Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki sunane wani kuma harda sunan Fatima a jiki,haka na ware kusan kala hamsin na aje zan kaima Mama,haka aka raba kaya har saida nayi saura.
Saida kafa ta daga sannan na bude later din nafara karantawa.





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*


_Dedicated this page to Ummu Mu'azzam&Aisha Mohd Musa inagodiya da kaunar ku agareni_



S1/E 35&36



_Assalamu alaiki_
_Fatan kina cikin aminci barka wannan lokaci ya karatu ina fatan kina maida hankali sosai akan karatunki domin cikar burinki nai maki alqawali sai kin kai_ _matakin da kikeso kikai a harkar ilimi Minal,ina maki murna kin kusa gama school Allah yasa kigama da saka_ _mako mai kyau ameen_
_from Major Taufiq Sarki Mukhtar._

A hankali na sauke boyayyar ajiyar zuciya saidai inaji araina ya rubuto mani itane dan cikar wani buri nashi na daban musamman dayaga ansa mani rana dashi.



Samun kaina nayi da murmusawa duk da ba wata wasikar soyayya bace yai mani adanata nayi cikin kayana masu mahaimmamci.

Bayan sati biyu muka fara zana jarabawar WAEC sosai tazo mana da sauki haka muka rubuta ta cikin aminci kowa najin dadi a cikin zuciyar shi.

Rayuwa a cikin GG gwanin dadi sai wake wake mate keyi Departing inda muke zuwa hall ko bakin dakin Momi indo ahau kidekide kowa yana baiti mai sosa zuciyar yan makaranta.
Haka rayuwa ta kasance mate basu da aiki sai wake waken bege na rabuwa wasu sukama kuka dan abin na taba rai,haka za'a hadu da daughters ana cashewa wani bima har Ovalti (immidiate) kenan mu haka muke cewa.


Bayan kwana biyu muna gab da gamawa tinda Neco ta matso sosai munata murna saidai wani sashe na zukatan mu yana kewar yan uwan mu dan munsan dayawan mu bazamu kara haduwa ba har abada,haka mukaita shirye shiryen zana NECO.



****** Mama ce zaune tagama aikinta zuwa yanzun tadan kwantar da hankalin ta tunda taga Baba ya sauko,saboda ta kwashe kayan dayace baison gani sunbar gidan baki ɗaya.

Sallamar da akayi ne yasata kallan mai shigowa tareda amsawa Anty Hafsat da aminiyar ta Anty Badariya cousin din su Mama ce,zama sukayi aka fara maida yanda akayi.

"Kinga ko Khadija da kaina nace maki karki yarda Amina ta auri yaran nan amman saboda kwadayi kika ƙi yarda gashi tun ba'aje ko inaba anfasa kinga yanzun sai asaka maki ya' sahon yan sa rana ana warwarewa Allah yasama kada a hadaku da wani mugun sharrin ai kwadayi baiba wlh."


Haba Anty inkina mani wani abun sai inga kamar ba mahaifa ɗaya muka fitoba kema mai bada shaidane akaina kinsan ni ba makwadaiciya bace uwa uba mahaifin ta ke kinsan halin shi

Kinga Khadija kidaina kare kanku,domin kuwa wasu kudin in sukayi yawa mutun bai sanin ya dulmiya a ciki.

Gaskia ne kawata karkiso kiji gari ya dauka ansaka rana dan anga kudi yanzun anfasa wai radi radi naji ance kayan ma kin badawa kukayi kun boye nace wannan wace irin masiface da kwadayin abin duniya azo har gida ace ba'ason yarka kuma ka rike kaya gaskia kwadayi baiba sam."
Cewar Anty Badariya

Kallan mamaki Mama ke masu tarasa mi zatace masu.
"Ai kadan kikaji ni jinayi ance wai sunce auren sai anyi kota halin ƙaƙa wasu ko cewa sukayi wai anji labari Amina bata da kamun kai shiyasa suka fasa."

"A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim Allah yatsari ya'ta da rashin kamun kai wlh sannan kaya tabbas basu ansaba saboda da Taufiq da Amina abu ɗaya yayisu asalin su ɗaya babu yar ramuwa tsakanin mu,kuma jibi jibin nan zanje Kaduna bikin Tariq da yar Mufida zumunci sai abinda ya turema buzu naɗi.!"
Ta ida maganar a zafafe


Wani irin shock ya kama anty tace.
Kaji wata sabuwa wato Khadija saboda rashin zuciya aƙi yar taki kuma ki kwasa kitafi biki tabdijam!ya tabbata zargin da ake maku kenan kwadayi ne kawai ke dawainiya dake kanwata."

Haba Anty miyasa kike magana irin haka insa da Yusuf da Maryam uwar su ɗaya uban su ɗaya,yanzn ke sai ace zaki aurar da ɗanki dan kawai irin haka ta hadamu sai ace bazanje ba,ki duba wannan lamarin kada son zuciya da kama kananun maganganun na magulmata yai tasiri akanki kuma sharrin daza'a daurama Amina wlh masuyi suci gaba shidai alhaki ɗan kuikuiyo ne kuma maishi yakebi mudai musan kaddararta kenan ba zata wuceta ba muna mata fatan alkhairi akoda yaushe.!"

Aidaman muma da alkhairi muke binta nidai matsayina na yar uwarki dole innaji zaki cuta in hankaltar dake Allah ya kyauta amman kusan abinda kukeyi shine bayani tashi muje kawata."

Mikewa Anty Badariya tayi sai kuma tace.


Kinga ina kayan sa ranar suke naga akwai butoci da kafat kafat bani buta biyu da darduma ɗaya ko sallah mun tada mu samu tabaraki daman inada karanci buta."

Kallan mamaki tai ma Yayar ta.

Aikam Anty kayan sunbar gidan nan an kaisu ajiya gudun haka, kada ace munajira har munfara anfani dasu,kinsan baka iyama yan adam amman bari inbaki buta inada ita."
Shiga tayi daki ta bata buta biyu sai kawarta guda ɗaya badan Anty tasoba ta fisga suka tafi rai bace.



*****Mami Pov


Dan haka Samir kamar yanda mahaifin ka yai maka maganar nan inaso kaba marada kunya ka wanke mani hawayen idanuna ka auri Samira na tabbata zakaji dadin rayuwa da ita kuma zata kula da duk wata ɗawainiyar ka kasan tana sonka."

Ajiyar zuciya ya shide yace
Mami gaskia duk duniya ba wadda nikeso kamar Amina amman ga abinda kanina yaimani inaso shima yana so gashi yanzun kowa ya rasa dan haka dole in bawa kaina hakurin rashin ta kibani nan da sati insha Allah in nasamu sassaucin zuciya ta zan auri Samira ba abinda ban tana daba,na rayuwa duk dan cikar burina, lokaci kawai nike jira ashe itadin ba matata bace."

Ya ida maganr a raunane.

Kayi hakuri Barrister Samir kada kadamu Allah yakaimu satin lfy insha Allah dakaina zanje inkara magana da ɗan uwan nawa."

Aaa Mami kada kije kamar yanda na bukata kibari satin ya cika sannan kidaina damuwa kici gaba da hidimar bikin Fiddausi shine masalaha."

"Nagode maka Samir ka wanke mani raina Allah yaimaka albarka."
"Ameen Mami."

Da haka sukaci gaba da shawarwarin su


Bayan kwana biyu yau asabar babban masalacin kofar gidan Major tamkam yake da bil'adama inda aka shaida auren Fiddausi Sarki Mukhtar Munzali da angon ta Bashir Shehu Yakasai anci ansha alhmdullh.

Haka cikin gida matane tamkan kowa ne side na Mami da Mum kowace tasha ado iya ado suna aurar da ya'yan su.


Taufiq ne ya fito sanye da Royal blue din shadda sai kyalli yake ya hadu iya haduwa saidai fuskar shi ba yabo ba fallasa dangin mahaifiyar su sai tsokanar shi suke suna gauro saidai yai murmushin yake, amman ta ciki na ciki,tako yake a nutse, ya gaida dangi mahaifiyar shi kamar baison maganar har zai wuce yaga Maman Amina zaune da kanwar Abban su,hakan yasa ta duka ya gaidasu cikin girmamawa.

Amsawa Mama tayi saidai ranta cike yake da tausayin Taufiq din domin harya saki kana ganin kasan yana cikin damuwa.


mikewa yayi ya kalli Zainab.
Yafara tsokanar ta
"Ke ba kauya baki iya gaisuwa ba."
Murmushi tayi tace Ya Taufiq ina wuni."
Lfy lau ya biki akwai dadi.?"
Eh."cewar tace mashi tana kara makale ma Mama kamar danko.

Shiko yai cikin bedroom din Mum can ya iske Tariq yana gaishe da mahaifiyar tasu sai addu'a take kwarara mashi yana tsugunne gabanta,shima tsugunnawar Yayi sunsha anko komai iri daya,haka ta gama shi masu albarka,aranta ko tanaji inama baki dayan sune zata aurar.


Kanwarta Murja tace suje lokaci keja.
Haka suka fito hannuwan su sarke dana juna duk inda zasu gifta sai ankalle su ana sam barka wasu kuma na gwasalewa a hanyar barin harabar gidan Samir ya fito cikin Brown shadda wani kallan tsana ya watsama Taufiq ya watsar ya shige mota,suma mota suka shiga Alaconda aka take masu baya da zugar abokai sai Malali.
Karfe biyu da rabi dai dai aka shaida auren Tariq da amaryar sa Aisha Manga duk yanda Taufiq bai murmushi ranar sai smile yake yana taya dan uwan shi murna rungume junan su sukayi sun dade ahaka wasu kwalla masu dumi sukayi nasarar ziraroma Taufiq har saida Tariq yaji saukar su abayan shi shima wani irin abu yaji take idanun shi suka kada sukayi jajir da haka akaci akasha kowa yana addu'ar zaman lafiya.

*Noted: wajen ɗaurin auren Tariq is Fiction daga barin su wajen Mum har aka ɗaura auren duk Fiction ne gaskia,saidai tace sun shiga cikin damuwa aranar marar misaltuwa,wannan nina tsara ahaka dan kuji dadin karatu much kauna💞*

Bayan angama daurin aure suka dawo gida saidai kana ganin su kasan suna cikin fargaba da tsoron rabuwa da junan su,da haka sukayi side din Abban su shima dawowar shi kenan.

A katan garden din gidan matane zaune cikin Kanopy anatacin abinci iri iri saidai da dangin Mami dana Mum kowa da runfar su saidai kallan hadarin kaji da akema juna da yan habaice habaice.


Mama da Anty Hafsat wadda ta nace saita rako Mama bikin,wai dan tai mata kara,suna zauna a waje ɗaya kowa nacin abinda yai mashi sai su Anty Murja da sauran dangin Mum,sunata yaba hadin kan su Taufiq da Tariq kowa nasa albarka.


A inda runfar dangin Mami ke zaune kuwa kannen ta da masifaffiyar kanwar ta wai Anty Wasila sai harare harare take da sun hada ido da Mama saita watsa mata kallan tsana tin Mama na daurewa harta fara shan jinin jikinta saboda ba yaban kaiba Mama batada fitina kuma batasan tashin hankali,bata gama sakar zucinyar take ba taji an dafa mata kafada daga kai tayi tana kallan wadda ta dafata.

Ga mamaki Anty Wasila ce,take mata kallan kaskanci


Wato kece uwar Amina ko? Tambayar ki nike sai akace maki da kikai kutun kutun kika hana ɗanmu Samir auren gwida yaran ɗiyar ki sai akace mutuwa zaiyi?in banda kaddara ke kinsan Samir dake da aji,kudi ga kyau yafi karfin yar talakawan yarki matsiya ta,kalla da kyau ki gani kinga yarinya nan san kowa kin wanda ya rasa itace tsarar Samir kuma insha Alalh bada jimawaba zakiji ya angon ce saidai ki mutu munafuka daga ke har waccen gantalalliyar Maryam din wai ita mai karfin iko ai sai muga iyakar ikon naku,ku aurama Taufiq in kun isa yan iska talakawa.!"
Cewar Wasila dakeji kamar ta shaƙe Mama.

Itakam takasa ko magana saima kanta dake sarawa,maimaikon Anty Hafsat yar rakiya ta shigarma yar uwarta ko kuma ta bada hakuri saima cin namanta da lemu kawai takeyi.
Anty Murja autar su Baba tace.
"Haba Wasila miye haka zakici zarafin ta yanda kikazo hidimar auren yar yayarki itama haka tazo auren ɗanta, baki fita da komai ba dan haka baki isa ki daga mata hankaliba wlh,kuma Maryam ta isa da uban Amina shiyasa ta hanashi yaba Samir yar mu,koda kike kirarin an hana Taufiq ai ince daga uban shine baccin haka ke kinsan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane ko mai idon wlh saiya shirya,ki shiga hankalin ki tunkan ki kwashi kashin ki a hannun ki.!"

Ta ida maganar tana ingiza Wasila dayake kaf dakin su Baba Anty Murja tafi rikici ana shakkar ta, sosai.


aikuwa sai balli ya bude aka fara bata kashi,duk abin nan daga Mum har Mami suna side dinsu da tasasar jama'ar su.

Sajida babar yar Major Sarki wanda Samir da Samira suke binta kardai ku manta S² (twins ne) suka iso wajen tare da Zakiyya autar Mami suka iske wannan kici milli kowa cikin su naso ya wulakanta ɗan uwan shi Anty Murja ta buga Wasila da ƙasa ta haye taita ɗuma kafin kace haka dangi anshigo kowa nashi yake karewa ganin kanwar mahaifiyar su ƙasa yasa Sajida da Samira shiga fadan gidan duk yagama hargitsewa,Fatima da ta taho gun Mama itada Sholi da gudu sukayi side din Abban su suka fada yana zaune da manyan mutane a ƙawataccen falon shi sai su Taufiq yanata yima Tariq da Fiddausi nasihohi akan aure.


Yanda suka ganta saida kowa ya maida attension din shi kanta.

Abba ana rigima dasu Anty Wasila.!"
da Major bai niyar tashi ba ganin zasu iya kunya tashi wajen bakin shi hakan yasa ya fita Tariq da Taufiq na maye mashi baya suna isa suka iske har yanzun Murje ke murzar Wasila ankasa banbare ta harda jimata ciwo a fuska rai bace Major ya daka masu tsawa duk mata suka kama kansu banda Murja dakeji zata iya kashe Wasila domin ta kule bata iya rigima ba ko kadan.

wani soja na rike da doguwar bindinga irin ta baushen nan wadda suke anfani dan razanawa Taufiq ya fisget ya dagata sama ya ɗana Daram haka ta bada sauti aiko mata aikaita gudu hatta Anty Murja batasan ta shida kan ruwan cikin Wasila ba tayi cikin side din Mum itako Wasila takasa ko motsi haka su Samira suka kamata suka tafi da ita side din Mami da ita sai jini ke ɗiga a fuskar ta.
A kidime Samir ya iso yakamata yana tambayar ko lfy haka suka shige ciki.

Shiko Sarki ko martani bai nema ba ya kirawo kanwar shi Anty Habiba yace ta same shi side dinshi bayan magrib da haka suka koma.

Taufiq side dinshi ya wuce yarasa dalilin rigimar dan har kanshi yafara ciwo kwantawa yayi kafin su dauko amaryar Tariq da yamma.

Labari ya samu Mami ganin kanwarta a wulakance yasa ta ziri gyalen ta tayi side Mum duk yanda Samir yaso ya hana mahaifiyar tashi tafiya takiya su Sajida suka maye mata baya,tana zuwa personal falon Mum ta nufa dan duk da ake biki ba kowa ke shiga cikiba ko lokacin daga Anty Murja sai Mama sai Anty Hafsat da Anty Luba itama kanwar Major ce dayake sunada yawa dangin Baban su Taufiq.
tana isa basu san hawa ba basu san sauka ba sukaji ta.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

*Garabasa! Garabasa!! Garabasa!!!💃💃💃💃💃💃*

*Ga dama tasamu yar uwata karki bari wannan garabasar ta wuce na karanta littafin Daukar Fansar Budurcina,yar uwata idan kinsan baki soma karanta littafin fansar budurcina ba maza garzayo domin kada ayi babuke kawata,labari daya kunshi abubuwa iri iri na rayuwa,musamman matsalolin mata yanda rape ya zama ruwan dare,kwantata da kanki* *ace kece yarinyar nan yar shekara goma a duniya wani gardi yai maki fyaɗe dan kawai kudin baku da galihu kuna aikin aikatau agidan su keda mahaifiyar ki,dan mahaifiyar ki takai koken ta wajen mahaifiyar shi,tasa ɗan nata yakara yi maki fyaɗe a idon mahaifiyar ki da tasa😭,turkashi wace irin cakwakiya ce ke cikin wannan labari,wace kalar Daukar Fansace Aisha zatayi akan Ahmad duk*
*wannan kulalliyar tana cikin wannan daddaɗan labarin mai taken DAUKAR FANSAR BUDURCINA na Jameey Yar Mutan Kankia, mai dauke da dinbin* *darasi,ilimantarwa,fadakarwa,nishadantarwa,harma da wa'azantar wa, garzayo domin kar'ayi babu ke,zakisame shi*
*cikin sauki da rahusa.*
*Mai bukatar karanta* *wannan book ya tuntubi wannan number👇*
*08160508316 domin karin bayani*
*Yar uwa idan kinsan ba saye zakiba karkima wannan number magana nagode*

_Hausawa nacewa sayen nagari maida kudi gida🥰_


S1/E 37&38



Shakar wuyan Mum tayi takai mata wani mugun bugu a fusace, ta rike mata wuya itako Mum kokarin kwace kanta take dayake wani ɗanyen Less tasa pitch sai digon coffee sai Mami dake sanyi light blue shadda tasha stone work, Anty Murja na ganin za'a kashe mata yar uwa ta cakumo Mami ta shake takama kaima ta naushi,su Sajida suma suka dinga aikama Anty Murja naushi da kyal su Mama suka shiga rikicin rabasu lamarin yafi karfin su sunki rabuwa jikin Mama na bari ta janyo waya ta kira Ya Taufiq har zai shiga toilet domin shiryawa zasuje daukar amaryar Tariq yaji kira azahiri cewa yayi.

Ohni Hassan ba zama anyi aure baka minti biyu kakirani sai kace za'a gudu da Eshar kekam kinga takanki da Tariq.

Sake kiran shi tayi ganin Mama yasa da sauri ya daga ko magana baiba Mama tace.
"Taufiq kazo dakin Anty suna fada kai sauri."
Ai jallabiya ya zira sai wandan shadda dake jikin shi yai side din Mum zuciyar na harbawa.

Duk wanda ya ganshi sai kallo ake binshi dashi.
anajin hayaniya amman ba damar zuwa ganin kwakwaf domin kowace cikin su tanada soja mace mai kula da private side dinta shiyasa inba doleba baka wucewa main side din Mum.

Yana isa ya banka kofar maki mancin falon da karfin tsiya har saida suka razana,zuwa lokacin an gama hargitse falon ganin iyayen shi na dambe baisan ya tsaya ba,tin daga bakin kofa yake watsama Sajida matsiyacin kallo dake dukan kanwar Mum,duk da ta girmi Taufiq akalla tabashi shekara hudu a duniya amman saida ta kama kanta haka Samira duk suka tsaya cak suna raba ido,sai alokacin ya akaraso Mami ta kara daga hannu zata daki Mum ya daka uwar tsawa mai razanar wa.

"Enough Mami,ya isa Mum miye haka.!?"
Cak ta tsayar da hannun ta tayi kan Taufiq tasha kwalar shi tana cewa.
"Kaidin banza zakai mani tsawa wayen kai Hussein.?"

Kiyi hakuri Mami kuna hidima zaku tarama kanku yan kallo makiya suyi maku dariya haba gaku da surukai kiyi hakuri mana.!"
Sakin shi tayi tana
"Dole ka zageni Taufiq tunda ba mahaifata ka kwanta ba dole amman aini matar ubanka ce ko.?"

"Eh ba mahaifarki ya kwanta ba ja'ira ni zaku zubdama kima ku wulakanta mani wannan ranar farin ciki a gareni ranar bikin ya'yana gaban bakin kunya yau zanyi maganin tsagerancin ku,na fahimci jin dadi yai maku yawa,na baku nan da minti biyar kowace ta nemi gidan ubanta in kuka bari lokaci ya kure maku sainasa bindiga na halbe ku kowama ya huta."
Major Sarki kenan wanda ya gama maganar yana juyawa ko ajikin shi aifa sai yan koke suka fara tashi da sauri Taufiq da Samir da shigowar shi kenan suka bi bayan mahaifin nasu suna begging dinshi ko sauraran su baiba yai side dinshi yacema sojan dake tsare shi, koda Taufiq ne baice ya shigar mashi side ba.

dole Mami tabaro side din Mum riga a cukurkude itadasu Sajid sai kuka suke kallan su kawai akeyi ana kus-kus.
Basujima ba baki dayan suka fito Mum hand bag kawai ta dauko su Aisha na binta suna kuka,itako Mami hadda jawo troly kowa na kallan iyayen amaryar Fiddausi da ango Tariq sunata kuka.

Bada jimawaba za'a kawoma Mum sirikarta akai Fiddausi gidan iyayen mijinta ammn biki ya buge da rigima.

Ku tsaya sukaji ance baki daya suka tsaya harda su Mama dake tareda Mum.
Wata dattijuwa ce kana ganin ta kasan asalin barumiya ce kuma tana kama da Major Sarki,babbar yayar suce suna cemata Baba Asabe,Taufiq ne ya mike daga dukiyar da yayi agabanta da alamu shike sanar mata da komai dan bata jima da zuwa ba danma ta matsa sai tazo da Sarki ya hanata acewar shi ta huta tunda ta tsufa.

Tana zuwa bakin side dinshi sojan yafara gardama tace zatasa ya rasa aikin shi don dole yabata hanya ta wuce can cikin falon shi ta iske shi ya kure AC yaje yadawo yaketayi yarasa mike mashi dadi a duniya yana ganin ta yasha jinin jikin shi da kallo tabishi tace jeka maido su yanzun nan."

To hajia kiyi hakuri."
Gaba yayi tana bayan shi har ya isa katan harabar gidan kowa tasha kukan ta harta gode lillahi,kowa ta koma side dinta."
Shine abinda ya furta yakasa komawa side din shi dan baisan mi yayar tashi zatace ba.
"Allah yaimaka albarka *Rumah* ka kara hakuri da iyalinka kaji."
"Ameen Ba'ba insha Allah."
Jinjina kai tayi tace.
"Jeka abinka."
Godiya yai mata ya koma side din nashi.

Haka akaita biki sakwa sakwa ba wani kwari angama bata komai,ba'a jimaba su Baba Hamza suka dauki Fiddausi zuwa gidan mijint.

ba'a jimawa ba Taufiq ya fito da milk din boyel yahau mota zuwa malali.

Haka kuwa aka kawo Aisha side din Mum waje na musamman,washe gari akayi walima saiya kasance duk kusan dangin Mum ne domin dangin Mami suna gidan Fiddausi,haka akayi aka gama akayi shagali sannan da yamma akai mata rakiya gidan Ya Tariq wanda fadin haduwar shi bata bakine.

```Wannan kuma sai in Anty Hafsat na baka labarin tsarin gidan zakasan ya hadu iya haduwa dan sun kashe kwarkwatar idanun su wannan kenan```

Washe gari yan biki suka fara sallama zasu koma gida kattin laziriyos guda biyu Major ya kawo ɗaya dangin Mum,ɗaya kuma na dangin Mami yace amaida kowa har kofar gida dayake Mami yar asalin kofar Gugace cikin kwaryar binin Katsinan Dikko.
Haka aka cika kowa da tarkacen kayan biki har ya Taufiq yaja Zainab yabata wata leda duk yanda Anty Hafsat taso sanin abinda yabata taki yarda koda Mama tagani dan dole ta hakura har suka dawo gida itama har kofar gidan ta akakaita sannan aka aje su Mama haka aka maida kowa gida lfy wannan kenan.

******Amina Pov

Ranar litinin muka fara NECO da lissafi muka fara kuma alhmdillh antai makemu tun a hall Dady shekare yace inje gate idan na gama aiko ina gamawa naje gate na iske Zainab muka gaisa tace inji Ya Taufiq yace hannun ta hannuna shiyasa ta tsaya saida nazo,nidai na amsa ba yabo ba fallasa.
Na tambaye ta su Mama da Baba da Husna tace suna gaidani Husna tana jarabawa.
Murmushi nayi nace ai mun kusa gamawa da haka mai gadi yace lokaci ya cika ni kaina nayi mamaki da jinin su ya hadu da mai gadi domin kuwa munjima muna fira daga haka nayi hostel.
Ina zuwa wanka nayi na huta na janyo ledar lokacin Hafsat tana hada mana abinci a lokata ina budewa naga kayan bikine ciki barkatai harda su lemu da kwali bag su chewgam cake alkaki dibilan kai abubuwa dai murmushi kawai nayi nace.
"Uhmm Ya Taufiq ya iya yaudara shi dole in so shi wai dan in saki jiki dashi." kuma ba laifi nafara dan sakewa da kyautatawar da yake mani inajin dadi.
Haka na dibarwa Hafsat nata na bata,mukaci da kawaye na sannan muka tafi Hausa Club aikin kenan wakar departing.
Haka rayuwa taita tafiya gwanin dadi Exam ta mika sosai komai sai hamdala.

Baba Pov"""""

"Danasan haka zata faru bikin wlh da bakije ba dani kadai din naje daurin auren wannan wane wulakanci ne ana harkar arziki kun buge rikici.!"

"Wlh Baban Zainab ko uffan bance ba Allah kuwa."
Yiman shiru kece silar komai."
"Gaskia itace saidai agode Allah tinda komai yazo da sauki dan wlh da yanzun Maryam ta tsufa gidan nan."
Cewar Anty Hafsat.

"Itama Yaya miyaja mata wannan ba kyautawa bane abin kunya Allah ya kyauta ke kuma anyi dan auta baki kara zuwa hidima Kaduna bare har asake maimaita wannan katobarar.!"

Itadai Mama takasa magana dan ranta ya baci ganin yayarta nata ziga Baba maimakon ta kashe wutar bata gama al'ajabi ba saida taji tace.

"Yaka mata ka hanata dan ba amfanin zuwan ta,kaga in takama ni sai in wakilce ta shikenan."

"Aa Anty Hafsat basai kinba kanki wahala ba ni ya isa inje daurin aure shikenan Allah ya kyauta gaba."
"Ameen ta amsa bisa labbanta.
Itako Mama sai kallan Mamaki takema yayar tata saidai batace komai ba,itako ganin haka yasa ta tafi gida ko sallamar kirki bataima Mama ba.
Har yau Mama tana mamakin abinda Antyn tata taimata,uwa ɗaya uba ɗaya.

Bayan kwana biyu angama biki kowa ya watse har an dan huta Major Sarki ya tara matan sa da ya'yan sa harda Sajida da Samira wanda gobe zasu koma ma'aurin su kallan kowa yayi yace.
"Ina Taufiq.?"
Yana gidan Tariq inji Fatash.
"Okay Maryam,Mufida.?"
Duk suka amsa cigaba dacewa yayi.
"Kun zubda mani ƙima ba abinda zakuyi ku kara birgeni a rayuwar nan daman ina zatan kuna da hankali ashe har yanzun da sauran ku,gaskia bansan mi zance maku ba ina aurar da ya'yana kun keta mani haddina saukina daya na sallami manya manyan mutanen da sukazo mani baici wlh kunci darajar Ba'ba da kuntafi kenan dan ni nasan abinda zan aikata agareku.!"
Kowa jikin ta yai sanyi da hukucin da mijin nasu ke neman yi masune a sabule sukaita bashi hakuri.

Taufiq ne cikin kananan kaya dawowar shi kenan gidan dan uwan nashi wanda tunda aka kai amarya bai kara zuwa ba sai yau shima dan ya takura mashi,saboda Taufiq baisan takura sanin hakan ne yasa Tariq magiya saida Mum tasa baki yaje shine yajima acan shigowar shi kenan zaiyi side dinshi wani Soja ya sara mashi yana kamewa yace.
"Well come Sir,Major is on the meeting."
Yana jin haka yai side din Abban nasu nan fa ya iske ta inda yake shiga bata nan yake fita shima zama yayi,saida yabar Abban ya tsagaita ya shiga bashi hakuri.
Dakyal ya hakura sannan yace.

"Kai Samir naji ance kayi matar aure

Please Login or Register in order to submit comment