Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

chan gefe ana kashe mata hoto, Kallonta yakeyi cike da so da k'auna, ya shagala da kallonta sai ji yayi Me daukar hoton tace"The Groom is here, come over here" Hankalin Seebi ya koma kan Rafeeq, gani yakeyi Yafi ko wa Dace tunda yana da Seebi, itama hakan ne, don yau ya mta kyau matuk'a, a hankali ya taka har gunta yana mata kallo kasa kasa, ta sadda kanta k'asa ya sa hannun shi ya dago fuskarta ya kai bskinshi kan kumatun ta ysyi kissing a hankali, daburcewa tayi Lokaci guda ya sa hanayenshi duka hya ya rike kafadunta, idonta a runtse ta bude su a hankali, Cikin muryar rada yace "Calm down baby, i got you" Me hoto tace "Oya Romeo Shall we?" kao Kawai ya gyada mata, nana aka fara kashe musu hotuna kala kala.

8:10pm
Ko wacce ta samu gurinta a Mota, Motoci aka kawo sun fi 20, yawancin Manyan duk sun tafi, Mami da Aminanta sun wuce, yanmatan ne dama suka rage, Rafeeq da Seebi a bayan Motar Uncle Zaid, Miemee da Maalesh a gaban Motar, Usheey na motar wani friend din su Maalesh Faisal, tun farkon biki suka hade, kuma da alamu suna son junan su,
Nene ta shigo gidan, Da sauri tana murnan ga motoci nan basu tafo ba, dama sai da ta tabbatar ta sallami kowa a gidanta kafin ta fito, Daga dan Nesa ya hangota, a zuciyar shi yace "Neh-neh? ina take tunanin zata?" wata zuciya tace "Dinner"da sauri ya girgiza kai, In har ka bari Matar nan taje Dinner dinnan, to sunan ka sorry, zata kwafsa maka, ta bada kai gaban Friends dinka, zata ba ka kunya gaban Manya mutane, you have to stop her from coming, unless yiur name will turn to Apology" gargadin da zuciyarsa ke ma sa kenan, da sauri ya bude k'ofa yace "i'll be right back ya fice" ba su lura da ita ba, da sauri ya tare ta, ta yashe baki "Ahh su dunkum da manya kaya, ka ga kyan da kayi?" yayi Murmushin yak'e yace "ban Kai ki ba" Nene akaji dadi tace "Allah ko? Ni naga k'auna, ga motoci nan bari in dirje In shiga"Da sauri Feeq yace "No No Neh-neh, Mami tace " ki tafi mata da wasu kaya" Nene tace wasu kaya kuma dunkum?" ko dar yace ina jin kayan da zata raba wa mutane ne" suna ina? Yace Suna daki, kaje ka dauko min kar a tafi a barni" yace "wa zai tafi ya barki, ke ke da Ango" Nene ta ji dadi tace muje mu kwaso, suka jufa hanyar dakin Rafeeq, Rafeeq ya bude dakin shi, Nene ta shiga tace "ina kayan suke?" yace duba kewaye, aiko tana shiga yayi saurin fita ya sa Mukulli ya kulle K'ofar, ba ta lura ba illa ma cewa take "Ina kayan suke dunkum?" yana fita ya ma motovin gaban gida Signal da su fara tafia, aiko duka motoci suka kumna Motar su, da sauri ya hau tasu, Maalesh ya tada Motar suka bar haraban gidan fuk suna masu kunna fitilar motocin su, abun za kyau Convoy din ya hadu.
Haka su ka wuce NYSC hall, inda a Nan ne zaayi Dinner.
*******
"Bara'uba Salatin gwarawa" cewar Nene da ta fuskanci Dunkum ya kulleta a Dakinshi.
****
A Convoy suka isa har NYSC camp Hall, suna isa Maalesh ya kira Mom dinsa yace sun iso, Mom din ta sanar da MC Lubna Sufyan, nan MC ta buk'aci kowa da ya mik'e tsaye don shigowar Amare. Dj ne da Makadi(Mai Asharalle) nan da nan DJ ya sa wak'ar Nura M Inuwa na Amarya, Mom ta fita ta hada kan Amaren, Layi ne biyu, daya dogo na mata, daya na maza, in twos zaa shiga, Feeq da Seebi a tsakiya, ofcourse Miemee ce a gefen Maalesh su ne a gaba, Ushee kuma da Faisal a bayan su, Maalesh yayi kyau sosai, kayan shigen na Rafeeq ya sa, Abokan Ango Masu jiji da kai, duk ba zasu wuce shekarun Rafeeq ba, sai shan k'amshi sukeyi, ko don sun ga suna da kyau sun hadu ne oho, Kawayen Amarya kuwan sun sha kyau sun gaji, Anko suka yi na wani atamfa mai touches din Ja, sun daura Head Ja, ga kuma Amarya da Ango sunyi turquoise blue abun duk sai ya bada color, Mom tace da Miemee oya Yarinya na ku fara shiga da taku kunji?ta kashe ma Maalesh ido, nan suka fara taku sukayi hall din, aiko sauran suka bisu a baya, Fuskar Rafeeq ba yabo ba fallasa, shidai ba Murmushi yake ba, shi kuma ba daure fuska yayi ba, Suna shiga hall din Gaban Seebi ya fadi, ganin haduwar Hall din, ga Idon Mutane kan su, Hall din babba Ne kuma cike yake Mak'il, Rafeeq ya lura da ita, a hankali ya sak'alo hannun shi cikin nata, dumin hannun shi kawai taji a nata, da sauri ta kalleshi tare, ya kashe mata ido, a hankali yace "I got you" idonta ya kai kan Ummi, Mami Abbii da Daddy a chan gaba, duk kunya ya lullubeta, Zata zame hannunta Rafeeq ya matse hannun, ya ja ta suka cigaba da tafia har sai da sukaje suka zauna wurin da aka tanada domin su, kafin aka fara gudanar da Shirye shirye, Daddyn Maalesh aka bukata don bude taro da Addua, Alhaji Habib ya zo yayi Welcome Speech(Sannu da zuwa), sannan aka bukaci Baban Abokin Ango da K'awar Amarya su fito don bada takaicecen tarihin Ma'auratan, Muhawara ya kaure tsakanin Miemee da Ushee, Miemee tace "Oya Ushee tashi jeki yi Jawabi kan Amarya" Ushee tace "Tabdi, kinsan dai bazan iya magana gaban crowd ba, ai ke zakiyi, so kije dont waste time"Miemee ta harareta tace "don ace baki da hayaniya ko?" sukayi daria, Maalesh ya taso ya zo kusa da Miemee, suka jera sukayi kan Stage din a tare, abun sai ya burge Mutane.
Maalesh ya fara magana; "My name is Mahmud Ali Umar, and Rafeeq is a brother from another Mother, we've been together for 20years, Rafeeq is a•••••••• nan Maalesh ya shiga koda Rafeeq tare da mai Fatan Alheri, Rafeeq ya taso ya rungume Maalesh tare da bubbuga bayan sa ya rada mai a kunne "thank you brother".
Miemee ta fara bada bayani kan Seebi, ta fadi kyawawan halaiyarta ta kare da mata fatan Alheri" aka tafa musu, MC tace kafin su tafi sai sun taka rawa, nan Surajo mai Maalesh ya fara wak'e Malesh babban aboki, da Maryam Miemee yar gayu, sin dan taka zasu koma MC tace da su "Are you a couple?" Maalesh yace "yeah we are" tace "You suit eachother" sukayi Murmushi aka tafa musu suka koma mazaunin su.
Aka gayyaci Ango da Amarya a fili, Marok'i sai kirari yake ma Ango, Mom ta hau sama don Rafeeq da Seebi sunki tashi, Ita kunya, shi kuma be son hayaniya, sai da Mom ta je ta sauko dasu, Wannan karon karon Dj ne, Wak'ar Work-Rihanna ft Drake aka samu su, dukkansu tsaye sukayi, ba me rawa, Mom ta rada ma Feeq a kunne Spray her, Ta wuce ta zauna aka barsu su kadai a fili, hannu ya sa cikin Aljihu, ya ciro bandir din1k ya fara lik'a mata, kanta a k'asa, ya dinga spraying, Yana mata liki'i, nan Daddy da Abokansa suka zo suka lik'a musu kudade masu yawa, gajiya Rafeeq yayi, ya kama hannun matarsa ya ja ta suka koma mazaunin su, nan aka ba Abokan Ango da Kawayen Amare fili suyi rawa.

Tagumi ta rafka hannu bibiyu tana tunanin irin dukan da zata ma dunkum idan ta samu ta fito, ita zai ci ma fuska? Don kar taje lanchin (luncheon)din shine zai kulle ta don bakin hali. Agogon dakin ta daga kai ta kall 9:15, ji tayi ana bude k'ofar dakin da Mukuli, da sauri ta mik'e ta la6e bayan labule don yau watan cin uban Dunkum ne ya shigo, fitowa tayi daga Bayan labule tace "Zaidu bawan Allah, kaine anan bakaje gun patin ba?" da mamaki yace "Nene, me kikeyi anan?" tace "ba wannan shegen yaron bane ya kulle ni a dakin don ya tsane ni, wai don kar inje partyn" Zaid yace "Wa kenan?" cikin fada Nene tace "Wa fa banda fitsararen Danka Dunkum" Zaid yace "shi Rafeeq din ya kulle ki? Saboda me to?" tace "Af Sabida ya tsanan mana" "aa Nene ki bar cewa Haka, bari in dauki abu mu tafi" ta yi Murmushi tace "Yawwa Zaidu Bawan Allah" da sauri Zaid ya bude Wardrobe ya ciro wata Envelop yace "muje Nenenmu, kai Nenen mu kinyi kyau wallahi" dadi kashe Nene tayi ihun murna tare da juyi tace "Ai nasani wallahi, kaima kayi kyau Sosai dama Zainabu ta na nan sa ta ganka" yana tafiya tana bin shi a baya yace "ai ta ganni" tace "ta ina? Ko ta zo ne? Yace " Aa Wallahi, ta Video Call, itama ta sa na makara" Nene tace "Miye Bidi'o kwal?" suka shiga Mota Zaid ya fara mata bayanin Video Call.

Yanzu lokaci ne na Nishadi(Entertainment) inda aka gayyaci Baban Cinedu da Baba Ari su fito don sa Mutane Nishadi, Baba Ari ya fito ya amsa Mike ya dinga Ma Feeq Ango kirari, ya dinga zazzafo zance, har gaban Feeq yaje ya na surutai, cikin Muryar shi yace Ango Rafeeq ka sha k'amshi, me zaka ce game da wannan Rana? Ya sa mai Microphone din daidai bakin shi, kamar ba zaiyi magana ba, chan kuma sai yace "Kana da Hayaniya" aiko duka hall din aka kwashe da daria. Baba Ari yace "Abun yazo inji me tsoron wanka, Amarya Nasiba, sai kin yi dagaske don Mijin naki, erhm erhm... Aka sake kwashewa da daria banda Rafeeq da ya murtuk'e fuska, Naseebah ta kalleshi ta sake daria, ya sa hannu ya tsinguleta tayi dan ihu me k'ara.
Yana daga ido idonshi ya kai kan Nene da Uncle Zaid baki bude a hankali yace "Akwai Damuwa" bacin ran Nene duk ya 6ace data ga Tsaruwar Hall din, da manyan Mutane da ke ciki, Ihu ta hada da Shewa da ta ga haduwar da Seebi da Feeq sukayi, ai da sauri ta k'arasa gunsu, tana washe Baki, Seebi ta mik'e ta rungume Nene, ta fara kwalllar farinciki, Nene ta bude baki tace "kwalliyar dubu dari da hamsin din zaki jika da hawaye? Maza Share hawayenki, ina nan tare dake" ta kalli Rafeeq tana mai Murmushi don ya mata kyaun da be taba ba, da tuno Abun da ya mata nan da nan ta galla mai harara. Mai hoto da gurbataciyar Hausarta tace "Mama siya a maka photo" Nan Nen ta pose aka fara kashe mata hoto, Nene har da rike su K'ugu duk Cikin style, sannan ta tunkude Feeq ta zauna a tsakiyar su aka musu hoto, har da dundu ta sakar mai ta baya ba tare sa Seebi ta gani ba, takaici ya hana shi Motsi.
Muryar Uncle Zaid ta kauraye hall, din inda yake ba Amarya da Ango Shawara yana musu Nasiha, Nene taji wani dadi, da sauri ta bar gunsu Seebi ta k'arasa gun Uncle Zaid, cewa take "Zaidu Bawan Allah ka bani abun maganar nima nayi".
"Assalam Alaikum jama'a, sunana Aminene Mamman" Rafeeq ya dafe kanshi da hanayenshi biyu cike da takaici, a hankali yace "Lord of Mercy! what is this crazy Woman doing?" Seebi ta dan rankwafo a hankali tace "Baby its your day, be happy dont be Sad" Murmushi yayi yace "Ina sonki kinji?" Murmushi kawai tayi, Nene ta cigaba da cewa "shekaru na Sittin da dori nice kakar Amarya wato Seebi, duk da wasu ba su so na zo gun nan ba, har kulle ni sukayi a cikin daki, toh Da yake ta Allah ba tasu ba, sai gani a cikin Fillin nan, hantar su sai ta fashe" ta karasge tana me hararar Rafeeq, shiko Murtuk ya dauke annurin fuskar shi, Nene ta cigaba da Surutan ta karshe ta Ma Maauranta Addua da fatan Zama lafiya, nan da nan hall ya kachame da tafi, da yawa Nene ta burgesu ta basu daria. Dj ya sa mata wak'a, tace "kai ni rabani da wannan wakar kafiran" Surajo kada min molimoli, aiko kamar jira surajo mai asharalle yake, suka fara kidi, Nan Nene ta fara taka rawar Moli Moli, nan da nan wuri ya kachame da tafi, Abii dai dafe kanshi yayi yana tunanin yaushe Nene zata bar abubuwan ta. Nene ta burge kowa, wani Abokin Daddy yace da Daddy i like this woman, this is what we call Entertainment" don shi a ganinshi Nene yar wasan kwaikwayo ce aka gayyato.
A tare suka Yanka Hadadden Cake din da Ummu Sudais ta Musu, cikin kunya Seebi ta sa mai a baki, shima ya guntula ya sa ma ta, nan aka hau tafi.
Dance! Dance! Dance, na Tsakiyar hall ta kacame da rawa, Yan Asharalle suyi, Dj yayi, dukkansu suna ta nuja tasu basirar, Rawa ko Nene kamar ta karya k'ugiu, lik'e kam anyi, an Watsar da kudi, (nima biebeen ku da na ga haka sai na fara rawa ina kaiwa k'asa kasa ina tsince yan dubu dubu dinnan, ban ankara ba naji Nene ta take min hannu).
Daga nan kuma aka hau Refreshment, wato cin Abincin dinner din, Babu ne kawai babu cikin kayan Abincin. Nan akayi serving kowa, Kowa ya ci ya sha. Nene tace tabb"Amma Dunkum yaso in tafka asara, da bani zaayi wannan shagalin, toh Allah ya tsare ni dai daga minahuncin shi, shege sai kyau kamar shi yayi kanshi" na kusa da ita suka tuntsire da daria, Abinci ake taci, Naga Yan Zauren Biebee Isa sai cin abinci suke, wasu har da kullewa a cikin tissue lols, Rafeeq kuwa wurin ya ishe shi, so yake kawai ya ganshi a gida, ya gaji da rawa ya gaji da hayaniyar gun. Fuska ya ma Uncle Zaid, Uncle Zaid ya bashi hakuri ta ido.
Haka taro ya tashi Lafiya, Komai yayi daidia, abun sai wanda ya gani, abun sai san barka. Sai fatan Allah ba Maauranta zaman lafiya.

Da Asuba Zaid da Rafeeq sun dade suna Magana, Sosai yake mai fada, da Nasiha, Rafeeq yayi Murmushi yace "Uncle Zee, you dont have to worry about anything, i love Baby so much, i wont hurt her, i assure you that" Zaid ya ja kunnen Rafeeq yace "In my presence her name Is Nasiba, idan a bayan idona call her anything in kaso ka kirata da Jaririya ba Baby ba" daria Rafeeq yayi yace "Are You Jealous?" Zaid ya tabe baki yace "Ina da Zainab din?" Rafeeq yayi daria. Alhaji Habib ya shigo, bayan gaisuwa Zaid yace "Yaya yanzu fa zan wuce Kaduna" 'Ba ka bari sai Gobe?" da sauri Zaid yace "Tab" Alhaji Habib yayi daria yace "toh kai wani Gida ka zaban ma dan naka? Gwara tun wuri a je a gyara ayi furnishing ya dauki matar shi su koma chan" Zaid yace "Yaya Akwai dan shirin da nake musu, nan da lokaci kadan zakaji" "Alright" inji Alhaji Habib, Suka fice, Uncle Zaid yace da Rafeeq "kai kuma kayi ma Seebin magana, in ta amince to, in bata amince ba sai kuje ku dawo, duk dai yanda kukayi sai ka sanar dani" Ya rungume shi yace "Thank you, You are the best" "shuttup boy" sukayi daria, tare suka hau sama wurin Mami Uncle Zaid ya mata Sallama, ya ma Seebi da Aneesa Sallama, ya wuce Gidan Nene ya mata Sallama, ta mai Addua Sosai, ya dauki Abii da Ummi da Anan suka wuce Kaduna.
A yau Lahadi yan Nesa suka koma garinsu, yan biki aka watse. Nene ta tarkata ta koma Gidan Lema don kwana daya da tayi ba Seebi duk sai ta ji ba dadi Sabo turken Wawa.
Karfe tara na dare taji sak'o ya shigo wayarta, ta bude "Baby, I'm hungry" ta kalli Nene da ta bude baki sai surutu take mata tana bata labarin 'yan biki" ta dan muskuta, ta mik'e tace "Nene ina zuwa" Nene ta tsuke fuska tace "ina zaki da daren nan?" "Hamma zan dafa ma Indomie" Nene ta tabe baki tace "Ke Seebi ki fita idona, ke baki iya dan jan ajin nan ba, Miji ya kiraki jiki na rawa zaki kai kanki, tun kafin ki tare, wayace miki haka akeyi?" Seebi ta bude baki cike da Mamakin Nene, tace "Nene meye haka kike fada?Yunwa fa yakeji? Meye laifi don zan kai mai Abinci? Ai mijina ne ko?" Nene ta bude baki "Ehh lallai Seebi wuyan ki ya isa yanka, idon ki ya fedare, ke kin auri Dunkum, zaki gayan magana ke me Miji, ke dadi Miji, ke danubanki Mutunci nake neman miki" Wayar ta ya sake Ringing din, da sauri tayi hanyar k'ofa tace "Ni abinci nace zan kai mai ba wani abu ba" Nene ta daga murya tace "Ke kika sani, indai Dunkum ne gaki gashi". Kitchen ta wuce, tana shiga ta hango SlicedBread, tace " Yauwa" Ta bude fridge ta dauko Sardines da butter, da bama ta hade su gu guda, a gurguje ta shafa ma bread dinnan tayi toasting guda 4, ta Zuba mai Pepper Chicken din da ta ganj a cooler ta ciro Kwalin Exoctic a fridge ta sa a tray da Cup tayi k'asa dakin Rafeeq, a k'ofar Dakin tayi Sallama.
Bude wa yayi ta shiga da tray din kanta a k'asa, Hijab ke jikinta amma sai ta mishi kyau sosai, hannu ya sa ya karbi tray din hannunta ya ajiye kan stool, ya riko hannunta ya zaunar da ita kan Gado, yace "Thank you" da sauri ta kwace hannunta ta mike ta isa ga Tray din ta mik'a mai Sandwich din tace "kaci, you are hungry" ba gardama ya amsa, ta tsiyaya mai lemun ya kurba, yanda yake taunawa a hankali cikin aji, sai taji ya burgeta, guda biyu kawai yaci yace ya k'oshi, ta so ya k'ara amma ya shaida mata ya ishe shi, ta mik'e ta kwashe kayan tace "to sai da safe" da sauri ya mik'e ya karbe tray din ya dire a k'asa yace "Baby i want to talk to you about Something" jin yanda yayi maganar ne ya sa ta gane maganar Muhimmiya ce, wuri ta samu ta zauna, k'asa ya zauna yana me fuskantar ta, a hankali ya fara magana;
Baby, i know we had a rough start, i kept the way i feel for you for a quite a long time, ,kin shigo Rayuwata as a Blessing, you Sacrificed and did alot for me, And nagode miki for all that, Yanda Allah ya tsara, you are now My Wife, I know be kamata na sa ki ki min wani abu ba bayan abubuwan da kika min a baya, na son ba kya min son da nake miki, i'm not even sure if you love me at all, well I dont care about that, Ni ina sonki, ina kaunarki which is why nake so ki taimaka ba danni ba, ba don bakya so na ba, idan Wannan shine abu na k'arshe da zaki min ki min shi, ba zan tilasta miki kiyi abun da bakya so ba, but i'll be happy if you grant my request. DonAllah". Yanda yake magana ya sa taji tausayinshi, to me yake bukata daga gareta haka har yake rok'on ta? Kuma wai a ganinshi bata sonshi?" muryar Mimi ya fado kanta a lokacin da take ce mata "Seebi, sai kin cire kunya zaki iya zaman aure, he is your husband, take care of him or Someone will" runtse ido tayi tace
"Hamma, ka daina cewa bana sonka, ko ban sanka ba ai ba zance bana sonka ba, balle kuma Yanzu da kai Mijina ne, and Please ka daina rok'ona haka, ka fadi ko me kake so, InshaAllah zan maka shi in har befi karfina ba" Sosai maganganun ta suka mai dadi, ya samu k'arfin guiwan yi mata magana, hannunta ya sake kamawa yana mursawa a hankali yace "Baby, ina so ki dauki Zuwanki UMYU Matsayin Zuwa na ba zuwan karatun ki ba, ina nufin Don ki hadu dani ne kikazo Garin Katsina Gabaki daya, i want you to Sacrifice the 1year you spent in UMYU for me, ina so Ki Hak'ura da karatun da kikeyi a UMYU" idon Naseeba ya kawo ruwa, Tayi saurin maidasu, a ganinta kishinta yakeyi shiyasa be da Raayin tayi Karatu, amma Feeq beyi kama da Mazan da ba son Matansu suyi karatu, k'ila yana da reason dinshi, Sonshi da takeyi zai sa tayi mai komai, Ko don ta k'arasa ladarta, ko ba komai Aljannarta na tafin k'afarshi, a hankali tace "Hamma na, ba sai ka rok'eni haka ba, nafa kawai Umurni ne, umurni kawai zaka bani, kace Nasiba kin gama makaranta, ba zaki koma Makaranta ba, kai Mijina ne, ba sai ka rok'eni haka ba, ko da a ce ina Level 400 ka bukaci da na yanke karatu na, wallahi ni me yi ne, balle Level 1, ban ma gama sanin kan makarantar ba, Allah ya sa hakan yafi Alheri Amin" ta mik'e tsaye zata tafi,tausayinta, Sonta da k'aunar ta suka k'ara shigar shi, nan ya sake bata babban Matsayi a cikin ranshi, yace "Baby, baki gama karatu ba, yanzu dai zaki fara, i have plan for us, Abun da ya faru a baya tsakaninmu da Saude and All, hakan ya sani tsoron Mutanen mu, baka san wanda suke kewaye da kai ba, ba ka san ma su nufar ka da Sharri ba, hakan ya sa na tsani fara sabon rayuwa a k'asar nan, ina tsoron sharrin Mai sharri, ina tsoron Hassadar mai Hassada, Ina so muyi Nesa da k'asar nan, ina so mu fara Sabon Rayuwa inda ba wanda zai matsa mana, ba wanda zai cutar da mu, inda zamu gina Rayuwar mu cikin Aminci da k'aunar juna, Na gaya ma Uncle Zaid bukata ta, sai ya sanar dani dama Zai shirya mana Honeymoon a London mu hudu, sai yace in tambayeki idan kina da raayin Zama chan, zai Samo mana gida, ki fara Karatunki, And ni in fara Masters dina, idan baki da raayi, sai muje muyi 3weeks mu dawo, toh Alhamdulilah kin Amince, So help me Lord! I'll make you Happy, you wont regret this I promise, i'm going to shower you With Love and Care For the Rest of our Lives" kallo daya zaka mata ka ga Murnar da takeyi a zuciyarta ya baiyana, Dadi ya mamayeta, Farinciki ya ziyarci zuciyarta, ina zata saka ranta don Dadi, Alhamdulilah ta gode ma Allah a cikin ranta, ji take kamar ta rungume shi, ta bashi tukwicin wannan Albishir da ya mata, wai ita yau Seebin Nene zata je London? Bata taba zaton zataje ko nan da Airport ba, Amma da yake baka cire rai daga rahamar Allah gashi Aure zai kaita London. Kashe mata ido yayi yace "Baby, we'll be there, alone, just me and you, Just Us, then i would teach you how to love me" a hankali tace "You dont have to teach me how to love you, because i Do" Wani dadi yaji a ranshi cikin wata murya me sanyi yace "You What?" gangar Soyayya ta shigeta, bata son lokacin da tace "Yes Hamma, I believe In Destiny, My Destiny is to Meet you, Marry you and be with You, I love you So much" Dadi ke mai chalugude a k'irji, Farinciki da jin dadi ya ziyarceshi, takowa yayi ya matso gaf da ita, har suna iya jin hucin Juna, a hankali ya zare Hijab din jikin ta, nan da nan ta daburce, idonta ya juya don tsoro, shikam yana son yanda idon ta ke juyawan nan idan ta tsorata da abu, murmushi yayi ya Rungumeta sosai, ido ta runtse saboda tsoro, a hankali ya rada mata a kunne "Shhhh, keep calm, I got you" lamo tayi a jikinshi, shikuma ya sa hannu ya ware ribbon din da aka daure gashin

Please Login or Register in order to submit comment