Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manufar sa.
Muna zuwa aka fara mana kunshi na jan lalle wasu na wanke mana gashin kanmu dayake duka kowa nada suma kasancewar ta sashen Mum su buzaye ne ta wajen Abban su kuma Rumawane,nikam ta Mamata ni fulani ce ta Katsina ma'ana sulubawa,haka muka zama abin kallo saidai duk da haka nafisu yawan gashi da tsawo haka gama gyara mana gashin mu da kunshi dayake saloon din akwai ma'aikata aikin su kenan harda masu gyaran jiki duk akwai dayake 9am ya kawomu sadda karfe ɗaya zatayi angama har mun wanke hanna din mu,haka muka tsaya jiran shi,cikin ikon Allah sanda 2 zatayi harya iso ba African time haka ta rakomu muka shiga mota muka tafi,direct Mall yakaimu yace kowa ya dau abinda yai mashi,samun waje yayi ya zauna yana kallan mu kowa na zabar son ranta.
Nidai wajen after dress nafi auki harna dauki wata riga sai kuma na ajeta wucewa nayi sau biyu ina daga rigar ina ajewa taimin kyau saidai kudin ta nike ganin sunyi yawa ganin bani zan biyaba kuma bansan inzake da yawa harnayi gaba na hakura naji yace.
"Minal choice it nice."
Kallan shi nayi dan banyi tsammanin hankalin shi na kanmu ba,jinjina mashi kai nayi ba dauko bakina har kunne ina murmushi,saidai abin mamaki harya dauke kallan shi akaina ya kama sabgar gaban shi.
wucewa nayi wajen turare na dauka,can naga wani turare wai DOLVE amman na mazane hakanan na dauke shi nasaka akayana,mikewa yai baki ɗayan mu,muka taho ya biya mana kayan mu,aka sama kowa a leda gaba yai abinshi haka muka iske shi a mota,muna shiga muka wuto gida a falo muka iske Mum ita daya tsaraba na bata aikam taji dadi,a sifar zolaya mukaji yace.
"Wato ya'yan nan naki sun fiye son kai,sun san banda time din daukar kayana da kaina ko su iya yiman shopping kansu kawai suka sani."
Baki daya kunya ta kamamu duk mukaji ba dadi take turaren nan ya fado mani akai bude ledata nayi na fiddo shi,murmushi nayi nace.
"Sorry Yaya ga turare na siya maka."
Kallona kawai yake shi bai ansaba kuma bai daina kallona ba nakai sakan shidda a haka sannan yasa hannu ya karba murmushi naga yayi yace.
"Wow Minal kin iya zaben turare mai kyau thank u."
Murmushi nayi nace.
"Never mind."
Gefen shi ya aje shi ya maida idan shi ga tv anayin film din Tarizanifam a Zee Aflam,Mum ce tace.
"Muga saloon din fara duba na autarta tayi tace
Gaskia yai kyau hakama na Fatash tanata yabawa ganin naki budewa tace.
"Mamana muga naki gyaran mana."
Matsawa nayi na kwance kallabina,Masha Allah tace tana shafawa,ta gefen ido ya kallemu still yana kallo,har kunshin mu ta yaba da haka mukayi sama da shopping dinmu.
Koda dare yayi anata fira saiga Ya Samir yazo hannun shi dauke da wata karamar leda zama yayi muka gaida shi,ya Taufiq ne ya gaida shi,fiddo kit din sarkar yayi yace.
"Amina ga tsaraba nayo maki yan matana."
Da murmushi na,na karba nace nagode Ya Samir.
Bakomai,zanyi kewar ki dayawa yan matana."
Nima zanyi kewar ka nace mashi,sai jin dadi nike dan sarkar fashion ce amman tayi kyau matuka,kallan Ya Taufiq nayi ina zumudi nace
"Ya kagani tayi kyau ko.?"
"Nice."
Yace rai hade.
Ban dauki wani abuba domin inda sabo da halin shi mun saba.
Komawa nayi na zauna,jin sakkowar Mum daga sama yasa natashi na tareta da sarkar ina murna nace.
"Kinga Ya Samir ya siya mani."
"tayi kyau aikam angode."
ta ida maganar tana zama.
"Wow yan matana daman haka kike da gashi gaskia u re beautiful."
Sai a lokacin nadawo tunani ashe gyalen kaina ya zame ban saniba zanyi magana kenan naji yace.
"U re very stupid Minal,daman kun saba zama ba kallabi akanku baki ganin dare yafara.!"
Ya ida maganar rai bace,nikam jikina yafara bari da kyal na dauki gyalena na rufe gashina.
"Sorry Ya Taufiq bansan ya fadi ba."
Shut up ke Fatima kutafi daki kema auta bisu muddin nasake ganin wata cikin ku ba kallabi sai ranta ya baci."
Ba shiri mukayi sama duk da bawani darene yaiba kwarai karfe 9 kwata kwata.
Da haka muka barsu falo,banjima da komawa dakin ba sadda 10 zatayi har bacci yai awon gaba dani.
Washe gari da safe nagama shiri na tsaf cikin doguwar rigar da Ya Taufiq yace in dauka itace na sake dayake coffe ce sai ratsin brown kadan fitoman da kayana akayi zuwa mota shiga nayi side din Mami aikam na isketa itada Ya Samir sai Zakiyya suna zaune har sungama break fast gaisawa mukayi nai mata sallama,cewa tayi injira ta daman shigowata take jira.
Dakin ta ta shiga,kallona Ya Samir yayi yace.
"Yan matana zanyi missing dinki fa,sai yaushe zaki kuma zuwa hutu.?"
"Idan nayi candy zanzo isha Allah."
Murmushi yayi yace.
"Kinga shikenan sai akaiman Yan matana gidan Ya Samir ko.?"
Murmushi kawai nayi dan yasani a duhu a raina cewa nayi su nan gidan Samir dinsu har nawa?
Maganar Mami ta katse mani tunanina wata jikace tabani tace.
"Ga wannan kikaima Umman ki.?"
"Nagode Mami sai wani lokaci."
"Allah yasa ya'ta."
Da haka nafita zuwa sashen Mum lokacin ta fito duk jikin su yai sanyi tana kewata tun jiya take magiyar akan cewa abarni har waya tayi da Baba amman yace karatu tayi hakuri cewa tayi indawo wajenta inyi karatun yace,aa tabari komai lokacine ba yanda ta iya dole tayi hakuri dan tasan halin kanin nata idan yace eh itace hakama idan yace Aa ba fashi duk da yana giramama umurnin ta amman wannan karan sam yaki amincewa.
Ya Tariq ne ya shigo mukayi ban kwana kudi yabani yace in kara inyi pocket money mukayi mashi,shiru Ya Taufiq ya shogo amman ba alamun shi,har 10am,Mum ce tace muje kada inyi dare,munzo fita Abba ya shigo gaishe shi mukayi a mutunce ya amsa wata anbulan ya bani yace inkaima Baba godiya nai mashi,inaga tunda Abba yadawo daga kasar waje gashi har yau zan koma gida inaga kwata kwata sau ukku na ganshi duk da ganin yau,fita mukayi a parking space har driver ya shiga mota ina zuwa nima shigan nayi ina dagama su Fatash hannu sosai nike missing dinsu har na rufe kofa naji yace.
"Minal sauko bada wannan motar za'akaiki ba."
Sunan daya kirani dashi nasan Ya Taufiq ne sakkowa nayi yasa aka maida mani kayana cikin motar dayace wanda driver dinta Sojane can na koma aiken driver din nasu yayi,ina shiga ciki na zauna ji nike kamar intafi da Fatash itako harta fara kuka,nima so nike in kukan.
"Kada kibiyeta kibata hawayen ki,ki gaida su Umma."
Jinjina mashi kai nayi ina waving dinsu da haka muka kama hanyar gida ina missing dinsu da garin baki ɗaya.
****bani na koma gidaba sai wajen karfe ukku na rana,har kofar gidan mu suka saukeni sannan suka daukar mani kayana zuwa cikin gida,nice gaba da sallama a bakina ina shiga kannena suka kadaddabe ni sai murna suke ta ganina,iso nai masu wajen Baba,yana fitowa suka gaida shi godiya yai masu sannan suka juya zuwa Kaduna.
Sosai Baba yai murna da ganina sosai zama mukayi a falo baki ɗayan mu.
"Mamana ya kikabaro yan uwan naki.?"
"Lafiya lau Baba Mum na gaisheku."
"Muna amasawa wannan irin kyau gaskia Anty ta shagwabaki sosai."
Murmushi nayi nace wlh kuwa da Mami Ya Samir ya Taufiq da Tariq sai kawata Fanash sun nuna mani gata sosai."
Cikeda jindadi Mama tace.
"Allah yasaka masu da alkhairi."
"Ameen."
Haka naita fiddo kaya iri iri naita nunama su Mama saijin dadi sukeyi,sannan na mikama Baba sakon da Abba yabani godiya sukayi haka naba kowa tsarabar shi.
Mama ina Asma'u tadawo kuwa.?"
Baku wayane.?"
Eh gaskia Anty Naina bata da waya shiyasa,sai akai akai mukayi waya bada yawaba."
"Nasan itama tana a hanya."
Cewar Baba.
"Anjima zanje in gaida Mama sai inbata tsarabar ta,ta ajiye mata."
Hakan yayi itama Allah ya maidota lafiya."
"Ameen ya rabbi."
tashi nayi na shiga dakin mu nai shirin wanka,ina fitowa nasaka atamfa riga da sicket,ba kadan sukai mani kyauba haka Baba yaita yabawa da kwalliyata ni kuwa saijin dadi nikeyi.
da yamma na shiga gidan su Husna ina sallama da gudun kannen ta sukayo kaina suka kadaddabeni suna cewa Oyoyo Anty barka da zuwa.
Rungume su nayi inajin dadi sosai dakin Mama muka shiga sai murna takeyi.
"Ya'ta ya hanya munyi kewarki sosai ya kika baro mutan gidan.?"
"Lfy lau suna gaidaku."
"Muna amsawa."
Anty ce ta shigo muka gaisa tana mani barka da zuwa.
Abba ne ya shigo yanata murna.
"Amaryata saukar yaushe.?"
Dariya nayi nace.
"Dazun banjima ba."
"Masha Allah kin shirya zama ga dakin kican na fente maki shi."
Dariya nayi nace.
"Sai marar hakori ita ta dace dakai."
Haka mukaita fira cikin jindadi sannan nabasu tsarabar su,data Husna.

Murna sukai tayi da haka natafi gida suna shiman albarka.
Washe gari haka naje gidan kakarmu munjima sosai,ranar haka muka wuni mun fira da ita,saijin dadi sukeyi ana isha'i muka dawo gida.

Haka rayuwa ta kasance gwanin dadi,saidai dawowa ta,ba Husna saina fara missing dinta fiye da sanda nike Kaduna saboda can Fanash na debe mani kewa,wasa wasa saida nayi kwana ukku sannan ta dawo da yamma.

Aiko ranar nayi murna sosai,danaga kawata sosai mukayi kewar junan mu,tana aje jikarta direct gidan mu ta shigo saida Mama tace.
"Asma'u kika biyema wannan labaran naku bazaki hutaba kije kihuta da kanta zatazo yi maki bangajiya."
Tom mama cewar Husna saida na rakata har zauren gidan su sannan nadawo gida sai jindadi nikeyi Baba ne yake tsokanata saidai nayi murmushi.
Lamura nata wanzuwa yanda yakamata farin ciki da aminci nata wanzuwa a cikin zuciya musamman idan naganni cikin yan uwana.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰

*Dedicated this page to Gorgeous Girls Comment dinku na dabanne,Minal na gaisheku🥰*


S1/E 17&18


******Bayan kwana biyu saura kwana ukku cif mu koma school inata parking kayana,nayi sabbin uniform morish blue color sai House wire dina Pink duk na kammala parking dina sai murna muke zamu koma SS1 mun zama Seniors.
Zuwa nayi wajen Mama nace mata zanje gidan su Husna,batai mani musuba tace saina dawo.
Hijab kawai na zira na shige gidan su,aikam na isketa tagama tuwon madara da yar gullisuwa ta zuba a makimancin farin botiki guda biyu,tana ganina taita sakin smile,daki muka shiga muka fara fira,labarin saurayin datayi Kano tafara bani Abdallah taci gaba dacewa.
"Kanin Ya Moh'd ne karkiso kiga yanda yake nuna mani so da kauna kullin sai yazo ganina,kai ashe haka soyayya take da dadi?gaskia masoya sunji dadin su kawata."
Dariya na saki nace wayaga JJC ba saban ba,amman yana da kyau ko.?"
Sosaima kuwa fari fes dashi kuma dan kasuwane yanada arziki.
ta ida maganar cikin zumudi da jindadi.
Aikam kice munyi miji."

Kwarai kuwa kinga wannan kayan da takalmi shine yabani."
Murnar da mukayi bata wasa bace.
Nikam dai banyi wani sauryi ba saidai yan uwana sunada kirki,sunaji dani amman kinga Ya Taufiq.
Nan fa na kwashe labarin Ya Taufiq nabata kaf,murmushi kawai take mani cewa tayi.
"Ke wlh Ya Taufiq sonki yake sosaima kuwa.!"
Murtuke fuska nayi nace.
"Dan Allah daina fadin haka rufaman asiri Allah ya tsareni inyi soyayya da Ya Taufiq ai kasheni kawai zaiyi."
"Ke bakiga yanda yake baki kulawaba jifa kiga yanda yai maki fada dan kawai Ya Samir ya yaba da gashin ki amman....


"Kinga Husna mukama wani labarin kaina bazai iya daukaba,ko Ya Samir din shima wasa yake mani yanada sakin fuska da yawa.
"Shikenan kawata naji amman kinsan abinda yafi burgeni sunan da yake kiran ki dashi,nima daga yau Minal zan dinga ce maki."
Murmushi nayi nace.
"Nice as u wish Husna, bari intafi gida zan ida parking."
Harara ta galla mani tace.
"Wato ke har murna kike zaki koma ki barni ko.?"
Girgiza mata kai nayi na mike nace Aaa amman ai kema kinsan dole hakan saita faru ba yanda muka iya."
Fitowa mukayi taimani rakiya na shige gida,naci gaba da shirin komawa makaranta.
********yau takama nike komawa makaranta tunda na tashi duk naji jikina ba dadi kasala ta dirar mani hakanan nike parking Babane ke jira dan har anfidda mani kayana,sai nawa nikeyi bansan komawa sannan kuma inason inyi ban kwana da Husna,taje dubo kakar su asibiti nayi da ita sai bayan azahur zan koma school shine tace taje harta dawo.
Shine Baba yace baiso inkai 12 gida dayake ranar monday ne ba yanda na iya na shirya muka tafi cikin kankanin lokaci muka iso principal dinmu muka gani bamu wani bata lokaci ba aka bani class A shine ajin da aka ajeni dayake mu,makarantar mu A science class ne.
Ranar da mukaje akaita kawo new commers mune tsofaffin dalibai shiyasa kowa yasan mu,ranar ba'ayi wani lesson ba sai ranar alhamis mai chemistry din mu malam Usman yazo ya koya mana meaning din Chemistry da branches dinsu sai state of matter haka ya koyar damu kuma kowa yagane sosai.
Har aka tashi daga class ba wanda ya kuma zuwa sai next week monday aka fara lesson gadan gadan ba kama hannun yaro.

Ranar labara mukaje Assembly ana gamawa,muka wuce class kafin teachers su shigo muka fara self introduction.
Kowa ya tashi ya gabatar da kanshi,in kana da nick name kafadi sai school din daka baro haka mukagama mai Agric (Animal Husbandary) shine ya shigo yafara mana lesson gaskia Malan Adamu Garba ya iya koyawa,yana fita mai Hausa Baba Sani Nasir ya shigo yai mana daga nan aka tashi muka wuce hostal.
Muna komawa aka taramu dayake lokacin yan 2007 ke mulki suma ba laifi sunyi zalinci saidai ba dukan suba zamanin Asma'u Mani itace SP dinsu,haka rayuwa ta kasance inyau da dadi gobe saidai zaman hakuri.


Kafin mu kwashe lokaci har hayakin SS1 din ya fitar mana akai dan wahala da muke sha duk da lokacin SS2 sunfimu shan wahala saidai muma muna shan iyakar tamu.

Rayuwa taja lamura da dama sun faru a ciki kuwa harda rubuta first term exam akayi mana hutu muka koma gida cikeda farin ciki saidai hutun baki dayan shi na sati biyu ne.

Har saida nayi kwana biyar ba Husna ba alamun ta,hakan yasa naje gidan su,ina ganin yanayinta nasan tana fushi dani tambayar ta nayi da kyal ta kulani tace.
"Haba Minal amana tace haka taya zaki koma makaranta daga inje asibiti indawo saidai na iske fili."


******Haba Husna banda zabi daya wuce intafi makaranta saboda Baba ya dage sainaje school shiyasa."
"Shikenan Ya school.?"
Uhmm yanzun akan wannan zakiki zuwa yiman barka da zuwa yaufa kwana na biyar."
"Sorry ai komai ya wuce nayi missing dinki."
Rungume juna mukayi ,sannan na cire abayar jikina muka shiga kitchen muka fara girki muna fira.
Har muka gama girkin shinkafa da miya mukaci muka gama sannan natafi gida ina zuwa banjima ba muka tafi gidan yayar Mamata Anty Hafsat,ta kasance macece mai kirki da hakuri ko a lokacin mijinta yanada wadata tinda haryafi mahaifina kuma tanada kyauta gata dasan yan uwa,ranar haka muka wuni a gidan har aiki muka tayata muda cousins din namu Umaima,Amira, Sudat,Hauwa'u sai kuma karamar Khadija sunan Mamata,baki daya mazan su biyu Lukman da Khalid haka mukayita fira dayake ta bangaren mamarsu yayyena ne tunda mun hadu a mata ziryan.

Da haka mukayi masu sallama bayan anyi magrib muka koma gida.
Wasa wasa hutunmu ya kare kuma yau nike komawa school daga hutun zamu koma SS2 koda na koma makaranta maida hankali nayi kan karatu musamman Science courses tinda inasan nakaranta Medicine.

zuwa lokacin duk wahalar makaranta tayi sauki sosai wani bima in za'ayi duka nakanyi dojing bamu zama tunda mun kara wayau sosai,saidai duk wani case na mate muna kan gaba hatta rayot in za'ayi saina shiga wasa wasa dai mun hada team criminal disturbance saidai muna cikin best students a sate dinmu shiyasa mukecin lallai haka rayuwa ta kasance.

Wasa wasa har mukayi hutu muka dawo gida rayuwa nike da yan gidan mu ba wani challanges dake hawa kaina lokacin bansan me ake cewa duniya ba haka nayi hutuna a gidan mu cikin jin dadi saidai godiyar Allah.


Bayan wani lokaci har mun koma SS2 bamu jima ba aka bada shadows ga SS3 yan 2008 kenan,gaskia iskanci ba dadi domin mun bugu kamar ganga ashe daman haka SS2 keji saidai duk iskncina a school ban yarda nayi dojing ba ina gudun kada aga nakaraya ace ashe iskancin mu na banza tunda muka gaza daukar azabar da ake gana mana.

Akwai wata rana da bazan taba mantawa da itaba ranar wata alhamis da marece.
Na dibo ruwa daga Monon Amina House ina cikin tafiya ta,bansan hawaba bansan sauka naji anyi jaking dina an wakeni da maruka har biyu dafe kuncina nayi inajin wani uban zugi da radadi,kallan wadda ta mareni nike cikeda al'ajabi ban gama mamaki ba,naji tafara surfa mani masifa da zagi kamar zata rufeni da wani dukan.

"Shegiya da kin dauka bazan gane kiba nabaki dibar ruwa kikaki dawowa daman inada labarin iskancin ki da taurin kai irin naki to yau zan shide maki shi."
Nana yar jega ke wannan masifar tana zagina,haka tayi jacking dina har gaban Daurama House wanda ake cema New Bulding tasakani rage tsawo cikin kankanin lokaci mate dinsu anzagaye ni duk mai ɗan karamin case ya hadaman shi a ranar saida suka taso shi,nikam ko gezau banba dan nasan dai yau saina bugu amman nariga da nasama raina bazan yarda a wuce bulala hamsin a jikina duk wadda tabiyo baya saina rama.


Aiko hakan ta kasance wadda naima laifin saida tamin bulala takai ashirin sannan yan tayi sukaita dukana nikam inata lissafawa bulalar data zama ta karshe ana laftaman an daga za'a karamin na mike tsaye tareda rike bulalai nace ya isa.

Ai wani uban ashar suka antayo mani suna.
Babbar bura'ubancan kutumar uwa ke harkin isa ki rike mani bulala kina ya isa.
Nidai bance komai ba kuma bansaki bulalar ba aikam tafara kokarin ansheta nikam na riketa gam naki yarda in saki ban ankaraba naji ta wasgamani mari,rike kunci nayi.
Kai kai ni kika mara.?"

An mareki dan uban....
Tas tas haka nima na aunata mata nawa marin tunkan ta ida zagin ubana datai niya hakan yasa sauran zancen ta ya tsaya cak,rigima ta kaure tsakanin mu,sai dambe mukeyi Mate dinsu kuwa suna zuwa suka farayi mani ruddubu suna buguna nima ramawa nafara duk da ance sarkin yawa yafi na karfi amman cikin kankanin lokaci nagama haukacewa nafara takan mai uwa da wabi aikam duk suka watse da gudun tsiya.

Wata ce ta tunkaroni da wani uban icce nikam tana zuwa na janyo botikin ruwa na sharara mata shi ajiki,ajiyar zuciya ta sauke gashi lokacin ana sanyi ranar dai na bugu ba laifi nima nayi rashin kunyar dan suna buguna ina ramawa har saida wata Prefect tazo ta ansheni wajen su,da kyal suka hakura ina komawa daki bisa gado na kwanta sai a lokacin nafara kuka mai taba zuciya ba bugun da sukai mani bane ya sakani kuka ba,
Yanda kowa yazo sai yace bani da kunya banda mutunci ga uban zagi nasha harna godema Allah da ace zagi na fitoma mutun tabbas ranar saiyayi ajalina.

Haka rayuwa ta kasance a GG ba ragi ba ragowa ana haka har sukayi sauki domin sun kusa fara WAEC,baifi kwana biyu ba,ranar monday kuwa suka fara da Math haka suka gama WAEC da satittika suka cigaba da NECO sai lokacin yan makaranta muka fara Terminal Exam saidai kanmu yanata fidda hayaki domin mu tinkan abamu Shadows muka fara wulakancin mu son ranmu da haka har mukayi hutun wata ɗaya.

Koda mukayi hutu ina gida ba inda na kuma zuwa tunda naje hutu Kaduna hankalina kwance sai kibata nikeyi.

Akwai wata rana da safe ina zaune a falo saiga wata yar uwar Mama,tazo gaidata mukayi,bada jimawa ba Mama tafito falo suka zauna suka gaisa nan fa suka fara fira suna cikin magana cousin dinta tace.
"Ke kam bakisan mike faruwa ba a garin nan.?"
Aaa bansani ba,cewar Mama.

"Toh inma bacci kike ki farka domin ana nan ansakama Yarki ido wai yarinya ta girma samari suna zuwa suna cewa suna sonta amman ku kunki kun dauki burin duniya kun aza akanta,gwara tunda wuri kusan halin da kuke ciki.!"
Nauyayen ajiyar zuciya Mama tayi tana mamakin lamarin.

Haba Rukayya ina wani girma yake ga Amina dahar za'ace mun aje yarinya samari na zuwa munki aurar da ita,kwata kwata yanzun zata shiga shekara sha bakwai a duniya kuma in banda abinki inba Mustapha fa ba,muba wani saurayin dayazo mukace bamu bada yarmu,kuma shidinma lokacin tana JS3 fa."

"To aidaini gaskia nagaya maki don karkuzo yarinya tayi Candy kuzo kusata agaba dan aure dai shine gatan ta."
"Hmmm Alalh yaimata zabin abinda yafi alkhairi a rayuwarta shine addu'ar."
"Bawani shine addu'a akwai abinda yafi alkhairi daya wuce aure."
"Eh hakane amman kada ki manta komai fa rubutaccen al'amarine kuma tinkan tazo duniya Allah yarigada ya rubuta kaddarar ta,kuma ance bakin alqalami yarigada ya bushe komai bi muke yanda Allah ya kaddara mana."

"Hajia kinga tafiyata dan na fahimci kamar zargin da yan gari keyi gaskia ne,dan haka Allah ya kyauta gaba."
"Ameen."
Da haka ta tafi, ranta a bace dan ba haka tasoba taso Mama taita kananun maganganu sai Allah yasa batayi ba.

Bayan sati biyu ina gama gyaran gidan mu,na shirya cousin dita Hajara tazo gidan mu,tace muje mugaida Anty Hafsat.
Haka muka tafi har gidan Anty Hafsat,ba kadan taji dadin ganin muba,muka fara fira da sauran cousins dina muna cikin fira sai Umaima tace.

"Ke Hajara abinda baki saniba samari keta sintiri kofar gidan mu,aini wlh akwai farin jini,sai wanda na darje zan aura,dan haka karkiso kiga yanda nike wuta."
Ta ida maganar tana mani wani kallan ƙasa ƙasa nikam yinayi kamar bangani ba,duk da Hajara takeba labarin.

"Kinji dadin Umaima ni kingani nan saurayina ɗaya Mu'azu kamar chewgam haka ya nanike mani."
"Aike kinji dadi wasu ko masinsini basu dashi ai kwara ke,wasu kam antsaya ruwan ido a gari ga kanne nan sun fara bada himma!"
Ta ida maganar da sifar wulakanci duk da nasan dani take amman ni ka'idana bani sa'insa da kanne indai nasan nafi karfin mutun zaitai mani abu ban tagawa,sai abu yakai karshe.

Bugota Hajara keyi alamun tayi shiru,a tsawace tace.
"Ke rabu dani ai gaskia ce ba ruwan idon aka tsayaba ai mutun yana nan zaune zaiga mun shige daga ciki mun barshi.

Wani irin matsiyacin kallo na aika mata mai razanarwa har saida ta kama kanta,dan fuskar ta ta bayyana hakan mikewa nayi nace.
"Inkin gama ki iskeni waje."
Fita nayi raina na kuna amman na dake a tsakar gida na iske Anty na,yayar mamace uwa daya uba daya,Umaima kuwa babar yartace mace.

Ganin Hajara bata fito na kama gabana naima Anty sallama na tafi saida nai nisa Hajara ta iskeni da gudu rikoni tayi ina juyowa naga itace tafiya mukayi a tare.
"Kiyi hakuri akan abinda Umaima ke cewa."
Karki damu Hajara mubar wannan maganar.
A haka muka tafi gidan mu,muka wuce har yamma sannan ta tafi gida.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Comment
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*


*Alhmdullh,Allah yasa mun kammala BANSAN INDA SUKEBA ahalin yanzun,insha Allah zaku dinga samun posting ALQALAMI kullin banda Week Ends,ina mika godiya ga dukkan fans dina musamman Bansan inda sukeba Paid grps Allah yabar kauna🥰*


S1/E19&20


*******KADUNA*******


"Mami dagaske nike maki Amina nikeso kuma ita nikeda burin kasancewa da ita a matsayin matata."
Cewar Samir.
Kallan mamaki Hajia Mufida taci gaba dayima ɗan nata duk da bataso ya zabi Amina ba amatsayin matar da zaiyi rayuwar aure da itaba saboda zaman doya da manjan da sukeyi da kishiyar ta,duk da suna kishin su cikin Class amman kuma mai zafi sukeyi domin kowace na gasama yar uwarta gyaɗa a hannu a gaban mijin su ko gaban bako basu yarda su nuna halayen su a fili,itadai Mami macece mai izzar tsiya ga dara da bala'in son mulki,ita kuma Mum bata daukar raini ko miskali zarratin sannan kuma tanasan a giramamata ma'ana mutunta ta,shiyasa basu jituwa da Mami,wannan dalilin yasa bataji dadin zabin Samir dinba domin kuwa taso ya auri ɗiyar kanin ta,amman sam yace batai mashi ba,itako a halin yanzun ba abinda takeson ta gani a duniya sai auren Samir da ya'yan shi,dan ko auren Fiddausi bai dame taba akan na Samir.

Shikam kallan mahaifiyar tashi yayi wadda tai nisa a tunani batasan yanata yi mata magana ba,har saida ya riko mata hannu sannan ta dawo firgigi tana aje sanyayyar ajiyar zuciya.
"Haba Mami mi yasakaki wannan dogon tunanin bayan baki da burin daya wuce kiga na fidda matar aure kuma gashi Allah ya karbi addu'ar ki,wlh Mami tsakanina dake ba boyeboye ko jin kunya bantaba ganin yarinyar datai mani ba kamar Amina ina sonta ina kaunarta,dan Allah ki sanarwa Abba wannan zancen."
Ya ida maganar kamar wani maraya.
Wani irin tausayin shi ne ya dirar mata a zuciya saidai bata da zabin da ya wuce tabi ra'ayin danta indai tanason taga jinin shi a duniya tunda har ansamu

Please Login or Register in order to submit comment