Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

i'm eager to hear, nace idan kin dawo sai ta sake baki labarin"
Seebi tace " I am sorry Miemee Wallahi ba haka bane, abunda Usheey ta fada gaskia ne, Wallahi i love you both equally, kiyi hakuri please don't think otherwise" Miemee ta kalli bestfriends dinta, ta amince ba k'arya suke mata ba, don ta yarda dasu tayi murmushi tace "Group Hug" suka rungune juna su 3. Nasiba ta sa hannu cikin jakkarta ta ciro wayarta Iphone Ta daga musu sama a tare sukace "Nooo way" tace "Yes wayy" Miemee ta amsa tana Omg, this is real Wallahi Iphone dince" suka ta Daria, Seebi tace " da kayan jikina da wayar nan, Uncle Zaid ya bani su" Miemee tace "Uncle Zaid?" Seebi tayi daria tace "wannan da kika ma lak'abi da Azababbe, shine wannan da kika zauna gaban motarshi randa mukayi lectures 4-6, randa mukayi trekking har bakin gate, wanda kikace ya hadu Sosai, wanda ya fara kaiki gida Kafin ya kaimu namu gidan" Miemee ta katse da murna tace "ya isa Seebi, na ganeshi wallahi ko ba me waya ta AUX ba? Kuma shine ya kawo ki School? Babe whata are you hiding? Ki fada mana Please" tayi daria tace "to kunji kunji......" ta gaya musu komai tsakaninta da Lema Family Amma banda Mafarkanta. Sun tausaya ma Rafeeq matuk'a amma Miemee ta ta6e baki, tace "Poor R-Lema, He's lost, but thats no reason da zai dinga treating mutane asif they are trash or something" Seebi ta Usheey suka hada baki sukace "kina da Damuwaaaaa" daria sukayi duka, Usheey tace "Seebi, gaya min kinason Uncle Zaid ko?" tace "Wallahi i dont know nidai nasan kawai ina ganin girman shi" Miemee tace "Shegs kina so,lemme lecture you on how to keep a boyfriend" Seebi tayi daria ta dauki jikarta tace ku tashi mu tafi gida, kunsa munyi missing lectures ba gaira ba dalili, saura 15mins a gama kun ga kuwa zuwan mu be da amfani" Usheey tace "ba Sallah ba salati, labarin ne kamar kar ya k'are kamar a film, saukin ma dai munci Abinci" Miemee tace mu biya Central Mosque muyi Sallah, in munci Sa'a mu samu bus muna fitowa" haka Miemee ta biya musu Plate dinsu 600duka don cikin su 3, ta fi su hali, suka bar CAF.
********
"Lahh ga motar R-Lema da alamu yana cikin Massalacin nan" Miemee tace sai me? Ga bus nan kuzo mu shiga kafin a ciketa, Seebi tace "Aa, mu jira ya fito, kinsan ko ganin mu yayi anan bazai barmu ba, gwara mu jirashi" Usheey, tace "Ni wallahi nagaji kafin mu isa Bus ta jigata mu" Miemee tace banson raini wallahi, duk me ya mana yau kuka ja mana, Nasiba tayi daria tace naji na yarda, wurin motar suka tsaya, sai ko gashi kamar an jefo shi yana tafiar nan nashi cikin isa, kallo daya ya musu ya dauke kai, a ranshi yace "Wannan ta kile yau ita ne da Veil, tayi kyau" chan kuma yayi tsaki yace "sha its none of my Bussiness" ya bude motarshi ya zauna, shi be tafi ba shi be basu damar shiga ba, Seebi tayi Jihadi tace mu shiga, suka bude suka shiga, tace "Hamma ina wuni" kamar ba zai amsa ba yace "lafiya" Usheey tace Ina wuni yace "Sannu fah" Miemee kuwa ta dauke kai duk abun Miemee bata san Raini da wulakanci, bata fiye hakuri ba(waya ga Diyar Aminene Mamman) Shi be ma lura da ita ba ya ja motarshi ya bar School, duk suka kasa magana sai gudu yake tayi dasu, ya bi ta Ringroad, kamar ya rufe bakin su duk sukayi shiru, sai gasu sun bullo ta Salamah, har ya wuce k'ofar Gidan Nene zai yi kwanar Gidan Lema Nasiba tayi saurin cewa "Hamma zamu sauka a nan" "Oops na manta" ta k'irkiro murmushi tace "bakomai" yayi parking suka fita, Miemee ta cika tayi pam, tace "Wallahi Gayen nan dan rainin hankali ne, abun nashi wallahi harda Iskanci" Usheey tayi daria tace mu ai munzo gida, muje ki samu Napep, Seebi tace "ai tunda tazo nan sai ta shiga ta gaida Nene, kuma taga Daughter na" suka sa Shewa, suka nufa Gidan Nene.
Nene na ta dirka ma Ayman Kokon da rage dazun da safe, tana ganin Seebi ta mik'e ta mata Oyoyo, duk sai ta burgesu, Seebi ta daga ta sama Oyoyo my baby" Ahh su Miemee 'yar gayu, da Usheshe, sannun ku, shigo ku zauna, A'ah Nene mu gaisa wucewa ma dai zamuyi, nan suka gaisa, sukayi Ayman tazo gunsu ta mak'e ta lafe gun Seebi, Seebi tace Nene bari in rakasu, sai da suka tsaida ma Miemee Napep, sannan ta raka Usheey gida kafin ta gangaro gida.
****
Daga Nesa Aneesa ta hango Nasiba rungume da baby, tace "Ohh dama nan Unguwar kike? Matsiyaciya aiko zaki ci Ubanki, ta dinga bin bayanta a hankali a motar ta, har taga Nasiba ta shiga wani gida, Aneesa tace a ranta ban minti 10 yanzu zan dawo gareki" kuma in dai idonta be gaya mata k'arya ba, to tabbas diyar Zaid ce a hannun Seebi, tace "Bala'in chan" Nasiba na shiga ta zauna kusa da Nene, ta na tambayarta abunda Ayman taci, Nene tace "Baban ta be dade da maido ta ba, yanzu taga ina shan kwakwo naga ta na kallo na, ko da na bata sha take tayi, mik'ota ta shanye kingin" Kafin Nasiba tace wani abu taji Sallamar shi, da Mamaki ta dago ta kalle shi, tace "Hamma" be kula ta ba ya kalli Nene da ke dirka ma Ayman Koko yayi cukun cukun da fuska, ya danyi tsaki yace "Neh-neh, meye wannan take sha?" ta kalleshi tace "Ahh Neh-neh Naji kace? Wai kai in tambayeka komai sai ka fade shi da turanci ne? Nenen ma sai ka fade Shi da boko? To nidai ba sunana NehNeh ba, in ka koyi kiran sunana Sai kazo in baka Amsa" yayi dan guntun tsaki tace "Tsukakke" ya kalli Nasiba yace "Meye take bata?" tayi murmushi tace "Kokko Ne" "shine ya bata mata baki haka?" ya sake dan guntun tsakin yace "Zanci Indomie and Egg" jiki na rawa tace "Bari in dafa maka" tayi saurin shiga kicin ya zauna kan kujera yana mik'a ma Ayman hannu yana cewa "Come here Angel, hamma is here" Ayman ta mak'e kafada alamun Aa, aiko Nene ta fashe da daria, tana ma R-Lema gwalo, daria ta bashi, gudun kar yayi daria gaban Nene ya sa shi dauke kai.
******
Ta dibar ma Ayman a dan bowl ta zuba ma Rafeeq a plate ta tsiyayo mai Ruwanshi ta kawo mai, "Thanks" yace yace "Nene in zubo miki? nene tace ni rabani da Indonie dinnan, zan shi waina na nan anjima, Nasiba ta zauna tana ci tana ba Ayman A baki,
Bam Sukaji an bugo k'ofa da k'arfi, Nene tace "oh Allah, Iska ne haka? Allah na tuba nidai kar k'ofata ta 6alle Kafin wani ya sake magana sai ga Saude ta shigo gidan tana ma gidan kallon wulakanci, ta chakare dankwali gaban goshi, hannunta kan k'ugu, Meema da Aneesa na bin bayanta, ashe Aneesa taje ta gaya musu k'arya da gaskia, Nene tayi saurin mik'ewa shi ko Rafeeq tunda ya musu kallo daya ya dauke kai ya cigaba da cin Abincin shi, Nasiba tuni ta fara kyarma, Aneesa tace "Ya Rafeeq me kakeyi a nan?" kallo bata ishe shi ba, Saude ta kalli Nene galala tace ke tsohuwa, nazo in ja ma wannan kilakin kunne, amma tunda gaki to gwara in miki sai ki ja mata kunnen da kyau, Wannan karamar kilakin na bibiyar Mijina, tana bibiyar k'anin mijina, Kuma tana bibiyar dan mijina don ga zahiri nan, ta nuna Rafeeq, har ta isa ta daga hannu ta mari diyata? Ta sa k'awayenta su mata duka? Wannan 'yar iskar har ta isa? Meema ta chafe "ni ai kamar na so in gane wannan tsohuwar, Anee ba ita bace ta taba tsaida mu a hanya ta bamu waya ko mu kira mata Uban wa? Matsiyaciya, Asiri suke ma mutane dube Rafeeq da be ko kallon pampon gida ya zage ya bude ciki yana cin Abinci, dubi kayan jikin ta komi irin na Anee, Asiri suka ma UncleZee ya siyo mata irin shi, banzaye matsafa kawai. Har yanzu jikin Seebi be bar rawa ba, Nene ko sai dai ta bi wannan da kallo ta bi wannan da ido, sai da ta gama karance su tsaf. "Ke Aneesa dauko Ayman mu ta fi gida, idan na k'ara minti 1 anan zan iya sik'ewa don nan ko gidan Karena Albarka" Aneesa ta dauki Ayman, Ayman ta 6are baki, sai a sannan Rafeeq ya dago, da rinannun Idanunshi yace "Let her Go" be san meyasa ya kasa tanka su Saude da suke cin Zarafin su Nene ba, "Saboda mene Rafeeq?, mune fa dolen ku, baku da kowa, mune yanuwanku ba su ba, You are not related by any chance" cikin tsawa yace "I said let her go" da sauri Aneesa ta direta, ta tattaka ta nufa Nasiba ita kuwa ta kasa daukarta, don gudun abunda zai dawo, Rafeeq yace "duk abunda zakuyi ko zakuce kuce, but dont you dare touch this Soul" Saude ta kalle su ta watsar tace "ku taho mu tafi, tsayuwan mu nan is useless, ke dai Na gaya miki ki jama jikar ki ne ko diyarki kunne, in ko ba haka ba to sai zaman Katsina ya gagareki"
Nene tayi murmushi tace "nidai tambaya daya zan muku, donAllah kune kuka taran ma Nasiba jiya da daddare?" Aneesa cike da Rashin kunya tace "Eh mune, yanzu ma ba ita ba har ke sai mu taran mawa" Nene tayi daria tace "Alhamdulilah MashaAllah dama amsar da nike son ji kenan" ta kwance dankwalin kanta ta daura a kai, ta kalli Nasiba tace ke dauki Aymana ku shige daki kar ki sake ki fito, Nasiba ta san Nene ba Alkhairi zatyi ba tace "Nene DonAllah--" Nene tayi saurin katse ta da cewa "dan Ubanki ku shige daki nace ko, zaki dauketa ko sai na fara da ke? Jiki na rawa ta dauki Ayman ta shige daki, Meema tace " What is she trying to do" Aneesa tace 3 against 1" sukayi daria duka.Nene ta k'ulu ga turanci sun yi, sun k'ara da6awa ta kalli Saude tace " Uwarki ce Ogan kilakai, cikin dakin kwarto ta mutu, ke kuma randa na baki waya nace ki kira min, ai baki tsaya kinji wanda nace ki kiramin ba, Ubanki nake so ki kiramin a lokacin, cikin ku wa ya fara taba fatar Seebi? Saude da ta gama harzuk'a da zagin da tsohuwar nan ke musu tace "Nice nan" bata ankara ba taji Nene ta buggan mata Baki, bata ankara ba taji Alamun gishiri gishiri a baki Aneesa tace "Laaaah Jini? Kika fidar ma Mom dina Jini? Tayo kan Nene gadan gadan, nene ta kwashe ta da Mari, Marin da ta ga Stars na walkiya, tace "ga Marin Da kika ma Nasiba,Yo ni Allah na tuba Ai Ba Uban da ya isa ya sa Zaman Katsina ta gagareni, naci uwarki in baki hana zaman katsina gagarata ba" Rafeeq yayi murmushi yace "Interesting! Thats what i'm talking about" ya kwashe plate da cup dinshi ya kai kitchen, ya fito yana daria yace dasu "You all can leave while you still can, this the only opportunity you have, is now or never" Saude ta dago ta kalleshi cikin masifa tace "I never back down from a fight, this woman will regret doing this to us" Rafeeq yayi murmushin mugunta yace "in that case, i'll sit back and Watch" Nene tace "Uban me kake ce musu? Yayi Daria yace "ce musu nayi su fita shine tace wai ba zasu fita ba sai sun koya miki hankali, wani abu ma da tace ba zan iya fada miki ba saboda yayi nauyi da yawa" Nene tace "kayi wa Allah ka gaya min? Girgiza kai yayi, Nasiba daga ciki take cewa "Hamma stop, its not funny" Nene kuwa cewa tayi ''in kika fito sai kinci ubanki Nasiba" ta damk'o wuyan Saude ta chusa ta a hammata, ta matse, Meema tayo kanta,Nene ta wurga Saude kamar kayan wanki Saude ta buge da bango, Nene ta ci nasarar damk'o gashin dokin Meema ta dinga ja, Meema sai ihu takeyi, Nene ba ta bar Meema ba sai da tsinka kitso daya, kan Meema sai jini itama ta yadata k'asa, ta cicibo Aneesa da har yanzu bata gama kukan marin da ta sha ba, Nene ta buge bakinta tace ke me bakin rashin kunya ko? Ni kikeyi wa turanci? ta waiga ta hangotayizar da ta dauko jiya don dukkan Rafeeq, ta waiga taga Rafeeq na darian mugunta harda rik'e ciki, tace "kai dunkum mik'on Chazar chan" da sauri ya dauko ya mik'o mata, ta dinga shauda ma Aneesa, Aneesa na ta ihu, Saude ta taso don cetar diyarta ita ma bata tsira ba, Nene ta hau shauda mata itama, Meema kuwa lafe wa tayi chan baya, dafe da kanta, Saude Ihu, Aneesa Ihu, Rafeeq Daria harda Hawaye, jin Alamun zaa shigo yasa tace "kai dunkum maza kaje ka rufo gidan nan" Rafeeq harda tuntube gun fita don tsabar dariya, nan suka ci Karo da Zaid, cikin tashin hankali yace "Feeq ihun me nakeji haka?" Rafeeq daria ya hana shi magana sai nuna baya yake tayi, Zaid ya shiga da sauri, ganin Nene na laftar Saude, Aneesa da Meema kamar Allah ya aikota ya sa shi cewa "SubhanAllah, Nene me zan gani haka?" ba ta fasa laftar su ba tace "Wallahi Zaidu bawan Allah ka matso gurin nan sai na Lafta maka kaima".
(Toufa Readers, shin Hankalin Nene Daya?)

_Bibilicious Biebee,_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣0⃣

Zaid ya daga hannun shi alamun ban hak'uri, yace "Nenen mu DonAllah kiyi hak'uri" Inaaa sam Nene Hankalin ta yayi nisa ta ba ta jin abun da Zaid ke cewa, haka ta cigaba da kilar su, Zaid yayi saurin cewa "Nene kin ta6a cewa idan ina son wani abu a gunki, kar inya shakkan sanar dake, ko menene zakiyi min shi, in har befi karfin ki ba, Nene wannan ne abu na farko da na fara tambayanki Nene DonAllah, ki bar su haka, kiyi hakuri, sun ladabtu, na tabbatar ko me suka miki sun gane kurensu" Kallon Zaid tayi tana nazarin shi, chan kuma sai ta yada Chazar tace "Wallahi, sunci darajar ka, kai kadai ka isa ka hanani wlh, don ko Mamman ya dawo duniya yanzu sai mun kai ruwa rana kafin zan hakura wallahi" Zaid yayi murmushi yace "Nagode Sosai" Saude ta tashi tana kakkabe jikinta, Aneesa da Meema ba su bar gurnanin kuka ba Saude ta tuna cewa ba abunda Tsofin mutane ke tsoro kamar Yan sanda, tace "Wallahi Yan sanda zan kawo miki, sai kinyi nadamar ta6a Lafiyar jikin mu" aiko Nene ta tunzura tace "YanSanda? Naciii uwar Yan sanda, naci uwar hukumar jami'an tsaro dukkansu, Kinci uwarki idan baki dauko mun 'yan sanda ba, ke bari ma in k'ara laftar ku yanda zaki dauko mun su da hujja" ai ko Nene ta wawuro chazar ta, haba zo kuga relay tsakanin Miemee Saude da Aneesa, har suna tura junansu ko wannen su na rigerigen fita daga gidan Nene, a wannan karon ba Rafeeq ba hatta Zaid sai da ya dara.
Nene tace "kina iya fitowa me tsoro kamar farar kura" Simi simi Seebi ta fito daga dakin rungume da Ayman da ta ci kuka ya gaji, Rafeeq yayi k'okarin amsarta Ayman tak'i yarda sai dai Babanta ya amsheta ya sakata kan kafada, don yau taga tashin hankalin da bata taba ganin irinshi ba.

Zaid ya nisa yace "Wai me ya faru ne? Me ya kawo su Meema gidan nan?" Nene tayi charap kamar jira take ta shiga karanto ma Zaid abubuwan da suka faru tun bayan shigowar su Aneesa, ran Zaid ya 6aci matuk'a sai ya fi ganin laifin Rafeeq cikin 6acin rai yace da Rafeeq "why didnt you stop them da suka fara zagin Nene? Meyasa baka hana su ba? Kamar bazai amsa shi ba, sai dai ya daure yace "Saboda i know she'd handle them in her ways, which she did" ran Zaid ya 6aci zai sake magana Rafeeq yayi saurin cewa "Look Uncle i tried to warn them, i even told them to leave, but they didnt want to listen so i let them be, ko ba haka ba Neh-neh?" kamar ta san me ake cewa tace "Hakane Zaidu Bawan Allah" nan Zaid ya dai bata hak'uri ya ba Nasiba Hakuri, ya kalli Rafeeq ya galla mai harara shi kuwa ya dauke ido yayi kamar be ganshi ba, Nene tace "ka bar hararan shi, ai ni yau Dunkum ya burgeni, kasan shi ya mik'o min Chazar, kuma ya fassara min abunda suka ce" Rafeeq yayi dan guntun tsaki kamar ba shi ya gama daria dazun ba, Nene tace "Su dunkum ashe ana ganin hak'oran ka? Wato kai mugun abu ne abokinka ko? Sai kaga abun mugunta kake daria, ai da nasani da na shafda maka a gadon baya sai kayi darian da kyau" Zaid da Seebi sukayi daria shi kuma ya daure fuska.

Saude ta ja Majina tace "Sai na koya ma tsohuwar nan hankali, sai tayi nadamar abun da ta mana, sai zaman katsina ya gagareta, Wallahi sai ta yaba ma Aya zakinta" Meema na matsar k'walla tace "Wallahi Sis, in ke ba kiyi maganinsu ba ni sai nayi, wallahi zan iya kashe su da hannuna, duk tsanar da na ma tsohuwar nan, nafi tsanar Jikarta, na tsanesu, tsanar da ban ta6a ma kowa ba" Aneesa cikin kuka tace "Mommy, make them Suffer" Saude tayi darian mugunta tace "Ku zuba min ido" ta zaro wayarta ta lalubo Numbern tsohon Amininta *Mak'ale*.
*************
K'arfe 9:30am ta fito don zuwa makaranta, lectures take dashi karfe 11:00am zata fita da wuri ne don ta samu Abun hawa ta isa da wuri, don tafiar kusan minti 45 ne, sauri takeyi bayan ta gama shirya Ayman tana bacci tace da Nene "Uncle Zaid zai zo ya dauke Ayman, zai kaita gidan Kakanin su Rafeeq (Baba TJ) ta musu yini, in kuma ta yarda ta kwana toh, Nene tace "to shikenan sai yazo kema Allah ya dawo dake Lafiya" har sunyi Sallama Nene tace ba zaki tsaya kici wani abun ba? tace "da naje Makaranta zan siya Panke, na fiso in isa da wuri" ta mata adduar tsari ta fita daga gidan.
Kamar daga sama taji horn dinshi ta waigo da sauri ta sakar mai murmushinta, shi kuma kamar ya ga wani kashi ya wani tubune fuska tare ds kawar da kai, bude k'ofa tayi ta shiga, "Hamma Rafeeq Good Morning" tsaki yayi yace "Fine" ya dauke kai, tunda suka hau hanya ba me ma danuwanshi magana, har suka iso makaranta, anan ne tace ya kaita ta bayan Science Theatre, kamar ba zai yi kwanan ba ya sha kwanar da k'arfi har tana bugewa da window, daidai Theatre suka tsaya, ba mutane a gurin, sai jefi jefi ake ganin tsiraran mutane. A ranta tace "Ya Illahi! Gani gareka" me makon ta fita sai ta gyara zamanta ta sa hannu cikin jakkarta ta ciro zoben da Mami ta bata, ta sa a yatsar ta na kusa da k'arami, ta gefen ido ya ke kallon duk abunda takeyi, ta wutsiyar ido ya k'are ma Zoben kallo, wani abu ya ji game da zoben, da sauri ya juyo gareta inda take wasa da yatsunta tana juya zoben a yatsar ta, Mukut! Ya hadiye miyau, ya kalli yatsan hannun shi yaga Irin Zoben ne, ya sake kallon na hannunta, sai da ta lura da ya tantance kafin ta bude k'ofar tace "Hamma sai anjima nagode" har ta sa kai zata fita ta tsinkayi muryanshi inda yayi guntun tsaki yace "Nace ba?" murmushi tayi kafin ta dakata tace "ya kace?"
Sai kuma yayi nadamar tsaidata to me zai ce mata? Zuciyar shi ta tunzura shi yace "Ina kika samo zoben hannunki? Anzo gurin tace " Auu wannan Zoben yatsa ta? A wonderful woman, with a beautiful heart gave it to me, kasan mene? Ta bani tarihin Zoben, wai her Beloved Son gave it to her ranar Zagayowan haihuwarta randa ta shiga shekaru 40, wai ashe musamman ya je Dubai ya sa akayi mishi Zobe guda biyu, ya kawo mata as her birthday gift, ya sa nashi ya sa mata nata yace da ita '"Mamina, this is my love for you, ya nuna mata na hannun shi yace this is the twin of your ring, even if we are far from eachother, this ring is linked to our Hearts"' Hamma na DonAllah basu burgeka ba? Ya dago ya kalleta, ta kasa gane yanayin da yake ciki, idanun nan sun kada sunyi Jazurrrr, ta firgita har ranta amma sai ta dake ta na karfafa ma kanta guiwa tace "Laaaahhh Hamma kalli Zoben hannunka, kamar nawa, duba ka gani, iri daya ne Wallahi, How is that even possible? A lokacin kuma a ranshi yace "She met Mami" tsigar jijiyoyin jikin shi suka tashi saboda tashin hankali" bata fasa magana ba tace kaima Zoben ka na da dan biyu? Akwai wanda ka ba Zoben ka? K'ila kaima Maminka ka ba" da k'arfi yace "Shutup" a tsorace ta kalleshi tace "Hamma na, are you okay? Did i said something wrong?" cike da nutsuwa yace "Get Out" Tsoro ya gama cikata, ba ta taba ganin ya fusata haka ba, muryar shi ta sae ji cikin karaji ido rufe "I said get out" jiki na rawa ta dauki jakkanta ta bude k'ofa Zata fita sai kuma ta fasa, ta dawo ta kulle k'ofar, jin an kulle kofa ya sa shi bude ido a hankali, ganin ta zaune ya bashi Mamaki daure fuska yayi sosai yace "are you deaf? Dont you understand English again? Okay nace ki fita, ki fita ki Barmin Mota na Kai tsaye tace "bazan fita ba, you have to listen to what i am about to say to you, idan ka ga dama kayi aiki dashi idan ka ga dama ka watsar yabi ta bayan kunne, Rayuwa daya ce, you only get to live once, idan yau ka fadi ka mutu ka san makomar ka? Ni bansan kusancin ka da Ubangijin ka ba, amma yau ka mutu ina kyautata zaton kai dan wuta ne, saboda Me? Saboda kana Fushi da Mahaifiyar ka, baka neman Albarkar ta, kar ka manta akwai hakkinta akan ka, Fushi, duhu, emptiness, loneliness sun cika Zuciyar ka, kai kana tunanin kai ke da kanka, you can get to do whatever you like whenever you please with No Apology, kai komai kayi daidai ne 6acin rai ya hanaka facing reality, abu is very clear amma Zuciyarka ta mutu, ko ince ka kashe Zuciyar ka da kanka, alhali you are a good person with a beautiful heart, amma baka so ka ga hakan, you are forcing yourself to be mean, amma kasan Zuciyarka kai mutumin kirki ne, ga ka da tausayi, da kula, please realize that side of you, da tsawa ya katse ta cikin daga murya yace "Nooo, you think you know me? You know Nothing about me, nkw get out of the Damn Car" itama cikin muryar kuka take cewa "Nace maka ba inda zani, i am not done talking to you, if you dont want to realise your good side, then i'll make you realise them, lokacin da aka kai Nene Asibiti, mesa ka ke kula damu? Abinci safe rana da dare? Me sa kake kaini makaranta? Zuciyar ka me kyau ce amma ka danneta kai a dole ba ka damu da kowa ba, ko kuma ba wannan ba, ka tuna randa kace in fitar maka daga mota, randa zaka kawo ni Makaranta? Randa nake ta maka tsaki? Ka direni a tsakiyar daji? Na san ka tuna, ka tafi me ya dawo da kai? You could'nt leave me there because you care" da sauri yace "No i dont, i was only saving you from your Stupidity,

Please Login or Register in order to submit comment