Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakkinta na uwa" Nene tace "Ni da kun bi ta tawa tunda Ran Jumaa zasu zo ba sai an sha wahalar kai kaya Kaduna ba" Mami tace dai a kai musu su gani.
Su Miemee da Usheey sunzo ganin lefe, suna ta murna don Seebi tayi Goshi, kaya sai sambarka, nan suka ritse Uncle Zaid a Parlor suna zolayar shi, dariya kawai yakeyi, Miemee tace "Uncle Zee ya maganar Dinner? Kasan dai biggest hall of them all zaa kama mana, Soli Center nake ma bayani, yayi daria yace "Kar ku damu, ga Son nan kuyi magana dashi, zai yi komai" Meemee ta waiga taga Rafeeq na shigowa Fuskar nan murtuk'e, a ranta tace "kai dai ka sani".

Bayan Kwana Biyu
KADUNA
"Yaya Destiny brought Nasiba And Rafeeq Together, They belong to eachother, Ba ka tunanin dalilin da ya sa Allah ya kawo Nasiba garemu don ta auri Rafeeq ne, Nasiba da Rafeeq suit eachother, ko ban fada ba ka san Nasiba na Son Rafeeq, Mami kinsan dacin rabuwa da masoyi, please lets not deprive them of their chance to be Happy, lets help them be together, if you are worried and concerned about me, kar ka damu, i'll be fine eventually, mata da yawa a gari, i'll get one" Alhaji Habib yace "Zaid nagaya ma Times without Number cewa zan aura ma kowa Rafeeq but not Nasiba, Nasiba taka ce, Rafeeq is not worth her, he'll only hurt her da miskilancin shi, and Shes like a daughter to me, ba zan sa rayuwarta cikin kunci ba, shiyasa zan aura mata kai, kaine zaka kula min da ita" ran Zaid ya fara 6aci yace "Yaya you always tell me that you'll do anything for me, and Mami kullum cewa kikeyi kina so ki biyani for all i did to you, you all want to make it up for me, So this is what you'll do to make it up for me, Get Rafeeq married to Seebi, haka kurum zakuyi ku biyani duk abubuwan da na muku" Mami da Daddy suka kalli juna, Daddy yace "Zaid why are you so Stubborn, ban san ka da haka ba, i'm sorry i cannot do this" Mami ma tace "Sorry, Zaid ask for anything but not This" Rafeeq da ya shigo dakin Daddy ya gama jin duk abunda suka tautauna kasancewar wayar a Handsfree yake yace "ko sun amince ni ba zan amince ba, ba zan taba hada kaina da kai ba" cikin bacin rai Zaid yace "waya sa bakin ka Rafeeq? Who is asking for your opinion, shut the hell up boy, God!! you all make me sick" Dif Zaid ya kashe wayar ya cillar da ita kan kujera yana safa da marwa cikin Parlo, why is it that noone seems to understand? Shi gaskia ba zai shiga tsakanin masoyan nam ba, ya lura da irin son da Nasiba ke ma Rafeeq, ya lura bata sonsa, kuma ko kadan beji haushinta ba, ko kadan be ji kishin Rafeeq ba, tsaki yayi ta yanda zai bullo wa Yayanshi da Matarshi, ko ta halin k'ak'a bazai auri farincikin Rafeeq ba, a fusace ya bude fridge din Parlorn shi ya ciro kwalbar ruwa ya bare marfin ya cillar da ita ya kafa kai ya fara kwankwadar ruwan.

"Assalam Alaikum" wata zazzakar murya tayi sallama a k'ofar parlon tare da shigowa lokaci guda, fesar da ruwan bakinshi yayi tare da sakin robar a kasa sakamakon kwarewar da yayi, wata hallita ce tsaye da Bak'ar Jallabiya, kamar Maman Ayman, sai dai wannan tafi Maman Ayman haske, tafita kyau, tafita dan kauri da tsawo kadan, kamar Balarabiya, dam Gaban shi ya yanke ya fadi sakamakon hada idon da sukayi, lokaci guda ya ji shi a wani yanayi me wuyar fasaltuwa, rabon da yaji irin wannan yanayin an jima, yayi ta maza ya saita tunanin shi ya taka daf da ita, kamshinta ya bugi hancinsa, ya lumshe ido wani natsuwa na shigar shi, Ya tsura mata ido yana son gane wani abu game da ita, , itama shi din take kallo da sauri ta kawar da tunanin da takeyi game dashi, don duk yanda take zaton shi ya wuce nan, ya zarta tunaninta, da ta ga Kallon ba me k'arewa bane ta cira baki tace "Ina wuni, donAllah ina neman Zaid Lema" cikin sanyin jiki ya lumshe ido yace "Ni ne, how may i help you?" a tsaye tace "Sunana Zainab Sani Sister din-- bata karasa ba yace "Sistern my late Wife, Safiyya" tace "Exactly" yace "Ban sanki ba, but i've heard about you from her, and da kika shigo ina ta kallon ki, da kikayi magana kuma na ga tsantsar kamar da kikeyi da Ita" cike da k'asaita tayi Murmushi, da ya lura 'yar aji ce, sai shima ya ari fuskar dansa Rafeeq (lol) yace "So why are you here? ta kalleshi da mamaki tace " I'm not here for you, i'm here for my daughter, i came to take her with me, its time for her to Live with her Mother's Family". Da mamaki Zaid yace "What??".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣9⃣
(This Line is for all the Amazing Sisters that Sacrificed their Happiness for their Nieces and Nephews, i'm talking about the Sisters that gt Married to their Late Sister's Husband. Only Allah Can Reward them💙)

"Eh kaji ni sarai, nazo in tafi da Rafee'ah Aymana ne, jiya na dawo k'asar, an gaya min cewa Aure zakayi, Ba zan yi gangancin barin ta wurin ka ba, ba zan bari ta fukanci wahalar MATAR UBA ba, ba zan bari tayi kukan rashin uwa ba, shiyasa zan dauketa. Kallonta Sosai Zaid keyi, Sosai ta burgeshi, yanayin maganar ta, bata shakka ko tsoro, yanda ta nuna son da take ma Ayman ya burgeshi, da ta ga kallon da yake mata sai tace "Mallam ka dauko min diyata, sauri nakeyi" Zaid ya murmusa, yace "Ga dukkan alamu kina Son wannan diyar taki" tace "So fiye da kaina ma" yace "Good, amma kiyi hakuri, ba zan iya ryauwa ba Ayman ba, na rasa Mamarta ba zan iya juren Rashin ta ba itama, kiyi hakuri ba zan iya baki ita ba" Zainab ta bata rai tace "Bangane ba" ya yi Murmushi yace "Baki gane hausar ba? Oh ashe balarabiya ce, gashi ni ban iya turanci ba balle larabci, hakuri kawai zakiyi, ba zan iya naki Ayman ba, Kuma idan nayi aure Amarya ta zata rik'e min ita, yanzu haka ma ba ta tare dani a garin Kaduna, tana chan garin Katsina tare da Amaryar tawa" Idon Zee suka ciko da hawaye, ta sausata murya tace "Please ka taimaka ka bani ita, ina so in kasance tare da ita, ina sonta Sosai" Zaid ya girgiza kai tare da Murmushi yace "Nope, ai ina jin ganinta ma zai miki wahala balle ta zauna tare da ke, kinga ba ma lallai bane Mijinta ya Amince da ita ba" da sauri tace " Wallahi banda aure, kuma kafin inyi sai na tabbatar Mijin da zan aura ya amince zai riketa ya dauketa a matsayin Uba" yace "Tabdijam, da Mahaifinta a raye, har sai an nemi izini wani? Wannan ma na daya daga cikin dalilan da zai hana in baki ita, ba zan baki ita ba gaskia" ran Zainab ya gama 6aci tasan in ta k'ara bude Baki zata iya fashewa da Kuka, ta sa6i jakkarta ta juya ta bar Parlorn ranta a jagule, Zaid kuwa Murmushi yayi Sosai.
**********
Tana isa Gida ta fada kan Mamanta ta fashe da kuka, Maman ta hau lallashi tana cewa "Zainab me yasa ki kuka? Me ya faru? Wani abun ya samu Aymana?" cikin kuka tace "Umma, cewa yayi ba zai bani ita ba, wai Amaryar shi zai ba ita, yanzu haka Aymana na Katsina ita zata kular mishi da ita" Umma tayi Murmushi tace "Zainab dama sai da na gaya miki Zaid ba zai yarda ya baki Aymana ba" "wai ma Umma tun da Safiyya ta rasu mesa baki gaya min ta bar diya ba? Eh Umma? Meyasa kuka boye min ta bar diya, haka Aurenta, sai dai naga hotuna a IG, gashi har diyarta ta fi shekara, haba Umma me ya sa kuke min haka ne?" Umma tace "Zainab hakuri zakiyi, umurnin babanku ne, ya san halinki, kina iya cewa zaki dawo, kuma Lokacin kina tsaka Da rubuta Jarabawa, kuma in kika dawo kika ga Aymana kina iya cewa ba zaki koma ba, ko kuma ki nemi a baki ita ki tafi da ita, shiyasa yace in har aka bari kika dawo, sabon tashin hankali kowa zai shiga, kuma Zainab ki kwantar da Hankalinki, Zaid mutumin kirki ne, yana da Amana, ya kan kawo mana Aymana shi da Marikiyar Ayman, mutanen kirki ne wallahi, kar kiji fargaban komai, Zaid zai kular miki da diyarki" "Umma ba shi nake ji na, ina tsoron Matar Uba, ina tsoron Kar ta sha wahalarta, shiyasa nake so ya bamu ita, ai mu ke da hakkin riketa" Aa fa Zainab, shi ke da hakki, sai yanda yayi da ita" kafin Zainab tace komai sai jin Sallama sukayi, k'anin Zainab ya shigo yace "Umma ga Yaya Zaid nan a waje" Umma tace "Bismillan shi, ya shigo" Zainab ta 6ata rai tace idan be bani ita ta dadi ba, zan maka shi Kotun Musulunci" Daidai da Shigowar Zaid fuskar nan kamar kullum dauke da Murmushi, A ladabce ya durkusa har k'asa ya gaida Umma, Umma ta amsa mai cikin sakin fuska da girmamawa. Zainab ta hadiye fuska ta na karkada k'afa. Murmushi Zaid ya sake yi yace "Umma ashe 'yan makaranta sun dawo?" Umma ta kallo Zainab da ta hade girar sama da k'asa tace "Aiko dai su Dr Zainab an dawo" Zaid yace "Ahhh ashe Dr ce" Umma tace aiko Likita ce, jiya ta dawo ta kammalla karatun Likitamcin ta gaba ki daya, saura Housemanship da zatayi a Barau Dikko" Zaid yace "Allah sa Alkhairi" "Amin Amin" Abba ba ya nan ko? Umma tace "Ya je Government House" su ka danyi shiru na wani dan Lokaci kafin Zaid yace "Umma sai gashi Likita ta zo min da wani zance" Umma tace "ina ruwan Zainab, jiya ta dawo, daga ce mata Mijim Marigayiya Safiyya ma zai yi aure nan da Sati biyu, Kai Mu'allim sai kace nan za a kawo mana Aymana? Sai ta tambaya wacece Aymana, kasan ba a gaya mata Safiyya ta bar diya ba, ai fa tun da ta ji ance Diyar Safiyya ce take ta ruwan Wulakanci tun jiya, wai zata je ta daukota, ya zaayi mu bar maka yarinya, wacewace ita sai ta amso ta" Zaid ya fadada Murmushin sa, yace "Umma zan bata Aymana idan tana so" Umma da Zainab suka zuba mai ido, Zaid ya maida dubanshi ga Zainab da ta zuba mai idanuwanta, yace "kwarai kuwa, zan baki Ayman ki rayu da ita, har girmanta, har tsufanki, Aure kawai zai rabaku da ita" ba ta san sanda Murmushi ya kubuce mata, tace "Nagode Sosai, Allah ya biya ka, Allah ya ji kan Sofie, nagode da ka Amince zaka bani ita, Allah ya baku Zaman Lafiya da Amaryar ka" yayi Murmushi tare da cewa "Amin, amma fa da Sharadi daya, i have a condition" da Murmushi a fuskarta tace "Koma meye zanyi, tell me" a takaice yace "Marry me" idanuwanta ta gwalalo, tace "What?" ba tare da wani fargaba ba yace "Ki Aureni, and Ayman is yours" ta mik'e tsaye tace "Are You in your right sense? In bacci kakeyi ka tashi, bazan taba aurenka ba, ta ya ma zaayi in auri Mijin Yayata? Tabdijam, don nace ka ban diyarka zakace in aureka? You are using the love i have for your Daughter to use me, To ba zan aureka ba, ba zan auri Mijin Yayata ba" Murmushin dai yayi yace "Ina Yayar taki? Ba ta rasu ba? Idan tana da rai zance ki Aureni ne? Ai Aure tsakanin mu be haramta ba, and kuma if theres anyone Safiyya would like me to get married to is defintely You, for the sake of our Daughter" Wani kallo ta ke binshi dashi, tace "ko ma meye ne, ba zan aureka ba, ba zaayi wannan cin amanar dani ba".
"Zaid" cewar Umma da ta gama nazarin Zaid da Zainab , Zaid ya maida dubansa ga Umma, Umma tace "Bari in dan ga Zainab" ta mike tare da jan hannun Zainab suka wuce Daki. Daidai da shigowan Abban, "Ahh Zaid Sannu da Zuwa, ka dade da zuwa? Ya na ganka kai kadai?" Zaid ya durkusa har kasa ya gaida Sirikin shi, suna ganin mutuncin Juna, Zaid yace "na dan jima, yanzu Umma ta shiga ciki ita da Zainab" Abba yace "Toh toh, barin shiga inji". Dakin Umma ya shiga, ya tarar Umma na Ma Zainab fada ko da ya tambayi ba'asi, Umma ta danar dashi abun da ke faruwa, Sosai ya ji dadi, don har ranshi yana Son Zaid, yana son sake Hade iri da shi. Zama yayi sosai yana me kallon Zainab chan yace;
"Zainab ki saurareni da kyau, wannan Mahaifiyar ki ce, Ni ko Mahaifinki ne, ba zamu so wani abu ya sameki ba, kuma Hak'k'ina ne in za6a miki Mijin Aure, Zaid Namiji ne da ko wane Uba zai so ya za6a ma diyar shi shi a Mijin Aure, Zaid na da kirki, ni ba talaka bane amma duk wata Zaid sai ya aiko da Motar Abinci duk wani nauinka Abinci yana kawo mana, tun daga lokacin da yake neman Yayarki har zuwa rana irinta yau, Zaid na da kirki da mutunci da kuma girmama na gaba, Shekarar shi daya da dori Yayarki bata taba cewa ya mata ba daidai ba, Zainab idan nace zan gaya miki irin Kirkin Zaid to zamu dade ina miki magana daya, ke ba wani tsaiyayye ba, ba kya kula Samari, ba kya sauraronsu, da ta ni ne da tun kam ki gama karatunki na miki Aure, amma saboda ba wani tsaiyaye na bari kika kammala, Zainab ba zan miki Auren dole ba, amma in kin nemi shawara ta, to Zaid Mijin Aure ne, Allah shi ya kawo miki Zaid a lokacin nan, kuma tunda shi ya bukaci ki aureshi ai ta kwana gidan Sauki, ba zaki ce ana so a hadaki da wani ba, shi ya kawo kansa, na yarda dashi dari bisa dari, sannan kuma kina maganar Zaki ci Amanar Safiyya, me ya kawo cin Amana? Kar ki manta ta rasu ta bar diya, kuma na san ba zata so diyarta ta sha wahalar Matar Uba ba kamar yanda kika ce, zata so ke ki kasance tare da ita, da Mijinta, Shawara ce"
Shiru tayi Alamun maganr Mahaifinta ya shigeta, Umma ma ta sake k'arfafa mata guiwa, Abba yace "Maza Autan mata, je ki kuyi magana kinji" cikin kunya ta tashi ta fita.
Zaune ta ganshi yana bin hotunan Parlorn da ido, nan ta samu ta k'are mai Kallo Tsaf, Haddade ne son kowa kin wanda ya rasa, ya hadu iya haduwa, komai na sa yayi, to meyasa zata ki'sa? A hankali ta k'arasa tare da Sallama, ya amsa tare da mikewa ya na wurga mata Murmushi, ya karaso kusa da ita, tana tsaye har suna jin hucin juna, yace "So??" cikin sanyi ta tace "You like smilling alot" Murmushin ya sake sakar mata yace "Dont i have reason to Smile? I'm with you afterall" Murmushin kunya takeyi, yace "So? Will you Marry me?" a hankali tace "Yes i'll Marry you" Murmushi suke sakar ma Juna, ji sukayi kamar sun shekara da haduwa, wani So da kaunar junansu ke shiga jinin jikinsu, wani Shaukin k'auna ke shigar Zaid, be taba jin wannan yanayin a tare dashi ba. Ta samu kwarin guiwan cewa "Mu zauna" suka zauna su ka tsura wa juna Ido, a hankali tace "Yaushe zan ga Ayman? Yace $whenever You are ready" tace "A shirye nake yanzu" yayi daria yace "yamma yayi, ki bari Gobe sai muje ko? Alright?" ta gyada kai cikin murna.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaid Matar da zaka aura nan da Sati Biyu fa?" cewar Abba, Zaid yace "Matar Rafeeq ce, Rafeeq zata aura" duk suka kalleshi suna neman karin bayani, Abba yace "Toh a katin daurin Auren da a ka kawo min sunanka ne a jiki" Zaid yace hakane, amma abun da ya faru shine ita yarinyar da Yaro na suna matukar son junan su, cikin rashin sani aka sa ranar da ni, Ko da Allah be kawo min Zainab ba, gaskia na fasa Auren yarinyar, don D'ana take so bani ba" Karaf Zainab tace "Kai fa? Kana sonta?" duk suka bita da ido, itama sai taji kunyar maganar da tayi, yace "Ina sonta, amma sai bayan haduwar mu dake na san cewa irin son da nake ma Rafeeq nake mata, ba irin So na Aure ba" wani dadi ya lullube ta, Abba yace "Toh yanzu ya kake so ayi?" yace "Abba, so nake in gabatar da Maganar ga Yayana, sai a hade Auren da na Rafeeq din nan da Sati Biyu" Abba yace "Wannan gaggawa haka?" Zaid yace Abba ba Gaggawa bane, saidai in kana da bukattar yin bincike a kaina, sai ayi abu a tsanake " Abba yace "Haba Zaid, bincike na me? Zaid ai kai ba bak'o bane, mun sanka mun san kai ko waye, ba sai anyi bincike ba, ba komai zamu shirya nan da Sati Biyun, zan kira kawunta in sanar dashi, Allah ya sa Alkhairi". Sosai Zaid yaji Dadi yace " Gobe InshaAllah zanje Katsinar don yi magana da Yayana da Magabacin mu" "Allah ya kaimu" inji su Umma, Cikin In ina Zainab tace "Abba nima ina so inje Katsinar don ganin Aymana" Abba yace "Toh uwar azarbabi, ba inda zakije, ki bari har ya kawo miki ita" "Abba Please kar ka hanani, kaga ban taba haduwa da ita ba, i cant wait till two weeks, Please Abbana" Abba yace " "Abba zuwan ta zai taimakeni gurin yi ma Yayana bayani, a yi hakuri a barta taje" Abba yace "I know she's safe with you, Allah ya kaimu goben ya kuma tsare Hanya" Zaid ya ji dadi sosai sukayi Sallama da niyyar Gobe zasu wuce Katsina.

WASHEGARI
KATSINA
(Sorrynku, ku cigaba da min uzuri, Same excuse din dai ne, zaa cigaba daga nan InshaAllah)

👧KE ALHERI CE🙇‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

CIGABAN5⃣9⃣

Gaba ki dayan su suna Zaune a Parlorn k'asa suna lunch, Ayman na kan cinyar Seebi ta na bata a baki, ba tare da ya kalleta ba yace "Dame dame zaki buk'ata a hidimar bikin?" a takaice tace "Nima bansani ba" ya tsagaita cin Abincin ya kallota kamar ba zaiyi magana ba chan yace "bangane baki sani ba, ba naji wannan friend dinki tace meye meye ba" Mami da Daddy da suke binsu da ido suka kalli juna suja bata baki, sun lura da Rafeeq yanzu abu kadan yake harzuk'a shi, Mami tace "Rafeeq, ai ba haka akeyi ba, ba da ita ya kamata kayi magana ba, ai ga Aneesa nan, ko kuma friends dinta zaka sama sai kuyi maganar komai" ya dan bata rai "Ni ba wurin wata da zanje, suna da Hayaniya gasu da damuwa, Bari zan ma Lesh magana, sai ya same su" Nene dai ta ta6e baki, ba ta son tanka musu, don yanzu zata sake layi shiyasa tayi shiru".
Sallama Zaid yayi a tare suka amsa, ya kusto kai yayi dining area inda yake jin surutan su da karan plates da chokula, Daddy yace "Zaid, kaine a tafe? Kai ba kajin sintiri a hanya ko? Ka dauki hanyar Katsina zuwa Kaduna kamar Tafiyar minti 30, kai ba ka gajiya ne? Kullum kana hanyar Katsina, shekaran jiya fa ka tafi" Nene tace "Yanzu dai ya iso Lafiya, ai shikenan, Mita na ne? ya ajiye Mata ai dole ya ke zuwa ganinta ko" Yak'e kawai Zaid yayi, Mami tace Sannu da Zuwa Zaid, Aneesa da Seebi sukace "Sannu da zuwa Uncle Zee" ya amsa cikin sakin Fuska, Rafeeq ya dago kai suna masu hada ido da juna, ya sakar mai da Murmushi Yace "Kazo Lafiya?" "Lafiya lau Boy" Mami tace "Oya Zauna ka kwashi Gara, nasan kana nan da yunwa" yace "Eh Mami, amma ba ni kadai bane, mu biyu ne" "kai da waye? Ka barshi waje? Haba je ka shigo dashi" Murmushi yayi ya fita, suka cigaba da cin abincin su, chan ko sai gasu sun shigo, Zaid a gaba, Zainab a baya tana tafe sum sum, sanye take ta Hadaddar Jallabiya, K'amshin turarenta ya sa su dagowa gabaki daya suka zuba mata ido, Zaid na zuwa ya sa Hannu ya dauki Ayman ya mik'a ma Zainab ita, Zainab ta amsheta ta rungumeta take taji hawaye sun fara bin kuncinta, abun mamaki Lamo Ayman tayi a jikin Zainab, bata yi mata k'uiwa ba, Sosai ta matse Ayman a jikinta tana jin so yarinyar har 6argonta.
Nene tace "Zaidu bawan Allah, wannan fa?" yayi Murmushi ya kalli Mami yace "Sister din Marigayiya Safiyya ce, shekaran jiya ta dawo daga Makaranta" Allah Sarki inji Mami da Alhaji Habib, Sannun ki da zuwa, kun sha hanya, ya su Mamarku? Ya kuma k'arfin hakuri? Allah ya ji k'anta ya rahamshe ta" Zainab ta amsa gaisuwar Mami, sannan ta Mata gaisuwar Rafee'ah, ta gaida Nene ds Alhaji Habib, Seebi da Aneesa suka gaidata, with a big smile on Rafeeq's face ya gaida Zainab, farat daya ta mishi, ko don ta na son Angel dinsa ne? Matashiya ce da ba zata wuce Shekaru daya da shi ba, 24 zuwa 25.
Mami tace "Zauna kinji Zainab mu ci Abinci" Zaid ya Ja kujerar baya ta zauna shima ya zauna don cin Abinci.
Bayan sun gama cin Abinci suka hadu a Parlor, Ayman har tayi bacci jikin Zainab, Zaid ya kalli Alhaji Habib da Mami, yace "Erhm,Yaya, Mami, dama na kawo Zainab ne don taga Ayman da kuma in sheda muku cewa zan aure ta, ba wai don tana k'anwar Safiyya ba, aa saboda dai ina sonta" Rafeeq ya zaro ido yana mamakin furucin da Uncle Zee keyi, Mami ta dan razana a ganinta kamar cin fuska ne ga Nasiba, ace tun Kafin Aurenta har an fara maganar yi mata Kishiya Mami ta k'irkiro Murmushi, Daddy ya yi ta maza yace "Zaid, ina ganin ai kamar its too early, ya kamata ku k'ara fahimtar junanku, da ka bar wannan maganar an cigaba da Maganar ka da Nasiba, nan gaba sai ayi maganar Zainab din tunda ka nuna kana sonta, mu kuma abun da kake so zamu maka" Gaban Zainab ya yanke ya fadi, kar mutanen suk'i amincewa da ita, gashi ta bari Son Zaid ya mata Kamu ba na wasa ba, har ta fara tausayin kanta. Jin muryar shi tayi yace "Aa Yaya, zan aureta in the next two weeks, ba zan iya bari har mu kai wani lokaci ba tare da juna ba". "Kai Zaidu Bawan Allah kalle ni nan, ni tsarar kace? Ko don kaga ina daga maka k'afa shiyasa kake son Takani? Seebi ta maka kama da wacce zaka Wulakanta? Kai ka samu farar mace ko? Dangin larabawa zaka ma Seebina Wulakanci? In banda Wulakanci ya zaka fara maganar Auren wata tun kafin ka aureta? Don cin fuska kace rana daya zaa daura? To wallahi ka fita idona in rufe, ban ta6a watse maka karama ba, banso in fara yau, ina ganin girmanka, ka ja dan gemunka kayi fatali da wannan magana ta auren wata" Seebi ta dago cikin nauyin baki tace "kiyi hakuri Nene, ba komai Wallahi, bakomai don ya aure

Please Login or Register in order to submit comment