Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fidda mata da kanshi wanda yake shekara 40 cur a duniya ai ya zaunu da yawa ba iyali,sake ajiyar zuciyar tayi tace.
"Karka damu da'na indai Amina ce kasa aranka tazama matarka daman ance komai lokacine yau gashi nafara jiyo kanshi auren ɗana domin Allah ya tsara maka shi tun kan kazo duniya ta kasa aranka Amina itace uwar ya'yan ka,yau basai gobe ba kafin Abban ku yabar ƙasar zanje in sanar mashi dakaina batareda ɗan aike ba."

Rungumeta Samir yayi kamar wani yaro yanajin wani irin nishadi na ratsa shi tabbas burin shi yagama cika hakanan kwalla suka tarar mashi a ido ya rike hannunta.
"Mami nagode maki kin zama uwa abar kwatance insha Allah daga yau ba za'a kara yimaki kananun maganganu ba akaina wasu sunce aini naki aure saboda ina anfani da kudi ina lalata yaran mutane kowa da abinda yake cewa basu san ba haka abin yakeba komai Qaddararren al'amari kuma komai yariga da ya wanzu rubuce yake bi kawai mukeyi wlh Mami abu guda ke tsaya mani arai har yau na gaza mantawa a cikin dangin ki akwai wadda tace mani insa araina bakin ALQALAMI na ya bushe bazan taba aure ba kawai dan tai mani tayin yarta naki karba,to yau gashi ni dakaina na zaba kuma ina shirin auren Amina in rayu da ita har karshen rayuwa ta.!"

Ya ida maganar idanun shi sunyi jajir kamar garwashi,shafa gefen fuskar shi tayi tana mai tausayin dan nata.
"Wacece wannan Samir.?"
"Ba anfani Mami da zan sanar maki yau a kalla shekara ukku kenan dayin wannan zancen aida nafada maki kawai dai abin ne ya gaza fita raina dan haka muyi facing damuwar mu ta yanda zan mallaki Amina."

"Shikenan Allah yai maka albarka kuma sai inda karfina yakare saika aure Amina wannan alqawali ne Samir."
"Nagode Mami Allah yakara girma da nisan kwana.
"Ameen."


CHARANCI******


Zaune nike cikin House wire dina sai dauki nike zan koma makaranta ba kamar da ba wanda in zan koma ina bakin ciki kamar zan kuka Husna ce ta dauko jikkata ita da kanina Ahmad zasu rakani makaranta mun zama yan SS3 sai murna nike Baba ke tsokanata inda Mama ke mani huduba kada inyi zalinci a school da haka muka tafi sai Kankia.

Muna isa makaranta suka shigar mani da kayana bakin gate,sannan mukayi ban kwana dasu suka tafi ina ɗaga masu hannu.
Da haka har nakai kayana daki na jera a loka muka fita bakin masallaci wajen Amina House shan iska daman zuwa lokacin nanne House dinmu fira aka fara inda rabi da kwata duk akan yanda zamuci uwar yaran makaranta ne inda muke zaune nidasu Shafa,Baby, Maryam da sauran kawayena kowa yana fadin albarkacin bakin shi,kallan su nayi nace.

"Wlh blh bana fatan abani Prefect amman duk da haka sainayi yaga yaga da yaran makarantar nan wahalar da muka sha aibata misaltuwa wai Mama kar indaki ɗan kowa ai wlh saina taka inna tashi."

Hehhehhheh shegiya kawata kice kenan duk jirgi ɗaya ya kasomu,cewar Baby.

Aikam dai damma dai inajin tausayin su kadan."
Tabdijam!kima daina, danni nan wlh hada ido yarinya tayi dani saita raina kanta cewar Shafa.

Dahaka dai kowa yaita fadin albarkacin bakin shi har muka watse nida Shafa muka wuce dakin Momy indo munata kudire kudire aran mu.


Bayan kwana biyu ranar wata laraba akaba mate dinmu shadows saidai duk yan click din mu amma ba kowa banda ni da Baby ne kadai ba'aba ba,ko a jikina dan nasan da abani da kar abani ba abinda zan fasa nacin uwar yara,kwarama abani watakil na raga masu,akan inzama kafin karfi dayaji,ana gama Assembly kowa yai Class har aka kaɗa Break da gudu yaran makaranta sukayi dining duk da set biyu ne ƙasa damu haka akaita mai uwa da wabi akaita dukan yan makaranta hardamu kafi nikam da kawata muna kan yan SS2 sun bugu iya buguwa,labor ce ke cewa.
SS2? Na'am."
Bakuji dan ubanku.?"
Munaji!!.
Banjiba!,munaji."
Haka sukaita ihu suna kiran sunaji ku minene?Rakuma."
Banjiba!"
Haka akaita dukan yara,dan idan ana shadows ba kalar dabbar daba asa mutun ya hada kanshi da ita,dan keta da zalinci haka akaita shadows ba kama hannun yaro zalinci ziryan kai kace ba yan uwan mu bane,kowa burin shi ya rama bugun da akai mashi.

A cikin set dinmu akwai wata Prefect da tazama gagara badau ga dalibai,kuma tanada sama domin ba kadan ta natsar da makarantar ba yanda ya kamata kowa shayin ta yake musamman SS2 data zame masu kamar mala'ikan mutuwa haka take dukan yara ga aiki kafin kice kwabo tasa angama gyare school hatta Pc tanajin dadin aikin ta bata da tsoro ko kadan cikin kankanin lokaci intaga dama ta nitsar da yaran makaranta koda kuwa ita kadai ce,shiyasa kusan aikin makaranta sai sauran prefect su bar mata shi amman bata damuwa,shiyasa GG ba wanda bai santa ba.

Muko bamu da aiki daya wuce na saka yara haya,da wanki ba kalar aikin da bamu sawa.

Akwai wata rana ko sati biyu bamu cike ba ana shadows wata yarinya ce ta shigo case dina na bata wanki ashe data tsoma a ruwa take shanyawa aikam ranar monday ina saka kaya duk sunyi jirwaye koda naje class kasa fita Assembly nayi dan kunyar kaina,ga yan grp din mu sai iskanci sukemani gashi GG munada Yan Day shiyasa kowa bai yarda yatai da datti kodan kada arai naka,haka dai mukaje Assembly muka dawo kamar inyi kuka,muna dawowa Class naje dakin su bata nan haka naita neman yarinyar nan ba alamun ta,har saida aka kwana ukku,rannan naje tankin M.Bala zan dibo ruwa ranar banjin yan daukar hayar kawai sai naganta tana wankin kayan ta,ina zuwa na dauki ruwan botikin na kyara mata ajiki na dinga binta da ruwan bulalai har saida jikin ta yai jini,ina cikin zalinci idona ya kulle M. Bala yazo ya sauda mani reshe na gudu.

"Dan ubanki zalinci ko zaki amsa kira wajen Hajia Rabi dan baki bigi banza ba,ina yabanki sallah ashe kema azzaluma ce,kin biyema 6ukutur kunata iskanci

Mu dayake idan M.Bala yace Bukutur yana nufin masu shigar banza,nikam tunda naji yace saiya kaini wajen Pc sai ido ya raina fata domin nayi hukuncin da bai kamata ba,aikam.na maze ina tunanin ko zai manta washe gari muna zuwa class naji ance Pc na kirana kallan su Baby kawai nike duk na damu,haka naje ina zuwa na iske M.bala da yarinyar nan aiko Pc taiman wankin babban bargo tasa shekare ya bugeni a haukace wata bulalar injita wata kuma tabi hijab,nikam sai wani irin shu'umin kallo nike aika mata na saikin san sauran.

Maganar Pc ce ta razana ni,"Ubanki mutumin kirki ke kinzo kina zalinci wlh yau sai kintafi gida."
Aikam hankali yai masifar tashi bansan nafara kuka ba ina bata hakuri kota yarinyar banbi domin nasan mi zan iske gidan,aikam tai kunnen shaggu dani,tasa Hajia Wayis takaini gida muna zuwa zaure naki shiga cewa take.

"Sai kin shigo wayace kiyi zalinci?!"
Nikam duk na tsure,haka na shigo jin Mama nacewa wacece ku shigo man....
Gani na yasa Mama kin karasa zancen ta,nasha kukana kamar ba gobe.
Wayis ta zayyana mata komai dai dai nan Baba ya shigo yaji abinda nashuka.
Kallona kawai yake nikam na rabe jikin bango kana ganina kaga munafuka.

Baba yaima Hajia godiya yabata kudin mota,ta tafi.
Sadda zai dawo masallaci nafaɗa toilet inajin shi yana ,tana ina tazo tabar mani gidana ni bazan zauna da zalunci a gidana ba tunda ta zama azzaluma.
Nikam sai kuka nike ban komai a bayin amman naki fitowa.

Ganin da gaske yake yasa Mama tafara bashi hakuri sai fada yake yana inbar mashi gidan shi.
Mama tace,infito tinkan dare yai mani inroki yafiyar mahaifina.
Sai lokacin nafito idanuna kamar nama,na duka gaban Baba nafara bashi hakuri,aikam ya mike ya daga hannu zai sharara mani mari ya fasa dayake Baba yana iya shekara goma bai daki da'ba amman bai iya fushi ba,cewa yayi.

Tashi kibar gidan nan idan ina ganin ki zan iya illataki.!"
Da gudu na fita sai gidan su Asma'u ina zuwa na fada jikin Mamar su naita kuka da kyal ta rarrasheni tafara tambaya lafiya.
Nace Baba yace inbar mashi gidan shi
Ranar nan na wuni har Asma'u tadawo makaranta ta iskeni sai kuka nike tai tambyar duniyar nan na kasa bata amsa hakan yasa Maman su taje gidan mu.

Nan fa Mama tagaya mata abinda nayi,hakuri tafaraba Baba daga bisani gidan yabar masu.

Haka tadawo gida taitai mani fada kamar zata dukeni,koda Baban su yadawo baibi takan Baba ba,yaci gaba dayiman nasiha zalinci haramun ne inji tsoron Allah,haka na kwana gidan su Asma'u.

Washe gari Mamar su ta gika mani abinci da miya,Abban su ya maidani makaranta,saida PC takara yiman faɗa sannan ta ansheni na wuce class sukuku har aka tashi haka na kasance banda wani hope na cuta koda kawayena nayi har suka fara cewa na tsorata nazama sakara haka dai na kyalesu nidai nasan abinda na girba.

Ba abinda muke a GG nida Baby saidai mu dauki gayu muna wataya amman ban bugun yaran mutane hayarma saidai ko yan grp din mune suka dauka.
Saima mutinci ke tsakanina da yara ni kaina nayi mamaki saidai ba abin mamaki bane tunda nagane cewa Barno Gabas take haka rayuwa ta kasance a GG gwanin dadi.



*Kaduna*

Hajia Mufida ce......




*Masoyana ku cigaba da nuna man kauna wajen sayen kayiman hallaci farashi mai sauki #300, kiyi man numbers din nan magana 08160508316 sae 0810 836 2334 zakuji yanda zaku biya*




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Comment
And
Vote
❣️



*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*



S1/E 21&22



*Kaduna*


Hajia Mufida ce a side din General Major Sarki Mukhtar Munzali da alama akwai muhimmiyar maganar da take mashi maido kallan shi yayi a gareta yace.

"Inajinki Hajia mike tafe dake.?"
"Ranka shidade maganar ɗanka Samir ne ya taso nazo in shaida maka cewa ya fidda mata."
Murmushi fal a fuskar shi yace.
"Alhmdullh Samir da kanshi ya fidda gaskia naji dadi dan banyi tsammanin zasu fiddaba nadai fada masu ne dan intunatar dasu mahimmancin sa ina jinki wacece kuma wane gari take yanzun nan insanar ma iyayen shi aje anema masa izini bansan a wuce nan da wata ukku."
Kana ganin shi kasan yana cikin farin ciki.

"Amina ce yar gidan Alhaji Yusuf Caranci."
Jinjina kai yayi yana murmushi.
Gaskia ne yarinyar nan tazo mani da haske a gidana gashi cikin ya'yana harna samu wanda ya yarda zai zaman aure da ita gaskia naji dadin hakan ai abu yazo gida saboda Yusuf ɗan uwana zan iya kiran shi tunda ina auren Yayar shi,dan haka kice yasama ranshi yagama auren Amina,ada ina zatan bakin alqalami ya bushe ya'yana kamar sunyi ban kwana da aure ashe komi lokacine Allah nagode maka yanzun saura Taufiq da Tariq nike jira daman Mahmud yaje ya gaida iyayen Fiddausi sauran yan uwanta nike jira su fidda ayi bikin su baki ɗaya,kuma Allah yarda yanzun saura Hassan da Hussein suma Allah ya hadasu dana kwarai."
"Ameen cewar Mami.
Da haka suka taba fira ta koma side dinta cikeda jin dadi.

A gidan su Amina kuwa koda Baba ya dawo bai gantaba ko damuwa baiba bare ya tambayeta haka yaita rayuwar shi Mama nason ta gaya mashi Abban su Asma'u ya maidata amman takasa tana shakkar sake tarar shi da maganar,gashi yana fishi akan lamarin kuma saura sati biyu ai masu visting taga bai fara hada mata kayan Visting ba wanda tun kafin irin wannan lokacin yagama hada mata komai lokaci kawai ake jira amman ya fita harkar ta kwata kwata hakan ya dagama Mama hankali amman tasa ido saidai tana zulumi kada ya burkuce mata tasan bai iya fushi ba.


Mum Pov.

Bayan kwana biyu Mum ce da Abba a sashen ta yazo dubata tayi zazzabi suna zaune a falo yace.
"Hajia Maryam banji daga bakin kiba dangane da yaran nan akan fidda mata kinga Samir ya fidda tashi su nike jira."
Murmushi tayi tace

Aikam naji dadi da Samir ya fidda Allah yasa alkhairi,amman Hassan ya fidda nasa yaga maka dayake wannan zazzabin shiya hanani zuwa in sanar maka."

Kai amman dai naji dadi Allah yaima yaran nan albarka yadda suka faranta mani Allah ya faran ta masu,yar wacece ya fidda Allah yasa gidan mutunci yaje kamar yanda Samir ya samu gidan mutunci."
Ameen inasan ran gidan mutunci ne domin yar gidan Alhaji Manga Malali ce."
Gaskia kam Baban ta aiba boyayye bane mutumin kirkine Alqali nasan shi Allah yasa albarka."
Ameen Alhaji,to wacece Samir ya fidda haka naga kana farin ciki sosai."
Murmushi yakara saki yace.
"Kwarai kuwa dole inji dadi sai kuma yanzun dadin ya kara lunkuwa da naji zaben da Tariq yayi ba kowa bace sai Yarki Amina."
Da Mum ta dan kwantar da kanta bisa kushin sai ta dago tace.
"Wace yar tawa kainafa ya kulle."
"Haba Maryam akan mi kanki zai kulle bayan kema kinsan baki da yar da zai gani yace yana so bayan Amina taki yar gidan Alhaji Yusuf."

Tashi tayi zaune take idanun ta suka rine tace.
"Aaa Alhaji bai yuyuwa."
Mikewa yayi yana mata kallan kinyi kadan yace.
"Minene hujjar ki.?"
"Domin Taufiq ya gaya mani Amina yakeso kuma ita zai aura amman baisan kowa ya sani sai tagama karatun ta sannan."

"Aikin banza aikin wofi aikam yai ma kanshi da bai fito ya sanar mani ba har ɗan uwan shi ya riga shi dan haka ki gaya mashi ni uban shi Mukhtar Munzali nace bakin alqalami yariga da ya bushe ya nemo wata amman Amina Samir ya riga shi kuma shi taza aura.!"
Haba Alhaji ya kake yanke hukunci irin wannan bayan Taufiq ya riga sonta tun tana garin nan fa shekara kusan ta ukku kenan.!"

Ai shiyasa nace ko zasu kara shekara goma ni bazan kara masu maganar aureba tunda ni kaina bansan wannan tanawa bace,yanzun Allah yasa sun fidda shekarar Samir nawa kika sani shekara biyu yaba su Taufiq idan ya rasa Amina mikike tsammani.!?"
"Alhaji banki ta takaba da ace Taufiq bai ciki koni maima Samir jagorana koma ince na bashi Amina amman kaduba kaga wata kusar tafi wata."

Kee! Hajia Maryam ki.kiyayeni ko in saba maki ya'yana duk daya suke gareni koda ace Taufiq yaga yar Mufida yana so kuma ya riga Samir fada wlh dole ne yabar ma Taufiq dan haka nagama magana goben ma Hamza da Khalil zasuce nemawa Samir auren Amina dan haka ki adana kalaman ki.!"
Sakarcin banza da wofi!"
Zatayi magana Tariq dayazo shigowa yaji zancen iyayen nashi ya gyada mata kai alamun tayi shiru haka Major ya juya ranshi bace Tariq na gaida shi kota kanshi baiba yai side din shi.

Itako fadawa tayi bisa kushin tana maida iska mai zafi,shigowa Tariq yai sukai jugum jugum suna al'ajabi taya zasu bullowa lamarin.
Musamman Tariq yanda yasan Taufiq yai nisa akan son Amina tun ranar daya aza idon shi akan ta daga ranar sonta ya darsu a cikin zuciyar shi harya tabbatar da hakan da kanshi to yanzun taya zasu fara gaya mashi maganar Abba,idan yadawo kasar yaje U.K yin wani course da taraining da wasu sojoji kuma ya shaida ma Tariq yana dawowa da kanshi zaije ya sanar ma Abba tunda yana lissafi yanzun Amina tana SS3 takusa candy kullin da haka yake kwana yana tashi wannan kenan.


Amina Pov


Sosai nike rayuwa ta cikin farin ciki ban shiga harkar kowa saidai in za'aje Hausa Club nakanje idan ana rawa ta yan makaranta innaga dama inyi in banga damaba inzama yar kallo wanibi haka zakiga daga waka sai ta juye akoma yar habaici tsakanin juna musamman lovers din dasukayi faɗa ko akaima mutun raybol wannan situation din nasakani nishadi dan kasha dariya musamman idan ana bada zoben promise kai rayuwar makaranta akwai dadi a cikin ta danko in kinada lover kinsha kayan entertaiment ko ince gift haka za'a hado maki su biscuit choculate da kayan dadi lover tabada akawo maki haka rayuwa ta kasance a GG hankalina kwance banda wata damuwa.


Bayan sati biyu ranar ta kama ake Visting aikam na dauki wanka iya wanka duk da pink ne ajikina amman sun mani kyau matuka, ban fito filin visting sai karfe biyu dayake mune manya inba duty master yazo korar muba ba ruwan mu da takurar Prefect saidai su koro yara,haka naje filin Visting inata duba yan gidan mu,amman basu ba alamun su harna fara karaya lokacin 2009 ne akwai waya kuma ba laifi tafara wadatuwa ba kamar daba da muna JS1 ba hakan yasa na ari waya nakira Mama saida tayi 2miscall ta daga.
Mama nice kikira."
Shine abinda taji nace aikam takirani ina zumudi na daga saidai dagajin muryarta kasan ko batai kuka ba tabbas jikinta yai sanyi a kiɗime nace.
"Lafiya Mama naji muryan ki ta sauya."
Bakomai kiy hakuri bazanzo maki Visting ba Baban ku ya hana yace zalincin ki ya baki abinda kikeso,dan haka kinemi numbar shi kinemi afuwar shi kuma kinga abinda zalinci ya jawo maki."
tana gama fadar haka ta yanke wayarta aiban bi ta Juniors din dake gefen muba na kwalla uwar kara ina kuka mate dinmu sukayi kaina,sunsama wani mugun abin naji ko mutuwa haka sukaita tambayata nakasa magana sai Baba nike kira hankalin kowa ya tashi haka na kira Baba yana dagawa muryata na rawa nace.
"Baba dan Allah kayi hakuri ka kira nice Amina."
Saida sukaji nace haka sannan sukasan ba mutuwa akai mani ba, shiru baba yakirani amman yaki naitai mashi flasing harya gaji yakirani ina dauka nakasa magana sai kuka nike.

"Baba kayafe mani bazan kara bugun kowa ba."

"Indai wadda kika buga tayafe maki nima nayafe maki kije kinemi afuwar ta."
Ɗit ya kashe wayar shi da ido nabi wayar sai hawaye nike mikama mai waya nayi natafi inata kuka wajen SS2 naje ina kwalla.nakirata tana zuwa ta duka na tarota bansan na rungume taba ina kuka gashi nakasa magana da kyal na saketa ina goge kwalla nace.
"Dan Allah Hafsat kiyafe mani dukan danai maki a kwanakin baya nasan na zalince ki."
Yanda taga ina kuka ya karya mata zuciya tace.
"Bakomai Yaya Amina nayafe maki duniya da lahira kidaina damuwa ai rayuwar makaranta ta gaji haka nayafe."
Ba kadan naji dadiba haka nai mata godiya natafi nakara arar waya baba na dauka nace tayafe mani."
Kiramani ita kibata waya.
Haka kuwa akayi saida na kirata sannan Baba yakara bata hakuri kuma yace daga yanzun nazama Yayar ta sannan yai mani sallama inasan in tambaye shi Visting inajin tsoro.
Tun daga ranar nakara tsorata da lamarin Baban mu lallai bai iya fushi ba dole insan yanda zan dinga binshi sau da kafa a rayuwata.

Banfi minti goma da gama kuka naba saiga su Asma'u da kannenta sunzo mani Visting Abban su ya hado mani komai kaya niki niki haka akazo mani ina ganin su na barke da kuka inacewa.
"Baba ya hanasu Zainab zuwa Asma'u yai fushi dani."
Da kyal tabani hakuri taci gaba dacewa.
"Shiyasa Abba yace muzo maki kidaina kuka kinsan Baba bai iya fushi ba,ranar da kyal Asma'u ta iya rarrashina idanuna kuwa sunyi Ja inaga ranar ba mate ba hatta imidiate sunsan nasha kuka.mate ko cewa suke girmana ta zube nayi kuka gaban juniors kuma dan lalacewa har rokon Hafsat yafiya saida nayi gaskia na bata masu record nikan basusan abinda ba fuskanta bane shiyasa surutun su bai damuna.

Ranar kuwa sukuku haka nike hatta Asma'u jefi jefi muke yar fira hankalina na gidan mu baki ɗaya.
Ina zaune Mashi tazo tace ana kirana bakin gate wani Babba ne."
Take naji gabana ya yanke ya fadi gashi sai cewa ake Amina Yusuf Charanci,jikina sage na mike kamar wadda kwai ya fashemawa aciki natafi hakama Husna ganin banda kuzari yasa tabiyo bayana tafiya nike a hankali,ina zuwa wajen duty master naga ya nuna yatsan sa yace ga mai kiran ki can,waigawa nayi saidai kirjina da zuciya ta kamar zasu diro ƙasa dan tsoro da al'ajabi daya rufeni.

**********Ranar data kasance nayi ban kwana da duk wani farin cikina ranar da idanun mu suka sarke dana juna zuciya tana bugawa da sauri sauri ranar da hawayen idanuna suka dinga kwarara har zuwa yanzun da suka ƙafe itace ranar da bazan taba mantawa ba arayuwa ta,kuma itace ranar da take asalin bada wannan labarin nawa komai yafaru tanada sila atare dani domin ta haifar man da kalubale iri iri tun inada shekara sha bakwai, lallai kam komi rubutaccen al'amiri ne alqalami ya kafe domin komi ya gama wanzuwa,haka zuciya ta tsinke nakasa sauke idanuna akan shi kuma nagaza tafiya kuzarina ya kare shima ni yake kallo na tabbata shi kadai yasan yanda yakeji a cikin ranshi,a hankali na dinga takawa zuwa wajen shi duk da fuskar shi atamke take kamar kullin saidai tsoron yanayin shi ya darsu araina Ya Taufiq ne zaune cikin shadda coffee saidai ba alamar annuri a ranshi harna isa gaban shi ya kafeni da idanu ko keftawa baiyi saidai nina sauke nawa kallan akan shi,ina zuwa na duka gefen shi muryata na rabewa nace.
"Sannu da zuwa Ya Taufiq ina wuni."
Shiru yayi yana kallona domin kuwa yasan ina cikin damuwa."
"Minal."
Samun kaina nayi da dagowa na aza jajayen idanuna akan shi.
"Mi akai maki kikai kuka.?"
Ya ida maganar dagaji cikin damuwa yai mani tambayar saidai gano hakan a fuskar shi tabbas ba karamin abu bane domin ko yaushe bai fiye murmushi ba."
"Bakomai."
Shiru ya sakeyi saidai aikin kallona dayake yi."

"Baba ne ya hana su Mama zuwar mata visting,cewar Asma'u data kafe Ya Taufiq da kallo tana nazarin shi."
Waigowa yayi yai mata kallo ɗaya ya janye idon shi ya maidasu kaina.
"Yanzun dan Abba yahana su Umma zuwa shine kike kuka to gashi ni Yayan ki nazo maki dan Allah kidaina kukan nan Minal."
Tsintar kaina nayi da goge kwallana nace.
"Nadaina,ya hanya dasu Mum Ya Taufiq."
"Lfy."
Shiru mukayi kowa ya rasa abin cewa saidai inajin idanun shi akaina duk nafara takura inaganin shi ta gefen ido ya duba agogon hannun shi dagowar da zaiyi karaf idanun mu suka sarke dana juna yace.
"I went go,ga kayan visting din ki nan zantafi ki maida hankali kiyi karatu,ai kinason kici gaba da karatu ko?
Gyada mashi kai nayi bance komai ba duk da yagane amsata sai cewa yayi.
Ko aure kikeso muyi maki."
"Aaa nace kalmom na hardewa."
Good girl kada ki kuskura ki kula samari kinji ko.?"
Eh naji."
"Okay bye ki kula da kanki."
Tom kagaida mani Mum da Fatash."
"Zasuji."
Da haka Ya Taufiq ya fita yahau motar shi yatafi.
Haka na dauki kaya niki niki nida Asma'u,muka tafi.

kawaye na da suka ga Ya Taufiq tun shigowar shi sai santin shi suke wai suna son Yayana nikam saidai nai masu dariya nace an saka mashi biki dan azatona kenan nasan yai aure zuwa yanzun,haka sukai tajin haushi wai sunyi loosing,da haka Asma'u ta tayani kai kayana tsororya hanani saka yara sukai mani kayana hostel bansan na zama azzaluma haka muka jera kaya masu yawa su sardine lemuna complex kayan tea da dubu Ukku ya saka mani nayi murna sosai.

Siko Ya Taufiq koda ya fita gidan mu ya wuce akai sa'a yasamu Baba,sosai suka karrama shi nan yake ba Baba hakuri yai mamaki saida ya tambaye shi yace ai daga kano da jirgi ya sauke shi Air port shine yazo mani Visting yau dinma kano zai wuce gobe zai tafi Kaduna,godiya Baba yai mashi akan dawainiya da yayi yace.
Bakomai da haka yaci abincin da Mama takawo mashi da yamma likis ya wuce kano inda ya sauka gidan Yayan Baba ya zauna kafin gobe ya daga zuwa kaduna.

Nikuwa koda visting ya watse haka mukaci gaba da rayuwar mu cikin aminci saidai baki ɗaya lamarin jiya na raina da yanda Ya Taufiq ya zomani visting fa kallan daya dinga yimani ammab nagaza gane na menene kuma minene ma'anar shi.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Comment
And
Vote
❣️


*_ALQALAMI🖊️_*


*Na*


_Yar Mutan Kankia❣️_


_*TRUE LIFE STORY!*_


_THE STORY LIFE OF AMINA🥰_

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI._*



S1/E 23&24


Taufiq Pov


"Abba ai tuni nace maka lokaci zai sanar daku kuma gashi yazo naga Amina yarinya ce shiyasa nabar maganar araina sai yanzun in sanar maka."

Wani irin kallo Major ke aikama Taufiq.
"Kai Hussein ni ba yaro bane ba yanda za'ayi ace saida ɗan uwan ka yace yanasan Amina sannan kai zaka wanko kafa kace mani ita kake so,kafita daga idona in rufe.!"

Shiru yayi banda tsabagen bacin rai ba abinda ke dawainiya da Taufiq har kanshi ke sara mashi,ba abinda zuciyar shi ke hakaito mashi irin Minal da yanda yabarta a makaranta baiji zai iya barin ta.

Magana zaiyi yaji maganar Mami.
"Taya zasu samu kwanciyar hankali ai tunda Samir yace yana son Amina shikenan hatta uwar shi haushi takeji dan ba yanda zatayi."

Dakata Hajia Mufida bance kizo mani da wannan sakarkarun maganganun naki ba kamar ya jin haushi kinga kada kuzo kuraba mani kan ya'yana ni duk daya suke a

Please Login or Register in order to submit comment