Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajena dan haka nariga da na yanke hukunci Samir shi zai auri Amina.!"

Abba dan Allah kadubi uzirina wlh inson Minal har cikin raina dagaske nike maka Ab...

Yimani shiru Taufiq zan saba maka,ina magana kana magana bakai ba Amina wannan shine hukuncina kajecan zurfin cikin ka ya aura maka ita.!"

Shiru Taufiq yayi ya rasa abin cewa.

Aaa Alhaji kabi komai sannu kaga yaron nan yana san yarinyar nan koba komai kodan ni kabari ya aure ta,kodan kara donkon zumincina da ɗan uwana ka duba wannan lamarin.!"

Hajia Maryam kika kara wata magana nan wlh saina baki mamaki anzo wajen,daman nasan duk wannan zagaye zagayen da kikeyi nasan nan zakizo kina ikirarin Amina yar ɗan uwanki ce? Well kin kyauta,amman kada ki manta Taufiq dai ɗanane ko? Kuma nike iko dashi har ke! dan haka idan har kinsan Taufiq jinina ne ni Mukhtar nace ba Taufiq ba Amina da Samir nasanta.!"

Shiru Hajia Maryam tayi ranta nai mata zafi kamar zatayi kuka sanin halin mijin nasu datayi shiyasa tayi shiru dan Allah ya horema Major Sarki zuciya.

Hada ido tayi da Mami ta saki wani irin shu'umin Murmushi mai fassarori tana jefama Mum wani mugun kallo na kinsan sauran.

Abba nasan a halin yanzun zakaji haushin maganata dan Allah ka kara nazari akai,Allah yahuta gajiya."
Yasa kai ya tafi da kallo sukabi Taufiq,yana fita Samir ya shigo,shiko bedroom dinshi ya wuce kwantawa kawai yayi yanajin kirjin shi nai mashi kuna.
A ranshi ko yana ayyanawa ashe daman duk rawar kafar da Ya Samir keyi daman son Minal yakeyi a fili ya furta.
Never bazai yuyuba wlh.!"
Da haka ya tashi ya fada toilet.

******Bayan kwana biyu Abban su Ya Taufiq ya turo iyayen su (kannen shi) sukazo nemawa Ya Samir aurena haka sukazo har gidan mu Baba da Yayan shi sukai masu tarba ta girmamawa saidai bukatar da sukazoma Baba da ita ya gilgiza shi saidai ya boye shock dinshi agaresu cigaba dacewa sukayi.

"Sannan inba damuwa zamuso kafin asaka rana shi Samir yazo su gana da yarinya sannan in san samune kada a wuce wata Ukku anyi angama komai."
Cewar kanin mahaifin su.

"Munji duk abinda kuka ce saidai ni ban ƙi tatakuba amman Aminatu inasan tayi ilimi mai zurfi in Allah ya aramana rayuwa saboda yanzun dudu shekarar ta sha 17,amman bawai zata gagara zaman aure bane aa nidai ina shi'awar tayi ilimi domin shine gatan ta,sannan koba komai Allah ke babba itace babba a gidan nan."
Cewar Baba ya ida maganar ranshi ba dadi dan bai tsammaci haka daga garesu ba.

"Badamuwa Alhaji Yusuf Amina yar muce kuma bokon nan gadon gidan mune tazo gidan boko tunda ba ya'yan mu maza ba hatta matan su cikin yarinya batai ilimi saita kammala Masters dinta muke mata aure,wannan dinma saboda rayuwar Samir din,Alhaji basai mun boye maka komai ba kasan yanda akaita fama da ya'yan nan suyi aure sukaki kamar abin saka hannu sai yanzun aka wayi gari Samir yace ya fidda abin alfaharinmu yar mu Amina ya zaba kaga ai bamu da fargaba zamuyi tuwona maina tunda kasan asalin Samir kuma kasan halayen shi da addinin shi daidai gwargwado sannan zaku iya zuwa ku kara bin cikar halayen shi."

"Gaskia Moh'd wannan haka yakebamu da damuwa indai Amina ce mun aminta da neman aurenta mun baku in yaso daga baya ta ida neman ilimin ta,Allah ya tabbatar da alkhairi."
Cewar Baba Hassan kenan.
Dole Baba yai shiru domin kuwa kanshi ya kulle tabbas shidai ba haka yaso ba,amman ta Allah shine yasab dai dai kuma yasan komai yana faruwa bisa kudirar ubangiji.

Haka sukaci abinci sannan akai masu izini akan idan nadawo hutu Samir yazo ya ganni sai mu sasanta kanmu da haka suka koma gida

Tunda sukazo duk da Mama taji duk abinda yafaru nima dana dawo naji tana gayama Yayar ta abinda ke faruwa,hakan baisa bakin su ya hadu dana Baba ba akan maganar domin manta komai yayi ya aje komai kamar ba abinda ke shirin faruwa don dole itama tasa ido haka yaita rayuwar shi cikin aminci batareda ya bari neman aurena ya daga mashi hankali ba



Amina Pov


Wasa wasa lamura sun mika har mun fara shirin zana Exam wanda daga ita mun gama Terminal Exam saidai muy shirin yin NECO&WAEC,wannan karan ban wani maida himmaba saboda dayawan SS3 suna ganin jarabawar ba wani anfani ke gareta ba haka kowa ya maida hankalin shi akan SSCE da zamu fara da mundawo hutu zamu fara Extention haka kuwa akayi har muka gama Terminal Exam dinmu akai mana hutu kowa ya koma gida cikin aminci
Koda nadowa gida ba wani sauyi dana gani wajen mahaifina asalima ya karramani har abin yafara bani mamaki saiji yake dani kamar zai maidani ciki haka yaitayi mani dawainiya duk inda nikeson zuwa na daga dangi yabarni inje nida Husna.

Wasa wasa har munyi sati biyu a ranar da safe na iskeshi yagama waya yana zaune falo na duka na gaida shi,amsawa yayi.
"Mamana anfito ya kwanan gida inafatan ba abinda ke damun ki.?"
Eh Baba alhamdullh.
Jeki kiyi kalaci."
Toh Baba.
Haka na mike harna juya zan tafi kitchen in zubo kalaci naji yace zo

Zuwa nayi na duka ceman yayi.
"Kina gamawa ki shirya domin kuwa zakiyo baƙo."
Daram daram haka naji sautin kirjina har nakasa boye tsorona kamar ya zanyi bako ni kodai ya manta ba niba ganin hakan yasa yace ke mana inkin gama ki shirya zakiyi bako Yayan ki daga Kaduna."
Dan danan jikina yahau bari nasa Ya Taufiq ne mi hakan ke nufi minene manufar Ya Taufiq akaina ni daman tun visting daya zo mani ban lamunta da yanayin shiba
Ganin nakasa tashi yasa yace.."Mamana kitashi mana."
Baba mi Ya Taufiq zaizo yayi wajena."
Bansan sadda na jefa mashi wannan tambayar ba,shima naga mamakin shi akaina yace.
"Samir ne zaizo neman auren ki,sai ku fahimci juna zaki iya tafiya."

Bansan sadda hawaye suka shido mani ba nace.
"Baba bansan da....
Ya isa tashi kibani waje tunkan ki hassalani abinda kika shuka kenan da kikaje Kaduna soyayya ko bayan ni nahanaki kula samari dan haka yau zakiyi bako sauran in yazo kiyi mashi sakarci tunda haka kika zaba ni kuma zan aurar dake Amina.!"
A razane na ɗago na kalli Baba muddin yakirani da sunana tabbas na bakanta mashi rai inajin haka na mike da gudu nafada dakin mu na duke nasaki marayan kuka inajin kamar zuciyata zatabar kirjina dan zafi.
Hawaye sukaci gaba da sintiri bisa fuskata ba kadan na razana dajin zancen Baba ba,saboda ni kaina ban shirya zuwan wannan ranar ba,karatu shine burina musamman danaje Kaduna naga yanda yan uwana suke boko bil hakki da gaskia.

Kukan naci gaba dayi a hankali raina ba dadi sam,maganar zuci nafara kamar wata zautatta.
Miyasa Ya Samir zai min haka,wannan wane irin son kaine su sunyi karatun su shine ni zasuzo su katse nawa,wannan ai zalinci ne,wani kukan nasake saki mai sosa zuciya,nafi karfin minti ashirin ko yaunwar dake cina na nemeta na rasa ji nayi antaba bayana.

Mama ce ta zauna gefena tashi nayi ina kallan ta,amman kwalla na zuba a idona.

"Kiyi hakuri Amina kisa aranki komai ya sameki kaddarar kice,tunkan asan za'a halicci duniya da abinda ke cikin ta Allah yasa ALQALAMI ya rubuta hakan,dan haka kidaina damun kanki,mu nemi zabin Allah kuma karatu inda rabo zakiyi karatun gaba da secondary kukan ki shi zai kara karya mani zuciya ta."
Rungumota nayi ko magana na kasa banda aikin kwallan da nikeyi da kyal na furta kalmar.
"Mama shikenan ina kankanuwa ta za'aimin aure wlh bantaba maganar soyayya da Ya Samir ba kiyarda dani."

Bubbuga bayana ta dinga yi tace, Nafahimce ki ya'ta kibi komi a sannu insha Allah ba abinda zaki gani sai alkhairi kisa a ranki haka Allah yaso kinji."

Gyada mata kaina kawai na iyayi da haka tasamu na shiga wanka,ina fitowa ta fidda mani doguwar rigar after dress,mai kawai na shafa nasa dogon wando da t-shart sannan na daura rigar after dress data dauko mani da kallabin after dress dita na yafama kaina.

Komawa nayi kamar marar lafiya na zauna sallamar Husna ta yanke mani tunanina kallan ta nayi tasakar mani murmushi.

Kawata wannan madarar kyau har haka,ina zuwa.?"
Maida kaina nayi kasa wasu kwalla suka fara sintiri bisa kuncina da sauri ta rikoni tace.
"Lafiyan ki Amina mike faruwa."
Mikewa kawai nayi na shige daki,ta maye mani baya tana tambaya ta.
Kiyi magana mana mike faruwa.?"

Ya Samir....
Kukan dayaci karfina yasa nakasa ida maganar data zo bakina."

Mi Ya Samir yayi kiyi magana Minal."
Cak kukana ya tsaya sakamakon sunan data kirani dashi take kaina ya kulle na wucin gadi nace.

Zaizo neman auren Husna."
Aida sauri ta mike tana dafe kirji a razane ko magana takasa saidai bina da idanu da tayi tana mamaki wanda takasa boye hakan.

Zatayi magana naji Baba na kwalla mani kira goge kwallana nayi na amsa ina zuwa na duka nace,
Gani Baba."
Yanzun zai karaso ya shigo gari dan haka bance kitayima mutane kuka ba kinajina."
Eh naji."
Kamar marar lakka na koma daki ina kwalla toilet nafada na wanke fuskata nadawo na zauna nace ya iso Husna."

Sai a lokacin tace."kiyi hakuri kawata karki daga hankalin ki daga baya mun nemi mafitar wannan lamarin kinji.?"

"Shikenan Allah ya kyauta."
Da haka na koma ma zauna mikomin lipstick tayi irin mai kyalkyalin nan ansa nayi nadan shafa sai kwalli data matsa mani na saka banfi minti goma da gama shafawa mukaji sallamar su,Ahmad nai masu iso zuwa falon Baba,tabbas na razana iya razana.

Wai yau ni Amina nice zanje wajen saurayi da sunan zance! Saurayin ma Ya Samir anya kwakwalwata zata iya dauka?mike neman faruwa dani anya ba wani babin sabuwar rayuwa bane zan bude ba?

Kamo hannuna naji anyi a razane na kalli Mama wadda fuskar ta ke kwance da murmushi saidai tabbas na karfin haline takeyi gogeman kwallan da sukayi nasarar sakko mani a fuska tayi tace.
"Baban ki yace kije Samir najiran ki."

Uhmmm na iya furtawa, Husna ce ta fesa mani turare a jikina da kyal ta kama hannuna mika fito tsakar gida zuwa sitirum din Baba,saidai ni kadai nasan halin dana tsinci kaina,sallama dauke a bakin Husna muka shiga,gabana nata faduwa fat fat fat.
Baki daya nagama tsarguwa musamman danaji idanuwa kaina nasan kallona sukeyi.
Har nakarasa Asma'u ta zaunar dani kujerar dake facing din Ya Samir.
Itama zama tayi daga gefena gaidasu tayi tunda naji tace.
"Sannun ku da zuwa ya hanya."
Hakan ya tabbatar mani da cewa ba shi kadai bane.
Nima dago kaina nayi aikam idanun mu suka hade dana Ya Samir saina samu kaine da kasa daina kallan shi fuskar shi dauke da smile,maida kallona nayi ga abokin tafiyar tashi na gaida shi,ya amsa fuskar shi fal da annuri.

Daga nan ban kuma cewa komi ba,Husna itake magana da abokin nashi wanda naji ya kira da Bashir.

Haka sukaita fira daga bisani sukace zasu fita domin subar muyi,mugana jinayi kamar in rike Husna amman na daure kamar banjin wani shock a jikina.

Aikam suna fita ya dawo kusa da kujera ta ya zauna yace.
"Haba Yan matana ko bakiji dadin ganin Yayan naki bane.?"
Girgiza kaina nayi nace Aaa.
To kiymani murmushi mana ko bakya lafiya.?"

"Aaa." nasake bashi amsa still ban murmushin ba.
Mike damunki.?"
"Ya Samir dan Allah kace kafasa aurena na rokeka kaga kai Yayana ne kuma ban shirin aure yanzun ba sai na gama karatu.!"

Na ida maganar ina hade hannayena a suffar roko.
Shiru yayi yana kallona amman daka ganshi kasan ya shiga damuwa mai yawan gaske dan harya kasa boye hakan a fuskar shi,dan danan idanun shi suka kada yace......





_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


S1/E 25&26


"Amina?"
Ɗago jajayen idanuwana nayo na kalle shi,ajiyar zuciya ya sauke tareda fesar da numfashi yace.

"Kiyi hakuri bawai inasan auren kibane dan na cutar dake aa ko ɗaya,ina nemanki da alkhairi bazan taba cutar dake ba,sannan maganar karatu zan barki kiyi karatu a duk inda kikeso alqawali Amina dan Allah kitaimaka ki aminta dani."
Ya ida maganar a raunane nikam nakasa ce mashi komai dan tunanina da ilimina ko ince da wayauna a lokacin baikai girman da zanyi anfani da hikima wajen naganin na yakice Ya Samir yadaina ikirarin yana sona haryake burin aurena ba,cigaba dacewa yayi.
"Amina wlh kece wadda na aminta da ita na yaba da dabi'un ina sonki Amina."
Wani irin ansawa naji kunnena nayi kwakwalta taimin zafi narasa gane shin azahiri nike ko kuwa mafarki ne,kuma dagaske ne a gidan mahaifina kuma falon ake furta mani kalmar so bayan nasan dagani har Baba bamu da burin daya wuce inyi karatu musamman ni dake son in karanta Medicine,girgiza kaina nayi nace.

"Kayi hakuri ya Samir dan Allah kabarni nidai ban sonka.!"

Kuka nasaki sosa ni adole ban son Ya Samir ban dauki furta kalmar ƙi ga masoyi yana da illaba a ganina ra'ayina ne na gayama Ya Samir.

Jinjina kai yayi yana mamakin niko ko ajikina mikewa yayi yace.
"To Yan matana kidaina kuka kinji zan bari ki gama karatun ki kinji kinasan hak ko.?"
Da sauri nace Eh Ya Samir inason karatu.
Murmushi yayi mani yace.
"Good girl daina kuka kinji zakiyi karatu."
Aikam na share nawa hawayena harda murmushi na,akan fuskata.

Shima Murmushin yai mani ya aje mani wata leda yace ga tsaraba yai mani.
Murmushi nayi nace nagode.
Da haka yafita yaje wajen Baba suka kara gaisawa yaima Mama sallama suka tafi shida abokin shi Bashir,suna fita nayi dakin mu nida Husna muka dosa wani labarin dan ko maganar bansan ai mani tunda dai yace zaibari ingama har degree dina ai banda matsala daman burina kenan kuma yace zai barni in gama karatu.

Gaskia kam kuruciya dangajin hauka don har ga Allah nayi tunanin Ya Samir Haka yake nufi ashe kuruciya tasa bangane manufar shiba,haka mukaita jin dadi nida Asma'u.

Zainab kanwata ta shigo hannun ta rike da leda ta mikoman.
"Yaya kin manta ledar ki falon Baba.

Cewa nayi ta kaima Mama,kafin ingama maganar ma saiga Mama ta shigo ansar ledar tayi aka bude kayan Costimatic ne da kudi a ciki akalla sunkai duba ashirin,mamaki fal aran Mama hakan yasa takaima Baba,cewa yayi asamu waje ta aje su haka kuwa akayi.

*******Bayan kwana biyu da tafiyar Ya Samir,muna zaune tsakar gidan mu harna saki raina hankalina kwance Baba ya shigo yana waya amsar da mukaji yana maidawa shiya maida hankalin mu,garemu musamman ni dana gama kama kaina.

"Ya Maryam kijira kiji taya za'ayi iyayen yaran nan suzo da kansu neman alfarma muki yi masu aikodan ke mun basu wannan damar."
Bansan dai abinda tace mashi ba naji ya kuma cewa.
"Banda wani labari akan Taufiq amman tayi zanki da'na inso wani bata yuyuwa amman kinsan halina bani karamar magana dan haka kibar Wannan zancen shi Hussein din yazo cikin ya'yan dangi ya zabi wata mana."

Shiru ya kuma yi da alama Mum ke magana duk da munajin sautin fitar maganar ta saidai ba lallai bane kaji me take cewa ba,saidai yanda ta ida maganar a zafafe hakan yasa naji kalmomin karshe data furta.
"Dan haka wlh babu yanda za'ayi Taufiq na son Amina amman kaba Samir dan haka nakashe wannan maganar nadai gaya maka.!"
Ɗit ta tsinke wayar ta,da kallo Baba yabi wayar hannun shi,sannan ya jefo mani wani irin kallo wanda yasa yan cikina hadewa baki daya.
Mikewa nayi a darare zan shiga daki yace.
"Ke zonan."
Kamar in saki fitsari haka naji ba yanda na'iya na iso dukawa nayi gaban shi yace.
"Daman nacewar da kikayi saikinje hutu Kaduna ashe dan ki hada gurmi kikaje,yanzun Samir na sonki ga Taufiq shima sonki yakeyi kin hada fitina tsakanin yan uwa kinsan abinda hakan ke nufi kuwa.?"

Kat kat haka jikina yahau kyarma dan ban iya shiga bala'i ba har hakorana na hadewa take zazzabi ya rufeni bawai tambayar da Baba ke mani bace ta sakani rudu ba,jin wai Ya Taufiq yana sona mutumin dako kwakkwaran motsi bana iyayi a gaban idanshi taya zan fara soyayya da Ya Taufiq.?
Bakijina ko saina saba maki!

Hakan yasa nadawo akidime na fara kuka nace.
"Wlh Baba Dukkan su ban so kowa ba,kayar da dani ban....
Karya kike da Samir din yazo dayake kina son shi ba har kayan sa kioa karba ba,to kisa a ranki ni Yusuf ban maki tarbiyar banza ba,kuma dan haka magana Daya nike baja da baya saikin auri Samir ko kinki ko kinso.!"

"Haba Baban Zainab kabi komai a sannu Allah bazatayi soyayya dasu ba nafi zargin kawai dai su ke sonta."
Nasaka bakin ki Khadija.?"
Allah yabaka hakuri."

Ke kuma kisaka aranki nagama magana kuma aure ko gobe sukazo aurar dake zanyi tunda haka kika zaba,ita kuma ita kuma Umman Aisha dake maganar Taufiq aini iyayen su Samir sukai mani magana,dan haka tayi hakuri bakin ALQALAMI yariga ya bushe magana ɗaya itace girma bazan sauya wannan alqawalin ba saidai in Allah baiba wannan kuma haka yaso.!"

Yana gama fadar haka yai dakin shi,nikam bisa siminti na kwanta zazzabi ringis ya bugeni Mama ta kama ni itada Ahmad na koma daki ina kwalla narasa inda zan saka kaina a rayuwa tun in kankanuwa ta tension zai haye batare dana shirya ba da haka wahalallan bacci yai gaba dani.


Sarki Mukhtar Pov


"Nataraku baki ɗayan ku dan inkara jaddada maku hukuncina agaban kowa dan haka ku bani aran tunanin ku.

Samir,Taufiq,Hajia Mufida,Hajia Maryam."

Duk suka amsa da na'am.
Abinda yasa na ware sunayen ku wannan zaman akan kune yafi karfina domin banda matsala da Tariq hakama Fiddausi,inasan in gaya maku kamar yanda dangina sukaje suka nemawa Samir auren Amina ko ince neman izinin ganawa da yarinya to yaje harya dawo kuma sun sasanta abisa sharadin cewa zai barta tayi karatu,wanda koda basu nema ba ni nasan darajar karatu kuma zanbar ta nemi ilimi.kuma ko nawane zan kashe dan inganta iliminta."

Tunda Taufiq yaji ance wai sunsanta tsakanin Minal da Samir zuciyar tafar duka da sauri da sauri wani kunci fa kishi ya cakar mashi kohon zuciya.
Cigaba dacewa yayi.

"Dan haka kai Taufiq ka hakura kabarma dan uwan ka tunda ya rigaka furtawa,kai xurfin ciki ya cuce ka,sannan bansan kananun maganganu daga bangaren ku musamman ku iyayyen su mata fatan kun fahimce ni."

Da sauri Mami tace Eh Alhaji Allah yasa albarka,shima Taufiq Allah yabashi wadda tafita alkhairi.

Ameen cewar Abba.
Shiko Taufiq ya gaza magana idanun shi sun kada sunyi jajir har saida jijiyoyin kanshi suka mike.

Kai Taufiq kayi shiru inafatan ka hakura ko.?"
"Tabbas banji zan iya daukar kaddarar rabuwa da.Minal itace bugun zuciya ta inama ban kasance a cikin wannan mummunar qaddarar ba,Abba dan Allah kafahimce ni wlh inson Minal.!"

Karkada kafar shi Abba yayi yace.
"Wannan shike nuna karaina ni ko Hussein? Lallai kam ka kyauta toh dan ubanka bazaka auri Amina in kara yimani wannan zancen banzan dan saba maka kuma wlh saina baka mamaki sakarcin banza dana wofi.!"
Jinjina kan shi Taufiq yayi ya mike ya kalli Samir yace.
"Minal kake so ko Ya Samir? Shikenan Abba kusa a ranku ni kuma bani ba aure a duniya yaje ya auri Minal din.!"

Taufiq kada kace haka kadawo Taufiq.!"
Mum ta kirashi da karfi lokacin harya bugo kofa ranshi yai bala'in kuna,shiko Abba dakawa Mum tsawa yayi.

Karki.kuskura kafarki tabar falon nan Maryam bare har ki bishi ki rabu dashi zai gane nidashi waya haifi wani.!"

Haba Alhaji kaduba lamarin nan yar nan fa da ake rigima.akanta diyar kanina ce,ba wanda ya dace ya mallaketa sai jinin ta kodan zumunta miyasa zaka juyawa gaskia baya."

Dakata.Maryam na haramta.maimaita mani wannan maganar agaban idona kuma ba wata gaskia mganin mai zurfin ciki kenan kuma kadan yagani bashi ba Amina.!
Dakin shi kawai Mum ta fada tana bugo kofar.sai lokacin Tariq ya mike yace.

Allah ya huci.zuciyar ka Abba,kuma Allah yakawo mana mafita."

Ameen Hassan amman wannan itace mafita Samir ya auri Amina."
Wani mugun kallo ya aika ma Samir yasa kai yayi side dinsu,ya iske Taufiq yana kaima wardrope duka yana surutai kamar zautacce.

Janyo shi yayi jikin shi suka rungume juna yana bashi hakuri yana jin digar kwallan da sukayi nasarar zuboma Taufiq sun sauka bisa gadon bayan shi,shi kanshi zai iya cewa rabon dayaga. Kwalla ga Taufiq baisan yawan shekarun gaskia yasan dan uwan shi ya gama kamuwa da son Amina kuma shima.sai inda karfin shi yakare saidai in Allah yasa Amina ba matar Taufiq bace.


Amina******


Nikam al'amura sun cakude mani komai yai mani kunci tinda Baba yai mani maganar wai harda Ya Taufiq sai fargaba na yakara yawaita ina zani da kaddarar dake tunakaroni Miyasa zasuce ni sukeso a iya sanin ni ba wata muguwar kyakkyawa bace ta bugu da kari ba ina da kyauba dai dai gwalgwado ban kasance faraba ni wankar ɗarwaɗa ce saidai inada manyan idanu hancina madaidaici kuma ni ban kasance daga cikin dogaye ba kuma ni ba gajera bace ,sannan inada yalwar gashin kai kuma ni yar duma duma ce,daga wannan ni ban tunani za'a sakani layin kyawawan nata sahun farko kota ukku kilan dai tsaka tsakiya mi zaisa dage dole saini sukeso ,kuma ni ba yar wani bace asalima yanzun nike SS3 suko ba wanda baida Phd,dan ya Samir ma harya fara Professor dinshi a China taya zasuce ni zan zama tsarar rayuwar su.

Haka kullin nike cikeda zullumi da tsoro bare Baba daya daukar mani mataki duk da har ynzun yakan jani da wasa kamar yanda yasaba amman bai yarda ba dagani har Mama muka tinkare shi da zancen ba tsabar mataki daya daukar mana.

Haka rayuwa ta kasance saidai godiyar Allah abisa al'ada kamar yanda kowa yasani Lahadi itace kasuwar da garin mu keci saboda girman ranar ko biki da suna bamayi domin koda kayi taro ba lallai ka hada jama'a ba,ina zaune ankawo uwayen cefane nama Beef da kuma kaji sai kayan miya da kayan kasuwa inata garawa saiga Anty Hafsat tazo Mama tace su shiga daga ciki tace nan ya isa haka suka zauna bisa tabar ma,suna fira ni kuwa kitchen na shiga na basu waje bayan mun gaisa sama sama nike jiyo maganar su duk da ba gabana zancen su yake ba saboda nayi zurfi cikin tunani sama sama naji tana cema Mama.

"Wai ke Khadija zama zakiyi Amina ta auri Samir?aini a ganina wlh kika kuskura kikayi wannan gangancin tabbas kin shiga cikin kunci."
A tsorace Mama tace.
"Miyasa kikace haka Anty.?"
Ai baki gane ma zancen ba Hajia Mufida sun hada wannan tarkon dan yarki ta fada duk wulakanci da Maryam tai mata haka zata rama a yarki ammn ki duba shawarata ."
Jinjina kai Mama tayi tana nazari tace.
"Kusan haka amman sai inga kamar ba haka bane."
Kaji ko idan bacci kike to ki farka ko tababa babu haka take bare yanda yarki bata da ilimin nan ai zatasha wulakanci ne."

Haba Anty taya zakice bata da ilimi ga arabi ga boko duk anayi?"

Hmm Khadija kenan ina ilimin yake bayan kinsan gidan da akeson kaita sudin basu dauki matakin secondary wata tsiya ba ai kwara ki duba amman wlh kada ki yarda Samir ya auri Amina."

Hakane kam kice kwara Taufiq din kenan tunda shi dan uwanta ne kuma bazai wulakanta taba."

Kayya kanwata ina rabaki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu,ina ruwan aure sa zumunta,idan aka samu sabani fidda zumunci yake gefe ta wulakanta yarinya,abinda nikeso ki gane kinga dai mahaifin yaron nan tunda bashi yaso ya auri Amina ba zai tsaneta ne,sannan kuma kishiryar Maryam uwar Sarki zata dinga hada masu tuggu har saita wargaza maki auren ya'
Da afara gwara kada asoma kinji dai shawara ta a matsayina na yar uwa agareki ki duba da kyau da idon basira,dan wlh da ya'ta ta auri mai arziki ba kwanciyar hankali kwara na samu tallakan unguwar mu likis ta aura,dan haka takanas ta kano nazo dan wannan zancen sai anjima."

Toh cewar Mama duk kanta ya gama kullewa haka taima Anty rakiya ta rabka uban tagumi haka ta koma daki sukuku.

Ni kaina d kyal na ida girkom shinkafa da miya sai salad,ko bakina bai shigaba na koma daki zazzabi ya rufeni saida Baba yadawo yai mani allura sannan bacci yai gaba dani.






_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

*Garabasa!Garabasa!Garabasa!* 💃💃💃💃💃

Ina Kuke yan mata,zawarawa harma da iyayen Yara ku matso kusa ga wata dama ta samu cikin sauki zaki mallaki naki har gida.

Deezatu Air&Sea ta shirya tsaf domin ku,duk mai bukatar Order kaya ku hanzarta ku tuntubita domin biyar bukatar ku,zaki iya Shipping kaya iri duk abinda kike bukata kamar su.

*Kuloli,Blanders,Tv,Fridge,* *Kuker Gas,Blanket,Carpet,Dinner* *Set,Framefan,Dispenser,Tv* *Stand,Kettiles,Jugs,Flask* *etc,*
domin idan mukace zamu tsaya lissafa maku dalla dallan kayan da take order zamu kwana mu wuni bamu gama ba,ku hanzarto Amare,domin kwasar wannan garabasar a wajen *Deezatu Air&Sea* ,zaki iya shipping ke ɗaya,akawo

Please Login or Register in order to submit comment