna magana da turanci yana cema ta.
"Zuwa 2 daidai zan dawo daukar su,ki masu mai kyau,kuma bansan jira."
"Angama ranka shidade.
Kudi naga ya bata sannan ta kallemu,fita mukayi dan munsan

Please Login or Register in order to submit comment