Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasance.


"Kin kyauta shiyasa nace da kada kije nasan halinki bakida hakuri sai akai sa'a kika gani baki gani ba kuma kikaji baki jiki Allah ya kyauta.


Ameen, abinda yasa Samir din har part din Anty saida yazo sukayi sallama kuma duk da bawani jituwa tsakanin su a yanzun har gidan shi saida Tariq da Taufiq suka raka shi,kwarama Tariq yazo yana cema Mum wai Samir kecewa Taufiq yanda bai auri Amina ba shima bazai taba auren ta har abada kwarama ya daina wahalar da kanshi sannan tunkan dare yai mashi ya nemi wata can ya aura,dan haka saidai kowa ya rasa ta baki ɗayan su."

Ikon Allah cewar Baba sai kuma yace.
"Shi Hussein din miyace mashi.
"Baice komai ba kaima kasan halin dan naka magana bata dame shi ba,koda Tariq yakeba Anty labarin ana fara fada yabar side ban kara ganin shib sai yau da safe yazo mukayi sallama dashi,daman kwanan shi ukku da dawowa Malesia aka daura auren Samir din."


Tab ikon Allah banji dadi ba saboda ta hanyar Amina wannan rikicin ya faru shiyasa nike yawan nadamar barin ta zuwa hutu Kaduna domin kuwa yanzun komai ya lalace ya Alhaji zaiji."

Aaa Yaya ai kaddarar kenan kuma kai zumunci kakai yarka ba wani abuba daman can suna kishin su saidai ba irin wannan bane."

Hakane amman ai banda ya'ya domin ko gardama Taufiq da Samir basu taba yiba."
Aiko yanzun Taufiq bai kula Samir gaskia.
"Allah ya kyauta gaba."
Ameen ya rabbi.

Kiran sallah akayi hakan yasa Baba ya wuce masallaci mu kuma mukayi tamu sallar gida.

Bayan wasu watanni da suka shude jarabawar mu ta fito tayi kyau a Neco inada 5 credit Chemistry,Biology Physic including Math&Eng,hakama WAEC kuwa 7 credit nasamu itako Husna daga 8 sai 9 credit tasamu daman munyi applying ABU DA BUK saidai ita Husna harda UMYUK ta hada aiko ana nan admission ya fito a ABU 2nd list sunana ya fito suka bani Medicine and Surgery, daman shinayi applying aka kiramu PostUMT naje nayi CBT Exam.

Saida nasamu admission da wata biyu sannan Husna ta samu ita kuma UMYUK Bio Chemistry,munyi murna sosai hakama gida akaita samana albarka,sai dauki muke zamu zama yan Jami'a tunda nasamu admission da munzauna ana fira Baba zai farayi mani huduba danshi yaso in samu BUK acewar shi tafi kusa da gida Zaria nayi nisa, sosai hudubar shi ke shiga har cikin zuciya ta.


Hakama Mama ganin Baba ya dage kullin akan abu ɗayashiyasa ta daka daga batai mani tata nasihar ba.

Maman Husna itama taimana nasihohi Sosai bada bata lokaci ba mukafara registration Zaria na koma da zama gidan wata innar Mama Baba Zahara'u kullin saidai inshiga inje in fidda Course Form ina zuwa sign har na biya kudin makaranta dana Hostel nagama komai cikin kankanin lokaci,ranar wata lahadi zan dawo gida infara shirin komawa school baki ɗaya ina tsaye bakin titi Jafar ya rakoni zan tafi tasha in hau motar gida wata Anaconder baka sai kyalli take ta parka agaban mu,nidai kota kan mai motar banbi ba, naga anyi ƙasa da glass din mota dago kaina da zanyi domin ganin wake ciki naga......



*Bononza maza garzayo yar uwata*

_dama gareki/ka wanda suke bukatar jin yanda chakwakiyar DAUKAR FANSAR BUDURCINA zata kaya amman kash basu da halin biyan naira 500,inata ganin compling dinku akan kuna bukata 500 tayi maku yawa to ga dama ta samu daga yau 28/9/2021 ni Yar'mutan Kankia na rage maku 200 ma'na ku bada 300 dan jin yanda zata kaya amman akwae dateline fa wanann promo zai k'are ranar 3/10/2021 ta k'are sae ku cigaba da biyan yanda sauran suka biya wato 500 yi ma wannan number magana dan jin yanda zaki biya 08160508316 sae na jiku ba sae na gaya maku yanda labarin litafin yake ba tunda kun karanta free pages ,ki biya dan kiji yanda Aysha zata dauki fansar budurcinta a wajen Ahmad👌_


_Share fissabillilah👏_



_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️




*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*


*Dedicated this page to Alqalami fans two,Allah yabar kauna*



S1/E43&44



A hankali ya gama kasa da glass din motar shi daura idona da zanyi naga Ya Taufiq bansan sadda na sauke nawa idon ba domin kwarjini da yai mani fuskar shi dauke da murmushi wanda ya bayyana kyaun shi.

Shiko Jafar sai neman abinda zaikaini tasha yakeyi,ban ankaraba naji yace.
"Jafar saka mata kayan ta boot."
arazane na kalle shi jinjina kai yyi alamun Eh.
Shiko Jafar kallan shi yake domin baisan shiba kuma yaji ya kira sunan shi sai kuma ya maida kallan shi kaina,nima Jafar din na kal.


"Yayan tane Jafar, muje mota ko."
Samun kaina nayi da kasa yi mashi musu saidai bugu da kirjina keyi a, asirce hakan yasa Jafar saka mani kayana aboot musamman daya duba number motar shi yaga C.R.C
Saidai tsaye nayi ban shigaba gani nayi ya bude mani kofa.
Enter shine abunda ya furta jikina sanyaye na shiga ya rufe kofar ya zagaya shima ya shiga.


Bai cemani komai ba ya tada motar muka hau hanya sai lokacin na saci kallan shi naga ni yake kallo sauke idona nayi ba tareda na kalle shiba nace.
"Ina zaka kaini.?"
Sai kuma na daure fuska.

Murmushin dake neman subuce mashi naga ya maida ya sake hade rai wanda yasa nawa shan kunnen ya koma na tsoro domin sai yafi nako yaushe baice mani komai ba sai naji yace

Sace ki zanyi inbar kasar dake baki ɗaya."

Yanda naga yana maganar ba wani alamun wasa ko sassauci a ciki saina rude bakina na rawa nace.
"Ya Taufiq kayi hakuri kadubi girman zumunci kada ka cutar dani dan Allah ka saukini in hau wata motar na rokeka.!"

Ai baki sona ko?gwara in gudu dake kawai ba wanda zaki sake gani yarinya."


Hade hannayena nayi duk da naga kamar da wasa yake mani, ganin ya juya akalar motar a hanyar da bansani ba na fara neman balle motar zan dira naji yasa Lock a razane na kalle shi na kwalla kara ina nashiga ukku zai saceni wayyo Mama ku taimaka mani.!"

Dora hannun shi yayi bisa kunnen shi yanda na cika motar da ihu da gaske nagama yarda Ya Taufiq saceni zaiyi.

"Ke yiman shiru ko in....
Bai idaba maganar da yai niyaba nasa hannuna abakina ina raba ido fatana ya saukeni karya saceni.

Murmushi yayi yace.
"Funny girl look at u."
Dan Allah ka saukeni na tuba wlh ba laifi na bane bansan an fasa auren ba sai daga baya na tuba kada kasaceni Ya Taufiq.

Ganin da gaske nike na razana hakan yasa yai parking yai facing dina na sauke kaina kasa.
"Minal look at me."
Kallan shi nayi shima yake kallo batareda ya keftaba ina son in sauke kaina ina tsoron mi zai faru.

"Am jocking ba saceki zanba taya zan cutar da kanwata wasa nike maki gida zan kaiki kinji trust me."
Ya ida maganar yana marairaicewa da siffar ban hakuri,kuka na kece dashi harda majina dan kuka dan har yanzun ji nike zuciya ta kamar zatabar kirjini shiko kallona ya dingayi yana smile saida nayi mai isata na dauki handkichief dana gani gaban motar na goge nace.
"Saukeni inada kudin motar komawa gida."

Kallan da yai mani yasa na maida sauran zancena dan dole.
Tukar motar yayi still hanyar yakebi sai a hankali nafara fahimtar hanyar gida ya nufa ashe ta By past ya biyo dani.

Munkai minti talatin baice komai saka makon waya dayake yi da mutane saida ya gama ya kalleni yace.
"Congratulation yan Jami'a fatan zaki maida hankali kiyi karatu banda biyema samari."
Jinjina kai nayi kawai bance komai ba domin sai yanzun nadan samu natsuwa.

Minal."
Na'am,shine abinda nace.
Bakiji abinda nace maki bane."
Naji to zanyi."
Good ki kwantar da hankalin ki bazan taba cutar da rayuwarki ba Minal kinji."
Toh amman ka tsoratani dayawa."
"I know na gwadaki ne karki kuskura kibari wan yabaki lift kinji ko bin saurayin kawa a mota ki kiyaye kinajina."
"Insha Allah."
Ina Husna ta samu admission.?"
"Umyuk nace.
Wane course,Bio chemistry nace mashi.
Alright.
Wasa wasa kafin in ankara har munzo malumfashi mun dauki hanya.

Fatima itama nan tasamu Enginearing harta gama komai amman ita tace batason hostel saidai tinda kenan zaki zauna zansa ku zauna tare kinji."
Bansan nayi Murmushi ba saida hakorana suka bayyana.naji dadin ganin Fatash kusa dani.
Murmushi yayi kawai har anyi shiru yace.

Nima dariya nayi inajin sanyi araina ganin mun kusa sauka inajin kamshin gida.
Wayar danaji yanayi yasani kallan shi.
"Aaa kasamu Osama na bashi zanikan gidan saika zabi wanda kakeso zan fada maka price din su."
Aje wayar yayi yace.
Karki biyema samari Minal ki maida hankali kiyi karatu kinga Course da zakiyi babbane kinajina kuma banda yawon banza."
Da haka yaita mani huduba har muka shigo Jikamshi nace nagode.

Yawwa Ya Taufiq daman ,sainai shiru kirjina na duka saboda ina shayin sa sosai kuma inasan tambayar shi.
Inajinki kanwata.
A dake nace
"Inakasan Jafar.?"
Murmushi yayi yace.
Saboda ya rabi farin cikina shiyasa nasa aka bincika mani shidin wanene kuma nagano cousin din Mama ne that's all."
Jinjina kai nayi ina al'ajabi.

Sai gamu mun bullo gidan mutun ɗaya,mun hau babban titi hakan yasa kirjina ya tsinke ganin ya dau hanyar Caranci,nace.

"Ya Taufiq dan Allah kada ka kaini gida bansan mi zancema Baba ba kataimaka mani."
Kallan Mamaki yai mani baice komai ba yai parking kowa yai shiru.

Mi hakan ke nufi kina ganin zaiyi tunanin zan cutar dake ne.?"
Aaa,kawai ka barni in karasa zaifi Ya Taufiq.
"Okay."
Bakin Motar haya ya tsaya gefen titi inda masu motar ke cewa Kankia Caranci Katsina.

Nan na ziro kafata kasa zan fito.
Minal."
Jiyowa nayi ina kallan shi waya ya miko mani cikin kwali Android ce maki manciya ya bani."
Kallan wayar nikeyi ban amsaba, kara jinjina wayar yayi a hannun shi alamun in amsa na girgiza kaina alamun Aa.
Miyasa bazaki karba ba."

Bansan mi zance ma Baba ba shiyasa nagode.!"
Danji nike bakin titin ma kamar wani zai ganmu yaje yaga mashi shiyasa najini kamar bisa ƙaya duk na takura sosai.


Okay go kigaida mani dasu Umma."
Toh, fita nayi na shiga mota da kayana bamu jimaba muka dauki hanya wanda baifi minti talatin ba muka iso Caranci,nahau mashin na tafi gida Sadda ukku zatayi har na iso gida oyoyo kannena sukai mani wanka kawai nayi nahaucin abinci,ina cikin ci Baba ya shigo saidai yanayin shi ya sauya ranshi a dagule dan danan nasha jinin jikina tsoro kada ace yaji labarin haduwata da Ya Taufiq.
Ruwa Mama ta kawo mashi,ansa yayi yasha saida tabari ya ɗan sakko sannan Mama tafara Magana.
"Baban Ahmad mi akai maka naga ranka ya baci dayawa.?"

Dole ki ganni haka Khadija nagaji da wannan maganganun da akeyi akan Taufiq da Amina sun isheni wlh."


Wani irin kwarewa nayi inacin abinci,dan nasan kashina ya gama bushe domin Baba yasan Ya Taufiq ne ya maidoni gida.

Ruwa Mama tabani najima sannan nadawo daidai inata kwalla.

"Maida hankali Mamana ki halaka kanki a banza akan fargaba."
Nidai aikin kallan shi nikeyi.
"Sannu tashi kije daki ki kwanta."
Cewar Baba ganin haka nasan ba zargin da nike bane.
Zan huta nan Baba."
Jinjina kai yayi dan ya gano inasan jin abinda ke faruwa.


"Wlh duk wanda yakara tinkarata da wannan zancen haryace wai ya'ta ta like mashi dan son abin duniya wlh sai nayi karar koma waye, nagaji badan kada mahaifin yaron nan yaji ba dadi ba da kayan sa ranar saina maida masu tsiyatakun su,ina dalili bangaza rike ya'ta ba ni ba makwadaici bane.!"

Shiru Mama tayi dan tasan baiji komai akan abinda tajiba saidai ta bashi hakuri tanaji aranta ba dadi.
Sai dare sannan ya tambayeni ya Zaria."
Nace nagama komai yanzun saura lecture.
Masha Allah,haka nikeso Allah yabaki sa'a.
Ameen.
Muka amsa nida Mama,haka rayuwa ta kasance a gida wanibi da dadi wanibi sai a hankali.


zan wuni cikin kunci saboda kananun maganganun dake kai kawo ga yan unguwa.
Ko islamiya har naji tafara fitar mani rai domin da wahala inje ba'asakar mani habaici ba,shiyasa nafara rashin zuwa islamiya.

Yanzun baifi sati biyu ba mutafi Jami'a Baba ya siyo mani katan trolly na zuba kayana sai shiri nikeyi.
Washe gari da yamma ina zaune tsakar gida na saka kayan fulani a jikina masu dark blue din aiki, kaina ko kallabi babu ina fira da kannena naji sallama,a dana naso na gane muryar mai sallama sai kuma raina bai bani ba,jin an rungumo yasani daka tsalle nima na rungume Fatash,tare muka saki wani irin ihun murna da karfi har saida muka zube bisa shimfidar da muke zaune,Mama dake daki tayo waje da sauri tana tambayar lfy,isowar da zatayi taga Fatima,Murmushi dauke a fuskar ta.
"Lale marhabun da ya'ta mutan Kaduna ya Mum dasu Auta."
Lfy lau suke suna gaishe ku.
Muna amsawa sannu da hanya.
Mikewa mukayi nakama hannun ta zamu tafi dakin mu,mukaji wata sallamar ai kamar anzare mani lakkar jikina na tsaya cak ni ban gaba ba,kuma ban baya ba,ji nayi ana gaida Mama.

Waigawar da nayi naga Ya Taufiq duke yana gaishe da Mama.
Amsawa tayi tace.
"Hussein sannun ku da zuwa tareda kuke kenan sannun ku shigo daga ciki.

Kallan juna mukeyi sannan na sadda kaina ƙasa,ya shiga falon Baba sannan naja Fatash muka wuce dakin mu,yafo gyale nayi akaina na fito zuwa sitrum din Baba na gaishe da Ya Taufiq.
"Ya sannu da zuwa,ammn nan zaka barmana Fatash ko?"

"Itace damuwar ki kenan to da ita zantafi."
Dan Allah kataimaka kabar mani ita tai mani hutu."
Murmushi kawai yayi baice komai ba,niko sai wasa nike da yatsun hannuna duk nauyin shi da kwarjinin shi sun addabeni,jira nike inji yace zai bar mani Fatima amman shiru hakan yasa na ɗago na kalle shi sai kuma nayi murmushi sakamon Murmushin da ya sakar mani.

Aaa baki mukayi kenan.?"
Cewar Anty Hafsat wadda shigowar ta kenan,nasan motar da tagani kofar gidan mune yasa ta shigowa dan taga mike faruwa a gidan
"Ina wuni."
Cewar Ya Taufiq.
Amsa tayi fuska sake sai washe baki takeyi tace.
"Ya Umman ka."
Tana gaisheku."
Muna amsawa,da haka ta fita tayi wajen Mama.
Nikuwa boyayyar ajiyar zuciya na sauke a hankali nace.
"Dan Allah Ya Taufiq."
Okay shikenan zatai maki two weeks."
Yeeeh nace ko godiya ban masa na fita da gudu nayi dakin mu ina murna bisa gado na fada nace
Fatash wlh ya yarda zaki zauna."

"Alhmdullh kinsan kuwa kin yarda yayi tun jiya nike rokon shi wai saidai inje gidan Baba Saude katsina."
Nidai ai tunda yabarki shikenan sai musha yawan mu ko.?"
Aikuwa zamuga dangi.

Nan fa muka hau firar mu cikin jin dadi,Zainab ce ta shigo tace Ya Taufiq zai tafi yana kiran mu.
Fitowa mukayi,lokacin sun fito falon Baba suna sallama.
Kizo kidauki kayanki zan wuce.
Toh cewar Fatima.
Tsaye nayi,kamo hannuna tayi mukaje bakin motar ya bude boot muka dauki troly dinta.

Allah ya tsare hanya."
Nace baice komai ba ya shige motar shi ya tada.
sauke glass din fuskar shi yayi yace.
"Banda yawo ko inafa ku zauna gida."
Toh insha Allah.
Jinjina kai yayi ya tafi.
Maimakon mu dawo gida sai mukaba wani mai aikin gidan mu troly din ya shiga dashi mu kuma muka faɗa gidan su Husna muka hau fira itama tai murna da ganin Fatash.

Sosai muke fira nan fa takebani labarin bikin su Tariq da abubuwan da suka faru harda bikin Ya Samir wani muyi dariya wani kuma muji takaici har magrib sannan muka tafi gida muna zuwa wanka mukayi mukai sallah mukaci abinci tuwo miyar kubewa ɗanya.

Goma dai dai muka kwanta muna fira jefi jefi nida Fatash har bacci yafara gaba da ita.







_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️




*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*



S1/E45&46



Bayan kwana biyu nida Fatash ne a gidan kakanin mu,da sauran cousins dinmu,anata fira kowa yana fadin albarkacin bakin shi.

"Ni wlh nafison inga Ya Taufiq ya aureki Allah."
Cewar Na'im
Nima wlh babban burina kenan inga Yaya ya auri kawata kuma Anty na.
Bugun wasa nakai mata nace.
"Rife mani baki kinzo sai surutu kikeyi."
Daga fadin gaskia Allah Amina Taufiq mutumin kirki ne."
Ya Na'im kaidai kayi addu'a Allah yaimana zabin kwarai shine magana,kinga muje inkaiki ki gaida grandma dita."
Shikenan tunda bakison maganar muje.
Sallama mukai masu nan muka wuce gidan su Mama.
Muka gaida kakanin nawa can muka jima sosai ba kadan ta karrama Fatash ba har kawu Mannir ya iske mu shima dana gaya mashi wacece ita zama yayi mika hau firar tare sai shiddan yamma muka koma gida.
Haka naita gwadawa kawayena Fatima kowa ya santa har tsaraba suke kawo mata da yan kasuwa hakama Baba kullin zai dawo gida sai ya riko mata kayan dadi,sosai takejin dadin zaman gidan mu.

Washe gari litinin da yamma muka shirya mukatafi islamiya muna hanya akasha gaban mu yan matane guda hudu sanye da after dress,kaucewa mukayi zamu tafi naji anyi jacking dina andawo dani baya.

Itace kun ganta nan,itace ta dauke mashi hankali har yake wulakanta mana kawa,wlh sai munyi maganin yarinyar nan,shegiya mai bakar anniya."

"Haba taya muna tafiya zakuzo kusha gaban mu dan Allah kubamu waje."
Cewar Fatima.

Ke waya saka dake zamu ballaki,ke kuma kiyi gaggawar barin rayuwar Taufiq inba hakaba wlh sai munyi ajalinki,karuwa kun nanike mashi dan kuna kwadayaiyu dagake har iyayenki."

Jin ance za'a halakani bansan sanda jikina yahau bariba kamar mazari nakasa ko magana harna fara zufar bala'i ga tsoro ya gama tasiri a jikina."
Ita kanta Fatash zuwa lokacin saidai ido,dan ta tsorata.
Haka suka tafi suna dungurina tareda alwashin sai sun kasheni in suka kara ganina ko suji labarin na rabi Ya Taufiq.
Jiki mace naja hannun Fatash muka dawo gida islamiyar dana fasa zuwa kenan.


Koda mukazo gidan a rufe ba kowa hakan yasa naje gidan su Asma'u na anshi key na bude muka shiga, daki muka wuce ko uniform ban cireba nahaye gado tsoro ya gama kamani da zullumi.

Inajin Fatima ta kira Ya Taufiq tana gaya mashi abinda yafaru harda kukan ta,dan itama ta tsorota,cewa yayi tabani wayar.
Daura mani tayi a kunne sai sauke ajiyar zuciya nikeyi a hankali zuciya ta na bugawa.


"Minal calm down pls kinsan su waye sukai maki barazana."
Girgiza kaina nayi banji zan iya bude bakina in mashi magana domin kaina ke sara mani ganin naki magana yasa Fatash cewa.
Yaya bata iya magana kabarta bacci zatayi,sai in tatashi.
"Okay."
Yanke kiran tayi nikam daga haka bacci ya daukeni ban kara sanin wainar da ake toyawa ba.

Koda gari ya waye hana Fatash nayi sanar ma mutanen gida abinda ya faru,ko Ya Taufiq bankara bari ta kirashi ba,dan bansan kowa yasan zancen danko Asma'u banba labarin ba,haka naci gaba da rayuwa ta hankali kwance.

Nida Fatash ba kadan muke tsara yanda zamuyi rayuwar mu ta Jami'a ba,musamman da zamu zauna daki ɗaya kullin maganar mu kenan,kana ganin mu kasan dauki muke irin na JJC dan kuwa komai mun kammala nayi parking har ranar tafiya mun tsaida.

Ita kanta tace tana komawa gida da kwana ukku zata shirya ta tafi makaranta,nima ranar da zata tafi nace zan koma school din.

Washe gari tunda safe Fatash tagama hada kayan ta zata koma gida driver kawai take jira dan Mum tace an aiko a dauke ta.
Aikam Mama ta hada mata kaya iri iri harda su goriba magarya soyyayar fara da taura irin kayan mu na karkara sai su kuka kubewa da garin tuwo haka ta hada mata komai tace takaima Mum,goma daidai drivern su Fatash yazo ya daukarta.


Rakiya mukayi mata har bakin mota Husna tabata tsarabar tuwon madara a botiki dan karami,daga mata hannu muka dingayi har suka bacema ganin mu sannan muka dawo gida.


*********Bayan kwana ukku kamar yanda muka tsara nida Fatash ranar nayi shirin tafiya makaranta nida Zainab kanwata mukaje gidan kakarmu nayi mata sallama,sannan nadawo gida,tun kafin in shiga dakin mu najiyo muryan Anty Hafsat a falon Mama tanata masifar wai akan me za'a barni inje jami'a salon in lalace wannan gazawace ba tarbiya suke bani ba waima har shekara bakwai zanyi.
Wani irin zafi kirjini ke mani domin natsani maganganun da Yayar mahaifiya ta ke yawan yi akaina miyasa ta sakamani ido har haka miyasa komai nata yana kaina,maganar da Mama ke mata shiya katse mani tambayoyin da nike jefoma kaina wanda banda amsar su.


"Haba Anty miyasa kullin bakya kyautatawa Amina zatone kidaina fadar munanan maganganu akanta kema fa uwace a gareta baki gudun kada yau da gobe bakinki yai tasiri akanta mikikeyi har haka.?"

"Aaa Khadija nifa bazan zuba idoba cikin zuriyar mu kufita daban ba ita wani tafi ina laifin ko College ko Health taje tayi shine zaku kaita har Jami'a aaa wannan rashin lissafi ne sam taya zataje har Zaria ai tayi nisa ba dole tarbiyarta ta lalace ba daman ana cewa yan Jami'a yan iskane itama ta dauki hanyar lalacewa"


To Allah ya tsaremana zuriyar mu daga lalacewa,kuma ki bari indan Baban ta yadawo saikice mashi kada yabari taje nikam banda wannan ikon kuma Allah yatsare ya kyauta gaba."


Aaa ni dake nikeda iko bashi ba kece zaki tunkare shi da maganar tunda mijin kine bani ba."


"Kinaso yau in kwana gida kenan Anty kinsan yanda Yusuf yasa karatun yarsa a zuciyar shi kuwa bani cikin wannan zancen gaskia."



To ai shikenan ranar data bare maku karki kuskura ki nemeni danni banga kayan arziki ba a harkar jami'a ke Umaima tashi muje gida ma."


Fitowa sukayi nikam ina bakin daki ban shiga ba kuma ban bar bakin kofar ba wani mugun kallo na watsa ma Anty Hafsat wanda ni kaina bansan nai mataba dan nagaji da halayen ta,na fahimci kullin bata nufina da alkhairi so take taga sharri ya fada mani shiyasa natsaneta a raina.


Ke dan uwarki nikike harara wato rashin tarbiyarki da tsaurin idon ki haryakai nan ko? Kinyi abanza dan ba yanda zakiyi dani dole in magana mai mugun halin tsiya yar banza."


Kallan up and down nakara yi mata na shige daki ina banko kofa da karfe,can najiyo tana cewa.


Shikenan Khadija nan gaba ya'yan ki fara dukana zasuyi yanzun dan gantalewa a gaban idonki yarki zata bugamani kofa amman kisa mata ido yayi lalacewa takai karshe shinge ya koma turwa muje Umaima.


Har sun tafi sai kuma naji karar maganar ta
Dan haka wlh rayuwace dani take zancen sainayi maganin ta.


Haba Anty Hafsat miyayi zafi har haka.
Ke muje kema dan ubanki tunda banan aka binne cibinki ba.


da haka suka tafi jinayi an banko kofar dakin mu Mama ce tsaye ranta kuwa duk ya gama baci kallan da take aika mani dashi yasa sauke nawa idon kasa jinayi ta rike mani kunne da karfi tace.


"Kedai bakijin magana ko Amina yanzun ko kunyata bakiji ba,kika harari yayata anya kinso zaman lafiya duk abinda zatai maki ai saikiyi hakuri taci daraja ta ni uwarki karfa ki manta mahaifar mu ɗaya da ita,amman kin kyauta.!"


Ta dungureni ranta ya gama baci sosai,riko hannun ta nayi ina bata hakuri

Kiyi hakuri Mama nakasa boye bacin raina ne shiyasa amman insha Allah bazan kuma ba kiyi hakuri dan Allah."
Shikenan Allah ya kyauta gaba amman ki dinga bin komai a sannu.

Toh Mama insha Allah.
Wayar Mamace ta hau kukan neman agaji miko mani tayi tace,ga Fatimar Kaduna.
Amsa nayi nasa akunne.
"Minal kintaho ganina zan fita daga gida yanzun nan."
"Aaa Fatash Baba nike jira yaje Katsina sai anjima zantaho insha Allah."
Okay dan Allah kada ki wuce yau bansan in zauna ni kadai pls kawata."
Insha Allah yana dawowa zan taho karki damu aikinga ban dare ba."
Toh Allah yatsare.
Ameen ya Allah."


Wasa wasa har dare ba Baba ba labarin shi,kira kuwa nasha shi wajen Fatash har saida na daina dauka dan bansan mi zance mata ba.
Sai bayan isha'i ya dawo,kannena suka taro shi suna mashi Oyoyo falon shi mukaje duk muka rike mashi kayan daya dawo dasu a hannun shi,zama mukayi ya miko mani leda amsa nayi yace


"Bude Mamana tsaraba nayi maki,nasan yau naima Mamana laifi kinasan zuwa school amman nahanaki tafiya afuwan."
Dariya nayi nace bakomai Baba ai gobe sai intafi."
Aaa kibari sai ranar lahadi sai ki wayi gari litinin tinda kinga yau friday."


Badan nasoba nace shikenan Baba.
Saidai raina na wajen Fatash yanzun nasan tanacan tanajin haushina,amman ba yanda zanyi.
Bude ledar nayi naga kaya Baba ya siyo mani da kayan shafa harda turaruka sosai naji dadi.

Nagode Babana Allah yakara arziki da budi Allah yajikan iyaye.
Ameen Mama na,anshi wannan kiga."
Wata ledar ce ansa nayi bakina har kunne ina budewa kuwa naga Waya kirar Tecno mai touching bansan na rungume Baba ba inata murna,sai uwar godiya nike zabga mashi hakama Mama nata tayani.

"Bakomai Mama nidai fatana ki maida hankali kiyi karatu banda biyema samari kinji."
Toh Baba zan kiyaye.
Allah yai maki albarka keda kannen ki baki daya.
Ameen muka,amsa.
Nan yaba kowa tsarabar shi,amman saboda dauki saida nakira Husna ta wayar Mama nace mata Baba ya siyomani waya.
Aikuwa tara saura saiga ta tazo nanfa mukaita jin dadi sai tara da rabi ta koma gida itama gobe zata tafi makaranta shine Baba yace sai in mata rakiya tunda ni sai jibi zantafi,saina karajin dadi.


Washe gari kuwa da karfe goma Husna ta gama shiri

Please Login or Register in order to submit comment