Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi zaune gaban motar, k'afar shi kuma a waje, " Ta'al hoona Baby" Daria tayi tace stop embarassing me, kai keyi nike jin kunya" oh hakane? Barin zo in baki kunyar da kyau" ji yayi an buge mishi baki, Uncle Zaid ne, yace 'Kai baka da kunya ko, a gabana?" ya turo baki "Uhmmn baby kinga Uncle Zaid" Kirjinta ta dafe "Inalillahi Hamma wai gaban Uncle Zaid kake wayar nan ji yanda kake magana kamar wani baby?" toh ai babyn ne ko? Babynki" Uncle Zaid ya kaimai duka ya kauce yana daria, karbe wayan yayi daga hannun shi, yace "Seeebi Zooo nan" sallalami ta fara tace Uncle Zaid kayi hakuri ba zamu sake ba, byebye Aunty Zee na nema na" diff ta kashe wayar don kunyar Uncle Zaid da ya lullubeta, haka kurum Hamma ya sa ta jin kunya. Zaid yace "Baka da kunya ko Son?" Rafeeq ya kama kunnen shi yace "Sorry papa, shes just so beautiful, i cannot resist her" Uncle Zaid ya tabe baki yace "Thank God Matana tafi ta kowa" Rafeeq yace "Wallhi Baby ta fi Aunty Zee kyau" "haba Rafeeq kar ka rantse, Kalleta fa chan, kamar Balarabiya" Rafeeq ya ta6e baki yace "Fari kawai tafi baby" Uncle Zaid yace za ma ka dawo hanya, Oya muje tunda sun k'araso" suka fita, Sanye suke da Farar Jallabiya iri daya, sun yi kyau, kamar wasu abokai, suka karasa gun Amaren, Nasiba na daga gefen Aunty Zee, Suna hada ido da Rafeeq ya kashe mata ido, ta kawar da kai da sauri ta na smilling, "Aunty Zee kinyi Kyau Sosai" cewar Rafeeq, tayi Smile tace "Thank You Son" ya daga Ayman ya chafe yace Angel you look beautiful too ya mata kiss a kumatau, suka shiga Hall din a layi bayan an sa kusu wak'ar Sudan. Tafiya yakeyi kamar wanda aka ma dukkan tsiya, yayi doro wai duk cikin Gayu ne, aikuwa yanmatan gun duk idansu kanshi, Nasiba ta lura da wani Kallon Da Wata k'awar Aunty Zee Emjay (Talatuwa)Ke binshi dashi, cike da kishi Nasiba tace "Aunty Emjay, He's just 24, jin girmeshi fa" lols.
Haka aka watse daga dinner bayan an bar tarihi.
Washegari da Sassafe Mami, Ummi da Seebi, da wasu Friends din Naseebah su Softie, Maryam Aqeel, Jamie jamie, Azyza, Mufeen, Friends dinta na Secondary School Suka wuce Katsina, don yau Mami zatayi Yinin Bikinta a chan Katsina.
Tun Sati kafin bikin Daddy ya nemi Alfarma kan a raba Bikin Uncle Zee da na Rafeeq, saboda ba zaiyiuw a zo Kaduna a daura Auren Aunty Zee ba kuma a koma Katsina daura Auren Rafeeq ba, kuma ba yanda zaayi a hade bikin don Mutanen Daddy na Katsina na Abban Zee na Kaduna, shiyasa aka yanke hukuncin fara daura Auren Uncle Zee.
Bayan Sallahr Jumaa, daukacin Alumaar Musulmi suka Shaida Daurin Auren Zaid Iro Lema, da Amaryarsa Zainab Sani, bisa Sadaki naira dubu 50 lakadan ba ajalan ba.
Bayan Reception.Daddy, Uncle Zee, Rafeeq da Maalesh suka dauki hanyar Katsina, Maalesh ke tuk'i, Rafeeq a kusa dashi, Sai Daddy da Uncle Zaid a baya
****
A lokacin Gidan Mami na chan Mak'il ana yinin biki (Mothers Day) Farfajiyar ya sha Decoration, MC Lubna Sufyan aka dauko tun Daga Lagos don yin MC, yan kidan kwarya nayi, Mommyn Maalesh (Umm Eeman) sai chashewa take tayi tana ruwan kudi, Mami dai sai dai tayi lik'i amma ba dai rawa ba, Su Miemee Suka jawo Nene wai sai tayi Rawa, da Nene ta sake wani shewa sai ko ta fara rawan Allah bakace, Ummi kunya taji sosai, Seebi ko da ke zaune kan kujera sai dariar Nene take tayi, har kusan bayan Ishai kafin aka watse, sai da Nene ta bi Bayan masu kidin kwaryar nan tace suzo Gobe gidanta, don ita gobe bayan Daurin auren take nata yinin Biki. Sun ko amince zasu zo.

Bayan Isha'i suka iso Charanci, Daddy yace Maalesh maida min Companion Fm, takwas tayi inji Labarai me katsinar ke ciki, Rafeeq yace "Daddy wai dama akwai gidan Radio a Katsina ne? Maalesh yace " Dan rainin wayau kana nufin baka san Akwai Gidan Radio a KT ba? No wonder Nene tace maka no radio a gida" sukayi daria har Rafeeq yace "That woman never cease to amaze me"
Maalesh na tuning Stations din suka ji ana shelar
*Mallama Aminene Maman na farincikin gaiyatar ku zuwa Yinin Bikin Jikarta Nasiba Muhammad Seebi, da Angonta Rafeeq Habibu Lema Dunkum" be bari an karasa ba ya latse Radiom ta mutu, tare da dafe kai yace "Lord of Mercy, this woman is my Worsttttt nightmare" aiko duk suka tuntsire da daria banda Rafeeq da ya hade girar sama da ta k'asa.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg6⃣0⃣

Ya kallesu yayi dan guntun tsaki, yace "Ba abun daria bane, duk yanda na so to get along with her, i just cant, shes Annoooooying" Daria Daddy yayi, Uncle Zaid yace "shiyasa nace zata zauna maka 'yar zaman daki" Rafeeq ya gwalo ido yace "Wa? Aikuwa da wata rana na mata dukkan tsiya" Maalesh ya bude baki yace "Nenen?" Rafeeq yace "Ita fah" Maalesh yace "aikuwa kamar a kunnenta" "in ka fasa tsoron ta nakeji ne dama?" Maalesh ya fashe da Daria yace "Aa fa guy, kar fa kamanta randa tayi shirin Buje da gatari a hannu ka tsorata fa" Rafeeq yace "Randa tayi shigar 'Yan daba dai, everyone in my shoes will do the same, daga ganinta ta ta6a Daba" Zaid ya murtuk'e fuska yace "Rafeeeq" da sauri Feeq yace "Sorry".
Haka suka iso Katsina Lafia, straight Guest House suka nufa inda aka ajiye Abii da mutanen shi, Suna sauka Rfaeeq ya Sanfe ya tari Achaba ya haye sai Gidansu inda aka gama Mothers day, da sauri Feeq ya hau sama, haka ya dinga k'etara Mata har ya shiga dakin Seebi, wayam be ga kowa ba, ya lek'a dakin Mami, Zaune Mami take da Friends dinta su Mom din Maalesh da wasu yana ganinsu yayi saurin juya wa, don bai san surutu, amma kash Mom din Maalesh ta ganshi tace "Come here boy" sum sum ya shiga dakin kamar wanda yayi k'arya, Mom tace Yadai? Murya k'asa k'asa yace "Mom Naseebah nake nema" ta harareshi tace "If i slap you ehn, baka ga Aunties dinka ba? Cant you greet?" dan guntun tsaki yahi ya kallesu tare da Turo baki yace "Ina wuninku" duk suka amsa cike da faraa" ya juyo ga Mom din Maalesh yace "Mom where is she?" Mom ta ja kunnenshi tace "Listen to me boy, you are not to see the Bride sai bayan an daure Aure kaji ai?" Rafeeq ya turo baki kamar zaiyi kuka ya kalli Mami da fuskar tausayi ta ta6e baki tace "Kai da ita ba ruwana" juyawa yayi yana tafiar yara idan an hanasu abu, Mom din Maalesh tayi daria ta kalli Friends dinsu tace "Kun ganshi ko? Shine fa Angon, wai Amaryar sa ya ke nema" su ka kalli Mami "wai dagaske Hajia Aishatu?" Mami tayi daria tace "gashi Mom dinshi ta fada". Duk mamaki ya lullubesu.
"Yauwa Anee, ina Baby?" Aneesa tace "Yaya Rafeeq ta tafi gida bayan an gama Mothers Day" ya dan bata fuska, wani Gida?" "Gidan Nene mana" "Oh shit!" ya fada tare da yin hanyar k'asa da gudu yana mita.
°°°
Gidan Nene cike da dangi, kowa da abunda yakeyi wasu daga ciki kuma ana yankar Alaiyahu da zaayi Miyar Yinin Biki, wasu na 6are Ledar tuwo, su Nene kuwa an shige Dangi ana ta labari a lokaci guda kuma tana bada Umurni. Be san gidan cike yake ba, Cikin muryan shi yayi Sallama tare da kusta kai lokaci guda, Nene kadai taji Sallamar sa, sai ganinshi kawai sukayi a kansu, yayi nadamar shigowa da ya ga idanuwa sun mai chaaa, ji yake kamar ya juya, haka ya tsaya musu k'ikam, shi be juya ba, shi be ce dasu komai ba, Goggon Seebi tace "Wanene wannan ya shigo mana gida ba Sallama" Daure fuska yayi tamau, Nene tace "Ya fayi, haka yake sallamar sa kamar Wusir, Dunkum kike gani, Dangin Tsaka, Miskili yafi mahaukaci ban haushi" inji inna tani "Toh fa Shikuma fa?" "Shine fa Angon Seebi" wata Yayar Ummi tace "Ahh Nene kice duk kirarin nan ba a banza ba, ashe kishi kikeyi, Ya dauki Seebi yace beyi dake" Nene ta ta6e baki tace "Ni me zanyi da Dunkum? Ai Sai Seebin da ta ga zata iya" da Ummi suka hada ido, ta mishi Inkiya da ya gaida su, guntun tsaki yayi, a hankali yace "Ina wunin ku" suka amsa da faraa, Kakkanin Seebi suka fara jan shi da wasa, Yak'e me kama da Kuka yakeyi, nan ya samu ya sanfe daga gidan.
Tsaki ya buga da k'arfi da ya kira Wayar Seebi karo na 6 ya ji shi kashe, shi gaskia ba zai iya kwana be ganta ba, Wayar shi ya zaro ya latso Wayar Uncle Zaid "Boy ya?" Cikin Marairaicewa yace "Ba gani nazo gidan Neh-neh ba, na ga Mata sunfi 60, wai a gidan Neh-neh zasu kwana, kuma Baby na cikin su, duk sun matse ta, sun takura mata" Uncle Zaid yace "Boy ban san rigima, ba daga yau shikenan ba?, Danginta ne" Kamar Zaiyi kuka yace "Please Uncle Zaid, do something" ajiyar zuciya yayi yace ya kake so ayi to? Cike da shagwaba yace "Ni ta koma gida" Zaid yace "Ohh saboda ka hanata sukuni ko?" da sauri yace Aa Wallahi, ni da zan kwana Gidansu Lesh " Good inji Zaid ya latse wayar ya kira Wayar Nene, "Halo Zaidu Bawan Allah, ango, kayi hakuri ban hallarci bikin ka ba, Yanuwa na daga k'auye sunzo ne"Murmushi yayi yace "bakomai Nenen mu, ya taro? Ya jamaa?" "Alhamdulilah ya naku?" "Lafiya lao Nene, nace dama Seebi da k'awayenta su je chan Gida su kwana, an gyara musu daki Biyu" Nene bata kawo komai ranta ba tace "kamar ka san a gwamutse muke, bari ko su shirya su koma chan" bata kashe wayar ba ta shiga kwadawa Seebi Kira ta shirya su koma Gidan Lema.
*********
"Baby" jin muryar shi kawai tayi a tsakar Gida, Friends dinta sukace "lahh ga Ango" Mur ya sha, saida Seebi ta harareshi kafin yace "Sannun ku fa" su ka amsa sunso Magaanr tasu yayi Nisa, amma ba hali, Nasibah tace "zamu shiga ciki" yace kije ki rakasu ina jiranki" zatayi magana ya tsareta da idanun sa, Alright tace tayi cikin gida da Friends dinta, shi ko dakinsa ya shiga ya ciro Key din motarsa ya bude ya shiga tare da kunna AC, ya ga fitowarta, yana ganin yanda take dube dube ta window da alamun shi take nema,horn ya mata da ya dan firgita ta, a hankali ta tako ta side dinshi, a taka'aice yace "Get In"
tace "Hamma Please"kallonta kawai yayi, ta san maanar kallon da ya mata da sauri ta zagaya ta bude motar ta shiga, Gyara zamanshi yayi ya maida hankalin shi kachokam kan ta, yana binta da kallon so da k'auna, sadda kanta tayi k'asa, ya sa hannu ya kamo hannayenta duka biyu da suka sha zanen Lalle, ta yi ta kwace hannunta ta kasa, ya fi minti 3 a haka shi be tanka ta ba, da k'yar bakinta ya lalubo " Ina jin Bacci" Murmushi yayi yace "Baby, kin kashe wayanki, kin hanani ganinki and now kina jin bacci? Oya zo ki kwanta" ya karashe tare da nuna chest din shi, Ido ta ware tace "Hamma"yayi Murmushi yace "Alright, kije ki kwanta, I love you so much baby, I got you, I got Us" Smile tayi tare da fadin "Goodnight" ta bude murfin k'ofa zat fita ya rik'o hannunta daya ya kai bakinshi yayi kissing, Lokaci daya Seebi ta daburce, ya sake hannun tare da cewa "Goodnight Baby" da sauri ta fita ta bar Motar tayi cikin Gida, shikuma ya ja Mitar ya fita daga Unguwar ya nufa Unguwar su Lesh.

SATURDAY 11:30AM

Massalacin Commasie Cike ciki da bai, har toshe Hanya akayi saboda chunkosa, Manyan Mutane k'usoshin k'asa, yan Siyasa, Yan Kasuwa Yan Uwa da Abokan Arziki zaune Cikin Massalacin, Abbii na gaisawa da mutanen shi, suna mai Murna, Liman yazo, ana jiran zuwan Waliyyin Ango, har 12:30 ba alamun su, Daddy cikin bacin rai ya ciro Waya ya danna kiran Uncle Zaid, yana dauka Daddy ya rufe shi da Fada, kai Zaid kar ka maida mu k'ananun mutane mana, ka tara mu a nan, ka k'i zuwa, kowa fa na da abun yi haba" daddy na iya jiyo Sautin Murmushin Zaid, yace "Kwantas Yaya, i had to make sure My Son is looking Good, yanzu dai juyi daman ka, gamu muna kallon ka" Da sauri Daddy ya kallo Daman shi, Aiko sai ganin Zaid yayi sanye cikin Shiga ta Alfarma, Babbar riga ce Milk color, Rafeeq a kusa dashi wanda ke sanye da Farar Shadda da ta sha Bakkin Aiki harda Baban riga, sai Maalesh da ya sa Skye blue Shadda shima da Babbar rigar shi, Wani farinciki ya ziyarci Zuciyar Daddy, ya dade be ga tilon danshi cikin wannan farin ciki ba, Dukda fuskar sa Murtuke yake, kallo daya zaka mai kasan yana cikin farinciki Mara Misaltuwa, Tafiya sukeyi cike da Tak'ama da Isa, suka je har gaba suka samu wuri suka Zauna bayan Zaid ya nemi Afuwan mutane na Latti da sukayi.
Liman ya fara da cewa Ina Waliyyan Maauratan? Su matso gaba, Uncle Zaid da wani d'an k'anin Nene suka matsa Gaba, Aka buk'aci Sadaki, Zaid ya sa Hannu cikin Aljihu ya ciro bandir din 1000, dubu Dari, bayan anyi yanda Addinin musulunci ta tanada, nana Dubannin Mutane suka Shaida Auren RAFEEQ HABIB LEMA da Amaryar sa NASIBA MUHAMMAD Bisa Sadaki naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba, Rafeeq ya ji hawaye a kuncinshi da sauri ya goge ya zaro Wayarshi tare da tura mata Text, nan aka shiga gaigaisawa ana taya juna Murna, Rafeeq ya ji dadin ganin Old Friends dinshi a gun Daurin Aure, na University dana Secindary, yasan aikin Maalesh ne, daga nan suka zarce KATSINA MOTEL inda zaayi Reception.
Tun Safe suka dawo gidan Nene, Gida ya cika Makil, tun wurin 8 aka fara zuwa yinin biki, Nene tayi kyau abunta cikin shiga ta Lifaya, sai wani kankanba take ma kawayenta tsofi irin ita jikarta ta dangwalo arziki, ana ta ba ciki hakkinsa, Abinci sai wanda ka zaba, Amare na rawan kidin kwarya, Nene na tayasu, Nene ta kalli Miemee tace "Miemee Yar gayu je ki hankado min Seebi yanzu" da sauri Miemee tayi hanyar Dakin.
Usheey ta mik'o mata Wayar ta, don ta ji kamar Alamun shigowar Sak'o, tana duba wayar ta ga BABY ne, da sauri ta bude Sak'on *"YOU ARE MINE"* abunda ke ciki sak'on kenan, wani Farinciki ya ziyar ce ta a hankali ta zame ta yi Sujjudushukur don nuna Godiar ta. Usheey tace "yadai? Cikin Sanyin jiki tace "An daura" Miemee ta shigo k'uryar tace "wai me kukeyi ne? Nene tace kar ku bari ta iske ku Wallahi, ku fito bak'i nata zuwa" Usheey tace "Sorry Sallah mukayi" Miemee tace donAllah ji an daura miki Dankwali kin kwance" Seebi tace "Alwala fa nayi" Miemee ta harareta ta hau gyara mata dankwalin kanta, suka fita Masu kidan kwarya na ganinsu suka fara wak'ar *giringibishi*.
Yinin Bikin Nene yayi Armashi Har wurin bayan Laasar ba a bar zuwa ba, anan ne aka kira Nene aka sanar da ita 'yan daukar Amarya zasu zo, Nene ta lek'a chan k'urya ta ga Seebi rakube tana Kuka kamar ranta zai fita, zuviyar Nene ta karaya, ta dai dake tace "Ke kika ce kina so, da ba kice kina so ba da ba a baki dunkum ba, to kuka na me? Tashi muje inkai ki gun Babanki ya miki fada da Nasiha" Aiko Seebi ta sake fashewa da kuka, ta ba Nene tausayi sosai, nan ta samu ta shiga lallabata har ta ja ta sukayi Parlo inda Abbii da Kawu Magaji ke zaune, Nene ta aika aka kira mata Ummi, aka gurfanar da Seebi gaban Abbi, Nene tace "to Mahammadu ga Seebi nan kai mata fada" Abii yayi hamdala yace "Toh Seebin Nene Allah yayi yau na ga Aurenki, Seebi, duk me hankali zai yi duba ga lamarin Aurenki, kin shiga rayuwarsu a Matsayin wata Haske ba tare da ke kanki kin sani ba, Haduwarki da Rafeeq har zuwa yau itace K'addaraki, abubuwan da kikayi domin shi, shine Jarabawarki, ki kasance me boye sirrin Mijinki, Abubuwan da suka faru, na dadi da na rashin Dadi, hakan ya zama ishara gareki,, ina Miki gargadi da ki rike gaskia da Amana, kin taimaki Mutanen nan, suma sun taimake ki, Suna sonki Sosai, Kar ki zama butulu, ki kaunce su da zuciya daya, na sanki da hakuri, ki kara a kan wanda na sanki dashi•••• Nasiha me ratsa jiki Abii ta cigaba da yi ma 'yarsa, tana kuka yanayi, Ummi nayi, sai da ya gama Nene ta sa Ummi daura mata kan na Abii, Kawu Magaji ya mik'a Ma Seebi Sadakin ta yace "ga Hakkinki" Seebi kasa amsa tayi sai dai Nene ta sa hannu ta amsa, suna cikin haka sai ga yan daukar Amarya sunzo, Suna Guda sosai, dangin Mami da dangin su Daddy yan Azare ne sai Mom din Maalesh, Bayan an gama yan surutai aka basu Amarya Nene ta yana Lifayar ta zata bi bayansu, wata abokiyar wasanta tace "Kai Aminene ba dai binsu zakiyi ba?, ke fa ce Uwar Amarya" Nene tace "Yo saboda me? Ai wallahi kafata kafar Seebi in gaya miki" ta bi bayansu da sauri.
Gidan Habib Lema akayi Da Seebi, dama chan zata fara Zama cewar Uncle Zaid saboda dalilin shi daga shi sai Rafeeq suka sani, sun dai ce ma Mami tun Kafin ayi Bikin nan zata zauna, saboda haka nan akayi da Amarya, ba abunda ke tashi sai Guda, Sama akayi da ita aka kaita Dakin Mami, kan tsakiyar Gadon aka ajiyeta, inda take kuka a Hankali.
***********************
"Sweet Zee ka huta kaji? Bana so wata ta ganka ta lik'e maka a Dinner dinnan a Son" Cewar Aunty Zee da ke kwance rigingine tana waya da Mijinta, Uncle Zaid yayi dariya yace "Cute Zee ki kwantar da hankalin ki, ba wacce zata ganni, kowa ya san nima fa Ango ne, dont worry kinji Cute Zee? I'll keep myself for you alone, I love you so much, Gobe First thing in the Morning zan taho, i cant wait to set my eyes on you" Murmushi me sanyi tayi kalamanshi sun kwantar mata da Hankali, Sallama sukayi bayan ya shaida mata zai dinga tiro mata Pictures da Videos ta Whatsapp.
"Beautiful Akwai Sauran Gate Pass a gurinki" Miemee tace "Handsome Wallahi duk sun k'are, Wasu Friends din Seebi 'yan Zauren Biebee Isa da Miemee Bee Novels group sukazo kuma duk na rabe musu Gate Pass din" "and kuma dukkansu sai da kika basu?" Miemee tace "duka Wallahi,Friends din Amarya me, daga wurare daban daban, garuruwansu nesa da na kusa suka zo, they mean alot to Seebi, kaga dole a sama musu gate pass" "Alright ba Matsala, barin je in shirya Ango, Please ki cema Friends dinku su shirya, Immediately Isha zaa zo ayi kwasa daya a tafi, kinsan abun ba African Time, saboda harda su Daddy da Friends dinshi, so Everything has to be on time" Miemee tace "Alright Handsome baka da Matsala, ana chan ana Makeup din Amaryar, mu kuma a shirye muke ku muke jira" "Alright bae, i love u". Me too bye.

A kan idon Nene Mami ta ba Ummin Seebi gate pass da yawa tace "gashi ke da mutanen ki" Ummi tace yanzu sai munje?" Mami tace "Ehmana, duk zaaje har Alhaji da mutanen shi zasu, kinga kema harda Abii dinsu zaki" sukayi daria duka.
'Toh wadannan takardun da ake rabawa na meye?" Mami da Ummi suka juya ta inda sukaji Muryar Nene, Nene ta k'araso tace "ko bakuji ba?" Mami tace "Gate Pass ne" Nene ta yatsuna fuska tace "meye haka nan?" Mami tace "Kati ne Nene, na shiga wurin Dinner, idan baka nuna ba, ba zaa barka ka shiga ba" Nene tace "ina wai?" Mami tace "Dinner kamar Walima aka hada, zaa hadu duka a ci Abincin Dare don murnan Biki" Nene tace "Tab, Munafurci ya sa ba a a gaya min ba? Ya ake abu ne ba a sanar min?" Ummi tace kiyi hakuri, dama katittikar mu ne nanz shine yanzu zan kai gida a shirya a tafi" Nene ta harari surukar ta tace "bani su nan" da sauri Ummi ta mik'a mata IV's din duka jiki na rawa, Nene ta zaro daya ta mik'a mata, tace "muje gidan, zan ba wamda ya dace yaje don kar muje su ba mu kunya, sai wanda yayi wankan Suwaga(Swagger) zaije" duk sukayi Daria, Mami tace "to Nene ku je ku shirya da anyi Sallahr Ishai zaa tafi, Nene tace bari mu je da sauri suka fita ita da Surikarta Ummi.
Mami kuma ta wuce Parlorn Daddy inda aka ma Nasiba Makeup, Sanye take da Turquoise Blue Wedding gown, da dogo Veil dinshi wanda Houseofkaya suka dinka mata, Rigar ta hadu iya haduwa, Aneesa ce ke koya ma Nasiba yanda zatayi tafia gun dinner din, Mami ta shigo da Sallama, Nasiba tayi saurin Sadda kai, Mami ta isa gunta ta rungume Nasiba tace "MashaAllah Seebi kinyi kyau sosai"Murmushi kawai tayi, Wayar Mami yayi k'ara, ta dauka " Yeah Okay, we are ready as well" Mami ta kalli Lynaz me Makeup tace "Thank you Lynaz, you've transformed my daughter" Lynaz tace "thats my job maam, we bring out the beauty in you" Mami tayi Murmushi suka tarkata kayansu Aneesa tace "i'll show you the way out" Mami tace daga nan ki kira min Wayr Maalesh, Rafeeq yazo ga EventsUnlimited(masu hoto) nan sunzo, yazo ayi Post wedding pictures kafin a tafi dinner din, Aneesa tace "Ok Mami" Mami ta tsura ma Nasiba kyau, duk kunya ya kamata ya sadda kanta k'asa, Mami ta kamo hannunta tace "Nasiba Wallahi ina sonki ina jinki kamar Rafee'ah, kinyi kyau sosai, Allah ya Albarkaci Rayuwanku duka" a hankali ta amsa da "Amin".
Ta k'ofar baya aka shigo da Masu hotunan, don kar a dauki hankalin mutane, aka bi dasu ta baya suka hau sama Parlorn Daddy. Bayan gaishe gaishe suka hada kayan hotunan su. Mami ta fita waje don kiran Rafeeq ko Maalesh ta ko ci Sa'a wayar Rafeeq ta shiga, " "Hello Feeq kana ina? Mam ina tsakar gida, Oya ka shigo ciki ka hayo Sama, ga Eventsunlimited nan, kazo ayi Postwedding pitures, ya marairaice kamae zaiyi kuka, Mami ta ya zan shigo, Mutane da yawa, tace "ta baya fa zaka shigo" "ni Mami i cant" tace "Ina Maalesh ya rako ka mana?" Mam Lesh yaje tattaro Friends dina yanda zasu a kwashe mutane a tafi at once" tace "Alright gani nan zuwa in taho da kai".
Ta sauka kasa ta ga Rafeeq, sanye yake da shiga irinta Nasiba, manya kanya Turquoise Blue ga hularsa yayi kyau fiye da tunanin me tunani ga wani k'amshi yana zubawa, Mami ta rungume shi tare da mai kiss a kumatu, tace " Yaro na ya girma " Sake rungumeta yayi ta ja hannunshi har Sama ta sada shi da Parlorn Daddy ta turash ciki. Sandarewa yayi da ya hango Sanyin idaniyar shi daga

Please Login or Register in order to submit comment