Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baba ya yaba da kyawawan halayen yaron saidai ya bashi uzurin ba yanzun zai mani aureba saboda karancin shekaruna da kuma karatu da nikeyi wanda ban tsoma hannu ba a harkar neman ilimi da haka yaba Mustapha hakuri saboda uxurikan daya bashi d haka sukayi sallama Baba ya dawo cikin gida ya zauna ya kirani da Mama duk muka maida hankalin mu kanshi yace.
"Maman Amina kinji abinda wannab yaro yazo dashi sannan ga uzurin dana bashu,saidai ke Mamana dalilin dayasa nakiraki bansan ki saka soyayya a cikin ranki ki dage kiyi karatu bil hakki domin shine gatan ki,kinajina.?"
"Eh Baba insha Allah."
"Allah yaimaki albarka."
"Ameen Mama ta amsa,sannan taci gaba dacewa.
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi kuma yai mata zabi a rayuwar ta."
"Ameen ya hayyu ya qayyum."
Da haka Baba ya sallameni na koma daki hakanan naji ina smile wai nice za'ace yau ga saurayi yazo neman aurena duk da Baba baiba shi izini ba amman wannan shine first life dina da zance saurayi yace yana sona da karancin shekaru sai smile nikeyi inajin dadi araina.

*******bayan sati ɗaya zaune nike ana mani kitson wibin duk da kasancewa inada gashi ba laifi amman hakan bai hanani son kitso ba haja mai kitsona tagama yarfa mani kitso gwanin ban shi'awa yau yakama sauran kwana biyu intafi hutu Kaduna sai jin dadi nikeyi,haka aka gama mani kitsona na saka hijab dina kenan naji sallamar Asma'u da kawar mu Naja'atu murmushi muka sakar ma junan mu sannan naima maikitsona Huwaila sallama muka tafi a hanya muke yar fira har Naja'atu tai mamu sallama sannan muka iso kofar gidan mu kasancewar Asma'u makobciyar muce a kofar gida muka tsaya nace.
"Kawata wlh akwai labari."
"Uhmm daman ai dole kice haka tunda kina murna xakije Kaduna kibarni nima wlh Baba nadawowa zance Kano zani dan bazan iya zama in baki nan ba."
ta ida maganar a marairaice dariya sosai naima Husna nace.
"Wlh ba murna nikeba kema kinsan banjin dadin rashinki a kusa dani kawai dai inason inga Goggo Maryam shiyasa,kinsan mine?"
"Sai kin faɗa."
"Gobe kizo ki mani lalen salataf daga nan zan gaya maki labarin da nai maki tanadi."
Cikeda zumudi tace.
"Naji kuma nayarda tunda kin lakaikayeni d dadin baki Allah yakaimu goben."
"Ameen ya rabbi,kinga bari inje gida aiki zan danyi karki rikeni da surutu."
Murmushi kawai nai mata da haka ta fada gidan su nima na shiga gida na iske masu siyan kankara sunzo Ahmad na zuba masu a cikin buhu haka ake zuwa sarin kankara a gidan mu da yawan gaske,toilet na shiga na dauro alwalla na tada sallah.
*****koda dare yayi ana isha'i Asma'u tazo gidan mu already ba hada lallai tana zuwa sallataf kawai ta yanka tafara gera mani mai gidan siga haka taita samani muna fira ina bata labarin Mustapha sosai Asma'u ta murna dayake abun namu sabon shigane shiyasa zumudin yai yawa da murna cigaba da cewa tayi.
"Kinga munayib Candy sai yazo a daura maku aure kinga tuwona maina ina zuwan gidan ki muna girki."
Sosai mukasa dariya saijin dadi nikeyi jin yanda muketa tsara lamuran mu,idan Mustapha ya dawo ya aureni,haka mukaita fira kala kala bamu ankaraba mukaji anfara kiran assalatu kallan juna mukayi muna mamaki da al'ajabi motsin Baba mukaji zaiyi alwalla ya tafi masallaci da sauri muka kwanta kamar masu bacci nanko lambo mukayi da haka dai baccin kuwa yai awon gaba damu,bamu muka farkaba sai shidda na safe ni na wanke kunshina nayi salla itama tayi alwallah tayi sallah,Mama ce tace.
"Kuzo inga kunshin naku jiya kunjima bakuyi bacci ba har 12 na dare gaskia kunjima bakuyi bacci ba."
Gaishe da Mama mukayi ta yaba da kyaun kunshin domin kuwa yai jajir dashi kallan hannun Asma'u tayi tace.
"Miyasa bakima hannu ba.?"
Sosa kai nayi nace.
"Mama batayi komai ba har kafarma batai mawaba."
Aiko Mama tahau fada tana cewa,ya za'ayi ta wuni wajenki tana maki kunshi ke bazakiyi mata ko ba lallan ne.?"
Aa mukace ma Mama cigaba da cewa tayi.
"Dan haka sai an ramama kura aniyar kema sai kin mata koda kuwa da rana ne."
"Toh Mama."
Aikuwa hakan akayi,muna gama kalaci nasama Asma'u kunshi sadda biyu xatayi ya kama yai kyau saidai ni mai tabarma nai mata,ba ita ta koma gidaba sai bayan la'asar sannan na naci gaba da parking kayana.
Washe gari da safe nagama shirina mama kema nasiha akan zama da mutane lafiya sannan ingani ban ganiba sannan inji inkiji haka na fiddo akwatina kannena duk sunji ba dadi harda kwallan su,gidan su Asma'u na shiga tana ganina ta mike da wanke wanken da takeyi dakin su na shiga nan naima Mama sallana sosai tayi min addu'a haka naima step mother dinta,da ido Asma'u ke bin ganin ta gaza yiman magana hakan yasa nayo waving dinta a fuska nace.
"Besty nifa zan tafi kinki magana ko so kike ki sani damuwa."
Sauke ajiyar zuciya tayi tace.
"Mikikeso ince maki besty da dayanda zanyi tabbas ba inda zakije amman dole in hakura Allah yatsare hanya."
ta ida maganar kamar mai shirin yin kuka,da haka na fito zuwa itama gyale ta yafa tai mani rakiya ganin Ahmad ya fiddo mani kayana nan nayi sallama da Asma'u tana kuka ina kuka haka natafi kamar infasa zuciya ta cike da kewar yan uwana


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


S1/E 9&10



******* ina isa Kaduna bayan sallar la'asar na samu mai taxi nace yakaini unguwar Sarki haka muka dauki hanya,bamu jima sosai ba,muka iso cikin unguwar har kofar gidan Alhaji Sarki Mukhtar Munzali ana saukeni na bashi kudin shi, daukar jikan hannuna nayi na shi ga cikin gidan Mai gadin sune na iske bakin dakin shi gaida shi nayi kallona yayi yace.
"Yan mata daga ina.?"
Charanci
Nabashi amsa ataikece koda yaji garin da nafada bai kuma tambayata yace
"Sannu da zuwa aiko Hajiar tana cikin sashenta muje nai maki iso."
Akwatina na waje.
Fita yayi ya dauko mani,muka wuce ciki har babban falo ya aje mani shi,sallama ya dinga kwadawa kamar wani bako daga saman bene naji ana cewa gani nan zuwa.
A hankali Anty Maryam ta dinga sakkowa bisa benen dake tsakiyar falon wanda ya gaji da ƙayatuwa,ni kam na gama shagala da kallan tsarin falon da kayan alatun dake cikin shi na ban mamaki,haka natsaya kamar wata sakara ina kallan tsaruwar wajen,maganar da naji Baba mai gadi nayi yasa na dawo hayyacina.
"Barka da yamma Hajia ga bakuwa kinyi daga Caranci,shine nace bari nayo mata.....
Tun kafin ya karasa maganar dake bakin shi naji Anty Maryam ta rungumeni tana kiran Oyoyo Mamana kece haka sannu da zuwa,gaskia kin kwashi gajiya sosai."
Murmushi nayi ba duka zan gaida Yayar mahaifin tawa da sauri ra taroni tace.
"Aaa haba Ya'ta muje ki zauna ki huta,Malan Idris gaskia ka kawo mani albishir mai dadin gaske anjima kazo ka anshi tukwici."
Dukawa yayi ya hau godiya.
Niko kallan mamaki kawai nike masu,kamani tayi ta zaunar dani cikin ni'imtaccen falon da sanyin AC ya gama karade shi,cikin kankanin lokaci ma'aikatan gidan suka fara kawo mani kayan alatu irin nasu na masu kudi,sallama muka tsinkaya Fatima ce ta shigo cikin falo ita da Aisha,aiko da gudu sukayo kaina sunata murn,nima murnar ganin cousins din nawa nikeyi,Anty Maryam ce tace.
"Ku rakata daki tayi wanka ta huta saitazo tayi dinner."
Tom Mum,tashi muje Amina."
binsu nayi har cikin tankamemen bedroom dinsu wanda yake dauke da gado guda ukku maki manta da katuwar wardrope din dakin tasu mai part part,bamu jima da zama ba mai aikin su ta shigo da akwatina ta aje dukawa tayi tace.
"Barka da zuwa ga akwatin ki nan."
Sannu nace mata Fatima ce ta dauki kayana ta dinga jerawa cikin wardrope haka ta gama shiryasu tsaf,Aisha ce tace.
"Anty Mina kishiga kiyi wanka an hada maki ruwa."
Tashi nayi na shigo hadadden bathroom dinsu irin na turawa wata cobelt ce aje gefen bango budeta nayi na dauki towel wanda gasu nan jere wajen kala shidda daurawa nayi na debe kayana na saka cikin basket danaga suna aje kayan wanki,kallan kaina nayi jikin madubin dakin ina smile saboda komai nasu yai masifar burgeni,wanka nafarayi inason in kunna shawer ina tsoro gani nike kamar ruwan zai iya kasheni abinka da ban saba ba,haka nagama wanka na sannan na daura towel na fito ina tsane jikina da makimancin towel dake hannuna,ina fitowa naje bakin mirrow nashafa mai ba wani kwalliya naiba ba saka doguwar rigar material marar nauyi, Fatima ce tace.
"Kawata kinganki kuwa masha Allah,kinyi kyau muje dining yunwa nikeji."
To nace mata ina fesa turare a jikina tare muka fita zuwa falo,Mum muka iske a falon ita daTarik,tunkan mu zauna Mum tace.
"Sannunki Ya'ta muje dining aci abinci ko.?"
Murmushi kawai nayi kallan Ya Tarik nayi na gaida shi,cikeda kulawa yace.
"Yawwa Amina Ya hanya saukar yaushe.?"
Yau,na bashi amsa atakaice.
Koda mukaje dining saving dinmu mai aikin su tayi.
Sinasir na zaba ta zuba mani da roman anta sai kuma mango juice ta zuba mani haka ta sama kowa abinda yake bukata,kafin inci abinci lemon na dauka nakai bakina zan kurba kenan,naji wata irin dakkkar murya mai ratsa kunne da zuciya kanaji kasan mai maganar ya amsa sunan shi da akira shi cikakken namiji,aje cup din nayi,amsa mukayi baki ɗayan mu,a hankali na waigo ina kallan kofar daya shigo,kallo ɗaya nai mashi na kauda kaina dayake naba kofa baya,tsaye yake ya goya hannayen sa bisa bayan shi,yana ta kallan mu Mum ce tace.
"To Soja kazo kayi tsaye kikam ka karaso mana cikin mu waye bakon ka,Aminar ko wa.?"
A hankali na dinga jin takon shi ta bayana dan danan na tsargu da kaina,duk da bawai wajen nawa yake yowa ba,kafin in ankare naga harya iso kusa da Mum yaja kujara ya zauna,wadda take facing dina,maida kallan shi yayi kaina,wani irin kwarjini yai mani ga nakasa kallan kwayar idanun shi.
Ya Taufik sannu da zuwa."
Cewar Fatima wadda ta janyo kula zata zuba mashi abinci ba tareda ya kalleta ba,ya daga mata hannu alamun ya koshi, ɗago kaina nayi a hankali na kalle shi,saidai kamar yanda nike zargin kallona yake ashe kuwa nidin yake kallo,sadda kaina nayi nace.
"Sannu da zuwa,ina wuni."
"Lfy."
Itace amsar daya bani atakaice.
"Taufiq kaidai ba zaka daina wannan halin naka ba na miskilanci nasan bakaci komai ba amman kace wai ka koshi,minene haka.?"
"Mum kidaina bazan iya cin komai ba sorry."
"Ki kyale shi Mum ai cikin shi sai kace dai wani yaro."
Cewar Tarik.
"Enough Hassan,ba ruwanka tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah."
Murmushi kawai Mum tayi bata kuma cema ya'yan nata komai dan alamu sun nuna inda sabo ta saba,dayake Tarik da Taufiq twins ne, Hassan da Hussain ne Taufiq shine karami.
Kansu hade yake suna matukar kaunar junan su kwarai da gaske saidai su kanyi yar tsama tsakanin su saidai basu fada na tashin hankali kuma duk abinda daya zaiyi sai daya yasani,hatta kaya iri daya suke sawa saidai ba koda yaushe ba,ma'ana suna da banbancin ra'ayi.
Maganar shice ta daki kunnuwa na yace.
"Ya Abba da Umma.?"
"Lafiya suna gaidaku "
Jinjina kai yayi ya tsiyaya lemu yasha,nikam nagaza sakin jikina inci abinci tunda ya shigo duk narasa sukuni ke kince ba dan uwana ba,hatta Mum ta fahimci nakasa sakewa.
Ki saki jikin ki kice abinci Mamana."
Kallan Mum nayi nace nakoshi."
Zatayi magana mukaji yace
"Kyaleta Mum aiko da kaina zan mata dure yanzun nan kintaba ganin mutun yayi tafiya irin wannan sannan yace wai bazaici abinci ba."
Kallan shi nayi saidai kamar ba shi yayi maganar ba dandanan ya hade rai,har abin yafara bani tsoro yanda naga ya hade rai hakan yasa nafara yagunar abincin tashi yayi ya koma falo yafara kallo,still yana danna wayar hannun shi,lokacin waya mai latsa latsa sai wane da wane shiko tashi irin open and close din nan ke gare shi.
Kamar jira nike yabar wajen nafara hakar abinci na,baki dayan su dariyar dake cinsuce suke dannewa dan sun fahimci kwarjinin Tariq ne ya hanani sakewa haka muka gama muka dawo falo saidai nikam jinike kamar ina bisa ƙaya,na gaza sakewa saboda danayi kwakwaran motsi sai inji kamar kowa ni yake kallo,haka na matsama Fatima ba shiri mukayi daki ina sauke ajiyar zuciya wannan kenan.
******Washe gari da safe bamu muka sauko kasa ba sai after 10am lokacin kuwa ba kowa a falon amman angama hada dining,hannuna Fatima taja mukaje mukafara zuba break fast kula ɗaya doyace da kwai sai arish wani vowel cast kuma Sandwitch ne sai ruwan lipton da bread sai kayan tea,dake gefe zuba man sandwitch tayi duk da bawani cimata bane amman ni hakan bai hana inci abu koda ban taba ciba,a hankali na gutsire shi nafara ci hankali kwance domin kuwa yai mani dadi matuka,kallan kawar tawa nayi naga tasa fork ta debo dankali da kwai takai baki maimakon taci ta kasa ci kuma bata aje fork dinba,fahimta nayi akwai abinda take kallo dago kaina nayi nabi inda take kallo aikam take naji gabana ya yanke ya fadi Ya Taufiq sanye cikin kakin sojoji fuskar nan murtuk kamar an aiko mashi da sakon mutuwa saidai baki ɗaya falon ya hargitse da fitinannan kamshi,gani nayi Fatima ta duka tace.
"Morning Sir."
Nikam na kasa ko magana saima tattaro jarumtata da nayi nace.
"Ya ina kwana."
Jinjina mani kai kawai yayi still hannun shi na goye a bayan shi,a hankali ya dinga tunkaromu harya zauna da sauri Fatima ta hada mashi tea ta aje mashi.
"Ya bakunta da dadi ko.?"
Yanda yai maganar kamar bashi domin harya kurbar tea din da Fatima ta aje mashi.
"eh akwai dadi."
Na bashi amsa a takaice domin Allah yasani ni dai duk cikin Danginmu ina shakkar Ya Taufiq tunkan ya zama soja bare yanzun da yazama babban soja Landa Army a jahar Kaduna domin igiya ukku ke jikin kayan shi ga stars dayawa a jikin kayan nashi hatta hular kanshi akwai hoton meki ajiki,abin mamaki yana gama shan tea ya mike tareda cewa.
"Ku gaishe da Mum."
To shine abinda mukace,haka ya fita inaji sojoji sunata sara mashi can najiyo jiniyar su alamun sun tafi.
"Kai Ya Taufiq yafiye zafin rai ni wlh yana razani ina dalili mu yazo yai aure ko mun huta.
Murmushi kawai nayi mata,hararar wasa ta balla mani tace.
"Ni wlh dama ki aure shi da kinji dadinki."
Zaro idanuna nayi waje nace.
"Rufa mani asiri ina zankai Ya Taufiq."
"Ke wlh shekarar shi 38 bai wani tsufa ba sosai."
"Aa wlh ya kusa arba'in fa,nifa 15 taya zaki hada dan Allah kidaina."
Dariya da dinga yi mani ganin duk na tsure dan har idanuna sun kawo ruwa.
Sallamar Ya Tariq mukaji fuskar shi dauke da murmushi yana sanye a cikin kayan Doctors yasha suite bakake daya su dukan su farare ne kuma identical twins ne saidai inda ake gane su shi Ya Taufiq bai dariya ko kadan saidai yai murmushin gefen baki,sannan bai magana saidai jefi jefi kuma yana magana a kausashe ta cikar namiji jarumi,shi kuma Ya Tariq yana dariya in anyi abin dariya shi mai fara'a ne sannan yana mgana sannan muryar shi nai sanyi ce,tanan ake banbance su amman ta kama baka isa ka gane waye Taufiq ba sannan kuma waye Tariq ba hatta Mum tana take banbance su.
Zama yayi yafara break gaishe shi mukayi ya amsa cikin sanyin rai yace.
"Hajia Amina ya Kaduna."
"Lafiya lau."
Baki da wata matsala ko.?"
"Eh babu."
Masha Allah yace yana cin abincin sosai yakeci,sai a lokacin Mum ta sauko kasa tana isowa muka gaidata zama taya sannan muka tashi muka dawo falo muka fara lido.
Munaji yaima Mum sallama yatafi wajen aikin shi.
Aisha ce tazo muka tafi ɗayan sashen kishiyar Mum wadda suke kira Mami sunan ta Hajia Mufida,muna zuwa muka iske falon nata daga ita sai yarta Zakiyya suna zaune saidai suma part din nasu ya hadu amman kowa da kalar kayan furnichas dake ciki,ita Mami leaders dinta ash color ne sabanin Mum da nata ke black muna zama muka gaidata cikeda sakin fuska ta amsa sannan tace.
"Fatima dagani wannan yar Baba Yusuf ce ko.?"
"Eh Mami Amina ce."
Gaidata nayi cikin girmamawa,amsa mani tayi tana tamabayata hanya.
Hajia Mufida itace babbar matar Sarki Mukhtar Munzali ta kasance yar mulkice ma'ana tanasan duk inda take anuna itadin ta isa takai,kyakkyawace fara mai kyau bafullatana banbancin ta da Mum ita mun bakace kyakkyawar gaske kuma ita buzuwa ce wanda shine gadon gidan mu,Mum bata daukar raini ko kadan tanasan girma kuma tanasan a mutunta wanda mutunta mutun ya zama kamar dabi'ar tace,sabanin Mami da take yar gadara.
"Yaushe kikaso Amina.?"
Jiya da marece."
Masha Allah,ya maman taki.?"
Tana gaishe ku.
Zakiyya ce tace."Mami Ya Samir yace,ki tura mashi sakon sauri yake baison ya makara basai ya shigo part din nan ba."
"Ke rabu dashi koda yake sauri ya biyo ya gaishe ni ko.?"
Muryar shi muka tsinkaya yana fada yana cewa,ke auta shine kika barni a shanye saida kika sa na shigo bayab kinsan i have a meeting in office."
Magana zatayi a tsawace yace.
"Keep quite zan ballaki."
"Enough Samir be a man nice nace tabari saikazo koba komai ai mun gaisa."
"Mami ina sauri dan Allah kibani in wuce."
"Ina kwana Ya Samir?"
Cewar Fatima
Sai a lokacin ya ganmu a cikin falon,nima kallan shi nayi nace.
"Ina kwana."
Baki ɗaya bai amsamu ba saidai kallo daya rakamu matashi ne saidai kuma bazaka ce mashi saurayi ba saboda akalla zaikai shekaru arba'in cif a duniya sanye yake cikin kayan lauyoyi wa'anda suka dace da fatar jikin shi,shima din farine saboda ina lura kaf ya'yan gidan farare kamar mahaifin su,banda Aisha sa take choculate autar Mum kenan.
Murmushi ya sakar mana still bai amsa gaisuwar tamu ba,Mami ce tace......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*

https://chat.whatsapp.com/DGZai5QkoRk3fa6JblTaOq domin shiga group dan samun shi akan lokaci,saidai comment muke bukata🥰


*Noted:- Masoya Alqalami naga sakoninku ta hanya daban daban akan kin posting kullin gaskia abubuwa ne sukai mani yawa,kuma ina posting wani book still duk dashi paid ne,amman insha Allah yanda nai maku alqawali zan cigaba da posting dinshi saidai ba kullin ba son so nike maku*


*Sako* _Amina tana godiya da kaunar ku agareta duk da yanzun akafara labarin koma ince har yanzun bamu dauki hanya ba,ina fata Allah yai mana jagoranci a koda yaushe ameen._


_*Ranakun posting*_

*Monday*
*Wenesday*
*Friday*

*Insha Allahu inna samu sarari zaku samu posting fiye da hakan,sannan inaganin comment saidai ince Allah yabar zumunci🤝🏻*


S1/E 11&12


"Samir lafiyan ka,kuwa ana gaidaka kayi shiru.?"
Nauyayar ajiyar zuciya ya sauke yace.
"Lfy lau,Timo bakuwa akayi.?"
"Eh yar Baba Yusuf ce Amina Caranci."
Jinjina kai yayi yace mani
"Sannunki ya akabaro mutanen gida."
"Alhmdullh."
Na bashi amsa atakaice.
Mami ce ta dauko wayar ta, naga tayi yan latse latsen ta naji tace.
"Tom kada kasa a daureni naturo maka kabari in huta ya halinka ya aikin ka wlh Barrister Samir ka rage naci."
Murmushi yayi yace.
"Mami na, kenan ai aikin mu saida haka yanzun gashi kinbani cikin lokaci da naimaki ta sanyi zakijima baki bani ba."
Dariya suka saka baki dayan su,nikam dai ko murmushi banba dan a wajena banga abin dariya ba,harya juya zai fita ya sake waigowa ya kalleni sosai idanun mu suka sarke dana juna saidai ni banji komai ba dan bai bani tsoron sa Ya Taufiq yake bani murmushi ya sakar mani,nima martani na mayar mashia cewata shidin ya cika sanyin hali,fita yayi yana waving dinmu,wanda Zakiyya ke maida mashi da martani.
Bangama shan mamaki ba saida naga wata budurwa ta sakko daga bisa bene sanye take sa suite bakake sai glass din idonta shima baki tana isowa naga taima Mami dinsu kiss a kumatu ta kalli Fatima tace.
"Ya Mum da auta."
Lafiya lau wai Anty ainasa kin tafi wajen aiki.?"
"Aaa wlh yanzun dai zan fita,wai bakuwa mukayi daga gani yar Mum ce domin tana kama da buzaye."
Tayi maganar cikin sifar zolaya."
"Aikuwa kin canka Anty Fiddausi,sunan ta Amina."
"Sannun ki da zuwa."
"Yawwa ya muka sameku.?"
"Lfy lau."
tana gama fadar haka taima magaifiyar tasu sallama ta tafi tana amsa waya.
"Ni wlh aikin Fiddausi na bani haushi kyaun aikin nan namiji dama itace Lawyer din Samir ne SS dayafi tsari ace yarinya komin dare tana iya fita ankira duty Allah ya kyauta."
"Ameen Mami."
Cewar su Zakiyya.
Nikam ina mamakin kalar boko irin na yan gidan duk da kasancewar baban su babban Sojane Major General Sarki Mukhtar Munzali Kaduna,kuma cikken ɗan boko ne, ya'yan shi takwas ɗakin Mum Taufiq da Tariq ne manyan ya'yan ta sai Fatima sai Aisha autar ta,sai dakin Mami Sajida sai Samir sai Samira suma twins saidai ita tayi aure kuma babbar Lecturer ce a University of Yola kuma Dean Student Affairs ce dayake can take aure,ita kuma Anty Sajida yar Jaridace ta ƙasa da ƙasa wadda yanzun haka tana Malasia da zama sai Zakiyya autar Mami wadda take tsarar Fatima sunyi JSCE.
Nan fa labarin boko ya kaure inda Mami take tambayata ajina nawa nace mata JSCE nayi cikin sakin fuska tace.
"Mi kikeson karanta idan kinyi candy a University.?"
"Inason inyi Medicine."
Wow Doctor kikeson zama kenan kin zama Tariq kenan,kinga ɗan uwanki Taufiq cikakken Arthtector ne amman yanzun kinga ya zama Soja duk da yana bussiesd dinshi amman ba sosai ba."
Murmushi nayi nace.
"Aikam daya cigaba da zanen shi dayafi mashi sojan nan."
"Aikuwa nikam inason inyi Enginearing."
Cewar Fatima.
"Ni kuma Pharmacy."
Inji Zakiyya,kallan su kawai nikeyi dan baki dayan zuriyar Major Sarki Mukhtar bamai karamin karatu ko mai karamin aiki kowa naira ta zauna ajikin shi banda dukiyar mahaifin su wadda baisan adadin taba,cewa nayi.
"Itafa Aisha mi takeson yi."
Dariya suka sakar mani wai nace auta duka duka yarinyar dake JS1 saida sukayi mai isar su sannan Fatima tace.
"Wai tace Ganicology zatayi."
Wow masha Allah gaskia tafiku koba komai zata taimaki rayuwar mata yan uwan ta.
Da haka muka taba fira sannan muka koma sashen Mum,koda muka shiga bedroom dinmu muka wuce nidai ina al'ajabin yanda suka dauki boko kamar ibada tun duniya na kwance.
******Akwana atashi ba wuya wajen lillahi hutun mu yai nisa harna kwashe wata da kwanaki a gidan su Fatima wadda muka shaku sosai dan tsakanin mu d Ya Tariq sosai muke wasa daman sudin abokan wasa nane amman Ya Taufiq kuwa kullin jiya iyau ba wani sauyi bai dariya bare murmushi saidai in anyi abinda yakai makura wajen ban dariya yai murmushin gefen baki yakai karshe wajen murmushi kenan,har kwarani yakan labari dani saidai amsa baifi ya ban ita sau biyu idan yakai makura sau ukku to aranar yayi magana sosai.
*****Bayan sati biyu compound din gidan Major Sarki Mukhtar tamkam yake da sojoji kai kace villa ce sunyi sahusahu kamar masu fareti ga busar su sunayi abin gwanin burgewa Major Taufiq Sarki Mukhtar Munzali ne ya fito da zugar sojoji a bayan shi,jin jiniya data gama karade illahirin unguwar su,wasu kattin motoci ne na sojoji sai kuma Corolla baka dake tsakiyar su suka danno cikin gate din gida sojoji nabin bayan su da gudu haka sukayi parking baifi minti ukku ba wanda ake ma zugar ya fiddo da kafafun shi busa intalot din dake compound din,take suka kame suna sara mashi,sai a lokacin Taufiq ya iso wajen sojan da ake makemawa saidai kana ganin su,kasan mahaifin shine dan kamar su harta baci,sarawa mahaifin nashi yayi yace.
"U re wellcome Sir.!"
Ya ida maganar yana kamewa."
"Major how re u."
Haka yai gaba suna maye mashi baya,cikin katon side dinshi yayi suna take mashi baya,suna zuwa main entrance duk sukaja baya suka tsaya shida Taufiq suka wuce cikin hadadden falon shi.
Basu jima da zama ba su Mum suka shigo suna mashi wellcome,kowacen su tasha adon ta iya haduwa haka suka tari mijin nasu basu jima da zama ba muma muka shigo cikin falon,sumane kawai banba domin duk yanda nike ganin haduwar part din su Mum ashe wasa ne,haka muka zauna bisa carpet muka gaidashi haka yaita wasa da ya'yan nashi sannan ya maido kallan shi kaina yace.
"Masha Allah kice Amin dago angirma ashe yaushe kikazo ya Baban naki.?"
"Lfy lau suke najima da zuwa."
"Sannu ya bakunta koda yake anzama yan gida."
Murmushi kawai nayi mashi.
"Hajia Mufida yaran naku."
Sunanan shigowa."
aikam rufe bakinta keda wuya saiga su Ya Tariq da Samir sun shigo suna zama suka gaishe da Abba haka suke kiran mahaifin nasu,cikin so da kauna ya amsa su,sannan ya kalle su yace.
"Samir,Tariq,Taufiq wannan dawowar danayi inason in shaida maku cewa bansan ku kara wata ukku baku fidda matar aure ba nagaji da zama daku cikin gidan nan kaf dinku ba wanda baida mahalli ba mace daya ba ko huduce zaku iya riketa kunajina."
Shiru sukayi suna kallan mahaifin nasu jin shirun nasu yasa na dago kai ina kallan su,na maida kaina kasa jin su Ya Samir da Tariq sunce ma mahaifin

Please Login or Register in order to submit comment